Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ajikin mudi fuskarsa ajike da ruwa da alamar ruwa aka shafa masa

Yaja ajiyar doguwar zuciya wanda saida yaji kirjinsa ya motsa yaji wani nauyi idonsa yayi

Dakyar ya iya bude idanuwa yatashi zaune saida yadau mintina yadawo hayyacinsa ashe momy laila da Alh suma suna dakin kusa dashi

Dasauri Alhajin yajanyoshi jikinsa yana fadin "sannu Aliyu ka farfado,sannu meya faru dakai?


Hjy laila ma tahau antayo masa tambayoyi '"Aliyu me akai maka harka fadi ka kasuma?


Gaban gadanga ne yafadi Suma!?

ashe suma yayi ma

Kalaman Zainabu yadawo masa "Gadanga sun kashe mana inna...

Wasu hawaye ne masu quna suka xubo masa lallai inhar da gaskene abunda zainabu tafada to za.ayi tashin hankali kuwa dan baxai bar wanda yakashe masa inna da raiba kakar dabaida kamarta wacce ta maye masa gurbin iyaye baisan maraiciba baisan wahalaba itace kominshi tun yarinta tayi aikatau sbd taga yaci yasha yasa sutura itace surfau wankau da saide saide na kayan miya danye da bushashshe da kuma saida itace saida yagirma tarage yin wahala

Tabbas za.ayi tashin tashina a kauyen marina

Hankalinsa ya dugun xuma ransa yabaci idanunsa sukai jajir kwanjinsa suka tashi suka murde kumatunsa yahau rawa lebensa yahau motsi duk ckn bacin raine

Dady yadafashi yana rarrashinsa don yafara fahimtar wani abun atattare dashi yasan akwai matsala

Gadanga yaja wata sassanyar ajiyar xuciya yana hawaye yace "dady sun cuce ni sunmin illa sunkuma yimin gibi arayuwata...yafashe da kuka me tsima rai


Dady akidime yahau tambayarsa

"Su waye?me sukai maka Aliyu?

"Sun kashe min inna yanzu aka bugo aka gayamin walh baxan barsuba.

Zumbur dady ya mike tsaye yadafe kai yana fadun "innalillahi wa inna ilaihir rajiun.

Momy ma rikicewa tayi harda hawayenta hannunta aka tana fadin "lahaula wala quwwata illaillah...

Mudi ma hannu yasaka aka yana fadin "wayyo Allah inna ta mutu? suwaye suka kasheta?


Aliyu yahau kuka yana basu labarin da zainabu tabashi wai daukan fansa sukazo yi masa shine suka kashe inna.

Dady yace "Amma kosu waye saimun dau mataki akansu maxa shirya muje kauyen.

Ba wani shiri da Gadanga xaiyi sai mikewa yayi kawai yai waje suka mara masa baya

Allah sarki dady yamance damuwar ma dayake ciki na rashin d'iyarsa wanda ahalin yanzuma waya sukayo kancewar inbai basu naira miliyan ukuba to zasu kashe masa "ya.


Dukansu suka tafi har mudi da ilu a mota daya banda momy

Don ita zuciyarta akarye take bazata iya xuwa taga gawar innarba gashi dama ba lfy ce ta isheraba tunda aka rasa khalisat take fama da rashin lfy

********
Koda suka isa kauyen ba.a kai taba shi ake jira amma anhadata

Sosai yan kauyen suka shiga tashin hankali ancika kofar gidan inna makil kowa yai jigun jigun gefe guda yaran gadanga ne sunata kuka

Mata sunata shiga gidan
Iya kulu mahaifiyar Alh makwabciyar inna tamkar yar,uwarta take kuka da shabune harta gaji dayi ita da abin yafaru akan idonta

Tafi kowa shiga tashin hankali kuka kawai tana kiran sunan Allah

Mutane suka mimmike ganin isowar motar Alh

Akaita basu guri

Mudi na rike da hannun gadanga wanda ke xubda hawaye dukda cike yake da jarumta amma yakasa tsaida hawayen

Ashe dai dagaskene innar tasa ta mutu knn

Ya dade tsaye akan gawar inna yana kuka ana hanashi don bata bukatar kukansa sai addu.arsa

Zainabu na can kurya tana jiyo sautin kukan Gadanga itanma kukan take sosai gwaggonta na kusa da ita

Kowa a tu,ajjibi yake

Saida aka sallaceta aka tafi kaita

Gadanga yai matuqar jarumta da akaje makabarta don kukan sa daukewa yayi shiya rike kafafunta aka shigarta kabari

Sunyi mata addu.o.i

Saida aka dawo gida suna xaxxaune akan tarbarmi suna karbar gaisuwane yaji hawayen yadawo masa natuno inna dayanda take masa kirari inya dawo daga farauta ko gangi...

"Gadanga kusar yaki!
inbasuyi subada guri ga zaki ya faso!

ka gagara kasha kansu na inna!!

Ali gadanga jan zaki!!
sha gwagwarmaya dodon maza!!!!

Cau!cau!!inna Allah dai yabiya.abinda yake ce mata knn intana masa wadannan dad'ad'an kirarin baisan suna masa dad'iba sai yau

Shikenan yarasa me faranta masa knn yanzu wazai ringa masa kirarin nan masu dadi!?


Yaso ya kebe da yaransa donjin mafita ammaba dama gun acike yake dam da al,umma harda na makwabtaka da kauyen sunji labari sun zoxxo


Ashe Alh yayiwa yan sanda waya aranar sadakar uku saigasu motoci biyu sukai shammata a kauyensu Amadi aka dank'o yaran amadin har amadin da baida ishashshiyar lfy tunda shiya turasu su kashe Ali gadanga sukuma suka kashe masa inna

Mutane na kallonsu ana musu tofin alatsine akai birni dasu don mikasu ahannun hukuma aimusu hukunci daidai da abinda sukai

Dady yasan inba hakan yayiba to tabbas za.ayi barna yasan gadanga zai iya komi shikuma bayason azo ayi danasanin barna gara yasa hukuma aciki

Gadanga yaji dadin hakan

Ranar sadakar uku Alh yatara yaran gadanga yai musu nasiha akan sudaina yin gangi su zauna agidajensu sukama sana.a yafi musu mutunci yakumace subar mgnr kada su tayar don zasu girbi abinda suka shuka

Yana shirin yi musu sallama yakoma birni aka bugo masa waya da bakuwar namba

Wadanda suka dauke masa khalisat ne ba nambar da suka kirashi kwanaki bace da suka bukaci kudi sun rufe ta wannan etisalat ce

Da kakkausar murya suke masa worning da tuni kan cewa inhar bai turo kudin nan da sati gudaba to kada yakara tunanin yanada "ya aduniya zasu sheketa

Suka saka masa muryar khalisat tana kuka

Agigiyace yahau kiran sunanta khalisat!khalisat!!

Tace "dady dan Allah katuro musu kudin kosa sakeni walh zasu kasheni yauma sun kashe wasu awahalce nake dady....tsit suka katseta

Yadaina jin yar tasa sai muryar namiji yaji yana fadin "yaushe zaka kawo mana kudin?

Dady yace a gobe ko yau inkun fadi inda zan kawo muku.

Gadanga ne ya warce wayar ahannun Alhajin don yaji komi ransa abace yahau fadin "waiku su waye ne marasa mutunci.!!!

Aka sheke da muguwar dariya akace masa "yan garkuwa ne wadanda basu san raini ka iya bakinka don inkai mana shishshigi zamu kasheta kudaina jinmu

Jikin gadanga yahau tsima "metayi muku kada ku kasheta ko nawane za.a baku.


"Miliyan uku ma kawai mukeso ba yawa

""to.,!to..za,a baku a ina za.a kawo muku?


"Zamu fada muku gurin dakuma sharadai masu tsanani don inhar kuaka karyasu to baku ba "yarku.

Gadanga yace "wadanne sharadai zamuyi


Diffff!yaji sun kashe wayar "yan rainin wayone na karshe sunkuma iya yawo da hankali.


Gadanga yaita fadin "hello!hello

Dayaji shiru yaduba yaga ashe sun kashe saiya mikawa Alh wayar asanyaye yana hawaye

Alh yakarbi wayar yadafa shi yana fadin "kada ka damu Aliyu haka Allah yakaddaro mana jarabtace abinda yafi kawai mubisu ahankali har Allah yakawo rabda zasu bamu itan zankuma tanadi kudin nasu don jiran kiransu

"To amma Alh kasanar da hukuma aduk lokacin da suka baka kada ayi abu aboye atabbatar ankamasu

Murnushi kawai Alhajin yayi

Baikara cewa komiba sukai sallama

Yatafi ko mahaifiyarsa bai gayawa halin da yake cikiba kada hankalinta yatashi tunda tana ckn alhinin inna


Gadanga abunne yahadar masa amma harga Allah yaso yabi Alh ayi komi yananan domin ashirye yake dayai gaba da gaba da "yan garkuwan nan.

Tunanin khalisat yarungayi yana tausayinta don yasan tafuta hayyacinta kuma kamar horo sukai mata hakan zaisa tarage wasu halayyar tata marasa kyau


Yakamata ace yabi Alh domin yataimaka da wani abun

To ta wace hanyar gadanga kaiba hukuma ba? πŸ˜ŠπŸ˜‚



Ya qudurta aransa ana sadakar bakwai zai koma birni cikin shirin kota kwana don dole zaije ceton khalisat shiya kamata yakai musu kudin don ya isar da qudurinsa akansu......






_Muje zuwa_







*Auntyn Sayyada da Shahida* ce?*ALI GADANGA...*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹






*Short Story*




*Nabilancy Luv*πŸ’˜
(Auntyn S&S)





*Dis page dedicated to my Sisters*

*Batul mamman*( Gumin halak)

&
*Ummi Aisha*(Dan Asali)




Page 1⃣7⃣


ANA gobe sadakar bakwan inna mallam baffale wani dan,uwan innar da suke "yan maxa zir daga nijar yazo suka keb'e shida kawun Zainabu agidan iya zulai suka tattauna akan daurin Auren da suke da shirinyi da safe in anyi addu.ar bakwai su daura Auran gadanga da zainabun wanda ko gadangan baisan bikin da akeyiba

Suka gama shirya komai iya kulu ce tabada kudi dubu ashirin da d'anta yabata kafin yatafi amatsayin sadakin gadanga baffale yaita gode mata tace "ai ba komai gadanga nima ai nawane balle yanzu rikonsa na hannun d'ana


Kawun zainabu yace su sanarwa gadangan da zarar andaura yadauketa kawai yatafi da ita birni


Washe gari kuwa ana yin addu,ar bakwai aka hau daurin aure tun mutane basu watseba dama adaren baffale yaje yasiyo goro da alawa

Gadanga yasha mamaki najin andaura masa aure batare daya saniba

Yarasa bakin magana yai shiru kansa yadaure yama rasa mezaice yashiga wani yanayi shin farin ciki xaiyi ko bakin ciki?

Yanaji yana gani aka daura masa Aure akan sadaki naira dubu 20 lakadan ba ajalanba.

Akaita tayashi murna ana masa Allah yasanya Alkairi yanata washe baki yana amsawa

Yaringa jinsa wani iri waiyau yazama ango,angonma ga wacce yake so,

Saida aka watse yahau farin ciki wai zainabu taxama matarsa to yanzu yakenan zaiyi baida kudaden da xaiyi mata hidimar aure gashi gidan innar babu wani kyakykyawan gyara balle ya ajiyeta ack


Yana zaune shikadai ackn gidan yana tunanin inna yana ckn kadaicinta yasan rashin tane yasa akai shawarar yi masa aure don su faranta masa.

Baffale yashigo shida iya kulu

Iya tazauna akusa dashi haka shima baffalen zaman yayi yana ce masa "gadanga kukan me kake kaxauna kana hawaye kamar karamin yaro.

Baimasan hawayen naxuba ba saida baffale yafada yai saurin saka hannu yafara gogewa yana kirkiro murmushin dole

Iya kulu ta gyara xama tace "Allah dai yasa ba karanbanin da mukai maka na aure ba shawara bane yabak'anta maka rai har kake xubda hawaye ba?

Gadanga yace "a,a haba dai iya kada kiyi wannan tunanin sam banji haushinkuba komai kukai akaina daidai ne baxaku taba yin abinda xai cutar niba kumafa iyaye ne aguna ko bana son xainabu baxanji haushin kuba balle ina sonta godiya ma yakamata nayi muku dan nasan manufar ku danku faranta minne.


Baffale yace "wannan haka yake gadanga nasanka da hankali da bin nagaba dakai kaga wannan tsohuwar ka gode mata itace ta kawo wannan shawarar mekyau takuma bada sadakin da aka baiwa zainabu na auranka munkuma yi hakanne sbd mu maye maka zuciya da farin ciki don munsan zcyrka na cike da bakin cikin rashin kakarka


Iya kulu ta cafe da cewa "gadanga inaso kadaukeni tamkar yadda inna take agunka banaso kabar kauyennnan kwata kwata inaso inka tafi karinga waigomu nasan inba zainabun aka bakaba inhar kayi aure a birni baixama lallai muringa ganinka akan kariba yanxu kuwa nasan koka tafi da zainabu to dole wataran xaka ringa xuwar mana.


Gadanga yai murmushi yace "to ai iya baxan tafi da xainabu yanxun ba saidai nan gaba inna sama mata matsuguni tukunna.

Iya kulu tace "akan me , a,a katafi da matarka kawai don nasan baxaka rasa dakuna agidan Alh ba


Akwai qudiri aran gadanga shiyasa yakeso yaxille tafiya da xainabu don so yake ya gina kansa yakuma sami gidan kansa ba karereba gashi inya koma yanxun yanaso ya shirya futa artabu da "yan garkuwa


Duk yadda su iya kulu suka so yatafi da zainabu birni gadanga yaki yai musu dabaru kancewa saiwani xuwan in yayi zaije yayi mata shiryeye


Sannan ne suka hkr suka barshi ammafa suntausaya masa don harya fad'a


Adaren yaxiyarci amaryarsa xainabu wacce tunda taji andaura musu aure take ckn farin ciki d'okinta kawai angonta yaxo taganshi

Aiko dai dayaxo din tamkar ta rumgumeshi taringaji gashi dai kunyarsa takeji gashi kuma babu fuska gun gadangan ba yabo ba fallasa tunda inna tarasu ma basu kebe ba tasan yana ckn alhini shiyasa tayi masa uxuri takuma tausaya masa ganin yarame

Basuyi wani hirar arxikiba kamar yadda suka saba inyazo ita tafara masa mgnr tafiya ma

"Yaushe xaka koma birni.?

Yayi jim kana yace "gobe in Allah ya yarda.

Kamar tace masa Amma dai tare xamu tafi ko???....

Saita kasa amma tayi addu.a ckn ranta Allahv yasa yace mata hakan

Kash!ranta yai baki dataji sabanin hakan

"Ki kama kanki banaso kiringa futa koina infutar taxama dole ki kirani awaya kigayamin tunda yanxu kinxama matar aure dole ki kiyaye inna tafi baxan dade ba xan dawo intafi dake

Ta gyada kai kawai.

Yakawo dubu biyar yabata (Alh yabashi kudi kafin yatafi yakuma sami kudin sadaka.)

Tayi godiya kamar tafashe da kuka suka rabu ckn shaukin juna

Yaso yatafi da itan amma ba dama saiyayi shiri gashi yanajin wani abu atare da ita

Itanma tashiga wani shauki dabata taba jinsaba mijinta xaiyi nisa da ita.

******
Ilu ne yaxo daukansa tun sassafe

Yayi sallama da kowa yatafi sungaisa da ilu dayake ganin girman gadangan yanzu

Ilu akwai surutu yaita zayyanewa gadanga halin da ake ciki na labarin khalisat

"Ai ayau akayi xa.a kai musu mak'udan kud'ad'en da daddare
Cewar ilun

Gadanga yace "waye xaikai?

Ilu yace "kudin suna hanun sipeta musa jami,in nan dan tsamirmiri me kama da k'olawa sunce kada afadawa jami,an tsaro inko aka taho da hukuma to za.a rasa khalisa

Gadanga yace "inkasan gidan sipeta musan ka kaini can, nixan karbi kudin nakai musu amma kada kagaya kowa nadawo akwai abinda nakeso nacimma karike wannan alqawarin.

Ilu yahau gyada kansa "to...to.,angama ranka ya dade.(ilu nashakkar gadanga don yaga bayason wargi yakuma ga yadda akai maganin uwar gidansu khalisat agabansu yakuma xauna lfy.)

Koda suka shigo kano kai tsaye gidan inspector musa yakaishi kai tsaye

Daya sadashi da insp.musa nan yatafi yabarshi

Koda suka kebe gadanga yabayyana masa qudirinsa nason yabashi kudin yanada shirinsa akansu zaikuma karbo khalisat ckn kwaciyar hankali

Yanayin gadangan ne yagamsar da insp. Amma yatambayeshi cewar "amma bakaga zaka iya fuskantar matsala koka taki wani abunne?

Gadanga yace "nayo shirina tsaf daga kauyen mu nasha maganin bindiga da wuka babu abinda suka isa suimin ashirye nake dana kara da "yan boko haram ma kada kaji komi inspector saina danko maka duk wanda yashigo hannu na aranar acknsu.

Insp. Yakarewa gadanga kallo yana gyada kai don yaga k'irar karfi atattare dashi ga kamannin "yan maxa ma atare dashi to amma duk da hakan saiya bashi tsaron sirri baxai bari yaje shikad'ai ba sbd gudun tab'aci......



_Muje zuwa_………




*Auntyn Sayyada da shahida ce*πŸ‘ŒπŸΌπŸ˜ƒ?🏼*ALI GADANGA...*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹





*Short Story*




*Dis page Dedicated to my Sisters Batul mamman &Ummi Aisha*





*Nabilancy Luv*πŸ’˜
( Auntyn S&S)





Page
1⃣9⃣




Kowa saida yakadu dajin wannan batu na mutumin hatta likita saida ya mamakantu lallai duniya abin tsoro ce wanda kaba amanna shike neman halakarka

Gadanga ma yaji mamaki tunda yasan Safraz din abokin sheke ayarta ne lallai zai gane kuransa dan ba.a barshiba

Hajiya laila ta hau gyada kai tana masa allah ya isa ackn ranta

Alh kuwa kasa magana yayi don takaici nacin amanar nan me ban al,ajab

Insp.musa ne ma yamatsawa wannan mutumin da tambayoyi akan bayanan adress din gidansu safraz dake kaduna

Mutumin yahau kwana kwana yanaso yabada bayanan bogi dan asake amma abin yaci tura domin duk unguwar daya ambata take insp.musa zai hau tambayar sa gidan waza.ace domin shi din haifaffen kd ne aikine yakawoshi kano yasan koina akaduna

Ganin zai raina musu hankali yasa suka fara dukanshi ba tausayi duk da yana gadon asibiti

Aifa dayaji najidu take yafara bada bayanan gaskiya

Dady yace "kubarshi hakan, kuma tunda yafada kada abarshi atafi ashi kawai yaxama jagora yafi.


Hakan kuwa akayi dama don sunga yana kwance agadon Asibitine shiyasa basui niyyar xuwa dashiba amma dasuka gano nufinsa na sanfewa dole dai aka tusa shi gaba aka nufi kd unguwar T/wada dashi


Koda suka isa kaduna amotarsu ta aiki tareda jami.ai hudu da insp.musa ack suspect din yana baya atsakiyarsu yana daure da ankwa yai tsuru tsuru dashi



Da yammaci suka isa gdn mahaifin safraz ya dawo gidansa shida baki suna farfajiya ckn wata yar rumfa suna tattaunawa sai ganin motar yan sanda sukayi ta shigo har ckn gidan

Horn sukaita matsawa me gadi dole yabude suka shiga basubi takansaba dayake dan filanin rigane atsorace yabude musu


Sukai faking kuda da rumfar dasu Alh Zakari suke suka fito sudukansu banda suspect din da jami,i daya dake tsaronsa


Alh zakari mahaifin safraz yayi mamakin ganin jami,ai har ckn gidansa take jikinsa yabashi da alamar Safraz ne yaja masa magana yau kwana biyar baisakashi a idoba yabar gidan yana hkr da halin safraz gashi shi kadai Allah yabashi yakuma jarrabeshi da mugun hali yana basu wahala ainun suna matukar nuna masa so kuma


Azaton Alhn ma ko duka yaiwa mutumin ckn motar dayagani kusada dan sanda fuska a kumbure

Ya kadu matuqa dajin abinda yakawo su insp. Domin bai zaci abin yakai nan ba


Dan sa safraz yazama dan garkuwa? To yaushe yazama hakan? Meya nema yarasa duk arxikinsa bai nema gunsa ba zai nema ahanyar haram tabbas mugayen abokaine suka sashi ahanyar hakan.


Alh zakari yagoge kwallar takaicin data xubo masa yadubi insp musa yace "ayau nayi tir da haihuwar safraz banxaci zai iyayin wannan muguwar ta.adarba duk da ina tsammanin mugayen abokai ne zasu sakashi yin hakan tunda nakaishi kasar waje yai karatu shikenan kyawawan halayensa suka canxa ayanzu hakan zaman da kukaga munyi da wadannan abokan nawa zancensa muke aure xamu kulla atsakaninsa da yar abokina duk dan yagyara halinsa yau kwana biyar bansashi a idoba bansan kuma inda xance muku xa.a sameshiba


Insp. Musa yace "to mudai kam xuwan da mukai baxamu tafi ba sai dashi kokuma kamaye gurbinsa har saiyashiga hannunmu kana musake ka.


Take abokan Alh sukahau fada akan baxa.ayi hakan ba sunata cacar baki suna fadin akan me zaku yarfatashi kunsan matsayinsa kuwa walh ba,za ayi haka muna kalloba……

Alh zakari yadaga musu hannu yace "kada kufadi hakan komi da kuka gani yafaru akaina kaddarata tace kuma aidama dan kuka shike jawa uwarsa jifa kumuje kawai. Yamike xaibisu knn yaji ankurma ihu ana kuka

Hjy jamila knn matarsa mahaifiyar safrax cewa take "walh Alh baxaka tafi kabarni da tunani b saidai in ahada dani atafi


Abokansa suka hanata tana kokarin shiga motar tana kuka hkr suke bata amma ina saida ta sami mazauni dama da hijab dinta ajiki taji komi akunnenta dama taga shigowar motar yan sandan

Alh zakari yace "kubarta muje taren kunga dole labari zaije masa cewar iyayansa duka suna hannu hakan zaibashi damar mika kai inhar yana sonmu kamar yadda muka soshi .



Jin abinda yafada suka gaskata hakan

Dole hakan akai aka tafi dasu dukan zuwa kano

Abokan Alh zakari sunji ba dadi aransu sosai su ukune manyan aminansa na arxiki aiko dai sai suka baxa jami.an tsaro da "yan gari neman safraz

To ashe mutuminku safraz yana wata mabuya aboye yanada labarin iyayen Khalisat sunji komi ahalin yanxu tunda sunkama yaronsa yasan dole inyaji wuya zaifadi gaskiya dole tasa ya buya ko gidan iyayansa baya xuwa

yana shirye shiryen barin kasar knn yakunna television yaga ana nemansa ruwa ajallo daya mika kansa zuwa state C.I.D kano don ankama iyayansa adalilin anxo kamashi ba.a sameshiba

Ya girgixa ainun harda xu da hawaye take yakunna wayarsa daya dade da kasheta

Take yaringa ganin sakonnin bayanin kama iyayansa nashigo daga abokansa "yan arear


Bashiri tafiya abroad ta fasu yanufi kano don yamika kansa sbd yana son iyayansa ainun bakuma zaiso sukunyata ba

Jami,an tsaron basuyi mamakin ganin saba don dama sunsan hakan xai iya faruwa ansha yin hakan kuma

Koda aka damkeshi aka turashi sell sai aka fito da iyayansa

Hjy jamila kuka tayi tayi tana cewa "kacuci kanka safrax ga abinda rashin jin mgnr iyaye yaja maka

Shiko uban cewa yayi "kaje munyafe ka kada kasaka ran zan fito dakai dakudina sbd kacutar dani bantaba shiga sell ba sai adalilinka


Haka yanaji yana gani suka tafi

Abokansa yaiwa waya sukazo daukarsu suka maidasu kaduna.



*****
Koda khalisat ta samu sauki tafarko hjyrta tafara gani akusa da ita

Hjy takama hannunta tana fadin "sannu khalisat Allah yasaka kinji wannan abu dasukai miki baxamu yafeba sun miki ciki gashi har Allah yasa yabare Sannu mungode Allah ma da kk kubuto dg garesu amma da kokarin Aliyu komi yazo mana ckn sauki har muka gane wanda yai xamo silar da aka saceki.

Arikicd ta tashi xaune tace da momyn "waye momy ?plz waye yasa akaimin hakan?

Hjy laila tace "wanda aka kama daya dg cikin yan garkuwar yace saurayinki Safrax ne ……


Ta dafe kirji idonta awaje tace "innalillahi wainna ilaihir rajiun. Safraz kuma momy,?shida yace min zaibar kasar zaikoma karsa waje auren dole za.ai masa da "yar kanin babansa amma Allah ya isana safraz aibansan macuci bane sai yau Amma nayi nadama yacu eni yaimin ciki gashi har.... 🀭 sub'utar baki tayi tayi saurin yin shiru tana kuka

Momy ta kura mata ido tace "wato dama ashe ma kina makale da cikinsa baki gaya min ba amatsayina na uwarki amma kinbani mamaki khalisat to ai gashinan yakaiki yabaro don ma mun samu yaxube da bamusan yazamui da abin kunyarba don kin san dole asirinmu yatonu dabai xube ba tunda in yana hannu yazamui da cikinsa

Kukan da khalisat keta sharbawa na nadama yasa taja baki momyn tayi shiru don bataso tasata adamuwa

Nadama sosai tayi ayau taringaji inama batasan safrax ba gashi yaso yazama ajalinta yaci amanarta

Momyn futa tayi tabarta adakin ita kadai

Ba waya agunta data kira kawarta khairat

Ta lumshe idonta tana tuno artabun da gadanga yayi da yan garkuwar nan tabbas yagama burgeta ashe haka yake da karfi shine yazo cetonta tabbas baxata mance a alkairin saba taji wani qaunarsa aranta duk tsanar datayi masa taji tagushe fuskar gadanga taringa mata gixo lallai naka sai naka yau gashi gadanga yai mata rana inama zai maye mata gurbin safrax...


Momy nafuta adakin tasa waya ta kira khairat kawar khakisat

Khairat na dagawa tahau tambayar momyn ko gaisawa basuiba "momy ya labarin khalisat dafatan sun basa ita.?

Momy tace "inkina gia kitaho yanzu Nabnur hospital muna can ansamu nasarar karbo ta kizo yanzu maza.


Ckn gaggawa khairat tahau shiri bata tsaya jiran dreba yakawata bama ta tuko kanta sai gata a ckn asibitin ta faka a farking space takira momy donta fada mata lambar dakin da suke momyn tace mata ta taho lambu tasameta tana can

Can bayan dakunan dake ckn asibitin aka ajiye kujeru ckn wani dan lambu nashakatawa

Data iso lambun tahango momy tanufota da sauri tagaidata har kasa

Momy ta amsa tareda cewa "zauna khairat ingaya mk damuwata.

Khairat

Kha taxauna tana fuskantar momy

Momy tazayyane mata komi tana kuka tana cewa "bansan khalisat lalata take yi inta futaba saiyau data furta min cewa ckn daya zube na safrax ne dole zan damu najin haka khairat amatsayina na uwarta zanso inga tayi aure to gashi ta lalata rayuwarta ta bata lokacinta abanza gun dan iska mayaudari yanzu waye xai aureta alhalin tana wulakanta samari acan baya gashi kuma tagama xubda mutumcinta?.


Khairat ta dafe kanta "oh my god! Momy kiyi hkr komi zaizo ckn sauki wannan tamkar wata kaddarar tace haka Allah yarubuta dole sai hkn yafaru kada kisa abin aranki yadameki plz momy addu,a zakiyi mata akan Allah yafuto mata da mjn aure kawai amma yanzu na tabbata itama tana ckn damuwa olx mom.

Ta durqusa kasa tareda rike hannun momyn

Hjy laila tace "ba damuwa nagode khairat zantayata da addu.ar kema kuma inaso kiringa bata shawar me kyau dan Allah kuzama nutsatstsu kuyi aure kafin mutuwarku ta riskeku agidan iyaye aure shine mutuncin "ya mace da kuma ci gabanta arayuwa.

"To momy zamuyi ayi mana addu.a.


Cewar khairat.

"To tashi muje na nuna miki dakin da take.

Suka mike suka nufi dakin da aka kwantar da khairat din.……




*Auntyn Sayyada da Shahida ce*πŸ‘ŒπŸΌπŸ‘ŒπŸΌ
*ALI GADANGA...*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹




*Short Story*





*Nabilancy Luv*πŸ’˜




*Dedicated to Batul mamman & Ummi Aisha*



Page 1⃣8⃣


Ali gadanga baiyi rintsaba yana kan dadduma yanata yin nafilfili yana addu.a akan Allah yadorashi akan wadannan muggan mutanen da xai tunkara

Dayake sunyi dasu ckn dare karfe biyu su hadu awata mahada da babu gine gine a arear


Ta wayar inspector suke communicating sbd yaboye matsayinsa na ma,aikaci yace musu shi kanin mahaifin yarinyar ne ,don sun kafa dokar kada asake asanarwa jami,an tsaro inhar suna son "yar su to dole abi dokarsu.


Baida nufin yaje da kowa amma gadanga ya karya masa qudiri yace lallai shi xaije musu da kudin yakarbo khalisat sbd wata manufarsa kuma yace kada yagayawa Alh dan baxai barshiba

Insp. Musa yagargadeshi akan ya kiyaye inyaje garesu yabi dokarsu da kaidojin da zasu kafa masa kfin su hadu

Insp.yabashi wayarsa don yasan zasu kirashi

Tare suka tafi mahadar ya ajiyeshi tare da bashi jakar kudaden shikuma yabuya a wata mabuya

Yakarbi wayar gadanga sbd ko zaiji wani abun dg gareshi

Gadanga yafi minti goma atsaye ckn duhun daren kan wani dutse yadauko wayar insp.dake aljihunsa yaduba yaga biyu da kwata na dare

Sosai sunyi targeting din komi shida inspecta kan cewa zai taimaka masa da kawo hari garesu na harbi inyaji wata hatsaniyar.

Yananan tsaye yaji wayar ta dau b'urari

Yadauka tareda karawa akunne "dafatan kazo gurin da mukace mk kuma dafatan kai kadai kaxo?

Gadanga yace "nazo tun daxun kuma ni kad'ai naxo.

"To kajira muna nan tafe.

Aka katse wayar

Ko d'ar gadanga baijiba aransa ya dada gyara tsayuwar don jira.


Daga nesa yaga haske ya dunfaroshi na mota

Yahau

Please Login or Register in order to submit comment