Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mijin,Aunty bilki ya saketa wai tana mashi sata

Sai ta dawo gida tana taimaka mata …
Shima ba komae take iyayi ba sae ta ga dama……

【】

Ganin har an kwana amma JB bai dawo ba yasa hankalin mum dinshi ya tashi ta sami
Dad dinshi ta fada mashi ……

A fusace yace "Wae taya zaki takurawa yaro da girmanshi ,Jabir bai isa ya
kwana bane a waje ?koko yarone da zaa matsa mashi dole sae ya kwana gida……"

Kwantar da murya tayi tana fadin "Ba haka nake nufi ba ,naga bai taba kwana ba
har ya yini bai dawo gida ba ……"

A Zafafe yace "To yau ya kwana har ma zai kara kwanan sae muga wanda ya isa ya
takurawa yarona……"

Tabe baki tayi zata juya taji yana fadin "Ki sa ahada abinci sossae zanyi baki
daga abuja yanzu ma zan fita na daukosu don a guest house dina zasu sauka……"
Banza ta mashi tana gunguni ta fita……

Ko da yaje ya dauko bakin nashi daga airport guest house dinshi ya nufa dasu ……
Da yake duhu ya fara ya bude masu falon suka shiga suka zauna ba tare da sun
lura da Jabir dake sandare gefen falon ba ……
Sai da aka kunno Gen sannan suka ga mutun kamar gunki tsakiyar falon ……
Su duka suka mike tana kiran "Ekilisiya……"abunka da ba musulmai ba……

Dad dinne ya isa gurinshi tare da dagoshi a rude yana kiran sunanshi ……Shirun da
sukaji ne yasa wani mai karfin hali ya dauko robar ruwa suka watsa mashi ……

A firgice ya bude ido yana fadin "Muga dan iska a cikinmu……"yana yi yana karkada
kai ……
Dad din ya rungumoshi yana fadin "Jabir me ke faruwa……?

"Muga dan iska a cikinmu ……"Abunda ya fada kenan tare da angaje Dad din ya ruga
da gudu zaya fita daga falon ……

Bakin Dad din sukayi namijin kokari gurin kamoshi sannan suka turashi mota aka
nufi asibiti dashi ……
A Can dinma sai da aka daureshi ya tsaya duk wanda yayi magana ko ba dashi
yake ba to shi zai bashi amsa da "Muga dan iska a cikin mu……"

Duk abunda zaa mashi akayi sannan aka mashi allurar bacci likitan yacewa Dad
din ba maganin asibiti bane ya dace dashi ……
A Maidashi gida a nemi wani malami ya mashi addu'a……

Wulakantaccen kallo Dad din ya aikawa likitan yana fadin "Kawae kace bara ku
iya ba amma babu abunda yafi karfin asibiti……"

Cikin natsuwa likitan yace "Wallahi alhaji ba maganin asibiti ya dace dashi
ba……"

Dariya dad din yayi ta izgilanci sannan yace "Kamar yarda ubanka ya kashe maka
kudi aka baka kwalin wannan aikin haka nima zan kashe kudi ko wane asibiti ne na
samama dana lafiya……"

Shima kallon Dad din yayi a wulakance sannan yace "Kamata yayi ka kashe kudi a
bawa dan naka irin kwalina sae ya nemawa kanshi magani ……asibiti kuma daga nan
har Sin ka kai danka dole ku dawo a nemi wanda nace ……marasa mutunci"

Daukar Jb din akayi suka tafi gida dashi ……Mum din na ganinshi ta hau ihu da
kururuwa kamar diyar arna har sae da Dad din ya taka mata birki sannan ta
zagaita tana fadin "Waya maka haka Jabir……?

"Muga dan iska a cikinmu……"abunda ya fada yana kokarin bude da idonshi dake
rufe ……da yake bata san abunda ke faruwa ba sae cewa tayi ……
"Haba Jabir nice mum dinka me ke faruwa haka ?waya maka haka?

"Muga dan iska a cikinmu ……"
Zata sake magana Dad din ya taka mata birki dole tayi shiru……

*ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..
[3:07AM, 11/19/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU

DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..

🌹*🌹*🌹*
🌹*🌹*
🌹*

© *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* )

*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE..53 to 54*ZAN RAYU DAKE..

Satinsu daya a asibiti aka sallamesu ……
Ishaq abokinshi ya kira ya mayar dasu gida ……
A Bayan motar suka zauna babu wanda yace kala a cikinsu sae dae kanta na saman
kafadarshi……
Tana ganin sun doshi hanyar gidan ta masa wata irin cakuma tana kallonshi ……
"A'a……"take fada da karfi tare da girgiza mashi kai ……

Matse ta yayi a kirjinshi ba tare da yace komae ba ……har cikin gidan ya shigar
dasu sannan ya fita daga motar jin Safeena na kuka ……

Ishaq na barin motar ta saki sabon kuka tana fadin "Kar mu zauna anan dan
Allah……"

Riketa yayi sossae yana fadin "Me yasa Safeena?

"Gidan JB ne Abdul maleek dan Allah ko gidan Baffanka ne muje mu kwana amma baa
nan ba ……"ta fada tana kuka a hankali……

Shafa kanta yayi tare da kara rungumeta yana fadin "Ba gidansa bane Safeena ……
dan Allah kiyi shiru wallahi,bana kaunar kukanki……"

"Ban yarda ba dan Allah mu tafi ni dae wallahi dawowa zasuyi……"

"Akwae sojojin da aka kawo Safeena babu abunda zai faru da yardar Allah……"
Lekawa tayi tana kallon sojan dake tsaye bakin gate din da katuwar bindiga ……
Ihu ta sake tare da kara makalkaleshi ……

Dakyar ya samu ta yarda da ba gidan jabir bane na Ishaq ne ……Sannan suka fito
har lokacin tana rungume jikinshi tana zare ido kamar karamar yarinya……

Bankwana sukayi da ishaq din ya mika masu ledar hannunshi sannan ya fita ……

Koda suka shiga falon da sauri ta rufe kofar tare da jingina da ita tana
kallonshi ……
"Common ……"ya fada yare da janyota ta fado jikinshi……
"Ki saki jikinki kinjo Twee……"

"Idan suka zo fa……"ta fada a,hankali…

Daukarta yayi ya daga sama yana fadin "Bama zasu zo ba……"
Shiru tayi har lokacin tana mazurai ……da wayau ya samu ta shiga dakin tayi
wanka sannan suka fito ya jasu sallah ……

Ledar Da ishaq ya basu ya bude ya fito da Potato'n chicken bundt dake ciki ya
juye masu a plate yana kallonta ……
Yatsina fuska tayi tana kallon gefe guda har lokacin jikinta bai koma dae dae
ba……
"Eat……"ya fada tare da janyo hannunta ya daura saman,spoon din yana kallon
blming face dinta……

Girgiza kai tayi tana lumshe idanunta a hankali tare da jingina da kujera……
"Eat kinji Twee……"

"Bana ci……"ta fada a takaice……

"Me yasa?ko bakya sonshi ne……?ya tambaya cikin sigar lallashi

Gyada mashi kai tayi alamun Eh ……
"To me kike so……?Ya fada a hankali

Cikin Salo tace "Awara……"
Dariya ya saki mai sauti yana kallonta tare da sake maimata Awaran a fili ……
Turo baki tayi tana kallonshi ta kasa kasa ……
Still murmushi yayi yana shafa sajenshi sannan yace "Ina zan samo awara yanzu
Twee……"

Ware Hannayenta tayi tare da bude manyan idanunta tana kallonshi ……
Murmushi ya kuma yi sannan ya mike yana fadin "Bara naje na bayar a sawo maki
……"

Bata ce mashi komae ba har ya fita sae dae gabanta dake faduwa da karfi ……
Har ya bar falon ta bishi da gudu tare da rungumeshi ta baya tana fadin "Na fasa
……bana son Awaran dan Allah ka dawo……"
Hannunshi ya sanya ya zagayota tare da rungumeta jikinshi yana kiran sojan dake
tsaye bakin gate din ……
Lamo tayi jin hannunshi na yawo tsakiyar bayanta ……
Sojan ya baiwa kudin ya sawo mata sannan ya dauketa cak ya shigar da ita falom
tare da zaunar da ita saman kujera ……

"Me kike tsoro……?ya fada tare da tsareta da manyan idanuwanshi ……

Dukar da kai tayi tana fadin "JB……" Kai tsaye

Kallonta yayi na yan mintina sannan yace "Baya lafiya ai……"
Da sauri ta kalleshi tana girgiza mashi kai alamun bata yarda ba……
Hannunta duka biyun ya riko yana kokarin saka idanunshi cikin nata amma taki
yarda ……Yar dariya yayi mai sauti yana fadin "Da gaske baya lafiya jiya Ishaq ke
fada man yanzu haka kamar ciwon hauka yake fama dashi ……"

Da sauri tace "Allah ya kara ……"
Hannunshi yasa tare da buge bakinta yana hararanta ……
Turo baki tayi tare da dafe inda ya buga tana shefa mashi hararan kasan ido……

"Allah ya baki hakuri……amma komae mutun ya maka idan kaji baya lafiya addu'a
kake mashi kinji Safeena……"

Turo baki tayi tana fadin "Shine fa……"
Da sauri ya katseta yana fadin "Ko da Aunty Fatee ce Safeena……"

Da sauri tace "Allah ya kyauta wallahi ……"

Kanne mata ido yayi yana fadin "Ko……?
"Uhm……"ta fada a takaice ……
Sallama akayi tare da bashi ledan awaran sannan ya dawo ya juye ……
Zata saka hannu ya janye plate din yana hararanta ……"Ki barni nayi aikina……"
Shiru tayi tare da kallon kasa fuskarta dauke da murmushi ……
Sae da ya gama bata awaran sannan suka,mike ya rufe kofar falon suka shiga dakin
dake kallonshi ……
Katon gadone a ciki an gyarashi kamar wata sabuwar amarya ……
Brush sukayo sannan ya sata tayo alwala sukayi nafila tare da kwanciya ……
Janyota yayi ya rungume kamar zaa kwace ta har sae da yaji bacci ya dauketa
sannan ya mike ya kunna fitilan wayanshi yana kare mata kallo……
Ya dade yana kallonta tare da kyalla mata photo kala kala sannan ya,kashe wayar
ya janyota ya rungume tare da rufesu da bargo……

【】

JB kam iyayen kudi dad dinshi ya kashe aka fitar dashi india ……
Cewa sukayi wai kwalwarshi ce ta samu matsala don haka suka dinga banka mashi
allurai kala kala na kwalwa……
Amma ba wani cigaba da aka samu sae dae ci baya tunda alluran da suke mashi sun
fara effecting brain dinshi ……
Hakanan sai dae aga yana fizge fizge kamar mai farfadiya baya ga surutun da hat
lokacin bai daina ba……

《》《》《》

Abba kam tun da Safe ya hawo motar haya ya dawo katsina ……
Abdul maleek ya kira lokacin da suka iso yace yazo ya daukeshi……
Safeena na wanka ya zame ya fita ba tare da ta sani ba ……Sae da ta fito ta
nemeshi bata ganshi ba sannan ta shiga zagaye gidan tana dubawa ……
Don tsaruwa ya tsaru Sae dae bai shigar mata rai ba tunda ta san ba nasu bane ……
Ita tama fi son su bar gidan su nemi nasu koma ko da daki dayane da toilet su
zauna don bata tunanin Abdul maleek din zai koma Cikin gidajen Abbanta ya
zauna……

Ko da ya dauko Abban nan gidan ya wuto dashi ……
Lokacin da suka shiga falon tana kitchen tana dube dube har ta bude wata yar
kofar da ta gani a gefe ashe tulun kayan abincine a ciki ……
Maidawa tayi ta rufe tunda ta san ba nasu bane ta fito tana kakkabe hannu ……

Tsalle daya tayi ta iso gaban Abban tare da rungumeshi ……
Kafin su gama gaisawa Abdul maleek ya shiga kitchen din ya daura masu ruwan zafi
sannan ya soya kwai……
Tana jin kamshi ta mike ta shiga kitchen din tana waro ido
"Waya sa ka taba masu kaya……"ta fada tare da jan kunnenshi……
Kashe mata ido yayi yana fadin "Allah ya basu hakuri……Zan biyasu idan na samu
kudi……"

Cikin sanyin murya tace "To dole sae mun ci abunda bamu dashi……"
Ganin yanayinta yasa shi janyota jikinshi yana fadin "Sorry ……Sun ce nayi

amfani da komae ne fa……"
Shiru ta masa tana kallonshi ……
Janyeta yayi daga jikinshi ya bata ta kaiwa Abban……

Sai da suka koshi sannan Abban yace su taso su tafi ……
Da "To……"Abdulmaleek ya amsa ……
Safeena kam waro ido tayi tana fadin "Ina?

"Gidansu Fateema……"Abban ya fada kai tsaye……

*ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..
[5:26AM, 11/19/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: *💧💧 ZAN RAYU

🌹*🌹*🌹*
🌹*🌹*
🌹*

© *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* )

*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE..

DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE..55 to 56*ZAN RAYU DAKE..

Daga Safeena har Abdulmaleek suka kalleshi lokaci guda a sanyaye sannan Abdul
maleek din ya shiga daki ya fito da hijab din Safeenar a hannu suka fito……

Babu wanda yace ma wani komae har suka bar gidan sannan suka dauki hanyar zuwa
gidansu Aunty Fatee ……
A bakin gate din gidan sukayi Parking kusa da inda wasu masu aikin kawo yashi
suke juyewa……
Kai tsaye Abban ya kutsa kai cikin gidan ba tare da fargabar komae ba ……Daga
harabar gidan suke jiyo muryar Aunty Fatee tana bala'in an dauke mata set na
gold dinta kuma sae an biyata ……

Murya Fadila suka jiyo tana fadin "To Uban Wa zai maki sata a gidan Aunty
Fatee……"

Kai tsaye tace "Ubanki ……"sannan ta cigaba da hargowarta……

Sallamar Abban ya sata juyowa a sukwane tana kallonshi tare da nuno shi da hannu
tana fadin "Khaleed kai ne ……"

Murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace "Nine Fateema kinyi mamakine……?

Uban ihu ta saki tare da dafe kai tana fadin "Wallahi karya ne ba kai bane ……
Hajiyarmu fito ki ga Khaleed wae shine bayan nasan karyane ya mace…… Kece Shaida
ya mutu Ni ce Shaida, Zuby ma shaida ce Abbah ma Shaidane ka mutu……"

Babu mai iya fitowa cikinsu sae Uncle Abbah da ya fito daure zanin atampha
yana kallon Abban ……Sannan ya koma da gudu tare da garkame kofar dakin yana
fadin "Fatalwa ……wallahi fatalwace hajiya bani hijabi na shige Hajiyarmu……"da
karfi……

"Shine Aunty Fatee Abbana ne ,ko kin dauka ya mutu ne da gaske……?cewar
Safeena dake tsaye tana kallonsu ……

Dariya Aunty Fateen ta saki tana fadin "Ni ce Shaida ……kai wallahi malan habu
ma shaidane kuma Malan bala ma shaidane ya mutu……a'a a'a ya mace nace maku ya
mace ……"ta karashe maganar cikin sautin waka tare da fara soshe soshe tana wurga
idanu……

Salati Abban ya dauka tare da binta da kallon ……Zuwa tayi gabanshi ta kai hannu
zata kamoshi ……yayi baya da sauri yana nunata da yatsa yace "Akul fateema karki
kuskura ki tabani……"

Itama baya tayi tana wurgawa Safeena kallon da ta fara tsorata da ita ……tayi
bayan Abdul maleek ta boye tana ware idanu……

Daga falon ta fita tana fadin "Malan habu shaidane Khaleedu ya mace ……haka
liman ma shaidane ka mace ……"Bin ta sukayi a baya Abban na salati amma kafin ta
fita gidan ta gama cire kayan jikinta tsab tana fadin ……

"Nace maku ya mace tunda sae da na barbada mashi a abinci daga baya ma na juye
mashi duka don yayi saurin mutuwa……Kai har Nafeesa na kashe, nace maku ta
mace……"
Motar dake kwaso yashin ce tayi gaba da ita tare da bi ta samanta ta wuce ……

Ihu Safeena ta saki ganin kwalwar Aunty Fatee a tayar motar tare da kankame
Abdulmaleek kamar numfashinta zai fice ……
Cikin Sauri ya kaita mota sannan ya dawo yana fadawa Abban zaije ya maidata gida
ya dawo……

Mutanen gurin kam salati suka dauka bayan motar ta daki bango ta tsaya……na ciki
ya fito amma ko kwarzane babu a jikinshi ……

Yan hanjin cikinta yashe saman hanya ……haka hannuwanta ko wane ya kama
gabanshi ……haka a ka tattarata aka shigar da ita gidan don babu maganar zuwa
asibiti……

Cikin Yan mintina labarin mutuwar Aunty Fatee ya karade ko'ina a lungun ……
Hajiya kam suna cikin gida babu kafafuwa, banda ihu babu abunda sukeyi……

Liman aka aika yazo amma ba'a sameshi ba wai yaje kauyensu ……
haka ladanin unguwar shima baya jin dadi ……
Abban ne ya taimaka aka mata wanka tare da sallah ,shima dukka mutanen basu cika
sahu daya ba ……

Da yan k'warorin mutane aka tafi da ita makabarta ……
Bayan anyi kabarin da za'a sakata ne aka ga kananan kunamu jawur kwance a cikin
kabarin……
Hankalin mutanen yayi bala'in tashi har ma wasu suka fara sabewa suna barin
makabarta……

Abban ne ya jajirce yace su taimaka a sake wani kabarin……
Haka aka sake gina wani kabarin amma the same abunda aka gani ana farkon shi aka
gani ana biyu……
Sai da aka gina kabari kusa biyar amma duk wanda aka gama ginawa kunamu za'a
gani a ciki ……
Wani dan dattijo yace a saka a haka saboda idan zasu gine dukkan makabartar to
da alama abunda zasu gani kenan……
Haka aka kamata aka saka cikin kunamun ……Sannan suka juya a sanyaye cikin
tashin hankali suka tafi ……

Basu fita makabartar ba kabarin Aunty ya kama da wuta……
Cikin kidima suka juya suna kallon tashin hankali ……
Abban bai san sadda kuka ya kwace mashi ba yana fadin "Wallahi indae Alhaki na
ne Fateema na yafe maki duniya da lahira ……Allah ka tausayawa wannan baiwar taka
dan darajar Fiyayyen halitta……"

Ruwa Aka fara kawowa da kasa ana kokarin kashe wutar amma ko alamun mutuwa
batayi ba ……
Lokaci guda wutar ta tsallake kabari biyu dake kusa da na Aunty fateen ta kama
ana uku sannan ta kara tsallake kabari Biyar ta kama ana shiddah ……Duk da
makabartar zagaye take da ciyawu busassu hakan bai shafi sauran kabarurrukan
dake zagaye da makabartar ba ……

Kusan Awa uku wutar naci yayin da mutane ke zagaye da makabartar har saman
gini……ruwa kan har firefighter sun zo amma a banza sae da suka gaji suka zubawa
sarautar Allah ido……Wasu hotuna suke dauka wasu kuma video sukeyi wasu kam kuka
suke cike da tashin hankalin da basu taba gani ba……

A hankali kuma wutar ta dinga baya har ta mutu kurmus dan kanta……sannan mutanen
suka fara tafiya cike da al'ajabin tare da tambayar wace mata aka kawo me take
aikatawa haka?
《Wa iya zubillah……Wallahi tallahi baku bina bashin rantsuwa abunda ya faru
kenan akabarin wata baiwar Allah kuma ni,ganau ce ba jiyau ba ……Muji tsoron
Allah mu gyara aiyukanmu domin karshenmu……》

Cikin mintina dukkan unguwar da kewayanta an dauka cewa an kai wata mata
kabari amma kafin a fito kabarinta ya kama da wuta……

Da labari ya isa gurin su Hajiya karku so kuga tashin hankalin da suka shiga
har dasu Fadila da Uncle Abbah ……
Lokacin ne Hajiya tayi kukan da ake kira kuka tare da nadama mai tarin yawa ……
haka Aunty Zuby wadda dama ta rigaya ta yi nadama amma ranar sae da ta gwammace
da ba'a haifeta ba har ta ga wannan bala'in ……

Abban ma kuka yayi cike da tausayinta tare da kwarara mata addu'a ……Dan zaman
makokin da akeyi ma mutanen kin zama sukayi wadanda suka zauna ma suna jin
abunda ya faru suka mike suna fadin ko an zauna ma babu abunda zaman zai mata ……
Haka duk suka watse suka bar Uncle Abbah da Abban Safeena durkushe ……

【】

Abdul maleek kam yayi niyar da ya aje Safeenar ya dawo amma ta kankameshi tare
da sakin kuka tana dafe kai ……

Tambayar duniya ya mata ta fada mashi meke damunta amma taki magana sae zabura
take tana kara kankameshi ……

Ya tabbata tsoro taji don ko ba'a fada mashi ba yasan bata taba ganin mutun a
haka ba ……
Addu'a ya fara tofa mata a hankali yana rungume da ita har sae da ta fara dawowa
natsuwarta sannan ya dinga maimaita mata Inna illahi wa inna ilaihir raju'un a
hankali tana maimaitawa……

Kin barinshi tayi ko nan da can ya tafi tana jikinshi har dare ……sannan ya kira
Abban ya fada mashi ……
Abban cewa yayi kar ya damu shi har ya wuce gida ma……

Haka suka kwana ko magana ta kasa yi sae zare idanu take kamar mage,……
Kwanansu biyu a haka sannan ya samu ta saki jikinta dashi……

【】

Tana kwance jikinshi ya zagayeta da hannunshi yana karanta mata wani english
novel mai suna tears drops at the sun set……

Dukkan hankalinta ta maida akan littafin tana saurarenshi cikin natsuwa har da
su lumshe ido……

A je littafin yayi yana fadin "Meye date yau……?

Dan turo baki tayi tana fadin "19 Nov 2017 mana……"
Lumshe ido yayi tare da matseta a jikinshi ……
Dagowa tayi tana kallonshi tare da shafar sajenshi tana murmushi ……
"Menene……?ta fada a hankali

Waro ido yayi ya tabe baki sannan ya janyeta ya mike ba tare da yace komae ba
……yatsina fuska tayi tana Spreading arms dinta a hankali tace "Kai ka sani ……"a
hankali

Juyowa yayi yana kashe mata ido yace "Ko……?
Tsuke baki tayi ta gyada kai sannan ta mike ta dauki littafin ta koma saman
one siter ta zauna tana fadin "Thank God nima na iya karatun……"

Dariya yayi mai sauti sannan ya shige daki yana girgiza kai……

*ZAN RAYU DAKE..FEEDOHM*💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
[9:21AM, 11/19/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU

🌹*🌹*🌹*
🌹*🌹*
🌹*

DAKE🌹**ZAN RAYU DAKE..

© *ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*Haske Writer's Association_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
( _Haske Writer's Association_*Home of expert & perfect writers_Haske Writer's Association_* )

*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*NA_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE.._Haske Writer's Association_*FEEDOHM💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*_Haske Writer's Association_**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE..Devoted to Ummi A'isha👌🏻**ZAN RAYU DAKE..
*ZAN RAYU DAKE..Bestowed to Aunty Sis💕**ZAN RAYU DAKE..

*ZAN RAYU DAKE..56 to 57*ZAN RAYU DAKE..

Sae da yayi wanka sannan ya fito sanye da kananan kaya sai kamshi yake zabgawa
yana waka a hankali " *ZAN RAYU DAKE..ZAN RAYU DAKE*ZAN RAYU DAKE.. Zan mutu dake *ZAN RAYU DAKE..ABADAN*ZAN RAYU DAKE.. Dani dake zamu
zauna……"

Kallo daya ta mashi ta yatsina fuska tana turo baki sannan ta cigaba da kallon
littafin don ba karantawa take ba ……

Kusa da ita ya matso tare da dukowa ya mata kiss a fuska yana kashe mata idanu
……"Twee zanta fita……"

Turo baki ta kuma yi tare da dagowa tana kallonshi sannan tace "Zan je ……"

Ido ya waro yana fadin "Ina……?
"Inda zaka ……"ta fada a hankali

Murmushi yayi mai sauti yana kallonta sannan yace "Alright bara na dauko maki
hijab ,dama JB zan gano kema ya dace kije ki ganshi……" Ya karashe maganar tare
da kafe ta da ido ……

Da sauri ta dago ido tana kallonshi tare da fadin "Sae ka dawo Allah ya kiyaye
ka yo man tsaraba……"

Dariyar mugunta yayi yana fadin "A'a Twee ki taso muje ……"

Turo baki tayi sannan ta cigaba da duba littafin ba tare da tace komae ba ……
Lakuce mata hanci yayi tare da kissing kumatunta sannan ya fita yana waigenta……

Mintina kadan ya dawo shida wata yar kyakykyawar budurwa a bayanshi ……
Cikin Fara'a ta tari matar tare da bata ruwa ……
Sannan ta dawo saman hannun kujeran da yake ta zauna ta kashe murya tana fadin
"Wannan fa?ban santa ba……"

Kallonta yayi suna hada ido ya kashe mata ido "Zata maki kunshi ta wanke maki
kai ta maki kitso……"ya fada tare da kamo hannunta

Waro ido tayi tana fadin "Kitso fa kace?
Gyada mata kai yayi yana tsuke bakinshi
"Bana so gaskia……"ta fada a shagwabe……Saboda har ga Allah bata kaunar kitso

Cikin wata irin murya yace "Ni kuma ina so ……Dan Allah kiyi danni kin ji ……?

Gyada kai tayi tana mashi murmurshi na musamman tare da komawa gurin budurwa
suka fara fira ……

Mikewa yayi ya fita ya basu guri……
Kunshin zallah bakin lalle yarinyar ta mata mai shegen kyau kamar an daura
zanen……
Sannan ta wanke mata kanta tare da yaryara mata kitso two step kanana kanana ……
wanda suka sauko har tsakiyar bayanta ……

Wani masifar kyau tayi kamar ba ita ba ……
Kusan magrib sannan aka gama ta shiga daki ta kirashi tace yarinyar zata tafi ……
Cewa yayi ta tafi kawae ya rigaya ya sallameta ……ko da ta dawo yarinyar tana
tsaye bakin kofa zata tafi ……tace ta jirata ta fito……

Yan kayan kwalliya ta kara mata dasu banda 5k da ta bata sannan budurwar ta tafi
kamar ta sude dob murna……don Abdulmaleek din 20k ya bata……

【】

Sai bayan isha'i ya dawo tana zaune falon sae kamshi take ……
Sae dae da ganin fuskarta kasan fushi take ……
Dariya yayi bai ce mata komae ba ya dauketa cak ya nufi da ita upstair din gidan
wanda tunda suka zo bata taba gigin hawa ba……
Lamo tayi har ya bude wani daki mai duhu ya shigar da ita tare da dagata sama
yana juyi da ita ……
"Ka sake ni……"

Cak ya direta kasa ……kai hannu tayi tana lalubarshi ganin dakin babu haske ko
kadan tare da kiran sunanshi a hankali ……
"Dan Allah ka kunna haske ……"ta fada kamar zatayi kuka
Jinshi tayi bayanta yana kokarin zage zip din rigarta tayi saurin rikewa tana
fadin "Meye kake yi haka ……"
Shiru ya mata tare da kamo duka hannunta ya matse a arms dinshi sannan ya
sabule mata rigar ta kasa ……
Bai ankara ba yaji hannunshi na yawo a dukka gabobin jikinta ……
Wuyanta ya fara kissing a hankali har ya gangaro shoulders dinta ……yayin da
hannunshi ya kasa zama guri guda ……

Kukan da ta sakine ya sashi lumshe ido tare da matseta a jikinshi ya bar duk
abunda yake sannan ya saka mata wata doguwar riga da iyakarta guiwa……Sannan ya
daura mata crown dake salki sossae……

A jiyar zuciya ta saki tana fadin "Meye kake yi haka Abdu ……"kasa fadin sunan
tayi saboda nauyin da taji ya mata ……

Hasken da ya gaurayen dakin ne ya sata waro ido tana bin bangon dakin dake
blming da *ZAN RAYU DAKE..Happy Birthday to my Princess……*ZAN RAYU DAKE..

Kallon jikinta tayi tare da kankame hannunta a hankali ta ware hannunta tana
juyi a hankali tare da fadin *ZAN RAYU DAKE..I Love you*ZAN RAYU DAKE.. da karfin karfe……

Fitowa yayi daga cikin labule ya dagata sama yana juyi da ita sae dariya take
……Sannan ya shige da ita wani dakin dake ciki wanda ke dauke da katon gado
kadae……Sae katon cake din dake gefe guda shima an rubuta sunanta a jiki……

Kallonshi take irin kallon da bata taba mashi ba sannan ta ware hannayenta
tana lumshe mashi ido……
Cikin Zarra ya,tako har ya iso ya shige jikinta ta mayar da hannun ta rufe tare
da daura bakinta saman wuyanshi ……

Tsawon mintinsu goma a haka sannan ta jiyo kara da karfi kamar fashewar wani abu
……
"JB ……"ta fada tare da fadawa saman gado ta janyoshi ta makale ……

A kunnenta ya rada mata "Baloon ……"tare da cije kunnen a hankali……

Duka ta kai mashi tana niyar tureshi ……Duka nauyinshi ya sakar mata tare da
kafeta da ido cikin salon soyayya……
Lumshe ido tayi a hankali har sae da ya gangare daga jikinta sannan ta bude tana
kallonshi

Please Login or Register in order to submit comment