Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

addu.a ckn ransa

D'an nesa kad'an suka tsaida motar suka bude suka nufosa

Subiyune jal maxane daya yaiwa khalisat kyakykyawan rikon da baxata kufceba ko motsi takasayi ahannunsa k'akk'arfane na gaske amma baikai gadanga kwanjiba

Dayan kuma baya yake take musu shike bugo waya

Sokoncin da sukai da basu taho da makami ko bindigaba kananan yan kidnapping ne ashe

Wanda ke rike da khalisat ya dubi dan,uwan nasa yace "maxa jeka yabaka kudin inyaso mubashi ita.

Gadanga ya gyara tsaiwa tareda ajiye kudin akasa mutumin naxuwa yaduka xai dauki kudin knn yaji muguwar shaqa awuyansa saida gadanga yakaishi kasa yabuga masa hannunsa aka take mutumin yafadi sumamme

Wanda ke rike da khalisat ya harxuka ya shake wuyan Khalisat tahau kakari yakai mata naushi ack

Takurma wani wahalallen ihu can kasa dan wahala

Gadanga yahau fadin "dakata kada ka kash
heta dani yakamata ka fafata bada mace ba.

"Gara nakasheta tunda baka son yar,uwarka gashi ka fanshi ran dan,uwana anata zan kasheta kuma natafi da kudin kaima kuma baxan barkaba.

Gadanga yace "kai karamin dan,iska matsoracin maxa kabarta kaxo gareni inba tsoro ba...kufula yayi yai wurgi da khalisat gefe yayo kan gadanga

Ji kake k'ummmm!!!

Tafada kan wani dutse me tsini take goshinta yabugu yafashe yahau xubda jini haka cikinta ma yabugu nan take abinda ke cikinta yafito yabare cikin jini yahau kwaranyowa


Tafita hayyacinta amma ihun data saki kafin takai kasa yakai kunnen insp.musa take yafito dg abuya yanufo gunsu gadanga

Yana xuwa yaga suna artabu sai caskalen dan bidda suke gadanga nakai masa naushi shima mutumin yana kawowa gadanga shikuma gadanga na kaucewa

Insp.yasaki harbi sama take mutumin yagigice yatsorata ainun ya ari ta kare yanausa ckn daji

Gadanga baibishiba yanufi gun khalisat da sauri tsoronsa kada ta mutu

Yahau girgixata yatsorata ganin jini akasanta yana xuba

Yahau cewa insp. "Wayyo inspecta ta mutu kaga bata motsi yaxamuyi ..

Insp. Yatabata yaduba sosai yace "da ranta bata mutuba sata amota muwuce da ita asibitin dasuke da file acan.

Gadanga yace" to amma kayi kokarin daukar motar mutanen nan gatacan kasaka wancan atafi dashi asibitin da alama suma yayi kaga inya farfado sai ayi bincike akansu.

Insp. Yadauko jakar kudaden yasaka amotar mutanen yakuma janyo mutumin nn dake sume akasa yasashi ckn motar tasu ๐Ÿ˜… yaji dukan maza


Amotar dasukaxo ta insp. Yasaka khalisat yaja yanufi NabNur special hospital dayake yajejje sau uku duba hjy laila data taba kwanciya


Yayi kokari dayakai kansa ckn dare bai bataba

Shima insp. Bayansu yabiyo

Saida sukaje asibitin aka basu gado sannan inspecta yakarbi wayarsa gun gadanga ya kira Alh yasanar masa duk yadda akayi amma insp yace yakwantar da hankalinsa kada yataho ackn tsohon daren nan ciwon na khalisat dinma kadanne likitoci na kanta

Dakyar Alh ya iya barin akai sallar asuba sannan yahau shirin tafiya asibitin koda yagayawa hjy laila itanma cewa tayi bataga taxamaba tabiyoshi

Ilu ne yakaisu ahanya yake gaya musu aitun jiyan shiya dauko gadanga akauye yakaishi gidan insp.

Alh yahau gyada kansa yana jinjina ga jarumtar da gadanga yayi

Lallai gadanga yai ms komi baxai manta da alkairin saba yau yakara yarda gadanga na masa son gaskiya dole yakara masa riko mekyau kuma xai kara masa matsayi ackn gidansa da gun aikin sa.

Koda sukaje asibitin Alh yatausayawa yarsa ganin yanda duk ta koma ta rame fuskarta tayi fiyaut ga goshinta da bandage anyi kokarin yin komi akanta jinin datake xubdawa yatsaya

Duk sun taru akanta gadanga,insp musa,ilu,Alh da hajiya likita yashigo donyi musu jawabi

Hjy laila sai share hawaye takeyi najin tausan "yarta

Likita yadubi Alh yace "Alh ai anyi babbar sa.a ma da bata sami wata babbar matsala acknta ba don ta bugu dayawa sakamakon hakan ma cikin dake jikinta yaxube...

"Ciki!Ciki!!???


Atare duka suka fada suka hau kallon kallo atsakaninsu

Alh yace "haba dai ciki likita ni bansan khalisat da cikiba

Likita yace "to ai da alamar cikin bai dade da shigaba na kwanannan ne koma dai meye mugodewa Allah kar mutsaya bude bude tunda har ya fita ta sauki ma

Hjy laila tasauke ajiyar zuciya tana goge hawaye wato ashe mugayen har ciki sukaiwa "yarta? Lallai dole tayi musu Allah ya isa.

Alh yace "likita ina daya patient din? Yadawo hayyacinsa?

Likita yace "eh munsamu yafarfado amma anyi masa allurar bacci domin da sambatu yafarko.

"To munaso yadawo dai dai sbd suspect ne zamu kawo yan sanda gunsa akwai binciken da zamuyi akansa sosai, cewar Alh



Gadanga waje yafice yana tunanin wananna Al,amari na xancen ckn daya futa ajikin khalisat zuciyarsa tashiga wasi wasi Allah yasa dai bacikin sa bane, take wata zuciyar ta kwabeshi daina wannan tunanin ma kamanta cewa tasaba bin maxa bakaine farau ba,kuma ai baka xuba mata aciki ba kafuta kaga kenan banaka bane dama.

To ai ance ma cikin kwanannane bai dade ba kaiko da ka dade dayi!!! Zuciyarsa ta sake jaddada masa

Yazauna akan baranda yadafe kansa tabbas khalisat ta cuci kanta domin yasan ba yan garkuwane sukai mata cikinba dama ashe knn da abinta ajikinta.,!


*****
Sai dare dan garkuwa yafarko ckn hayyacinsa yana bude idonsa yaga jami,an tsaro akansa sunkai 6 kowanne da kakinsa da bindigu ahannu

Cknsane ya duri ruwa lallai yau asirinsu yatonu kashinsa yabushe

Yatashi zaune dakyar don jikinsa yai tsami na bugun dayasha gun gadanga gashi goshinsa akumbure yake yataba yaji bandage

Likitane yabada sallamarsa ganin yafarko qalau.

Suka tisashi agaba sai station

A bayan kanta aka sashi yai tsuru tsuru ana masa tambayoyi masu tsauri

Abinda yafara fada shine si dan kadunane kuma uban gidansu ne yasaka su su sato khalisat

Alh yana gurin yai xaton ko ackn wad'anda yake huld'ar kasuwanci ne sukai masa hakan to ashe ba haka bane jin wannan mutumin yace " Saurayin yarinyar ne sunanshi SAFRAZโ€ฆโ€ฆ!!!





_MUJE ZUWA_





*Auntyn Sayyada da Shahida ce*๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ๐Ÿ˜Œ๐Ÿ˜Œ
*ALI GADANGAโ€ฆ*
๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน






*Short Story*






*Dis page Dedicated to my sisters Batul mamman &Ummi Aisha*





*Nabilancy Luv*๐Ÿ’˜
(Auntyn S&S)






page 2โƒฃ0โƒฃ

Khairat ta tura dakin tashiga da dokin ganin aminiyarta


Jingine atsaye jikin taga ta hangota tana goge hawaye

Takarasa gareta da sassarfa ta janyota jikinta tana fadin "kawata sannu kinji kinganki kuwa walh dun kin rame.

Khalisat tahau kuka tana fadin "khairat Safraz ya cuceni Allah ya isana shiya sakani awannan halin ashe dama ba sona yk tsakani da Allah ba ashe dama maganar daya gayamin karyace yace xaibar garin sbd za.ai masa auren dole? Walh yacuceni yasa ansaceni don ya sami kudi.yasa ansaceni don acutar dani walh kinganni tunda naje baci ba sha sbd tunani Allah ya isana badan Aliyu gadanga ba datuni sun cutar dani da mahaifina


Khairat tajanyota xuwa kan gadon suka zauna tace "bani labarin me gadangan yayi musu har yau kk yabonsa mutumin da kk tsana.


Khairat ta goge hawaye tareda lumshe ido tana cewa "tabbas Ali gadanga kusar yaki ne yaci sunansa sbd yai artabu da mutanen nan wanda saida ya sumar da daya daga ciki duk don ya cetoni da kudin mahaifina walh tun alokacin ina hannunsu naji Allah yadasa min sonsa araina har kawo yau kuma sonsa karuwa yayi jin cewa ma ashe wanda nake yima zallar so shine yasa akaimin hakan


Walh kawata ayau ina cike da tarin nadamar abubuwan dana ringa yiwa Aliyu duk don fadin rai da son zuciya nabiyewa rudin shedan., tafashe da kuka me cinrai


Khairat tahau rarrashinta "kiyi shiru kawata nasan tunda har kk furta to tabbas da gasken gaske zuciyarki take akan Aliyu kada kidamu ai abune me sauki shima zai soki nikaina gayen yaimin tun wani lokaci danaxo gidan yadawo daga aiki naga baiwar da Allah yai masa ta kyau da kira

Tabbas naso nakai hari gunsa domin nayi nazarin inhar yaji kiwo babban mutum ne na nunawa sa.a alokacin shiru kawai nayi ban gaya mk ba sbd nasan zakiyi challenge akai kiga kamar na fado to amma tunda zuciyarki tayi karfi akai xan taimaka mk naga kin mallakeshi kawata kinga yanxuma mun tattauna da momy tagaya min tashiga damuwa nahalin da kuka kasance da safraz gashi yakaiki yabaro yanzu momy so take inkin wartsake kiyi aure tunaninta kawai to wazai aureki kina wulakanta mutane


Khairat ta tsahirta jin khalisat din batai maganaba yasa taci gaba "kinga yanzu dole ki canxa halayenki kixama macen kwarai donki burge Aliyu yaxama kina masa biyayya da bashi girma ke inaso ma kizama me yi masa komi tun daga sharar daki da girki da duk wani abunda zaiji dadi aransa har yaji kin burgeshi


Khalisat tace "kai!kawata baxan iya zama yar aikin saba akarkashin mahaifina fa yake saikuma ni inxamo akarkashinsa kai haba never!


Tsaki khairat taja "ashe baxaki iya janyo hankalinsa akankiba kina mace lallai to xaki rako mata duniya kinsan kuwa kyautatawa najanyo soyayya? Kuma krmeda kk so kiga gaba kinzamo matarsa inbakiyi yagani ba kina zaton zai yarda da xaki iya yi masa wahala amatsayinki na wacce bata saba ba.?


Khalisat tanisa tace "toh! Xan gwada kawata Allah yasa na dace.

Khairat tace "Amin.

Suna rufe baki aka turo kofar aka shigo


Dady da momy ne da kuma gadanga

Sukai tsit suna kallon gadanga wanda yasha wata shadda milk da hula milk yayi kyau ainun

Dady yace "sannun khalisat kinji.

Tace" yawwa dady ansamu nasarar kamoshin?

Yagyada kansa "eh ankamo iyayansa dafarko da ba.a sameshiba Sai yau kuma yakawo kansa dayaji shine aka sakeshu shi aka kamashi.


Momy tace "Aliyu yataho da abinci inxakici.

Takai kallonta kan gadanga dayake ta latse latsen wayarsa ta lumshe idonta ta girgixa kanta alamar baxata ci ba knn.

Momy tace "a,a ko shayi yakamata kisha bafa komi acikinki.

"To " kawai tace tasan tanajin yunwar ranta ne kawai ba dadi.


Khairat ta hada mata shayi hadin mutuku ta mika mata

Ta karba tahau sha ahankali


******
saida ta warke tsaf kana aka sallamota suka koma gida

Kullum sai khairat taxo gidan donta debe mata kewa

Iyayan khairat sunxo dubiyar khalisat gidan kullum sai anyi baki nayin jaje


Gadanga yakoma bakin aikinsa hankalinsa yakwanta

Saidai kuma tunanin matarsa zainabu yacika masa rai

Yanaso yadaukota to amma yafiso yasami gidan kansa bayaso yakawota gidan sbd khalisat yana tunanin xata bashi matsala

Koda hakan takasance da khalisat baiji wani tausan ta ba har yanzun tsanar dayai mata nanan daram aransa duk abubuwan datayi masa yakasa mantawa dasu


Karshen wata Kamar yadda yasaba yabiya ma,aikatansa albashi

Amma wannan karan yaninkawa gadanga salary yace zairinga bashi dubu dari duk wata na abinda yai masa na ceto yarsa yaji dadin hakan sosai bai zaci jarumtar Alin takai hakan ba

Gadanga murmushi yaringayi yana godiya ga Alhajin

Alh yace "baya ganan ma mota nasiya maka tana can a parking space honda ce naga ka iya tuki shiyasa nabaka ita kyauta duk da ba sabuwa bace amma ina mk fatan kasai sabuwa wataran da kanka Aliyu


Gadanga yadukar dakai yana kara godewa

Hjy laila tace "kai Amma naji dadi alhaji ina tayashi godiya Allah yabar xuminci

Alh yace "Amin, saidai inaso Aliyu kayimin wani taimako badan wai danka taimaka min din adole ranka baiso ba nabaka motar a,a inaso kayimin taimakon nan tsakani da Allah ne Aliyu


Gadanga yadago kai yakalli Alh yace "fadi ko mene zanyi shi zuciya guda babu tantama Alh nadaukeka tamkar mahaifina xantaimaka da komeye Alh.

Alh yace "So nake kayimin rufin Asiri Ka Auri khalisat!


Da sauri gadanga yakalli Alh yasadda kai kasa gabansa yahau dukan uku uku

Yahau fadin "inna lillahi wa inna ilaihir raji,un

Alh yaga firgice sosai a idon gadanga amma saiya matse yaci gaba "nasan xakayi mamaki domin abinda khalisat tayi bakowane zai iya aurenta yarufa mana asiri ba saikai na hanga nahango kaine zaka iya zama da ita ckn rufin Asiri munyi shawarar nan ne da momynta fatana ka amince domin inhar ka amsamin to walh ko tanaso ko bataso bata isa tabujere minba inko har tanuna rashin amincewarta to saidai ta nemi wani uban bani ba.


Gadanga kansa akasa yarasa tacewa "rana xafi inuwa quna. Tabdijan, ya auri khalisat yafaranta musu rai shikuma nasa ya quntata mezaiyi da fanko? Ga gredinsa can akauye kodan Alh baisan yai aureba shiyasa zai kawo masa zancen yarsa? Toko gara ya sanar masa ko zai janye kudirinsa.


A hankali yace"Alh nayi aure aranar sadakar bakwan inna aka daura min Aure da yarinyar da muke soyayya zainabu iya kulu ita ta bada sadakima ayanzu hakama shirye shiryen danake naje nataho da ita nan garin


Alh yace "to wannan ba matsala bace inhar ka amince da khalisat din sai inbaka gida kyauta a GRA me part 2 kazauna dasu kada ka damu dole tazauna da matarka ai.

Hjy laila ma hakan bae daga mata hankaliba najin gadangan yai aure itama fatanta ya amince musu.


Gadanga yadulmiya tunani "to inya amincewa ai baikyautawa ubangidan saba bai masa adalciba yanemi abu yaki masa harya bashi gida da mota da karin salary duk don ya auri yarsa, hhhhmmm yasan kuma yana khalisat ta tsaneshi baxataji dadin hakan ba inhar taganta yau amatsayin matarsa dole zata koka ta ciji yatsa kuma shi dama akullum burinsa yaga ya rama abubuwan data ringa masa to ai dama ce tazo masa ckn sauki, to meya rage masa kawai ya amince shi yafiโ€ฆโ€ฆ






_Muje xuwa Fans_





*Auntyn Sayyada da shahida ce*๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ
*ALI GADANGA...*
๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน






*Short Story*




*Nabilancy Luv*๐Ÿ’˜
(Auntyn S&S)






*Dis Page Dedication to My Sisters Batul Mamman & Ummi Aisha*





page 2โƒฃ1โƒฃ


Gadanga ya dago da kansa yakalli Alh yace "na,amince Alhaji Allah yasa hakan yaxamo Alkairi agareni.


"Amin Amin Aliyu."cewar hjy tana farin ck ta furta hakan


Yau gadanga yafarantawa Alh rai akaro na biyu tun xuwansa gidansa dole shima yaxamto me faranta masa ya murmusa tareda fadin "Nagode Aliyu abinda kaimin Allah yai mk na kyautatawa kuma inaso kasani badan na cuceka nai hakanba don inkara dankon zumuncine duk da kataimaka min ma domin nasan aurenka da khalisat zai zamar min ci gaba nida ita domin natabbata duk halayenta daba na kwaraiba dole zata xubdasu sbd tana shakkarka kuma nasan kaine kadai zaka rufa mana asiri aduk yadda kasameta kuma nasan ko bayan raina xaka riketa dakyau baxata wulakantaba nagode Aliyu kaidin jan gwarxone me amana da kyawun hali Allah yayi maka albarka yakuma jikan iyaye da kakanni.


"Amin..cewar gadanga



dady yace "yaushe kake ganin xa,a tsaida ranar da xa.a dauka auren ? Don baniso adau dogon lokaci


Gadanga yace '"duk lokacin daka tsaida yayi saidai inaso inje kauyenmu sbd intaho da zainabu.


Hjy laila ckn raha tace "sunan "yar tawa zainabu.


Gadanga ya gyada kansa


Dady yace "yaushe zaka tafin?

"Gobe insha Allah "


"To ba matsala tunda gobe friday inyaso ranar Sunday sai adaura Auren naku in an idar da sallah ko baka nan bakada matsalar sadaki zanbada a aljihuna โ€ฆโ€ฆ

Momy takatseshi da sauri "A,a dady nizan bada sbd gadanga d'ane nima aguna


Hooo!๐Ÿค—๐Ÿ˜… gadanga dan gata shikam yaji dadinsa kowane sadakinsa kyauta ake bashi saidai yakwashi garabasa knn



Dady yace "barni nabiya momy zanbada naira dubu hamsin inyaso sai ke kiyi musu wata hidimar


Tace " to aishikenan in "yata zainabun tazo ita nayi mata kayan daki.


Gadanga yahau murmushi farin cikine aransa jin za.a gatanta zainabunsa lallai mutanen nan suna sonsa


******
Ranar Juma,a da sassafe suka dauki hanyar kauyen marina shida drebansa abokinsa kuma wato mudi

Suna tafe suna hira mudu nayi masa jinjina na yanda yayi artabu da yan garkuwa

Nan gadanga yagaya masa yanda sukai da iyayan khalisat yagaya masa cewar xa.a daura auransu ranar lahadi

Mudi yakama baki yana dariya yace "kai mutumina ammafa ka more dayawa dama nine haka dan gata


Gadanga yakarkata kai yana masa wani kallo

"Inafa gata anan zadai atakuramin nida amaryata xainabu walh banda ina ganin girman dady da babu yanda xa,ayi inkarbi fankon yarsa haba ai nacutu xayawa inhar nayi rayuwar aure da ita โ€ฆโ€ฆ

Mudi yace "to amma dai komeye gareta ai xa.asha kudi ko? Yafada yana dry


Tsaki gadanga yaja yace "hhhmmm kai idon cin nera ne baxaka duba yadda akeso kasamawa "ya"yanka uwa tagariba saidai nera kake hange wanda kuma inkace zaka nuna kwadayinka to kana tareda takaici kuma dole kajuri wulakanci


Mudi ya sosa keya yace "kuma fa hakane da wannan dan wannan, nasanka mutimina da tsaro da rashin jan mutum ajiki kada kaga an baka kyautarta kace xaka gallaxa mata kayi adalci tsakaninsu kaa kanuna kafi son uwar gida xainabu.โ€ฆ

gadanga yace "hhhhmmm fada ma bata bakine mudi ai dole khalisat ta dauri damarar yin hkr atare dani sbd kaima kasan akwai banbanci tsakaninsu balle xuciyata zainabu take so itako "yar sadaka baxan taba son taba ko kallon arxiki bazata isheniba intaga zata xauna ta zauna inko baxata iya hkrn xamaba to xata iya kara gaba nikam dai bana rigada na amsaba to banda laifi agun Alh inhar ta bijire ita zasuga laifi baniba


"Hhhmmm kaima kuwa xakai laifin inhar kaiwa diyarsa rikon sakainar kashi tunda kasan baxaiji dadin yaga kana gallaxa mata ba yardace yasa yabaka itafa.โ€ฆ


"Kaga murife wannan maganar tun kafin mushiga kauyenmu don banaso kowa yaji ma

Cewar gadanga yafada yana me kawar da kansa gefe

"Ko zainabun baxataji za,ai mata kishiyarba knn?

Yafada yana dariya


"Eh banaso taji sbd banaso ta tashi hankalinta kasan kishi gun mata fa. Dama ita ba kiba ba taje tarame.


Mudi yace "abokina kana son xainabu da yawa fa

Gadanga yace "itama tanasona dayawa kaga kuwa kaso me sonka ba laifi bane.

"Ina tausayin uwar dakina โ€ฆcewar mudi

Gadanga yace "kanka akeji.



Haka mudi yaita jansha da xolaya har suka shiga kauyen


Kai tsaye gidan iya kulu yasauka

Ta taresu da murna tana "maraba lale da mutanen birni sannu sannunku


Ta shinfida musu babbar tabarma takawo musu fura da dambu

Taxauna suka gaisa sannan tabasu guri suka fara aikawa

Da mudi xai tafi iya kulu ta hada tsarabar kauye tabashi yakaiwa surukarta hajiya laila

Har bakin mota gadanga yabiyoshi yana jaddada masa kan cewa yadawo ranar litinin yadaukesu shida amaryarsa

Mudi yace "gaskiya kai d'an gatan ma,aikacine bakaje yau juma,aba gashi monday ma baxakajeba lallai kanacin salary a b'agas kyanta nadawo lahadi nadaukeku inyaso kaga monday baxakai fashiba ko?


Gadanga yakai masa bugu na wasa yace "kaifa matsala ce dakai meye ack dan nayi fashi alhali mune da gurin kuma akwai me kular min da komi inbana nan.


Mudi yace "to amma ai kayi luzin na karatun weekEnd ko?


"Ba matsala nafara kwashe komi akaina nakusa daina xuwama tunda in turancinne ayanzu xan juya haka lissafin ma baxai xillemin ba.


Mudi yace "to aishikenan sai lahadin knn agaida amarya zainabu.

"Zataji dan sa ido. Cewar gadanga yana dry

Mudinma dariyar yake yatafi yana jin son gadanga aransa bayason rabuwa da gadanga shiyasa yafison yaga cewar shizai kaishi koina jininsu yahadu sun shaku tun xuwansa gidan shiya tarbeshi yazama abokin hirarsa dukansu kusan tsaran juna suke yana jin dadin tarayyarsu da gadanga don gadangan baida girman kai duk da yanxun yaxama babban yaro yana kama nera bai nesa dashiba yana kuma yi masa ihsani.



Sunsha hira da iya kulu kuma bai boye mata komiba jinta yake tamkar innarsa haka yazayyane mata duk yadda akai na sace khalisat da kuma alqawarin daurin aurensu da Alh ya kulla.


Iya kulu bataso hakanba domin tasan halin jikarta batada kunya ga girman kai da kyamar talaka gashi an shagawabata bata ganin girman nagaba da ita anya xaman nasu zaiyuwu kuwa dantasan halin gadanga baya jurar banxan hali


Basu shaku da khalisat ba irin yanda suka shaku da gadanga tunda khalisat bata zuwa inda take saidai in ita taje gidan su hadu kuma bata shiga jikinta amatsayinta na kakarta tafi shigewa angin momy dayake masu kudine hakan na konawa inna rai sbd batada wasu jikokin aduniya sai ita tunda kuma taga yarinyar ba yar arxiki bace ta yardata tasa ta agefe bata tunota kwata kwata batada kawazuci balle abin yadameta


Iya kulu takalli gadanga tace "to nidai abinda xance maka anan shine kaxama m adalci atsakaninsu baxan hana ba tunda bansan me Allah xaiyi agababa fatana ka kula mana da zainabu kada tacutu abirni batada kowa saikai yarinyar bame hayaniya bace gata da hkr kaga tunda aka daura muku aure takanzo tagaidani ta tayani aiki ta tafi inajin dadin hakan tana bani girma sosai dan Allah gadanga kariketa amana kaji.


Ya gyada kansa yana cewa "insha Allahu iya xanriketa bisa amana kitayamu da Addu,a kawai

Tace "to kenan da ita zaka tafi ko?

Yace "eh da ita zantafi sbd Alh yace akwai gidan da zai bani me sashe biyu sai insasu ack

"To madalla Allah yabada xaman lfy yasa abokan arxikin kane.

Gadanga yace " Amin iya "


***
Dare nayi yaje ga amarya zainabu bataji xuwansa kauyenba saijin zuwansa akofar gida tasha mamaki

Tafita tayi masa iso har ckn gidan yagaida iyayanta dayake babanta yarasu sai mijin mahaifiyarta mutumin kirki suka gaisa da gadanga ckn mutunci

Tashigarshi dakin yayanta takawo masa abinci da ruwa

Tazauna dan nesa dashi

Yace "ke dawo nan jikina kibani abaki yanxu fa bakamar da mukeba ni mijinkine komi kikai zaki sami ladana,

Tarufe fuska da gyale tanajin kunyarsa

Dayaga dagaske take baxata iya motsawa bama saiya mike asannu yariko hannayenta yazuwa kan doguwar yar kujerar dakin yazauna sannan yazaunarta kan cinyarsa

Duk taji kamar ta nitse kunya kamar me !! wai Allah yau itace a cinyar namiji!!

Ya janye lullubin fuskar datayi yace "bude idonki ki ciyar da mijinki Abun na kada ki kwari kanki ko kiyi sake wasu matan abirni su fiki iya kula da miji su kwace mk ni โ€ฆโ€ฆ

Da sauri tazaro manyan idanunta tace "kamar yaya su kwacen mini kana nufin kanada wacce tafini acan ?

Yace "a,a babu amma inbakiyi abinda xai farantamin rai ba to zan iya samun wacce zata faranta min acan.

Zainabu akwai kishi tuni ta saki jiki anmata wayo tadauki cokali tahau diban shinkafar ahankali tana bashi abaki shiko yana ci ckn yauki da yanga waishi nan dan gata ๐Ÿ˜…

Yature hannunta daya koshi tabashi ruwa abaki

Amma bata yarda sun hada idoba karfin hali kawai take don son ta faranta masa rai kada yaji son wata aburni ba itaba

Yakura mata ido yace " Abunah ina bukatarki akusa dani kifada agida ranar litinin zankoma tare zamu tafi mutum biyu kawai zamu bukaci yan rakiya sai iya kulu kinji .

Farin ck kamar tarumgumeshi taji mafarkinta zai tabbata kenan

Taringa murmushi batace komiba sai daga kai datayi

Yasan taji dadin hakan kawai dai tanuna azahirine baxata iyaba Abun gadanga kenan.



Haka suka rabu kamar kar arabun

Ranar asabar washe garin dayazo baije gun abun ba yana tare da abokansa da yaransa yana musu nasiha akan sudaina futa yawon gangi da farauta yai musu alqawarin xai ringa daukarsu daya bayan daya yanakai su birni yana samo musua aiki

Sunji dadin hakan sosai kuma sun masa alqawarin daina farauta da fadace fadace

Suka bashi labarin Amadi dan takararsa cewar har lokacin suna bursin aburni anyanke musu wasu shekaru a tara shida yaransa dayasa su suka aikata ta,asar


Shi gadanga ma ya mance dasu shidai kawai akullum yanaiwa innarsa addu,a dan tashi ma da xa,a fito dasu ko ajikinsa suda ubangijinsu kuma


Ranar lahadi ana gove zai tafi birnin yadade tareda zainabunsa adakin yayanta yana jiyaeta soyayya tafara sakin jikinta yashafa jikinta ckn salon sa na burgewa ta matsu iya matsuwa yasha bakinta yajiyarta dadin duniya wanda har jitaringayi dama su dauwama ahaka


Koda yatafi tadade bata iya rintsawaba tanata tuno yanda takaya atasakaninsu ta kankame filo tana murmushi lallai jikin masoyi akwai dadin tabawa haka harshe yake da zaki? Tab dole tazage wajen nunawa mijinta soyayya kada wata takwace matashi aburni don ta tsani kishiya arayuwarta โ€ฆโ€ฆ



*Auntyn Sayyad da Shahidace* ๐Ÿ‘Œ๐Ÿผ
*ALI GADANGAโ€ฆ*
๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน๐Ÿน






*Short Story*





*Nabilancy Luv*
(Auntyn S&S)







*Dis page Dedicated to my Sisters Batul Mamman & Ummi Aisha*






*MY REAL FANS*

*BUHARI YUSUF*
*PEN WRITERS NVLS*
&
*DR. ZAIN* *ONLINE HAUSA NVLS*
&
*YA,U TATTA Me waka*







page
2โƒฃ2โƒฃ




Aranar litinin Akayi taron biki agidansu Zainabu danginta suka cika gida anata bidiri ana kidan kwarya kowa na farin ciki


Amarya tasha kyau dayake iyayenta sunyi mata dinkuna tunda ango baiyi kayan lefe ba

a Al,adar kauyen duk macen da ba,ai mata lefe ba to kowa sai yaji anyita tsegumin knn ana cewa miji baya son matar shiyasa

To amma wannan Aure na dabanne domin kowa yasan yanda gadanga da zainabu suke son juna tunda anga yanda ya illata Amadi akanta kuma babu wanda ya isa yai tsegumin zancen gadanga bai mata lefe ba sbd tsoronsa da akeyi ta koina kuma yaransa ne agarin su kadaima sun ishi kowa

Dubu hamsin dama yabaiwa iya kulu takai gidansu zainabu itada wata makwabciyarta amatsayin kudin komi da bai mataba

Gidansu xainabu sunji dadin kudin dan da ace lefen zaiyima ba wani kashe kudin xaiyi dayawa ba a fanteku biyu ake zuba kayan kuma basufi kala takwas ko bakwai ba takalma biyu da dan madina da cover shoe da plate shoe komi na kyali ma biyu akeyi.

To amma wannan kudi sai aka dankasu ahannun wata yayar gwaggonta da za.ayi rakiyar amarya da ita akan insunje ayi mata siyayyar kayan daki da ita (lol

Please Login or Register in order to submit comment