Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakya iya kwaɓawa akan abinda duk ya kamata." Wajen ya ɗauki shiru, Hajjah Kakah na faman zare idanu,ganin yadda Raudah tayi kicin-kicin da fuska.A hankali su Hameedah suka fara tashi suna yiwa Hajjah Kakah sai da safe suna tafiya sasansu,takaici kamar zai halaka Sumayyah ta miƙe tayi gaba tana jin gabaki ɗaya ta muzanta a gaban su Bushirah domin bata ji daɗin yadda Hajjah Kakah ke yawan tunasar dasu irin zunubin da ubansu ya aikata a baya ba.....✍🏻
[10/9, 2:36 PM] Aysha Dansabo😍: *RAYUWA DA ƘADDARA*
*Arewabooks@ayshadansabo*

*Paida Book 08167768704*

_Free page_

*Chapter 8*

Misalin ƙarfe sha ɗaya na dare ne,Baba Lawal tare da ƙaninsa Baba Adamu ne zaune a dakalin shiga sasan Baba Lawal ɗin suna magana Maimunatu ta buɗo gate ɗin shigowa gidan irin na da ɗinnan ta shigo.Suka ɗaga kai a tare suna kallon wajen duk a tunaninsu cikin samarin gidan ne Abubakar ko Usman wani ya yi daren dawowa gidan a cikinsu.Idanunsu na sauka akan Maimunatu da ke tunkarosu cikin shigar baƙar Abaya,duka sai rayukansu suka ƙuntata,wani irin abu mai matuƙar nauyi ne ya taso ya danne zuciyar Baba Lawal.Baba Adamu da ya kasance mai zafi duk a cikinsu,shi ne ya daka mata tsawa tare da tsayar da ita lokacin da tayi musu sannu tana shirin giftasu ta shige cikin sasan nasu. "Daga gidan uban wa ki ke Maimunatu ƙarfe sha ɗayan dare?" Baba Adamu ya jefa mata tambayar masifaffun idanunsa fes akan Maimunatu da sam babu tsoro ko kaɗan akan fuskarta,domin zuciyarta ta riga da ta fara bushewa.Cikin yin ƙasa da murya ta bashi amsa kai tsaye da faɗin, "Bikin ƙawata ake yi Baban Zee, shi ne muka ɗanyi dare mun kai Amarya." Ba domin ya amince da abinda ta faɗi ba ya shiga balbaleta da faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba,ya kuma sanar da ita lallai gobe da safe ta same shi a sasansa yana son ganinta kafin su wuce makarata tunda gobe monday duk za a koma hutu.Tana shigewa ya maida dubansa kan Baba Mai Itace da takaicin duniya ya gama lulluɓesa ya ce, "Yanzu Yaya akan idanunka wannan Yarinyar ke iya kai wa har wannan lokacin a waje? Koda ace daga yawan biki take kamar yadda ta faɗi hakan sam bai kamata ba,domin rayuwa tayi sauyawar da ko kaɗan bai kamata mu riƙa sakaci da tarbiyan Yaranmu ba,musamman ƴan mata kamarsu da duk mai hankali da zaran ƴarsa ta balaga bashi da sauran sukuni,yakamata ka zama tsayayye a cikin gidanka,domin idan aka ce ka sakarwa mace ragamar tarbiya tabbas akwai ɓarna,musamman ma mata irin Karima da Safiya da sam basu san annabi ya faku ba wajen aikata son zukatansu." Ya ƙare maganar yana sake jin tsanar matar wan nasa da yake da tabbacin tana da kaso mai yawa wajen kangarar masa da Karimarsa da sake ɗaurata akan layin shaiɗana kala-kala.Baba Lawal ya ɗago idanunsa da sukai jajir ya sauke akan ɗan uwansa,shi kaɗai yasan me yake ji a cikin zuciyarsa game da lalacewar tarbiyar Maimunatu.Da wani irin karyayyen sauti ya furta, "Astagfirullah Allah! Allah na tuba ka duba mini lamarin Iyalina,Adamu tabbas na aikata kuskuren da har a zare numfashi daga gangar jikina ba zan daina danasanin taɓa mutuncin ƴaƴan wasu da nayi a baya ba,tabbas nayi tuba irin wanda Ubangiji ke so,domin tunda na bar zina ban sake marmarin komawa ruwa ba,tun daga randa Allah ya fara tara mini ƴaƴa mata na shiga ruɗu da fargaba mai tsanani,sai dai a yau gashi ina ganin aibun abinda na aikata,domin dama ance ita zina bashi ce,tabbas gashi ina biya da mafi munin ji da gani a cikin zuriyata..." Wasu hawaye masu ɗumi suka sakko daga kwarmin idanun Baba Lawal,yana jin yadda zuciyarsa ke masa tsananin zafi da ƙuna.Baba Adamu da kalaman ɗan uwansa suka taɓa zuciyarsa sai ya ji dukkanin jikinsa ya yi sanyi,ya dubi Baba Mai Itace ya ce, "Yaya ka yi haƙuri,ka kuma sake tuba zuwa ga Ubangiji,sannan ka sanya idanu a cikin gidanka ka kare mutuncin Iyalinka iyakan ƙarfinka,ka zama tsayayyen da mace ba za ta iya lanƙwasaka ba sai ka samu sauƙin al'amura." Baba Lawal ya jinjina kai yana yiwa ɗan uwansa godiya,sukai sallama ba don sun ƙarisa tattauna maganar da suke yi ba.Baba Lawal ya shige cikin sasansa a fusace,yayinda Baba Adamu ya nufi nashi sasan da yake shi ne daga can farko.

"Safiya!Safiya!! Kina ina ne?" Baba Mai Ice ya shiga kwaɗa mata kira yana isa bakin ƙofar ɗakin Anty Amarya.Bai kuma jira amsawarta ba ya ɗage labulen ya sanya kansa ciki a fusace,jikinsa har rawa yake sabida tsananin ɓacin rai da ke cin zuciyarsa.Sai dai me, suna haɗa idanu da Anty Safiya ya nemi dukkanin zafin zuciya da rawar jikin da ya shigo dashi na son cin mutuncinsu ita da Maimunatu ya rasa,da wani irin murya da ban san taya zan iya fassara muku ba ya dubi cikin idanun Anty Safiya yana faɗin, "Yanzu Safiya kin ga dacewar budurwa kamar Maimunatu ta kai har ƙarfe sha ɗaya na dare a waje da sunan wai ta dawo daga biki?Haka ta ga ƴan uwanta su Raudah nayi?" Anty Safiya tayi masa wani irin sakartaccen kallo ta ce, "Ka gama?" Ya jinjina kai yana satan duban Maimunatun da tayi musu tsuru da idanu tana kaɗa ƙafa bisa seater,gabanta ledar tsire ne mai yawan gaske a buɗe da alamu zasu fara ci kenan ya faɗo ɗakin.Ya ɗauke idanunsa daga kanta tare da rintsesu yana jin wani irin kibiya mai tsini na sukan zuciyarsa da tsananin zafi,maganan da Anty Safiya ta fara suka shiga kunnuwarsa kai tsaye lokacin da take faɗin, "Kar ka kuma haɗa mini ƴa da wasu banzayen ƴaƴanka marasa farin jini,suma da ka ke ganinsu biya-biya cikin hijab kasan ta'asar da suke aikatawa a waje ne? Musamman ita Raudar da kullum sake cika take ƙirjinta na tumbatsa,idan ba taɓa su ake yi ana basu taki ba banga ta inda za ta dinga ƙaro kyawu kamar wacce ake wa wankan inji ba,don haka ka cire idanunka akan ƴata ita kaɗai,domin idan an biye ta abinda ka aikata ne babu ƴarka ɗaya da za ta tsira ba a farke mutuncinta an moreta a titi ba,ko ka manta sanda na sallama maka budurcina ne a akan kujerar......" Wani irin tsawar da bai san yadda aka yi ya iya daka mata ba ya katse Anty Safiya daga cigaba da furta zafafan kalaman tozarcin da ta faro,zuciyarsa na wani irin zillo tamkar zai fito daga ƙirjinsa ya nunata da yatsa yana son yin magana amma ya kasa.Ya sauke hannun yana juyawa ya fito daga ɗakin hawaye na wanke fuskarsa,idanunsa suka rufe har baya ganin gabansa lokacin da ya kai kansa ɗakin baccinsa.

Tamkar wanda aka jefo haka Umma ta ɗaga idanunta tana kallon Baban Raudah da ya faɗo cikin ɗakin,tana zaune daga bakin gadonsa sanye cikin doguwar riga ta bacci da tayi mata kyau matuƙa.Shigowarta kenan bada jimawa ba bayan ta jiyo sallamar shigowarsa sasan,sai ta cidda bashi cikin ɗakin sai sautin muryarsa da take jiyowa daga ɗakin Safiya.Ta dubeshi tana kallon yadda sam babu sukuni a tattare dashi,tana son ta tambayeshi abinda ke faruwa to amma bata son shiga huruminsa da matarsa.Hakan ya sanya ta ɗauke kai tayi kamar bata kula da yanayin da ya faɗo cikin ɗakin ba,aka ɗauki tsayin mintuna tana sauraren yadda yake sauke wani irin ajiyar zuciya.Ta sake ɗaga idanunta a karo na uku ta sauke akan kyakykyawar black beauty face ɗinsa da idanunsa ke rintse,idanunta suka cigaba da yawo akan hannunsa ɗaya da ya kai ya dafe saitin zuciyarsa da shi.Wani irin abu mai ƙarfi ya fisgi zuciyar Umma har ta kasa daurewa ta ce, "Baban Raudah lafiya kuwa?" Sai lokacin ya buɗe idanunsa da suka firgigitata sabida ganin yadda suka rine sukai jajir,da wani irin karyayyen sauti ya ce, "Halimatu bani ruwa mai tsananin sanyi in sha,in son samu ne ma ki haɗo da ƙanƙara ki zo ki manna mini a saitin zuciyata ko zan samu sassaucin zafin raɗaɗin wutar da ke kama a cikinta.Umma ta rintse idanunta tausayinsa mai tsanani ya lulluɓe zuciyarta,ta miƙe a hankali ta fito daga turakarsa ta nufi ɗakinta.Zagawa tayi ta saitin windon ɗakin su Raudah ta shiga bugawa a hankali,domin tana fitowa suka rufe ƙofar ɗakin kamar yadda suka saba idan ita ke da kwana da ta fita suke rufe ɗakin sai da asuba suke buɗewa idan sun tashi yin sallah.A hankali take buga windon tana kiran sunan Raudah,Raudah da taƙi kwana a ɓangaren Hajjah kamar yadda Yaya Sadeeq yaso,suna kwance ne bisa katifarsu ita da Sumayyah da tayi bacci.Ita kuma chart suke da Yaya Sadeeq ɗin bayan kammala yin wayarsu,jin muryar Umman na kiranta ya sanyata aje wayar ta fito ta buɗe ƙofar falon.Umma ta wuce kai tsaye zuwa wajen da freezernta ke aje ta buɗe ta ɗauki pure water da take siyarwa guda biyu da sukai tsananin sanyi ta fice,Raudah ta bi bayanta da kallo tana mamakin abinda Umman za ta yi da ruwan da suka kusa yin ƙanƙara a daren,domin ta sani daga ita har Baba Mai Itace ba ma'abota shan ruwan sanyi bane.Bata zurfafa wajen tunani ba ta rufe ƙofar ɗakin ta nufi ɗakin baccinsu,wayar ta ɗauka suka cigaba da chart ɗinsu da Yaya Deekunta kafin daga ƙarshe ta kashe data tayi shirin kwanciya.

A ɗakin Baba Mai Itace kuwa,ruwan sanyin Umma ta tsiyaya masa a kofi ta miƙa masa.Ya tashi da ƙyar ya amsa kofin tare da ɗaɗɗakawa cikinsa ruwan,ya sake ya miƙa mata kofin a karo na biyu ta juye masa ragowan ruwan ya shanye yana sauke numfashi.Da wani irin sanyin murya ya ce, "Zo zuba mini a ƙirjina Halimatu." Umma ta matsa gareshi sosai tare da taya shi ya zare rigar jikinsa,a hankali ta dinga shafa masa ruwan sanyin bisa ƙirjinsa har sai da ya janye hannuwanta da kansa alamun ya isa hakanan.Ta ja baya tana kasa ɗauke idanunta daga dubansa,zuciyarta na son sanin me ya sabbaba masa shiga irin wannan yanayin haka? Sai dai duk yadda ta so sani ta kasa tambayarsa, ta zuba masa abincin da sam bai shigo gidan da wuri yaci ba sai yanzu ɗin.Kaɗan ya iya cin abinci ya ture yana miƙewa zuwa ƙaramin banɗakin da ke cikin turakan nasa,koda ya fito ya samu Umma ta kwanta domin ita mai baccin wuri ce sabida tashi sallan dare da ya zame mata jiki.Ya yi mata kallo ɗaya yana sake jin matsananciyar ƙaunarta da sake godewa Ubangijinsa da ya azurtashi da kamammiyar mace,kuma haƙurarriya kamar Umman.Ya dinga tuna lokacin da ya aurota shi ya fara saninta,a lokacin gani yake ya tsallake siraɗin da ake cewa mazinaci baya taɓa auren macen ƙwarai sai mazinaciya irinsa.A maimakon ya tuba tun a lokacin sai ya cigaba da sharholiyansa da matan banza,har zuwa lokacin da Allah ya haɗashi da Safiya.Kamar yadda ta faɗi shiya fara saninta,daga baya ne ta dilmiya har ta zama karuwa ta sosai,daga bisani kuma Allah ya jarabesu da son junansu.An sha fama kafin ya amince maganar aure ya shiga tsakani,har sai da uwarta suka haɗa har da asiri kafin ya amince da maganar aurenta.Bayan anyi auren kuma basu bar shi haka ba, suka sanya aka yi asirin da za ta mallakeshi tsaf sai yadda ta ga dama za tayi,asiri da yake gaskiya ne kuma ya ci har fiyayyen halitta, sai suka yi nasara akansa suka kuma samu yadda suke so ɗin.Domin duk yadda ya kai ga jin zafin Safiya bai isa iya ɗaukar mataki mai zafi a kanta ba,sai dai ya furta kalaman da basu kai sun kawo ba.Ba a ɗauki dogon zango ba ya gane dama can talala Allah ya yi masa da fari da ya azurta shi da mace kamar Umma,sai daga bisani aka jarabcesa da Safiya da ta zamewa rayuwarsa ƙarfen ƙafa.Ya kai hannu ya share hawayen da suka zubo masa yana mai ɗaga hannu sama yana faɗin, "Allah na tuba ya Allah!Ina kuma sake gode maka da ka bani mace kamar Halimatu, baka tara mini tarin kara da kiyashi irin Safiya ba.

Ya raɓa ya kwanta a gefen Umma ba don yana jin cewa idanunsa zasu iya rintsawa a wannan daren ba,domin har yanzu dafin kalaman Safiya basu gama illata zuciyarsa ba.Musamman yadda take ƙoƙarin jinginawa Raudah mummun ƙazafin da baya fata Ubangiji ya jarabcesa da ji da gabi,idanunsa kawai ya rufe fuskar Maimunatu na gilma masa a lokacin da Anty Safiya ke furta waɗannan miyagun kalaman a gabanta,ya dinga ji zuciyarsa na sake ɗaukan wani irin zafi da ƙuna.A kunnuwarsa Umma ta tashi cikin tsakiyar daren domin gabatar da ibadarta na sallan dare da ya zame mata jiki,ta sauka daga gadon tare da ɗaukar wayarta ta kunna haskensa ta isa ƙaramin banɗakinsa da aka tsafata a cikin ɗakin.Wanda babu matsuguni anyi shi ne kawai na wanka,sai wajen wucewan ruwa da za a iya tsugunawa ayi fitsari kaɗai.Alwala ta ɗauro ta fito ta tada sallah duk akan idanun Baba Mai Itace da ke kwance yana kukan zuci,idanunsa sunyi rayas babu alamun jin bacci ko ƙanƙani.Banda tunanuka da nadamar irin rayuwar da ya yi a baya babu abinda ke kai kawo a cikin zuciyarsa,abu mafi ciwo da nadaman da ke kassara zuciyarsa a lokacin bai wuce na aurensa da Safiya ba.Sai dai ya sani hakan na daga cikin kamun da Ubangiji ya yi masa,domin a nuna masa cewa bai ci banza ba na auren salihar mace da fari irin Umma. Har Umma ta idar da nafilfilinta daidai lokacin da agogo ke buga ƙarfe uku rabi na dare Baba Lawal bai runtsa ba,a kuma daidai lokacin nefa suka ƙyallo wuta.Fitilar ɗakin da sam Umma ta manta bata kashesa ba haskensa ya gauraye ɗakin,ta ɗaga manyan idanunta ta dubi sashin da Baban su Raudan ke kwance.Ga tsananin mamakinta sai ta gansa a zaune ya zubo mata idanu hawaye na sauka bisa fuskarsa,jikinta ya yi wani irin mugun yin sanyi.Ta taso a hankali ta dawo bakin gadon tana zuba masa idanunta ta ce, "Baban Raudah wai lafiyanka kuwa,wani irin damuwa ce haka da ya hanaka rintsawa duk sonka da bacci?" Baba Mai Itace ya jinjina kai yana kai hannu ya ɗauke zafafan hawayen da suka sulmiyo masa,cikin wani irin raunin murya ya ce, "Halimatu ba zan iya rintsawa ba,zuciyata ƙuna da raɗaɗi take mini irin yadda ba zan iya misaltawa ba,nayi nadama Halimatu,tabbas nayi danasanin haɗa jinina da na Safiya!" Ya dakata yana kai hannu ya dafe saitin zuciyarsa da ke wani irin zafi.Umma tayi ƙasa da kanta maganganunsu Anty Safiya da Raudah ta jiyo ɗazu da rana suka shiga dawowa kwanyarta,cikin sanyin murya ta ce, "Mai kuma ya faru Baban Raudah? Ka daina cewa ka yi danasanin aurenta domin auren soyayya ku kai da juna,kuma ta sha faɗin kai ne ka fara saninta a ƴa mace,ka ga ba laifi bane don Ubangiji ya yi mata sakayya ta hanyar haɗaku aure,sannan ita ma a lokacin da ka ɓata rayuwarta kar ka manta Ƴar wani ce,don haka ka daina danasani Baban Raudah domin shi Allah gwanin hikima ne da kuma iya kama bayinsa ta inda basu yi zato ba,ka sake komawa zuwa garesa kana mai ƙasƙantar da kanka da miƙa ƙoƙon bara akan ya kawo maka mafita,ya kuma yafe yawan zunubanka ta yadda zasu taƙaita har su daina bibiyan jininka da basu ji ba basu kuma gani ba... " Wani irin kuka silently ya ƙwacewa Umma,ta dinga yinsa tana jin wani irin tausayinsu na lulluɓe zuciyarta.Shi ma Baba Mai Itace kukan yake yana ji duniyar nayi masa matuƙar zafi,kalaman Umman suke shigarsa tare da sake raunata zuciyarsa.Muryarta ne ya sake shiga kunnuwarsa da wani irin sauti da ke ratsa har kwanyarsa, "Kana da sakaci Lawal wajen dagewa da addu'a da kuma tsayuwar dare,ka sani inda ace yadda ka tuba irin tuban da baka sake aikata zina a rayuwarka ba,da ace ka ɗaura da yin tsayuwar daka wajen riƙe addu'a da yawaita istigfari da tsayuwa a cikin dararen da bayi ke kwance suna bacci,tabbas da ka sake samun nutsuwar zuciya da kuma warwarewar wasu ƙulle-ƙulle da dama da suke kewaye dakai.Da ace zaka dage da gayawa Ubangijin da baya gyangyaɗi bare bacci matsalolinka,tabbas da ya yi maka mafita mai yawa cikin lamuran da kai kanka bakasan sun sha maka gaba ba." Ta ɗan dakata tana sake kallon yadda ya zubo mata idanunsa yana sauraronta da dukkanin nutsuwarsa,hakan ya sanyata ɗaurawa da faɗin, "Sihiri gaskiya ne domin kuwa ya ci fiyayyen halitta,amma da yawa ku maza bakwa yarda da hakan,sai ku shantake ku manta da tsaida azkar bare har ku dage da yawaita yin addu'o'in da zasu kare ku daga sharrin sihiri da ƴan surkulle,kafin ace kwabo sai matsaloli da kaidin mace su kewaye rayuwarku har ku tsinci kanku cikin yanayin da wani idan ya mutu direct wuta zai tafi sabida yadda aka juya zuciyarsa ya danne hakkin iyalinsa tare da cusgunawa rayuwarsu,ka tashi ka yi sallah koda raka'a biyu ne Lawal,ka koka wa Ubangijinka tare da yi masa kirari da yabo da mafiya kyawawan sunayen da yake son a ambacesa da su na AL-HAYYU AL-QAYYUM! Ka roƙesa ya yafe maka ya kuma kawo maka mafita cikin tarin abubuwan da suka dameka game da matarka,wanda ni Halimatu bana son ma in sani,Ina da yaƙinin idan ka jera hakan na tsayin kwanaki sai Allah ya baka mafita a lamura da yawa,ina ma ni ce Hajiya Kakah da sai in ce na wajabta maka tsayuwar dare ya zama ibadar za ka dauwama a cikinta domin da shi ne bawa ke gararan duk wani maƙiyinsa a duniya,sannan kuma ya rabauta ranar gobe ƙiyama,matuƙar zaka dage da kai wa Allah kukan ka a lokacin da da yawan bayi ke tsaka da ƙulla sharri ko yin ƙulunbota a tsakanin al'umma,tabbas Ubangiji zai dubeka ya kuma kare ka daga dukkan sharrinsu,babu kuma abinda zai sameka sai abinda aka riga aka zana shi cikin littafin RAYUWA DA ƘADDARAR ka." Umma ta kai ƙarshen kalamanta tana kashe Baba Lawal da wani irin kallon da ke kashe jiki da zuciyarsa.Shi kuwa ya zuba mata idanunsa ba ya ko son ɗauke ganinsa daga gareta,domin wasu irin feelings yake ji masu matuƙar ƙarfi na sake fisgar zuciyarsa zuwa gareta."Wace iriyar Rahama da soyayyah Ubangiji ya gwada masa da ya fara mallaka masa irin wannan kalar macen a duniya?" Ya tambayi kansa yana tashi da wani irin sauri ya dunfari banɗakinsa domin ɗauro alwala.Umma ta bi bayansa da kallo tana jin tarin ƙauna da tausayinsa mai yawa a cikin zuciyarta,ta ɗaga hannu sama tayi a addu'a a sarari tana faɗin, "Ya Allah ga bawanka nan Lawal,ka sake yin Rahama da gafara zuwa garesa,ka yafe zunubansa kar ka raba zunubansa da sauran ƴaƴansa da basu ji ba basu gani ba Ya Allah! Ubangiji ka warware dukkanin ƙullin da ke jikinsa idan har akwai sihiri ko ƙulunboto na shaiɗanci mace a cikin al'amarinsa." Ta sauke hannuwanta ƙasa tana kai tafin hannunta ta share hawayen da ke gudu bisa ƙuncinta,ta kalli fuskar Baba Mai Itace a lokacin da ya fito daga banɗakin ya doshi saman abin sallar da ta tashi akai.Sai ta zame ta kwanta idanunta akan sa har ya idar da raka'a biyun da ya yi su masu tsayi,tun a sujadarsa ta ƙarshe take jiyo shasshekar kukansa tana ji zuciyarta na sake shiga rauni da ƙarin tausayinsa.Ta fi kowa sanin koda baƙin cikin lalacewar tarbiyya da rayuwar Maimunatu kaɗai aka barsa an jarabcesa,koda ace babu matsalar zama da mace irin Safiya da bata san mutuncinsa dana aurensa ba ko kaɗan.Tunda bata shayin kallon tsabar idanunsa a gaban ƴaƴansa ta kirashi da kalmar ɗan bariki,bata taɓa jin nauyin kallon idanunsa ta tuna masa da kalar rayuwar iskanci da suka yi abaya ita da shi ba.A she ko ba za a lissafata cikin macen da ta san ciwan kanta ba,bare kuma sanin daraja da girman mijin aurenta.Lokacin da ta ga tashinsa daga saman abin sallar sai ta juya masa baya tana gyara kwanciyarta tara da rufe idanunta tamkar wanda bacci ya saceta,tana jin lokacin da ya hawo kan gadon ya kuma lalubeta ya haɗe jikinsu da juna yana jin tsananin ƙaunarta da ya jima bai ji hakan ba a cikin zuciyarsa......✍🏻
[10/11, 12:20 PM] Aysha Dansabo😍: *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo*

*Paid book 08167768704*

_Free page_


*Chapter 9*


"Sumayyatu bani da kuɗi,kiyi haƙuri zuwa wata satin zan baki kuɗin ki siya littafan kin ji ko?" Baba Mai Itace ke wannan maganar idanunsa akan Sumayyah dake shirye cikin uniform ɗinta da suka ɗauki guga sai ɗaukar idanu suke.Ta ɗaga manyan idanunta da suka gada wajen Umma ta sauke akan Baban nasu wani abu na taɓa zuciyarta,cikin sanyi da kuma raunin murya ta ce, "Amma Baba yanzu fa ka bai wa Maimunatu nata kuɗin sayen littafin." Ta dakata tana sake duban yadda nan da nan annurin fuskarsa ta ɓace,cikin kaushin murya ya ce, "To suke nan mini na ɗauka na bata,ke kuma sai ki jira sai na sake samun wasu kuɗin,idan kuma kuɗin cefanen da zan bayar ki ke so na ɗauka na baki sai ki gaya mini." Sumayyah ta miƙe jiki a sanyaye tana faɗin, "Allah ya baka haƙuri Baba sai mun dawo." Ya dubeta yana jin can ƙasan zuciyarsa na rawa,amma a zahiri sai ya buɗe baki ya ce, "A dawo lafiya,a kuma dinga mai da hankali,Allah ya yi albarka Sumayyah." Sumayyah ta ƙarisa ficewa da sauri tana jin yadda zuciyarta ke sake karyewa hayewa na cika idanunta."Har sai yaushe ne zai daina nuna musu bambamci?" Ta tambayi kanta tana sake hasko irin murmushin gayya da Maimunatu ta sakar mata sanda Baban nasu ya ɗauki naira dubu ya bata kuɗin wani littafi da aka ce lallai su mallakesa a satin farko da za a koma domin shi za a fara karanta musu.Ta isa ɗakin Umman zuciyarta na sake ƙuntata matuƙa,tana shiga ta ci karo da Raudah ta fito daga ɗakinsu sanye cikin dogon Jalbab ɗinta na zamani.Wani irin Jalbab mai haɗe da kamar niƙab da idan ta ɗaure jelar ɗankwanlin ta janyo shi zuwa goshinta,ta kuma ja ƙasan hular da ke ƙasan gemunta sai ya zamana ya rufe daga bakin zuwa hancinta.Idanunta kawai ake gani a buɗe,amma duk fuskarta sai ya zamana a rufe yake.Sosai kalar Jalbab ɗin da yake dark coffee ya haske farar fatarta,yanayin zaman jalbab ɗin a jikinta ba ƙaramin kyau ya yi mata ba.Ta dubi Sumayyah da dukkanin damuwa ya bayyana akan fuskarta ta ce, "Sumy lafiya,daga wajen Baba ki ke halan?" Sumayyah ta jinjina kai ta ce, "Don Allah Yaya Raudah ki bani aron dubu ɗaya idan na samu kuɗin zan mayar miki,tunda nima na ɗan fara sana'ar soya aya da tsami gayen nan zan dinga shiga dashi skull ɗin ina jarabawa." Raudah ta jinjina kai ta ce, "Ga jakata can a ɗaki ki ɗauki dubun da ta rage a ciki." Daga haka ta fito ta nufi bakin kitchen da Umma ke ciki tana ƙarisa aikin safe da ita Raudan ce ta fara,ganin zata yi latti ne ya sanya ta bar Umma da ƙarisa dama kunun tsamiyan da suka fi shan sa da safe. "Umma na fito zamu wuce kada muyi latti,a saka min fanken a leda na ci a can kawai." Umman ta ɗaga idanunta ta kalli Raudah tana jin ƙarin ƙaunarta mai yawa a cikin zuciyarta,ta ce cikin sanyinta, "To shikenan Raudah,amma da kin sha kunun koda rabin kofi ne da zafinsa." Raudah ta saki murmushi ta ce, "To Umma bari na gaida Baba na fito." Daga haka ta nufi ɗakin Baban nasu ta doka sallama daga bakin ƙofar,ya amsa tare da bata izinin shiga idanunsa akan ƙofar shigowa ɗakin. "Baba ina kwana,dafatan ka tashi lafiya,zamu wuce makaranta." Baba Mai Itace ya zubawa Raudah idanu wani abu mai ƙarfi game da ita na kewaye zuciyarsa.Maganganun Anty Amarya ne suka shiga dawo masa yana jin wani irin matsanancin tashin hankali na riskansa,ya sake kafeta da idanunsa kafin ya soma faɗin, "To Raudah Allah ya tsare,ku maida hankali ga abinda ya kai ku banda sakarci ko sakarwa samari da marasa tsoron Allahn Mallamanku fuska,ki ji tsoron Allah wajen kare mutuncinki Raudah kin ji ko?" Raudah da kalamansa a yau suka taɓa zuciyarta,domin bai taɓa furta mata makamancinsu ba sai a yau ɗin.Ta

Please Login or Register in order to submit comment