Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya zama dole in miƙe in har zata shiga rayuwa ta ko da na kwanaki ne kuwa".

"Me kake gani, mu bata hutu zuwa lokacin da komai ze tabbata ta fara amsa sunan matar ka ko yaya?".

Relaxing yayi cikin kujerar da yake kai yana lumshe ido

"Kasan meye damuwa ta?, Ƴaƴan ta, bana san a cutar da kowanne saboda ni, bana a ringa cutar da yaran da basu ji ba basu gani ba saboda wani ƙiyayya da ake min".

Ya ƙarashe yana buɗe idanun sa da lokaci guda suka canja kala zuwa jajaja brownish

"It hurts, it deeply hurt Haisam".

Ya faɗa yana dafe ƙirjin sa ɓangaren hagun sa alamun yana masa ciwo

"Calm down Abu Aulad, calm down insha Allah ba abinda ze same su".

Rufe idon sa yayi tare da kife kan sa kan table ɗin gaban sa ya shiga ajiyar zuciya akai akai tare da haɗiye wani ƙullutu me matuƙar ɗaci da ke taso masa duk sanda ya tuno yara, yana matuƙar san yara a rayuwar sa hakan yasa ake masa Indiya da Abu Aulad tun yana saurayi, da ya zama magidanci kuwa yayi aure burin sa da fatan sa ya haihu ne kawai, lokacin da Allah ya bawa matar sa ciki irin murnar da yayi ba me misaltuwa bace sedai Allah be nufa rayayyu bane daga uwar har ƴaƴan.

Miƙewa yayi ya zafi key ɗin sa ya fice da sauri kamar ze tashi sama haka ma Haisam ya bi bayan sa, yau dai kam ba abinda suka tsinana....................✍🏻.




©️ Ouummey 📚✍🏻.




☑️ Ote, Comment and share fisabilillah.
[12/13, 10:35 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 09 [ 12/1/2022 1:04 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★


_*PAID BOOK*_

Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.



From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*











₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.











                     FREE PAGE 009



₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.






_________________________📖 tafiya ce sosai daga Gamji kafin a kai ƙauyen Ba muni dan har se dasu Ibty suka gaji da kwaramniya suka yi bacci a jikin Haisam dake baya a tare dasu.

Ita kam salma wani irin nervousness da faɗuwar gaba ne ya sarƙe ta, after good five years da barin ta gida yau gashi zata koma kan mau'idin da bata san wanne bane, abu ɗaya ta sani shine akan maganar auren ta ne aka tashi tafiyar.

Motar shiru baka jin tashin komai se numfashin su a hankali a hankali da kuma gudun Ac dake tashi, Haisam kam wayar sa yake pressing hankalin sa kwance yana chat abinsa da budurwar sa yayinda a ta gaban motar kuwa tamkar wasu kurame ko saƙaguna haka suke zaune.

Shi tuƙin sa kawai yake ita kuwa ba abinda take se bin hanya da kallo kamar me irga bishiyun da suke wucewa, tunanin yadda zata riski garin bayan shekara biyar da tayi bata cikin sa take, maganar tarba kuwa tasan ba wata tarba da zata samu a wajen ƴan uwan mahaifin nata.

Abu ne ba ɓoyayye ba cewa murna da jin daɗi suka yi lokacin da ta zaɓi barin su saboda ƴaƴan ta, irin wulaƙancin da suka yi mata na ƙin barin ta ta ɗau ko tsinke a gidan be bar kanta ba kuma bata jin ze barin har nan da gaban abada.

Wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta saki lokacin da suka shiga garin tana me lumshe ido cikin kiran sunan Allah a ranta, a kaikaice ya kalle ta dan sosai ajiyar numfashin nata ya fito fili.

Gidan maigari ya nufa kamar jiya, seda duk suka fita daga motar suka barta dan ji tayi gaba ɗaya kamar bata da wani sauran laka a jikin ta, jikin yayi mata nauyi kamar baya tare da ita, Haisam da ya lura bata biyo su bane ya juya ya tabbatar sannan ya maida kallon sa kan Abu Aulad

"Madam fa bata fito ba, ina ganin kaje kaji ko da damuwa ne ni Bari in ƙarasa ciki". Ya faɗa yana yin gaba da sauri dan yasan kaɗan daga aikin bawan Allah yace shi yaje ya duba.

Ganin yadda ya tafi yabar shi a wajen yasa cikin takaicin abinda tayi kamar wata ƙaramar yarinya ya koma wajen motar, murfin ɓangaren da take zaune ya kama ya buɗe da ɗan ƙarfi dan ransa ya ɓaci da abinda tayi, ya zata wani nemi waje ta zauna a mota bayan tasan suna da abubuwan yi da yawa a gaban su.

A ɗan firgice ta buɗe idon ta da ke lumshe hakan yasa suka yi wani walai kafin suka shige cikin nasa da ya tsare ta dasu, da sauri ya kau da kan sa dan jin wani dam da gaban sa yayi ganin ƙwayar idon ta, be taɓa sanin haka ƙwayar idon ta take ba se yau,

"Kina jira a ɗauke ki ne kafin ki fito?".

Tsam tayi jin abinda ya faɗa dan bata gane me yake nufi ba

"Malama ki fito mu yi abinda ya kawo mu dan ba kwana zamu yi ba kin sani ko?".

Ƙafarta dake ajiye gaban motar ta ɗaga a hankali ta fitar waje kafin ta fara ƙoƙarin fitar da gangar jikin ta hakan yasa aya matsa daga tsayuwar da yayi jikin motar, seda ta gyara mayafin kanta sannan ta yi gaba shi kuma ya kulle motar da mukulli bayan ya buɗe glass ɗin baya kaɗan saboda su Ibty dake kwance suna bacci.

Gaba ɗaya ido mutanen wajen suka zuba mata suna kallo yayinda ƙananan maganganu ke tashi dan jiya da yawa da suka san abinda ya faru da ita da suka ji batun ɗaurin auren ta ba ƙaramin tu'ajjabi suka yi ba barin ma da suka ga zuƙeƙen mijin da Allah ya bata.

Yanzu kuwa ba wai sun gane ta bane maganganun kan irin kyan ta da kuma na kayan jikin ta ne, ƴan gayu irin ta dasu Haisam ba kasafai suke shigowa garin ba shiyasa duk sanda suka shigo suke zama abin kallo da sha'awa ga jama'ar garin.

A hankali ta saluɓe brown heel shoe ɗin dake ƙafarta ta kai zaune kan shimfiɗar fadar maigari kafin cikin sanyayyar Muryar ta ta shiga gaida shi kamar yadda suke yi a al'adance.

Cikin rawar jiki maigari ya amsa duk da bai shaida cewa Salame bace, a tunanin sa wata ce daga dangin su ɗan birni suka zo da ita tare maybe dan taga mahaifar matar da ya aura ko wani abu.

"Ala gafarta malam, ga Salman nan gaban ka mun zo da ita dan kayi mata bayanin yadda auren ya ƙullu jiya a kuma bata sadakin ta dan ta shaida".

"Ikon Allah, yaro kana nufin nan Salame ce a gabana, lallai Allah mai iko, sannu Salame, sannu kinji".

Maigari ya faɗa cikin ruɗewar jin wai wannan tsaleliyar budurwar ce Salame da suka kora da goyon ƴaƴa biyu shekara biyar da suka gabata, yarinyar da ko da ta bar garin ba komai gare ta se tarin tsumma dan hatta takalmi babu a ƙafarta ranar.

"Nice baba maigari, fatan mun same ku lafiya".

"Lafiya lau salamatu, ya yaran naki? Ko kin bar su a gida ne?".

"A'a baba suna mota bacci suka yi shiyasa ba'a ɗauko su ba".

"Allah Sarkin hikima, yanzu sun girma abin su ko, hekara biyar ai ba nan bace dole yanzu sun girma".

"Aikuwa dai". Ta faɗa tare da jan bakin ta ta tsuke ganin surutun na maigari bame ƙare wa bane ita kuma ta zaƙu taji bayanin da aka ce yayi mata da in ba kunnuwan ta ne basu jiyo daidai ba kamar taji ana batun an ɗaura mata aure ne tun jiya

"Wato salamatu jiya yaran nan suka zo nan suka same Ni da batun neman auren ki, duk da ko a Shari'a ni me bayar da auren ki ne amma se na bawa iyayen ki haƙƙin su ta hanyar sawa a ka kira su na shaida musu abinda ke shirin aukuwa sedai dake Habibu ba ɗan bana da arziƙi bane se yace shi sam babu shi a lamarin ki haka ma iro, se Adamu ne shi dake wani sa'in yana da tunani ya saurari yaran nan amma yace sedai in a ɗaura auren a jiyan dan baze juri a Kuma tado shi daga wajen sana'ar sa domin ki ba wannan yasa dole aka ɗaura auren bisa sadakin da shi mijin ki ya biya wato dubu hamsin gashi nan a zaune, yanzu bari in tashi in ɗauko su gare ki, kin ji yadda batun ya kasance".

Wani irin suya zuciyar ta ta shiga yi cikin ƙirjin ta jin irin cin kashin da ƴan uwan mahaifin ta suka aikata yayin neman auren ta, shin me ta kashewa mutanen nan ne da suke neman se sun wulaƙanta ta ido rufe?, Shin akwai ɓoyayyen dabi ne tsakanin mahaifin ta dasu ko kuwa, su dai ba ƴan uba ba balle tace ƴan ubanci suke gwada mata, ko kuwa duk ƙiyayyar mahaifiyar ta ce ta shafe ta har haka.

Hannu tasa ta goge hawayen da suka gangaro kan kuncin ta daidai lokacin da maigari ya miƙawa Abu Aulad sadakin ta shikuma ya ajiye mata kan cinyar ta, murya na rawa ta shiga magana

"Nagode sosai baba, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara girma sedai Ina son ganin su baba habibun game da gado na dake wajen su".

"Babu komai salamatu, ke ɗin ai ɗiya ce gare ni, abinda ya faru a baya ma saɓanin fahimta da kuma zugar iyayen ki ne, yanzu bari in aika su zo se ayi batun gadon naki".

Ɗaya daga cikin dogaran sa ya aika azo dasu baba Habibu dukan su, ba'a jima ba dogarin ya dawo tare dasu suna bin shi abaya se ƙunƙuni suke na yadda ake shiga rayuwar su kan wata banza can Salame da suka daɗe da tsamewa matsayin jinin su.

Gaban maigari suka zube suka yi gaisuwa, salma ya nuna musu bayan ya amsa ya shiga kora musu bayani

"Ga Salame nan mijin ta ya kawo ta na mata bayanin auren su da aka ɗaura jiya se kuma gashi tazo da batun gadon ta dake hannun ku tana neman a bata kason ta".

Maigari ya ƙarashe yana gyara saɓa hannun babbar rigar jikin sa tare da furzar da tiƙar goran dake bakin sa, ido waje baba Habibu da ƴan uwan sa ke kallon tsaleliyar budurwar da aka nuna musu wai Salame, cikin rashin yarda baba Habibu ya furta sunan ta

"Salame".

"Na'am baba barka da rana".

Ta faɗa tana buɗe idanun ta sosai a kan su dan su san fa yanzu ba da bane da take shakka da tsoran su, cikin sanyin jiki baba iro yai gyara zama dan ƙwayar idon ta kawai ya kalla ya shaida ita ce.

"Dama nace gadon baba na dake hannun ku nake buƙata baba dan Ina son yin amfani dashi".

"Eh to, gado ko, tabbas kam kamisu ya bar gado sedai yana wajen Adamu ai bani ba".

Da sauri baba Adamu da yaji baba Habibu na neman zame wa ya bar shi a ciki ya buɗe baki

"Ina ce gona ce kawai a wajena Habibu?".

"Ai dama ita nake nufi, am ke Salame sedai fa kiyi haƙuri dan kiwon da ya bari tuni babu su, da su ne mukai ta amfani wajen ciyar dake har zuwa lokacin da kika bar wajen mu dan haka gona dai tana nan ban da ita kuma babu komai". Ya faɗa yana kai da kai gefe cikin rashin gaskiya.

Girgiza kai akwai tayi dan tasan ba wani an ciyar da ita an cinye ne kawai babu su yanzu, gonar ma tasan ban da albarkacin yanayin da ya ganta na wadata da kuma waɗanda ke tare da ita da baze bayar ba itama cewa ze yi an siyar an kula da ita.

"Allah ya amfana gonar, sedai ina da buƙatar ta ujila zan yi amfani da ita".

"Amma ina ce kinji ance tana hannun Adamu, shima amfani yake da ita dan haka sedai kiyi haƙuri, gona na mazaunin taki amma ya riga yayi shuka dan haka se yayi girbi se ki karɓa".

Cikin rashin tsoro ko shakka ta dubi baba Habibu dake maganar cikin hatsari da gadara

"Zan bar tane sabida a hannun baba Adamu take banda haka bana jin da wani ne ba shuka ba kome yayi se dai ya kwashe ya kai inda yake dashi tun da dai gona mallaki nace".

Daga baba Habibu har baba iro tsumu suka yi cikin kunya dan sun san da su take, wato da ba Adamu bane dole a bata a bar ta, lallai yarinyar nan ta goge.

Abu Aulad da yaji an kawo matsaya ya miƙe dan tuni yake kallon agogon hannun sa, baya san suyi dare kamar jiya dan a tsarin sa a yau yake son ta tare a gidan su dan ya nuna wa duk wani dake tunanin ce iya juya shi ko iko dashi ƙarya yake, be isa ba kuma be kai ba, anyi a da amma banda yanzu!.

"Mungode sosai, ga wannan a siya horo, Allah ya ƙara girma, ku tashi ku tafi ko?".

Ya faɗa yana ajiye wa maigari bundle ɗin ɗari bibbiyu, miƙewa tayi tana adjusting pin ɗin mayafin ta da taji ya ɗan matse ta, har bakin mota maigari ya raka su inda su baba Habibu suka zama ƴan kallo, Haisam ne ma yayi tunanin basu ƴan canjika dan shi uban gayya ko kallo biyu basu samu daga gare shi ba.

Tun jiya mutuncin su ya zube tsaf a idanun sa saboda abinda suka yi, me ɗan daman cikin su ne baba Adamu dan shine kawai ya samu gaisuwa daga gare shi.

Haisam na buɗe bayan motar Ibty ta fito tana mutsittsika ido tare da tura baki gaba cikin son fashewa da kukan rashin ganin Mamman ta, da sauri Salma ta riƙo hannun ta tare da jawo ta gaban ta.

Duƙawa tayi zuwa tsayin yarinyar ta cire mata hannun ta dake kan fuskar ta, ɗaga mata gira tayi tare da jan kumatunta tana sakin mata murmushi itama yarinyar ta maida mata sannan ta shige jikin ta tana sakin ajiyar zuciya, seda ta tabbatar ta dawo daidai sannan ta kama hannun ta ta buɗe gaban motar zata shiga baba maigari dake kallon su ya magantu

"Masha Allah, tubarkallah, hala wannan ɗaya daga cikin yaran ne salamatu?".

"Eh baba, Hassana ce Ussaina na bacci bata tashi ba".

"Allah Sarkin hikima da buwaya, tubarkallah yarinya kyakkyawa kamar ƴar turawa, Allah ya raya yayi musu Albarka, Allahu Akbar da girma yake".

Da Ameen ta amsa masa tare da shigewa motar dan shima tasan borin kunya ne ya ke yi na abinda yayi mata lokacin da tafi buƙatar taimakon su shiyasa duk wani rawar ƙafar sa be ɗaɗata da ƙasa ba.

Numfashi ta sauke na samun relief lokacin da motar su ta fara tafiya kan burjin har ƙasar dake garin, tasbih tare da godiya kawai take yi cikin ranta wa Ubangiji da ya canja mata rayuwa daga wata mara ma'ana zuwa wadda take ciki yanzu.

Nauyi taji ƙirjin ta yayi mata lokacin da ta tuna cewa yanzu fa ita ɗin matar aure ce, matar Abdallah Abdulsalam Gamji shugaban fitacaccen kuma shahararren kamfanin A.A Gamji.

Bata san wace irin rayuwa ce kuma ke jiran ta nan gaba ba a gidan auren ta sedai tana fata koma wace irin ce ta zo mata da sauƙi, akasin haka kuma Allah ya bata wuyan ɗauka ya kuma yi riƙo da hannun ta wajen ganin ta samu mafita akan dukkan matsalar da zata tunkaro ta.

Ta daɗe da sanin ita rayuwar gaba ɗaya jarrabawa ce, gwaji ce da bawa ba zai daina samun shi ba har se lokacin da rai yayi bankwana da gangar jiki wadda ranar ce ba wanda ya sani tunda ita mutuwa ba sallama take ba haka kuma ba wai notice take bayarwa ba bakuna allo ne da ake rubuta jadawalin sunayen mutanen da zasu tafi yau, gobe jibi da ma kullum ba.

Cikin wannan tunanin suka shigo garin Gamji, tafiyar ba kamar ta ɗazu ba yanzu kam hira ce suke yi shida Haisam jefi jefi yayinda ita tayi nisa cikin duniyar tunanin da take yi tana daga zaune rungume da Ibty a jikin ta.

Haisam ɗin suka fara saukewa inda suka yi sallama da abokin nasa kuma shugaban sa kan se sun yi waya yayinda cikin nutsuwa ya cigaba da driving motar har zuwa gaban gidan su da bata san yaushe ya sani ba kuma ya wa ya sanar dashi ba.

Parking yayi a ƙofar gidan, ganin yadda ya kai kai gefe yasa ta shanye mamakin ta ta buɗe ƙofa Ibty ta fita zuwa cikin gidan ita kuma ta zaga baya ta ɗau Ifty dake bacci har lokacin ta kai ciki wajen Hajiya dan bata samu zarafin tsayawa buɗe ƙofar ɗakin su ba ta koma gare shi.

Gefen ƙofar da ta fita ta tsaya tare da duƙar da kai ƙasa

"Mungode sosai Allah ya huta gajiya, a gaida gida Allah ya tashe mu lafiya".

"Shigo".

Kallon shi tayi tana sake nanata kalmar shigo ɗin da yace, to ta shiga tayi me bayan yanzun nan suka dawo tare dashi?.

Ganin kallon da ya ɗago ya jefa mata yasa bata san sanda ta kai zaune kan kujerar motar ba sedai ƙafafun ta na waje...............................✍🏻.

©️ Ouummey 📚✍🏻.

☑️Ote, Comment, share and patronize fisabilillah.
[12/13, 10:35 PM] Maman kalisat Novel: Ouummey 08 [ 11/30/2022 3:14 PM ]

★★★ *ANJANE* ★★★
(Rashin sani)
★★★★★★★★★


_*PAID BOOK*_


Story/written by Ouummey.

Wattpad @ouummey.

From The author of:

*HAƘORIN DARIYA*
*ƘASAR MU A YAU*
*BA NI DA LAIFI*
*SARAKI (the accused prince)*
*ABOTA CE KO SOYAYYA*
*And now.......ANJANE (Rashin sani) PAID BOOK*







₦300 to the below account details
Rabiatu Abdullahi
2391368231
ZENITH BANK, screenshot and send the evidence of payment to 09013101854 or MTN recharge card o 09013101854, note VTU is not acceptable.







FREE PAGE 008












_________________________📖 Gaban tanƙamemen gare ɗin gidan ya tsaya yayi horn, cikin sakanni gate ɗin ya fara zugewa da kan shi har ya gama ya tura hancin motar cikin babbar harabar gidan.

Daga kallo ɗaya in kayi wa cikin gidan zaka san gidan family ne ma'ana gida ne da ya kasu kashi kashi (parts-parts).

A lot ya kashe motar ya fita cikin cikakken takun sa da yake da ƙarfi ya nufi sashen mahaifin sa, a yanzu base anjima ba yake san isar da saƙon sa gare shi.

Yana yin sallama ya ɗaya labulen ƙofar tare da shiga falon, zaune kan kyakkyawar shimfiɗar da ta kewaye falon gaba ɗaya yake zaune tare da dattijuwar matar sa, dattijo ne da kallo ɗaya zaka masa kasan shekaru sun tura amma ba alamar yanƙwanewa ko wani rashin ƙarfi tattare da shi.

Zama yayi gaban sa bayan ya tanƙwashe ƙafafun sa ya gaisar dashi cike da ladabi sannan ya ɗora da batun da ya kawo shi batare da ya dubi tsohuwar dake zaune ko ya nuna ya san da ita ba.

"Na samu matar da nake son aura har ma mun gama daidaitawa, nasan an kawo maka wata jarida game da ni to yarinyar jiki ce zan aura ɗin, sunan ta Salma, magabatan ta na garin BA MUNI bana san a ɗau lokaci sosai ne, ba budurwa bace ta taɓa aure da yaran ta biyu".

Tun da ya fara magana wani irin firgicin ya wanzu kan fuskar matar har hannun ta ya fara ɓari wanda se da ta jimƙe shi tukunna ya tsaya, da sauri ta maida duban ta ga mijin ta dan jin me zece

"Amma ai ka bari ayi bincike a kan ta ko, banda rashin hankali irin naka Abu Aulad ka rasa matar da zaka aura se wadda hotunan ta ya gama zaga gari da sunan ɓatanci, to sam ban lamun ta ba ma, hakan ba ze taɓa yiwuwa ba, ga nan babar ka ta daɗe da sama maka mata tsoron halin ka yasa ta kasa faɗa maka amma ni yanzu na sanar da kai kuma sati biyu masu zuwa za'a yi auren".

Wannan karon gaba ɗaya ya ɗago yana kallon mahaifin sa cikin yanayin ba fa zan yarda ba

"Sam hakan baze yiwu ba Baba, a wancan karon ka kawo min nafisa ban yi musu ba amma a wannan karon kam bana jin akwai wanda ze dakatar da ni, bincike akan yarinya ni duk na gama shi, hotuna kuma nawa da nata ne sukai yawo dan haka ba matsala mata da miji dan sun zaga gari an san su, batu na wata ƴa kuwa bani da uwa balle ta zaɓar min, infact babu wani mahaluƙi da ya isa ya min auren da bana so a wannan karon, ka samin albarka dan a gobe zan je in auro ta Dan addini ya bani damar nemawa kaina aure kasancewa ta namiji, se an jima".

Yana gama bayanin sa ya miƙe tare da ficewa da sassarfa, yana fasa bari nan da sati ɗaya tun da ya fahimci abin iskanci ne, a gobe ze je ya auro ta ya ga wanda ya isa yace ya sau ta in akwai shi.

Dan anga yana yin shiru se a dinga maida shi wani soko ko wanda be san kan sa ba, to an shigo da'irar da ba ragayya tsakanin sa da kowa yanzu, ze fubi ifon kowane mahaluƙi da yanemi shiga hanyar sa sannan ya kawar dashi.

Waya ya ɗauka ya shiga kiran Haisam da tuni ya wuce gida tun lokacin da ya tabbatar gida ya nufa, ringing bitu ya ɗaga

"Ka fito bakin titi gani nan zuwa, ina nufin a ƙafa".

Ya faɗa batare da ya jira jin me Haisam ɗin zece ba haka be tsaya sauraren me ze faɗa ba bayan ya gama bayanin sa ya kashe wayar.

Kamar yadda ya faɗa a titin ya same shi, gefen sa Haisam ya shiga yayi wa mota wuta batare da ya sanar dashi ina suka nufa ba, shima tun da yaga yanayin sa se be tambaya ba.

Gudu ya dinga tsugawa a titin har suka fara fita gari, be tsaya ba seda aka kira sallar Azahar suna idarwa kuma suka sake ɗaukar hanya.

Ƙarfe biyar sannan suka shiga ƙauye BA MUNI, kai tsaye gidan me gari ya tambaya aka nuna masa ya wuce, suna zuwa suka fita sannan ya kalli Haisam

"Auren yarinyar can muka zo nema, gobe zamu dawo a ɗaura aure".

Baki sake Haisam ya bishi da kallo jin wani sabon tsari kafin kuma ya bi bayan shi ganin har ya kusa shigewa fadar me garin.

Kan shimfiɗun wajen suka zauna maigari kuwa se rawar jiki yake yaga ƴan gayu cikin kaya masu kai da walƙiya, cikin ƙanƙanin lokaci ya sanar dashi abinda ke tafe dashi aikuwa da sauri maigari ya tashi ɗan aike aje a taho da su kawu iro.

Ba'a daɗe ba se gasu sun bayyana gaban maigari kowanne futu futu dan yawancin su dawowar su kenan daga gonaki da wajen aikin ƙira.

Baɓata lokaci maigari ya sanar dasu dalilin kiran, baba Habibu yayi tsalle yace shi ba shi a cikin maganar yarinyar da ya zaɓi shegun ƴaƴan ta akan su haka ma baba iro.

Baba Adamu ne yayi sassaucin cewa sun bayar a ɗaura yanzu in har da gaske yake kawai dan shima ba ze yadda a Kuma tado shi daga wajen sana'ar sa ba gobe kan batun auren wata can wai Salame.

Ba ɓata lokaci kuwa aka ɗaura auren Salma Khamees da Abdallah Abdulsalam Gamji bisa sadaki dubu hamsin da ya bayar lakadan ba ajalan ba a fadar maigari.

Basu kuma jiran komai ba suka juyo da

Please Login or Register in order to submit comment