Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka naji jita jitar ze aure ƴar uwar Hajiya Babba".

"Kam babban bu**uba, ni za'a kawo wa iskanci har gida, lallai Hajiya Babba ta ɗebo ruwan dafa kanta, ki kwantar da hankalin ki Audu bashi da wata mataa gidan duniya suke, da alama zan gwada musu barikanci na da basu sani ba".

Cikin jin daɗi matashiyar ta gyara zama tana kai fuska gefe

"Atoh abinda ya kamata dai muyi kenan dan yana auro wata kin san dole zamu bar gidan nan tun da yaya da ta haɗa mu ta raba Ni kuma shine bana fata".

"Ki sa a ranki hakan ma baze taɓa faruwa ba, mu da gidan nan kuma mutu ka raba, mun shigo shi kenan fita kuma ba rana".

★★★★★

"Amma dai kin san ni ke san auran yarinyar nan shine kike wani batun wancan lusarin, yanzu da nayi magana kuma kice komai dan mu kike yi, ko ina basira a wannan tunanin naki oho, na daɗe ina faɗa miki tsufa yasa duk wata basira taki gujewa amma kin ƙi yarda, to wannan karon kam sedai kiyi haƙuri dan wallahi ba zan iya bin tsarin ki ba".

"Kai kam ai dama baka da fahimta, komai se an zauna an maka gwari gwari kafin kake ganewa, yanzu kamata yayi mu kama yaron nan a hannun mu kuma dole se ta hanyar matar sa dan ai shi ba sakarai bane da ze dawo ya yarda damu bayan duk abinda suka dinga faruwa, amma ina matar sa ta zama tamu ai ruwa tasha kaga ta nan zamu dinga samun duk bayanan da muke so a kan sa kuma mu dinga aiwatar da shirin mu a kan shi hankali kwance har mu kai shi ƙasa".

"A soke shi, ban yarda da wannan tsarin ba in har se ita zaki aura masa to a fasa".

"Zo tsaya mana jarumina, tsaya ka saurare ni kaji?".

Ta faɗa tana bin bayan shi da sauri sedai ko juyowa be yi ba balle ya tsaya saurarar ta kamar yadda take so, seda ya kai bakin ƙofar falon ya juya gare ta

"In har aka gabatar da tsarin nan tabbas za'a samu matsala dan haka kar kuce ban faɗa muku ba, a soke shi shine kawai kwanciyar hankali".

Yana faɗa ya fice yayin da dattijuwar ta dafe kanta tana koma wa bedroom ɗin da sauri ta ɗauki phone ɗin ta ta shiga dialing wasu numbers, tsawon lokaci tana ringing amma ba'a ɗauka ba har ta katse, tsaki taja ta kuma dialing, wannan karon ma kamar ba za'a ɗauka ba dan se a kusan ringing ɗin ƙarshe aka ɗauka, bata jira wani gaisuwa ba ta shiga kora dalilin kiran da tayi

"Plan cancelled, a daƙile komai a kuma tsayar da komai zuwa lokacin da zan sanar dake yanzu akwai matsala a ƙasa".

Tana gama faɗa tayi hanging call ɗin tare da wurga wayar kan bed itama ta biya cikin tunaninnikan dake yawo a kwanyar ta.

                         ★★★★★★
                         5 years later
                         ★★★★★★

Cikin sauri sauri take Rolling veil ɗin a zagayayyar fuskar ta, pin ta manna a jiki bayan ta daidaita zaman mayafin sannan ta matsa daga wajen mirrorn, rashin ganin su a ɗakin yasa ta ja ƙwafa ta kwashi bags da food flask ɗin su ta fita dashi tare da jawo ƙofar ɗakin ta sa mata key.

Ɗakin dake kusa da nata ta idasa tana ɗaya labulen

"Barka da asuba Hajiya".

"Barka kadai uwar biyu, ina dai kun tashi Lafiya".

"Lafiya lau na tashi, su kam na san tuni kin san ya suke tin da sun ƙaura nan".

"Aikuwa dai muna tare da ƙawaye tun ɗazu muna gaisawa".

"Ai yayi kyau, bari mu wuce mun kusa makara, Ibty, Ifty maza ku taho mu tafi".

"To se kun dawo, Allah ya tsare ya bada Sa'a".

"Ameen Hajiya, mungode".

Daga bayan labulen Hajiya suka fito se zarar ido suke yi dan sun san sun yi ba daidai ba, ita kam bata tsaya wata wata ba ta kama hannun su a each hand ɗin ta suka fita daga gidan.

Napep ta tare musu suka hau inda ta e ya kai ta Star light Academy wato makarantar yaran.

Juyowa tayi ta kalli Ibty dake gefen daman ta, da sauri yarinyar ta sunkuyar da kanta haka ma da ta kalli Ifty kafin kuma su haɗa baki wajen faɗin

"We are sorry Mamma".

Girgiza kai tayi ta maida hankalin ta batare da tayi responding masu ba

"Please kiyi haƙuri Mamma, Allah Ifty ce tace muje mu gaida Hajiya tun da baki gama da wuri ba".

"So Ifty ce yayar ki ko kece yayarta?".

"Ba zamu kuma ba, insha Allah Mamman musu".

"Allah yayi muku Albarka". Ta faɗa tana rungume kawun su, suma sosai suka kwanta a jikin ta suna faɗin ameen.

Ko da suka je school ɗin bata bar su ba seda ta raka su class ɗin su primary one Sannan ta tafi bayan ta sake jaddada musu zama good girls.

Cikin rashin jin daɗi ta tare wani napep ɗin ta shiga zuwa wajen aikin ta, sam bata so ba yau tayi latti, tun da ta fara aiki dasu zata iya cewa yau ne kawai ta makara amma se ta ke jin kamar ta aikata wani crime babba duba da yadda aka dinga maimaita mata rashin son makara a gare ta kasancewar tana riƙe da post ɗin secretary ɗin C.E.O na wajen baki ɗaya.

Bakin makeken building ɗin ta tsayar da me napep ta biya shi kuɗin sa ta nufi gare ɗin.

Ƙarin building me da yaji glass ta kusan ko ina haka kana kallon shi zaka bashi hawa kusan biyar ko bakwai a ƙiyasce, daga can saman building ɗin aka rubuta da manyan harufan, A.A GAMJI Company.

Kamar ko da yaushe yau ma se da aka caje ta duk kuwa da kasancewar ta ma'aikaciya a wajen wanda wannan doka ce hatta shi kan sa C.E.O ɗin in ze shiga ko so nawa ne se an caje motar sa da shi kan sa, wannan yasa kamfanin ke daga cikin manyan kamfanonin da ke da cikakken tsaro da doka.

Tun a bakin gate ta zare baƙar after dress ɗin da ta ɗora kan white hijab ɗin ta iya kafaɗa da rigar jikin itama fara iya gwiwa se dogon dark blue ɗin wando daga ƙasa, ƙafar ta kuma sanye da blue ɗin socks da takalmin ta wedge baƙi.

Da sauri da sauri ta dinga takawa batare da ta kula gaisuwar da ma'aikata ke mata ba ta wuce lifter tayi pressing kan fifth floor inda nan ne office ɗin C.E.O ɗin yake, seda tayi wani gasping air ganin yau ya rigata zuwa dan ga nan office ɗin a buɗe alamun yana ciki.

Kan table ɗin ta ta ajiye jakar ta da komai ta ƙara sa cikin office ɗin sosai da sallama, kanta a ƙasa amma yaji sautin amsawar sa can ƙasa.

Ta jima a tsaye shiru tana jiran yace wani abu da zata sami damar bashi haƙuri kan lateness ɗin da tayi sedai shiru bece komai ba kamar ba kowa a ciki se sautin Ac dake aiki a hankali.

"Ehm..am..amm..sorry sir..for the...lateness...it wasn't intentional, am sorry please".

Ta faɗa a rarrabe baki na ɗan rawa jin shiru be da niyyar cewa komai.

"Any schedule for today?".

Da sauri ta ɗago tana gyaɗa kai uwa ƙadangaruwa

"Yes...sure sir".

Ta fice da sauri zuwa table ɗin ta tare da fara ƙoƙarin ciro iPad ɗin ta, inda Allah ya taimake ta duk sanda ta zama less busy ba wai ɓata lokacin take a banza ba, a'a tana rage wasu ayyukan ne kamar wannan schedule ɗin tun jiya ta haɗa shi gashi kuwa se mata amfani.

Komawa tayi office ɗin.ta matsa gaban table ta ajiye masa iPad ɗin ta shiga yi masa bayanin schedule ɗin ɗaya bayan ɗaya, seda ta gama gaba ɗaya sannan yasa hannun sa dake cike da gargasa ya ɗau ipad ɗin yana bi, sanar mata da wanda zeyi attending yayi yayinda yace ayi postponing ragowar.

With due respect ta karɓa ta juya ta fita first office inda nan take, gyara kayan ta tayi kana ta zauna ta shiga aikin ta cike da ƙwarewa da sanin makamar aiki.

Tana nan zaune ya taho shiga office ɗin, kamar kullum cikin mutunta juna suka gaisa dashi, tana matuƙar girmama shi domin yasan mutuncin ma'aikata haka kuma ya riƙe nashi mutuncin, manager kenan HAISAM ƘADEER, babban makusanci ga CEO ɗin su da alama dan shi kaɗai ne bashi da wani shamaki na shiga office ɗin sa a duk wadda yaso.

Alarm ɗin da ya shaida mata lokacin meeting ɗin da zasu yi yayi yasa ta miƙe ta tafi duba tsaruwar wajen, komai yayi yadda ya kamata se gabatar wa kawai, komawa tayi ta sake daidaita nutsuwar ta sannan tayi knocking a ƙofar, sakanni kaɗan aka bata umarnin shiga, kanta a ƙasa ta shiga

"Its time for the meeting with Al-azhar group of companies sir".

Takardun kan tables ɗin sa ya tura mata ta ƙarasa ta shiga tattara su har ta gama shirya su tas sannan ta riƙe a hannun ta ta fice dasu.

Duban sa ya maida kan Haisam dake zaune ba shida ko alamun tashi

"Haven't you heard what she said or you're deaf?".

"Won't mind repeating sir".

Dukan table ɗin yayi da hannun sa cikin nuna ɓacin ran sa da ba wanda ke katarin yawan gani se Haisam ɗin

"For God sake ba wasa nake ba Haisam ka kuma san ba lokacin wasan bane, when it comes to business kafi kowa sanin wane ni dan akan haka zamu samu matsala, babbar matsala wallahi cos I won't mind suspending you".

"Ai fa an taɓo rayuwar ka dole bakin ka ya buɗe, dan rashin mutunci tun ɗazu nake maka magana kamin banza amma yanzu ka cika min kunne da ihu, an ƙi aje meeting ɗin in ka tashi ba suspending ba kayi firing ɗina oga sir, aikin banza kawai".

Haisam ya faɗa yana ficewa daga office ɗin bayan ya doka ƙofar da ƙarfin da har yasa salma ɗan firgita.

Fashionable wrist watch ɗin ta ta duba taga its five minutes past exactly lokacin meeting ɗin, me yake damun boss yau, shine abinda take tunani, he's always a man of his word and time, Yana mutunta lokaci ta yarda ba'a jiran sa sedai ya jira, wannan principle ɗin sa ne.

Buɗewar ƙofar yasa ta gyara tsayuwa ta yi ƙasa da kai, seda ya wuce gaba sannan ta bi bayan sa har zuwa scheduled hall ɗin, kamar yadda tayi zato kuwa kowa ya hallara hatta da manager kuwa se ita dashi ne kawai.

Wajen zaman su suka ƙarasa ya zauna ita kuma ta ajiye kayan hannun ta ta gaida mutanen wajen ta shiga gabatar da bayanan da ya kamata ta wajen ta har ta gama tsaf kafin ta zauna ana tafa mata manager ya miƙe yayi nashi ƙarin bayanin da su kaɗai suka gamsar da mutanen siyan share a Company ɗin so shi bece komai ba se negotiation kaeai da aka yi dashi.

Ya daɗe yana respecting yarinyar dan ta san ta kan aikin ta uwa uba tana da kaifin tuanni ga basira ga kuma kamewa ba kamar sauran mata da ya dinga ɗauka kan post ɗin ta ba da ko daɗe wa ba sayi yake sallamar su saboda halayyar akuyancin da suke yi......................✍🏻.




©️ Ouummey 📚✍🏻.





☑️Ote, Comment and share fisabilillah.
[12/13, 10:35 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 07 [ 11/30/2022 3:18 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★




_*PAID BOOK*_


Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.



From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*











₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.













FREE PAGE 007














________________________📖 Seda ta tabbatar an gyara an kuma rufe hall ɗin sannan ta koma bakin aikin ta.

Haka ta wuni aiki kamar yadda ta saba se in ta samu ɗan lokaci ta huta se kuma ta ɗora, ƙarfe biyu lokacin sallah yayi dan haka ta ajiye ta wuce cike da tunanin dawowa ta gyara wajen da tayi mistake.

Ana idar da sallah cikin babban masallacin Company ɗin da suke sallah ta miƙe bayan ta idar da azkhar ɗin ta ta nufi komawa ta steps Wanda haka kawai taji tana son bi ta nan dan ta motsa jiki.

A step na kusan Ashirin da something suka yi bumping into each other batare da sun lura ba, baya tayi zata gangara ya yi maza yasa hannu ya tallafe ƙugun ta yayinda itama cikin firgicin tasa hannun ta ɗaya ta riƙe rigar sa ta wajen ƙirji ɗayan kuma ta zagaye wuyan sa dashi.

Se da tayi regaining balance ya sake ta sannan ta lura da abinda tayi, da sauri ta zare hannun jikin ta na ɗaukar rawa, raɓawa yayi ta gefen ta ya wuce yana adjusting rigar sa da ta cukurkuɗa masa.

Ranar har suka tashi aiki by 4 kamar yadda suka saba she wasn't herself tana dai daurewa ne kawai.

Seda ta biya ta makarantar su Ibty ta ɗebe su dan four thirty ake tashin su kasancewar boko haɗe da Islamic school sannan suka wuce gida.

Ta daɗe kwance kan katifar su kafin tayi ƙarfin halin miƙewa ta dafa musu ruwan wanka ta musu itama tayi sannan ta dafa musu spaghetti Dan tana da soyayyar miya.

Ranar kasa gane kanta tayi dan gaba ɗaya jikin ta ya rikice kasancewar wannan karo na farko da ta taɓa samun close intimation da namiji babba kamar haka, a duk rayuwar ta tsakanin ta da maza baya baya ne ma'ana daga nesa nesa se gashi yau itace ɗare ɗare kan ƙirjin wani baligi hannun sa a cikin jikin ta.

Duk da it was an accident amma se take jin ta wani guilty, kamar wata me laifi ko wadda ta aikata wani gagarumin laifi.

Da ƙyar ta yaƙi tunanin ta shiga rayuwar ta kamar ko yaushe, ka shegari bata bari sun makara ba da wuri ta miƙa su school ita kuma ta wuce.

Tun daga bakin gate ta lura da wani irin kallo da security ɗin ke bin ta dashi kamar wata mai laifi ko kuwa irin kallon kin shiga ukun nan, sosai ƙirjin ta ke bugu ta dai daure ta shiga ƙara sawa kaina building, ko a nan ɗin ma bata canja zabi ba haka mazan wajen ke mata kallon kamar munafuka ko me fuska biyu matan kuma na mata kallon an ji kunya.

Jiki a sanyaye ta ƙarasa office ɗin sa ta gyara abinda ya kamata itace zata gyara ta gama ta koma nata, a irin kallon da mutanen Company ɗin ke mata yau se taji sam ba zata ko iya sarrafa jikin ta wajen yin wani aiki ba har se taji ba'a sin kallon hakan ya sa ta zauna jiran CEO ko manager taji gagarumin laifin da ta aikata.

Har ƙarfe tara ta wuce ba CEO ba labarin sa haka ma manager abinda bata taɓa ganin ya faru ba haka kuma ya ƙara sata cikin zulumi, se after ten sannan CEO ɗim yazo, yanayin yadda fuskar sa take a haɗe yasa ta sha jinin jikin ta ta tabbatar tabbas laifin da ta aikata maigirma ne tun bare ma da ya tsaya ya ƙare mata kallo na kusan minti biyu kafin ya shige office ɗin sa.

Be daɗe da shiga ba manager ya ƙaraso shima dai expression ɗin fuskar sa wasn't helping ko kaɗan, yau kam ko da ta gaishe shi hannu kawai ya ɗaga mata ya wuce.

Jagwab ta koma ta zauna cikin seat ɗin ta tana addu'ar ko meye Allah ya kawo mata da sauƙi ya kuma taƙaita yasa kar su kore ta daga aiki dan in suka kore ta ba bata san ina zata kama ba.

Ta daɗe tana shan wahalar neman aiki kafin ta samu wannan da ta ke ɗaukar ɗawainiyar kanta da ƴaƴan ta dashi, ta ya ba zata yi fatan kar a kore ta ba.

Kusan hours ɗaya da shigar su office landline ɗin kan table ɗin ta ta hau ƙara, manager ne ke bata umarnin shigowa office ɗin CEO ta same su, a tsarge ta miƙe ta shiga takawa zuwa office ɗin, bata jin ɗaya daga cikin su ya amsa mata sallamar da tayi dan ita dai bata ji ko tarin ɗayan su ba

"Have a seat miss Salma".

Taji muryar manager Haisam haka kuma baya Musa ba ta samu kujera ta zauna kanta a ƙasa

"Take a look at this newspaper please".

Ya sake inquiring bayan ya ajiye mata takardar kan table a gaban ta.

Hannun ta na rawa ta ɗaya ta kai kan takardar tare da juya front page ɗin ta shiga bin heading ɗin da kallo, cikin mugun sauri ta yar da takardar ta miƙe tsaye jikin ta na ɓari gaf gaf gaf kamar wadda aka watsawa ruwan ƙanƙara lokacin tsananin hunturun sanyi, girgiza kan ta ta shiga yi bakin ta na rawa tana son yin magana amma takasa, daga ƙarshe tasa hannun ta biyu ta dafe kanta tare da sulalewa ta faɗa kan sofar wajen tana ambatar kalmar innalillahi wa Inna ilaihi rajiun.

"Relax, take it easy miss Salma, everything is gonna be fine".

Abinda Haisam ya ringa maimaita mata kenan ganin yanayin da ta shiga sedai ita ba saurarar shi ma take ba

"Bani bace, it wasn't me sir, wallahi bani bace".

"Is okay, keep calm Please".

Shiru tayi tana sauke numfashi tare da ajiyar zuciya kamar wadda tasha tseren gudun kilomita dubu ko sama da haka, sedai ta fara dawowa daidai kafin Haisam ya sake mata magana

"Shin kin gane hoton nan miss Salma?".

"Bani bace sir, taya zan gane hoton da bani bace a jiki".

"Har na farkon ma bake bace?".

"Sure, babu ni ko ɗaya a nan, editing kawai aka yi aka sa fuska ta, taya ma zan iya wannan abun and with someone I do respect the most, wannan wani tuggu ne kawai na maƙiya".

"The first picture is real, kece a jiki and nima nine a jiki, it wasn't edition".

Ya faɗa for the first time tun shigowar ta office ɗin

"But taya ya zama real sir, yaushe har ma, har".ta kasa ƙara sawa

"Yesterday's accident, we accidentally bumped into each other shine aka sami wanda yayi snapping iya inda suke buƙata wajen ƙulla makircin su".

"Hasbunallah wani'imal wakeel". Ta faɗa tana dafe kanta dan ita se yanzu ma ta tuna da abinda ya faru jiyan dan tun da ta tursasa kanta mantawa bata kuma yarda ta tuna ba sam.

Tsawon lokaci suna zaune shiru bame magana kafin Haisam yayi cutting silence ɗin

"He'll marry you".

A firgice ta ɗago jin wani sabon batun yashin hankalin

"Who, how, why?".

Ya jero tambayoyi ukun a tare, duk yadda suke cikin tashin hankali seda Haisam ya murmusa ganin yadda ta kiɗime da jin batun har ma fiye da lokyda ta ga hotunan

"Firstly, lemme answer your question why, ko kun san a garin nan ba inda wannan jaridar bata shiga ba lungu da saƙo inda jama'a ke ta zagi da tsine muku ke da boss ɗin naki, a dalilin haka ba abinda zaki yi da ze dakushe batun se aure dan kullum maƙiya da mahassada zasu sami sabon abin faɗe ne akan hakan kuma duk ɓacin suna ne gare ku musamman shi da yake harkar kasuwanci ya kuma zama sananne, tun farko na ke kawai kin taka sawun ɓarawo ne amma ɓacin sunan wa shi ake nema nake ba.

For your question how, to yadda ake kowane aure haka kuma za'a yi naku in less than a month insha Allah.

For the last question, who, the answer is Alh ABDALLAH ABDULSALAM GAMJI.

Hope I answered all your questions?".

Gana ɗaya she's totally speechless, ita a bayanan sa ba kowanne ta gane ba, tukunna ma Who's Abdallah Abdulsalam Gamji?

"But sir who's with the name da ka faɗa yanzu?".

"Your boss here, the CEO A.A.Gamji company".

Zuwa yanzu kam bata da abin cewa, to me kuma zata ce.

"Kiyi haƙuri, auren ne kawai ze zama solution dan a yadda aka ɓata miki suna nan da shekara goma na bana jin akwai namijin da ze yarda ya aure ki, dan dai baki karanta abinda aka rubuta bane, yanzu ki sanar damu a ina zamu sami magabatan ki".

"Bana tare dasu, ina rayuwa ni kaɗai da ƴaƴana a gidan haya".

A hankali ya buɗe idon sa ya zuba kan Haisam irin me wannan take nufi, kau da kai Haisam yayi

"Na fahimta, sedai su ɗin a ina suke dan kin san dole a wajen su za'a nemi auren ki".

"Ƙauyen BA MUNI sedai bana tunanin zasu saurare ku dan ni ɗin korarriya ce".

"Bangane ba, korarriya kamar yaya?".

"Nayi aure ina secondary school batare da sanin su ba inda na haifi ƴaƴana biyu, bayan mun gama WAEC muna shirin zuwa gida mijin ya gudu se ni kaɗai na koma da ƴaƴan shine suka shegan ta su suka buƙaci in ba da su akai inda ban sani ba dan gujewa abin kunya acewar da naƙi shine suka bani zaɓin bada yaran ko kuwa barin su nikuma na zaɓi ƴaƴana".

Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Haisam da Abdallah inda kowa da abinda yake kitsawa a ransa, ture komai dake ransa Haisam yayi

"Ina ce dai ƴan garin ku sun san wannan labarin in Kuma na faɗa za'a gane ke nake nufi?".

"Sosai ma kuwa".

"Shikenan za ki iya tafiya yadda ake ciki kuma zan sanar dake".

Miƙewa tayi zata fita ya dakatar da ita

"Ji nan, rabon ki da garin naku shekara nawa yanzu?".

"Shekara biyar da watanni".

Da kika shigo garin nan a ina kika fara zama, ko kuwa kuna da ƴan uwa ne?".

"Sam ban san kowa ba a nan, na fara zama a gidan haya da nake zaune har yanzu".

"Waye yayi sponsoring karatun ki".

"Ni na ɗau nayin kaina da sana'ar haɗa turaren wuta da na dinga yiwa wata ƴar Maiduguri tana rarrabawa a faɗin Nigeria gaba ɗaya".

"Sunan product ɗin fa?".

"Ƙamshin amarya".

"You can go". Fita tayi tana sauke ajiyar zuciya jin wasu tambayoyi daga boss ɗin ta kamar wani ɗan jarida, bata taɓa sanin yana magana haka me tsayi ba se yau, ita bata ga wani point ba a auren ta da suka ce ze yi, ita da sun ƙyale ta dan sam ita aure baya gaban ta balle mazan gaba ɗaya sedai dole saboda ƴaƴan ta da suka kasance mata tana buƙatar garkuwa irin ta ɗa namiji wanda ba ta inda zata sama musu ita se ta hanyar auren.

"Amma meye point a tambayoyin da ka dinga yiwa yarinyar?, Beside Ina cewa kayi bayan komai ya lafa zaka sake ta?".

"In shi kuma yaje ya jiyo abinda mu bamu sani ba a kanta ya riƙe matsayin makamin hana auren fa?".

"You so stupid man, ya Ina tambayar ka kana maida min tambaya matsayin amsa?".

"And what did I say wrong?".
Dunƙule hannu Haisam yayi ya kai masa duka a kafaɗa shi kuma ya goce yana sakin silent smile na ganin yadda ya harzuƙa Haisam ɗin wanda ba wanda ke iya tolerating halin sa se shi kaɗai da Allah ya sallaɗawa so da ƙaunar sa.

"Please bawan Allah let's be serious, kaga wannan auren ina so ya faru at all cost ko banda hatsaniyar jaridar nan har ma da jama'ar gidan ku, na rasa gane wace irin cukurkuɗaɗɗiyar rayuwa ce ke faruwa a gidan ku, da na zauna nayi tunani dole se da mace a tare da kai zamu fahimci kome ke tafiya dan na tabbatar wanda suka farmaki nafisa zasu sake yunƙurowa tun bare ma in ya zama kai ka samo matar da kanka".

"Rayuwar gidan mu bahaguwar rayuwa ce da hatta ni da nake cikin ta ba komai nake fahimta ba, abu ɗaya na sani shine kowa mara gaskiya ne, kowa macuci ne haka kuma kowa mugu ne shiyasa na zaɓi na rayu on my own haka kuma bana don shigar da kowace ƴa cikin haɗarin dake tattare da rayuwa ta dan maharana suna da yawa Haisam, dalilin kenan da na haƙura da aure amma for now

Please Login or Register in order to submit comment