Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sune tarin abubuwan da tuntuni suke hana shi aure sedai a yanzu da yayi ba wai ze saki jiki da ita bane, hasalima auren su na da wa'adin da ya ɗibar masa wanda yana cika ze sauta, zaman sa shi kaɗai ya fiye masa dan be yarda da kowa ba baya kuma jin ze yarda ɗin.

Yaro ya samu ya aika gidan, tana cikin sawa Ifty rigar school ta jiyo Muryar yaron na faɗin aiken da aka turo shi

"Wai salma ta fito inji Abdallah".

Sedai rigar ta kubce ta faɗi daga hannun ta saboda yadda zuciyar ta ta doka da jin sunan sa, hannun ta na rawa ta sake ɗaukar rigar ta shiga kici kicin sa mata sedai ta kasa saboda ruɗewar da tayi, Hajiya ce ta amsawa yaron da gata nan fitowa saboda jiya ta zauna tayi mata bayanin komai dan kamar mahaifiyar haka ta ɗauki Hajiya saboda ba ƙaramin taimako tayi mata ba a rayuwar ta.

Ɗakin Hajiya ta shigo ta karɓi shirya Ifty dan tuni ta gana da Ibty

"Je ki bashi uzuri daga nan ki nemo yara su fara fitar miki da jakunkunan, in an kwana biyu insha Allah zan zo in ga mazaunin ki, tashi kije".

Jiki ba laka ta fita, zaune cikin motar ta same shi ƙafar sa duka biyu a waje ya lumshe idanun sa tare da jingina kan sa da makarin kujerar, seda ta tattaro duk dauriyar dake gare ta kafin ta iya gaida shi

"Barkada safiya".

Saukar Muryar ta yasa ya buɗe idon sa, kallo ɗaya yayi mata ya kau da kai tare da maida ƙafafun sa cikin motar ya fara ƙoƙarin kunna ta

"Kayi haƙuri Ban ƙara sa shirya Ifty ba amma yanzun nan zamu ƙarasa, Bari in Sami yaro ya fitar min da jakunkunan".

Fasa kunna motar yayi ya koma ya kwanta kamar ɗazu ita kuma ta matsa ta sami wani almajiri suka koma ciki tare, ko da ta shiga tuni Hajiya ta gama shirya Ifty tare da haɗa musu launch box ɗin su, manyan jakunkunan kayan su dake shaƙe ta fara jawowa tana fitarwa tsakar gida almajirin na fita dasu har suka gama, kallon ɗakin take cike da matsanancin kewar sa da zata yi kafin kuma ta maida kallon ta kan Hajiya, matar da tayi mata halaccin da har abada ba zata manta ba, a rayuwa da ita da bana Husaila sun mata abinda in har ta manta to ita ɗin butulu ce cikakiya.

Nasiha sosai Hajiya ta yi mata da har tasa ta kuka ba dan komai ba se dan kewar mahaifiyar ta da kakarta da ta taso mata, ta sani da suna nan su zasu yi mata wannan nasihar.

Haka Hajiya ta rakata har mota, ko da suka je tuni ya zuba jakunkunan a booth ɗin motar sa ita kawai yake jira.

Duk yadda yake moody be san lokacin da ya saki fuska ba da Ifty ta ƙarasa tana ɗane shi Ibty kuma na gaida shi, haka ya ɗauke su duk biyu ya riƙe yana kallon su cike da shauƙi yana sauraren shirmensu har Hajiya ta gama mata nasihar da zata yi suka idasa bakin motar, har ƙasa ya tsugunna ya gaida Hajiya abinda yayi salma matuƙar daɗi a rai.

Hala suka ɗau hanya zuwa gidan da bata sani ba tana cike da kewar rabuwa da Hajiya da ragowar ƴan uwan zaman hayar ta da basu san da maganar auren ba ma se yau da safe amma duk da haka suka bita da fatan alkhairi.

Har bakin ƙofar party ɗin mahaifin sa ya kai motar sannan ya fita ya zagaya ya buɗe mata itama ta fito a ɗarare sannan ya buɗe wa su Ibty baya suka fito, hannu yasa ya ɗau Ifty yayinda ya riƙewa Ibty hannu ya nufi falon mahaifin nasa ta rufa masa baya itama.

Gana ɗaya mutanen ɗakin suka zuba musu ido zuciyoyin marasa gaskiya na dukan uku uku, masu gaskiya kuma na musu kallon rashin fahimta.

"Barka da safiya baba, ga salma matata da ƴaƴan ta kuma nawa".

A zabure mutane shida dake falon suka miƙe tsaye kowanne da kalar tambayar da yake jefowa

"What?, Me?, Kutumar uba?, Mata?, How comes?, Haba da Allah!.

Wannan sune ruwan tambayoyin da suka dinga yawo a falon cikin ihun muryoyi daban daban yayinda Abu Aulad ya saki hannun Ibty ya saka hannun ya jawo salma cikin jikin sa ya rungume.........................✍🏻.


Tooooooooh jama'a, gamu a ƙarshen free page da izinin Ubangiji, ko yaya paid pages zasu kasance?!.

Shin wacece Abu Aulad ya karyawa hannu jiya da dare?!

Wacece shuraiha?, Wai ma tsaya ita kanta Hajiya babbar wacece, meye alaƙarta da Abu Aulad?!

Jarumi, jarumi!, Shin kun Tuna shi?! Wanne shi?.

Nuriyya ƙanwar nafisa ƴa a wajen Anna, ko meye ƙudurin ta kan Abu Aulad?!.

Yace be yarda da kowa ba se kan shi kaɗai, what about Haisam?!.

Haisam, Haisam, anya shima babu wani ƙulli kuwa a under sunan nan?!.

"Wai ma ku tsaya, wace irin rayuwa ce Abu Aulad ya taso a cikin ta, meye tarihin wannan gidan, wane irin bahagon rayuwa ake yi a cikin sa.

Duk ma ba wannan ba, yaya rayuwar auren Abu Aulad da salma zata kasance, me kuke hangowa, gashi dai auren ya ƙayyade masa wa'adi, shin kuna ganin ze sake ta?!.

Ni abinda bangane ba shine shi kan sa Abu Aulad ɗin waye shi, ina mahaifiyar sa, anya baba mahaifin sa ne kuwa, to in ba mahaifin sa bane waye mahaifin nasa?!.

Shin ina labarin dangin mahaifiyar Salma, zata haɗu da dangin mamanta ko kuwa?, Baba Husaila da mama Hadiza principal, shin shikenan an rabu ko kuwa akwai wata rawa da zasu taka a rayuwar salma nan gaba?!

Duk amsoshin wannan tambayoyin na cikin paid pages, sister kar ki yadda ayi tafiyar nan bake domin na tausaya miki rashin da zaki yi dan littafin ze tabbatar da sunan sa akan ki wato ANJANE (RASHIN SANI) dan da kin san irin nisa da ƙarkon da tafiyar zata yi da ba zaki yadda a yi ta bake ba,!.

Ga duk me buƙatar yin payment ɗin sa ne bi ta wannan procedure ɗin,
₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment