Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ce, "Idan an sallameki kar ki tafi gida Raudah,kiyi ta zama har sai Baba Mai Itace ya zo ya ce miki sannu akan gadon asibiti kin ji ko?" Raudah jin maganar da Umma tayi a fusace ya tabbatar mata da cewa ranta ya ɓaci matuƙa da gaske,hakan ya sanyata sake shagwaɓe murya ta ce, "Kiyi haƙuri Umma ni ba haka nake nufi ba,abin ne kawai ya yi mini ciwo ace kwana biyu ina gadon asibiti bai zo ya dubani ba,bare har ya sauke hakkinsa na biyan kuɗin asibiti,duka hidiman ke ce kika yi kuma ba don ya rasa ba sai don kawai mune bai damu da mu ba bare ya damu da lafiyarmu." Raudah ta kai ƙarshen maganar murya na rawa hawaye na biyo fuskarta.Umma ta miƙe tsam ta fice daga ɗakin,domin idan ta cigaba da zama kusa da Raudah tabbas sai ta bige bakinta tunda ita mita ne da ita da shegiyar kafiyar tsiya.Sumayyah ce ta dubi Raudah bayan fitar Umman ta ce, "Yaya Raudah kiyi haƙuri ki bar maganar tunda Umma ta nuna bata so ana yi,amma ni kaina abinda Baba Ya yi ya min ciwo matuƙa ya kuma bani mamaki,domin baki ga yadda yake kashe musu kuɗi ba,babu maganin da bai siya ba duk yabi ya hana kansa sukuni." Rauda ta jinjina kai ta ce, "Babu komi Sumayyah Allah na nan,shi muke roƙa ya zama gatan mu ba shi ba,Allah zai yi mana sakayyah idan har shiga tsakaninmu da shi aka yi." Ta kai ƙarshen kalamanta ƙiyayyar Anty Amarya na sake yawa a cikin zuciyarta.
Sumayyah ta ɗauki farantin plastic roba ta zubawa Raudah faten ta miƙa mata tana faɗin, "Gashi Yaya Raudah,ki daure ki cinye koda wannan ɗin ne." Babu musu Raudah ta amsa plate ɗin tana fara cin faten shinkafan.Suna yi suna tattauna matsalolin gidansu da irin ƙalubalen da suke fuskanta a cikinsa,a haka Umma ta turo ƙofar ta shigo bakinta ɗauke da sallama.Sumayyah ta amsa sallamar suna mai bin Umma da kallo,tayi kamar bata gansu ba ta isa wajen da ta gama haɗa komi nasu tana faɗin, "Idan ta gama ki maida komi gida zamu wuce,ya rubuta maganin sai ki je ki sayo a can bakin titin lemu,mu zamu rigaki wucewa gida." Sumayyah da ta gane da ita Umman ke yi,sai ta amsa ta da faɗin, "To Umma,har anyi sallaman kenan?" Umma ta jinjina kai ta ce, "Anyi Sumayyah,na kuma biya kuɗin komi sai fatan Allah ƙara rufa asiri." Suka amsa tare da Raudah a tare,kafin Raudah ta dubi Umma tana bata haƙuri.Umman ta waiwaya ta dubeta tana faɗin, "Matuƙar ba zaki daina yawan mita da wannan nacin maganar ba Raudah,to mun dinga samun saɓani dake kenan domin bana son mutum mai naci da yawan mita." Raudah tayi murmushi tana jinjina girman ƙaunar da Umman ke wa Baba Mai Itace,domin idan ka ji tana faɗa akan yawan mitanta to tabbas ta biyo ta kansa ne akan irin rashin adalcin da ba yayi akan su.

Sumayyah ita ce ta taro musu napep har bakin asibitin,ta shiga ta taya Umma fiddo kayansu zuwa napep ɗin.Sai da ta ga tashin napep ɗin nasu sannan ita kuma ta nufi hanyar zuwa wani pharmacy a lemu domin ta nemo maganin da aka rubutawa Raudah.

*JUSHI*

Mai napep ɗin ya diresu a ƙofar gidan Musa Mai Itace,Umma ta fiddo kuɗinsa ta bashi sannan suka fito daga cikin napep ɗin.Da kanta ta fiddo kayansu tana aje su daga ƙasa,kafin ta waiwaya ko za ta samu Yaron da zai taya su da shiga da kayan zuwa ciki.

Cikin sa a sai ga wani Yaro ɗan maƙwaftansu ya zo zai gitta,sai ta kiraye shi tana nuna masa kayan da zai taya su dashi zuwa ciki.
Cikin nutsuwa a hankali Raudah ke takawa biye da bayan Ummansu zuwa ciki,suka ɗauki hanyar sasansu tana jin wani abu mai nauyi na taɓa zuciyarta akan irin rayuwar da ahalin gidan keyi na babu ruwan wani da wani.Kwanakinta biyu kenan a asibiti babu lafiya amma ace an rasa waɗanda zasu rufa mayafi su je suyi mata sannu cikin matan ƙannin Ubanta,banda Gwaggo Salamatu da ke da jituwa da Ummansu babu wata mace da ko a waya ta kira ta ce ashe suna asibiti Allah shi sauƙe.Har suka danna kai cikin sasan nasu zuciyar Raudah ƙuna take yi mata,ba kuma laifin kowa tafi gani ba sai na Hajiya Kakah,wacce ciki har da ita karan kanta bata je ta dubota a asibitin ba.Kuma tayi imani da cikinsu Asiyan Baba Auwalu ne da tayi mayawa biyu ko uku ma cikin kwanaki biyun,amma da yake su ba ƴaƴan so bane gashi har ta kwanta ta fito bata ko leƙa ta ce sannu ba.

Umma ce ta kwaɗa sallama a tsakar sasan nasu,daga ciki muryar Maimunatu ta amsa sallamar.Suka wuce zuwa bakin barandarsu suka buɗe ƙofar ɗakin Umman suka shige,ko aje mayafi basu kai ga yi ba sai ga muryar Baba Mai Itace daga bakin ƙofar ɗakin yana faɗin, "Halimatu kun dawo? Sannunku da zuwa ya jikin Raudatun?" Wani irin takaici da baƙin ciki ya taso ya lulluɓe zuciyar Umma,ta dake cikin aro jarumta da danne ɓacin ranta ta bashi amsa da faɗin, "Jiki Alhamdulillah! Ta sama sauƙi za a jaraba dafa mata ƴan ganyayyaki ne ta haɗa dasu tunda na asibitin baya yi." Ya ƙarisa shigowa cikin ɗakin yana sauke ganinsa akan Raudah da ko kaɗan bata yi niyyar dubansa ba ya ce, "Hakane ita ma Safiya ɗazu na saka Ashiru almajiri ya nemo ganyayyakin har Hajiya Kaka ta ɓararraka mata,sannu Raudah ya jikin naki?" Ya ƙare maganar idanunsa akan Raudah da zuwa lokacin ta kasa riƙe hawayen da suka cika idanunta.Bata ɗago ta kallesa ba ta ce, "Na ji sauƙi Baba,dafatan mun yini lafiya ya jikin Anty Amaryan?" Da wani irin karsashi ya amsa da faɗin, "Ta samu sauƙi,bari na je na ɗebo miki maganin da Hajiya ta dafa kema sai ki duƙa sha ko?" Raudah ta jinjina kai ba tare da ta iya sake cewa komi ba ta lalubi ɗakinsu ta shige ciki.Umma ta rakata da ido tana sake danne wani azababben ɓacin rai da ke taso mata,Baban nasu ya miƙe yana duban Umman ya ce, "Halimatu kiyi haƙuri ban samu na leƙo ba har aka sallameku,nawa ne aka caza kuɗin maganin sai na fara rage miki tunda kuɗin hannuna duka dashi na biya kuɗin maganin Safiya." Umma ta saka idanunta da kyau cikin nasa tayi masa wani irin duba da ke sanyaya jiki da zuciyarsa a duk sanda ta jefeshi dashi,da wani irin karyayyen sauti ta ce, "Karka damu Baban Raudah,bama sai ka rage mini ko sisi ba,don na yiwa Raudah hidiman neman lafiya da aljihuna ai ban iya asara ba tunda zafin naƙudar da nasha nata bada wani muka raba shi ba,fata dai kullum shi ne Allah ya cigaba da buɗawa Halima hanyoyin samun da zata cigaba da ɗaukar ɗawainiyan ƴaƴanta babu gazawa." Tana kai wa ƙarshe ta shige ɗaya ɗakin da yake mallakinta ne tunda 2 bedroom ne,sai ta ɗauki ɗaya ta bar wa ƴan matan nata guda ya zama mallakinsu.Baba Lawal jikinsa ya yi mugun sanyi da kalaman Umma,domin ya sani maganganu ne masu zafi ta dunƙulasu cikin takaitattun kalmomi ta gaya masa.Jiki a saluɓe ya juya ya fice daga ɗakin,yana ji sam bashi da sauran kuzarin amso maganin da ya yi niyya ya kawowa Raudan.

Koda Sumayyah ta dawo siyo maganin ta samu fuskar Umman sam babu walwala,domin da gaske maganganun Babansu ya ɓata ranta da har zai iya kallon idanunta ya gaya mata akan Safiya kaɗai zai iya ƙarar da kuɗinsa wajen nema mata lafiya amma ƴar cikinsa ko oho! Ya manta dukkaninsu suna da girman hakki a kansa,amma shi bai damu da hakan ba burinsa kawai ya fifita Safiya a ko yaushe ita da ƴaƴanta.

Dukkaninsu kwanciya suka yi sukai bacci domin kwana biyu ba wani isasshen bacci suka samu a asibitin ba,sai can yamma sakaliya suka tashi suka sallaci sallan la'asar.Raudah na idarwa Sumayyah ta kai mata ruwan wanka banɗaki,ta fito ɗaure da zani ɗaurin ƙirji da ƙaramin hijab ta nufi banɗakin da ke gefen ɗakinsu wanda shi ne mallakinsu da shi suke amfani.Ita ma Anty Amarya nasu daga gefen ɗakinta ta ɓangaren hagu,don haka basu haɗaka da banɗaki kwata-kwata sai dai kitchen kaɗai suke da haɗaka da shi.

A wanke bayin yake tsaf dashi,hakan ya sanya Raudah ta yo wankan ta fito cike da karsashi tana sake jin ƙwarin jikinta.Tana fitowa Anty Amarya da Inna Karimatu na fitowa daga ɗakin Anty Amaryan,tayi musu kallo ɗaya tana ɗauke kai tare da gaishesu a ladabce kamar yadda ta saba.Inna Karimatu ta gyatsine fuska ta amsa a gajarce tana ɗorawa da faɗin, "Ya jikin naki,Allah ƙara afuwa ko." Ita ma Anty Amarya ta yiwa Raudah ya jiki a lalace, suna yin gaba zuwa zauren fita daga sasan.Raudah ta shige ɗaki tana jin zafinsu sosai a cikin zuciyarta,idan da sabo yaci ace ta saba da halayyar waɗannan mutanen guda biyu,amma sai dai ta kasa sabawan.Musamman ƙiyayyarta da kullum take hangowa cikin idanun Inna Karimatu abu ne da ke kiɗima zuciyarta,domin tana matuƙar jin tsoron kada ƙiyayyar ya shafi irin soyayyar da gudan jininta ke mata.Jikinta a sanyaye sosai ta shafa mai tare da zura wata doguwar riga mara nauyi ta shan iska,sosai tayi kyau fuskarta tayi fayau irin na wanda ya tashi daga jinya.Ta rame sosai a fuska amma jikinnan na nan a cike luwai-luwai babu rama,dama kuma da wuya kaga tayi ciwon da ramarta zai nuna a jiki sai dai ya nuna a fuskarta kaɗai........✍🏻
[10/4, 8:46 PM] Aysha Dansabo😍: 📱 *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo*

*Paid book 08167768704*

*Free page*

*Chapter 3*

Raudah na zaune a tsakar ɗakinsu da ke shimfiɗe da kafet ja da ya fara tsufa,amma irin guga da gyaran da yake samu ya sanya zaka gansa fes babu ƙura bare datti sam a kansa.Akwai setin kujeru zagaye da falon masu rangwamen tsada,waɗanda suma yadinsu ya fara nuna alamun tsufa.Daga ƙasan kafet ɗin take zaune wayanta riƙe a hannunta samfurin android mai matsaikacin kuɗi,wanda ta siya da kuɗin sana'o'in da take yi na hannu, na yin su cin-cin buns,alawar madarane,gullisuwa da aya mai suga.Sannan ta iya kitso sosai ana zuwa tana yi har ma a kirata gidajen masu hannu da shunin unguwar tayi musu su biya ta kuɗi mai tsoka,shiyasa take samun rufin asiri da kuma kuɗin yiwa kanta hidimar karatu idan Baban nasu bai ga damar saye ko biyamata kuɗin wasu abubuwan ba.Da yake ta kwana biyu ba lafiya bata kunna wayar ba,shiyasa tana kunna data wayar ta fara hucking alamun saƙonni sun yi yawa abin ka da wayar da ba wata babba can ba.Tilas ta goge whatsapp ɗin baki ɗaya ta sake ɗakko wata ta buɗe,hakan yasa wayar ta samu tsayawa saƙonni suka dinga shigowa na group-group da take ciki na skull da kuma na karatun novels da sauraron wa'azizzikan malaman addini na sunnah.Sannu a hankali take duba saƙonnin tana replaying wanda za ta iya,ta zo daidai kan lambar Yaya Sadeeq kamar yadda suke kiransa idanunta ya sauka akan saƙonsa.Ta buɗe ta karanta wani irin murmushi na kwanciya bisa kyakykyawar fuskarta,kalamaine na tsantsar soyayya da fatan samun sauƙi a gareta,sai kuma ƙorafin rufe wayarta da ta yi da biyo baya.Tana replying ɗinsa ta fahimci yana online,ko mintuna biyu ba a yi ba kuma sai ga kiran shi ya shigo mata.Ta ɗaga wayar cikin shagwaɓe muryar da ke sake susutashi,ta dinga amsa sannunsa a narke tana faman juya idanu tamkar yana a gabanta.A haka ta jiyo sallamar Zainab ƙanwarsa tare da shigowarta baki ɗaya kamar an jefo ta,sai Raudah ta ɗaga kai ta dubeta lokacin da Zee ɗin ke samun wajen zama bisa seater. "Raudah ya jiki,ashe an sallamoki? To Allah ya ƙara lafiya." Zainab ɗin ta furta hakan idanunta akan Raudah da gabaki ɗaya hankalinta ke kan wayar da take yi da Yaya Deeku tana sauraran tausasan kalamansa.Sai ta ɗagawa Zee ɗin hannu tana ɗan cire wayar daga kunninta kaɗan ta ce, "Ai nayi fishi Zainab,ace kwana biyu ina kwance babu wacce za ta iya wanke ƙafarta ta je dubani,ina nan Jushi ina cikin asibitin Jamawa? Allah ya bamu lafiya daɗin abin ciwo yasan makwancin kowa." Daga haka ta mayar da wayar kunni ta bar Zainab nayi mata wani irin duba.Cikin zallar fusata ta miƙe tsaye tana jifan Raudah da harara ta ce, "To sarkin iya tsiwa da baƙar magana,baki gode biyoki da nayi yanzu har ɗaka ina miki ya jiki ba har sai kin bini da fatan ciwo ko?" Raudah ita ma ta ɗago manyan idanunta ta sauke akan Zainab ɗin,wacce take baƙa mai kyawu da diri daidai misali.Cikin nuna ko oho ta ce, "Eh an yi miki!" Zainab da ta kasance tsarar Raudan ce,domin kuwa shekarunsu ɗaya tseran watanni biyu ne kacal a tsakaninsu,sai ta sake tsuke fuska ta ce, "Babu laifi kin yi da ƴar halak!" Daga haka ta juya ta fice daga ɗakin.Rauda ta rakata da harara tana jin zafi mai yawa a cikin zuciyarta na irin rashin haɗin kan da basu dashi a cikin ahalin gidansu.Umma ce ta fito daga ɗakinta tana duban Raudah da ta sauke waya daga kunni bayan kammala wayarta da Yaya Sadeeq ɗin,cikin tsare gida ta je fa mata tambaya da cewa, "Ke da waye ki ke magana a tsiwace Raudah?" Raudah ta narke fuska ta ce, "Zainab ce mana Umma,shigowa tayi gaida ni shi ne na salleta akan ƙin zuwa asibiti da basu yi ba." Umma ta ja ƙwafa ta ce, "Ki dai cigaba da nemo min magana Raudah,idan basu je asibiti sun dubaki ba ina sha dubunsu abokanan arziƙina da naki sun je ko? Hakan bai isheki ki godewa Allah ba har sai kinyi ƙorafi?" Raudah ta sake tsuke fuska ta ce, "Umma su da daban mutanen arziƙi daban,su ahalina ne da suka fi kowa kusanci dani,koda ace mutanen duniya duka sun halarci dubani su ɗin ne sukai saura dole abin ya yi mini ciwo,musamman idan na duba ƙarfin jini da zumuntar da ke tsakaninmu dasu,uwa uba ni da Zee da Aliya dukkaninmu tare muka taso,ya dace ace kanmu a haɗe yake duk abinda ya shafi ɗayanmu ɗaya zai ji a jikinsa, amma hakan sam bai samu ba sabida bambamci da nuna fifiko da tun fil azal ya yi katutu a gindin iyayensu mata da kuma Hajiya Kakah mai ɗaurewa abin gindin zama." Raudah ta dakata da kalamanta tana yin ƙasa da kanta sabida irin kallon da Umma ke aiko mata.Umma ta sake jan ƙwafa ba tare da ta ce komi ba tayi gaba ta fice daga falon,domin kuwa bata san me za ta ce ɗin ba tunda dukkanin kalaman Raudah su ne asalin gaskiyar da babu wani kwaskwarima da za a iya musu.Ita kanta rashin haɗin kan ahalin nasu nayi mata ciwo,musamman da ya zama su mata sunfi rinjaye a yanzu,mazan duka su uku ne kacal a cikin ƴan mata su tara da ke gidan.Ashe kuwa suna da buƙatar haɗin kai matuƙar ana so familyn ya ɗaga da kyau ya kuma samu cigaba irin yadda ake fata,domin kuwa babu familyn da zai cigaba babu haɗin kai da ƙarfafa zumunta a tsakanin juna.Musamman idan aka ce ƴaƴa mata sunfi yawa a ciki,sabida su ne ƙashin bayan da in suka riƙe zumunta tayi ƙarfi take ɗorewa,idan kuma suka bijire to cikin daƙiƙa za a iya wayan gari kan ahalin gidan ya tarwatse baki ɗaya.

Raudah ta bi bayan Umma da kallo tana sake shan alwashi a zuciyarta cewa ta gama yin shiru akan ire-iren waɗannan halin ko inkulan da ake nunawa,wanda yin shirun shi zaisa abin ya yi ta cigaba ana ƙullin juna a arai.Amma idan za a yi maka ka fito ka nuna abin ya yi maka zafi,to sai a dawo daidai,wanda ya yin idan zai gyara ya gyara in ma ba zai gyara ba ya dai san baka rufeshi ba ka faɗi abinda ke yi maka ciwo a zuci game dashi.Ta miƙe a hankali tana aje wayarta ta fito barandar ɗakin nasu inda Sumayyah ta shimfiɗa tabarma tana bitan littafan Islamiya kasancewar alhamis ce babu Islamiyar a yau,Sumayyan ta yiwa Raudah ya jiki tana jin daɗin yadda jikin ya yi mata ƙwarin da har za ta iya fitowa barandar ta zauna.Raudah ta amsa tana maida dubanta sashin da Umma ke shirin hura wutan gawayi daga wajen kitchen ɗin,ta dawo da dubanta kan Sumayyah ta ce, "Sumy Umman ce za ta yi girkin ke ba za ki yi ba?" Sumayyah ta murmusa ta ce, "Ita ta ce inyi zamana ita za ta yi,kinsan dai halin Umma dama bata faye son a karɓeta aikin girki ba tafi gane tayi da kanta." Cike da gamsuwa Rauda ta gyaɗa kai domin tabbas hakan ne,Umma bata son a taya ta girki sam.Duk aikin da za ka ɗauke mata ta yarda amma banda girki,tafi gane tayi da kanta sai dai su taya ta da gyaran kayan miya ko wani abin daban.Da yake mai zafin jini ce nan da nan ta hura gawayin ya kama,ta ɗaura ruwan tuwon dawan da shi take da sha'awa su ci da dare.Tana aikin suna jefa hira tsakaninta da ƴan matan nata biyu,cikin hakan Gwaggo Salamatu da Suhailah suka sanyo kansu cikin sasan bakinsu ɗauke da sallama.Raudah suka amsa da fara'a tana dire ganinta akan kyakykyawar autarsu Suhailah mai shekaru tara,wacce ta nufo wajanta direct tana faɗin, "Anty Raudah har kin warke dama?" Raudah ta saki murmushi tana janyo Suhailah jikinta ta ce, "Na warke autar Umma,hala unguwa ku ka je ke da Gwaggon taki?" Suhailah ta jinjina kai ta ce, "Kasuwa na rakata Anty Raudah." Raudah tayi murmushi tana gaida Gwaggo Salamatu da ke yi mata ya jiki,sannan ta maida dubanta kan Suhailah tana faɗin, "Lallai Suhailah ki ce kin sha na kasuwa shiyasa baki nemeni ba har muka dawo gida." Suhailah tayi dariya tana faɗin, "Na ji daɗi tunda kin warke,Gwaggo har ta siyo kifi za ta soya miki ta ce mai ciwo yana jin kwaɗayi idan ya samu sauƙi." Raudah tayi murmushi tana ƙin tanka maganar Suhailah sabida surutu ne da ita da rashin sirri irin na Yara,tunda girman jiki ne kawai gareta da shegen wayo.

Suna nan zaune a barandar Umma tare da Gwaggo Salamatu suna hira Anty Safiyyah ta fito daga ɗakinta,tayi musu kallo ɗaya ta watsar tana taku ɗai-ɗai ta nufi kitchen.Kamar Gwaggo Salamatu ba za ta tanka ta ba sai kuma ta ɗaga murya ta ce, "Safiya sannu da gida, ya ƙarfin jiki? To Allah ya ƙaro afuwa." Daga bakin ƙofar shiga kitchen ɗin Anty Safiyan ta ja ta tsaya, ta waiwayo ta zubawa Gwaggo Salamatu ƙananun idanunta da suka gama soyewa a bariki ta ce, "Jiki nayi garas sai godiya,tunda gashi da ƙarfina zan shiga madafi in yiwa rabin raina girki." Tana kawai ƙarshen ta saki malalacin dariya ta faɗa cikin madafin ranta fes! Gwaggo Salamtu ta jinjina kai tana mayar da dubanta kan Umma da ke talge ta ce, "Ummansu bari na koma ni ma girkin zan ɗaura,Raudah Allah ƙarfin jiki sai kin ga saƙo idan na kammala girki." Ta ƙare maganar tana maida dubanta kan Raudah,wacce ta maida hankali akan Suhailah dake faman yin game da wayarta da ta ɗakko daga ɗaki.Ta ɗago kai ta dubi Gwaggo Salamatu ta ce, "To Gwaggo na gode Allah bada lada." Daga haka Gwaggo Salamatu ta miƙe tana kallon Suhailah ta ce, "Auta ba za a bini mu koma mu yi girkin bane ?" Suhailah tayi saurin tashi tana faɗin, "Zani Gwaggo ba ni ce zan dafa miki taliyar ba ki ka ce." Umma suka saki dariya Raudah na faɗin, "Lallai Gwaggo yau babban girki za a yi tunda Suhailah ce mai dahuwar." Gwaggo Salamatu tayi dariya tana kama hannun Suhailah suka fice,sosai Yarinyar ta shaƙu da ita kamar yadda ita ma take jin Suhailan a ranta sosai.

"Momy! Momy!!" Muryar Maimunatu ke ƙwallawa maman nata kira tana fitowa daga ɗakin nasu duk a lokaci guda.Ta sauke ganinta akan su Raudah da ke zaune suna hiran sana'arta da take son gobe tayi abinda suka ƙare a ciki,cikin wani irin banzar murya ta ce da Raudah, "Yayar su Sumayyah ya jiki?" Raudah ta haɗe rai sosai tana amsata a taƙaice.Ko kaɗan bata sakarwa Maimunatu da take tsarar Sumayyah fuska,sabida yadda ko kaɗan bata da kunya ba ta ganin kowa da gashi sai Uwarta.Hakan ya sanya ita kuma ta kama girmanta a matsayinta na babba a sasan nasu baki ɗaya,sam bata ganin haƙoranta a waje da sunan murmushi ko dariya.Abinda ya janyo Maimunatun ke ɗan shakkarta kenan,sanin halin Raudah na rashin ɗaukar raini.Suka bi Maimunatun da kallo wacce duk kwanan duniya ninka bilicin ɗin da take yi take,ta sake wani irin ɗashewa da fari babu kyawun gani.Gabaki ɗaya ta ɓata kanta ta kuma canza halittar da Ubangiji ya halicce akai na baƙar fata,domin kuwa baƙace sosai ada kamar Momyn nata.Sai dai tana da kyawunta daidai gwargwado,amma bata godewa Allah ba gani take yi sai ta koma fara tamkar su Raudah sannan ita ma za a san tana da nata kyawun.Kuma Babansu na gani amma bai taɓa kwaɓa mata akan hakan ba,domin duk abinda zasu yi basa laifi a wajensa haka uwarsu ta ɗaurashi akan rashin ganin aibunta dana ƴaƴanta komin girman laifin da zasu yi kuwa.Ta riga ta mallakeshi ta wannan fannin sai abinda suke so shi suke yi a cikin gidan,ba kuma wanda iya isa ya ɗaga musu murya ko ƙanƙani.

Anty Amaryan ce ta fito daga kitchen ɗin tana aje ganinta akan Maimunatun,wacce ke sanye cikin wasu riga da skat na atamfa da suka matseta matuƙa da gaske.Duk wani albarkatu na jikinta ya gama bayyana,musamman saman ƙirjinta da tana rankwafawa rabinsu ne zasu bayyana a waje.Wani ɗan figigin mayafi ne ta rataya a saman kafaɗarta guda,sai ɗaya ɓarin kafaɗar rataye da wani ƙaramin hand bag.
"Kin fito Maimus?" Cewar Anty Amarya idanunta akan tilon ƴarta mace mafi soyuwa a cikin zuciyarta.Maimunatu tayi wani fari idanu tana duban cikin idanun Momyn nata ta ce, "Na fito Momy ya riga ya iso yana mota a waje,sai mun dawo me za a taho miki dashi?" Anty Amarya ta saci duban sashin da su Umma da ahalinta ke zaune,sannan ta maida dubanta kam Maimunatu tana ɗaga murya yadda zasu jiyota ta ce, "Irin kazar nan da ki ka taho dashi shekaranjiya nake so,ai mu dole mu wataya mu ji daɗi tunda kin kawo girma,Allah kuma ya zuba miki farin jinin masu hatiman nasara,ba irin su o'o da babu mashinshini ba,sai ɗaya da aka kama da ƙyar wanda ba a da tabbacin uwar za ta aminta a haɗa jini dashi." Ta kai ƙarshen kalamanta tana sakin ƙaramin shewa tare da shigewa cikin kitchen ɗin,ita kuma Maimunatu ta juya tana kama hanyar fita daga sasan nasu zuciyarta fes da samun lalatacciyar uwar da take barinta cin duniyarta da tsinke yadda take so.

"Allah ka shirya zuriyyanka,Ubangiji ka sanya mana hannu cikin tarbiyyan Yaran mu kar ka bar mu da wayo ko dabarar mu ya Allah!" Umma ta furta hakan a cikin zuciyarta tana jin wani abu mai girma na ratsata,domin ko kaɗan irin rayuwar da Maimunatu ta ɗakko yi a cikin gidan ba mai sha'awa ba ce.Amma kuma idan ta tuna karin maganan Bahaushe da kan ce " _Barewa bata gudu ɗanta ya yi rarrafe!_ " Sai ta sake godewa Allah da ya sanya ta fito daga gidan dattijai da suka san tarbiyya suka kuma tsare mutuncinsu.Amma kuma har ila yau zuciyarta kan tsinke ta shiga firgici mai tsanani idan ta tuna cewa shi ma fa Baba Lawal ɗin kansa ba baya bane,idan har za a raba zunubansa tare da ƴaƴansa ne tabbas tana da sauran fargaba da razani mai yawa a cikin zuciyarta har sai randa Allah ya nuna mata aurensu Raudah lafiya.Wani gumi ya tsatstsafo mata ta kai hannu ta sharceshi jikinta na sake yin sanyi matuƙa,cikin dabara da bai wa kai ƙwarin guiwa ta rufe talgen da ta gama domin ya dahu kafin ta kai ga tuƙesa.A hankali ta sauke ganinta akan Sumayyah da Raudah,ƙauna da kuma tausayinsu ya dinga shigarta tana sake yi musu addu'ar neman tsari da kariya daga sharrin wannan zamani da kuma na ibilisan samari mayaudara masu lalata ƴan matan mutane.Can ƙasan zuciyarta kuma tana sake roƙawa Mahaifinsu shiriya da yafiya akan zunuban da

Please Login or Register in order to submit comment