Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akunne


Wato tun kafin ma yabar kauyen ta canxashi lallai mata sai abarsu ashe yaudararsa take tabbas yau xaiyi maganinta kafin yaje ga dan,iskan nata


Afusace yashi ckn gida inna tana tsakar gida tana tankade sai ganin dawowar gadanga tayi ckn yanayin bacin rai

To fa! Wa kuma ya tabo Ali maxan fama Ali gadanga kuar yaki


"Meya faru gadanga ? Ta tambayeshi

Bai bata amsaba saiya wuceta kawai yashige dakinsa


Ta mike tsaye tabar tankaden don tasan ba qalau ba

Tayi tsaye tana jiran intaganshi ya futo da makami to tabbas wani yatabo matashi awaje fada ne xai tashi knn aiko dai baxata bariba zata kwace inya futo


Sallamar da Zainabu tayine yadawo da hankalinta gunta ta amsa mata tana mata lale marhabin


Suna ckn gaisawa saijin tayi gadanga yaguto da wayar wuta yahau dukan zainabun

Zainabu tahau ihu tana neman ceto

Inna ta rikice tana kokarin yin ceto ana hadawa da ita

Dakyar ta finciko zainabu takaita dakinta tana cewa "yau nashiga uku da mugun yaro zaikashe yar mutane.


Takaita dakinta tana rarrashinta " kiyi shiru kada makwabta suji su shigo tsegumi.

"Me kikayi masa ne Abu?


Ita dai zainabu ba bakin magana kuka kawai take tana faman murza jiki


Tunda batasan me tayiba balle tabawa inna amsa


Inna tadawo tsakar gida ta taddashi yana faman huci yana buga kafa akasa


Ta karbe bulalar tahau rambayarsa


"Kanutsu gadanga ka gayamin me yar gidan taka tayi maka?

Yai mata banxa

Dayaga xatayi masa kuka tuni yadawo hankalinsa don bayason tashin hankalin inna yann mugun sonta bayason ranta yabaci balle ganin hawayenta yana sashi awani hali.


Ta xaunar dashi tace " meya hadaku haka gadanga?


Yayi tagumi da hannu bibbiyu yace " inna kinfi kowa sanin halina banason raini.!bana son yaudara!!banason karya ko!!?


Ta gyada kanta " nasani gadanga.

"To Abunah ta aikata min su dole ne ta karbi humunci dai dai da abinda tayi.


Naganta yanxu tana zance da ita da Amadi dan gidan mahauta suna zance suna nishadi Alhalin dama tayimin laifi shine taxo layinmu tana xance danta sake kunnani kenan to walh bata isaba zankumayi maganin sa shima.


Kafin inna tayi magana saiga zainabu tafito daga dakin tana xubda hawaye jikinta asanyaye ta taho ahankali tawuce inna taje gabansa ta durkusa ckn muryar kuka tace dashi " kayi hakuri kagafarceni walh banda niyyar yaudararka ko kusa bana son Amadi shiyake bibiyata yana takuramin sosai natsani ma ganinsa yanxuma shiya taren hanya wai baxan wuceba harsai nace ina sonsa ko insaki rai inyi driya kana yaban gu


Walh bada son rai nayi dariyaba dan bayadda xanyine baxan sakeba


Abin tausayi tana magana tamkar agaban babanta take


Inna kanta taji tausanta

Tajanyota ajikinta tana goge mata hawaye

"To kaji fa yanda akai sarkin "yan fushi da xuciya kadaina yanke hukunci da wuri kada kaje wataran ka kashe aurenka koka kashe "yar mutane.


Ta dubi zainabu " kiyi hkr kinji Abu baxai sake ba kada ki fada agida. Yana sonki tsananin kishinki yaja hakan.kin fahimta?


Zainabu tagyada kanta kawai tareda mikewa tayi waje tana share kwalla


Ita dai fatanta Allah yasa ya yarda da ita yafahimci ba son Amadine arantaba


Sam ba kukan dukan dayai mata takeba ganin ransa yabacine ita bataji xafin dukanba, daxai kwana yana dukanta ma ba komi agunta ganin datayi masa ayanxun yakwantar mata da hankali agobe zata dawo don sake bashi hakuri don itace da laifi.


Inna tayita masa fada don bataji dadin wanan yanke hukuncin ba

Saida yabata hakuri yace baxai kuma ba

Tace" naji to amma kaje anjima kabata hakuri yarinyar nan taa sonka gadanga.


Ya gyada kansa "naji zanje inna.


Sai daga baya yaji a dadi aransa daya sani yahauyi yana tausan zaibunsa tabbas xaije ban hakuri


Ammafa Ahmadi xai gane kuransa saiya huce akansa dama akwai jik'akk'iyar gaba tun da to gashi yakuma tsokano tsuliyar dodo.....



*ALI GADANGA...*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹





*Short Story*




*Nabilancy Luv*💘
{ _Auntyn S&S_}






*Dis page dedicated to my Sisters*
*Batul mamman* 💖 (Al,adun wasu)

&
*Ummi Aisha* ( Wani haske)



page 5⃣

Magribar fari Ali gadanga yahau shirin zuwa zance gun zainabu domin yatanadi kalamai dad'ad'a naban hakuri.

Ya dauro alwalarsa ya zira kayansa

Wata shadda yasaka tsanwa dinkinta har kasa sawa na biyu knn yau tun dayasaka ranar daurin auren babban yaronsa wawurau

Yafito yana b'alle botir din gaban rigar

Inna tafito da turare d'an d'uri ahannunta akamar kwalba tana fadin " ga tawa gudunmawar ajewa Abu da qamshi.

Ya karba yana shafawa yana murmushi yace

"Wato ma inna ko kishi bakyayi lallai kindaina sona.


Ta kama baki tace " ni na isa indaina son mijin fari, kawai dai ba yanda zanyine tunda biko za.aje.

bai kara maganaba yafice yana mata sallama

Ita kuwa da kirari tabishi kamar yadda tasaba masa

"Cau!cau!! Na zainabu me komi doxin

Ali gadanga sha gwagwarmaya
ALI jan zaki
Ali gadanga kusar yaki
Sun buga sunbarka jikan inna!!!


har yafice daga xauren gidan yana jiyota

Ransa fari qal wani farin ciki yke ji



*****

kamar kullum yadda tasaba biyo dan aike yauma hakan tayi

Yayi mamakin hakan don yayi tsammanin ko fushi take dashi sai anja aji kana afito


Amma bakamar kullum ba yanayinta don yau asanyaye tafito tana taku ahankali kamar kazar da kwai yafashewa aciki

Kanta akasa ta gaidashi

Ya amsa da sakin fuska

" *ABU NAH* yakirata yana kallon fuskarta

Ta dago ahankali takalleshi ta amsa murya can kasa

"Nasan ban kyauta miki ba kiyi hakuri nayi miki hukunci akan rashin sani ki yafeni sonkine yaja hakan.


Ahankali tafurta "bakomi nayafe maka Allah yakiyaye gaba.

Har ransa yaji dadin lafaxinta qaunarta ta karu fiye da da

Tabbas yayi sa.ar mace me yafiya da hkuri

"Nagode Allah yabarmu tare

Tace " Amin.

Ji tayi kamar taje ta rumgumrshi amma tana jin kunya kuma tana gudun wani yaxo wucewa ta lungun nasu ya ganta ta tafka abin kunya don har tsufanta ta kade

Amma jira kawai take taji yace ta sumbaceshi tabbas yau bazataki ba don zataso hakan tayi kewarsa sosai

Saiji tayi yace mata "zan tafi Abu ki kula da kanki ki kuma kama kanki ina sonki.

Kamin tace wani abun harya juya yatafi

Tabishi da kallo tanajin wani abun aranta akansa

Matsalarta daya da Aliyunta bai iya dadewa a zance ba

Da xarar yafadi abinda ya kawoshi zai tafi koda ita bata gama ba to meyesa hakan? Ta share hawaye akuncinta tanason Aliyu sai fatan Allah ya mallaka matashi amatsayin miji.

€€€€€€€€€


Ranar wata lahadi Ali gadanga yatashi da ciwon kai baifuta farauta ba don ranar basa fashin futa amma ba yanda ya iya don kan ya matsa masa yaransa ne suka futa

Inna tasashi gaba tana masa sannu

Saijin shigowar Alhaji da iya zulai sukai katsam

Da fara.a ta taresu tabasu wurin xama

Alhaji ckn damuwa yatambayi inna meke damun Aliyun haka yaganshi kwance yadafe kai

Inna tace "walh tun safe yake fama da ciwon kai.

"Ayya yasha magani ? Cewar Alhjin.

"Yasha panadol. Inji innar

Iya zulai tace " toko juko zansa namadi yayo masa.

Inna kulu tace "kayya ai ko ankawo basha yakeba sam gadanga bai yadda da jike jikeba sai yace wai suna lalata hanji da hanta dasu k'oda.

Alh yace "da gaskiyarsa tunda dai yasha maganin zai sakeshi da yardar Allah bari nakama masa kan.

Nan Alhajin yakama kan Ali gadanga yana tofa masa Addu,o,i


Bacci ne yadauke gadanga baisan tafiyar su Alhajinba yadaiji kafin yarufe idon sama sama Alhajin nafadawa inna yaxo su tafi birni da shi Amma tunda baida lfy zai dawo rana ita yau su wuce.


Sai Asuba yafarka kuma cikon ikon Allah yajishi sakayau kan yasaki Allah yaye masa

Saida yagabatar da salloli har wanda ake binsa kana yafito ya gaida inna


Nan tahau tambayarsa jiki yace da sauki

Tace "Lahadi Alhaji zai dawo kutafi yabar sallahu kancewa kazauna cikin shiri yabar kudi yace insai kayan abinci don inka tafi wata biyu zakayi kafin kadawo

Gadanga ya jinjina kai yace "to Allah yanuna mana lokacin.

Inna tace "Amin.

Tabishi da kallo yafita yakoma dakinsa

Taga yanayinsa yacanxa jikinsa yai sanyi tabbas itama natan yai sanyin jin har yau saura kwana shida gadanga yatafi birni yabarta lallai xatayi kewarsa tun dare ta kwana da tararrabin abin dan dai ba yanda zatayine addu.a kawai take Allah yasa hakan shine mafi alkairinsa zata karfafa masa guiwa ne kawai dan karya sare dan ko inhar ta nuna damuwa to zai iya fasa tafiyar....



_Muje xuwa_





*Auntyn Sayyada da Shahida*💘
_Muje zuwa_




*Auntyn Sayyada da Shahida*💘

*ALI GADANGA..,*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹




*Story Short*




*Nabilancy Luv*💘
{Auntyn S&S}





*Dis page Dedicated to my Sisters*

*Batul mamman*💖 ( Al,adun wasu)
&
*Ummi Aisha*(Wani haske)





Page 6⃣


A ckn "yan kwanakin daya ragewa gadanga yatafi birni duk yakoma wani iri baya tabuka komi ko futa farauta yadaina kullum yana gida


inka ganshi sukuku dashi kamar wanda ke ckn rashin lfy


Akullum kuma sai yaje gurin zainabunsa wata shaguwace ta shigesu soyayya ta karu

Yarage mata miskilancinnan nasa da jinkai Da ixza kamar dan sarki yakan kuma dade atare da ita suna hirarsu

Hankalin zainabu akwance dan baigaya mata tafiyar tasu ba kawai dai taga canji na wasu abubuwan

Sai ana gobe xai tafi ranar asabar yazo mata da maganar hankalinta yai matukar tashi takasa dannewa tahau kuka

Sai alokacin yaji tafiyar tafita aransa badan inna ba da takeso da tabbas zai fasata sbd ganin yanda Abun sa ta rikice masa

Yajanyota jikinsa yana rarrashi

"Haba Abu nah kiyi shiru dan Allah kinsan yanda nakejin kukan nan naki kuwa to walh har raina

Badan naso xantafiba sbd inna ta matsa ne kuma bansan ko Alkairi ne ke kiranaba inkuma bakison na tafi to sai inhakura infasa kawai...


Ta dago kai da sauri ta kalleshi

Ya gyada kansa da sauri yakuma daga mata gira "kwarai kuwa inhar xaki shiga wani hali sbd rashina gara naxauna amma ki sani baxan taba yin Aureba har sai in nasami aikinyi

Ckn kasalalliyar murya tace

"Na amince kaje kawai Allah ya taimaka.

Yayi murmushi yace

"Da gaske har ranki?

Ta gyada kai kawai

Yace "inkinaso na yarda saikinyi dariya kin saki ranki

Tayi dariyar kuwa tana fadin " da gaske fa nake Aliyu zan hakura amma dai baxaka dade ba ko?

Yace " banajin zan iya fin wata.

Ta xaro ido "har wata zakayi ashe

Yayi dariya yace " eh! mana inkuma naji gidan baiyiminba to sati biyu kawai zanyi indawo abina


Taringa dariya kawai

Shiko kallonta kawai yake yanajin dadi aransa yau yaga takara masa kyau ainun

zainabu me kyauce ga wushirya data kara mata kyaun

Inbadan tana bata fuska da fente fenten janbaki da gaxal ba daxatayi simple make up da kyanta ya rikita maxa


Aranar ya dade agun masoyiyarsa suna shan hira ana raha kamar karsu rabu

******

Da safiyar lahadi kuwa yagama shirinsa tsaf yana tunanin Abunsa yaji sallamarta

Baiyi tsammanin xataxo ba dan baice taxo dinba

Atsakar gida inna ta tarbeta tabata gurin xama taxauna suka gaisa

Suna cikin hira Ali yafito daga ckn dakin

Yasha wani bluen yadi taxarce ya kure gayu amma bakyauye sak!

Yana gyara hula yana kallon Abu ta gefe

Ta rankwafa tana dg zaunen ta gaidashi

Ya amsa yana cewa " yasu inasu gwaggo suna nan qalau?


Tace "lfy qalau sunce ma suna maka fatan Alkairi Allah yakiyaye.

Yace "Amin.

Inna tace "gadanga kada kamance da nasihata karike da kyau fa shi birni daban yake ba irin karkaraba saika kiyaye asaka hkr arai arage xafin xuciya akuma kula dan Allah.

Yayi murmushi yace "naji zankula insha Allah.

Suna ckn tadi sukajiyo dirin motar Alhaji ya iso

Atare gabansu yafadi da inna da Zainabun

Shiko ido ya lumshe yana karanto addu.a aransa ya bude idonsa yaxubasu akan fuskar zainabu yaga yanda fuskarta ta canza

Inna tahau fadin tashi kaje ku gaisa ba saikasa yashigoba.

Yace "to inna .

Alhaji yaji dadin ganin Aliyu ashirye suka gaisa iya xulai na tsokanarsa saura inkaje burnin dadi yasa kaki dawo mana koka yo mana kishiya

Shidai dariya yake mata kawai

Alhaji yacika su inna da mutan unguwa da abin Alheri yatada mota suka tafi Ali gadanga na gaba ya nutsu yana kallon hanya.

Koda suka isa ckn kwaryar kano kalle kalle kawai yaringayi na yanda benaye da manyan gidaje masu get da fulawowi suka yawaita sai abin yabashi sha,awa

Yaringajin nishadi jikinsa yamace yanajin wakar larabawa na tashi amotar

Ya lumshe idonsa yana tuno fuskar Zainabu

Shiko Alhaji yayi xatonma bacci Gadangan keyi

Ackn unguwar NNDC quaters gidan Alahjin yake

Akofar makeken gidan yayi faking

Megadinsa ya wangale get Alhaji yashigar da motarsa gun da ake farking kusada wasu manyan motoci masu kyau

Gadanga yasha mamaki ganin wata bufurwar matashiya tafito aguje da kananan kaya ajikinta ta rungume Alhaji tana fadin
"Oyoyo my dady ina granny? Yaka barota?

Alhaji yahau fara.a yana fadin " munbara lafiya tace agaidaki tunda kinki xuwa inda take.

Ta xobara baki ckn shagwaba tana fadin " niko me zai kaine wannan kaxamin kauyen haba Allah ya kiyaye dady ita dai inta damu taxo taganni.

Wani haushinta gadanga yaji najin furucinta lallai wannan yarinyar yar rainin wayo ce kauyen nasu ne kaxami lallai taci darajar mahaifinta daya koya mata hankali.

Alhaji yasha mur yace " khalisat bakiga bako ba? Ki gidashi anan xai xauna.

Wani mugun kallo tabi gadanga dashi saida tadau mintina kana tace masa "hay! Ya kke !


yahade rai baice mata ko kanzil ba yaharde hannaye akirji yana kallonta


Dady ya kwallawa Mamuda me baiwa shuka ruwa kira

Da gudu mamuda ya iso gun yana masa sannu da xuwa

Alh yace " mamudah ga bako nan dan,uwana ne daga yau yazama dan gidan nan ka share dakin kusa dakyau nan xai xauna ga kayansa can abut ka dauko ka kai masa dakin.


"To angama Alhaji.


Yadubi gadanga "muje ciki ka gaida hajiyar khalisat.


Suka shige ciki ya rufa musu baya yana kallon yanda yarinyar ke karayraya kamar ta karye ajikin daddyn nata

"Da alama dai yarinyar nan batada tarbiya kuma zan gyara mata zama. Gadanga yace aransa....





*AUNTYN SAYYAA DA SHAHIDA*💘
*ALI GADANGA..*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹




*Short Story*




*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)





*Dis page Dedicated to my Sisters*

*Batul mamman*💖(Gumin halak)
&
*Ummi Aisha*( Dan Asali)




_I great All members of_ *TASKAR NABILANCY* Ina yinku dayawa dayawa💋💘





Page 7⃣
Zaman gidan Alhaji yayiwa gadanga dadi naganin yanda Alhajin ke bashi kulawa gakuma hajiya Laila na girmamashi da mutumtawa

Tun aranar daya iso gidan Alh yasadashi da Haj. Yaji matar ta burgeshi bayama da Alh yabata amanarsa takumace ta karb'a xakuma ta rike bisa amana tamkar d'an cikinta

yakuma fara gani da idonsa domin akullum saita fito taga lafiyarsa har daki

Ta kuma aiko masa da abinci me kyau da lfy

Musamman tagyawa me aikinta dije kan cewa ta tabbatar ta bambanta abincinsa dana "yan aikin gida dana me gadi danshi d'an masu gidane takuma gargad'eta akan taringa kula da lokacin cin abincinsa kada taringa bashi ak'urarren lokaci

Ali gadanga baiyi gidadanci da kuma bak'untaba don sosai yasake agidan yakuma q'ulla abota da mamuda da wasu kecr masa mudi

A koyaushe suna tare da mudi afarfajiyar gidan kan benci suna hirar duniya mudi na bashi labarukan almara daban dariya da abinda ke wakana abirni

Shikuma gadanga nabashi labarikan kauye da abubuwan dasukeyi agun farauta da gangi

Jininsu yahadu sosai wani sa,inma tare suke cin abincin rana kona dare

Hankalin gadanga akwance saidai kewar kauyensu da tunanin xainabunsa ke damunsa gashi yakanji son yaje yayi gangi ko futa farauta saidai kuma ba dama dan ko da wai Alh yaji baxai bariba



Abu daya ke tsaye masa arai ganin yanda khalisat ke wulakanta ma.aikatan gidan daxarar tsautsayi yasa sunyi kuskure kadan to yanxu catayo kansu da fada harma tayita bori akan sai ancire mutum abakin aikinsa ankawo wani

Masu musu girki kuwa tacanxasu yakai sau biyar daga dawowarta daga turai

Dije tana kiyaye kaidojinta akan kari take yi mata komai jiki na bari bata yarda tayi kuskure tana mata biyayya fin yanda takewa matar gidan

Hajiya laila mace me hakuri magana bata dameta ba sai ayi abu akan idonta amma dakyar xata tanka bayama abinda zai jayo mata bacin rai

Tanada gudun magana da kaffa kaffa

Sau dayawa in khalisat tayi ba dai dai ba to bafa ta iya ta tsawatar mataba inhar dadynta na gurin

Yanzu yahauta da fad'a yana cewa antakura mata shikam abar masa yar lele ta sake gidan ubantane bana wani ba

Duk da abin na q'ona mata rai bata nuna masa saidai taja bakinta tayi shiru

Hakan ne yakara shagwaba khalisat dasata ahanyar tab'arewa

khalisat yarinyace me girman kan tsiya ga rashin ganin girmn nagaba da ita koda mutum yahaifeta ne

Mahaifinta kawai take ragawa

Momynta ma dole ke barinta anaa ra.ayin bata mata dole

Gata da fadin ran tsiya gata da kishi me tsanani ko kaya tasako taxo wucewa taga me irin kayan to dava ranar ta barshi

Tafi saka englishi wears masu kama jiki kuwa

Saurayinta d'aya me suna SAFRAZ

Wanda suke matuqar son juna

Tun asch suke tare a abroad

Atare suka gama sch

Shima dan nigeria ne amma mazaunin kaduna ne iyayensa masu kudine babansa ne mataimakin gwamna

Safraz yana son khalisat amma sonta yafi nashi domin shi yanada yammatansa a boye suna shanawa bata saniba

Ita kuwa batada kowa bata yarda ta hada sonsa dana kowaba.

Amma fa irin soyayyar da sukeyi kare baya tonaba

Yanda suke gudanar da soyayyarsu aturai dasuka dawo kasarsu ma basu chanxaba agaban kowa zasu rumgume juna suyi kiss basuji kunyaba

Kanta kuwa tabashi yafi akirga tamkar ma.aurata suke

Duk sati biyu ko daya yake xuwa kano yasauka a hotel yayi kwana biyu atare da ita

Amma bata kwana duk dare xata dawo gida

Tanada kawa me suna khairat wacce suka hadu a shopping yar manyace itama don da body guard take yawo babanta k'usane a k'asar nan.

Khairat "yar karya ce ta bugawa ajarida bata mu.amula da " yayan talakawa bakuma ta soyayya da dan talaka ga ixxa da ji da kai hhhhmmm dan ma da abin dan abin.....😊🤔



******
Zaune suke akan benci suna hirarsu hankali kwance gadanga na baiwa mudi labarin zainabunsa da yanda take sonsa take masa biyayya

Labarin abinda yawakana na dukan dayai mata na rashin sani yake bashi

Sun tsunduma ahirar tasu

Taxo kansu ta tsaya tana kada mukullayen mota riga da wando ne na pakistan ajikinta kanta yasha attach har baya tayaneshi da siririn gyale

Ta tuga musu tsawa

" kai! Wane irin wawaye ne ku ana muku sallama kuna shashanci

Nan majalisa ce da zaku kafa sansanin hira

Ta nuna mudi da jikinsa ke tsuma ya sadda kansa kasa ckn biyayya yace " kiyi hakuri ranki ya dade bamujiba ne.

Ta nunashi da bacin rai " kai rufa min baki kafin nasallameka daga aiki maza tashi ka kaini unguwa tunda ilu dreba baya nan.

Mamuda ya tashi da rawar jiki yanufi motar da zasu futa da ita

Har ta juya xata bar gun saiku
a tajuyo ga Ali gadanga

Ta kare masa kallo na raini kana tace

"kai ! Meye sunanka!

Yai mata banxa

Saida takara tambayarsa kana ya bude baki dakyar yabata amsa

"Ali gadanga...!

Tace "inma DAMANGA NE ' ni baruwana da wani gadangar ka doka xan kafa dole abi kuma

Ali ya karkata kai yana kallonta ckn tsana

"Uhhuumm kanaji ko, daga yau adaina zaman majalisar nan ka kama wani aiki agidannan baxa.a ci dakai abanxa ba inba hakaba kuma insa amaidaka kauye


Ransa yai quna ya mike tsaye ya nunata da yatsa "ke ki iya bakinki maxa bisa kanki karamar alhaki kawai wacce baifi na matseki ahammata ba mara kunya.

Tayo kansa da hargagi tana fadin " ni kake gayawa haka? Walh yau saina nuna maka kurenka zakasan kataboni zaka bambance matsayina agidan nan walh saika koma kauye dan akuya kawai.

Horn mudi yaita matsa mata

Ta juya afusace tayi gaba tana fada

Me gadi ya wangale get da sauri

" *Dan Akuya...!*


sunan yatsaye masa arai


Yaciji yatsa


Babu wanda yataba gaya masa wannan kalmar me xafi sai ita kuma dole saita gane kuranta saiya nuna maya akuyanci saitayi dana sanin fada masa haka...




_Muje zuwa_



*AUNTYN SAYYADA DA SHAHIDA*💘
*ALI GADANGA..*
🏹🏹🏹🏹🏹🏹




*Short Story*



*Nabilancy Luv*💘
{ _Auntyn S&S_}





*Dis page Dedicated to my Sisters*

*Batul mamman* 💖 (Gumin halak)
&
*Ummi Aisha* ( Dan Asali)







Page 8⃣



Ali Gadanga yananan Zaune ransa na masa suya yakasa yatsare yana jiran dawowarsu khalisat dan ya dau mataki akanta

Yau me rabashi da ita sai Allah xaiyi mata hukuncin dazaisa tayi shakkun kowane da namiji yanda koda wasa baxata sake kallon kwayar idon wani namijin tasake kiransa da dan akuyaba koda karamin yarone



Har gajiya yayi da xaman don sunfi awa basu dawo ba

Ya hada kai da guiwa yana tunano karshen maganganun da sukai da innarsa

"Gadanga dan Allah kaxubda wadannan halayen naka ka canxa da masu kyau wadanda xa.a yabeka ko bayan ranka

Ka kadance me hakuri ako,ina aduk abinda akai maka koda kaine da gaskiya karinga koyi da halin ma.aikin Allah kkoda mutum ya takaleka karinga danne xuciyarka kada ka zama kumurci sarkin fada kaxama salihi gadanga na...!"


Yaja wata doguwar ajiyar xuciya tabbas yakamata yafara jin maganar innarsa ko don yaxama me faranta mata dayin alfahari da hakan

To amma baxai iya barin khalisat taci abinci akan saba ko xai hakuri akan komi to banda wannan baxai dauki rainin taba.

Ji yayi andafa masa kafada

Ya dago kansa da sauri yadubi mamuda da mamaki yace dashi

"Ya naganka kai kadai ina shaidaniyar yarinyar take.

Mudi ya murmusa yace "bari kawai na barota can gun watsewarta...

"Watsewa kamar yaya ? Kana nufin kacemin karuwa ce.?


Da sauri mudi ya rufe masa baki yana waigen bayunsu gudunsa kada wani yaji.


"Bari fadan haka kada ajika, yar masu gida ce ko me zatayi bme mata kallon hakan.

Gadanga yace "to ina ka kaita kuka dade hakan.?


Mudi yace " ai da futarmu tayi ta fada ita kadai inajinta kamar taci babu nidai ko kallonta banyiba kada ta hucr akaina, can ta gaji takira daddynta tagaya masa yanda kukayi tana kuka,to bansandai me yace matab da alama rarrashinta yayi.

Filin jirgi tasa nakaita ta muka dauko saurayinta dayaje wata seminer can

Munsha jira kafin saukar jirgin nasu

Hotel nakaisu na barosu acan ita dashi

Gadanga ya xabura yace "hotel fa kace,

Mudi ya gyada kansa yace "kwarai kuwa ai duk lokacin dayaxo ina kaita inbarota acan in dare yayi saiya dawo da ita amotar wani abokinsa

Gadanga yace "tab lalli yanzu yarinyar nan tana haka amma Alh yasani baya mata fada?

Mudi yace "kai ka kuwa san son da Alhajin keyi mata to ko fad'a bai tab'a yi mata ba balle kallon banxa wanda duk yai mata ma ransa ke b'aci

Kaima inaso inbaka shawara akan kada ka k'ara d'aga mata murya sbd shed'aniyace ba abinda baxata iyayiba don ganin an bak'anta maka rai


gadanga yace "hhhmmm kasan Allah mudi saina nuna mata nafi karfinta saita gane kurenta agidan nan zan nuna mata ni dan akuyan ne yanda ta kirani kuma in xauna lfy

Mudi yace "me kke shirin yi mata ne?

Gadanga yai masa banxa yana huci

"Kana so ka koma kauye ba shiri knn.

Ali gadanga ya harxuko "to saime dama dole akaimin bansoba

Dan anmaidani ko ajikina dama har yanxun kewar garinmu bata sake niba.

Gyada kai kawai mudi yayi bai kara cewa komi ba dan bai hango tsoro a idon gadanga ba zai iya yin komi akan wannan lamari

*****
Anyi haka da kwana biyu gadanga yana zaune shi kadai akan benci yanajin labarai a Aminci Radio

Mudi ne yabashi don ta ringa tayashi hira shikam yabar xaman xaibi doka

Alh ne yafito xai futa yanata sauri dayaga Aliyu saiya tsaya

Da sauri gadanga ya gaidashi aladafce

Ckn fara.a Alh ya amsa yana cewa "badai wata matsala ko?

"Eh, babu Alh.

"To!to! Aishikenan dama inaso ingaya maka ma xaka fara xuwa Aiki a kamfanina na kera Alminium akwai matsayin da neso kasamu aciki office nasaka agyara maka don haka kafin agama shirye shiryen abubuwan inaso karinga kai khalisat duk inda zataje kafin drebanta ilu yadawo daga garinsu

Cikin biyayya yace "to bakomai Alh nagode.

Duk da abin bai masa dadiba nakai kalisat unguwa da xai ringa amma bayanda xaiyi baxai iya ma Alh musuba

Yana ckn tunani yasamo mafita dan yaci burin wulak'anta ta amma ko ta wannan hanyar saiya rama abinda tayi masa.

Itanma acan b'angarenta murna takeyi gadanga yaxama drebanta na "yan wasu kwanaki wanda ta hakan zata yi masa wulak'ancin da bata taba yiwa wani d'a namijiba saiya gwammace dama baizo birniba

K'awarta khairat tabata wannan shawarar kan cewa ta mayarsa dreba kawai don tasamu hanyar wulakanta ta tunda shi tsagerine baya ganin martabarta na "yar manya

Tunda gadanga ya muxantata taji ta tsaneshi ta damu matuqa harta gayawa khairat kai hatta SAFRAZ saida tagaya masa

Shi hakuri kawai yabata don bame tashin hankali bane


Tofa! Muje xuwa...

****
Aranar farko dazatasa yakaita unguwa ta tsala ubansun kwalliya da kananun kaya matsatstsu yar figil din riga ko bra batasaba don abubuwan atsaye suke

Bayan sallar magriba ne dinner xataje na kawarta da akeyi a ROYAL HOTEL


Yana xaune kan benci yana jan carbi yayi sallar magriba

Taxo kansa ba sallama

Taja kerere ta tsaya da gadara da ixxa tace masa

"Kai ji mana.

Zan fita anguwa kadau mota ka kaini.

Azuciye yakalleta sama da kasa cikin tsana yace mata

"Ni ba kai bane bakuma xaniba har sai kin kirani da sunan dana gaya miki

Please Login or Register in order to submit comment