Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tambaya tana kallonsa

Yagirgixa kansa yace "na koshifa na biya gidan momy taxuba min abinci naci.


Tayi murmushi don taxaci ko yaci agun zainabu ne

Tace masa "Allah sarki momy amma dai tace tana gaidani ko?

Babu fara.a afuskarsa yace "eh tace tana gaisheku tabani kaya aleda ma tace nakawo muku yana but din mota.


Hhhmmm wato harda zainabu tabada knn aitasan momy bata kishinta batasan me yasa takeson yarinyar can ba me kama da bulala.


Ta dawo kusa dashi ta xauna tace "yaa dady fa?

Ko kallonta baiyiba yace "yanana qalau.

Taringa masa hira ta gida harda tambayar su mudi

Bai bata amsaba don bayason surutun tagaji tayi shiru

Yasan tambayar su mudin datayi najan baki ne don yace wani abun aibai mantaba yanda take ciwa su mudin mutumci alokacin tana hida sukuma shakkarta sukeyi to yanzun meye nawani tambayarsu

Daya gaji da xaman ma tashi yayi yabar mata falon yakoma daki yakwanta bafa baccin yakejiba

Tunanin zainabunsa yahauyi da tunifa yanxu suna manne da juna

Yaja tsaki adaidai lokacin data shigo dakin


Karaf akunnenta taso takoma amma saita dake tadage tarinjayi xuciyarta domin akwai qudirinta ayau


Ta durkusa gaban gadon tafuskanceshi ckn rage murya kamar xatayi kuka tace "Aliyu dan Allah kayi hkr da duk abinda ya taba wakana mara dadi atsakaninmu natuba nayi nadama baxan sake ba


Yace "kima sake mana.

Tahau kukan karya "walh baxan sakeba na tuba nagane ba abune me kyauba wulakanta dan,adam haba mijina inasonka inaso yaxamo naxami aljanna tasanadinka

Saiyaji xuciyarsa ta karye yaji tabashi tausayi amma saiya dake

Taci gaba "walh xanmaka biyayya Aliyu duk abinda kace inyi zanyi kuma zanyi biyayya ga zainabu amatsayinta na uwar gida bazamuyi hatsaniya ba insha Allahu.


Hhhmmm namiji ba wuyar ansamokaπŸ˜…


Tuni yadauka hakanne data fada yatashi zaune yakalleta da nutsuwa yace "kintabbatar abinda kk fada har zuciyarki ne?


Tace "walh babu karya aciki


Yaja ajiyar zuciya yace "naji nayarda shikenan komi yawuce Allah yasa dagaske ne kuma sainagani akasa.


Tayi murmushi tace "zaka gani ma insha Allah.

Yajuya yakwanta kawai

Ganin hakan yasa taje ga sif dinta taciro kayan baccinta hadaddu taxira tareda fesa turaren bacci me sanyi da tada sha,awa taje bayansa ta kwanta ta matsu dashi yanajinta baiyi mata maganaba

Har ransa yafara sakkowa kuma inya tuna ta baiwa wani kanta harda yin ciki saiyaji kuma wani abu yatokare masa arai yaji sam baxai shiga ba don yanada kishi gadanga kowa yasani


Har bacci yakwasheshi batayi baccinba don taso ace ayau tarinjayeshi amma taga Aliyun baida sha,awa akusa dole ta hkr gadai suga akusa da ita amma ba damar dandanawa har sakala hannunta tayi ajikinsa amma ina baisan tanayibama yayi baccinsa



Da asuba yatashi yaje yai sallah yadawo yatararta tana baccinta hankali kwance

Yagirgixa kai da takaici da alamar bata saba sallar asuba akan lokaci ba tab yatuna xainabunsa jiya ita ta tasheshima aranar farkone ma yatasheta don yai mata uxurima sbd agajiye take amma yatabbatar zainabu tanada ibada


Ya bubbuga gefen fulonta tafarka babu addu.a ballantana salatin annabi

Tahau yamutsa fuska wai nan bacci bai ishetaba ganinsa atsaye akanta yasa tayi saurin tashi xaune

Yace mata "maxa tashi kije kiyi sallar asuba kada lokacinta ya gudu.

Tace "zanyi ai sai anjima inna tashi.

Yazauna gefen gadon yace mata "ban ganeba?kina nufin bakiyi sabo da yin salla akan lokaciba,?to baxamu taba shiryawa dakeba domin ita sallah itace kan gaba a addini kuma itace xata ceceka akabari sannan Allah fa muke gaidawa kuma alamun munafiki zaibayyane ne muraran inya kasance meqin sallah bakuma xan iya xama dake inkina kinyin sallah akan lokaciba.


Tajishi sarai takuma yarda da batunsa da sauri ta mike ta shige toilet dan dauro alwala

Baccinsa yakoma baitsaya ganin tayadda take sallar ba dakwa tasha gyara


Yarigata tashi da safe harya shirya yafuta bata tashiba saida ta tashi taga wayam

Saida yashiga dakin zainabu yaganta tagaidashi yayi mata kiss akumatu yace "akwai wani abunne? Tace "a,a babu.

Yace '"to natafi gun aiki.

Tayi masa adawo lafiya.

Kwata kwata yamance da sakon momy amotarsa saida yaje office ma yabude motar zaifito yahangi ledojin a sit din baya


Da wuri yakoma gida daya taso bai tsaya akoina ba


Amma yadade a part din zainabu sunsha hirarsu ta masoya yabata sakon momy wata laffaya ce ackn ledar da turare da doguwar riga yayan tane ya dawo daga saudiyya ya aiko mata da kayayyakin

Yayan momy me kudine sosai yanaji da momyn ita ke binsa a katsina yake


Yanda kayan ckn ledar zainabu yake haka ma na khalisat din yake

Zainabu tayi murna sosai dukda ba iya nada laffaya xatayiba ama doguwar rigar tayi mata kyau


Khalisat tana can adakinta tashaqa sosai domin taji dawowar gadanga tun yamma amma bai shigo mataba sai bayan magriba

Bata isa ta nuna jin haushin taba tunda so take tasamo kansa

Takawo masa abinci falo

Yau baiciba ko kadan yace mata akoshe yake

Tasan yaci agun zainabu bata ji dadin hakanba

Yau kam taso Aliyu yajiyarta dadin amma yai mata biris duk yadda takwanto abayansa tana masa tausa hakan baisa yatabata ba ammafa yaji maganad'isu nashigarsa wato sha,awa dai tafara motsuwa πŸ˜… muje zuwa khalisat mahakurci mawadaci


*******
Wata guda dayin tariyarsu Alokacin gadanga yaje kauye yahado kan mutanen da zasuyi aiki a kamfanin dady sunyi mutane 40

Sosai mutan kauyen sukaji dadin hakan babu wanda yanuna baxai xo burniba murna ma sukai su to wannan ai cigabane yaxo musu to albashifa dubu talatin talatin zasu samu wanda akauyen duk buga bugar da suke awata basa samun 20 aikin gini da diban yashi a jaki yafi karfi ma akauyen sai masu hakan rijiyafa da masai wasu kuma dama yan zaman banza ne sunfi yawa


Ba tsofaffi ciki duk samarine da magidanta masu aure masu jini ajika

Gidaje dady yakama musu na haya kafin yagina musu dan Estate da zasu zauna kowanne gida mutane hudune aciki dubu hamsin shekara zai biya


Sunkuma fara aiki ka,in da na,in basusha wata wahalaba don akwai wasu ma,aikatan baya gasu

Gadanga ma yana kula da kamfaninsa na Rooffing Saman gida dasu kayan gini na zamani dai wanda ake shigo dasu daga waje


Alokacin suna wata biyu da tarewarsu agidan zainabu tafara laulayi bata cin komi kullum tayi amai yakai uku arana ko kamahin turaren gadanga batasonji


Rashin lfy tahauyi saida aka kaita asibiti ma


Momy ta aiko mata da dije takula da ita dasuka dawo gida don kwananta uku a asibitin aka sallamesu


Har lokacin Aliyu baibada kai bore yahau ga khalisat ba kullum kuma cikin nuna kissarta take donta rinjayeshi


Yafara cin abincinta domin tafara gyarawa tun zuwan khairat tayi mata taci taji yanayin girki baikai acishiba aiko taringa mata fada "ke yanzu haka kk yiwa miji girki baya dahuwa kk saukewa bakuma yajin maggi lallai xaki kashe kanki to tun wurima gara ki gyara don kinganni nan walh duk hutun da nake ciki agidanmu inayin girki ina shiga kicin in taya mommyn mu sbd dadyna bai yarda dame aikiba


Nanfa taringa nunnuna mata akwanakin da zainabu takwanta a asibitima kullum take xuwa tana koya mata wasu abubuwan har girki sukai aka kai asibitin


Aranar momy taji dady har ranta don tayi zaton khalisat din zaman daditake da zainabun batasan duk khairat ce tamatsa sujeba duk don su burge Aliyune kuma yaji dadi shima


Abinda khalisat ta dage dayi shine addu,a akan Allah yarinjayo mata mijinta kanta dan yabata hakkinta


Addu,arta kuma ta karbu alokacin da zainabun tana asibitin don kasa jura yayi saida yashiga rijiyar khalisat din

Ba laifi yaji dadi tunda guri yasha gyara anmatse anxak'ak'a

Da asubama saida yakarayi kafin yafuta asibiti gun xaunabun


To sai lokacin hankalin khalisat yakwanta ganin Aliyu yajiyarta dadi yakuma fara sassauta mata lallai addu.a takobin mumini ce ta yarda


itako zainabu takanta takeyi don koda aka sallamota bata ta gadanga ko yana dakinta bata bashi hakkinsa ji tayi abin yafuta aranta ma


Sbd son dayake mata yasa yai mata uxuri kuma yana samu agun khalisat saidai baikai yadda yakesoba kamar gun zee dinsa


Saida cikinta yashiga wata biyar sannan ta dawo dai dai komi yai normal tadawo yi masa girki inyana dakinta tafara bashi kanta amma ada bata iya komi to koyaushe bacci kasala batacin komi inma taci amai ne kwadon xogale kawai takeci fa sai tuwon dawa da dijen ke mata sai ruwan lipton datakesha amma data dawo komi yai nrml sai dije takoma gidan momy shima yahuta da kawo dafaffen zogale

Ma,aikatan dady hankalinsu kwance suke aikinsu suna daukar salarynsu duk wata mutun goma wasu ke xuwa kauye ganin gida insunyi sati saisu dawo wasu suje da haka har sukai sabo da burni yaxamo ma sai sunga dama suke tafiya saidai suyi aike kawai dady yana musu adalci sosai haka akeso kuma, Allah yabamu shuganni adalai


Ranar wata lahadi watan zainabu uku da kwanciya a asibiti knn tana kwance agado da cikinta qurbibi kamar ankifa kwarya ajikinta


Safiyace wajen 11am tunanin gadan takeyi yana dakin khalisat haushine fal ranta yasaba fito da safe tara ko takwas inba ranar aiki bane to amma yau gashi har shine fin shadaya lfy?


Tananan shiru tana kallon agogon wayarta taga har sha daya ta sake gotawa da kwata amma bataji yashigoba tasake shaqa

Hoo!zainabu kishiπŸ€” ba dakin matarsa yakwanaba ina ruwanki

Duk laifin na Gadanga ne yakoyarta gane agogo sannan yai mata sabon dawowa da wuri dakinta to gashi yau yayi laifi ……





Muje zuwaπŸ˜…


_Fans laifin dadifa zai kare domin saura one page Ali gadanga yakare muku domin akwai wani shaharerren novel da zaizo muku me suna_ *"Yar fillo* _dan haka inaso kununamin farin cikinku akan yanda kukafi jin dadin wani guri ackn Ali gadanga kokuma kubayyana rashin jin dadin ku awani gurin haka kuma in akwai gyara ko shawara ina maraba hakan shixai karamin kwarin guiwa sainajiku nabilancy luv_
*ALI GADANGA...*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹






*Short Story*




⬇
*THE* πŸ”š
*KARSHE*





*Nabilancy Luv*πŸ’˜
(Auntyn S&S)





page

3⃣0⃣

Gadanga bashi yashigo dakin zainabu ba sai sha biyu na safe yatararta tana cika tana batsewa

Yasan meyasa sai yahade ransa don bayaso takawo wani korafi

Yaxauna kusa da ita yace "lafiyarki kuwa maman "yan biyu?


Tajuyar dakai gefe batayi magana ba

Ya murmusa yace "yau ba gaisuwa ne?


Tayi masa banza again

Ya juyo da ita da karfi yace "ko nayi laifine Abun nah?

Cikin shagwaba tace masa "to bakaine kaje kai xamanka dakin matarka ba kamance dani sai yanxu


Yayi dry yace "to kema bakiji me bakinki yace ba, dakin matata fa kk furta kinga knn ai banyi laifiba ko?

Tayi sakato tana kallonsa mamaki take toko dai Aliyu yafara son khalisat bata saniba?

Yakatseta dacewa "zamu futa da khalisat zankaita asibiti taga likita batajin dadi daga nan zan wuce da ita gidan momy sai dare zamu dawo.

Ta hadiyi wani abu axcyrta me daci

Tace "to adawo lfy kurum. Babu fara.a afuskarta


Yace "kina bukatar wani abune ataho mk dashi?

Ta girgixa kanta kawai

Ya mike yace "ok muntafi to.

Tabishi da kallo harya fice gadanga ya fara canxa mata kodai anhadosune lallai dole ta tashi da addu.A ta neman tsari dan kar ashiga tsakaninta da mijinta asa yarabu da ita donko tasan mutuwa zatayi kawai zaifi mata dadai araba da Aliyunta wanda yaxama rayuwarta ahalin yanzu baxata iya xaman kauye ba tayi sabo da jin dadin rayuwa zaman birni yafi na kauye nesa ba kusaba balle kana xaune dame sonka aika gama samun jinddin rayuwa

Aliyu gadanga yanzu ya goge yakara kyau yazama dan burni zam fatarsa tacanxa yayi haske yYi fresh har saje yatara agefen fuska ga turanci yaxauna abakinsa lallai m.m haruna ta taimaka masa duk da yashiga wata daban datafita karatu


-*******
Khalisat kwana tayi ba lfy jikinta zafi rum ga ciwon ciki da take fama dashi zazzafan zazzabi ne ajikinta


Saida yakaita asibitinsu likita yaganta akayi mata gwajegwaje

Azatonsu ma ko cikine da ita Amma likitan daya kawo musu sakamako sai jikinsu yayi sanyi don ba cikin bane Maleriyace dakuma typhod daya shigeta kawai



Abinda yafi daga mata hankalima sakamakon da likita yafada agame da mahaifarta yace baxata haihuba don kwayayan haihuwarta sun gaxa sau daya rak zata dau ciki kuma ta dauka yaxube abaya.


Taci kuka tagodewa Allah Aliyu gadanga yaita rarrashinta donta bashi tausayi

Taringa kuka tana cewa tayi nadama gashi Allah yajarabceta Alokacin datake bukatar haihuwa yahanata.

Aliyu yace mata "kidaina fadin haka ba hanaki yayi ba jarabtace kiyi kokarin cin jarabawarsa kawai kisa hkr aranki kiyita Addu,a akan yayafe mk yadubeki da idon rahama zai iya baki agaba kada kiyarda da fadar likita don komi na iya faruwa amma inkinyi tawakkali.


Saida yaga ta dan kwantar da hankalinta sannan suka wuce gida domin tace tafasa xuwa gun momyn ba dama zuwanta daya tunda tayi Aure daya kaisu da zainabun suka gaida su dady da daddare


Khalisat tasaka abin aranta duk da tadau shawararsa tana addu,o,in ammafa kullum tunaninta shikenan yanxu ba ita ba ganin kwanta aduniya

Aiko dai jikinta yai tsamari ba shan maganin da likita yarubuta mata takeba

Garama in gadanga na dakinta yakan matsa mata ta balla tasha

Maleriya kuma tayi mata ragargaxa ko daga hannunta bata iya yi ga damuwa data tarar mata kullum jikinta azafafe take kwana rumm


Kullum zaunabu na hanyar dakinta tana kula da ita tunda taganta taringa tausaya mata dama gata da tausayi da raguwar zuciya koda taga khalisat din duk ta rame har kuka tayi mata


Ita kanta khalisat taxaci mutuwa xatayi taringa neman afuwar zainabu tana cewa ta yafe mata abinda taringa mata don Allah kada tariketa

Itako zainabu takance ni ban rikekiba inma kinmin wani abun bansaniba to nayafe mk Allah yabaki lfy


Har wata guda khalisat bataji saukiba zainabu na hidimarta ga cikinta yafito sosai wata bakwai duk ta kumbura dayake sunyi test Ance musu twins ne duk mata saiya zamo dije me aikin momi ta dawo gidan da zama a part din khalisat saboda khalisat tafi bukatar taimako dan dai duk biyun take yiwa hidima ne


Da momy da dadynta sukaga abin yakici yaki cinyewa Aliyu na bakin kokarinsa sungani sai suka fitar da ita kasar waje


Tareda gadanga suka fita da momynta

Gadanga baiso binsuba dan bai isa yamusa bane tunda dady yabukaci hakan amma yaso yai zamansa a nigeria tunda yanada patient zainabu itanma tana bukatar taimako


Da taimakon Allah da taimakon likitocin malesia jikin khalisat yafara samuwa domin da gasken gaske suka tsaya akanta ana mata magunguna da kuma wankin mahaifa ana bata magungunan larurarta

Cikin wata guda tasamu ta dawo khalisat dinta ta da


Koda aka sallameta suka dawo kasarsu ma ba.a tsaya dayin magungunan ba domin momy taringa kawo mata magungunan hausa da rubutu akan mahaifarta data sami matsala sannan tasa asauke mata alqur,ani


Alokacin cikin zainabu wata takwas duk ta kumbura batayin komi dijece ke mata hidima haka khalisat ma takan shiga gunta ta tayata hira

Sun hade kansu tamkar wani abun baitaba faruwa atsakaninsuba


Aliyu yaji dadin hakan don hakan shima sai yadaina musu bambanci saidai dole zainabu nada wani matsayi na daban ackn ransa amma baya nunawa khalisat ta gani don kada asami matsala



**********
Aranar da Nakuda takama zainabu Aliyu bayanan yana gun Aiki khalisat itace tayi mata kokarin kaita Asibiti amotarta


Ckn awa biyu "yanbiyu suka iso duniya ba atare suka zoba saida suka bada ratar minti talatin talatin atsakaninsu kowacce nakudarta daban

Yara farare kyawawa masu kama da uwarsu tamkar larabawa


Khalisat tayita kallon yaran tanajin wani abu aranta qaunar yaran takeji da sha,awar inama natane amma inta tuna cewar jinin gadanga ne sai taji ddi domin itanma yanxu tadaina fidda ranta tunda Allah me yanda yasone ga bawansa xai iya bata alokacin dayaso yabata


Zainabu qalau take shiyasa aka sallameta taringajin son yaran nata


Khalisat ta bugawa momy tagaya mata aiko ba bata lokaci saigata da kayan jarirai data siya dama sunkai arbain abut

Khalisat tashammaci gadanga domin saida tagayawa momy ba kana takirashi tayi masa albishir da samun "yan biyu


Yaji dadin wannan albishir din yace "yaushe akai hakan shine ba.a kirani asibitinba?


Tace "wannan shiri nane banaso atayarwa da mijinmu hankali shiyasa,walh bakaga yaranba masu kyau sunyo kyan uwarsu


Gadanga yaji dadi sosai yace "nagode khalisat zan baki goron Albishir da zakiji dadi kema.


Koda yadawo gidan yatarar da momy sai yaringajin kunyar yadaumi yaran agabanta

Saida ta daukosu one by one tadorasu duk acinyarsa


Wani dadine yaringa shigarsa yana kallonsu yanzu wadannan kyawawan yaran duk nashine?lallai yagodewa Allah mai kowa mai komai mai kyauta da karawa shikam ko haka Allah yabarshi yaji dadi mata Ai rahamane gasu kyawawa kamarsu da uwarsu futuk.daya tuno inna saida yayi kwalla yagogeta ba wanda yagani sai zainabu tasan kukan dadine amma dasuka kebe adaki saida ta tambayeshi tace "Abban twins meyasaka ka hawayene dazun?


Yace "ummun twin natuno inna ne inama tananan taga yaran gadanga da zainabu,inna tafi kowa son taga munyi aure nidake akaf kauyen nan yabaxan kokaba ayau ga kwanmu aduniya ita bata duniyar


Zainabu taji itama kwallar taxubo mata

Gadanga yasa hannu yagoge hawayen nata yana cewa "zainabu kin gamamin komi kin haifamin yara masu kyau kamarki saidai ina neman Alfarma gunki.


Tace "fadi mijina zan maka ita kowace irice.


Yajanyota jikinsa yana shafa fuskarta "so nake insaka sunan khalisat akan hussaina hassana kuma inna ko yaya kk gani?


Ta murmusa tace "hakan yayi mana nima tun A asibiti dasukazo duniya na ayyana hakan kaga damuwata zata ragu kuma tayimin taimakon da dan,uwana na jini xaimin takuma nuna murnarta daxuwansu fatana itama Allah Yabata itama.

Yace " amin nagode"


Anata shirye shiryen suna kullum khalisat na dakin zainab sbd qaunar twins datakeyi sai magriba kuma take komawa part dinta tare ake karbar "yan barka da ita

Sai ana gobe suna ma gadanga yafada mata hussaina fa sunanta zataci

Aiko dai bakuga murnaba harda kukanta taji dadi


Dan hakanma saida ta kama wani gun akai partyn suna *Nabnur event Center*


Anci ansha anyi rabon abin suna

Dama gadanga yayi musu dinkuna iri daya ma kala biyu suka samu daga gunsa


Momy ma tayi musu dinkin tsadadden less don itanma ranta yayi fari dataji ansa sunan khalisat a kan baby hussaina

Iya zulai taxo daga kauye a bangaren zainabu tadira itace me wankan jego

Khalisat ma takawo kayan jarirai amma dole saida ta banbanta na takwararta yafi yawa

Zainabu tayita mata dariya tana cewa "Auntyn Hussaina bandafa banbanci kinsan Abbansu baxaiji dadiba inkin nunawa innarsa banbanci


Khalisat tace "to nadaina momyn twins daga wannan ne kawai banaso aga laifina.


Khalisat tayita nan nan da iya zulai tana kama kafa da ita

Har gadanga tasa yarokar mata yafiya agunta

Da kansa yazaunarsu yashiryasu

Iya tace "toni me tayimin aibatayimin komi ba kowa yai nagari dan kansa.

Khalisat harda kukanta wai yanxu tagane tayi hankali itace kakar daya kamata taja ajiki


Iya zulai dai ta hkr tasake mata har kwana tayi a part dinta kafin ta tafi


Da zainabu tayi arba,inma tare dukansu har khalisat sukaje kai iya kauye

Sun hada mata sha tara ta arxiki


Kwanansu biyu akauyen gadanga yadawo daukarsu

Khalisat takwana daya gidan iya daya gidansu zainabu kuma bata nuna kyamaba komi aka kawo mata ci take hankali kwance


To kansu dai hade yake dan haka hankalin gadanga akwance yake shima


Shekarar twins biyu zainabu tasake samun ciki anan hussaina takoma gun takwararta khalisat da zama zainabunce tabata kyauta ammafa kullum suna part din zainabun kwana kerabasu zasu tafi sashinsu



Duk siyayyar da zatayiwa baby khalisat haka zatayiwa inna karama bata musu banbamci


Zainabu ta haihu lfy tasami namiji wannan karanma gadanga yayi kara dan sunan dady yasaka Tahir akece masa jinior

shima wannan Taron suna yakawatu ainun dady yayi rawar gani yayi hidima keko takwara ba doleba


Shekarar junior guda akasaka twins amakaranta don suna magana radau shekararsu uku khalisat ke kaisu ta daukosu amotarta sch din ba nisa sosai

Gadanga yanata samun budi ba laifi yabude account yanata ajiya kudadensa aciki daga karshem uwar gida zee tabashi shawara yabude gun car wash da bude gidan buredi da gidan pure wata *Al,kaleezai Car wash* da *Twins Bired* da *Tahir pure water*
ya ringa samun nasibi takoina a business din

Dady ya aikowa zainabu motar yar panadol extra tayita murba hargida yakaisu tayi godiya khalisat ce me kaita koyo ckn watanni kuma tafara iyawa


Gadanga kuwa visa yayi mus xuwa kasa mai tsarki kudin kujera uku dama watan tafiyar Alhazaine sukaje hajji suka sauke farali tareda taya Khalisat addu,ar Allah yabata haihuwa itama

Sunyoyyo tsarawa wa mutanen arxiki shi gadanga dady dasu mudi da "yan kauyensu yayowa tsarabar


Ita kuma zainabu momy da iya zulai da yan gidansu tayowa sai yaranta da kanta


Dayake gadanga yabasu kudi ahannunsu

Khalisat kuwa ko kanta batayiwa ba sai "yayanta su twins da junior


Zainabu tanuna mata jin dadinta afili tanajin tausayin khalisat shiyasa har kullum take tayata addu.a aduk sallolinta to ai dolene tunda ciwon "ya mace na "ya macene


Zaman lafiya ya wanxu ackn gidan gadanga matansa tankar ya da kanwa khalisat nabaiwa zainabu girma amatsayinta na uwar gida ita kuma zainabun tana baiwa khalisat girmane amatsayinta na wacce tabata shekaru biyar


Da umarar maulidi taxo khalisat ta tafi donyin addu,o,inta acan


Har lokacin zainabu bata sami wani cikinba dan ta yaye junior har gadanga yana zaton ko plannig tafara


Tanuna ms sam batayi bakuma zatayiba


Allah maji rokon bawansa wata guda da dawowar khalisat dg umara Tafara laulayin ciki atare suka fara itada uwar gida zainabu itama cikinne da ita



gadanga murna fal ransa


Haka Khalisat taringa godiya da Allah daya cika mata burinta


Alokacin da sukayi nauyi basa futa saidai in awo zaikaisu dan EDD dinsu wata daya yakama tsiran satine likitan yasa musu a result


Asatin khalisat ta haihu aka fara hidimar bikin kawarta khairat wacce zata Auri wani malamin makaranta Mal.Anwar dan ta sauko tace Auren talaka shine samun kwanciyar hankali kuma sunfi iya tsadaddiyar soyayya β€πŸ˜…


kyakyawar baby khalisat ta haifo me kama da ubanta tace lallai asaka mata sunan zainab tanaso


Zainabu taji dadi kuma har lokacin hussaina tana can gunta bata karbetaba don kyauta tabata don tana mata raino twins sun girma anfara zama "yammatafa


Satin khalisat biyu da haihuwa zainabu ta haifo santaleliyar baby itana mace steel me kama da ubanta


iya Zulai dama tananan tunda tazo da khalisat ta haihu aiko dai yan kauye sai aike akai musu na sanarwar haihuwa



Jaririya taci sunan momy laila sukece mata Afnan


Bayan suna gadanga yana manne da zainab akan gado suna tadi tace masa "Abban twins kaifa angon karnine yakamata kayi turaka sbd irin haka munhada mk gwarama babu inda zaka fake


Yaja dogon hancinta yace "ba matsala ko banyi turakaba zanci gaba da kwana bibbiyun ahakan har kuyi arba,in

tace "inajin dadin mijina me hakurine walh.


"hhhhmm nikuma inajin dadin za.a cikamin gida da albarkar iyali,plz uwar gidana kada kiyi tsarin iyali inaso wata shekara kihaifamin me sunan gwaggo...


Taturo baki "ni kam inaso n nahuta haka haba honey 4 fa aiyakamata kuma nabarwa khalisat ta dora akan inda natsaya.


Yace " inaso kiyi goma ita kuma tayi biyar.... "laaalaaa tab …… yakatseta da sauri ta hanyar saka bakinsa anata yakamo harshenta yafara sha....





tofa gadanga nabarku lfy na fece Allah yakara dankon kauna kaida iyali πŸ€šπŸ»πŸ€šπŸ»πŸ™ŒπŸ» byeee



Fans saimun sake haduwa a sabon novel dina me suna


*"YAR FILLO*
_Dijen kauye_


tabbas zakuji dadinsa,zaku yaba zakuyi fahari

Zaifadakar zai nishadantar,zai ilimantar.


Taku har kullum

*Auntyn Sayyada da Shahida ce*πŸ‘ŒπŸΌ

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490

Please Login or Register in order to submit comment