Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya aikata na keta alfarmar ƴaƴan wasu da ya yi a baya,duk da cewa a yanzu tana da tabbacin ya daina ya kuma yi tuba irin wanda ake so.

Raudah ita ce ta fara miƙewa ganin shida har da rabi ta shige ɗaki,ta bar Umma da Sumayyah zasu kwashe tuwan tunda already akwai miyan kuka da zasu yi amfani dashi cikin freezer.Da yake Umman na da madaidaicin freezer da take sana'ar sayar dasu ruwa da yin su zoɓo da ƙanƙarar kuka,sosai take samun alkhairy da sana'ar sabida suna kusa da wata babban makarantar primary na gwamnati ne da ke nan cikin jushin.Baya ga sana'ar sayar da su ruwa da ƙanƙara tana sayar da kayan ƙulle-ƙulle irin su kuka,kuɓewa da sauran kayayyaki na yau da kullum na girki.Sosai kuma tayi suna a sayar dasu mangyaɗa da su omon wanki har ma da sabulai,duk tsukin unguwar ita ce tayi fice a fannin waɗannan sana'o'in.Tana kuma jan zarenta sosai, domin Allah ya dafa mata ciniki kota'ina take samu.Hakan ne kuma ya sake jefa ƙiyayyarta a zuciyar kishiyarta Anty Amarya,da kuma kishiyar saurin da aka haɗe mata kai da ita suka zama tamkar su uku ne mijinsu guda sabida yadda suke kishi da ita.Ba kowa bace kuma sai Inna Karimatu da ke ji tamkar ta buɗe idanu ta ga cewa babu Umma a cikin gidan, sabida yadda take jin tsanarta da yin hassada ga nasibin da Allah ya yi mata a harkar neman na kanta take kuma samun buɗi da rufin asirin da babu macen da ke da sana'aryi mai ƙarfi a cikinsu irin ta......✍🏻
[10/4, 8:49 PM] Aysha Dansabo😍: 📱 *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo*

*Paid book 08167768704*

*Free page*

*Chapter 4*

Suna zaune suna cin abincin dare bayan sallar isha'i suka jiyo sallamar Hajiya Kakah ta shigo sasan nasu,Umma ce ta ɗaga murya ta amsa sallamar tare da yi mata barka da shigowa.Maimakon su ga ta fara yowa ɗakin Umman sai suka jiyo muryarta a bakin ƙofar ɗakin Anty Amarya tana rafsa sallama,Raudah ta dubi Sumayyah da ke kai loman tuwa baka ta ce, "Kin ji tsohuwar can bama nan za ta fara yowa ba, ikon Allah!" Umma tayi saurin hararar Raudah ta ce, "Raudah ki fita idanuna wallahi! Wai ke komai ne aka yi da bai miki ba sai kin tanka? Da nan da can ai duk ɗaya ne,tunda dukkanmu suna ɗaya muke amsawa na surukanta." Raudah ta ɗan zumɓure baki ta ce, "Umma ke dai kawai baki son a faɗi laifin Kakah da Baba idan sun kauce." Umma ta sake jefa mata harara ta ce, "Eh bana so tunda dukkansu babu abokin wasanki a ciki." Raudah bata kuma magana ba ta maida hankali akan cin soyayyan kifin da Gwaggo Salamatu ta aiko Suhailah dashi ta kowa mata,ita Suhailan ma tuni tayi bacci a cinyar Umma bayan gama cin tuwan da tayi.

"Salamu alaikum masu ɗaki." Muryar Hajja Kakah ya doki kunnuwarsu Raudah.Sumayyah ta amsa sallamar tana faɗin, "Sannu da ƙarisowa Hajja Kakah,ko in fito in kamaki ne na san jikin tsufa." Hajja Kakah ta ɗaga labulen ɗakin Umma ta shigo tana faɗin, "Wane ke ƴar nema,ai ni nafi ƙarfin a kamani da ƙwarina nake ras in gaya miki." Umma ta gaida Hajjah Kakah cike da ladabi,ita kuma ta amsa tana kallon Raudah da tayi kicin-kicin da fuska ita a dole fishi take da Kakan da bata je ta dubata a asibiti ba.Hajjah Kakah ta ƙanƙance idanu ta ce, "To ke kuma mai jiki har yanzu babu lafiyan ne ki ke wannan cika da batsewar,ko kodai tsiwar ne ya tashi za a min fitsaran da aka saba?" Raudah ta sake tsuke fuska ta gaida Hajjah Kakan a gajarce,ita kuma ta amsa tana faɗin, "Ya jikin naki Raudah? Allah ƙaro afuwa,ban je na dubaki a asibiti ba nima atini na dinga yi a kwana biyun shi ya sanya,sannu kin ji ko." Raudah ta ce a shagwaɓe, "Hajjah Kakah kenan,jiki na warware ai,Allah ƙara mana lafiya amma dai a dinga kwatanta adalci tunda dai dukkaninmu jininki ne." Raudah ta kai ƙarshen kalamanta tana ƙin duban side ɗin da Umma take,domin ta gama ji a jikinta harara Umman ke zabgo mata.Hajjah Kakah ta miƙe idanunta akan Raudah ta ce, "Ai dama idan har na fita baki nema zagina ba sai an canza miki suna Raudatu,to na gode gara da kika min tukuici da waɗannan kalaman, ladan tasowa na dubaki,kuma gobe da safe ki sani ke ce za ki cika min robobin tara ruwana da wanke mini bayi." Raudah tayi saurin faɗin, "Wallahi Hajjah Kakah bani da wannan ƙarfin,daga fitowata daga asibiti abin babu ko tausayi?Allah ba zan iya ba gara ma ki nema mai miki." Hajjah Kaka ta fice tana faɗin, "Idan baki yi ba sai uwarki ta fansheki tunda a gabanta ki ke min fitsara ba za ta iya gwagwgwaɓe bakin tsiwa da fitsarar taki ba." Umma kaman jira take Hajjah Kakah ta fita ta dirarwa Raudah da faɗa kaman za ta kai mata duka,Raudah ta dinga bata haƙuri tana faɗin ta daina,ba za ta sake kula Hajjah Kakah ba.Umma ta ce cikin ɓacin rai, "Ki daina janyo mini ɓacin rai Raudah,bana son wannan tsiwar taki da rashin kama baki." Raudah ta jinjina kai ta ce, "Amma Umma kin san idan ba a shiga gonata ba magana ma wahala take mini ko,kuma ita Hajjah Kakah da duk wanda kika ga na daina raga mawa a gidan nan to wallahi hakan ne maganinsu,domin idan mutum yana nuna musu shi sakarai ne sai ayi ta taka shi ana mayar dashi banza." Umma ta jinjina kai tana sake ayyanawa a zuciyarta cewa,Raudah ba za ta canza ba,ita haka halinta yake na rashin barin abu.Amma kuma miskilace ta ƙarshe idan ba ta so magana ko shiga shirgin kowa a gidan ba,sannan bata da rashin kunya da raina babba sai wanda ya zubda girman nasa.

Ƙarfe tara da rabi suka ji shigowan Baba Mai Itace sasan,bai nemi inda suke ba kamar ko yaushe idan Anty Amarya ne dashi.Kansa tsaye turakarsa ya nufa bai ko yi tunanin ya sake duba ko ya jikin Raudah yake ba,shigansa bada jimawa ba suka jiyo sallamar Maimunatu.Da alamu tun fitar da tayi da yamma sai yanzu take shigowa gidan,Raudah da Sumayyah suka haɗa idanu dukkaninsu abin na musu nauyi da ciwo a zuci.

Daga can ɗakin Baba Lawal ɗin kuwa,yana jiyo sallamar Maimunatu ya yi wuf ya fito yana tambayarta daga ina take? Kafin ta bashi amsa Anty Amarya ta fito daga ɗakinta tana watsa masa wani irin kallon raini.Cikin murya mai cike da isa da gadara ta ce, "Wuce ciki Maimus kin ji." Maimunan ta wucesa tayi cikin ɗakin Uwarta tana sakin wani malalacin murmushi.Baba Mai Ice ya dubi Anty Safiya rai a ɓace ya ce, "Yanzu Safiya irin rayuwar da kika ɗaurewa Maimuna gindi tayi kenan a cikin gidana?" Yadda ya yi tambayar da wani irin karyayyen sauti zai tabbatar maka da cewa baƙin ciki na matuƙar cinsa a zuci.Cikin nuna halin rashin damuwa ta dube shi kai tsaye ta ce, "Ƙwarai da gaske kalar rayuwar dana zaɓa mata kenan,ina sha nima a cikin irin kalar rayuwar ka ganni ka auroni? Ko kana tunanin barewa zata yi gudu ƴarta tayi rarrafe ne? Ko kuwa ka manta bashin da ka ɗauka na mutuncin ƴaƴan wasu yanzu ka ke gudun kar a fanshe a naka? Ka fita idanuna Lawal tun wuri,don wallahi yadda ta taso da farin jini babu wanda ya isa ya yi mata shamaki da jin daɗin rayuwa kamar yadda a baya kai ma ba a yi maka shamaki da morewa bariki ba." Ta kai ƙarshen maganarta tana kai hannu ta shafi gefen fuskarsa tare da sakin masa wani makirin murmushi.

Baba Lawal ya ja ƙafafunsa da suka yi mugun sanyi ya juya zuwa turakarsa,wani irin hajijiya na tsananin ɓacin rai ke ɗawainiya da zuciya da gangar jikinsa.Safiya ta zame masa masifa ta kuma zame masa ƙarfen ƙafa cikin rayuwarsa,ya sha yin nadamar aurenta a ƙasan ransa domin sai yanzu ne yake gane kuskuren da ya yi na auro ƴar bariki da suka san juna tun waje ya kawota cikin gidansa yana tunanin zata sauya.Duk iya yadda yake jin baƙin ciki na cinsa a zuci ya sani ba zai taɓa iya ɗaukar wani mataki akanta ita da ƴarta ba,domin ya sha gwada yin hakan amma sai ya ji ya kasa.Da zaran ya haɗa idanunsa dana Safiya ko Maimunatu da sunan ɗaukar mummunar mataki a kansu yake ji zuciyarsa ta tsinke ta raunata matuƙa,daga ƙarshema sai dai Safiyan ta ɓige da ci masa mutunci kamar yadda tayi a yanzu ɗin.

Dukkanin kalaman da Anty Amarya ta furta su ga Baba Mai Itace akan kunnuwar su Raudah da Ummansu ne,ba kuma yau ɗin ne karon farko da ta saba furta kalamai masu zafi a gareshi kamar yau ɗin ba.Shiyasa hakan bai zama baƙon abu a kunnuwarsu ba,sai dai a zukatansu suke jin tsananin zafi da ƙunar kalaman.Raudah ta miƙe zuciyarta na mata wani irin suya ta nufi ɗakinsu,ta samu bakin katifarsu ta zauna wasu zafafan hawaye suka shiga gangarowa daga cikin idanunta. "Meyasa Mahaifinsu ya fito a haka?" Raudah ta tambayi kanta da kanta tana ji a cikin zuciyarta cewa,tabbas basu yi sa'ar uba ba,domin dukkanin kalaman da Anty Amarya ke yi na sake jadda hakan a cikin zukatansu.Tunda suka taso suka yi wayo suke ji tana alaƙanta shi da kalmar zina da rayuwar bariki,wanda hakan ke nuna ya bibiyi matan banza a lokacin ƙuruciyarsa.Sun sha ji tana tunasar dashi a irin rayuwar da ya sameta ya aurota har ta zama uwar ƴaƴansa biyu,wanda idan har lissafinsu zai tafi daidai ne to hakan na nuna ita ma a karuwa ya aurota ba kintsatstsiya bace.Ta kai hannu ta share hawayenta tana ji zuciyarta na sake mata nauyi,wani irin abu mai tsananin ɗaci na cika maƙoshinta.Sumayyah ce ta shigo ta dubi ƴar uwarta da ke share hawayen tsananin takaicin kalar rayuwar da Babansu da Anty Amarya ke yi a cikin gidan,ta rakuɓe ita ma daga gefe guda tana faɗin, "Yaya Raudah Baba bai yi mana adalci ba sam!" Raudah ta ɗago idanunta ta sauke akan Sumayyah tausayin kansu da kansu na sake mamaye zuciyarta.Da wani irin sanyin murya ta ce, "Sumayyah na so ace Baba Auwalu ko Baba Adamu su ne suka kawo mu duniya,ko banza basu da abun faɗi da za a dinga bibiyan zuriyyansu da gori ana tunasar dasu zunubin da Ubansu ya kaita tun basu san kawunansu ba,ina jin ina ma Umma Ƙaddararta bata zaɓa mata miji irin Baba ba,domin tabbas aikin Ƙaddarace sabida kota'ina basu dace da juna ba." Raudah ta ƙarisa kalamanta tana share wasu zafafan hawayen da suka sakko daga cikin kwarmin idanunta.Sumayyah ta ja numfashi tare da sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ni ma nasha auna hakan a zuciyata Yaya Raudah,sai dai kawai muyi haƙuri tunda Rayuwarmu da irin kalar Ƙaddarar da ta zo kenan na samun uba kamar Baba." Haka suka dinga tattauna halin da suke ciki su da Ummansu a cikin gidan,har zuwa lokacin da bacci yazo suka yi shirin kwanciya suka kwanta bayan Raudah ta gama waya da masoyinta kuma Yayansu Yaya Deeku.

*WASHEGARI...*


Ƙarfe tara saura suka kammala dama koko da soya ƙosai,Umma ce tayi ƙosan Raudah kuma ta dama kokon ta juye shi a flask.Umman ta dubi Raudan ta ce, "Ɗakko wancan ƙaramar kular ki zubawa Hajiya Kakah ƙosan ki miƙa mata ɓangarenta tun da zafinsa." Raudah ta zumɓuri baki alamun bata so hakan ba,amma sanin bata isa cewa komi ba ya sanya ta ɗakko kular aka zubawa Hajjah Kakah ƙosan.Sai da ta koma ɗaki ta ɗakko ƙaramin hijab ta sanya sannan ta koma kitchen ta ɗauki kular ƙosan,tana fitowa sukai kaciɓus da Anty Amarya ta fito da ledar bread da kayan tea daga ɗakin Baban nasu.Raudah ta gaida ita a gajarce ta fito daga sasan tana jin ƙarin tsanar matar a cikin zuciyarta,sannan gefe guda tana jiyewa Babansu tsoron yadda zai tashi a gaban Ubangijinsa da shanyayyen ɓarin jiki sabida nuna fifiko da rashin adalci a tsakanin Iyalinsa,matuƙar bai tuba ya daidaita adalci a tsakaninsu ba.Har ta isa sasan Hajjah Kakah saƙa da warwara take yi akan lamarin Babansu da irin halakan da Anty Amarya ke sake jefashi a ciki,tayi sallama daga bakin ƙofar shiga ɗakin Hajjah Kakan tare da tsayawa jiran izinin shiga.Daga ciki Hajiya Kakah ta amsa sallamar tare da bai wa Raudah izinin shiga,ta shiga ta aje kular a kusa da Hajjah Kaka tana mai gaida ita cike da ladabi.Hajjah Kakah ta amsa da kulawa tana kallon Raudah ta ce, "Me kuka yi ne na karin safen yau?" Raudah ta nuna mata kular tana faɗin, "Buɗe ki gani mana Hajjah Kakah." Kafin Hajjah ta kuma magana sallamar Asiyan Baba Auwalu ya shiga kunnuwarsu,ba tare da ta jira an bata izini ba ta danno kanta cikin ɗakin tana faɗin, "Ƴar tsohuwa ina kwananki." Hajjah Kakah aka washe baki tana kallon kular da ke hannun Asiya ta ce, "Ƙalau na kwana Asiyatu,ya Iyayen naki suka tashi?" Asiya ta yatsine baki ta ce, "Ƙalau!" Ta waiwaya ta dubi Raudah da ta sha kunu ta ce, "Yayansu Suhailah ya jiki,ashe kin dawo gida daga asibitin?" Raudah ta ce, "Alhamdulillah na warware." Daga haka bata kuma magana ba sai kallonta da ta mayar kan Hajjah Kakah da ta buɗe ƙosan da ta kawo mata,ganin ƙosai yana turiri sai ta maida murfin kular ta rufe tana janyo kular da Asiya ta aje tayi gaba ta buɗe.Ƙamshin lafiyayyen doya da ƙwai ya bugi hancinansu daga ita har Raudah da ta jirayi ganin ikon Allah,nan da nan fara'a ya ƙaru akan fuskar Hajjah Kakah tana faɗin, "Ma Sha Allah! Auwalu ba dai sanin kan cima mai daɗi ba,me za a yi da wani gayan ƙosai babu mahaɗi babu komi?Raudatu ga doya nan ɗauki guda ki maida mugun yawu." Ta ƙare maganar tana duban Raudah da har ta miƙe tsaye,cike kuma da takaici ta dubi Hajjah tana girgiza kai ta ce, "Allah amfana Hajjah Kakah,ko zaki kawo kular ƙosan a mayar tunda kin sama abin ƙwalaman da yafi maiƙo da daraja?" Hajjah Kakah ta haɗe fuska ta ce, "Daɗina da ke ba dai iya yaɓa baƙar magana ba,to ba zan bayar ba ko almajirina na bai wa sadakarsa,dama kuma sadakan ƙosai falalane dashi musamman idan ka baɗe shi da yaji ka bayar da ɗuminsa duk sai ka wayi gari ka garari maƙiyi." Raudah ta saki murmushin takaici tana juyawa ta baro ɗakin Hajjah Kakah tare da ficewa daga sasan baki ɗaya.Har ta ɗauki hanyar sasansu sai kuma ta ga dacewar ta shiga wajen Gwaggo Salamtu su gaisa ta kuma yi mata godiyan kifin da ta aiko mata,sai ta karya kwana ta nufi sasan Baba Auwalu tana cigaba da takaicin halayyan Kakah na kwaɗayi da nuna fifiko ƙarara.Da sallama ta sanya kai cikin sasan Baba Auwalun,ta tadda Asiya da Hameedah zaune daga bakin barandar ɗakin Inna Hauwa suna karyawa.Plate ne a gabansu shaƙe da soyayyan doya mai ƙwai,sai kofunan shayi biyu a gabansu suna korawa dashi.Suka yiwa Raudah Bismillah lokacin da ta gittasu za ta wuce ɗakin Gwaggon Salamatun,bayan sun gaisa sa Inna Hauwa da ta fito daga madafinsu,sai ta girgiza tana faɗin, "Wallahi na gode a ƙoshe nake." Daga haka ta nufi bakin ƙofar Gwaggo Salamatu tayi sallama,daga ciki Gwaggo Salamatu ta amsa tana bata izinin shigowa.Ta shiga suka gaisa ta cidda ita tana cin zazzafan ƙosan da Umma ta aiko Suhailah dashi ta kawo mata,sanin cewa tana son ƙosai sosai da safe.Daga gefe guda kuma soyayyan dankalin hausa ne da egg,tayi masa haɗin sauce sai ƙamshi yake.Dukkanin sasunan uku babu wacce ke girkin haɗaka da kishiya,tun asali kowa girkinsa yake yi daban sai dai a raba kuɗin cefane a bai wa kowacce.Shiyasa kowa gashin kansa yake ci babu ruwansa da ɗan uwansa,mai ƙarfin sana'a ma sai dai ta ƙara ƙawata abincinta tare da cin duk abinda tayi ra'ayi ita da mai gidanta idan ranan kwananta ne.Juyin duniya Gwaggo Salamatu tayi akan Raudah ta ɗauki dankalin ta ci amma ta ce ta ƙoshi,haka ta haƙura ta ƙyaleta sanin halin Raudah na kafiya.Ta fito daga ɗakin Gwaggon kenan za ta fita daga sasan Baba Auwalu ya fito daga turakarsa,ta gaidashi cike da ladabi ya yi mata ya ƙarfin jiki? Ta amsa a sanyaye tana jin wani abu mai ciwo na danne zuciyarta. "Dama duk sun san bata da lafiya har ta kwanta asibiti amma babu wanda ya yi kara ya leƙa ya dubota?" Raudah ta tambayi kanta tana sake jin ciwon wannan rashin zumunci da rashin haɗin kan na ahalin Hajjah Kakah."A ce ƴar ɗan uwanka uwa ɗaya uba ɗaya ta kwanta asibiti kuma kuna rayuwa ne a muhalli guda,amma a rasa wanda zai yi kara ya je ya duba maka ƴa? Anya wannan rayuwa da suka ɗaukarwa kansu mai bulle musu ce su da ahalinsu baki ɗaya? " Raudah ta sake tambayan kanta tana tunasar da kanta cewa,ai shima kankat ɗin da ya kawota duniya ta manta ne bai je ba? Sai tayo gaba ta fito daga sasan tana jin cewa tabbas akwai gyara a cikin rayuwar ahalin Hajjah Kakah,kuma babu wacce ke da laifi sama da ita domin ita ce tushen komi.

Ta fito kenan daga sasan Baba Auwalun ta ji ƙaran shigowar mota cikin ƙaton filin compound ɗin nasu,wanda rabinsa kaf tsibin Itace ne na Babansu a jirge.Wasu an faskara ba a kai ga kasasu ba,wasu kuma an ware su dami-dami alamun na ƴan sari ne zasu zo su kwashe abin su.Wata baƙar golf ta hango ta shigo cikin filin wajen ta tsaya,sai ta ɗan ja ta tsaya tana son ganin wasu baƙi ne suka yi da safe haka? Idanunta ya sauka akan baƙin matashin da ya fiddo jikinsa daga cikin motar,dogo ne sosai ma'abocin kyawu daidai misali.Sanye yake cikin ƙananun kaya red da suka amsa jikinsa tare da fiddo ƙuruciyarsa na matashi mai ganiyar cin lokacinsa,daga ɗaya ɓarin ma ƙofar ta buɗe,wani matashin ya futo mai hasken fatar da bamai yawa ba.Bashi da tsayi kamar wancan baƙin na farkon,shi kuma yana sanye cikin farar shadda da ya yi masa mugun kyau.Take wani irin murmushi ya ƙwacewa Raudah,ta maida idanunta akan baƙin matashin tana sake gano zallar kyawun da ya ƙaro daga nesa.Cikin nutsuwa ta juya ta ɗauki hanyar shigewa ɓangarensu domin bata da buƙatar wani ya hangota ya tsaida ita a cikinsu,shiyasa cikin sauri ta shige sasansu zuciyarta cike da murnar dawowan zaratan Yayun nasu guda biyu Yaya Abubakar da Yaya Usman..........✍🏻
[10/6, 8:52 PM] Aysha Dansabo😍: 📱 *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo*

*Paid book 08167768704*

*Free page*

*Chapter 5*

"Ma Sha Allah! Allah ya sanya albarka a cikin iliminku,Ubangiji yasa an yi wa yawan rai ne Sadeeku da Usmanu,Allah kuma ya kawo aikin yi ya ƙarawa sana'ar ɗinkinku da nemanku albarka.Madallah! Madallah!! Da ganin wannan rana da kuka amso sakamakon ku mai kyawun gani." Baba Adamu ne zaune daga ƙasan shimfiɗaɗɗen ledar tsakar ɗakinsa yana jero waɗannan addu'o'in cike da farin ciki.Abubakar da Usman tare da Inna Karimatu ne zaune kewaye dashi fuskarsu ɗauke da fara'a,suka amsa addu'ar Baban nasu cike da farin ciki.Inna Karimatu da kanta ya sake girma ya fashe da tarin alfaharin kammala deegree ɗinsu,sai ta dubi Abubakar tana faɗin, "Yanzu yaushe za a fara turaku bautar ƙasar kenan?" Yaya Sadeeq ya dubeta da walwala ya ce, "Muna saka rai mu tafi a first batch In Sha Allah!" Ta jinjina kai tana sake faɗin, "To Allah yasa,sai batun cigaba da aikin ɗinkin naku,za ku cigaba a Kadunan ne kuna dawowa duk sati kuna dubamu ko kuwa dawowa za ku baki ɗaya ku tare a garin nan da sam babu cigaba a cikinsa sai ƴan hassada?" Yaya Sadeeq ya murmusa yana sake shiga mamakin yadda halayyar Innarsu sam basa sauya ya ce, "Muna can In Sha Allah,ai ba za mu iya rabuwa da Ubangidanmu ba idan har ba wani ƙwaƙwƙwaran aiki ne ya samu gare mu ba,domin wannan sana'ar ita ce mu Inna,mun samu rufin asirin da ba zai ƙidayu ba da ita." Baba Adamu ya jinjina kai ya ce, "Tabbas haka yake,zamanku a can ɗin zaifi kafin ku tafi bautar ƙasar,zama anan Zaria ba zai yiwu muku ba alhali ga inda kuka fi samun rufin asiri sosai." Wannan karon Yaya Usman ne ya yi magana ta hanyar faɗin, "Haka ne Baba,Allah dai ya cigaba da rufa asiri,dama akwai maganar da nake so in sanar daku." Ya ɗan dakata yana kallon fuskar Inna Karima da ta zubo masa idanu.Baba Adamu ya jinjina kai ya ce, "Faɗi maganarka muna sauraronka Usmanu." Yaya Usman ya gyara zama ya fara da faɗin, "Baba dama akwai Yarinyar da nake nema ne a can Unguwar Kawo Kaduna,to Iyayenta sun matsa da in tura magabatana ayi magana koda kuwa ba za a yi auren nan kusa ba, ya zamana dai manya sun shiga cikin maganar." Ya sake dakatawa yana kallon fuskokin Iyayen nasa biyu domin ganin a wani yanayi suke amsar maganar tasa? Inna Karimatu tayi zaraf ta ce,"Gidan waye a can ɗin?Ina nufin wane ne Ubanta,shin akwai maiƙo ko babu? Domin ba zai yiwu ka nemo ƴar da ba za ka ƙaru da Iyayenta ba sai dai kai su yi ta tatse min kai da ɗan abinda ka ke rorowa." Da wani firgici da zallar mamaki Yaya Usman ya dubi Mahaifiyarsu maganganunta na sake kaɗa zuciyarsa,cikin sanyin murya da sadda kai ƙasa ya ce, "Inna Babanta ma'aikacin gwamnati ne, suna da rufin asiri daidai gwargwado,kuma Inna ai ba gidan maiƙo ake dubawa ba,gidan mutunci da tarbiya ake dubi masu nasaba mai kyau." Inna Karimatu ta taɓe baki ta ce, "Haka ne kam,to ammafa kasani rayuwa tayi sauyawar da babu mai son ya raɓi talauci ko jajibo ma kansa ƴar gidan mataulata,wacce komi suka zo suka samu suke handamansa,don haka gara dai kusan ina ne zaku ɗakko aure ehe!" Baba Adamu ne ya riga yin magana wannan karon ta hanyar faɗin, "Kin gama Karimatu?" Inna Karima ta jinjina kai tana wani harare-harare,Baba Adamu ya girgiza kai yana maida dubansa ga Yaya Usman ya ce, "Usmanu ka kwantar da hankalinka,matuƙar dai kuna son junanku kai da Yarinyar to babu matsala,zan sanya a bincika min su wane ne Iyayenta kafin a tura a nemo maka izinin fara zuwa gidansu,kai kuma Abubakar a wani babi ka ke akan zancen aje Iyalin?" Yaya Sadeeq ya dubi Baba Adamu yana yin ƙasa da kansa gami da kwantar da murya ya ce, "Baba ni Raudan Baba Mai Itace ita ce zaɓina, domin ita zuciyata ta jima tana ƙauna har ma mun fara fahimtar juna ni da ita." Ya kai ƙarshen kalamansa yana kallon yadda murmushi mai faɗi ya bayyana a fuskar Mahaifinsa.Sai dai kafin Baba Adamu ya ce komi sai ganin Inna Karimatu suka yi a gaban Yaya Sadeeq,bata kuma jira komi ba ta sanya hannu ta ɗauke shi da mari.Cikin wani irin kakkausar murya take faɗin, "Ƙarya kake yi Sadeeku! Wallahi baka isa ka tozartani ba,ka rasa ƴar wacce zaka so sai ƴar maƙiyiyata da bani da wanda na tsana a duniya sama da uwarta? To bari ka ji tun wuri ma ka iya bakinki kada na sake jin ka furta kalmar so ka jingina shi da jinin Halimatu matuƙar nonona ka tsotsa ka rayu a duniya!" Ta kai ƙarshen kalamanta tana wani irin huci tamkar kumurcin maciji.Baba Adamu ya daka mata wani gigitaccen tsawa tare da nunata da yatsa ya ce, "Karimatu a gabana? A gabana ki ke faɗin kar ya sake danganta kalmar so ga jinin ɗan uwana ciki guda? To bari kiji matuƙar Raudah tana son sa bata da miji sai shi,sai dai duk abinda zaki yi kiyi,ki daina ganin ina zuba miki ido kuna yadda kuka ga dama ke da kishiyar Halimatu ki ɗauka cewa nima kin mallakeni ne,wallahi baki yi wannan isar ba Karimatu, kar nake kallonki zan kuma tabbatar miki da cewa Adamu ba sakarai bane kamar yadda ita ta mayar da Yaya Lawal ɗin sauna." Yana kai ƙarshen kalamansa ya dubi Ƴaƴan nasa ya ce su tashi su basu waje.Kaman jira Inna Karimatu take yi su fice ta sakar masa wani gigitaccen kuka tana faɗin, "Me kake nufi Baban Sadeeq? Wallahi matuƙar ni nayi

Please Login or Register in order to submit comment