Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dubesa da wani irin duba da ke bayyana rashin jin daɗin kalamansa,cikin sanyin muryarta mai cakuɗe da shagwaɓa ta ce, "In Sha Allah Baba zamu kiyaye,amma ko dai wani ya kawo ƙaran mune ya ce muna wani abin a skull ɗin,sabida na ji kamar jirwaye ka ke mini mai kama da wanka,wallahi Baba ka tambayi Baba Auwalu da ke aiki a cikin makaranta ka ji,muna iya ƙoƙarinmu wajen kare mutuncinku da namu baki ɗaya." Jikin Baba Mai Itace sai ya yi sanyi,ya dubi Raudah duba mai cike da so ya ce, "Ba haka bane Raudah,lamarin ƙanwarku Maimunatu ne ke bani tsoro da sakani cikin tarin damuwa da kokwanto,bana so ya kasance ku ma kun ɗauki layin da ta bi,duk da cewa na san tarbiyyan da Halimatu ta ɗaura ku akai ba iri ɗaya bane,ku ji tausayina Raudah kar ku yadda ku sallama mutuncinku a titi,sannan ina roƙo ku yafe mini akan dukkanin abinda kunnuwarku suke jiye muku a bakin Safiya kin ji ko?" Raudah ta jinjina kai tana jin wani abu mai nauyi na sake danne zuciyarta,cikin sanyi da raunin murya ta ce, "Baba In Sha Allah zamu tsare kanmu,kuma ku cigaba da yi mana addu'a, Allah zai kare sai mun dawo Baba." Daga haka ta miƙe ta fito daga ɗakin bayan ya yi musu addu'ar samun ilimi mai amfani.

"Umma na fito bani fanken kawai na wuce sasan tsuhowarcan mu gaisa,na makara kada ya zamana su Aliya na jirana." Raudah ta faɗi hakan tana duban Umman su da ke zuba kunu a wani ƙaramin flask da take zubawa Hajja Kakah,ta miƙawa Raudah fankenta da ta riga ta ƙulla mata a ledar tana faɗin, "Gashi nan,sai ki haɗa dana Hajjah Kakan ki wuce mata dashi." Raudah ta amsa tana mita a zuci na cewa,ba lallai ma Hajjah Kakah ta ci fanke da kunun ba idan ta samu abin da ya fishi daga sasan sauran ƴaƴan nata.

Tana fitowa daga sasan nasu riƙe da flask na kunu da fanken Hajjah Kaka,ta hango fitowar Yaya Deeku daga sasan su.Ta ɗan ɗauke kai daga dubansa tana cigaba da taku a nutse ta doshi sasan Hajjah Kakan,tana daf da sanya kai cikin zauren sasan ta jiyo muryarsa yana kiran sunanta.Ta ɗan waiwayo tana dakatawa tayi tsaye har ya ƙariso,ya dubeta da wani sassanyar kallo yana bin shigarta da kallo daga sama har ƙasa.Wani kishi ne ya turnuƙe zuciyarsa har ya kasa haƙuri ya furta,"Habeebty anya wannan hijab ɗin ya rufe wani abu kuwa? Kin ga irin kyawunki da ya fito ne,please a shigar da hannun nan ciki don Allah kin ji?" Raudah ta ɗago ta dubesa tana shagwaɓe fuska tare da narke murya ta ce, "Yaya Sadeeq gud morning!" Ya sake zuba mata idanu bayan ya amshi flask ɗin hannunta na fanke dana kunun ya ce, "Habeebty ni ba gaisawa nake so ba,kiyi abinda zai rage min zafin da nake ji a zuciyata please!" Raudah ta kalli kanta tana mai maida hannun jalbab ɗin ciki kamar yadda ya buƙata.Ta dube shi ta ga yadda idanunsa ke yawatawa a saman ƙirjinta da ta tabbatar fitan tudunsu ta sama time ɗin da hannun ke waje ne ya sanya shi jin kishi,sai ta ji wani irin kunya ya lulluɓeta har tana saurin juya masa baya.Ya sauke wani sassanyar ajiyar zuciya yana yin ƙasa da muryarsa ya ce, "Babu laifi dai an ɗan rage ganinsu Habeebty,amma don Allah idan akwai hijab ɗin da yafi wannan faɗi da sakewa ki taimakeni ki koma saka su,ina fata dai baki taɓa fita da gyale zuwa skull ɗin ba ko?" Raudah ta dube shi da wani irin narkakken kallon da ya ji tasirinsa har ɓargonsa,cikin shagwaɓe murya ta ce, "Ka tambayi Zee Yaya Deeku,na tabbatar za ta faɗi maka ko cikin mafarki ban taɓa sha'awar saka gyale na fita zuwa haɗararriyar makarantar nan ba." Yaya Sadeeq da ya ji wani sanyi a cikin zuciyarsa,sai ya furta, "Das very good Habeebty,I luv u so very much!" Suka jera kafaɗa da kafaɗa har cikin sasan Hajjah Kakah,Sadeeq na sake jin ƙauna da azababbiyar soyayyar Raudah na kekketa zuciya da jinin jikinsa.Da fara'a sosai Hajjah Kakah ke amsa gaisuwar ƴan jikokin nata da take jinsu a tsakar zuciyarta,ta dubi Raudah da ta miƙe tsaye sabida gudun makara ta ce, "Har za ku wuce makarantar Raudatu? Yanzu Aliya ta fita nan ita ma cikin sauri,Zainabu ne ƴar ikon bata miƙo tata gaisuwar ba tunda ita da uwarta wuyansu ya yi kaurin da ba kullum nake samun darajar da za a tako a gaidani ba. Raudah ta fice da sauri-sauri tana faɗin, "Hajjah Kakah ni dai na wuce sai mun dawo,Baby sai na dawo." Sadeeq ya miƙe ya rufa mata baya yana jin daɗin kalmar Baby da ta kiraye shi a karon farko. "Wait Habeebty!" Ya furta hakan lokacin da ya cin mata tana dab da ficewa daga sasan,ta tsaya tana jin kunyan waiwayowa ta dubeshi.Suka jera da juna yana kasheta da kalaman soyayya masu narkar da zuciya har suka isa ƙofar shiga sasan su Yaya Deekun,suna shirin sanya kai Baba Adamu dasu Zee na shirin fitowa.Raudah wani uban kunya ya rufeta domin kuwa Yaya Sadeeq riƙe yake da jakanta,tayi saurin risinawa ta gaida Baba Adamun idanunta akan Zee da ke bin Yayanta da wani irin kallo.Baba Adamu ya amsa da fara'a yana musu fatan dawowa lafiya daga skull ɗin,ya wuce su kai tsaye zuwa sasan Hajjah Kakah. Zainab da Aliyah suka gaida Yayan nasu,ya amsa yana sake tsare gida tare da miƙawa Raudah hand bag ɗinta.Ta amsa tana dubansa ƙasa-ƙasa kafin shi ma ya ɗan matso kusa da ita sosai yana faɗin, "Take care Angel,banda kula kowa please!" Raudah ta sakar masa murmushi ya wucesu ya shige zuwa ciki su kuma suka nufi ƙofar fita gate ɗin gidan nasu.Suna tafe ne Aliyah na tsokanar Raudah da cewa duk ta fara susuta musu Yaya da soyayyarta,ita dai Zainab bata tanka ba sai ma time to time da take sakin ƙaramin tsaki har suka fito bakin titi suka samu napep da zai kaisu har bakin gate ɗin FCE.

"Salamu alaikum masu gida!" Muryar Hajjah Kakah ya ratsa cikin kunnuwan Inna Karimatu da ke jan ruwa daga bakin rijiyan sasansu da ke daga shigowa sasan babu tazara sosai.Ta ɗaga idanunta ta sauke akan Hajjah Kakah da fuskarta sam babu alamun annuri,cikin tsare gida ita ma ta amsa sallamar Hajjah Kakan tana faɗin, "Barka da shigowa Hajjah Kakah,ƙarisa daga cikin ɗakin gani nan zuwa." Hajjah Kakah da ta hango kujera a tsakar sasan sai ta nufi wajen kujera ƴar tsugunon tana faɗin, "Bari na zauna anan Karimatu wajen ma yafi daɗin zama ga hantsi,gama ɗiban ruwan shigowar taki ce ta musamman." Inna Karimatu ta taɓe baki tana faɗin, "To shikenan bari na kai ruwan kitchen Hajjah Kakah.Daga haka ta nufi hanyar kitchen da botikin da ta cika da ruwan,Hajiya Kakah ta rakata da ido tana jinjina kai haɗe da mamakin yadda Karimatun ke ta juyewa zuwa wata ƴar ƙwarya-ƙwaryan mara mutunci da ɗa'a.Fitowar Innar su Aliya daga ɗakinta ya sanya Hajjah Kakah mai da hankali zuwa ga Inna Aminatu tana amsa gaisuwarta,ta ɗaura da faɗin, "Ameena daga ke har Karimatu dai kun daina zuwa gaidani sai idan kun bushi iska kun yi ra'ayi sabida kun raina mazajenku shi ne nima rainin da rashin albarkan ya shafeni ko? To ku kula da rayuwa na faɗa muku,domin duk wacce ta rainani ta raina uwar da ta kawota duniya ne,sabida idan akwai kara da ɗa'a uwar miji ai uwarku ce." Ta ƙare maganar tana watsawa Inna Amina wata muguwar harara,Inna Amina ta sadda kai ƙasa tana cuskune baki da yin ƙuƙunai ƙasa-ƙasa. Inna Karimatu ne ta iso wajen da wata kujerar zaman a hannu tana zabgawa Inna Amina harara ta ce, "Hajjah Kakah kin ce wajena kika shigo na ga kuma Innar Aliya tayi tsaye a kanki lafiya?" Hajjah Kakah ta ƙanƙance idanu ta ce, "Ni dai Allah ya gani sai da na gama karanta li'ilafi,sannan na bada sadakan ƙosai da zafinsa kafin na tako ƙafafuna zuwa sasan nan,don haka duk sharrinku sai dai kuci kawunanku ku sha baƙin ruwa,ke Amina bani waje bana son gulma." Inna Amina ta wuce a fusace zuwa ɗaki tana jaddada jarabar Hajjah da iya ci maka mutunci idan ta so a cikin zuciyarta.Ta nema kujerar da ke daga bakin ƙofarta da an shiga ɗakin ta zauna,domin so take ta baza kunnuwa ta ji da wacce Hajjah Kaka ta zo wa Inna Karimatun?

"Karimatu Saddiku da Usmanu dukkaninsu sun sameni da zancen cewa sun samu matar aure,sai dai shi Sadeeku ya zo da wani ƙauli na cewa wai kin ce ba zai taɓa haɗa jini da jinin Haleematu ba ko miye dalili?" Inna Karimatu ta sake gimtse fuska tare da haɗe girar sama da ta ƙasa ta dubi Hajjah Kakah kai tsaye ta ce, "Dalili kenan bana son ta kuma bana ƙaunarta,sannan ba zan taɓa son jinin Halimatu da ita kanta ba har abada,don haka indai ina da hakkin haihuwar Sadeeq to ba zan taɓa amincewa ya auro mini ƴar maƙiyiyata ba." Hajjah Kakah ta kama baki tana faɗin, "Ƙalu innalillahi wa'inna'ilaihirraju'un! Yanzu Karimatu a gabana ki ke maimaita waɗannan munanan kalaman?" Inna Karimatu babu ko ɗar ta jinjina kai ta ce, "Hajjah Kakah ai gara na faɗi miki gaskiya domin ba zan ji kunyar kowa a auro mini ƴar da za ta zame mini masifa su haɗu ita da uwarta su mallake mini shi ba,sai dai inga yana musu bauta ni ko oho,to wallahi ba zai saɓu ba wai bindiga a ruwa,dole ya rabu da Raudah ya je can waje ko cikin dangina ya zaɓo matar aure,ai ba a kanta a fara samun kyau da diri ba,mu ma zuri'armu akwai kyawawu masu nono da ɗuwawu sai ya zaɓo a ciki ya aura amma ba dai jinin Halimatu ba." Tana kai wa ƙarshen kalamanta ta miƙe ta shige ɗakinta a fusace ta bar Hajjah Kakah na sakin salati tana jan majina,sosai take kuka bilhakki na baƙin cikin kalaman da Inna Karimatu ta gaggaya mata babu kunya bare tsoron Mahaliccinta.Ta miƙe da ƙyar tana ɗaga murya ta ce, "Dani ki ke zancen Karimatu,ina ga kin manta wacece Zuwairah amma zan tuna miki,zan kuma tabbatar miki da cewa har yau ba a auro wacce ta isa in yanke hukunci a cikin ahalina ta tada zancen ba,wallahi sai dai ki zaɓa ko aurenki ko kuma auren Raudah da Abubakar Sadeeq matuƙar ina numfashi!" Hajjah Kakah na kai wa ƙarshe ta fito a fusace daga sasan Baba Adamu ta nufi na Baba Lawal.Tun daga zauren shiga sasan take ƙwalla kiran, "Halimatu! Hali dubu!! Kina ina?" Umma da ke daga cikin ɗakin tana ƙullin siga dasu maggi ta jiyo kiran,sai ta saki ƙullin ta fito da sauri tana faɗin, "Na'am Hajjah Kakah." Hajjah Kakah da ta shigo ciki zuwa lokacin,sai ta sauke ganinta akan Umma tana faɗin, "Yauwa mu shiga daga ciki,yau banda lokacin kula kowa wajenki kaɗai na zo." Umma ta jinjina kai ta ce, "To Bismillah Hajjah Kakah mu je ɗaki." Hajjah Kakah tayi gaba Umma na biye da bayanta har zuwa cikin falonta.Ta nemi kujera ta zauna tana sauke idanunta akan yawan ƙullin siga da su maggi da Umma ta tara su,cikin wani irin murya ta ce, "Allahu Akbar! Duk fa wannan rufin asirin da buɗin ake ma hassada da baƙin ciki Halimatu,wallahi babu abinda ke ɗawainiya da zuciyar Karima sai muguwar hassada da adawar da take yi da nasibi da buɗin da Ubangiji ya yi miki akan kasuwancinki,kuma In Sha Allahu tayi ta gani kenan tunda ita dai zuciyarta babu khairan." Umma da bata san inda zancen Hajjah suka dosa ba sai jinjina kai tayi tana murmushi,Hajjah Kakah ta sake gyara zama tana cigaba da faɗin, "Wajenki na zo Halimatu akan batun Raudatu da Sadeeku,na san dai kema zancen cewa suna son juna tuni yazo miki,inma bai zo kunnuwarki ba na tabbatar a kallon rashin kunyar da yake bin ɗiyarki dashi kaɗai zai fassara miki ba ƙaramin tafiya da zuciyarsa tayi ba,don haka kar ki zamo cikin masu cewa za su ja da hukuncin mai duka,domin duka bamu san meke ɓoye ba,babu ruwanki da ƙiyayyar da uwarsa ke miki ki ce ba zaki lamunce masa ya auri ƴar uwarsa kamar yadda ita waccar shashashan ke tada jijiyan wuya tana faɗin ba a isa ba,to ke ki nuna halin dattako da ilimi,ki sake nunawa maƙiyanki ke ɗin mai ilimice da sanin yakamata wacce ba zata shiga hurumin Ubangiji ba,domin shi sha'anin aure addu'a ake binsa dashi ba jayayya da furta munanan kalamai ba." Hajjah Kakah ta ɗan dakata tana kallon Umma da ta nutsu tana saurarenta,hakan ya bai wa Hajjah Kakah damar cigaba da faɗin, "Mun gama magana da Adamu da Auwalu akan cewa ƙarshen watan nan kowacce a cikin su ukunnan da zasu kammala babban makaranta su fito da tsayayye,ita Raudah tunda Allah yasa na gida ne,ina so a fara aje mini goron saka ranar aurenta da Sadeeku cikin ƙarshen watan nan domin so nake na nunawa Karimatu cewa bata isa ba,kuma tayi kaɗan ta hana Sadeeku auren zaɓin zuciyarsa matuƙar nina tsuguna na haifo mata ubansa ta aura,don haka ina so ki kwantar da hankalinki a matsayinki na haƙurarriyar mace da duk cikin surukaina aka shaideki,ki bisu da addu'a Halimatu kada ki yadda ki yi ma abin mummunar fata ko baki kamar yadda Karimatu ta fara,ina fata kin fahimceni?" Umma ta jinjina kai ta ce, "Na fahimceki Hajjah Kakah,Allah ya tabbatar da alkhairi idan akwai,idan kuma babu Allah ya yiwa kowa zaɓi mafi alkhairy a cikinsu." Hajjah Kakah ta jinjina kai ta ce, "Ameen Halimatu,ai akwai ma alkhairy In Sha Allah! Halimatu ke dai kawai ki zuba ido ki kuma bisu da addu'a tunda har Allah yasa na gano ita ma Raudan da gaske shi zuciyarta ke so." Daga haka Hajjah Kakah ta miƙe domin ficewa daga ɗakin,Umma tayi saurin tashi ta ɗauki ƙullin kwatan siga ta saka a baƙin leda ta biyo bayan Hajjah Kakah dashi tana faɗin, "Hajjah Kakah ga wannan kya saka a koko babu dai yawa." Hajjah Kakah ta amshi ledar tana faɗin, "Allah ya yi albarka,bama dole ki dinga cigaba ba tunda Allah ya halicceki da hannun ungu,wasu kuma hannu kaman na ƴan dambe,indai ance maka ungo to abincin da ɗanka ya saka kuɗi ya siyo mai kyau ne,ko kuma shi ya shigo da abin masarufin da dole a ɗibo a baka naka kason,Allah ya yi miki albarka Halimatu ya kare ki daga kaidin ƴan hassada da maƙiya,ki dage da sadakan zazzafan ƙosai bayan kin baɗe shi da yaji,tunda ke mai tsayuwan dare ce dama,to ina tabbatar miki da cewa sai kin gagari kowace shegiya a cikin kishiya ko kishiyoyin saurinki." Umma ta jinjina kai cike da zallar tu'ajjibin halayya irin na Hajjah Kakah da ke canzawa kamar wata hawainiya.Yanzu za tayi dakai anjima ta ce kai ne baka iya mata ba,ta saki murmushi tana juyawa zuwa ɗakinta bayan Hajjah Kakah ta fice daga sasan ba tare da ta lalubi ɗakin ƴar gaban goshin nata Anty Safiya ba.........✍🏻
[10/11, 1:12 PM] Aysha Dansabo😍: *RAYUWA DA ƘADDARA*
*Arewabooks@ ayshadansabo*

*Paid book 08167768704*


_Free page_

*Chapter 10*


Umma na cigaba da ƙulla siga da maggin ne amma zuciyarta cike take da tarin ruɗani da damuwa,Allah ya sani har cikin zuciyarta ta yaba da Sadeeku za kuma ta so ya zama miji ga Raudarta.Amma sanin hali irin na Inna Karimatu da irin ƙiyayyar da take gwada mata ya sanya tana tsoron wani al'amari mai girma kamar aure ya shiga tsakanin Raudah da Sadeekun,tabbas tana tsoron halin da Raudah ka iya shiga idan har Hajjah Kakah ta kafe akai wannan haɗin ba tare da amincewar uwar Sadeeku ba.Addu'a ta dinga yi akan matuƙar babu alkhairy Allah warware ƙullin cikin hikimarsa da gaggawarsa,domin tabbas ba za a ji bakinta a cikin batun ba matuƙar ba alkhairy za ta furta ba. Ta kintsa komi bayan ta kammala ƙulle-ƙullenta ta fita zuwa kitchen domin shirin ɗaura girkin rana,sabida bata so Suhailah da Khaleel su shigo gidan bata gama girkin rana ba.Yaron ya riga ya saba da ita matuƙa har fiye da uwarsa,sabida kulawar da take haɗesu shi da Suhailah ta basu Anty Amarya bata tsayawa ta kula da shi kamar hakan ba.Shi kuma Yaro dama wajen duk da aka fi tarairayarsa anan yake,babu ruwansa da rashin jituwan da ke tsakanin Iyayensa.

Tana cikin gyaran kayan miya Anty Amarya ta fito daga ɗakinta,hannunta riƙe da ledan cefane da alamu ita ma girkin za ta fara shirin ɗaurawa.Ta kalli Umma ta watsar tana cigaba da tauna cingam ɗin dake bakinta,sai da ta zo ƙofar shiga kicin ɗin ta saki tsaki tana faɗin, "Aikin banza munafurcin wofi,har ni za a shigo ba a nemi inda nake ba sabida ana so a haɗa kai a cuci Sadeeku a aura masa ragowar lacturers,ahayye! Allah sarki!Hala an sha bamu san abinda ake aikatawa a cikin hijaban munafurcin da ake zumbulawa bane,ai shi ɗan iska idan ya cika ɗan iska wallahi baya munafurci da badda kama,fitowa da iskancinsa yake sarari kowa ma ya gane tunda babu ɗan iskan da ya isa ya sauya maka kalar rayuwar da kaso gudanarwa,kuma Sadeeku ba zai taɓa auren ragowa ba koda ace ita ce hurul inin duniya,sabuwa dal zai ɓare a leda tunda ubansa ba ragowar bariki da ya ci ya suɗe bane da za a lulluɓa ragowa akai ma ɗansa." Ta kai ƙarshen kalamanta tana sakin ƙaramin shewa tare da jan mugun tsaki tayi cikin kitchen ɗin.Umma da ke ta gyaran kayan miyanta sam bata ɗago ba,duk da yadda zuciyarta ta kai ƙoluluwa wajen ɓaci da irin kalaman ɓatanci da Safiya ke jingina Raudah dashi.Wani abu mai azabar nauyi da ƙuna ya tokare wuyanta har numfashi na son yi mata wuyan shaƙa,sai kawai ta shiga nanata kalmar Innalillahi har zuwa ƙarshe.A hankali ta ji zuciyarta na samun sassauci,ta kammala gyaran kayan miyan ta nufi ƙofar ɗakinta ta ɗebo ruwa a cikin ƙaton roban tara ruwa da ke barandar wajen ɗakin nata.Ko kaɗan ba tayi gangancin tanka Anty Safeeyah kamar yadda ita ta so hakan ya faru ba,ko kalma guda bata furta ba har ta kammala daka kayan miyan ta kwashe.Kitchen ɗin da tayi niyyar shiga tayi girkin a ciki ma sai ta fasa,ta fito daga waje ta ɓangaren barandar ƙofar ɗakinta ta kafa murhun gawayin a nan.Tana hura gawayin da tafi amfani dashi fiye da itacen da Baba Lawal ɗin ki jibge musu na amfani,tana tunanin idan ta samu faraga ma ƙaramin kamfin gas kawai za ta siya su riƙa maneji dashi suna amfani da abu biyu.Anty Safeeyah ta ƙulu iya ƙuluwa da yadda Umma ta maida ita mahaukaciya karya da ke haushi ita kaɗai,ta dinga roran masifa a tsakar gidan tana sakin maganganu amma Umman tayi biris bata tanka ta ba.Har su Suhailah suka shigo gidan ƙarfe sha biyu da rabi na rana Anty Safeeyah bata koma ɗaki ba,tana tsakar gidan tana sakin habaici da maganganun banza kala-kala.Umma tuni girkinta ya kusa kammala,tunda dama jallof ce na shinkafa da ta haɗa da taliya ta saka wani ragowar kifi da take dashi a aje.Khaleel ya rugo da gudu zai nufeta amma sai Anty Amarya ta kwaso a guje ta suresa suka nufi ɗaki tana faɗin, "Wuce mu je ɗan banza makwaɗaicin Yaro,na faɗi maka idan baka kiyayesu ba sai na ci ubanka,tunda duk abinda suke hilatanka dashi ina siya maka amma kullum zuciyarka na garesu kamar wanda suka lashe kurwansa,wallahi ba don boka ya tabbatar min ba asiri suka yi suka kama zuciyarka ba da sai anyi bala'i akan yadda ka ke liƙe musu kaman kaska." Umma da ke jiyo dukkanin kalaman da Anty Safiyan ke yi sai kawai ta girgiza kai tana sakin murmushin takaici da baƙin ciki,ta kama hannun Suhailah suka nufi ɗaki domin ta cire kayan makarantan kafin abincin ya ƙarisa nuna.

Ƙarfe ɗaya su Sumayyah da ke makaranta guda su huɗu suka shigo gidan,kowacce ta nufi sasansu ita da Maimunatu suka jero zuwa sasansu Maimunatun na faman wani harare-harare.Gabaki ɗaya huɗubar uwarta akan ƴan uwanta shi ne kada ta taɓa raɓarsu domin su ɗin ƴan uba ne da babu abinda suke mata sai hassada,haka take karanta mata tun daga ƙuruciya har girmanta,kawo yanzu kuma da idanunta suka gama buɗewa da bariki da sanin daɗin maza.Sai ya zamana babu wanda take kallo da gashi tsakanin Ummansu dasu kansu su Raudah,Baba Lawal ɗin kansa a sakarai take kallonsa tunda uwarta ta gama kwance masa zani a kasuwa a wajenta _,(Kaicon duk wata mace irin Anty Safiya,wallahi ƙalubale ne a gareku matan auren da sam bakwa ragawa mazajenku,ba ku tashi yiwa miji ɗiban albarka sai agaban idanun ƴaƴan cikinsa,wannan babbar musiba ce kuma babban kuskuren da idan kina aikata shi sai kinyi mummunar danasani a lokacin da ba zai yi miki amfani ba,sabida ita ƴa mace da irin tarbiyar da ta tashi ta ga kina wa ubanta take koyi,abin duk da kike yi shi za ta je gidan wani ta aikata,in ma sharran ko khairan,shiyasa tun asali aka ce maza su zaɓarwa ƴaƴansu uwa ta gari,kamar yadda muma mata akace mu zaɓarwa ƴaƴayenmu uba na gari,Allah ya shiryatar damu baki ɗaya)._ Sumayyah ita ma ɗauke kanta tayi har suka shige ciki kowacce ta nufi ɗakin uwarta,tana sanya kai cikin falon nasu Suhailah ta rugo ta rungumeta tana faɗin, "Anty Sumayyah sannu da dawowa,ita Anty Raudah bata dawo ba har yanzu." Sumayyah ta shafa fuskar Suhailah ta ce, "Za ta dawo Suhailah,amma sai can yamma kila,dafatan kinyi karatu mai yawa a skull." Suhailah ta ce, "Nayi sosai Yaya Sumayyah,idan Anty Raudah ta dawo za ki ce ta bani gullisuwa?" Sumayyah tayi murmushi tana faɗin, "Zan ce ta baki,ni ma idan na soya aya nayi tsami gaye zan baki ko bakya so?" Cike da murna Suhailah ta ce, "Ina so mana Yaya Sumayyah." Sumy ta saki murmushi mai faɗi tana faɗin, "Das my baby luv! Ki ce Allah ya sanya mini albarka a cikin sana'ar kin ji autar Umma?" Suhailah ta ce, "Allah ya kawo kasuwa da yawa irin na Anty Raudah,kema ki dinga sawa a robobi ana kai wa shagon Usy ko?" Sumy ta saki murmushi tana nufan ɗakinsu ta ce, "Haka nake fata autar Umma." Uniform kawai Sumayyah ta cire ta fito ta nufi banɗaki,tana fitowa ta ɗaura alwala ta nufi ɗaki domim gabatar da sallar azuhur da basu yi ba.

Suna cin abinci gaba ɗayansu a falon Umma ke bai wa Sumayyah labarin shigowar Hajjah Kaka akan batun soyayyar Raudah da Yayansu Sadeeq.Ta ƙare maganar da cewa, "Sumayyah ki taya ƴar uwarki da addu'a domin muna buƙatar hakan,sabida ina tsoron kaidin maƙiyi,musamman Karimatu da kowa ya fahimci da gaske take ƙina ni da ku baki ɗaya,ban kuma san me na tsare mata a wannan duniyarba,duk iya yadda na yaba da nutsuwa da hankalin Sadeeku zuciyata ta kasa nutsuwa da soyayyarsa ga Raudah,domin ina ji ajikina babu abinda za ta tsinta a cikin aurensa face ɓacin rai,sai dai kuma idan Allah ya riga ya rubuta hakan a cikin littafin RAYUWA DA ƘADDARARsu daga shi har ita ɗin." Umma ta kai ƙarshen kalamanta a sanyaye tana duban yadda ita ma Sumayyah duk jikinta ya yi sanyi.Da wani irin sanyin murya ta ce, "Hakane Umma,nima ina hango tarin ƙalubale,ba kuma na fata Hajjah ta tunzura ayi komi cikin gaggawa,ya dace ta bari ayi addu'a a kuma bi komi a sannu dokin nuna ƙarfin iko tamkar sake ruru wutar ƙiyayya da tsanarmu a zuciyar Inna Karimatu ne." Umma ta gyaɗa kai ta ce, "Nima dai abinda na hango kenan Sumayyyah,sai dai na ɗauki alwashin ni Halimatu ba zan taɓa tsoma bakina da sunan ja da hukuncin da zata zartas ba,zan dai dage da addu'a ina gaya ma Allah,In Sha Allah shi zai bamu mafita cikin sauƙi,jikina na sake yin sanyi ne a duk lokacin da na fahimci cewa zuciyar Raudah na ƙaunarsa,da ace bata son sa ne da nayi dukkan kasada wajen fahimtar da Hajjah Kakah akan kar ta zafafa,amma yanzu ina magana nawa ne zai fi zafi domin dama suke da fada a wajenta ita da Safiya basa laifi,sai dai su aikata kuskuren da kana shiga cikin maganar kai ne zaka kwana a ciki,don haka

Please Login or Register in order to submit comment