Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata waiwayan baya.Hakan ya sanya wani irin ƙaunarta mai tsanani a zukatan su Raudah da dukkanin ahalin gidan,tafi ƴar uwarta Gwaggo Murja kyauta da yawan alkhairy da hidimtawa ƴan uwa cikin ni'imar da Ubangiji ya yi mata.Duk da cewa a zahiri mijin Gwaggo Murja yafi mijinta arziƙi,ita ma kanta tafi Gwaggon Shatun samu domin tana manyan business da take juya manyan kuɗaɗe.

Raudah ta fara shanya kayan ɗaya bayan ɗaya,tana yi tana ɗan hutawa idan ta ji ta gaji.A haka ta cika igiyan farko har ta kawo ƙarshensa,ta zo daidai ƙarshen igiyan ta miƙa hannu za ta shanya wani skat ɗin kayanta ta fara jiyo muryar Anty Safeeyah da Maimumatu.Da yake saitin window ɗin uwar ɗakin Anty Safiyan ne daidai wajen da take tsayen,sai ya zamana tana jiyo muryoyin su Anty Safeeyan sosai sanda take faɗin, "Maza ki shaye wannan tsumin ki bani kofin,ke da kanki kika faɗi amfaninsa da irin rawan jiki da sumbatun da ya yi tayi miki,ai tsumin Maman Faridah duniya ne,ga aiki ga kuma magani riba biyu,ni dai burina ki dinga wankansa sosai muna kama manyan kaya a hannunsa,da shi za a riƙa siyan miki kayan ɗaki na garari,ki sakar masa jiki sosai,babu abinda zai faru ko ciki ya shiga zamu ɓarar das....." Ƙafafun Raudah ne suka kasa ɗaukarta,ta sulale zuwa ƙasa tana kai hannu bibiyu ta toshe kunnuwarta wasu irin hawayen da bata san sanda suka ɓalle mata suka shiga zarya akan fuskarta."Yanzu har abin na Maimunatu ya kai hakan? Da gaske bin maza take har ta riga da ta sallama mutuncinta a titi? Innalillahi wa'inna'ilaihirraju'un!" Raudah ta jerawa kanta tambayoyin tana sakin salati daga ƙarshe.Kanta ya yi wani irin nauyi,zuciyarta na bugawa da matsanancin saurin da take ji kamar numfashinta zai sarƙe.Da ƙyar ta iya miƙewa tana kallon saitin window ɗin uwar ɗakin Antyn Amaryar da yake a sakaye,hakan ya sanya ko kaɗan ba zasu iya ganin ko da mutum a kusa ba.Kuma dama idan Ubangiji ya nufeka da mummunan ji ko gani,saika rasa wani abin ma taya akayi ka jiyosa ko ka gansa? Haka Raudah ta ayyana a zuciyarta domin ta san tabbas da sun san da wanzuwarta a kurkusa ba zasu saki jiki da murya suna tattauna irin waɗannan mugayen kalaman ba.Da ƙyar ta iya ƙarisa shanya ragowar kayan ta koma ciki ta nufi ɗakinsu,kwanciya tayi kalaman Anty Safiya na sake mata amsa kuwwa tana ji kamar zazzaɓin da ya tafi mata ne zai dawo."Maimunatu fa,tsarar Sumayyah da watanni uku ne a tsakaninsu kacal! Yanzu ita ce har ta san kalar rayuwar bariki har suke tattauna batun tsumi na maganin mata da uwar da ta kawota duniya kuma ba tare da aure ba?" Raudah ta furta hakan a ƙasan zuciyarta tana jin saukar wasu zafafan hawaye na tsananin tausayin Mahaifinsu,domin kowani masifa Maimunatu ta janyo sunansa za a fara kira ace shiya janyo musu wannan abin kunyar, domin watakila da bai yi kalar rayuwar da ya yi abaya ba da watakila Maimunatu bata fito a haka ba."Meyasa Baba? Meyasa ba ka yi tunanin za ka haifemu watan watarana har mu girma mu ma mu zama ƴaƴa tamkar waɗanda ka ɓata rayuwarsu a baya ba? Meyasa ka zaɓowa Maimunatu uwa irin Anty Amarya?" Raudah ta furta dukkanin tambayoyinta a fili tamkar za ta zauce.Wani irin zafi zuciyarta ke yi tana sake jin ina ma ba Baba Lawal bane ya kawota duniya,domin tunda ta taso ta ji haramci aikata zina da irin azabar da aka tanadarwa mai aikakata idan har ya mutu bai tuba ba ta ji tana ƙyamar zina da mai aikata shi irin ƙyamar da ba za ta iya misaltawa ba.Daga lokacin kuwa da ta gano cewa Babansu ya aikata wannan kalar zunubin,shikenan take jin tsananin ciwon da a lokuta da yawa take jin ciwon yadda ta fito a jikinsa.Har Umma ta shigo ɗakin Raudah bata kula ba domin tunaninta ya yi nisa da gangar jikinta,sai da ta jiyo muryar Umman na kiran sunanta sannan tayi firgigit ta tashi zaune. "Kukan me kike yi kina sambatu ke kaɗai Raudah?" Umma ta jefa mata tambayar tana samun gefen katifarsu ta zauna akai.Raudah ta kai hannu ta share hawayenta tana faɗin, "Bakomi Umma." Wani irin kallo Umman ta jefeta dashi tana faɗin, "Kin sani bana son ƙarya ko ɓata mini lokaci ina nanata tambaya,sanar dani abinda ke damunki tun raina bai ɓaci ba." Raudah tayi ƙasa da kanta tana rasa ta yadda za ta sanar da Umman abinda ta jiyo su Anty Amarya na faɗi.Sai dai sanin ranta ne zai ɓaci idan Umman ta fusata ya sanyata sadda kai tana sanar da ita abinda kunnuwarta suka ji,da wani irin kaɗuwa Umma take duban Raudah hankalinta na mummunar tashi.Cikin wani irin karyayyen sauti ta ce, "Raudah ba kuka zaki yi ba addu'a yafi cancanta ku taya ta dashi,sannan ku sani ita zina masifa ce,fitinan rayuwace da duk wanda ya jefa kansa a cikinta to ƙarshen rayuwarsa nadamace da ba zai taɓa ƙarewa bawa ba koda ko kuwa ya tuba ya bar abinda yake,domin ita zina bashi ce da duk wanda ci sai ya biya,don haka ku ji tsoron Allah ku tsare mutuncinku,kada ku taɓa bari ruɗun duniya ko kuma makauniyar soyayyah ya sanya ku sallama mutuncinku wajen kowani namiji titi."


*_This is chapter 6 of my new story! Shin labarin ya fara taɓa zukatanku ko har yanzu da saura dai? Mu haɗu a comment section domin ina buƙatar jin sharhi akan wannan Labari_* 🥲😍


*Ɗansabo na yabawa da yadda ku ke bibiyan labarin* 😘😘😘😘
[10/8, 2:29 PM] Aysha Dansabo😍: 📱 *RAYUWA DA ƘADDARA* *Arewabooks@ayshadansabo*

*Paid book 08167768704*

*Free page*

*Chapter 7*

Umma ta jima sosai tana yiwa Raudah nasiha masu ratsa jiki da zuciya akan illar zina da haɗarin da ke tattare da ita,har Sumayyah ta dawo ta samesu tare da Raudan a haka.Ta haɗa har da Sumayyan tana cigaba da musu nasiha tare da nusar dasu muhimmanci yawaita yin addu'a da neman kariya daga dukkanin fitintunu na zamani,ta cigaba da faɗin, "Ku dage da yiwa kanku da ƴan uwanku addu'a,ku riƙa haɗawa har da Mahaifinku shi ma,domin yana da buƙatar addu'a game da yadda mace ta sha gabansa,kuyi haƙuri da Rayuwa domin cike take da tarin ƙalubale kala-kala,sannan ita RAYUWA DA ƘADDARA tare suke tafiya da juna,sai dai kawai muyi addu'a idan an tashi jarabtarmu a jarabe da Ƙaddarar da imaninmu zai iya ɗauka,Allah ya tsare mana ku ya tsare mutuncinku da namu baki ɗaya." Raudah suka amsa da cewa, "Ameen Umma,mun gode Allah ya ja kwananki tare da lafiya mai ɗorewa." Umma tayi murmushi ƙaunar Ƴan matan nata da tarin tausayinsu na sake kassara zuciyarta.Tare da Sumayyah suka fice domin ɗaura girki,ita kuma Raudah sai ta koma ta kwanta tana sake jujjuya dukkanin kalaman Umma,tana sake jin ƙauna da alfaharin samunta a matsayin Uwa ta gari da suka yi dace.Tana daga kwancen ta jiyo sallamar Aliyan sasan Baba Adamu,ta amsa daga cikin ɗakin nasu tana jiyo takun isowar Aliya zuwa ɗakin nasu.Da sallama a bakinta ta shigo ɗakin,Rauda ta ɗago manyan idanunta ta sauke akan baƙar budurwar da ke tsaye ta zubo mata ido.Aliya kyakykyawace kamar Innarsu Ameena,sai dai ita ta biyo baƙin fatar Baba Adamu ne.Cikin rashin walwala Raudah ta dubeta tana faɗin, "Habawa Aliya sai yau kika ga damar shigowa?" Aliya ta ɗan narke murya tana zama daga gefen katifar da Raudah ke kai ta ce, "Afwan Raudah,nima wallahi mura ne ya ɗan kwantar dani,ya jikin naki?" Raudah ta taɓe baki ta ce , "Lafiya lau na warware,ya naki jikin to?" Aliya ta ce, "Da sauki Raudah,ki saki fuskar to mana wannan haɗe gira haka." Raudah ta galla mata harara tana sakin ƙaramin murmushi ta ce, "To ya aka yi? Ya batun shiga skull jibi?" Aliya ta gyara zama sosai tana cire mayafin jikinta ta aje tana faɗin, "Zamu shiga mana Raudah,mu da zamu shiga semestern ƙarshe ina muka ga ta ɓata lokaci,ni wallahi duk na ƙosa mu ƙare wannan jarababben karatun muyi aure ko muma ma huta." Raudah ta zuba mata idanu tana mamakin masifar son aure irin na Aliya,wacce duk cikin su ukun da suka taso kansu ɗaya ta fisu kula samari.Ko a skull lacturers da dama suke sonta,Raudah da Zainab ne kaɗai basu kula kowa,duk nacin samarin FCE sai da suka shafa musu lafiya domin basu basu fuska ba sam.Ta dubi Aliya ta ce, "Aliya manyan mata,wannan aure dai gwara azo ai miki shi tun kafin mu rasa gane kanki,yanzu waye gwanin da za a shafa fatihan da shi mu fara shiri?" Aliya ta saki wani irin murmushi tana faɗin, "Dakta Shamsu mana,shi ne ya yi nasaran sace nan ɗin baki ɗaya Raudah." Aliya tayi maganar tana nuna saitin zuciyarta da hannu.Raudah ta saki murmushi tana tuna wane ne ma Dakta Shamsun da Aliya ke faɗi,domin dai tana da samarin da yawa da take kulawa.Can ta tuno shi, wani lacturer ne a jami'ar ABU da ke Samaru,Aliya ta haɗu dashi ne a cikin FCE ɗinsu lokacin da ya kai wa wani lacturer ɗinsu ziyara.Raudah ta ce, "Allah ya tabbatar da alkhairy Aliya,ai auren abu ne mai kyau,Allah ya yi mana zaɓi nagari kawai." Aliya ta amsa da cewa, "Ameen Raudah,ke ma ai naji cewa Yaya Sadeeq ne gwanin naki har ma ya sanar da Baba,amma jiya har cikin dare na ji Innarsu Zainab na bala'i akan bata amince da maganar ba." Raudah da wani irin abu ya doki zuciyarta,sai tayi saurin duban Aliya ƙirjinta na bugawa da matsanancin ƙarfi ta ce, "Da gaske Aliya? Dama ni na san Inna Karimatu ba za ta taɓa amincewa dani ba." Yadda Raudah tayi maganar cikin karyewar murya ba ƙaramin tausayi ta bai wa Aliya ba,cikin muryar rarrashi Aliya ke faɗin, "Kiyi haƙuri Raudah,In Sha Allah idan har akwai aure a tsakaninki da Yaya Sadeeq za ki aure shi koda kuwa duka duniya ne za su taru domin su hana aukuwar hakan,Baban mu jajirtacce ne da bai yi saken da Innar su Zee tafi ƙarfinsa kamar yadda Anty Amarya tafi ƙarfin Baba Mai Itace ba,don haka ki kwantar da hankalinki ban faɗa miki hakan don hankalinki ya tashi ba,sai don na sani kona ɓoye miki hakan dole za ki sani domin ƙiyayyar da take wa Umma daku a fili yake ma ba a ɓoye ba,kuma kowa yasan son zuciyarta da hassadace kaɗai ba domin kun taka mata ko kun zubar mata ba." Aliya ta ƙare maganar cikin bayyana ɓacin ranta ga halayyar matar uban nata Inna Karimatu,domin suma kansu haƙuri suke da halinta a matsayinta na kishiyar uwarsu Inna Aminatu.Raudah ta ja ajiyar zuciya tana aro dukkanin jarumta ta sanyawa zuciyarta,cikin son danne duk wani damuwa ta ce, "Haka ne Aliya,amma matuƙar Inna Karimatu ba ta amince dani ba,zan cire Yaya a cikin zuciyata koda hakan na nufin rasa rayuwata ne,domin ba zan iya rayuwa da uwar mijin da ba za ta ƙaunaceni ba." Aliya tayi saurin duban fuskar Raudah da ko kaɗan babu alamun wasa a tare da ita,cikin matsanancin damuwa ta ce, "Kar ki masa haka Raudah,domin a kallon da Yaya Deeku ke miki kaɗai za a fahimci cewa bada wasa soyayyarki ta kama zuciyarsa ba,kuma ko kunyi aure bata so na tabbatar ba zai taɓa zama a garin nan dake ba, domin gujewa ɓacin rai da tseratar dake daga dukkan sharrin mahaifiyarsu." Raudah tayi murmushin takaici ta ce, "Waya gaya miki ko birnin sin ya kaini ƙiyayyar da take mini ba zai yi tasiri ba Aliya,kin san sharri da haɗarin auren wanda uwarsa bata ƙaunarki kuwa? Na sha karantawa a littafai duk da ban taɓa ganin ƙiyayyar a zahiri kalar wanda nake karantawa ba,amma zuciyata ba za ta iya ɗauka ba Aliya domin kin fi kowa sanin halina ni mai zafi ce da saurin hasala,maganin kar ayi kar a fara kawai,ƙiyayyar da Inna Karimatu ke ma Umma damu kan mu ba mai sauƙi bace,dama na bashi dama ne domin nayi masa adalci na kuma yiwa soyayyar da yake mini adalci,ina son Yaya Sadeeq Aliya ba zan ɓoye hakan ba,amma soyayyar da nake masa bai yi ƙwarin da zan iya jure matsananciyar ƙiyayya da rashin sukunin da zan fuskanta daga gareta ba,don haka addu'a kaɗai za ki taya ni dashi,Allah ya kawo mana mafita cikin sauƙi ko rabuwar ce ayi irin wanda rayuka ba za su ɓaci ba." Daga waɗannan kalaman Raudah ta kashe bakin Aliya daga furta duk wata kalma data shafi alaƙar soyayyar da Yaya Deeku ke mata.Suka cigaba da hiran skull ɗinsu har zuwa lokacin da Khaleel ya faɗo cikin ɗakin kamar an jefo shi,kyakykyawan Yaro mai shekaru bakwai zuwa takwasa a duniya.Shi ne Autan Anty Amarya wanda daga kansa bata kuma haihuwa ba,ya rugo da sauri ya faɗa jikin Raudah yana faɗin, "Anty Raudah na dawo ki bani gullisuwa." Raudah ta rungumeshi tana jin ƙaunarsa mai tsanani na ratsata,tun yana ƙaraminsa Allah ya ɗaura mata son sa kamar yadda shi ma Yaron ya taso da ƙawazucinta a zuciyarsa.Tun Anty Amarya na masifa akan za a mallake mata ɗa,har ta gaji ta daina domin kuwa Khaleel baya iya yini a wajenta sai ɗakin Umman.A hankali ta fahimci cewa ba cutar mata dashi ake ba,domin Yaro baya zuwa inda ake cutarsa.Cikin sakin fuska Raudah ta shafa kansa tana faɗin, "Oyoyo my boy ka dawo?" Ya gyaɗa kai cike da zumuɗi ya ce, "Na dawo Anty,dama duk na ƙosa na dawo ki dinga bani gullisuwa da alawar madararki ko?" Raudah ta shafa bakin kwaɗayin tana faɗin, "Nima duk nayi kewarka Khaliluna,to me ka kawo min tsarabar hutun da ka je ɗin?" Ya ce cikin sauri, "Biskit kaɗai aka bani sai kuɗi,kuma ina dawowa Anty ta ƙwace kuɗin." Raudah ta saki murmushi tana aje shi gefe guda ta tashi ta ɗakko masa gullisuwa da bata rabo dashi a gidan sabida ƴan skull da ke shigowa siya bayan wanda take kai wa shago,tana kawo masa ya amsa yana sakin murmushi mai yawa akan fuskarsa ya ce, "Na gode." Daga haka ya sake komawa jikinta ya manne yana kallon Aliya da ke harararsa akan yaƙi ce mata komi.Aliya ta dubesa ta ce, "Yanzu Khalil ni kake ƙyalewa sabida bani da abin baka irin na Anty Raudah ko?" Ya kuwa jinjina kai ya ce, "Aike da Anty Zee duka bakwa bani abin ku,Anty Amarya ta ce rowa ne daku ai." Raudah da Aliya suka kalli juna suka saki murmushi,cikin dariya Aliya ta ce, "To shikenan tunda haka Anty ta ce ba zan kuma baka sweet ba, ai za ka je har sasan mu wajen Innarsu Zee ka sameni." Khalil ya yi murmushi yana faɗin, "Ai bana zuwa,nafi son wajen Gwaggon Suhailah ko wajen Umma ko Anty Raudah?" Raudah ta jinjina kai tana ƙara jin sonsa a zuciyarta sabida surutu da wayonsa,gashi duk mutanen da bata shiri dasu baya raɓarsu,Anty Amaryar kanta don dai uwa uwace amma yadda yake damuwa da lamarin Umma sam baya ƙawazucin Anty Amarya sosai.

Aliya kusan yini tayi a sasan nasu Raudah sabida dama ita ɗince ta hannun damarta da suka fi shiri fiye da Zee da babu wuya sun haura sama da Raudah,domin dukkaninsu suna da zafi da rashin haƙuri.

Kamar yadda Yaya Sadeeq suka rabu da Baba Lawal cewa da yamma ya same shi bayan la'asar hakan ce ta kasance,suna dawowa daga masallacin dake gabansu kaɗan suka zauna daga bakin dakalin ɓangaren su Gwaggo Shatu da wajen yake shiru babu gilmin ƴan shige da fice masu yin siyayya a wajen Umman.

"Malam Saddiku ina sauraronka,ina fata dai lafiya?" Yaya Sadeeq ya sadda kansa ƙasa ya soma da faɗin, "Baba dama ina so idan kai mini izini wajen fara tsayuwa da Raudah a matsayin wacce nake fata ta zama uwar Ƴaƴana,na gabatarwa da Baba da ita a matsayin zaɓina." Baba Lawal ya ɗago kansa ya dubi Sadeeq wani irin farin ciki da ba zai zata ba na mamaye zuciyarsa,ya jinjina kai yana murmushi ya ce, "To in banda abin ka Sadeeq ai Auwalu shi za ka tunkara domin shi ne maɗaurin auren Raudah idan da rayuwa,Allah ya tabbatar da alkhairy a tsakanin junanku,ina fata ita Raudar ta san da zamanka ko?" Cike da jin nauyi Sadeeq ya gyaɗa masa kai alamun ta sani.Baba Lawal ya sake jin farin ciki sosai,ya kuma yi addu'a mai yawa akan Allah ya tabbatar da alkhairi.Yaya Deeku duk sai ya ƙosa Baba Auwalu ya dawo ya gabatar masa da zancen Raudah a matsayin wacce ya zaɓa ta zama uwar ƴaƴansa,sai dai Baba Auwalun bai shigo gidan ba sai bayan magriba.Yaya Deekun bai yi ƙasa a guiwa ba ana idar da sallar Isha'i tun a bakin masallaci ya fara yi masa zancen yana son magana dashi,suka ƙarisa gidan Baba Auwalu ya jashi har ɗakinsa suka zauna.Ya dubi Yaya Sadeeq ɗin cikin fara'a yana faɗin, "Sanar dani Sadeeq me ke faruwa?" Sadeeq bai tsaya sanya ba wajen sanar da Baba Auwakun komi,ciki har da
kalaman da Innarsu ta fara yi na son kawo masa matsala ga cikar burinsa.Baba Auwalu ransa ya ɓaci,cikin kausasa murya ya ce, "Bata isa hana Allah ikonsa ba,ka kwantar da hankalinka ai matar mutum kabarinsa,matuƙar Raudah matarka ce za ka aureta ko Karima na so ko bata so,domin tayi kaɗan ta ja da hukuncin Ubangiji! Idan har kaga aure tsakaninku bai yiwu ba to dama ka ɗauka ba rabonka bace,zan samu Hajiya Kakah da maganar dama ƙarshen watannan nayi niyyar tara duka ƴan matan akan kowacce ta fiddo zaɓinta tunda karatu ya zo ƙarshe,da zaran sun kammala zamu miƙa su ɗakin miji sai kuma mu ji da da ragowar masu tasowa,sannan ina so dama inyi wata magana game da Yarinyar nan Maimunatu da surutu ya fara yawa a kanta akan yadda take neman ɓarar mana da mutunci,a matsayinku na manya maza a gidan yakamata ku tayamu sanya idanu matuƙa a kanta tare da koran duk wani saurayi mara kamun kai da zai tunkaro ƙofar gidannan,shi ma kuma Yaya Lawal ɗin zan same shi mu tattauna domin bai kamata ya sakarwa mace ragamar kulawa da rayuwar ƴarsa babu control ba." Baba Auwalu ya kai ƙarshen maganar yana jin ɗacin kalaman da abokinsa ya tare shi da shi akan Maimunatu,wacce ya ganta a cikin wani hotel da ke cikin GRA Zaria ita da wani babban magidanci ma ba saurayi ba. Yaya Sadeeq ransa ya yi mummunar ɓaci,hankalinsa kuma ya tashi domin shi ma ya gama fahimtar rayuwar Yarinyar ta fara lalacewa tabbas.Cikin sanyin murya ya ce, "In Sha Allah za mu sanya idanu a kanta sosai Baba Auwalu,Allah ya shirya mana zuriya." Baban ya amsa da cewa, "Ameen." Suka yi sallama da Yaya Deekun,wanda yana fitowa daga sasan Baba Auwalun ya nufi ɓangaren Hajjah Kakah.

Daga cikin zauren sasan ya tadda Zainab ƙanwarsa tare da saurayinta suna zance,sun shimfiɗa tabarma daga cikin zauren tare da kunna hasken waya kasancewar babu wuta a lokacin.Saurayin ya gaida Yaya Sadeeq ɗin a ladabce sukai musabaha,Yaya Deekun ya wuce zuwa ciki yana yaba ɗan nutsuwar da ya gani tattare da saurayin Zee ɗin.

Da sallama ya sanya kansa cikin harabar sasan,idanunsa ya sauka akan kusan duka ahalin jikokin nata zagaye da ita daga bakin barandar shiga ɗakinta.An kunna babban lanta mai tsananin haske da ya haske ko'ina na tsakar sasan,Hajjah Kakah na zaune a tsakiyarsu gabanta farantin da ta zuba lafiyayyen tuwan shinkafa miyan taushe ne da aka saka manyan kifi a cikin miyar.Daga sasan Baba Auwalu Gwaggo Salamatu da ke da girki a ranar ta aiko,domin dama duk mai girki ita ce za ta sanyawa Hajjah Kaka da mai gidan abinci haka dukkanin matan gidan suke yi.Ya ƙarisa bakin barandar yana sake haɗe face ɗinsa babu ko ɗigon murmushi akan fuskarsa,ƴan ƙannen nasa suka shiga gaida shi a ladabce yana amsa su cike da basarwa.Ya aje ganinsa akan sahibar tasa Raudah,wacce ke zaune kusa da Hajjah Kakah sosai hankalinta amma na kan wayarta ne.A jikinta kawai ta ji idanunsa akanta suke,sai ta ɗago manyan idanunta a hankali ta sauke a kansa.Wani abu ya doki zukatansu a lokaci guda,kafin ta ɗan shagwaɓe murya tana gaida shi.Ya amsa da wani irin kulawa yana sake bin ta da kallo,tana sanye da free gown ne a jikinta sai ɗan ƙaramin hijab da bata rabo dashi a wuyanta sabida ita kanta tasan akwaita da cikar halittar da bata iya gilmayya tsakanin sasunan gidan ba tare da mayafi a jikinta ba.Aliya ita ce tayi saurin tashi ta ɗakko masa kujera domin ya zauna,bai musa ba ya amsa ya zauna yana gaida Hajjah Kakah.Ta ɗago daga kai loman tuwanta tana faɗin, "Saddiku ka shigo,ya naga hannunka rabbana bayan ka saka mini rai zan sha fura?" Yaya Sadeeq ya saki ƙaramin murmushi idanunsa akan Raudah da ke duba waya tana murmushi,haka kawai ya ji ransa na ɓaci wani azababben kishi na mintsininsa domin zuciyarsa na raya masa anya bada samari take chart ba?Maimakon ya fara bai wa Hajjah Kakah amsa sai ya miƙa hannu saitin Raudah yana faɗin, "Habeebty! Give me ur phone." Raudah ta ɗago da sauri tana jin kunyar sunan da ya kirata dashi a gaban kowa ba tare da ko ɗar ba,ta miƙa masa wayar bayan ta ɗan zumɓure baki kaɗan.Ya amsa wayar yana sauke idanunsa akan page ɗin da take karantawa na wani novel da take bibiya a wani group da aka sanyata na karatun novels,sai ya saki ajiyar zuciya mai ƙarfi ganin ba zarginsa bane ya tabbata.Bai maida mata da wayar hannunta ba ya dubi Hajjah Kakah ya ce, "Za ki sha Hajjaju, ai yanzu daren ya fara ko? So nake na haɗo miki da wani gashin nama ko bakya ci ne?" Hajjah Kakah tayi saurin dubansa tana faɗin, "Wane mutum ni Zuwairah! Ai kai ma kasan ni da nama kamar tare aka haliccemu,ka ce kawai kar na rufe sasa da wuri akwai cin daɗi yau." Ya jinjina kai yana duban Raudah kai tsaye ya ce, "Habeebty ke ce zaki taya ta kwana yau?" Raudah tayi saurin girgiza kai ta ce, "Hameedah ce yau da tayata kwana Yaya." Bai ji ko ɗar ba ya ce, "Ke za ki kwana ina so muyi magana anan idan na dawo,gobe sai ita Hameedar ta tayata kwana." Hajjah Kakah tayi saurin faɗin, "Kamar kasan nama fi jin daɗin mu kwana tare sabida da ta tashi za tayi mini komi cikin zafin nama babu komawa wannan shegen baccin asaran,amma ita sam bata ƙaunar ranar tayani kwanan ya zagayo kanta." Hajjah Kakah ta ƙare maganar tana makawa Raudah harara,sai dai can ƙasan ranta sosai take jin ƙaunarsu ita da Yaya Sadeeq ɗin.Raudah ta zumɓuri baki tana kallon yadda Yaya Sadeeq ya kafeta da idanunsa da ke da wani irin tasiri a kanta,ya miƙe zai fice daga sasan tayi saurin sake shagwaɓe murya ta ce, "Yaya Deeku wayata please!" Kamar ba zai bata wayar ba sai kuma ya miƙa mata wayan ya jefeta da wani sassanyar kallon da ya ratsa har ɓargonta.Ya fice a sukwane Hajjah Kakah na masa a dawo lafiya,kamar jira Aliya take yi ya fita ta ce, "Shegiya luv! Gaskiya Raudah kina kashe Yaya Sadeeq da soyayyah, ke kinji yadda ki ke masa wata shagwaɓa kamar za ki narkar dashi." Rauda kunya ya rufeta amma sai ta maze ta aikawa da Aliya harara tana faɗin, "Kin shiga uku Aliya da sharri,ni babu wata shagwaɓa dana iya bare har nayi masa na kusa narkar dashi ɗin." Hajjah Kakah da ke saurarensu sai cewa tayi, "Allah dai ya kai mu gobe ayi wacce za a yi tsakanin ni da Auwalu da ya ɗaurewa balagarku gindi wai sai kunyi boko,Yara duk kun fitsare da iya jan zuciyan maza kamar su narke babu ko kunyar idanun tsufa,to ai gara kawai kowacce ta fito da nata tsayayyen a kaiku ɗaki a huta,dama ga waccar jarababbiyar ƴar da ta fara bibiyan maza tana raba musu komi arha a titi,wallahi Safiya ta cuceni ta kuma cuci Lawal,amma ba laifinta bane laifinsa ne da ya auro ragowar bariki ya kawo cikin tsarkakakkun ahalina,shi ma kuma ya cuci kansa da bai zama kintsatstse ba tun a zamanin ƙuruciya,ai gashi a gaban idanunsa ake yawon hotel da ita ana....." Raudah ce tayi saurin katse Hajjah Kaka tana faɗin, "Don Allah Hajjah Kakah kiyi shiru,addu'a ita ce tafi cancanta kiyi ba tashin-tashina ba,ai kema har da naki laifin da

Please Login or Register in order to submit comment