Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waɗannan kawai zan zuba musu,makamina shi ne addu'ata kaɗai!" Umma ta kai ƙarshen maganar tana yiwa Sumayyah nuni da idanunta,nufinta shi ne idanun kaɗai za ta sanyawa Hajjah Kakah da Inna Karimatu akan lamarin har su ga abinda Allah zai hukunta.

*Ƙarfe 9:05pm*

"Na tara ku ne akan maganar Sadiku da Raudatu,tunda har suna son junansu to ni banga abin ɓata lokaci ba,don haka ina so a cikin satinnan Sadiku ya kawo goro da duk wani kayan saka rana da ake buƙata daga gidan maza,so nake a fara saka lokacin aurenta kafin sauran su daidaita da nasu tsayayyun,sannan kai Lawal ina so ka faɗiwa Maimunatu da uwarta cewa,ni Hajiya Zuwairah ba zan laminci rayuwar yawon ta zubar a cikin ahalina ba,ko dai Maimunatu ta fito da miji a haɗata da Yayyinta a aurar da ita kafin ɓullowar abin kunya a jikinta,ko kuma ita da uwar su haɗa shirginsu su bar cikin ahalina,wannan umurni ne daga gareni kai tsaye tunda ni tamkar sunyi asirin da suka rufe bakina bana iya tsawarta musu yadda yakamata a gaban idanunsu." Hajiya Kakah ta kai ƙarshen kalamanta idanunta akan Baba Mai Itace da ya yi ƙasa da kansa.Baba Lawal ya jinjina kai tare da ɗagowa ya dubi sauran ƴan uwansu su Baba Auwalu sannan ya soma da faɗin, "Na ji Hajiya,In Sha Allah zan isar da umurninki,dama kuma haka muka yanke shawara ni da ƴan uwana akan gara tayi gaggawar fito da miji ayi mata aure,amma maganar Sadiku da Raudah me zai hana abi komi a hankali Hajiya? Ni ina ga abari sauran su fito da nasu tsayayyun sai a sanya lokaci guda,tunda dai ba wani ne zai zo daga waje a shure batun na gida a bai wa dawa ba,in dai ni na haifi Raudah ga ƴan uwana nan su zama shaida cewa, na bai wa Sadiku ita,bata da wani miji sai shi matuƙar bashi ne da kansa ya dawo ya ce baya sonta da aure ba,don haka kiyi haƙuri a daidaita da sauran maneman ƴan uwanta da suka taso kansu guda." Hajiya Kakah ta jinjina kai cike da gamsuwa,idanunta cikin na Baba Lawal ta ce, "Ban ƙi ta taka ba Lawallina,abinda nake so ku fahimta shi ne,akwai shaiɗanan da ke son shigowa cikin maganar matuƙar ban nuna isata da ikona akan ahalina ba,a yau ɗinnnan Karimatu ta gaya mini zafafan kalaman da nayi rantsuwa sai na nuna mata ƙarfin ikona akan ku da zuriyyanku,don haka babu gudu babu ja baya a gaggauta fara saka lokacin auren Raudah da Sadiku a raba goro kowa ya shaidi hakan,in yaso duk wanda aka daidaita da nata manemin sai a faɗi masa lokacin da aka yanke za a yi na ƴar uwarta a haɗe tare,kuma bana so ya wuce watanni uku kacal tunda ance saura watanni biyu suka rage musu su kammala karatunsu baki ɗaya." Hajjah Kakah ta dakata da maganar tana duban duka ƴaƴan nata da suka nutsu suna saurarenta.Baba Adamu ne wannan karon ya yi magana yana faɗin, "Hajiya maganarki akan hanya take domin nima kalaman da Karimatu ke furtawa akan wannan lamarin sun fara kai ni bango,don ni cewa nayi ba domin kar ayi saurin ɗaura musu aure bata kammala karatunta ba ya hargitsa mata lissafi,da nace a ɗaura aurensu a ƙarshen satin nan ma,in yaso a haɗa bikin ayi tare dana ƴan uwan nata daga baya,amma lamarin ƴaƴan yau da basu da haƙuri da kawaici ya sanya ba za a yi hakan ba,amma tabbas gara a tsaida lokaci domin ta gane cewa mu ke da iko da ƴaƴan ba ita ba." Baba Auwalu ya jinjina kai ya ce, "Duka na gamsu da kalamanku,amma ina so in mana matashiya akan zurfafa addu'a akan dukkanin lamuran da suka kunno mana kai suke neman kawo hargitsi da rashin fahimta a tsakanin junanmu,mu bi komi a hankali domin aikin gaggawa mafiya yawan lokuta daga shaiɗan ne,duk wani bore da kalaman banza da ke fitowa da daga bakin Karimatu aikin banza ne domin kuwa tun ran gini ran zane ne,idan har Allah ya riga ya hukunta aure a tsakanin Sadeeq da Raudah cikin littafin RAYUWA DA ƘADDARAR su tabbas babu mahalukin da ya isa ya hana wanzuwar hakan sai dai idan lokaci bai yi ba,idan kuwa Allah bai rubuta ba duk yadda zamu kai ga son su dasu mallaki junansu hakan ba zai faru ba,don haka mu maida lamura zuwa garesa mu taya su da addu'a sai mu ga komi ya zo ya wuce cikin sauƙi." Baba Lawal ya sauke numfashi a hankali,cikin matuƙar gamsuwa da kalaman Baba Auwalu ya jinjina kai yana faɗin, "Wannan batu haka yake Auwalu,maganarka ita ce abar dubawa." Hajjah Kakah ta ƙanƙance idanu ta ce, "Dukkaninku na ji hanzarinku da shawarinku,sai dai ku sani ba zan taɓa yin kaffarar rantsuwar da nayi ba,don haka ƙarshen wata nake so in ga kayan sanya rana sun bayyana a gabana,ku tashi ku bani waje na sallameku." Tana kai wa ƙarshen kalamanta ta ɗauke kai daga dubansu tana faman huci.Suka tashi gaba ɗayansu suna haɗa baki wajen faɗin, "Allah ya baki haƙuri,za a cika umurninki In Sha Allah!" Ta taɓe baki tana duban Baba Mai Itace ta ce, "Idan ka shiga ɓangarenka ka turo mini Raudah da Maimunatu ina son ganinsu." Baba Lawal ya jinjina kai ya ce, "Za a turo su yanzu,mu kwana lafiya Hajiya." Hajjah Kakah ta amsa shi a dake tana rakasu da wani irin kallo na cewa,dani ku ke zacen.

Suna tafe jere da juna ne suna tattauna maganar Hajiya Kakah na dagewa akan lallai a fara sanya ranan auren Raudah da Sadiku,shi ma kuma Baba Adamu da alamu hukuncin mahaifiyar tasu ya yi masa daidai.Hakan ya sanya Baba Lawal da Baba Auwalu yin fatan alkhairy,Baba Auwalun na faɗi ma Baba Adamu cewa,zai yi magana da Sadeeq ɗin zuwa da safe domin a yanzu akwai ayyukan da zai gabatar idan ya shiga cikin gidansa.Sukai sallama da junansu kowanne ya nufi sasansa yana jinjina rigima irin ta tsohuwar tasu,wacce idan ta kafe akan ra'ayinta samun mai sakko da ita sai Allah.

"Raudatu maza sanya mayafi ki je Hajiya na son ganinku ke da Maimunatu." Baba Lawal ya faɗi hakan lokacin da yake ɗage labulen ɗakin Umma yana mai sauke ganinsa akan su Raudah dake zaune a falon suna kallo,da yake yinin ranar anbar wuta sosai har daren.Rahdah sukai masa sannu da shigowa tana ɗaurawa da faɗin, "To Baba." Daga haka ta miƙe ta nufi ɗakinsu domin ɗakko hijab ta je amsa kiran mutuniyar tata Hajjah Kakah.Ya saki labulen tare da juyawa ya nufi ɗakin Anty Safiya,da sallama ya shiga cikin ɗakin ya sameta tare da Maimunatu suna zaune a falonta su ma kallon suke yi.Ya dubi Maimunatu ya ce, "Ke! Tashi ki je Hajiya na son magana da ke." Maimunatu ta ɗan zumɓuri baki ta ce, "To Baba zan je." Ya sake haɗe fuska ya ce, "Tashi yanzu ki fice." Anty Safiya ta ɗago kai ta dubeshi ta ce, "Yo wannan kira na mene ne haka da za a azalzaleta?" Bai tanka maganarta ba ya cigaba da tsayuwa har Maimunatu ta miƙe ta nufi ƙofa domin fita,ya bi kayan jikinta da kallo yana faɗin, "Wuce ki ɗakko mayafi mara kunyar banza da wofi kawai." Anty Safiya ta ja ƙwafa ta ce, "Rashin kunya ai gado tayi ta wajen uwa da uba." Baba Lawal bai tanka ba stilll,ya cigaba da tsayuwa har Maimunatu ta ɗakko mayafi ta fice sannan ya shi ma ya rufa mata baya.Kusan a tare da Raudah suka isa ɓangaren Hajjah Kakan,sun samu su Yayah Sadeeq da Yaya Usman a ɗakin suna mata hira.Ganin shigowarsu ya sanya Yaya Usman tashi yana faɗin, "Hajjah Kakah sai da safe." Ta amshi idanunta akan Maimunatu da ta ja tayi tsaye bata da alamun samun wajen zama kamar yadda Raudah tayi,cikin tsare gida ta ce, "Miye kuma haka zaki yiwa mutane tsaye kamar wata soja?" Yaya Deeku ya ɗaga kai ya watsawa Maimunatu wani mummunan kallo,babu shiri ta lalubi kujera ta zauna tana faman zunɓure baki.Raudah ta fara gaida shi ya amsa da kulawa yana aika mata wani irin sassanyar kallon da narkar da zuciyarta,Koda Maimunatu ta gaida shi a tsume ya amsa yana sake kallon yadda Yarinyar duk ta ɓata kanta da bilicin.Ganin alamun magana Hajjah Kakah ke son yi dasu sai ya miƙe ya fice daga ɗakin bayan ya yi sallama da Hajjah Kakah,Raudah ta raka shi da ido tana jin ƙaunarsa a cikin zuciyarta. "Maimunatu ina so ki sani sam ba zan ɗauki kalar rayuwar sakarcin da ki ka ɓullo dashi ba,don haka tun wuri ki fiddo miji cikin samarin da kuke gantalewar tare,idan ba haka ba sai dai ku tattara ke da uwarki da ke ɗaure miki gindi ku bar gidan nan ehe!" Ta dakata tana kallon yadda Maimunatu ke jifanta da wani irin kallo kafin ta buɗe baki tana faɗin, "Hajjah Kakah kema munafurcin da ake ƙulla mini har ya iso gareki kenan? To ni babu ajandar aure yanzu a shafina sai na kammala secondary,wani irin maganar aure kuma ana zaune ƙalau mutum na watayawansa son ransa? Gaskiya ki dai sake shawara su dai da suke son aure kuma sune manya sai a fara kawar dasu,idan iskanci ne ai kowa da kalar nasa bani kaɗai bace ƴar iskar ehe!" Ta ƙare maganar tana kaɗa ƙafafu.Hajjah Kakah ta ja salati kai ka ce mutuwa aka rafka,kafin ta riƙe baki tana faɗin, "Eh! Lallai ba shakka kin san daɗin maza Maimunatu,babu ko kokonto kin haɗa gado da namiji dole ki kalli tsabar idanuna kina gaya mini wannan kalaman babu kunya bare tsoron Ubangiji,tabbas barewa bata gudu ɗanta ya yi rarrafe,Safiya da Lawal sun cuceni da suka yi tarayyan da har suka san juna sukai aure suka haifo mini tambaɗaɗɗiyar jika kamarki." Hajjah Kakah ta ƙare maganar cikin rawar murya sosai.Maimunatu kuwa miƙewa tayi a fusace tana jan dogon tsaki ta fice daga ɗakin,Raudah da tayi mutuwar zaune sai ta rakata da idanunta da ke cike da zallar mamaki da firgicin kalaman da ke fitowa daga bakin Maimunatun.Har Hajjah Kakah ta share hawayenta ta juyo kanta ta kasa ɗaga ido ta dubeta,cikin wani irin sauti Hajja Kakah ta ce, "Kin ga sharrin aurowa kai ragowar bariki ko Raudatu? Kin ga kaɗan daga illar cin bashin zina ko? Ita zina na so gareta,tayi ta bibiyan jini ana ganin masifu kala-kala,yanzu kin ji dai babu kunya bare tsoro ta amsa sunanta na ƴar iska,yo uwarta tayi iskanci da ubanta tun kafin ya auro uwar su haifota,ke kinga laifi ne don Allah ya basu magajiyar da ta gajesu a iskancin?" Raudah ta rintse idanunta tana jin matuƙar zafin kalaman Hajjah Kakah,cikin matuƙar rawar murya ta ce, "Please! Hajjah ki daina furta irin waɗannan kalaman,ki bar abinda ya wuce a matsayin ya wuce,tunda wannan laifin da kuskuren da aka aikata ba ke aka aikata mawa ba,tsakaninsu da Mahaliccinsu ne Hajjah Kakah,kuma shi mai yawan gafara da yafiya ne matuƙar bawa ya tuba izuwa garesa da kyakykyawar niyya,addu'a ita kaɗaice za ki taya Maimunatu dashi,bawai ki dinga furta mata irin waɗannan kalaman ba." Hajjah Kakah ta ja hanci tare da sake share hawayenta ta dubi Raudah ta ce, "Hakane Raudatu kin fini gaskiya,amma ki sani ina matuƙar baƙin ciki da ganin wannan lalacewar a cikin ahalina,ban taɓa ƙaunar Safiya ba domin macen kirki ka ke fata ta dauwama tare da jininka ba watsatstsiya ba,yanzu dai mu koma batun soyayyarki da ɗan uwanki Sadiku,shin da gaske har cikin zuciyarki ya yi miki ko kina da wani da ki ke so bayan shi?" Raudah ta girgiza kai tana faɗin, "Hajjah Kakah me kuma ya kawo wannan titsiyen?" Hajjah Kakah ta aika mata harara ta ce, "Ki bani amsa kawai sarkin baki." Raudah tayi ƙasa da kai ta ce, "Hajjah Kakah ni bani da kowa bayan shi." Hajjah Kakah farin ciki ya cika zuciyarta,cike da ɗoki ta ce, "To ƙarshen wata za a tsaida ranar aurenku Raudatu,don haka ki toshe kunnuwarki ki kuma rufe idanunki akan duk abinda zaki ji ko ki gani daga Karimatu,kada ƙiyayya da adawar da take yi da wannan haɗin ya dameki domin kuwa bata isa ba, tayi kaɗan ta ja dani akan batun aurenku tunda har kuna son junanku,shiyasa nake so ayi komi cikin gaggawa." Raudah ta ɗaga manyan idanunta ta sauke akan Hajjah Kakah zuciyarta na wani irin bugawa.Da rawar murya ta ce, "Ƙarshen wata fa Hajjah Kakah saurin me ake yi haka?" Hajjah Kakah ta haɗe fuska ta ce, "Ba huruminki bane,ke dai tunda kin gamsu dashi kina kuma ƙaunarsa to tashi ki bani waje." Raudah ta zumɓuri baki ta ce, "Ni dai gaskiya Hajjah abi komi a sannu gaggawa fa aikin shaiɗan ne." Hajjah Kakah ta ja tsaki ta ce, "Na ji dai,ki gaida Halimatu sai da safe,ki turo Sumayyah na ga alamun ba za ta zo tayani kwanan bane yau." Raudah ta fito daga sasan Hajjah Kakah tana jujjuya hukuncin Hajjah Kakah tana ji sam zuciyarta bata gamsu ba.......✍🏻



*To masu karatu duka anan na kawo ƙarshen free pages na labarin RAYUWA DA ƘADDARA,ba sai na ce muku komi ba game da irin ƙullin da ke cikin wannan tafiyar. Labarin duka yanzu ne za a fara wasan,don haka kada ki bari ayi wannan tafiyar babu ku,domin kuwa baku ji komi ba,kamar yadda yanzu ne zaren labarin zai fara ja.Ku dai kawai ku nuna wa labarin ƙauna ta hanyar yin rufdugu domin cika gidan ahalin Hajjah Kakah,domin jin ya rayuwar ahalinta dana surukukanta zai kasance? Wai shin ma mine ne a cikin RAYUWA DA ƘADDARAR Raudah? Amsar duka na tare da Aysha Ɗansabo lemu,tafiyar ta dabance kamar yadda salon labarin kawai ya sha bambam da sauran labaran da na saba kawo muku,don haka mu haɗu a paid group domin jin cikakken wannan labarin da tarin darussa na rayuwa da ke cikinsa.*



*Ina godiya ga ɗinbin masoya masu ƙaunar wannan labarin,Allah ya hore muku kuɗin siya ya kuma rufa asirin mu baki ɗaya duniya da lahira.Akwai promo da zai bai wa kowa damar mallakar labarin akan kuɗi ƙalilan,Bye👋🏻*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment