Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗimbin goron da suka siya a garin na ɗaurin aure, basu kai gida ba se wajejen goman dare, Haisam ya fara saukewa kafin yayi masa godiya ya wuce gida shima.

**********

"Ina sam ba zan bari haka ya yiwu ba wallahi, taya ya yaran nan ze shammace ni haka bayan ina nan ina shirin aura masa shuraiha, kai dole ma ita ce aura dan ba zan yi sanyar ya ɗauko wata a waje ba, nasan duk ma wannan fuffukar ta banza ce dan haka bari gobe tayi zan yi wa tufkar hanci, auren nan da sati za'a yi inga ta tsiya".

Hajiya Babba ta faɗa wa kanta cikin tabbatar da abinda zata iya taba kaiwa zaune cikin sauke ajiyar numfashin samo mafita da tayi, ta daɗe tana zaune ƙafarta ɗaya kan ɗaya tana karkaɗawa ciki sake zurfafa tunani har dare yaja kafin ta haƙura ta kwanta bayan ta sake maimata shawarwarin da ƴaƴan ta suka babbata ta ɗau na ɗauka ta watsar da na watsarwa.

********

"Anna da zafi zafi fa akan daki ƙarfe ya kamata gobe kije ki sami baba ki Masa magana kan meze hana na maye ɗakin yaya ta, kinga wancan karon shi ya Abdu yace a bar zancen tukunna amma yanzu ai yaci ace a tada maganar, shekara takwas za'a shiga ta tara da muke, kar mu tsaya garin kallon ruwa kwaɗo yayi mana ƙafa".

"Bari haka za'a yi, shi Abdallahn zan fara kira nan nayi masa kuka ta yarda baze Musa min ba kinga da kan sa ma se ya kai zancen naku can wajen baban nasa ta yadda ba wanda ze zargi ni nake son tusa ƙi ko".

"Sosai ma kuwa Anna, wannan idea ɗin tayi, bari in je in kwanta Allah ya kaimu goben da rai da lafiya".

Da Ameen Anna ta amsa mata yayinda ta shige ɗakin kwanan ta dake part ɗin marigayiya yayar ta nafisa da suka gaje tun bayan mutuwar ta.

A can kuwa baiwar Allah salma ta tasa ƴaƴan ta a gaba tana kallon yadda suke bacci hankali kwance ba abinda ke damun sa yayinda ita take cikin damuwa, damuwar da bata san dalilin ta ba wadda haka kawai take samun faɗuwar gaba duk ta tuno boss ɗin ta da auren da yake batun zasu yi, aure kuma kwana kusa in less than two weeks abinda bata taɓa shiryawa ba balle ta zauna tsara yadda ze kasance.

Alwala ta ɗaura ta shimfiɗa sallaya ta shiga nafiloli tana kaiwa Allah kukan ta kan ya shige mata gaba, seda ta gaji kafin ta zauna ta ɗau ƙur'ani ta shiga karatu har seda ta ji bacci yaci ƙarfin ta kafin ta rufe tayi addu'a ta kwanta.

Safiyar Laraba yazo wa mutane da dama cikin wani irin yanayi, ga salma wani irin nauyi take ji a ƙirjin ta da kanta kamar wadda ta aza dutsen dala a kanta, yaran kansu da ƙyar ta iya shirya su dan har se da suka makara yau, jiki ba ƙwari ta rakasu ajin su ta koma ta tare wani napep ɗin zuwa wajen aikin ta.

Ko da taje ta tabbatar boss ya rigata zuwa amma yau bata ji wannan fargabar ba illa wani nauyi da ta tuno sunan sa da abinda ke ƙoƙarin shiga tsakanin su.

Seda ta ajiye jakar ta da files ɗin hannun ta ta gyara wanda zata kai masa Sannan ta ƙwanƙwasa ƙofar, amsa mata da akayi tareda bata izinin shiga ya sa ta buɗe ƙofar ta shiga ta ƙara sa gaban table ɗin sa ta ajiye masa files ɗin duk da bata gan shi a kan kujerar sa ba, juya tayi da zummar fita amma ya dakatar da ita daga cikin inner office ɗin sa kan ta zauna ta jira shi, zama tayi ta shiga bin office ɗin da kallo a hankali cikin admiration, office ɗin ya daɗe yana birge ta ba tun ba yau ba yadda ba'a cika masa shirgi da hauragiya ba amma komai a tsare fes wajen da ya kamata.

Cikin haka ta sauke duban ta kan ƙofar inner office ɗin dake buɗe ko kafin ta kai ga ɗauke idon ta tuni ya bayyana cikin shadda riga da wando ɗinkin tazarce sedai maɓallayen wuyan a buɗe suke yana gyara su, haɗa idon da suka yi yasa ta maza ta sauke nata gaban ta na faɗuwa, iya zaman ta a Companyn zata iya rantsewa yau ne ƙwayar idon su ta shiga cikin na juna dan indai tana gaban sa kanta ya kan kasance a ƙasa ne har se sanda ta bar wajen sa shiyasa ba zata iya cewa ga cikakkiyar ainahin kamannin sa ba dan kwarjinin sa kaɗai kan hana mutum iya kallon sa fuska da fuska.

Idon sa a kanta ya shiga takawa har ya ƙarasa ya ja kujerar opposite ɗin ta ya zauna tare da ɗaukar wayar sa ya shiga kiran Haisam

"Kasan tafiyar da zamu yi da tsawo amma kabar mutane na jira?".

Yana gama saurarar abinda yace ta can ɓangaren ya kashe wayar tare da ajiyewa ya shiga gyara agogon hannun sa, files ɗin ta jawo ta shiga yi masa bayani cikin mamakin yau kam be da niyyar zama kan kujerar sa sedai tuni ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu se kuwa taja bakin ta ta tsuke.

Ƙwanƙwasa ƙofa masinjan sa yayi ya bashi izinin shigowa, leda ya ajiye masa cike da girmamawa sannan ya juya ya fita, ledar ya jawo ya buɗe tare da kallon kayan ciki sannan ya tura mata gaban ta

"Ki shiga ciki ki canja wannan uniform ɗin dan ba zan iya tafiya dake dasu a jikin ki ba".

Binsa tayi da kallo har ya fice kafin ta sauke ajiyar zuciya, ta canja kaya to akan me, ina ruwan sa da kayan jikin ta ko basu ne suka bata a matsayin kayan aikin ta ba da yau ze kawo mata wani sabon sanaben ta canja.

Haka dole ba dan taso ba ta ɗau ledar tare da shiga toilet ɗin sa ta cire kayan jikin ta ta maida wannan, doguwar riga ce ta mata se mayafin ta, kayan coffee and milk se suka yi mata kyau sosai dan tana da hasken ta daidai gwargwado.

Cikin ledar ta fito tana ninke uniform ɗin ta zuba su ta sake neman kujerar da ta tashi ta zauna

"Mrs Gamji bismilla ko".

Haisam ya faɗa daga ƙofa bayan ya buɗe, da rashin fahimta take kallon sa jin sunan da ya kiraye ta dashi yau

"Muje salma, inda zamu ba nan kusa bane".

Jiki ba laka ta miƙe ta bi bayan shi dan har ya fita, Allah ya sani bata san zuwa ko ina da su tunda ba muharraman ta bane haka ba wani cikakken sani tayi musu ba banda na wajen aiki yanzu kuwa mutum abin tsoro ne bare ma ita da bata da galihu ba wanda ze tdaya mata in wani abu ya same ta.

Gaban mota Haisam ya buɗe mata, cikin ɗarɗar ta shiga tana me karanto addu'a a bakin ta, wani irin sanyi ne ya ratsa fatar jikin ta na Ac dake tashi yayinda hancin ta ya shaƙo mata daddaɗan ƙamshin turaren motar da na jikin sa da suka gaurayu suka bada wani launi na ƙamshi daban.

Rufe murfin Haisam yayi ya koma ya buɗe bayan motar ya shiga, tada motar Abu Aulad yayi suka fita daga Companyn yayinda ma'aikata ke aikin kallon su sedai shi kam ko mutum ɗaya be nuna yasan da zaman shi ba balle ya kalle shi.

"Garin ku fa zamu je Madam".

Da sauri ta shiga ta kalli Haisam da yayi maganar kafin ta juyo ta kalli Abu Aulad da idanun sa ke bisa titi, bakin ta na ɗan rawa ta furta

"Taraba, suna school, ba wanda ze je ɗaukan su".

"Ba ze yiwu muje mu dawo kafin su tashi ba?".

Da sauri ta girgiza kanta,

" ƙarfe huɗu suke tashi".

"Ze yiwu muje har mu dawo". Da sauri ta shiga girgiza kanta

"A'a nidai mu tsaya a ɗauke su, ba zan iya tafiya in bar su ba, pleaaseeee".

Ta faɗa wannan karon directing to Abu Aulad

"Ya sunan Makarantar?".

"Star light Academy".
Be Kuma cewa komai ba ya saki hanyar da yake kai ya ɗauki wadda zata kai shi makarantar da ta faɗa.

Har ciki ya shigar da motar sannan ta fita zuwa wajen principal, uzuri ta bayar kan dalilin da yasa za'a ɗauki yaran, be Musa ba ya yarje mata dan yaran ta are one of their daily and punctual students da basa fashi sake da ƙwaƙƙwaran dalili.

Rungume su tayi a tare lokacin da suka fito daga aji kafin ta ja hannun su zuwa wajen motar suna ta yi mata surutu.

Tun da suka tunkaro su ya kafe yaran da ido cike da sha'awa da muradi, sha'awar dama nasa ne, muradun samun kamar su ya cike ransa.

Buɗe musu bayan motar tayi suka shiga a hankali sannan ta sa musu lunch box ɗin su, gaishe da Haisam suka yi inda suka kira shi da uncle batare da sun lura da Abu Aulad ba se da ta nuna musu shi

"Babies, baku gaisar da other uncle ba".

"Yes, baku gaishe da daddy ba". Haisam ya gyara mata da sauri

"Mamman wai daddy ne da gaske?".

Gyaɗa musu Kai tayi a sanyaye dan bata so yace daddy ba, in suka girma suka san ba daddyn su ne ba fa.

Da sauri Ifty da tafi ƙiriniya dan itace Ussaina ta tsallake ta shiga gaba tare da faɗawa kan shi tana tsallen kiran Daddy

"Daddy dama mamma tace Mana kayi tafiya ne, daddy yanzu ka dawo kenan?".

Da murmushi a fuskar sa ya gyaɗa mata kai tare da shafa fuskar ta cike da shauƙi, juyawa yayi ga ibtisam da tayi tsaye ya ruƙo ta itama ya zaunar kan sa, wasa wasa seda suka ɓata kusan 30 minutes sannan suka tafi bayan yaran sun koma baya kusa da Haisam ita kuma ta koma mazaunin ta.....................✍🏻.



©️ Ouummey 📚✍🏻.




☑️Ote, Comment and share fisabilillah.
[12/13, 10:35 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 10 [ 12/1/2022 1:07 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★


_*PAID BOOK*_


Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.



From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*












                     FREE PAGE 010





LAST FREE PAGE!!!

This is the last free page, make your payment and continue enjoying the movies else you'll be left behind 😜!

₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card to 09013101854, note VTU is not acceptable.




________________________📖 Shiru na ƴan wasu sakanni kafin ya motsa bakin sa

"Na so ki tare yau sedai baze yiwu ba tunda munyi dare but be ready gobe da safe insha Allah zan zo mu wuce".

Tsrewa, yau, gobe da safe, wucewa, gaba ɗaya bata gane ma'anar wannan kalaman ba.

It may sound funny ko kuma a ɗauka rainin hankali ne but dagaske a wannan lokacin manta ma'anar su tayi, sam bata gane me yake nufi ba haka yasa tayi saurin yin magana

"Wucewa, gobe, zuwa ina?".

Seda ya kalle ta sosai kafin ya kau da kai trying not to look at her face again, tun lokacin da ya ga ƙwayar idon ta a ƙauyen su yaji yana sha'awar sake gani, so yake ya tantance wane kala ne da eyeballs ɗin ta tunda ya tabbatar ba baƙa bace sedai baya san ta ɗau hakan da wata manufa shiyasa yake kauda Kai

"Nace ki tattara abubuwan da kuke buƙata na iya suttura zaki koma gidan auren ki gobe insha Allah".

Zuwa yanzu kam she's speechless dan ba zata ce bata gane me kuma yake nufi ba yanzu tunda gwari gwari yayi mata, ita kam ta rasa a wane layi zata ajiye wannan auren nata, da neman auren da ɗaurawa duk cikin kwana ɗaya zuwa biyu aka yi su, yanzu kuna ga tariya, a al'adar malam bahaushe dangin amarya kan haɗu su rakata gidan auren ta cikin soyayya da ƙauna amma ita gata ana batun tariyar daga ita se mijin ta da ƴaƴan ta, lallai auren ta wani iko ne na Ubangiji.

A hankali ta saci kallon sa cikin son furta abinda take so sedai bata san ya akayi ta tsinci harshen ta da furta abinda ba shi ne a zuciyar ta ba

"Allah yasa zamu ga goben da rai da lafiya".

Ameen ya faɗa daga nan kuma suka cigaba da zaman shiru, ita bata ce komai ba shi ma haka, tsayin lokaci har ta gaji da zaman ta gyara amma bashi da niyyar cewa komai

"Ki taso yaran mu tafi".

"Mu tafi, ina kenan bayan dare kuma yayi, its almost ten fa".

"And me kike nufi da zaman da kike yi a nan?".

Wani irin tuƙuƙin takaici ne ya cika mata maƙogaro, daga ɗazu zuwa yanzu ta fahimci mutumin nan wani bahago ne na daban, ko saboda ba wani kusanci ne tsakanin su na daban ba a office maybe shiyasa bata San hakan ba tuntuni.

Bata ce komai ba ta fita daga motar tare da maida murfin ta rufe masa ta wucewar ta cikin gida tana gunguni ita kaɗai.

Seda ya ga shigar ta gidan sannan ya tashi motar ya fita daga layin cike da sanyin jikin da gajiya ta haifar masa, wannan dogon tuƙin da yayi jiya da yau sam be saba masa ba shiyasa gaba ɗaya jikin sa yayi masa nauyi.

Kulle motar yayi ya fita batare da ya kula ganin ta da yayi tsaye ba, da sauri tabi bayan sa har tana haɗawa da gudu saboda takunsa irin na cikakkun maza ne masu isasshiyar lafiya

"Yaya Abdu, ya Abdu".

Yana jin ya tsaf amma yayi mata banza hakan yasa ta kuma kwasa da gudu tasha gaban sa lamarin da ya tilasta masa tsayuwar dole sedai tuni ya sake ɗin ke fuska tsaf kamar wanda be taɓa sanin wani abu wai shi annurin dariya ko murmushi ba a duniya.

"Dama Anna ce ke neman ka, tuntuni nake kiran wayar ka in faɗa maka yaƙi shiga, gashi ita kuma se kuka take da kiran sunan yaya nafi wuni guda yau taƙi cin komai".

"Kije ki faɗawa baba".

"Zuwa yanzu ya kwanta yaya Abdu, Please ka taimaka kazo muje kayi mata magana ko zata ji, na bata baki amma taki saurara ta".

Sam baya son kallon ta sabida irin shigar dake jikin ta, duk da kasancewar dare ne amma gidan nasu tarwai yake da haske da ko allura ce ta faɗi tsaf mutum ze tsugunna ya ɗau abar sa ya tashi.

Tun ba yau ba yasan ita da yayar ta nafisa Allah ya ji ƙan rai kamar gabas da yamma ne, sam bata inda suka yi kamanceceniya se ko ta fuska da kuma jini shiyasa ko da sam be sake mata fuska balle ta samu damar kawo masa raini bare kuma yanzu da yake jin kowa ma daidai yake dashi.

"Kije zan zo in nayi wanka, nayi gumi da yawa I can't go to her a haka".

Ya faɗa yana wuce ta cikin tafiyar nan tasa me cike da karfi da isa, bin bayan sa tayi da kallo cike da maɗaukakin shauƙi, lumshe ido tayi tare da rungume hannuwan a ƙirji inda take ji kamar shine ta rungume, wannan maganar da ya mata ji take kamar an mata albishir da shiga aljanna.

Tun yayar ta na da rai take so da ƙaunar yaya Abdu sedai tayi ta ƙoƙarin dannewa, yanzu kuwa da babu yayar ta bata tunanin akwai abinda ze tsayar da ita kuma.

A saɗaɗe ta juya zuwa part ɗin su, bakin ƙofa ta tarar da anna tsaye, da sauri ta riƙo hannun ta suka ƙara sa ciki kafin ta dube ta

"Yaya, cewa yai baze zo ba?".

"Yace zezo amma se yayi wanka, dawowar sa kenan baze iya zuwa gare ki a haka ba".

"Kai masha Allah bari maza in shafa rob ɗin nan a ido na ɗan suyi ja su dinga hawaye, insha Allah buƙatar mu zata biya bari ki gani".

Tsohuwa Anna ta faɗa tana murza Rob a fuskar ta, duk yadda idanun ta ke hawaye be sa ta fasa ba se da ta saka sosai ta yadda in ka kalle ta zaka ce ta daɗe tana kuka dan yadda fuskar ta tayi jajir kasancewar ta fara haka ma idanun ta suka yi ja suka tasa.

A can ɓangaren Hajiya Babba kuwa da sauri shuraiha dake tsaye jikin window riƙe da curtains tana kallon abinda ke faruwa tsakanin Abu Aulad da Nuriyya ta saki uban ashariya

"Kan uba".
Ta faɗa da sauri tana sakin curtains ɗin, bata tsaya wata wata ba ta zura bedroom slippers ɗin ta tayi waje without minding cewa kayan bacci ne a jikin ta ba, burin ta a lokacin shine ta kai gare su taji me suke tattaunawa a wannan tsohon daren.

Baza tayi sanyar da wata can daban zata ƙwace mata Abdallah ba bayan an gama kwaɗaita mata shi tare da lasa mata zuma a baki yanzu kuma a ce za'a janye, ina ba zata yarda ba.

Sedai kash ko kafin ta kai ga fita daga part ɗin su tuni ya shige nasa part ɗin ita kuma Nuriyya ta koma nasu hakan yasa ko da ta fito compound ɗin bata tadda kowa ba se ma'aikata dake ɗan kai kawo dan wasun su ma tuni sun nemi makwanci.

Haka ta koma part ɗin nasu tana cizon yatsa, taso taji me waccan karuwar ke faɗa masa wanda har ya tsaya saurara haka sedai kash bata samu ji ba, ya zama dole ta tunzura Hajiya Babba ayi ayi ai bikin su ko hankalin ta ya kwanta, daga lokacin da ta sami wannan damar a lokacin ita kanta Hajiya babbar zata raina kanta dan kallon ta kawai take itama da tata tsarin da buƙatar akan Abdallah ɗin.

A hankali yake rage kayan jikin sa cike da gajiya, wanka yake buƙata yake kusan sanyi dan yadda yake jin jikin sa na ƙaiƙayi shine kawai abinda se yi yaji sauƙi.

Singlet ɗin jikin sa yake ƙoƙarin cirewa se kuma ya fasa sanadin hango inuwa da yayi jikin labulen sa alamun akwai wani laɓe a ta wajen.

Cikin nutsuwa ya shiga takawa har ya kai wajen yasa hannu ya yaye curtains ɗin da suka rufe tagar, tsaye take cikin shaiɗanun kayan da dasu da babu a jikin ta basu da wani banbanci, suna haɗa ido ta sake masa wani arnen murmushi cike da barikanci kafin cikin kwarkwasa ta shiga lauya jikin ta tana magana da wata seducive voice

"Sannu da zuwa Abu Aulad, ga dukkan alamu ka gaji, don't mind I can takeaway all your stresses, yanzu dai muje kayi wanka ko super man?".

Kamarw anda garwashin wuta ya taɓa haka yayi watsi da hannun da takai jikin sa, ya rabbal alameen be san ya zai yi da rayuwar sa a cikin wannan gidan da a wajen sa gara kabari dashi ba.

Wani irin birkitaccen mafi ya watsa mata da yasa ta yin katantanwa ta faɗi can gefe kanta ya bugu da jikin Centre table ɗin dake falon, cikin wata irin zuciya da ta ciwo shi ya bita yasa ƙafa ta taka sangalalin hannun ta har se da yayi ƙarar dake shaida alamar in har bata sami fracture ba to tabbas ƙashin nan ya fita daga bigiren sa.

Wani wahalallen ihu ta saki da be wani fita da karfi ba saboda tsabar wahala yasa a take Muryar ta ya shaƙe, cikin wani dakusasshen Muryar da ɓacin rai ya haifar masa ya shiga yi mata concrete warning

"This is the first and last time da zan kuma ganin ki a part ɗina, na rantse da Ubangijin da ya busa min rai da second time na kuma ganin ki zan iya ɗaukar ranki dan ko banza an rage mugun iri, annoba kuma jinin shaiɗan, before the count of three ki fice min ɗaga ɗaki in ba haka ba wallahi rataye kibzan yi jikin fanka, fitsararriyar fasiƙa kawai mara kunya da tsoron Allah".

Ai ko kafin ya gama bayanin sa tuni ta tarkata hannun ta tayi waje da mugun sauri dan a yadda ta gan shi da kuma rashin imanin da ya gwada mata ta tabbatar ze iya rataye tan kamar yadda ya faɗa.

Da numfarfashi da komai takai kanta part ɗin ta zube kan kujera tana maida numfashi, wani irin zufa ne ke keto mata na wahala da azabar da take sha a jikin ta, bata taɓa sanin haka zafin karaya yake ba se yau.

Ƙwalla take zubar wa tana bin hannun da kallo yayinda cikin ranta take shan mugayen alwashi kala kala a kan shi, tun da ta riga ta ɗora ido a kan shi takuma kwaɗaitu da shi ta rantse ita kuma se ta same shi, in kuwa ba haka ba to tabbas sedai ayi biyu babu uku ba ko ɗaya ma'ana indai ba zata same shi b ato sedai kowace mace ta rasa.

Da sauri ta runtse idon ta lokacin da ta auno shi a idanun ta tare da wata mace, inaaa, ba'a haifi macen da zata amfane shi ba, ada dai tayi wannan imanin amma a yanzu zata iya yin komai in tace komai tana nufin komai wajen ganin ta saka kyakkyawar barrier tsakanin sa da duk wata ƴa mace kowace ita kuwa.

Ranar haka ta kwanan cikin azaba da raɗaɗin zuci da na jiki, ga dai jinya ya kwantar da ita kuma wai batare da ya bari ta amfanu da komai daga gare shi ba, ita da ta samu abinda taje nema to da sauki ba karya ta ba ko kashe ta yayi ba zata damu ba tunda ta cika burin ta.

A ɓangaren Abu Aulad ma haka ya kwana a zaune cikin wani irin yanayin da baze fassaru ba, be san da wane suna ze Kira gidan da yake ciki ba haka be san da wane suna ze kirayi mutanen cikin sa ba, be taɓa sanin bawa kan zaɓi mutuwa kan rayuwar sa ba se a kan shi, da ace kisan kai ba haram bane a musulunci da tuni ya daɗe da sheƙe kan sa ya huta.

Tun tasowar sa be san wani abu wai shi farin ciki ba, kullum cikin baƙin ciki da damuwa yake tun fara wayo sa har kawo yanzu da yake shekarun sa na cikakken namiji mai ji da sabon jini da ƙuruciya.

Rayuwar sa a hagunce ta faro kuma har kawo yanzu a haka take, be san se yaushe ne ze samu daidaito na rai, ruhi da rayuwa ba balle har ya samu salama, a duk sanda yaga mutane na rayuwa suna dariya da nishaɗi ya kan tsinci kansa da ayyana dama shine, so da yawa yasha kusan yin saɓo in ya zauna tunani dan ya kan dinga aiyana me yayi wa Allah da yasa ƙaddarar jarabawar tazo a haka, me yasa ba wata daban ba.

Kiran sallar asuba da ake yi ne yasa shi miƙewa yana dafe kan sa dake sara masa ya shiga toilet, daga tsayen da yake ya sakarwa kansa ruwa masu sanyi sanye da wandon shaddar da singlet ɗin batare da ya cire ba, tsayin lokaci Sannan ya gabatar da wanka ya ɗaura alwala ya fito.

Jallabiya ya zura a jikin sa tare da ɗaukar tasbah ɗin sa ya wuce masallaci, seda aka idar da sallah har gari yayi haske kafin ya taho gida.

Jiri yake gani dan rabon shi da abinci tun na safen jiya kafin su tafi ƙauye ga kuma rashin bacci sedai kasancewar tsayayyen namiji ba wanda ze fahimci hakan se wanda yayi masa sani na sosai.

Wata jallabiyar ya canja kawai ya ɗau key ɗin motar sa zuwa gidan su, ɗauko ta ze yi dan se yayi hakan hankalin sa ne kwnata, mutanen gidan su are so cunning, gwara tun kafin su farga yayi outsmarting ɗin su ya shayar dasu mamaki ya kuma basu tsoro ba kuma ta kowace hanya ba se ta kawo macen da ya nema wa kan sa auren ta cikin gidan.

Ya sani in da mace a tare dashi abubuwa da yawa zasu masa sauƙi sedai matsalar shine shin itama irin su ce, wane assurance yake dashi na ba zata zama kamar su ba, shin in aka mata tayi da zunzurutun kudi ko matsayi zata karɓa ko kuwa?!.

Wannan

Please Login or Register in order to submit comment