Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi kukan ta har ta gaji baccin yunwa ya ɗauke ta kafin itama ta haƙura ta goge fuskar ta ta maida ta baya dan ba zata iya riƙon hannu ba ta cigaba da tafiya.

Se da rana ta faɗi gaba ɗaya kafin ta shiga wani ƙaramin ƙauye dan gaba ɗaya gidajen dake ciki basu fi a ƙirga ba haka kuma daga ganin gidajen su kasan har yau su kam suna cikin duhun rayuwa wato ba wayewa ko ta misƙala zarratin dan duk bukkoki ne ba gidan ko ƴar jar ƙasa ɗaya.

Kan wani kututturen dabino ta kai zaune tana ajiyar zuciya tare da numfashin ta dake fita ɗaiɗai saboda wahala da jigatuwa, nan take zaune har se da wani tsoho ya zo wucewa ya ankara da ita kafin ya ɗan matsa nesa da ita ya shiga ƙare mata kallo Sannan ya gyaɗa kai ya wuce.

Be daɗe ba ya dawo dashi da wasu dattijan da kuma matasa suka dinga magana da Yaren su da bata san wanne bane kafin ɗaya daga cikin matasan ya nufi ta.

Tambaye ce daga ina take, me ta shigo nema a shiyyar su, me take buƙata haka dai, amsa ta bashi da sunan garin su wato BA MUNI wanda sunan ya samo asali ne daga yadda duk wani ɗan garin yake kyakkyawa sedai wani yafi wani amma mummuna kam babu sedai ko baƙo shiyasa suke saurin gane baƙo a cikin su.

Iyayen sa ya koma ya sanar da amsar da ta bashi, sunan garin su da kuma taimakon da tace ta zo nema, seda suka kuma sake zantawa cikin dai Yaren nasu kafin wani saurayi ya tafi be daɗe ba ya dawo da wata tsohuwa sedai ba tukuf ba, nuna mata ita suka yi inda ita kuma ta ƙarasa ta kamata ta miƙe kuma cikin fara'a tace mata

"Kunto min jikokin nawa mana, da alamu sun daɗe a goye".

Bata ƙi ba ta kunto Hassana ta bata ta bar Ussaina

"Ita ma sauko ta ta huta hakana".

"Tana da kuka ne Inna".

Murmushi innar tayi alamun ta gane kafin suka shiga tafiya hannun ta dafe da zanin ta dan cikin sa ta ɓoye jakar ta da zasu je wajen Maigari ashe Allah ne yayi suna da rabo da yadda kawu iro yace ba zata koma masa gida ba shikenan sun salwanta.

Bukka ce me ɗan girma suka shiga sedai abin mamaki har dasu gadon ƙarfe a cikin ta, fita Inna kamar yadda ta kira tsohuwar tayi bayan ta kwantar da Hussaina tsawon lokaci tukunna ta dawo da bahon katako a hannu, ruwa ne masu zafi a cikin sa haka kuma ba fari bane da alamun an zuba wasu abubuwan banda kuma ganyayyaki dake ciki, tuɓe Hassana tayi ta mata wanka da yasa yarinyar ta ringa sauke ajiyar zuciya a jejjere, Ussaina kam ta sha ihu da ana yi mata dan alamu sun nuna ba su taɓa shiga ruwa masu zafi haka ba.

Se da ta tabbatar sun gasu kafin ta ɗau abin ta fice inda Salame ta yi saurin isa ta ɗau yarinyar ta shiga jijjiga da lallashi har tayi shiru,

"Ga can ruwa ki je kiyi wanka kema ko kya watsar da gajiya".

"Toh Inna".

Tace tana kwantar da Ussainar a hankali gudun kada ta tashi daga ɗan baccin da ya fara sanɗar ta............................✍🏻.




©️ Ouummey 📚✍🏻.

☑️Ote, Comment, share and patronize fisabilillah.
[12/13, 10:35 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 05 [ 11/27/2022 9:24 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★


_*PAID BOOK*_


Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.



From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*







₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.









                    FREE PAGE 005










_________________________📖 A sittin ta runtse ido tana taune leɓen ta sabida zafin da ya ziyarce ta ita kuwa Hassana da zaƙuwa take zuƙa tana sauke ajiyar zuciya har ta ƙoshi kafin ta saki.

Se lokacin ta buɗe idon ta da ya ɗan canja kala ta kalli yadda yarinyar ke numfashi a hankali a hankali tana ciccilla ƴan ƙafafuwan ta tare da wasa da hannayen ta se ta ji wani sabon farin ciki ya kamata har ma taji zafin ya tafi.

Zanin ta ta gyara a ƙirji ta miƙe ta saɓa ta a kafaɗa ta shiga jijjiga ta dan tayi gyatsa, a haka baba Husaila ta tadda ta se ta kwantar da Ussaina ta karɓi Hassana ta fita da ita a kafaɗa ita kuma ta koma ta zauna tare da ɗaukar Ussaina.

Haka ta shayar da ita itama sedai ba kamar Hassana ba Ussaina akwai ci dan se da ta daɗe kafin ta ƙoshi hakan ma se da ta canja mata ɗayan shiyasa gaba ɗaya ƙirjin nata ya ɗume da zafi.

Tun daga lokacin take shayar dasu amma duk da haka baba Husaila na haɗa musu da ƴan dabaru musamman Ussaina da ta fahimci yarinyar akwai tsotso in aka barta bata ƙi ta wuni da nono a baki ba.

Iya ƙauna da mutuntaka baba Husaila da ƴan uwan ta sun gwada mata, Abinci da abin sha bata taɓa rashin su ba, ga kula da ita da ƴaƴan ta da suke yi tun bare baba dan ko rigimar Ussaina ce ta tashi da dare bata bari ta tashi cewa take ta koma tayi kwanciyar ta ita kuma tayi ta fama har se tayi bacci tukunna hankalin ta ze kwanta.

Ruwan wankan su kuwa kullum se ta sa musu magani shiyasa alhamdulillah jikin su yayi ƙwari se fatar su da ta ɗan dafe saboda zafin ruwa da kuma kalar magani duk da yanzu sun fara sabawa da zafin ruwan.

Sannu a hankali har ta cinye wata ɗaya tare dasu basu ankara ba saboda zama da yayi daɗi, jakar ta kuwa baba ta adana mata dan ce mata tayi da su ne za'a bar ta ta shiga makarantar in taje, yadda ƴan uwan baba ke son ta ita abin har mamaki yake bata, wai yau ita Salame da kowa ke gudu itace yau ake so ko da yake ai ba ita ake so ba ƙaunar ƴaƴan ta ce ta shafe ta dan haka be kamata tayi wani kauɗi ba.

Mace ɗaya ce ta taɓa son ta a Karan kanta yadda take wato Hajiya Hadiza principal ɗin su, Allah ya sani tana son matar a ranta irin son da bata san yadda zata kwatanta shi ba.

Ta so ta a lokacin da kowa ya ƙi ta, ta bata gatan da bata taɓa zaton samu ba, a bayyane yake badan ita ba da ba zata taɓa samun damar karatun da take so ba, ita ta ɗau ɗawainiyar komai na makarantar ta, kuɗin PTA, uniform, littattafai, takalmi, Safa, abinci da komai da zata buƙata a makaranta tun da ta fara kuwa bata gaza ba har wata ɗaya da kwanaki baya da ta gama, ita kuwa ai sedai tace da ita Allah ya saka da kuma ya zame mata wajibi ta so ta.

Kallon baba Husaila dake zaune gaban ta tana mata lissafi kawai take yi yayin da idanun ta suka tara ƙwalla, kuɗi ne daga kan ƙwandala zuwa na takarda wai wanda aka haɗa mata dan tafiya makarantar su da zata yi duba mijin ta in yazo (kamar yadda tace musu).

Hannu ta sa ta share hawayen

"Dan Allah baba ki maida musu kuɗin nan kin ji, zan fa iya zuwa da ƙafa".ta faɗa murya na rawa

"Amma dai salamatu baki da kirki, ya za'a yi mutum yayi alkhairi a maida masa, to kul kar in Kuma ji ko ke kin yi hakan kin ji ko?".

Da kai ta amsa wa baba kafin ta shiga yi musu godiya da addu'a kamar Allah ne ya aiko ta har se da baban ta gaji ta fice ta bar mata ɗakin.

Tuhumar kanta take kan me yasa tayi masu ƙarya gashi su kuma sun yarda da ita sun zauna da ita da zuciya ɗaya, jaddada wa kanta take Allah ma ya sani ba'a san ran ta tayi ƙaryar ba, bata so a raba ta da yaranta ne kawai.

Da wannan ta tattara kuɗin da suka tasamma dubu ɗaya ta zuba cikin jakar makarantar ta, ta kuma haɗe kayan ƴan biyu ta ninke ta zuba cikin jakar su ta rakuɓa nata kala huɗu da take dashi.

Kashegari tayi sallama dasu cikin rashin daɗin rai dan har da kukan ta haka ma baba Husaila da ta zauna wajen ta, ji take kamar yarinyar ta dawwama tare da ita dan bata da matsala sam, yarinya ce me kirki ga ladabi da biyayya, gata ba har dama, ga nutsuwa da rashin ƙyuya, duk sanda taga ta tashi aiki bata bari tayi komai se karɓe ta shiga yi shiyasa so da yawa ma bata tashi yi saboda tasan ba zata bari tayi ba.

Su kuwa ragowar ƴan gari da matasan su ƴaƴan ne suke jin kamar su ƙwace ta tafi ita kaɗai dan sun shiga zuciyoyin su barin ma Hassana da bata da rigima, in aka fita da ita har se an tausaya an dawo da ita dan bata kuka se dai in ko Bata da lafiya ko kuwa ta kai maƙura wajen jin yunwa, toh haka dai aka rabu kowa na mararin kowa, rayuwar kenan!

Ganin tana da isassun kuɗi a hannu se kawai ta tare mota bayan ta fita sarari, sunan Makarantar su ta faɗa masa suka yi ciniki ta hau ya kai ta har bakin gare kuwa.

Wajen baba megadi ta bada ajiyar jakar kayan su ta wuce office ɗin Hajiya Hadiza wato principal, ba abinda ya dawo da ita makarantar illa son karɓar sakamakon ta tare da certificate ɗin kammala karatun ta dan tana so a duk inda taje ta ɗora karatun ta dan shine burin ta tun bata san ze iya cika ba ko kuwa ze rushe ne har zuwa lokacin da ta fara hasashen cikar sa wato da maigari ya sanya baki a kan karatun.

Ba kaɗan ba Hajiya Hadiza taji daɗin ganin Salame wadda ke amsa sunan Salama kamisu a makarantar, cikin nutsuwa ta bata takardun ta da WAEC result ɗin ta dan dama alƙawari ne tayi mata ana sakin result zata bada a ciro mata nata.

Cikin ikon Allah tana da credit bakwai da excellent biyu, Salame kam har dasu kukan godiya ga Allah dan ta san shi yayi mata komai ba wai ita ba haka kuma ta sanadin wannan matar me kyakkyawar zuciya ne wato Hajiya Hadiza, godiya kam haka ta dinga zuba ta tana yi tana hawaye lokacin da take faɗa mata ga Form nan na College of Education ƴan gora, wata local government a babban garin da ƙauyen su yake ta cike ta mata submission in tana so ita Kuma zata biya mata komai, da ƙyar ta iya tsayar da kukan ta sukai sallama ta tafi.

Se da ta tsaya ta karɓi kayan ta wajen Maigadi ta ma sallama tukunna ta wuce, mota ta tara zuwa tasha inda batare da tunanin komai ba ta biya motar garin GAMJI dan a can ne makarantar da take son yi take.

Motar na cika aka fara tafiya inda ita kuma ta fara nata tunanin kan irin rayuwar da zata yi a can ita da yaran ta dama yadda rayuwar karatun ta zata kasance, shafa Form ɗin da Maah Hadiza ta bata ta sake yi tare da lumshe ido tana ayyana batutuwa da yawa a ranta.

Zata cike Form ɗin tayi submitting a can makarantar a karan kanta batare da jiran Maah Hadiza ba dan bata jin nan kusa zata kuma komawa koda hanyar ƙauyen BA MUNI ne, da kanta zata tsaya wa kanta tayi komai sedai ta yaya tunda ba kuɗin hakan ne da ita ba, gashi yanzun nan in bata manta lissafin da Maah take mata na kuɗin da za'a kashe kusan dubu sha biyar ne, registration goma da ɗari biyar ragowar kunji kunji kuma su cinye sauran.

A ina zata samo wannan kuɗin ita da ba ta da kowa bata da kuma komai?

Wannan shine tunanin Salame yayinda mota ke ta tsuga gudu a titi, ragowar passengers kowa da abinda yake yi, wasu hira, wasu kallo, wasu karatu wasu kuwa bacci.

Itama dai cikin tunanin ta da yake kakare mata sanadin rashin abokan rayuwa wato kuɗi nata baccin ya saɗaɗa saɗaf saɗaf yayi wuf! Yayi gaba da ita.

Hayaniyar da ta cika wa kowa kunne ce ta sanar da masu barci an iso in da zasu wanda Salame na cikin su, miƙa tayi a hankali ta kalli Hassana dake ɗaure a gabanta tana baccin ta hankali kwance, tun da aka fara tafiyar bata yi wani rigima ba se Ussaina da ta ɗan yi kuka ta kunto ta ta bata tasha ta kuma maida ta bayan ta ɗan bata ruwan leda da ta saya guda biyu tun a can tasha kafin su tashi.

A hankali ta sauka daga motar hannun ta riƙe da jakar kayan su ɗayan kuma jakar makarantar ta da ta saka Form da ragowar takardun ta a ciki.

Tun da ta sakko taji ana shelar kowa ya kula da jakar kuɗi ko kayan sa saboda ɓarayi ta kuma damƙe jakar makarantar a ƙirjin ta ɗayar kuwa ta mata riƙon da tasan ba me iya fincike ta a hannun ta ta sauƙi.

Tunanin inda zata nufa ta shiga yi se kuma ta tuno yadda suka yi da Maah Hadiza da ta tambaye ta ko ina zata zauna in ta zo karatun tace mata ai duk me napep ɗin da tace ya kai ta gidan haya ze kaita dan ba ya wahala a garin GAMJI.

Bakin tashar ta fita taƙi kula duk me napep ɗin dake cikin tashar dan bata yarda dasu ba, suma zasu iya zama ɓarayi ne, a nan titi ta sami wani tace ya kai ta gidan haya.

Seda suka fara tafiya ya tambaye ta gidan mutane da yawa ko kaɗan

"Kamar dai biyar ko bakwai".

Amsar da ta bashi kenan shima be kuma magana ba ya shiga tuƙa abar sa cike da ƙwarewa, wata unguwa ya shiga mara wadatacciyar tsafta ga nan gidaje a wajen ba fasali se uban yara da suka cika layin jikin su ba kyan gani.

Gaban wani gidan bulo yayi fakin tare da nuna mata gidan

"Ko a layin in kika lura gidan na cikin gidaje masu kyau haka ma ɗakunan su suka da yawa megidan ma a nan take rayuwa a ɗaki ɗaya, yanzu dai bani kuɗi na in tafi".

"Tsaya dan Allah, nawa ake biya na hayar?".

"Wata shida dubu uku shekara kuma dubu shida".

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sauka tare da fidda kayan ta ta bashi Naira hamsin ɗin shi ya tafi.

Cikin ɗari ɗari gaban ta na faɗuwa ta shigar da kayan zauren gidan ta shiga doka sallama kamar sabuwar warkewar makanta

"Kai haba wannan wane irin bala'i ne tun ɗazu ake ta waalaikumussalam amma dan baƙin rashin mutunci an ƙi shigowa, to dan Allah mutum ya ɗige a wajen ƙarƙari in na gaji in ɗau taɓarya in jirge mutum dan na gaji da iskancin ƴan unguwar nan, me ake da gidan haya ni saratu ban da dai ƙaddara".

"A ƙaddarar dai ya rufa miki asiri in ba haka ba mutum ya fita titi mana ya kwanta, se shegen baƙin faɗin rai yawa ƴar ƙaruna, naga kuɗin hayar ma har yanzu ina bin ku ciko amma har kika samu bakin kankanba ".

Salame dake zauren banda zarar ido ba abinda take yi jin sabuwar duniyar da ta shigo yau da rana tsaka, a gidan hayar ma wato dai ba hutawa mutum ze yi ba, ya baro masifar dangi ya shiga masifar wasu mutanen daban kuma.

"Bismilla, ina me sallama ta shigo in ga kowace da kuma me ya kawo ta tunda Allah ya rufa asiri yasa nidai ba'a sanni da cin bashi ba".

"A'a Hajiya wannan magana taki kuma me kike nufi, ina ce faɗan ku tsakanin ke da saratu ne to me kuma ya shigo da ni ciki?".

Matar ɗaya ɗakin ta yi but ta fito tana faɗin haka acewar ta Hajiya ita take neman faɗawa magana da tace ba'a san ta da cin bashi ba.

"Ai ba zan yi mamaki dan kin yi uwa kin yi makarɓiya a zance na ba Huwaila, in ma Baki yi magana ba ai se a canja miki suna, to ni dai na faɗa ba'a sanni da cin bashi ba sedai in ke aka biyo dan kece gandun bashi mara haƙuri da kaɗan a gidan nan".

Turo ɗankwali gaba Huwaila tayi da alama zata karta rashin mutunci ne se kuma ga Salame ta shigo dan ta gaji da tsayuwa ta kuma fahimci da ɗaiɗaya da ɗaiɗaya wannan maganar se ta fiddo duk matan gidan ita kuma ba zata iya jumurin su gama ba, so take ta sami wajen sauke yaran nan ta huta.

Kallan kallo aka shiga yi tsakanin ta da magidanta biyu wato Hajiya da kuma saratu se kuma matashiya ɗaya wato Huwaila,

"Dama nace a kai ni gidan haya zan kama ɗaki shine aka kawo ni nan".

"Aiho Allah sarki, ashe abin arziƙi ne ya same ni saratu da Huwaila ke neman yi min tawaiwai, shigo baiwar Allah ai nice me gidan ɗaki kuma Allah ya soki akwai ɗaya da masu shi suka tashi".

Ajiyar zuciya Salame ta saki tana ɗaukar jakar ta ratse Huwaila da saratu ta shige ɗakin Hajiya da tace ta shiga.

Ruwa me sanyi ta bata ta sha kafin tayi mata bayanin kuɗin ɗakin da ya ragu be kai sauran ba dan duk shine ƙarami dan haka zata bada dubu biyu wata shida dubu huɗu kuma shekara se ta zaɓa in sunje ta ga yayi mata.

Buɗe ɗakin tayi suka shiga a tare sedai gani kaya a ɗakin yasa Salame juyowa ta kalle ta

"Wanda suka saki ɗakin basu sami kwashe kayan su bane?".

"To ni dai abin ne da mamaki, ganin gida suka tafi basu dawo ba dama sun ce min ba lallai su dawo ba dan haka suka kwashe kayan sawar su, wannan kuma suka ce in suka rufa wata uku basu dawo ba to sun bar min, yanzu kuma ana batun watan su na shida kenan basu dawo ba, ina ta son ɗaukar kayan ina kuma tsoro amma tun da gaki ga yara kuma naga baki taho da komai ba se ki yi amfani da kayan sedai zan ɗau ƴan abubuwan amfani da nake so acikin kwanikan".

Saroro tayi tana bin Hajiya da kallo kamar wadda bata gane abinda tace ba, se da Hajiyar ta taɓa ta sannan ta sunkuyar da kai

"Amma Hajiya daga gani na yau har se ki bar min duk wannan kayan arziƙin bayan ke aka bawa?".

"Kin shiga ɗakina fa kin gani mene bani dashi da zan ce zan ɗauka?, wanda nace ɗin ma sha'awa ce kawai irin ta ɗan Adam amma gwargwado ai Allah yayi min suttura, kinga ki kwantar da hankalin ki ni ba haka nake ba dan haka ki shiga ɗaki in har yayi miki gobe zaki bani kuɗi na".

Tana faɗa tayi gaba abinta Salame ta bi bayan ta da kallo tana murmushi, da alama matar zata yi daɗin zama ɗan alamu sun nuna bata da ƙyashi da hassada haka kuma bata da san kai.

Jakar su ta shigar sannan ta shiga ta tsaya tana sake bin ɗakin da kallo, labulaye masu kyau kuma sababbi, fenti me kyau ga katifa ma me taushi da tudu, flower vase ƙarama a gefe, dustbin, tiles, carpet ƙarami tabarma nannaɗe a tsaye ga kuma wardrobe madaidaiciya itama a gefe.

Hamadala ta shiga yi tana hawaye kafin ta kwance yaranta ta shimfiɗe kowacce kan zanin ta ta shiga gyara ɗakin..........................✍🏻.



©️ Ouummey 📚✍🏻.




☑️Ote, Comment and share please.
[12/13, 10:35 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 06 [ 11/27/2022 9:29 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★


_*PAID BOOK*_


Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.



From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*









₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.









                      FREE PAGE 06








_______________________📖 Seda ta Gama gyara ko ina dan dama ƙura ce kawai a ɗakin sannan ta lura da ƙaramin toilet tsayuwar mutum ɗaya, wanke shi shima tayi da ruwan da Hajiya ta bata jarka biyu ta roƙe ta gawayi ta ɗora musu ruwan wanka.

Ƴan biyu ta fara yi wa wanka sannan itama ta samu tayi, bata iya ta nemi abinci ba ta kwanta bacci saboda gajiya.

★★★★

"Haba bawan Allah, ya kamata a ce ka saurara wa kanka wannan ɗimbin damuwar, fisabilillah shikenan kai in aka ga fara'a a fuskar ka sedai fake, ka sake kayi rayuwar kamar kowa ka ƙi, in ance dalilin da yasa rayuwa take zamar maka baibai kuma kaƙi yarda".

A hankali mutumin da aka kira da bawan Allah ya shiga ɗago kan sa daga sunkuye da yake har ya ɗago baki ɗaya.

Tsurawa wanda ya gama magana ido yayi na wasu sakanni kafin ya miƙe tsaye yana duban agogon hannun sa, bece masa komai ba ya shiga tarkata takardun sa ya zuba cikin briefcase sannan ya fita.

Baki buɗe ɗayan mutumin ya bishi da kallo kafin kuma ya gyaɗa kan sa ganin yau iskancin bawan Allah har a kan sa, halin sa ne dama Amma ze iya rantsewa ya manta rabon da ya karta masa in ba yau ba.

Fita yayi yana sanar da masinjan sa ya kulle office ɗin shima ya fita, kamar yadda yayi tsammani be ga ko shatin tayar motar sa a parking space ba, tasa ya shiga ya bar building ɗin shima.

★★★★★

'Ban san wane irin aiki na tafka ba, ban san wace irin ƙwaƙwalwa gare ni ba da kullum bata bani mafita miƙaƙƙiya, duk da Riyya ta faɗa min nayi gaggawa in jira tukunna amma ni gani nake in na zauna to zan ta jira ne har na gaban abada, in bana son haka ya faru me zanyi kenan, me zan yi?!'

Wannan shine tunanin da matashiyar ke tayi tana kai kawo a madaidaicin falon da yaji kayan alatu da alama dai tana cikin state of confusion ne dan se cije yatsun hannunta take cikin son samun mafita.

Shigowar wata dattijuwa ɗakin yasa ta nemi kujera ta faɗa kamar wadda bata da laka, kallon ta dattijuwar tayi tana kaiwa zaune itama kan wata kujerar kafin ta shiga mata kallon tambaya

"Yanzu shikenan Anna mu haka zamu zuba ido muna kallon komai na faruwa a gidan nan, ki duba fa watan yaya nawa yanzu da rasuwa amma ba wanda ke bin takan mu ke kuma naga ma abin ko ɗaɗa ki da ƙasa be yi ba".

"Ni kin sa ba wani gane magana cikin magana nake ba gwara ki fito fili ki sanar dani me ke faruwa a gidan bamu sani ba".

"Amma Anna kin san in mukai sake mun kusa barin daular nan mu koma kwana ƙarƙashin gada ko?".

"Tuf tuf, Allah ya tsare ni.....". Anna ta faɗa tana tofar da miyau a gefe

".....banda neman masifa da bala'i irin naki me yakawo batun komawa ƙarƙashin gada kuma da ko a mafarki na gani in na tashi se na yi sadaka".

"Nima ba so nake yi ba sedai in dai bamu motsa ba abinda ke daf da faruwa kenan".

"Dan Allah yi min dalla dalla dan kin san bana san jan rai a magana".

"Kamata yayi ace nice Abdu ze aura amma muna nan mun zuba ido yanzu

Please Login or Register in order to submit comment