Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk gidan ba wanda ya taɓa saurayi me maiƙo kamar ta dan ɗan gidan maigari ne, kukan da yaran suka kuma sanya wa a tare yasa taji takaicin ta ya ƙaru.

Ji take kamar taje ta shaƙe su har se sun mutu sedai rashin imanin ta be kai haka ba so se ta dubi Salame da bata ko numfashin arziƙi saboda wahala ga kuma azabar da ciwukan jikin ta ke mata

"Kin tashi kin kwashe wannan tsiyar dake neman hanani nutsuwa ko se na kwashe su na watsa a rijiya?".

Duk yadda jikin ta ya kai ga nauyi saboda dukan da tasha ban da azabar da take ji amma haka ta miƙe ta shiga takawa cikin ƙarfin hali har ta kai inda suke kwance se ciccilla hannaye da ƙafafu suke yi, a kafaɗa ta ɗora ɗaya tana runtse ido saboda zafin da taji dan akwai ƙuna a wajen ɗayar kuma ta rungume ta wuce akurkin ɗakin ta da ke daf da zubewa saboda yadda ya takwarkwashe, duk da gidan dukan sa na ƙasa ne amma babu ɗaki mafi muni kamar nata dan madafar su ma tafi shi nesa ba kusa ba.

Kan yagalgalallen buhun da take kwanciya ta shimfiɗar da yaran kafin ta kuma fice wa ɗauko jakar buhun ta, cikin ɗan hanzari ta ƙara sa ta ɗauke jakar ganin Inna mariya bata wajen da alamu ta shiga bayan gida ne.

Cikin cije baki ta kai zaune gefen yaran ta shiga bin su da kallo tana yaba kyan su a ranta kafin kuma ta ji wani sabon so da tausayin su na ratsa ta tuno yadda aka kashe mahaifiyar su,

'duk abinda ze faru bazan yarda in rabu da ku ba, mutuwa kawai zata  raba tsakanin mu insha Allah".

Ta faɗa a ranta tana jingina da bangon ɗakin sedai da sauri ta janye jin raɗaɗin da ya ratsa kwanyar ta hakan na shaida mata akwai ciwo a nan ɗin ma.

Ƙofar ɗakin taje ta saya kafin ta tuɓe kayan makarantar jikin ta da suka yagalgale saboda ƙunan wuta da kuma dukan ice, wani koɗaɗɗen zani ta ɗauko wanda dama uku ne kawai da ita kuma da su take rayuwar yau da gobe ta ɗaura, wanka take son yi sedai ta san yau ko mutuwa zata yi ba zata samu ruwan zafi ba se kawai ta ƙudure yi da na sanyin ta fita zuwa ƙatuwar rijiyar su dake tsakiyar gidan.

Babbar rijiya ce dan dukkan su na iya ɗiban ruwa a lokaci ɗaya dan tana ɗaukar guga sama da biyar, ƴan mata biyu ne suke ɗiban ruwa suna hirar su, tun da ta nufo wajen suke dariya suna nuna ta, duk da bata jin me suke cewa dan da ɗan tazara tsakanin su amma tasan ba abu me kyau suke faɗa ba, hakan ba sabon abu bane a wajen ta dan duk faɗin gidan ba zata iya ɗaga mutum ɗaya tace gashi me son ta da ƙaunar ta bane, daga masu ƙi da tsanar ta se kuma ƴan ba ruwa na sune wanda ba zasu dake ta ba ba zasu zage ta ba sedai ba zasu taimaka mata ba irin su kawu Adamu kenan.

Ƙaramin guga ta ɗauka ta zura cikin rijiyar ignoring all the curses da suke rending mata ta shiga ɗiban ruwan ta dan tun da da basu samu dalili ba ma ƴar iska suke ce mata balle yanzu da ta zo da ƴaƴa har biyu gida,

"Iyayen karuwa dai sun yi asarar haihuwa, ke in kika bibiya ma sule me shago ne yayi mata cikin da ta haifi yaran nan dan kin ga shine kaɗai yake kulata a garin nan".

"Kai anya kuwa sule ne, kin ga fa Inna tace yaran sun yi kusan watanni biyu da haihuwa shi kuwa ai rabon shi da ita tun da tayi ƙaryar jarabawa ta zauna wata goma a makaranta".

"Eh ba mamaki ma a can wani malamin ya ɗirka mata cikin, kin san dama buba ya faɗa mana kafirai ne".

Haka suka cigaba da maganganun su na aibata ta amma bata kula ba ta ɗibi ruwan da take buƙata ta koma sashen su, da saɗab saɗab ta zagaya wani ɗan fili dake bayan ɗakunan su ta yaye zanin ta kwara wa jikin ta ruwan, sauƙin ta ruwan rijiya akwai ɗumi ban da haka kuma yau ɗin an yi rana sosai shiyasa ya sake yin ɗumi kamar an gauraya dana zafi.

Zanin ta mayar tana barin cinyayyen bokitin a nan wajen ta koma ɗaki bayan ta leƙa ta tabbatar Inna mariya bata wajen, yarinyar da ta fi yin kuka ta ɗauka ta shiga jijjigawa har ta yi baccin wahala dan yunwa suke ji sedai bata san me zata basu ba, haka tayi wa ɗayar ma ta samu itama tayi bacci.

Tuno da wata hamsin a jakar ta yasa ta maza ta jawo jakar ta shiga zazzage ta, kayan sarƙar babar ƴan biyu da suke zube a ƙasa ta ɗaga ta shiga kalla tana yaba kyan su kafin ta shiga hawaye sanin me su ta daɗe da zama gawa, hawayen ta share ta shiga tattara su tana mayar wa haka dan ta san a yadda suke da kyau muddun Inna mariya tayi ido biyu dasu shikenan sun zama nata.

Hamsin ɗin ta shiga juya wa a hannun ta tana tunanin ta yadda zata fita daga gidan ba abin ta haura ta katanga ba jikin ta na mata ciwo.

Dan son samun sauƙin fita ta siyo musu kunu ta basu ta ƙara sa inda take ajiye gishiri dan tasan hakan kawai zata yi taji sauƙin raɗaɗin ciwon har ta iya haura katanga zuwa anjima.

Gishirin ta ɗauka tare da kwance ƙullin da tayi wa ledar ta ɗebo a hannun ta tana runtse ido saboda azabar da ta dan zata ji ta kai kan guraren da ƙunar take, duk yadda zugi da raɗaɗi ke ratsa ƙwaƙwalwar ta bata dena ba har se da ta gama kafin ta kwanta tana fidda numfashi ɗaiɗai kamar me cutar asthma.

Wannan horon kawu habibu ne lokacin da tana hannun matar sa Inna Abu kafin ta dawo hannun kawu iro, tun tana yarinyar indai tayi laifin da aka dake ta haka kawu habibun ze ɗebo gishiri ya dinga danna mata a wajen ciwon, karon farko da ya fara yi mata da hankalin ta suma tayi amma ko da ta farfaɗo haka ya sake yi mata.

A lokacin seda ta suma so uku amma ba hakan yasa ya fasa abinda yayi niyya ba, tun daga lokacin kuma yake mata wannan azabar, tun tana damuwa tana shiga tashin hankali har tazo ta daina ba kuma wai dan bata jin zafi ba se dan ta riga ta saba danne zafi da raɗaɗin a ranta.

Tsawon lokaci kafin taji kamar an yi ruwa an ɗauke duk ta daina jin azaba shigar gishirin jikin ta haka kuma tuni waccan azabar ta disashe ta zafin ciwon shiyasa se ta ke jin yanzu kamar babu ciwo a jikin ta, koɗaɗɗen zanin ta ta maida tare da zura rigar sa ta salallaɓa ta fita jin an shiga sallar magrib, ta katanga ta haura kamar yadda ta ƙudira.

Gudu ta sha sosai kafin ta kai ga isa wajen Sare me kunu, hamsin ɗin ta miƙa mata tana numfarfashi tare da faɗa mata ta bata na Naira goma ƙullin biyar biyar, a farar leda aka ƙulla mata ko wanne kafin a saka a baƙar leda ta miƙa mata,da hanzari ta karɓa sannan ta wuce wajen sule me shago, bata tsaya amsa tambayoyin da yake mata ba na ance ta dawo da ɗanyen goyon shegun yaran da ta haifa har biyu ba tace ya bata siga na goma se madara ta Ashirin.

Madarar kusan Naira ɗari ya zuba mata haka sugan ma ya fi na hamsin ya bata yana faɗin tabar kuɗin kawai dan ba ƙaramin so yake wa Salame ba, godiya ta masa ta juya zuwa hanyar gidan su cikin gudu sosai har ta kai, ta katanga ta koma kamar yadda ta fita dan ba wata katangar arziƙi bace kun dai san fences ɗin ƙauye.

Hango Inna mariya a Zaune kan tabarmar da take zama daga bakin ƙofar ɗakin ta yasa ta rasa yadda zata yi ta wuce, ta daɗe tsaye kafin taga shigowar kawu iro sashen nasu, kayan hannun sa Inna mariya ta karɓa ta shige ɗaki tana masa sannu da zuwa shima ya mara mata baya, da wannan damar ta samu ta saci kofi ɗaya cikin kofunan sashen ta shige ɗaki da sauri.

Seda ta saya ƙofar duk da ba mai shigo nata dan ko neman ta Inna ke yi sedai tai ta ƙwala mata kira, kunun ɗaya ta juye cikin kofi ta sa sigar kaɗan ta juya da wani kara kana ta ɗau yarinya ɗaya ta fara tashin ta har se da ta buɗe ido, buɗe baki tayi da nufin komai Salame ta maza ta sa mata kofin a baki, cikin yunwar da ta galabaitar da ita ta shiga sha ba wani musu, sosai tasha kunun kafin ta saki tana sa harshen ta tana lashe saman cute small lips ɗin ta, murmushi Salame tayi ganin yarinya ma ta san zaƙi dan ta tabbatar da bata sa sugar ba baza ta sha da yawa haka ba.

Ajiye ta tayi inda yarinyar ta shiga cilla ƙafafu tana wasa da hannayen ta, ƴar uwar ta ta ɗauka itama ta tashe ta tare da bata kunun, itama ta sha da ɗan yawa duk da be kai yawan na ɗayar ba, ajiye ta ta ƙara ɗaya na biyar ɗin kan wanda suka rage ta ƙara sugar ta shiga sha itama dan ta san yau kam ko itace tafi kowa maita ba zata samu abinci ba a gidan nan, da ɗan dama ta rage saboda kar yaran su ji yunwa su nema kuma babu, jakar ta ta ɗora ta rufe cup ɗin dashi sannan ta juya ga yaran ta ƙure su da kallo.

Kyawawan yara ne Masha Allah kamar ƴaƴan turawa, ba ramammu bane dan da ƙibar su daidai sanye da kayan masu kyau suma kansu an kakkama da soso da ya daɗa ƙara musu kyau, addu'a ta shiga yi musu tana tofa masu na Mayu da baki dan akwai Mayu sosai a ƙauyen.

Seda ta gama yi musu addu'a sannan tayi wa kanta ta nemi waje kan buhun ta ta kwanta dan zannuwan ta biyu ta haɗa ta shimfiɗa wa yaran da har yau bata san sunan su ba dan maman su bata faɗa mata ba ita kuma bata san da sunan da zata kira su ba.

Washegari kuwa tun kiran sallar biyu da ta tashi bata koma ba, tana idar da sallah ta fita tsakar gidan su ta hau aikace aikace kamar yadda ya zame mata wajibi muddin tana garin, tana gama wa ta ɗau bokitan su ta fita rijiya ta shiga jido ruwa, se da ta cika ko ina kafin ta hau kunna ruwan komo, tana juye kokon ta kai duban ta kan ƙofar su Inna mariya dake kulle har lokacin, da sauri da sauri ta dafa ruwan zafi ta kai ɗakin ta ta ɓoye cikin wata madaidaiciyar roba sannan ta dawo wajen ta kashe wutar.

Ɗakin ta ta koma ta surka ruwan a bokitin ta ta shiga yiwa yaran wanka, wankan jariri ba sabon abu bane dan tun tana shekara bakwai aka fara bata rainon yara haka kuma tana shekara sha biyu suka fara sa ta wankan jariran su, tana gamawa Hassana kamar yadda ta raɗa wa wadda taga tafi girma a idon ta ta ɗau Ussaina ta mata ita ma sannan ta ɗau ruwan nasu ta shiga banɗakin su ta kwarawa jikin ta ta maza ta fita tare da maida bokitin ta bayan ɗaki.

Ko da ta koma tuni yaran sun koma bacci da alama sun ji daɗin wankan, murmushi tayi tana jan kumatun Ussaina daidai lokacin da taji Muryar kawu habibu cikin ihun kiran sunan ta.......................✍🏻.




©️ Ouummey 📚✍🏻.






☑️Ote, Comment, share and patronize fisabilillah.
[12/13, 10:35 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 03 [ 10/12/2022 12:08 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★


_*PAID BOOK*_


Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.



From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*


₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.





                      FREE PAGE 003










_________________________📖 A gigice ta Fito daga ɗakin har tana yin karo da durƙusasshen bangon ɗakin wanda banda tsari da kariyar Ubangiji wata iska me ƙarfi nan in aka yi ze zube ne.

A firgice ta ja baya tare da maƙewa jikin garun ganin dukkan su mazan gidan ne a wajen wanda tasan ba dan kowa suka haɗun ba se dan ita.

Wani irin rawa jikin ta ya ɗauka haka ma zuciyar ta ta shiga addu'ar Allah ya taimake ta kar su ƙara mata wani ciwo da nauyin jikin da sabon dukan da ta san in ba Allahn ne ya tare ba se ta sha shi.

"Shegiya munafuka me suffar muminai, tana sussunkwi da kai tana baɗala a haka kuma take cutar wasu suke mata kallon saliha ta gari se gashi ƴaƴan namu dai da ake zagin sune nagarin, kin matso kusa ko se na harbo ki da ƙafa ta, tambaɗaɗɗiya kawai".

Da sauri ta matsa dan ta san kaɗan kenan daga aikin baba iro ya harba tan kamar yadda yace, ƙasa ta sa gwiwoyin ta tare da kai kanta ƙasa abinda su kuma suka fi tsana kenan dan sunce hakan wani salo ne na munafurci.

"Me zata zauna tayi mana a nan iro, kawai taje ta kwaso ƴaƴan shegun nata mu wuce wajen megari dan wallahi ji nake kamar in watsa a turmi in dake shegu ita kuma uwar in shaƙe ta har se ta mutu".

Baba habibu ya faɗa da iya gaskiyar sa yana demonstrating da hannayen sa, ita dai tana duƙe har lokacin dan ba'a ce ta tafin ba shawara ce suke yi a tsakanin su.

Uban dundu Inna mariya ta ɗuma mata ta kuma bita da zagi

"Ka ga min fitsararriyar da ba zata rama ragon sunan ta ba, wato ga sa'annin matacciyar uwar ki na magana shiyasa kika zauna kina kallon mu, to bari in kwaso shegun yaran in watsa a masai muga ta tsiya".

Ai kafin inna ta gama rufe bakin ta tuni ta ɗiba tayi ɗakin a guje jin za'a watsa mata su a masai, Hassana ta riƙe a hannu yayinda ta goya Ussaina dan ta fahimci Hassanar tafi haƙuri dan bata fiya kuka ba se in Ussaina nayi ta kama.

A saɗaɗe ta fito dasu wannan karon kanta a daidai tana bin su da kallo har ta kai gaban su ta sake tsugunnnawa, a yanzu kam Inna A'i da kallon da take bin su dashi ya ɓata wa rai itace ta kai mata duka a fuska, ba wai mari ba dan ba kuncin ta ta nufa ba kuma ta na sane ta kuma same ta a idon ta na dama, duk yadda idon ya ɗau raɗaɗi bata ko motsa hannun ta da niyyar taɓa wa ba.

Ta daɗe da sanin idanun ta na ɗaya daga cikin abubuwan dake jawo mata tsana, kyara da tsangwama a cikin gidan, wato wani irin ido Allah ya halitta mata me kamar na maciji ko mage za'a ce, dan ƙwayar idon ta ba baƙa bace haka ma ba brown ba, wata color so similar to golden, sedai golden ɗin irin me ɗan duhu kaɗan.

So da yawa su kawu, matan su ko ƴaƴan su sun sha goranta mata yanayin idanun nata duk tayi laifi, kai koma bata yi ba indai zasu haɗa ido se sun tanka mata, shiyasa tun lokacin da malamin Islamic studies ɗin su yayi musu addu'o'i ciki har da na baki shikenan ta ke yi, la haula kuwa kowane dare se tayi adadin da bata sani ba dan ba carbi ne da ita ba ta shafa a fuskar ta kafin ta kwanta haka kuma da asuba in ta tashi.

Bata san a wajen wa ta gado irin wannan idon ba cikin iyayen ta dan bata yi wayo da ko ɗaya ba sedai da alama ba wajen babanta da yake ƙanin baba Habibu da baba Adamu wa ga baba iro ba ne, tafi kyautata zaton wajen mahaifiyar ta ta gado ko kuwa dai Allah ne yayi mata nata halittan daban, ko a makaranta seda hakan yaso ya zame mata barazana dan har se da shugaban makarantar ta tsawatar tukunna shiyasa har tayi ta gama bata da wasu cikakkun ƙawaye sedai na gaisuwar mutunci, kowa gudu da tsoran ta yake saboda kalar idon ta da ba'a saba gani ba cikin jama'a, tun bata saba da hakan ba har ya zo ya zame mata jiki ba ta ma damuwa.

Zama suka yiyyi kan tabarmin da ke shimfiɗe a fadar me gari kafin suka shiga kai gaisuwa shikuma dattijon dake amsa sunan maigari na zaune kan kujerar ƙarfe kan sa ɗaure da rawani yana amsa musu.

Kafin kace me jama'a sun fara ciki dan haka ake wa duk ƴaƴan da suka yi ciki a garin amma fa marasa galihu dan da Allah yasa ƴar maigarin tayi shiru kake ji wai maye yaci shirwa, karuɗuf ƴar magulmaciya tayi ciki, ba wanda yasan da zancen seda faɗan kishiyoyi ya haɗa shima kuma har rana wata yau ba'a yi irin wannan zaman a kanta ba gashi har ta haife tuni.

Seda fadar ta gama cika sannan maigari ya fara sanar da abinda ya tara su wato dai batun cikin da Salame tayi ta haife batare da sanin su ba har gashi ƴaƴa sun kusa rufa watanni uku, hayaniya ce ta shiga tashi inda mutane da yawa ke Allah wadai da ita yayinda ƙalilan da abun ya faru kan ƴaƴan su suma suka shiga yi mata fatan Allah ya shirya a ganin su ai hakan ƙaddara ce (saboda ya faru ga nasu).

Se da gurin ya lafa kafin maigari ya shiga jawabin sa kamar yadda ya saba

"Bisa ga tsari na wannan gari bamu yadda da abun kunya ba ko yaya yake kuwa dan haka zamu aiwatar da abinda muka saba yi duk sanda aka samu irin wannan san zuciyar, a yanzu haka zamu karɓi ƴaƴan a kai su can nesa inda ba wanda ze san nata ne balle ayi mana gori kamar yadda muka saba tun da wannan shine karon ta na farko, da na biyu ne kuwa ko sama da haka to fa kun san hukuncin kora ne a kanta".

Yana gama faɗar haka wasu fadawan sa suka nufo ta da zummar amsar yaran inda ita kuma cikin matsanancin firgici da tashin hankalin jin abinda ake kiran ze faru ta sake ƙanƙame ƴaƴan ta ta shiga kurma ihun ba ta yadda ba ba zata bayar dasu ba, kowa a gurin ya shiga mamakin abinda tayi, a ganin su ƴaƴan shegen take ihu dan za'a raba ta dasu, to meye abin so cikin ɗan shege?!.

Muryar Salame da fiye da rabin ƙauyen zasu ce basu taɓa ji ba se gata ana jiyo ta tun daga farkon hayin maigari saboda yadda take ihun da iya ƙarfin Muryar da Allah ya bata, duk irin tsawa da zagin da babannin ta ke mata bata ma san suna yi ba balle ta saurare su ta daina ihun har se da maigari yasa fadawan su janye daga kusa da ita kafin tayi shiru ta sake matse ƴaƴan tana sauke numfashi sedai sam hankalin ta be kwanta ba dan tasan ba wai an ƙyale ta bane.

Seda megari ya gama ƙare wa jama'ar wajen kallo kafin ya muskuta yana zarar ido

"Tun da har wannan yarinya taƙi yadda da hukuncin mu to mun bata zaɓi biyu kuma a yanzu a nan gurin zata bayyana mana wanne ta ɗauka, na ɗaya ko dai ta bada yaran nan ayi kamar yadda aka saba dasu ko kuwa na biyu ta tattara ta bar mana garin ma'ana mun kore ta daga ita har ƴaƴan haka kuma duk sanda muka sami labarin shigowar ta to tabbas hukunci mai tsananin tsauri ya hau kanta, wannan sune zaɓin".

Shiru kowa yayi kallo ya koma kan Salame da take jin komai da aka faɗa haka kuma ba tare da second thought na halin da ita ko yaran zasu shiga ba sanadin zaɓin ta ta buɗe baki ta zaɓi abinda take ganin ya fiye mata

"Ba gari ba ko ƙasa ce zan iya haƙura in bar ta akan ƴaƴana dan haka na zaɓe su akan komai da nake dashi ciki kuwa har da asalina".

Kusan a tare duk su baba Habibu, baba Adamu da baba iro suka miƙe jin abinda ta faɗa, wato ta zaɓi ta bar garin saboda ƴaƴan ta haka ta zaɓe su akan Asalin ta wato su dangin ta kenan.

Shi kan sa maigari ba haka yaso ba dan a tunanin sa zata zaɓi bayar da yaran ne tun da in ta bar nan wa ta kama?, Bata da kowa banda dangin baban ta, mahaifiyar ta kuwa bama ƴar nahiyar bace, a yawon tuƙin babban mota baban ta ya auro ta dan haka ba wanda yasan komai a kanta kamar yadda basu faɗa wa kowa komai game da ita ba har kuwa ranar da ta bar duniya sanadin hauka da aka sa mata da ya kai sedai a ɗaure ta a ɗaki.

Umarni me gari ya bayar kan dogarawa su bita gida ta ɗebi abinda zata ɗauka a rakata bakin gari ta tafi sedai fir baba iro yace ba abinda ta aje a sassan sa bare ta koma ɗauka dan haka su rakata bakin garin kawai, bata Musa ba ta shiga gaba dogaran na binta a baya dan tun da ta shafa taji jakar makarantar ta na jikin ta hankalin ta ya kwanta.

Seda suka tabbatar tayi nisa da gari kafin suka juya zuwa gidan maigari suka sanar dashi an cika umarnin sa inda ya amsa da cuskunenniyar fuska dan ba haka yaso ba.

Abinda mutanen garin basu sani ba shine maigari siyar da jarirai yake wa ƴan birni da suka rasa haihuwa da kuma masu aikin asiri though be san me suke dasu ba, shidai kawai a bashi kuɗi shikenan, da an samu yarinyar da tayi ciki se ya hana a zubar yace ta haife shi kuma ya sami ƙarin jari.

Lokutan da kuma ba'a samun na banza hatta na sunna kaiwa yake dan akwai ungozomar da suka haɗa kai in ba na shege se a kai na sunna, yadda suke yi kuwa se an gama haihuwa lafiya lafiya se ta shafawa yaron wani magani da ta samo a wata asibiti dan ta taɓa zaman birni shikenan yaro se ya birkice da koke koke, ƙin kama nono da sauran su daga nan se a nufi wajen babban me maganin da suka yadda dashi da dukkan imanin su, dake shima nasu ne se yace ai ɗa ko ƴa na aljanu ne sun ɗauke naki sun musanya miki dan haka maza maza akai daji kaza daidai wuri kaza a ajiye musu kayan su, se an kai an ajiye ita kuma tabi dare ta ɗauka ta kaiwa maigari cikin gidan sa na sirri dake can bayan gari gefen dajika inda yake harƙallar sa.

Guri ta samu ta zauna tana haɗiyar busasshen yawu dan gaba ɗaya bakin ta ya bushe da ƙishirwa, tafiyar ƙafa sabon tace dan haka ba zata ce ta gaji ba sedai rashin ruwan ke neman kassara ta ga kuma ƴaƴa har biyu gaba da baya ga jaka me nayi se abin yayi mata yawa.

Mutsu mutsun Ussaina da taji yasa ta san ta farka dan haka ta sauke ta dan ta ɗan huta da goyon sedai ita ba hutun take nema ba abinci take nema da bata samu ba kuwa ta buɗe baki ta shiga canyara kuka da ƴar Muryar ta na jarirai, kukan Salame ta shiga yi itama dan abin ya haɗe mata goma da ashirin.

Haka Ussaina

Please Login or Register in order to submit comment