Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

arms tayi tana
fadin"Yeah ki daina Insulting nashi because I love him……"

"Lallae Fadila ……"cewar hajiyar tare da mikewa ta bar falon ……Fitowa ta kuma
yi rataye da gyalenta da gani kasan tsofa yayi gardama gurin "hajiya sae kuma
ina?cewar fadila da ta bita da kallon mamaki

Harara ta sakar mata tana fadin "Gurin tsalli zani na kai mashi wannan number
tun kafin ki fara duka idan an zageshi ……"

"Ban gane ba Hajiyarmu……"
Gaba tayi tana fadin "idan na dawo kin gane……"

《》《》《》《》

Karfe 10:15 ya iso katsina kasancewar tun da safe ya iso ……Gabanshi ke masifar
faduwa banda addu'a babu abunda ke fita daga bakinshi , da kyar yaje gida a
bakin zaure ya iske inna sahu tana neman aike saboda duk su nana sun tafi
makaranta ……karbar Aiken yayi ya sawo mata sannan ya dawo suka gaisa sama sam
yana tambayarta "duk yaran na lafiya……" ta amsa da "Lafiya lau ……" kadan kadan
suka taba hira duk hankalinshi baya jikinshi so yake ya kira ko Maryam ce yaji
yarda suke amma ya kasa ya dauki wayar da niyyar ya kira ya fi sau biyar amma ya
kasa ……

Sassayar ajiyar zuciya ya sake lokacin da yake mikewa ,kawae ya yanke yaje ya
gaido Alhaji kila ya samu saukin radadin da zuciyarshi ke mashi ……

A Falo ya sami Aunty fateen zaune tana breakfast har kasa ya duka ya gaidata
sannan ya tambayeta ko Alhajin nanan ……

Hankalinta ta maido kanshi sannan tace "Yana wanka Abdul Maleek ka jirashi
dama ina son muyi magana da kai……"

Kanshi na kasa yace "Ina saurarenki Aunty Fatee……"

"Yauwa Abdul Maleek dama diyata Fadila ce ta dameni tana sonka kuma kaki
kulata ko ta kiraka baka dauka shine nace ta bari na maka magana naji ……"

"Ita tace maki da bakinta tana sona?ya fada tare da dagowa yana kallonta

"Ita da kanta Mana Abdul Maleek ,kuma wallahi diyata ba mummuna bace idan kana
so ma bari na kirata yanzu sae tazo ka ganta ,don tace man baka santa ba……"

Murmushi yayi mai fitar da sauti yana fadin "Am sorry to say baran iya soyayya
da macen da ta zubar da kunyarta ta ya'ya mata da Allah ya mata tace tana son
namiji……"

Shigowar Alhaji ce ta katse maganar ya mike da sauri yana mashi barka da
fitowa ,ko zama baiyi ba ya nufi hanyar Fita yana fadin "Yauwa Abdul Maleek zo
ka kaini tunda gaka kazo wallahi tun dazu Jabir ke man waya don shaf na manta
jirgin marece zasu bi na dauka sae na dare ……"

Bin bayansa yayi yana fadin "to Alhaji……" a zahiri jin sunan jabir da yayi a
bakin alhaji ya saka gabanshi yayi mummunar faduwa ……jiki a mace ya fitar da
motar suka dau hanyar fita unguwar murya Alhaji yaji yana fadin "Dutsin safe
zamuje mu dauko Safeenar Abdul Maleek sae mu samesu bakin round din dandagoro
Kano zamuje ……"

Safeena……ya fada a ranshi kasa hakuri yayi ya juya yana kallon Alhajin a
raunane yace "Wace Safeenar Alhaji ba tayi aure ba me ya kaita dutsin safe ko
acan aka ajeta……"

"Tayi aure mana Abdul Maleeku ,Bata lafiyane shine zamu kaisu kano ita da
mijin nata zasu fita india a dubata……"

Lumshe ido yayi hawaye na bin kumatunshi ya rigaya yayi failing ……da yake
Alhajin a baya yake sam bai kula da halin da Maleek din yake ba……kofar gidan
yayi parking kafin ya zagayo ya budewa Alhajin har ya rigaya ya fito ya shige
yana fadin "Shigo Abdul Maleeku……"

Girgiza kai yayi a hankali kamar Alhajin na kallonshi sannan ya kwantar da
kanshi jikin gaban motar yana numfashi a hankali……Murya Granny da yaji ta sashi
naimo natsuwarshi ya dago da kanshi yana yake……

Maryam da ya hango ya sashi juya masu baya da sauri don ya tabbata tana tare da
Safeena Kuma bayajin zai cigaba da rayuwa indae yana kallonta ……

"Dole ka juya man tunda baka da gaskia……"cewar granny dake kokarin shinfida
katuwar leda a bayan motar ……

A hankali ya juyo yana yake tare da maida kanshi kasa don har ga Allah baya
jin zai iya kallon Safeena a yanzu da ya tabbata ta mashi nisa……"Ba haka bane
granny tafiya ta kamani ……"ya fada da murmushin yake a fuskarshi

Zuciyarshi ke neman rusa mashi duk wani plan na kar ya kalleta sam ya kasa
jurewa……a hankali ya fara bin kafafuwan mutanen dake tsaye gurin har ya sauke
bisa kafar daya tabbata ta Safeena ce ……

Sae da ya lumshe idon sannan ya fara kallonta tun daga kasa har ya kai kan
kugunta da razanannan kallo ya karasa kallon fuskarta ……Lumshe idonshi yayi yar
kwallar dake makale ta fado maida idonshi yayi ksn kugunta domin ya tabbatar da
abunda ya gani ……Tabbas idan idanuwanshi ba gizo suke mashi ba uwar tulluwa ya
hango a bayan kugunta sannan ga uban kalar da zanin ya sake daga sama ……

*ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..
[9:27PM, 11/2/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU

🌹*🌹*🌹*
🌹*🌹*
🌹*

© *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* )

*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..

DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE..

3⃣0⃣

A razane ya karasa yana kallonta "Wat happen Madam?ya fada yana kallon fuskarta

Shiru ta masa tare da janye hannunta daga jikin Maryam ta shiga bayan motar……
da ita da Abba ne a baya sae maryam da ta zauna gaba ……bakin fita gari suka hadu
da family din JB da Suka yo mashi rakiya wanda har mom dinshi ciki ……Bayan sun
gama gaisawa maryam ta koma baya JB din ya zauna gaba tare da juyowa yana kallon
Safeena ba wata kunya ya kashe mata ido yana fadin "Babynah ya dae?……You'll be
ok kinji ko da munje zakiyi enjoying life dinki better than nan garin,I'll be so
caring ……"

Lumshe ido tayi tare da kwantar da kanta a kafadar Abba ba tare da tace komae
ba ……kallon maryam yayi yace "Sister ya jikin baby?

Ita kam kunya ma ya bata gaban Abban zai dinga kira masu wani baby dan
murmushi ta saki tana kallon safeena sannan tace "She's ok……"

"Good " ya fada tare da juya ya fito da wayarshi yana latsawa……Maleek kam da
kyar ya iya controlling kanshi babyn da JB ya fada ya hargitsa mashi kwalwarshi
……

Masallacin kankia zuhur ta masu Abba yace su tsaya suyi sallah tukun ……Duk
suka fita sae Safeena dake zaune ita kadae ta kwantar da kanta baya ……har Maleek
ya gama alwala amma baiga ta fito ba……

Ruwa ya diba a buta ya matsa tare da bude bayan motar "Madam ki fito kiyi
sallah……"

Wani irin kallo ta watsa mashi tare da maida idonta ta rufe ……Ajiyar zuciya ya
sake a bayyane don ko hararan madam abun so ce sannan yace "Sorry Madam na
fahimci matsalarki amma kiyi tunani abunda ke jikinki ba normal Pes bane na
ciwone kuma Allah bai yafe sallah baga mai irin wannan ciwon indae ta tabbata a
normal pes dinta bane kiyi kokari kiyi sallah tunda tana kanshi ko bakiyi ta
yanzu ba sae kin ramata……"

Dan bude ido tayi tana kallonshi idan bata manta ba malamai suna fadin an
dauke sallah ne ga macen dake jinin al'ada ba wae jinin cuta ba ……idan har jinin
ya zama na cuta to duk lokacin sallah zatayi tsarkine sannan tayi sallarta……

"Thank you……idan mun isa inda zamu zanyi maleek"ta fada a hankali

Murmushi yayi sannan ya mike ya koma yayi sallar lokacin duk sun gama suna
addu'a ne sae da ya gama tashi sannan ya dawo suka cigaba da tafiya ……

Kusan karfe 3 Suka isa airport din dan restaurant din dake gefe suka zauna
amma banda Safeena dake zaune taki fitowa ……JB ya kirashi "Kai zo nan ……"

Ko nuna yaji alamun kiran baiyi ba har dae Abbah yace "Abdul Maleeku zo
mana……"sannan ya matso tare da dukar da kai gaban Abba

"Kazo kaci abinci mana ka ja ka tsaya gefe……"ya fada tare da nuna mashi
kujeran dake gefenshi

Dukar da kai yayi yana fadin "No Abba koshi sae dae wanda zaa mikawa madam
naga bata fito ba ……"

Kallon motar Abba yayi tare da juyo da kai yana kallon Maleek din sannan yace
"Bara ta ci ba Abdul Maleek tunda zamu fito na tambayeta me take so tace man ta
koshi……"

"Abba to ko cake na kai mata ……"ya fada a hankali ……Dan murmushi Abba yayi
sannan yace "To Abdul Maleeku ka shiga ciki ka dauko mata ka kai mata idan zata
ci……"

JB yayi saurin fadin "Abba kyaleshi ba wani cake din da zata ci yanzu……"

"May be taci Jabir kasan tana da kusanci da shi sossae ya fi kowa sanin abunda
zake bukata ……Jeka Abdul Maleek ka zabar mata sae ka kai mata kaga idan zata ci
kaji ko……"cewar Abba da murmushi shinfide a fuskarshi

Eclair cake ya daukar mata da freshmilk sannan ya nufi motar da addu'ar karta
yarfa shi don yafi kowa sanin yarfin madam……

Bude motar yayi ya shiga sossae sannan ya mika mata cake din yana fadin "Madam
ga cake……"

Dan Murmushi ta saki sannan ta bude idonta tana kallon cake din ……karba tayi
tana fadin "Thanks ……"sannan ta aje bayan motar ta lumshe ido

"Please madam ki ci yanzu dan Allah ……"ya fada kasan makoshi

"Na koshi maleek"ta fada atakaice……

"Dan girman Allah madam ba dan na isa ba……" bai rufe baki ba ta dauko cake din
tare da budewa ta kai bakinta tana kallonshi ta kasa kasa ……Tunda ta fara ci ya
kafe ta da ido yana jefa mata wani irin sassanyan kallo ……har sae da taci rabi
sannan ta dago tana kallonshi ,First time kenan da ta ji kunyarshi a
rayuwarta ,saurin maida kanta tayi kasa tare da juyawa ta kalli window ……

A wahale yace "Sorry……

Ba tare da ta juyo ba tace "How did you bear when i insulted you so badly
without understanding you?

Da sauri ya bude mata marfin fresh milk din tare da mika mata ……Idanuwanta
cike da hawaye ta juyo tana kallonshi,bai dauke nashi idon ba sae ma salon
kallon da ya sake mata ……

Muryar JB yaji yana fadin"Kai meye haka why are staring her?common dallah
fito malan baka san matar aure bace zata tasa ta gaba da wannan shegen
kallo ,Baby what happen?

Saurin juyar da kanta tayi ba tare da ta amsa
Maleek din ya bar motar sae da kamshinshi da ya
tana fitar da kwallah ……tabbas tana son JB amma
ranta to idan hakane tana Kaunar Maleek ne tana

masu ba tana jin lokacin da
bar mata rintse ido tayi gam
ta tabbata tana jin Maleek A
son Jabir……

Ganin Maryam da Abba sun taso ya tabbatar mata da tafiya zasuyi……shigowa
maryam tayi tare da sake bglass na motar ta mika mata zani ta canza sannan ta
kamo hannunta suka fito tare ……Da sauri JB ya karbi hannunta tare da rungumota

jikinshi ……

Juyawa tayi tana neman Maleek amma duk arean babu shi sae kamshin turarenshi
da ya cika masu gurin ……Hawaye suka taran mata a ido ta daga kai a sanyaye tana
kallon JB shima ita din yake kallo ……cikin salo ya kashe mata ido tare da kanne
guda daya ……murmushi ta danyi sannan ta juya tana kallon Abba dake gefenta shima
ita yake kallo idonshi cike da kwallah Sae maryam dake kallon kasa ko baa fada
mata ba tasan kuka take ,idanuwanta suka ciko da kwallah ……"Abba……"ta fada hade
da bata baki zatayi kuka

Lumshe ido yayi yana juyar da kai "May God be wit you love……" ya fada a
hankali tare da juyawa ya rike hannu Maryam suka tafi

,Wani kuka ta sake tana fadin "Please Abba maryam dan Allah wallahi na fasa
zuwa *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU DAKU*ZAN RAYU DAKE.. Abbana karku barni ……" Ta fada tana kokarin fizgewa daga
rikon da JB ya mata……sossae ya kara rungumeta yana shafa kanta har suka shiga
waiting room ……

*ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..
[3:00PM, 11/3/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU

🌹*🌹*🌹*
🌹*🌹*
🌹*

© *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* )

*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..

DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE..

3⃣1⃣

*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*This page is for you swthrt Aysha hameed🌹* Maryam Auntyn Maleek🌹* Maman
hanif🌹* besty firdaws Ahmed🌹* Meenarh parrot🌹* Meela Adeel🌹* Aunty Maijiddah musa🌹*
Ummi Muhsan 🌹*Abdul Maleeku Heart you 💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..

A cikin motar suka iske Maleek zaune ya kifa kai a sitiyari har suka shiga ba
wanda yace kala jin sun rufe kofar motar ne ya sashi kunna motar suka tafi ……
tafiya suke kamar kurame Abba na kallon window gefenshi Maryam na kallon ta
gefenta tana fitar da kuka a hankali ……Maleek kam gabanshi kawae yake kallo ba
tare da dauke ido ba ……

《》《》《》《》

Da daddare suka isa hotel din dake kusa da asibitin suka sauka tana rungume
jikinshi,har suka shiga dakin sannan ya zaunar da ita gefen gadon ya koma yana
kokarin shigo da kayansu ……

Lokacin da ya dawo tana kokarin shiga toilet da sauri ya matsa tare da
rungumota jikinshi ganin zata fadin "Baby bara ki jira nazo na kaiki ba……"

Dan murmushi tayi ba tare da tace komae ba ,hancinta ya dan ja yana fadin
"Inda kin fadi ba?Karki sake kinji ko zan maki komae kike bukata beside ma me
zakiyi toilet din?

A hankali tace "Zanyi wankane nayi sallah……"

Dan waro ido yayi cike da mamaki "Wane irin sallah kuma baby bayan kina Pes……

Common muje na taimaka maki kiyi wanka ……"

Shiru ta masa suka shiga toilet din a tare sannan ta kalleshi da raunannun
idanuwanta tace "Please ka fita zan iya wankan da kaina……"

Spreading arms yayi sannan ya fita tare da janyo mata kofar ……Mintina kadan ta
fito daure da towel sannan ta dauki kayanta da pad ta koma toilet din ta saka ……

"Bara nima nayo wankan ko baby ……"ya fada yana dan rungumota tare da kissing
wuyanta ……

Tsigar jikinta ne ta tashi cikin dubara ta janye jikinta tana murmushi ……
Shinfida abun sallah tayi shi kuma ya fada toilet din ,Da sauri ya fito yana
yatsina fuska "Baby wadancan kayan da kika cire ya za'a maki da su……"

A tunaninta ya san dae wankewa za'ayi sannan yana sane da barata iya wankewa
da kanta ba ……Shirun da yaga tayi ne yasa yace "Baby zaa zubar dasu ne ko?

"Zubarwa JB?Ta tambaya tare da kura mashi ido ……

"Yeah baby kinsan dae baran iya wanke wadancan kazantar ba ko?infact ma nayi
hating jini ko wane irina kinga kenan sae dae a zubar dasu……"ya karashe maganar
tare da fadawa saman gado

Gabanta ne ya fadi ta bishi da kallo sannan tace "Amma kasan baka son jini ka
yarda da aurena sannan kuma ka biyoni ai da kayi zamanka nigeria mun taho da
Maryam am sure zata man duk abunda nake bukata……"

"No baby jinyarki ai dole sae muharraminki zan maki komae jinin ne kawae baran
iya tabawa ba ……please ki dan shiga ki sakasu cikin leda sae na yardo ina son
zanyi amfani da toilet din……"

Uwar harara ta sake mashi tare da kabbara sallah abunta ……har ta gama
sallolinta yana kwance ya kasa shiga toilet din sae da ta gama addu'a sannan ta
dafa bango zata shiga toilet din ……da sauri ya taso yana fadin "Baby nace maki
ki bar tafiya ke kadae kada kije ki fadi ……"

Banza tayi masa har ya kaita toilet din ya fito yana rufe hanci ,ko da ta zuba
a ledar kin bashi tayi ta kama hanya zata je ta zubar kamar yarda yace ……tana
masifar don doguwar riga saboda lokacin da Abbanta yaje US ya sawo mata ita amma
tana gani ta jefar da ita a cikin GG din harabar hotel din ……ko da ta dawo yana
toilet yana wanka Cikin jikarsu ta bude ta fito da katuwar leda ta shifida saman

bed din sannan ta kwanta tare da rufe dukkan jikinta ……ya fito yana goge kanshi
da towel ganin ta lullube ya sashi karasa bakin gadon ya zauna yana fadin "Baby
ba dae har kin kwanta ba bakici abinci ba……"ya karashe maganar tare da yaye
blanket din yana kallon bayanta

Dan karamin tsoki yaja yana fadin "Gaskia wannan abun bai kyauta mana ba baby
da yanzu muna can muna enjoying life dinmu wallahi ……ko da yake sati biyu ne
zamuyi kuma assure kafin lokacin kin warke kinga daga nan istabul zamu je muyi
honeymoon dinmu ko……?

Ba tare da ta juyo ba tace "Waye yace maka sati biyu zan warke ……idan sati
biyun yayi ban warke ba fa?

"Daina fadar haka man baby ……yanzu dae tashi kici abinci ……"

Bata kuma cewa komae ba ta gyara kwanciyarta "Au bara ki ci abincin ba baby
……shikenan ai cikinki ne ni dae baran iya kwana da yunwa ba ……"

《》《》《》《》《》

Bayan sun isa garin Abba yace a fara kai Maryam gida sannan suka karasa cikin
unguwarsu kusa da wani mai dama fura Abba yace a tsaya yana so Abdul Maleek
dinne ya fita ya sawo mashi sannan ya dawo suka karasa shiga gidan ……

Cike suka iske gidan kamar ana wani biki Maleek na rike da ledar Furar suka
shiga falon Su Uncle Abbah ne da Fadila anyi rashe rashe kadsn carpet ana cin
abinci ……Suna ganin Abban suka mike tare da gaidashi ,daga masu hannu yayi cikin
fara'a sannan ya karbi ledar hannu Maleek din yana fadin "Karka tafi Abdul
Maleeku yanzu zan fito na baka sako ka kaiwa Hajiyar Safeena"

A falon ya zauna tare da fito wayarshi yana latsawa Number Safeena ya kurawa
ido yana yawo da hannunshi saman screen din wayar ……

Fadila ta kalli Uncle Abba tare da kanne mashi ido sannan ta dauki bottle na
swan da cup ta rarrafa kusa da Maleek din tana fadin "Ya Maleek ga ruwa ……"

Murmushin yake yayi sannan ya girgiza mata kai yana fadin "Alhamdulillah……"

Dan shagwabe fuska tayi tana fadin "Ruwan ma bara kasha ba?Dan Allah kasha
kaji……"

Kallonta yayi na secs ko baa fada mashi ba ya san sarae ita ce Aunty Fatee ke
mashi magana sannan itace ke yawan kiranshi da turo mashi message……

"Ka karba mana ……ta sake fada cikin muryar jan hankali "oh na manta ashe ban
zuba maka ba sorry……"ta karashe maganar tana kokarin zuba mashi a cup

Samun kanshi yayi da kiran Number Safeena bai damu da iyayin da Fadilan,ke
mashi ba ……Cikin saa ringing biyu ta dauka cikin sanyin murya tayi sallama

"Madam……"ya fada tare da lumshe idonshi

Zaune ta mike jin muryan Maleek din sannan ta kalli gefenta inda taji JB ya
kwanta amma wayam babu shi tabe baki tayi ganin baya dakin sannan ta maida
hankalinta gurin wayar da taji Maleek na fadin "Madam kina jina……?

"Eh ……" ta amsa a takaice

"Ya jikin naki?
"Am okey……"
"Alhamdulillah ……" ya fada tare da yin shiru na yan mintina sannan yaja
numfashi tare da fadin "Sleep well madam……ki rike addu'a Nothing will happen to
you Madam kinyi duka sallolinki……"

Gyada kai tayi kamar yana kallonta tare da goge yan kwallan da suka zubo mata
he's such a caring person ta fada a ranta ,jin ya sake yin shirun ne ya sata
komawa ta kwanta wayar na makale a kunnenta

A hankali tace "You done much to me Maleek……" Katse wayar tayi ba tare da ta
jira abunda zaice ba ……

Sam ya manta da Akwae mutane a falon sae da ya ga Fadilan ta mike tare da
fadawa dakin Aunty Fatee da gudu "Ikon Allah……"ya fada a fili tare da kallon
Uncle Abba dake ta faman zuban mashi harara

Yar dariya ya sake mai sauti to meye hadinshi dasu Spreading arms yayi ya mike
ganin Abban yana saukowa,Kudi Abban ya mika mashi yana fadin "Hajiyar Safeena
zaka kai mawa kace ta fara amfani da wannan gurin maganin kafin na shigo ……"

Hannunsa ya janye daga karbar kudin yana fadin "Zan bata Alhaji akwae kudi
hannuna……"

"Ka karba mana ka kai mata ……"Abban yace tare da sake mika mashi

Girgiza kai yayi kanshi na kasa alamun bara ya karba ba "Meye haka Abdul
Maleeku gardama zan tsaya da kai?ka karbi kudi ta kaiwa hajiya final……"

"Afuwan Alhaji in dai ni zan karbi kudinka na kai awa Madam dita magani banga
amfanina ba a rayuwarka ……dan Allah kayi hakuri na nemawa Madam dita magani da
zufar Aljihuna……" ya karashe maganar muryarshi na rawa

Shiru yayi yana kallonshi tabbas Maleek mutunne mai tsananin tausayi da
alkhairi shi Kanshi ya yarda da cewa Abdul maleek ya aje diyarshi wani guri na
daban a rayuwarshi ……hannunshi ya kama yana gyada mashi kai "Nagode Sossae Abdul
Maleeku Allah ya albarkaci rayuwarka……"

*ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..
[10:24PM, 11/3/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU

🌹*🌹*🌹*
🌹*🌹*
🌹*

© *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* )

*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..

DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE..

3⃣2⃣

*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Wannan page din nakine khadija bee bee ta Allah ubangiji ya raya mana ilham
sda sulteen Aunty Sis💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..

Shiru yayi yana kallonshi tabbas Maleek mutunne mai tsananin tausayi da alkhairi
shi Kanshi ya yarda da cewa Abdul maleek ya aje diyarshi wani guri na daban a
rayuwarshi ……hannunshi ya kama yana gyada mashi kai "Nagode Sossae Abdul Maleeku
Allah ya albarkaci rayuwarka……"

Fadila kam dan yalolan gyalenta ta dauko dake aje saman gadon Aunty fatee ta
fito tana kuka ……Aunty fateen ce ta biyota tana fadin "Ke fadila lafiyanki kuwa
me aka maki kike kuka……?

Shiru ta mata ta fita daga gidan ,har ta isa gidansu tana kuka ta fada dakin
mamanta ,"Me ke faruwa fadila?Aunty zuby ta fada cikin sauri tare da rungumota
jikinta

Cikin kuka tace "Mum wallahi sonta yake……"

,"Wacece ya ke so kuma?waye ma fada man kinji fadila……"ta fada cikin lallashi

"Mum Maleek mana wallahi Safeena yake so kuma na rantse da girman Allah sae
dae ya mutu mu duka mu rasa shi……"ta karashe maganar tare da sake kuka da karfi

"To Uban wa yace maki sonta yake?kuma an fada maki ana aure cikin aure ne……
Sakara ki kwantar da hankalinki ko jiya Hajiyarmu ta kai numbershi gurin boka
kuma ya tabbatar mata da naki ne……"

Share hawayen tayi tana kallon Mum din tata tana so ta gasgata abunda take
fada ……Tabbas indae Maleek ya zama nata She's the luckiest person a duniyar nan
……Cikin farinciki ta rungumo Aunty Zuby tare da manna mata dan kiss tana fadin
"I Love you Mum……"

Cikin Wasa Aunty zubyn ta harareta tana fadin "Da kinzo zaki daga man hankali
akan abunda kinsan dole ki sameshi ……"

"Sorry Mum……" ta fada hadi da turo baki

《》《》《》《》《》

Karar shigowar Message da tajine ya sata bude ido a wahale tare da kallon JB
dake kwance bisa doguwar kujera kafafu a hanbare kamar wani sabon arne ……Dan
karamin tsoki ta sake tana duba agogon dake makale jikin bangon dakin……

5:15am ta gani wayar dake haske ta saka hannu ta dauka sunan Maleek ke yawo
baro baro a jikin message din da aka turo ……Dan guntun message ne ya turo "Madam
ki tashi kiyi sallah……"Lumshe ido tayi sannan ta mike da kyar tana kallon inda
ta kwanta sam babu sauki, ta fasa a ranta……duk da kwannansu uku ana treating din
ta tare magunguna masu dan karan tsada……

Bango ta dafa da kyar tana hararan JB dake ta uban baccinshi sam bai da kula
da addininshi wani abu ya tokare mata kirji ,bata samu sauki ba sae da ta dauki
robar lemun dake aje gefen gadon ta wurga mashi a fuska ……duk da ta dakeshi
sosae amma ko motsi baiyi ba ……tayi tsoki yafi sau 10 sannan ta shige toilet din
da kyar tayi wanka tare da tsarki ta fito tayi sallah ,har lokacin baccinshi
yake

Kamar ta kyaleshi ta dai daure ta kai hannunta tana dukan pillow da ya daura
kanshi a hankali tare da kiran sunanshi"Jabir ka tashi kayi sallah ……"

Hannun da take dukan pillow dashi ya rike gam tare da bude idonshi a hankali
"Baby kin cika takura……" ya fada cikin muryar bacci

Tabe baki tayi tana harararshi ta kasan ido sannan tace " Sallan ne takura?

"Baby ai ko karfe 11:59am zan iya sallan asuba tunda baa shiga pm ba ……"ya
fada yana kokarin gyara kwanciya

Bata san lokacin da tace "In ji wane jakin malamin?

"Please Ki barni nayi bacci baby

promise da na farka zanyi kin ji ko ……"

Banza ta masa ta cigaba da addu'o'in da Maleek ya turo mata ……

《》《》《》《》《》

Duk wani abu da granny zatayi Maleek ne ya fansheta, har ga Allah nema mata
maganin musulunci yake iya karfinshi Tun lokacin da granny ta fada mashi cewa
ciwon Safeena bana asibiti bane hankalinshi yaki kwanciya…… harta office idan
yaje karfe sha biyu yake baroshi ,Duk inda yaji wani babban malami yana gurin……
Baya k'ashin kashe ko nawa ake bukata sannan ko Abba bai san me yake ba

Iyakarshi da Abban kullun dare zai kai mashi fura sannan su danyi fira kadan
ya tafi…… ko yarda baya yi su gaisa da Aunty fatee saboda wani mugun haushinta
da yake ji

Hajiyarsu Aunty Fatee kam ta dage iya karfinta dole Maleek din ya so Fadilanta
ko ta halin kaka……

Yau ma tun da safe ta kira Aunty Zuby tace ta turo mata Fadila su tafi gurin
bokan tare ……Mintina kadan Fadilan ta zo ,basu bata

Please Login or Register in order to submit comment