Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*ALI GADANGA....*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹



*_Short Story_*



Page1⃣


*_Nabilancy Luv_*💘 {Auntyn S&S}




*DIS PAGE DEDICATED TO MY SISTERS*
*BATUL MAMMAN*(Al,adun wasu)
&
*Ummi Aisha*(wanihaske)


Yammace Sakaliya shida da mintina ana gab da kiran sallar magriba Tawagar "yan gangi suka dawo daga sana,ar tasu ta gangin

Yau Tun asuba suka futa don har farauta sukaje kuma sun dawo cike da sa,a A fitar tasu

sunkai kimanin su ashirin suna tafe suna tada kura ana -kide Kide da -ife ife da yin kirari ga shugaban nasu uban tafiyar cikinsu dayasha kayan sak'i masu ado na yan gangi da farauta daka ganshi awannan yanayi saika furgita don yanayin dayake ciki bana wasa bane ga kayan wukake masu kaifi soke ajikinsa sunkai biyar suna walainiya na sheki ga mashi asoke a wandansa hannayansa rike suke da sanduna fuskarsa tasha farin kwalli gashi majiyin karfi faffada me baiwar kwanji kowa agarin tsoronsa yake Allah yabashi kwarjini da karfi gashi kyakykyawa black american nan dogone ashi qaunar raini *ALI GADANGA* Kenan dan cikin kauyan Marina

Saida sukaxo dai,dai mahad'a kuma maraba sannan suka tsaya suka fara yin sallama ga juna ana kawo gaisuwa gun oga ana tafiya shiko amsawa kawai yke da hannu baya magana fuskarsa babu fara.a tamkar afutar da sukai basuyi sa.aba

Mutane biyune kawai suka rage agun suka take masa baya xuwa cikin layin gidansu manyan yaransa kenan Wawurau da hangamau (kunjifa wasu sunaye da ake gaya musu na banza kuma dan haushi su amsa alhalin kowannensu sunansu me kyaune da dadi daga ibrahim sai yusuf)

Inna kulu kakar Ali tana tsakar gida tana kada miya tajiyo ana faman busa kaho

Duk da gabanta yafadi amma ta godewa Allah da taji dawowar Gadanga dinta lfy domin tana fargabar tafiyarsa daji ko yin gangi ko futa farauta sbd qaunar da take masa ji take kamar baxai dawo da raiba duk da tasan jikan nata gwarxone wajen kwarewa da gwanantaka a iya fadan takuba da masu da sanduna namun daji ma basa galaba akansa balle namiji kamarsa

Inna kulu bata qaunar wannan dabi,a tasa dan ba yadda zatayi dashine gashi tana sonsa sosai tana gudun bacin ransa akullum dai addu.ar shiriya take masa don burinta kawai taga yaxubda komi yai aure duk da "Yammatan garin na tsoronsa yarinya daya ke like masa take nacin sonsa Zainabu yana basarwa ama shima yana sonta takun girma dai yake mata itace sonta yafuto fili kowa yaganeta asati sau biyu ko daya yake xuwa zance gidansu Zainabun ita ke xuwa zance asauran ranakun gidansu Alin.


Saida suka kawoshi har kofar gida kana sukai Ms gaisuwar bangirma suka juya suka nufi nasu gidan


Yana shiga ko amsa sallamarsa bataiba tahu masa kirarin data saba masa

"Ali gadanga na inna!
Ali maxan fama!
Ali sha gwagwarmaya!!
Ali ka gagara kasha kansu!!
Ali ba kasan tsoro ba !!!!
*Ali...*


Ya katseta yana murmushi "cau !cau dai inna Allah dai yabiya yakaremin ke!


"Inna akai min ruwan wanka amma me zafi sosai.


Inna kulu tace " zafi kuma babana duk xafin nan da akeyi...


Yace " nasan da hakan jikina ke tsami yau anyi gwagwarmaya arangama mukai da wasu qungiyoyi nagaji da yawa.


Yawuce yashige dakinsa tabishi da kallo tana girgixa kanta " oh! Ya Allah ka kawomin karshen abin nan.


Saida takai masa ruwan kana tasanar masa


Duk wasu layu da guraye dake jikinsa ya cire dagashi sai gajeran wando yafada bandaki don yin wanka

€€€€€€€€€€€€€€

Yarane suka cika layin fal sunata murnar ganin motar Alh Tahir wakili dake kofar gidan mahaifiyarsa Iya zulai makwabciyar Inna kuluce


Iya xulai tsohuwace me kirkin gaske suna dasawa da inna kulu katangarsu daya saidai iya zulai gidanta na bulo da bulo ne kaf kauyen gidanta ne na bulon siminta har abin kwatance yaxama don danta yatsaya mata Alh wakili a birni yake da xama me kudin gaskene duk lahadi yake xuwa ganin gyatumarsa yana bata kulawa sosai shi daya ke gareta sai autarta dake Aure acan birnin itama amma mijinta bame kudi bane tana da manyan yaya itama saidai shi Alh wakili diyarsa daya jal tilo dayake ji da ita


Khalisat sunan yarsa bata dade da dawowa daga turai ba ta kammala karatu bata xuwa kauyen sosai saboda yanda take da kyamar talaka da kuma tsantsami gata yar wulakanci da jijji dakai.



Ali gadanga yana daga ckn dakinsa kwance yaji hayaniyar tayi yawa awaje da sauri yafito dan jin meke faruwa


baiyi mamakin ganin yaran ba don yasan suna samun abin arxiki gun Alh wakili kudi yake raba musu harda dattijan layin da samari

Dayake suna tsoron Ali gadanga tuni suka fara darewa ganin yabiyu da mugun kallo ransa abace


Tuni suka dare suka tafi sum sum ammafa buya sukai suna hango kofar gidan suka lallabe anesa suna jiran fitowar Alhn.


Yarara biyu gadanga yasa suka jido masa ruwa yafito da soso da omo hau wanke motar Alh wakili kamar yadda yasaba

Ckn mintina motar tahau kyalli duk kurar data dauka na kauyen ta gushe

Ali gadanga yasaba wanke motar Alh aduk randa yaxo inhar yaxo yatarddashi badan komiba sai dan kaunar da yakema Alhajin dakuma yanda Motar ke burgeshi kana bayason kazanta

Alh yasha yi masa alkairi saiyaki karba hakan yasa jininsu yahadu sosai suna mutunta juna ko xuwa kauyen yayi saiya shiga yagaida ina kulu yana mata alkairi itama


Alh yanada kirki da son talakawa hakan yasa kaf kauyen suke sonsa ake girmama iya zulai

Yau da gadanga yagama wanke motar gida yakoma yakwanta


Koda Alhaji yafito yagani yaji dadi sosai yayi murmushi ya ayyana abin alkairin daxai yiwa gadanga ayau

Bayan yagama rarraba kudi ga yara da manya saiya shiga gidan inna kulu da sallamarsa


Ta amsa daga daki tana lekowa data ga shine tahau fara.a tana masa maraba ta shinfia masa tabarma yaxauna suka gaisa

Saida yanemi Ali gadanga ta kwala masa kira

Yaji shigowar Alhajin baiyi niyyar xuwa ba saida yaji kira kana yafito ya gaidashi har kasa

Alh ya amsa yana masa kallon kauna arai yace a inna " inna naxo da alfarma me girma da nauyi Allah yasa kiyimin ita.

Ta gyara xama tana fadin " fadi komeye Alhaji xanm ita inhar batafi karfina Ba

AlhaJi yace da ita " dama inbaxaki damuba inaso ki amince nadauki Aliyu na tafi dashi birni yaxauna agidana nabashi wani aikin kodon ci gabansa

Da sauri gadanga yadago kansa ya kalli Alhaji yakalli innarsa yaga itama shidin take kallo yaji wani abu aransa naganin idonta yakawo kwalla shima xuciyarsa ce ta karye yasan me inna keji tabbas shima yaji bakua zai iya rabuwa da innar saba wacce tun yana yaro yarasa iyaye itace uwarsa da ubansa....






_Muje zuwa_




*Auntyn Sayyada da Shahida*💘
*ALI GADANGA...*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹





*Short Story*






page 2⃣



_Alherin ALLAH YAKAI INDA KIKE AMINIYATA FRESH UMMIEY XEEY DA KUMA AYSHA B NASIR .A.K.A._INAYINKU💘💋





*Nabilancy Luv*💘 {Auntyn S&S}




*Dis page Dedicated to my sisters*

*Batul mamman*(Al,adun wasu)

&
*Ummi Aisha*( wani haske)




*Ali* Gadanga ya sunkuyar dakansa kas ya zurfafa akogin tunani baima san yaxai ce da Alhajiba don yana matuqar jin nauyinsa baxai iya budar baki ya musanta masaba yana kaunar Alhji sosai aransa zaiso kuma yajishi akusa da Alhajin Amma shi bason zaman birni yakeba don yanada masaniya akn yan burni sunada rainin hankali bare ma shida baison raini gashi baida ilimin daxai iya yin zamantakewa a burni


Inna kulu ce ta katseshi da cewa " Gadanga bakace komiba kayi shiru kanajin bukatar Alhaji akanka kayi magana mana.


Ahankali ya dago da kansa yasaka idonsa acikin idon Alhjin yace dashi " baxan bujire maganarka ba Alhaji saidai inaso kabani lokaci me tsaho zanyi shawara


Alh yace " haba haidar saikace wani yaro karami ko mace wace irin shawara kuma kamar wani babban abu na roka agunka


Inna kulu tace " kayi hkr Alh tunda har yace abashi lokacin to abashin domin nasan halin kayana akwai abunda yake hange bawai ki xaiyiba kasan babban mutum.. takarasa maganar da raha tana kallon gadangan duk don yasaki ransa


Amma gogan dayake ba gwanin yin fara.a bane ko hakora bai budeba idonsa ma agefe yake

Alh yace " to ba matsala bari naje ina sauri inkoma don gobe zan tafi dubai zanyi wata biyu dan hka ina dawowa xaku ganni nadawo kan wannn bukatar.

Yadafa Ali gadanga yace dashi " kada kashiga damuwa haidar nasan sabo da dadi rabuwa da ciwo kadaure kai namijine dole kuma inba rabuwa nesa akwai mutuwa kaida innarka amma inaso kasani bawai dan natakuraka xan tafi dakai burniba akwai abinda nake hange akanka wata dama ce gareka kai namijine dole sai kanada dashi darajarka zata kara cia a idon al,umar karkarar nn.


Inna tace " hakane Alh kabar magnar ahannuna zaimaxo burni insha Allah, Allah yasa zuwan nasa yazame masa Alheri.

"Amin inna . Cewar Alhn

Yaxaro damin kudi rafar yan dubu yamikawa inna

" gashi yyi yan shirinsa kafin nadawo

Yadubi Ali gadanga yace "to mutumina nixan koma ka kula banason xaman banxa ina son kaxama gwani ackn gwanaye domin kai na daban ne Aliyu haidar.



Ali gadanga ya gyada kansa tabbas yayi na.am da batun Alh kua yaji dadin kalmansa zaikuma yi kokari wajen ganin yacika wa Alh burinsa xai bashi hadin kai donya faranta masa.


Alh yana futa inna ta rafka tagumi tashiga tunanin rabuwar da xatayi da Ali.

Gadanga yajanyota jikinsa hankalinsa ya tashi ganin tana hawaye

Yace " haba innata daga wannan yar maganar zaki shiga damuwa saikin kamu da ciwon zuciyata inkuma narasaki ainazama marayan gasken kima saka aranki ba inda xani kawai xanta jirgashine harya kyaleni haba yama za.ai natafi burni nabarki ke kadai anan kauyen alhalin bakida kowa.


" ina da Allah gadanga bakomi kada kaki bukatar Alh bawai kuka nake naxaka tafi kabar niba kawai kukan zakai nesa dani baka daina halayar kaba nakeyi


Ya xabura yace da ia " wace halayya gareni kuma inna.


" kanada halayyar bakar xuciya *ALI GADANGA* gashi xakaje inda bakasan kowaba babu wanda yasan yanda kake dan Allah kadan rage wasu halayyar tunda bakasan halinsuba.


" to wai inna waya ce dake xanma je din.?


"Zama kaje Alina banaso kayi gardama kaji


Ya kura mata ido xaiyi kuka abinda yamanta rabon dayayi yace " innata kinason kirabu dani ashe ?

Ta matse kwalla tana kakaro murmushi tace " ba haka bane kaga bana son dama wannan futar farautar da gangin naku amma kaga mafita taxo min hankalina zai kwanta inkayi gefe kacanxa sana.a mekyau tunda natabbatar inkaje burni zaka sami abinyi me nauyi


Yace da fushi " inna kin tsani wannan harkar tawa alhalin tashi nayi naganta agun kakana mijinki shiya koyar dani farauta yakuma sakani akan hanyar yin gangi tun ina yaro to meye dan naxama dan gado wannan fa abin alfaharine kima daina cewa komi akai dan walh ko naje burni baxan bar komi ba zankuma ringa xuwa duk wata guda ina taba harka.


Tayi murmushi jin haryana furta zaije burninma


Nan tahau masa kirarin data saba yi masa yanajin dadi tana kambamashi

€€€€€€€€€€€€
Baifi minti biyar da tsyuwarsa akofar gidansu zainabun ba yaron daya aika yakira masa ita yafuta yana sanar masa cewar tana zuwa kafin yarufe bakinsa saigata tafito kamar tare suka futo

Dama akwadaice take dashi kwana hudu bata sashi a idoba tajejje bata samunsa

Saida yayi fin minti biyar kana yadago yakalleta da niyar mata magana saiyaga ashe shi kawai take kallo kamar ta lasheshi

Kunya taji daya kamata tana masa kallon kurulla


Yace " ya akai ne Abu nah.?

Ta murmusa kawai don ranta yai mata dadi jin muryarsa akwance da sanyi tasan yau da arxiki yaxo mata


Tana son sunan dayake kiranta *Abu nah*


Tace " sannu da xuwa Aliyu nah.



Ya gyada kansa tareda daga mata gira


Yau gani yayi ta kara masa kyau fiye da kullum dukda kwalliyar ta bata mata fuska tasha xanen kwalli ga jan baki fal baka yasha diso


Shi yafi ganin kyan Abu inbatayi kwalliyarba


" kidaina bata fuskarki Abunah.


Kamar tace masa don me ?

Saikuma tace dashi "to zan daina .


Yayi jim can yace " kinbarni atsaye kamar wani soja yau babu abun zaman ne.?

Ta shafa fuska akunyace tace "kayi hakuri walh ina saurin inxo inganka na sha.afa amma bari naje na dauko.

Harta juya xata shia gida yakamo tsintsiyar hannunta ya juyo da ita yamatso gab da ita suna jin numfashin juna yakura mata idanu yace " barshi ba dadewa xanyiba magana ce me muhimmanci ta kawoni.

Jitayi kamar tarungumeshi amma baxata iyaba inama shi ya kawo harin

"Abuna xankoma birni.....


Zabura tayi taja baya dayake tana da saurin kuka take tafara kwalla yakamota yahadata da jikinsa yana cewa '" bafa yanxuba kada ki tada hankalinki andai fara maganar ne magana daya nakeso ingaya miki kirike amana banda mata saike


Yahau goge mata hawaye yana rarrashi

Kukanta ya tsaya cak ganin ya sharce mata hawaye yana suda aharshensa takura masa ido cikonso lallai Aliyu na qaunarta itama dole tazama jarumarsa

Yace " kixo gobe gidan inna zamuyi babbar magana me muhimmanci agabanta.


Tace to xanxo. '


Yasaketa yai mata sallama yatafi yana son zainabu sbd tanada hakuri kuma tana sonsa tana bin maganarsa ga iyayanta yan mutumci duk da marainiyace mahaifinta yarasu amma danginta da mamanta n sonsa

Saida yakule da mintina kana ta shiga gidansu tanajin mugun sonsa na kara shigarta murmushi kawai take tana tuna lokacin dayake shan hawayenta tabbas tanason *Ali gadanga...*






*AUNTYN SAYYADA DA SHAHIDA*
*ALI GADANGA...*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹





*Short Story*





page 3⃣




*Nabilancy Luv*💘
{Auntyn S&S}





*Dis Page dedicated to my Sisters*

*Batul mamman*💝 (Al,adun wasu)
&
*Ummi Aisha*( wani haske)






Aranar Da Ali gadanga yaje gidansu Zainabu kwana tayi tana juyi tana faman fara.a xuciyarta cike da farin ciki nakasancewarta da abin sonta ayau bayama inta tuna yanda yajanyota jikinsa numfashinsu ya gauraya ji tayi baya wannn rana ta yau inama ta dawwama ajikinsa da tafi kowa murna


Da Safiyar Allah ta,ala kuwa ko karyawa bata tsaya yiba ta caba uban ado taci damara ta tafi gidan inna kulu dan inba da wuri tajeba to baxata samu Aliyu agidanba yau ranar xuwa farauta ce


sallamar zainabu ce tafito da inna daga daki tana amsawa

" a.a Abun muce yau agidan.?


da fata.arta ta karasa gun innar ta gaidata har kasa


Inna ta amsa mata amutunce ta shimfida mata tabarma tace mata " zauna kishiyata kafin na kawo miki dumame.


Zainabu tace " lah barshi inna...


" don me xan bari, aiko sai kinci don cin tuwon kishiya ramako ne ,ko so kk gadanga yadawo yatarar nabar matarsa da yunwa


Gaban zainabu yafadi kada dai duk sammakonta harya tafi aikin farautar,


Jin tayi shiru kanta akasa tana murmushi inna tace " lafiya dai ko ? Naganki jiki ba kuxari dafatan ba wata matsalar bace?


Zainabu ta mur
usa tace


"Dama...Dama aliyu ne yace inxo yau gidanki zamuyi magana dashi dake me muhimmanci.


Inna tayi dariya tace " hhhmmm toshine kk wani rabe rabe ni nasan maganar amma bari nabari inyaxo ayita



"Ina yaje kuma inna,?


Cewar Abu tafada araunne


inna tace " yafita sana,ar tasa tun kiran assalatu sallah kawai yayi yafice shida ayarinsa.


Zainabu ta mike tace " to bari naje zan dawo da yamma kawai.

Inna tace " Au baxakici tuwon nawaba xaki tafi ai shikenn.

Xainabu sarkin yan murmushi da shiru shiru tahau dariya tana fadin "kiyi hkr inna narigada na karya shiyasa


" to agaida mutan Gidan.

Zainabu tace " zasuji sai anjima. Tana futa inn tagyada kanta tacr " oh! Allah sarki yarinya me nutsiwa da kamun kai Allah dai yatabbar da alkairi tsakaninki da gadanga dan wannann son da take masa inbai Aure taba saita iya shiga wani halin.


€€€€€€€€€€€€€€€

Gab da magriba zainabu ta dawo gidan inna tayi babbar sa.a kuwa gadanga bai dade da shigowa gidanba

Asanyaye tashiga da sallamarta


Inna ta tareta da fara.a ta bata gurin zama

Inna takawo mata ruwa akwanon sha

Zainabu tasha kadan ta dire tana baxa idanun taga ta ina Aliyu zai fito

Da sauri ta dauke kanta daga kallonsa ganin yafito daga bandaki dagashi sai gajeran wando zallarsa


Gashin kirjinsa yai luf bakikkirin ga faffadan kirji ga kwanji daya tara

Ta gefe yakallota yadauke kansa yaishigewarsa dakinsa ya xiro jallabiya yafito


Inna nakusa da zainabu wacce jikinta yadau tsima naganin aliyunta awani yanayi na tada sha.awa

Tsigar jikinta saida yatashi taji kaunarsa takaru aranta tanason namiji me fadin kirji da gasu


Yaxauna anesa kadan da ita akan wani katon ice


Anitse ta gaidashi ya amsa idonsa akanta


Ali gadanga yace " sai yanxu kikaga damar xuwa ?


Ta bude baki xatayi maga inna tacafe da cewa " kaga kada kaji haushinta ko kaga laifinta narashin xuwa da wuri sarkin yan fushi, taxo tun safe lokacinma futarku knn


Ya gyada kansa kawai

Xuwa can yace " inna kingaya mata zanyi tafiya ne ?


Inna ta girgixa kanta tace " kaban sallahu ne?

"ban fada mata komi ba

Yajinjina kai yace " Zainabu nah nakira kine gaban inna tazama shaida akanki na tunin son da nake miki nakuma yi mk alqawarin Aure insha Allahu nanda dan lokaci domin zan koma burni da zama badan naso ba da xarar kuma nakoma xanyi kokarin samun aikinyi yi domin ganin nasamu abinda xan dogara dakaina nakuma iya rike iyalina dakyau dan haka kirike amana ga inna itace sheda inada kishi kada wataran adawo nakamaki da cin amanata dan walh inhar nga wani tare dake to tabbas saidai wani bashiba zan kasheshi nakashe banza ke kuma in hukuntaki.


Inna ta kama baki tana kallon shi tama rasa bakin magana


Gadanga yakalli xainabu da tayi shiru kanta akasa yace

"tashi narakaki gida.


Ta mike asalube tayiwa inna sallama tafuce


Yabita abaya yana karewa surarta kallo ta iya tafiya gata da diri gata doguwa


Har kofar gidansu yakaita kana yaja tunga yace da ita " kalle ni Abu nah.

Takasa dago kanta tana hawaye

Yasa hannu yadago habarta jikinsa yai sanyi ganin hawayenta na xuba


Yace " meye na kukan kuma,?


Tace " to kuma yaushe zaka tafin?



Yagoge mata hawaye da tafin hannunsa ya murmusa yace '" Abu nah bansa ranar tafiya ba tukunna. Akwai wani abune?


Ta girgiza kanta tace " a.a babu.

Wani shaukinta yaji aransa yajanyota jikinsa yace " sunbaceni to .


Wata kunyace ta lullubeta sam bazata iyaba dan akwai mutane masu wucewa inshi bayajin kunya da tsoron mutane ayanxuma da take jikinsa don baxata iya xamewa bane data gudu.

Ganin tana nuku,nuku yasa ya turarta da fushi yace mata " to nagode jeki gida tunda ban isaba.


Tasan fushi yayi amma aguje tayi gida abinta


Shiko yajuya yatafi yana murmushi yace aransa " Zainabun *Ali gadanga* badai kunya ba.




*Auntyn Sayyada da shahida*💘
*ALI GADANGA...*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹




*Short Story*





*NabilancyLuv*💘 {_AuntynS&S_}







*Dis page dedicated to my sisters*

*Batul mamman💝*(Al,adun wasu)
&
*Ummi Aisha* (Wani haske)





page4⃣



Sati guda dayin hakan shiru shiru Zainabu batasa Gadanga a idon taba

Jikinta yagama bata tabbas fushi yke da ita akan yace tayi masa abu takasa yi

To ai kasawa tayi sbd tanajin nauyinsa kuma tana gudun bakin mutune kada aganta taji kunya

Saitaji inama tayi masa kawai ta huta dan rashin Aliyunta ba karamin gashin quma bane agunta


Ta jejje unguwar gidansu kawarta atika amma bata sami ganin Aliyun ba


Tasan yana sonta kawai miskilancinsa yafi gaban komi yana kuma basarwa ne dan yasan shi din me kyau ne kuma wanda yakai asoshin


Tun asalin mafarin soyayyarsu bashi yace yana sontaba


Ita tafara kamuwa da sonsa


Ali gadanga bai taba furta yana son wata diya mace a kauyen ba


Itanma ansha gwar
gwarmaya kafin ya amsa tayin soyayyarta adalilin abokinsa Sunusi yayan kawarta dayaita kai komo alamarin nayanda Zainabun tashiga akansa takoma abin tausai


Dayake kuma zainabun mekyauce dakuma biyayya saita rinjayeshi dasuka hadu aranar farko ya karbi tayinta


Tabbas ayanda take son Aliyu zata iya jure komi dantaga tasameshi


Aranar kwana na goma da tayi narabonta da ganin Aliyu ta wanke kafafunta tayi karfin halin nufar gidan innarsa kawai tunda tasan da soyayyarsu gara taje tagaya mata kota saka baki ahuce fushin da akeyi da ita.


Ahanyarta ta xuwa gidansu Gadangar ne taga wani D'an nacin saurayi dayake like mata tana nuna masa kiyayya ba dan unguwar bane amma yakan shigota jefi jefi shida abokansa unguwanninsu suna makwabtaka ne sunansa Amadi.


Ganinsa yasa ta hadr ranta takara sauri donta wuceshi amma ina saida yacimmata


yasha gabanta ta kauce yafi sau uku tamkar tasaka hannu aka tayi kuka ganin yanda ake kallonsu


Ita bakomi take jin takaicinsa ba mummunane shi gashi baki gajere


Kuma kowa yasan yana dan taba shaye shaye da dabanci


Tasha mur ta tsaya cak!


Batada niyyar magana ma sai kai data juyar gefe ranta abace


Yai murmushi yana shafa dan munafukin gemun daya tsayar kamar na bunsuru


"Yam matana ba magana ne ,haba zainabu me tagwayen suna kinsan ina sonki kamar in mutu amma kike basarwa yaya kk so nayi ,koso kike sonki yakarni,

Batayi magana ba dai ko kallo bai ishe taba


Yaci gaba " gaskiya yau bani barinki saikin gaya min da bakinki matsayina


Ta nunashi da yatsa "bani guri na wuce ko kaga rashin mutumci.


Yasheke da dariya yace " hakan nakeso ai, kome zakiyi ban matsawa walh harsaikin gayamin kina sona ko kuma kiyi dariya inyi ko zamu kwana nn tsaye baxan matsa mikiba inko bakiyimin daya cikin suba to walh zan rungumeki agaban jama.a.


Gabanta yafadi yau tashiga uku gashi layinsu gadanga ne ya knn zatayi ta tsira?

Batada amsa bakuma tada xabi saina tayi dabara kawai taxabi daya don ya barta kawai


Take ckn kissa da dabara tahau yak'e tana cewa ina sonka mana Ahmadi yama xa.ai nak'i ka kayiwa Allah nidai kabani hanya sauri nake aikena akai.


Jin ta faranta masa rai yasa yabata hanya ta wuce dasauri yana dariya shima " to,to naji nagode masoyiya jeki aikenki zanzo zance gida.

Da sauri ta wuceshi tana godiya ga Allah da bai bata kunyaba.

Tabdijan! Allah sarki zainabu Abu me tagwayen suna kokunsan tausayi tabani naganin yanda nahango Ali gadanga acan karshen layinsu yana hango komi daga nesa xuwansa kenan gurin idonsa ya nuna masa zainabunsa nayiwa wani fara.a suna tadi ckn nishadi wato hira tayi dadi knn. Shedan yaita masa kida da xuga

Please Login or Register in order to submit comment