Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har na tara ak’alla dinari dubu goma.” Sannan yaran suka yi ta bai wa junansu labarin abin da za su aiwatar a rayuwarsu har aka zo kan Aladdini. Suka ce da shi “ya shugabanmu Aladdini me za ka aiwatar?” Ya ce musu, “ni da na kasance tsare a rufi ban samu fitowa ba sai kwanan nan. Ban aikata komai ba sai zuwa rumfa sau ɗaya na zauna.” Suka ce masa, “ka zama maras amfani maras manufa tunda ba ka san ko’ina ba, ba ka da sha’awar tafiye – tafiye ballantana kasuwanci.” Wani daga cikinsu ya ce, “kai kam misalina tamkar kifi ne, wanda idan ya bar ruwa zai mutu. Sai ka yi ta zama a rufi cikin mata.” Gaba ɗaya suka fashe da dariya. Suka k’ara da ce masa, “ya Aladdini, daukaka da k’imar ‘ya’yan fatake shi ne su yi tafiya a bayan k’asa domin su samu amfani.” Aladdini ya fusata saboda dariyar da suka yi masa. Ya hau alfadararsa ya tafi gida yana kuka. Mahaifiyarsa ta gan shi cikin halin bak’in ciki da ɓacin zuciya, hankalinta ya tashi ta ce masa, “me ya sa ka kuka?” ya ce, “a gaskiya ‘ya’yan fatake sun sa na ji kunya, suna ce min kifin rijiya, kuma wai k’imar mutum shi ne ya yi tafiye – tafiye a bayan k’asa yana saye yana sayarwa, yana neman kuɗi.”

Uwar ta ce, “haka ne, yanzu wanne gari kake son zuwa?” Ya ce, “birnin Bagadaza za ni, saboda an ce a can duk abin da ka je da shi za ka sayar ka ninka riba.” Uwar ta ce, “ya dana, na fada maka mahaifinka hamshak’in attajiri ne, amma idan bai ba ka jari ba ni zan ba ka a cikin kudina.” Ya ce, “kyakkyawan abu shi ne a shirya da wuri, ga shi kuma fatake sun yi shiri, a yi hanzarin aiwatar min da wannan abu.” Ta aiki bayi zuwa wurin masu daure kaya suka zo suka bude taska suka daure tufafi da sauran kayayyaki laftu goma.Wannan kenan game da Aladdini da mahaifiyarsa.
Mahaifinsa kuwa da ya duba cikin gona bai ga ɗansa ba, sai ya tambayi yara suka ce masa ya hau alfadara ya tafi gida. Saboda haka shi ma sai ya hau ya tafi gida. Bayan da ya shiga gidansa ya ga laftu goma a daure cikin shirin tafiya, ya tambaya game da su. Matarsa ta faɗa masa dukkan abin da ya gudana tsakanin danta da sauran ‘ya’yan fatake. Da ya ji haka sai ya ce, “ya dana ka tsoraci Allah ka tsoraci wahalar tafiya. Ka tuna hadisin ma’aiki mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa, ‘ma fi arzikin mutane, shi ne wanda ya samu dukiyar a garinsu.’ Kuma magabata sun ce, ‘ku bar tafiye – tafiye komin kankantar haka.” Sannan ya kuma cewa ga dansa, “yalla ka k’udurta tafiyar da ba za ka dawo daga gare ta ba?”
“Ya Abbana, babu makawa na tafi Bagadaza tare da sauran fatake, idan ba haka ba kuwa yanzu na cire dukkan tufafina na shiga uwa duniya. Ni ba zan yarda na zauna haka ba, ni ba marok’i ba, ni ba talaka ba.” Uban ya ce, “duk masu tafiyar nan neman kuɗi ke kai su kai kuwamahaifinka yana da kudi yana da dukiya mai yawa.” Ya kama shi ya nuna masa dukiyarsa mai yawa da tsabar kudin da ya mallaka wadanda kowanne laftu ya kai dinari dubu. Ya ce masa, “ya dana dauki laftu arba’in ka hada da wanda mahaifiyarka ta ba ka ka tafi ya zuwa hukuncin Allah madaukakin sarki. Amma ya dana ina jiye maka tsoro wani daji ana kiransa duhuwar zaki da wani kuma da ake kiransa yankin karnuka domin a nan akan rasa rayuka ba da yardar mamallakansu ba.”.

ZANCI GABA GOBE INSHA ALLAH03 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

“Ta yaya haka ke faruwa?” Aladdini ya tambaya. “Saboda akwai wani Badawi ɗan fashi ne ana kiran Ajalanu.” Aladdini ya ce, “wannan nufi ne na Ubangiji, idan ina da rabo babu abin da zai same ni har na je na dawo.” Daga nan suka hau zuwa wajen taruwar fatake suna kora dabbobinsu, shugaban ayarin ya garzayo ya sauka daga alfadararsa ya sumbaci hannun shugaban fatake yana mai ce masa, “ya shugabana, na jima ban gan ka ba tun lokacin da ka ɗauke mu aiki ka ɗora mu bisa wannan sana’a.” Shamsuddini ya ce, “kowanne lokaci akwai sha’anin da yake zuwa da shi, haka kuma wanda ya yi wannan wak’ar ya yi gaskiya da ya ce:
Tsoho yana yawo a cikin duniya,
Har gemunsa yana taba gwiwoyinsa.
Ni ko na ce masa ‘me ya sa ka hakan nan?”
Ya ce min, ‘ya zubda k’uruciyarsa’
Na tafi zan nemo kuruciyar nan,
Ita ke sa wa na tuna yin wasa
Da ya k’are wak’arsa sai ya ce da shugaban ayari, “ba ni ne zan yi tafiya ba, wannan ɗan nawa ne zai bi ku.” Uk’amu ya ce, “Allah ya kiyaye shi domin ka.” Suka ce, “Amin.” Sannan shugaban Fatake, Shamsuddini mai alheri ya shirya yarjejeniya a madadin dansa sannan ya nuna masa cewa ya rik’e shi a matsayin ɗansa. Sannan ya ba shi dinari dari ya ce ya rabawa mutanensa. Daga nan ya saya wa ɗansa alfadarai sittin domin labtunsa. Sannan ya sayi fitilu da sauran kayayyaki ya ba shi domin ya kai ga kabarin Shehu Abdulk’adir Jilani. Ya ce da shi, “ya dana, ka rik’e wannan a matsayin mahaifinka, duk abin da ya umarce ka ka aikata. Kuma ka yi masa biyayya.” Daga nan ya juya bisa alfadararsa da bayinsa ya koma gida, a wannan dare ya sa aka sauke Alk’ur’ani mai girma aka yi walima domin girmama Shehu Abdulk’adir Jilani. Da gari ya waye ya dank’a wa dansa dinari dubu goma yana mai cewa, “idan ka shiga Bagadaza ka ga tufafi suna da tamani sai ka sayar, ka juyo, amma idan ka ga suna da araha sai ka sayo kayan da waɗannan dinaran.” Sannan aka shiga lafta kaya a kan alfadarai da rak’umma. Dukkan fatake suka shirya suka yi ban kwana da juna suka tafi zuwa ga birnin Bagadaza.
Shi kuwa Mahmudul Balhi ya shirya domin zuwa birnin Bagadaza ya fitar da laftunsa bayan birni ya kafa rumfa yana cewa a ransa, “ba za ka ji dadin yaron nan ba sai a sahara, inda babu mai tsaronsa babu mai kallon ka balle ya dame ka.” An yi muwafak’a mahaifin Aladdini yana bin sa dinari dubu a wani ciniki da suka k’ulla. Da ya zo yi masa ban kwana sai mahaifinsa ya ce masa, “idan ka isa Bagadaza ka ba wa dana wannan kudin.” Sannan ya hore shi da ya kula masa da dansa, yana mai cewa, “ka rik’e shi tamkar danka.” Aladdini ya shiga cikin ayari tare da Mahmudu Balhi, wanda ya faɗa wa masu dafawa yaron abinci cewar kada su dafa masa komai. Ya zamana yana ciyar da shi daga abincinsa da abinshansa shi da dukkan jama’arsa. Shi kuwa Mahmudul Balhi ya kasance yana da gidaje hudu; daya a Misira, daya a Sham daya a Halbiya daya kuma a Bagadaza. Suka cigaba da tafiya suna shige birane da k’auyuka har suka kusa isa birnin Dimashk’a sai Mahmudul Balhi ya aiki bawansa zuwa ga Aladdini ya same shi yana karatu, ya gaishe shi sannan ya ce, “ubangidana ya ce na fada maka yana da masauki dominka a Dimashk’a.” Aladdini ya ce, “ba zan amsa masa ba har sai na tuntubi babana a wannan tafiyar watau Uk’amu Kamaluddini.” Ya tashi ya tafi wajen Uk’amu ya fada masa. Uk’amu ya hana shi da haka. Suka wuce zuwa birnin Halbiya, a nan ma Mahmudul Balhi wanda ya ji k’unci sakamakon k’in amsa gayyatar da Aladdini ya yi a baya, ya sake aika masa da gayyata karo na biyu, amma Uk’amu ya hana shi. Suka hallara a birnin Halbiya, daga nan suka shirya suka doshi Bagadaza har ya rage tsakanin su da birnin bai wuce yini daya ba. Mahmudul Balhi ya sake aika gayyata ga Aladdini karo na uku Uk’amu ya sake hana shi. Amma sai Alladin ya ce, “babu makawa gare ni sai na amsa wannan gayyata.” Ya daura tufafinsa, sannan ya rataya takobinsa a baya ya tafi wajen Mahmudul Balhi, ya tashi ya tare shi ya zaunar da shi kusa da shi. Sannan ya halarto masa da abinci da abinsha, suka ci suka sha suka wanke hannayensu. Daga bisani Mahmudul Balhi ya karkata ga Aladdini ya sumbace shi sannan ya kama hannunsa ya tausasa su yana shafa masa jiki. Yaro ya ce da shi, “wai shin me kake so ka yi min ne?” Babu kunya ya ce, “na kawo ka wannan wurin ne domin ina so na ji daɗi da kai. Ni da kai za mu aikata abin da mai wak’a ke cewa:
Ka zo wajenmu a wannan lokaci,
Kamar madara na haskakawa
Ka ci a wajenmu ka sha dadi,
Ka samu rabonka da shak’atawa
Ka k’yale abin da da duk ba ka so,
Ka samu jin dadi babu matsawa
Ya matsa gaba gare shi yana so ya taɓa shi, cikin hanzari Aladdini ya mik’e ya fito da takobinsa ya ce, “Allah wadan furfurarka! Kai ba ka tsoron Allah da irin fushinsa gare ka? Ba ka san abin da mawak’i ya faɗi ba cewa:
Ka girmama furfurarka daga abin da zai turmuza ta,
Domin farin abu shi ne mafi saurin daukar k’ura
Da ya gama wak’ar sai ya ce masa, “ka sani waɗannan kayan nawa amanar Allah ce gare ni, ba shi sayuwa kuma ba a sayensa ko da za ka ba da dinari dubu da azurfa dubu. Ya kai wannan daddaudan tsoho ba zan sake mak’wabtaka da kai ba har abada!” Ya juya ya tafi ga Uk’amu ya shaida masa abin da ya faru, ya k’ara da cewa, “wannan mutumin batacce ne babu ni babu shi har abada, ba zan sake cin abincinsa ba balle na jera da shi cikin tafarki ba.” Ya ce da shi, “ya dana ban fada maka kada ka amsa gayyatarsa ba? Amma idan muka rabu da shi yanzu muna tsoron rayukanmu bisa aukuwar barnarsa gare mu. Saboda haka bari mu sake samun wani ayarin tukunna.”

Aladdini ya ce, “ni dai ba zan sake tafiya da shi ba ko da ni kadai ne zan tafi.” Suka yi laftu ga dabobbinsu suka tafi har suka isa ga wani kwari inda Aladdini ya ce a sauka a nan a huta. Uk’amu ya ce kada a sauka a nan. Ya ce da Aladdini, “mu wuce zuwa Bagadaza, idan mun yi azama sai mu isa kafin a rufe k’ofar birnin domin ba a buɗe birnin sai da rana, saboda suna tsoron mabarnata kada su shiga su kwashe musu littattafan sani su jefa a kogin Dujillati.” Aladdini ya k’i amincewa da wannan shawara ya ce, “ya babana, ka sani ban zo birnin nan domin kasuwanci ba, sai domin na ga gari kuma gari ya gan ni.” Uk’amu ya ce, “ya dana muna jiye maka tsoron farmakin Larabawan daji kai da kayanka.” Aladdini ya ce, “wai shin kai ne bawa ko kuwa ni ne mai bauta maka? Ba zan shiga Bagadaza cikin dare ba, da rana zan shiga kowa yana gani na tare da kayana domin su san ni kuma su ga irin dukiyar da nake tafe da ita.” Da ya ji haka sai ya ce, “to shi kenan, ka aikata abin da kake so, ni dai na ba ka shawara managarciya, amma ka iya yin duk yadda kake ganin shi ne daidai gare ka.”
Aladdini ya yi umarnin a sauke laftu daga kan alfadarai aka kafa tantuna, suka aikata haka sannan suka zauna nan har zuwa tsakar dare yayin da ya tashi domin gusar da lalura sai ya hango wani abu yana haske daga nesa. Ya ce da Uk’amu, “menene wancan abin da ke haske?” Uk’amu ya juya ya gasgata ganin, ya tabbatar da cewar kawunan masu ne da kaifin makamai. Kafin su Ankara sai ga Larabawan daji sun tunkaro su. Shugabansu sunan sa Ajlanu Abu Na’ibu Uban Masifu. Suka iso wajen suka ga laftu masu yawa a daddaure. Suka ce da junansu, “daren yau ya yi riba.” Da Uk’amu Kamaluddini suka ji abin da suke fada sai Kmaluddini ya yi kururuwa ya ce da su, “k’arya kuke yi ku k’ananan Larabawa!” Uban Masifu ya soke shi da mashi a k’irji sai da ya bulle ta baya yana walk’iya cikin farin wata, sannan ya jefar da shi k’asa matacce. Sannan Safa’u mai daukar ruwan ayari ya yi kururuwa ya ce, “karya kuke yi miyagun Larabawa!” kafin ya rufe baki wani ya lafta masa takobi a kafada ya tsarge shi gida biyu, ya fadi matacce. Duk wannan abu da ake Aladdini na labe yana kallo. Badawi ya yi umarnin a kewaye ayari, ya sa aka yanka dukkan mutanen Aladdini ba a bar ko guda daya ba, suka kwashe dukkan kayan suka laftawa alfadarai. Aladdini na labe yana kallon su yana cewa a ransa, ‘babu abin da zai kubutar da kai sai ikon Allah.’ Saboda haka ya cire rigarsa, ya jefa a bayan alfadari ya rage sai guntuwar riga da k’aramin wando ke gare shi kawai. Ya lallaba zuwa kofar hemarsa ya ga jini na gudana ya shiga cikin jinin har ya kasance kamar shi ma an kashe shi ne. Badawi Ajalanu kuwa ya ce da yaransa, “shin wannan tawagar daga Misira ta taho ko kuwa daga Bagadaza?” Suka ce masa, “wannan daga Misira ne za su shiga Bagadaza.” Sannan ya ce musu, “ku shiga ku dudduba min matattun nan, ina ji a jikina cewar mamallakin kayan nan bai mutu ba.” Suka shiga birkita gawarwaki suna tsikara musu mashi har suka zo kan Aladdini wanda ya jefa kansa a tsakanin matattu. Yayin da suka gan shi sai suka ce, “kai ka yi bulum kamar ka mutu, to kuwa yanzu za mu yi maka ta gaskiyar.” D’aya daga cikinsu ya girgiza mashinsa ya daidaici k’irjinsa zai caka masa ya rik’a addu’a a ransa ya ambaton sunayen Allah mai girma. Sai kuwa mai niyyar kisan nasa ya juya kan gawar Uk’amu Kamaluddini ya yi mata kaca – kaca. Daga nan suka juya suka tafi, Aladdin ya tsaya yana hangen su har suka bace, daga nan ya rik’a bin su a baya, a baya. Yana kallon wani tsuntsu yana bin su duk inda suka tsaya, shi ma sai ya tsaya. Idan sun tashi shi ma sai ya tashi ya bi su. Sun yi nisa sosai sai Ajalanu Uban Masifu ya tsaya ya ce musu, “ina sansanon wani yana bin mu daga baya.” Sai daya daga cikinsu ya juya baya yana lalube, sai kuwa ya hango Aladdini yana gudu, ya zabura ya bi shi da gudu yana cewa.

ZANCI GABA04 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

Bayan ya gama wannan jawabi sai ya ya kai shi wani ɗaki zananne da dinari, akwai gadaje huɗu a cikinsa, ya sa aka kawo musu abinci mai ɗauke da nama mai yawa. Suka ci suka sha sannan Mahmudu ya karkata domin ya sumbaci kuncin Aladdini ya tare shi da tafin hannunsa ya ce, “ kai har yanzu kana nan a kan ɓatanka? Ba na faɗa maka cewar ba zan sayar da wannan kayan gare ka ko da da dinari ba. Ka nemo wanda kake biɗa ni zan biya maka da jauhari?” Mahmudul Balhi ya ce, “ni ba zan ba ka komai na daga dukiyata ba sai a kan wannan farashin. Na jima ina matuka’ar k’aunarka, Allah ya ji kan wanda ke cewa:
Faɗa mana maganar tsohon nan kai tsoho,
Uban Bilalu maganar nan da za ka faɗe ta
Ƙ auna ba ta warkewa irin ta buk’ata
Har sai an zauna da sumbata da tsiraita
Aladdini ya ce, “a gaskiya wannan ba zai taɓa yiwuwa ba, ɗauki tufafinka da alfadararka ka buɗe min k’ofa na fita.” Ya buɗe masa k’ofa ya fita cikin duhun dare, karnuka na haushi, tsanya na kuka. Yana ta tafiya bai san in da ya dosa ba sai kurum ya hangi masallaci a gabansa a buɗe. Ya kutsa kai ciki ya zauna domin samun mafaka. Can sai ya hangi hasken fitila biyu sun nufo wajen, can sai ga bayi biyu ɗauke da fitilu biye da su wasu attajirai ne. Ɗaya daga cikin su saurayi mai kyakkyawar fuska, ɗayan kuma dattijo mai farin gemu. Sai ya ji saurayin na cewa da dattijon, “ya kawuna na haɗa ka da girman Allah ka dawo min da ‘yar baffana.” Dattijon ya ce, “ba na hana ka sake ta ba. Tun yaushe na sha gargaɗinka bisa haka har kuma ka yi mata saki na k’arshe?” Sannan ya waiwaya ga damansa ya ga Aladdini a zaune kamar jinjirin wata sai ya yi masa sallama sannan ya ce da shi, “wanene kai ya ɗana?” Aladdini ya amsa sallama sannan ya ce, “ni ne Aladdini Abu Shammatu ɗan Shamsuddini shugaban fataken Misira. Na nemi ubana ya ba nii kayan da zan yi fatauci ya haɗa min laftu hamsin.” gami da dinari dubu goma na taho nan Bagadaza har sai da muka iso duhuwar zaki Larabawan daji suka karkashe mutanena suka k’wace dukkan abin da na mallaka na daga dukiya da kuɗi. Na shigo wannan birni ban san kowa ba, ban san inda zan kwana ba, da na ga wannan wuri shi ne na zo domin na samu wurin barci.” Dattijon nan da ya ji haka sai ya ce masa, “ya ɗana me kake gani idan na ba ka dinari dubu da tufafi masu tsada na alfarma da alfadara da tamaninsu ya kai dinari dubu biyu?” Aladdini ya ce, “menene abin buk’ata game da ba ni waɗannan?” Dattijo ya ce, “ka ga wannan saurayin, ɗan ɗan uwana ne, kuma shi kenan shi kaɗai, ina da ɗiya sunanta Zubaidatul Udiyati, ta kasance ma’abociyar kyau da cikar halitta. Na aurar masa da ita ya kasance yana matuk’ar k’aunar ta amma ita ba ta son sa, to saboda yawan saɓani da suke samu ya yi mata saki uku. Yanzu aurensu ya zamana ya haramta sai ta fito daga gidansa ta rabu da shi. To amma yanzu yana tsananin k’aunar ta ya dame ni da lallai na maida masa ita, ni kuwa ba zan jirkita haram zuwa halal ba. Na shaida masa wannan aiki bai zama bisa doron shari’a ba har sai ta yi wani auren tukunna. Mun amince da shi cewar za mu aurar da ita ga bak’o domin gudun abin kunya ga jama’ar da suka san mu. To tun da kai bak’o ne muna gayyatarka zuwa gare mu domin mu aura maka ita. Sai ka kwanta da ita a wannan daren washegari ka sake ta mu kuma za mu ba ka abin da na faɗa.” Aladdini ya ce a cikin ransa, “wallahi kwana cikin ɗaki tare da amarya ya fi alheri da kwana a kan titi cikin duhu da sanyi!” Ya amince da haka. Suka tafi zuwa ga alk’ali wanda tun da ya haɗa ido da Aladdini ya ji yana k’aunarsa. Ya ce da dattijo, “mecece buk’atarka?” Ya amsa cewa, “muna so ka rubuta mana takardar aure na ‘yata da wannan saurayi bisa sharaɗin sadaki dinari dubu goma. Idan ya kwana da ita zai sake ta da safe, za mu ba shi alfadara da tufafi kowanne ya kai dinari dubu ɗaya da kuma dinari dubu na tsabar kuɗi. Amma idan bai sake ta ba, zai biya mu wannan kuɗi na dinari dubu goma bisa wannan sharaɗi.” Aka rubuta takarda a kan haka, sannan mahaifin yarinyar ya tafi da Aladdini ya ba shi tufafi masu kyau sababbi sannan ya wuce da shi gidan da ‘yarsa take ya bar shi tsaye a k’ofar gida ya shiga ciki ya ba ta takardar ya ce, “rik’e wannan yarjejeniyar taki da kanki, na aurar da ke ga wani saurayi mai kyawon gani sunansa Aladdini Abu Shammata, sai ki more shi gwargwadon morewa.” Ya tafi ya bar ta zuwa gidansa.
To tsohon mijin nan yana da wata tsohuwar kuyanga wadda yake aikenta wurin Zubaidatu yana kyautata mata, ya je wurinta ya shaida mata labari sannan ya ce mata, “wallahi uwata idan Zubaida ta ga saurayin nan za ta bashe ni ta juya min baya, ba za ta taɓa yarda da ni ba.

Ina so ki tashi yanzu ki shirya yadda ba za ta ga fuskarsa ba.” Ta ce da shi, “kada ka damu, zan yi maka haka albarkacin k’uruciyarka da ba na so ta wulak’anta, ba zan bari ya kusace ta ba ma.” Ta tashi ta tafi wurin Aladdini da ke tsaye a k’ofar gida ta ce masa, “ya ɗana ina da wata shawara gare ka, kuma ina rok’onka don girma Allah ka yarda da maganata domin ina jiye maka tsoron wannan matar.” Yaro ya ce mata, ‘wacce shawara ce?” Tsohuwa ta ce, “kada ka kusanci yarinyar nan kuma kada ka taɓa jikinta.”
“Ina dalili?” Aladdini ya tambaya cikin kokwanto. Tsohuwa ta ce, “saboda jikinta cike yake da cutar kuturta to ni ina tsoron kada ta shafa maka cutar da k’uruciyarka abar bege.” Da ya ji haka sai ya ce, “to ba na buk’atarta.” Tsohuwa ta shiga wajen Zubaidatu nan ma ta shirga mata irin wannan k’aryar a kan Aladdini, yarinya ta ce, “bana buk’atarsa, amma zan bari ya kwanta shi kaɗai da safe ya kama gabansa.” Sannan yarinya ta kirawo kuyanga ta ba ta abinci ta ce a kai masa, ya karɓa ya ci mai yawa har ya ishe shi ya sha ruwa. Sannan ya zauna yana karanta suratul Yasin da murya mai daɗi da cikakken tajwidi. Yarinya na zaune tana sauraron sa ta ji murya mai matuk’ar daɗi tamkar Annabi Dawuda ke karanta Zabura. Nan take ta ji son sa ya cika mata zuciya. Ta kuma tabbatar mai cutar kuturta muryarsa ba za ta yi daɗi kamar haka ba. A k’ark’ashin zuciyarta ta ce, “Allah ya kwashewa tsohuwar banzar nan albarka. Tabbas wannan ba zai zama muryar mai cutar kuturta ba, duk k’arya ce ta tsara a kansa!” Da ta ji ya yi shiru sai ta dauko molo ta gyara tsarkiyarsa sannan ta kaɗa shi irin yadda gwanaye ke yi ta rera waɗannan baitoci da murya mai daɗin gaske:
Ina k’aunar mai k’amshi mai farin idanu,
Mai murya mai tafiya kamar reshen bishiya
Ana hana mini ganinsa mai gwanin daɗi,
Nufin Allah ne ya haɗa da wanda ya yi niyya
Yayin da ya ji ta yi shiru shi kuma ya gama karatun sai ya wak’e waɗannan baitoci:
Na yi sallama ga mai k’amshi a ɓoye cikin rufi,
Ba a taɓa rasa wardi a gidan mai gona ba
Yarinya ta mik’e tsaye ta ji k’aunarsa ta daɗa shiga ranta. Ta yaye labule, Aladdini ya gan ta, sannan ta wak’e waɗannan baitoci:
Haske yake k’warai tamkar tauraro,
Numfashinsa da ganinsa kamar na barewa
Na auka tekun so zuciyata a gare shi
Na rasa me zan yi domin mallakawa
Ta matso kusa da shi tana mai karkaɗa kuturinta tana juya abin da ke ɓoye gare ta. Kowanen su ya kalli ɗan uwansa irin kallon da ya kimanci irin sa dubu. Yayin da kibiya ta tabbata a cikin zuciyarsa ya rera waɗannan baitoci:
Diyar watan sama ta riske a cikin duhun dare,
Na haɗu da ita idona huɗu duk sun ga wata biyu
Ta sake matsowa kusa da shi ya rage tsakaninsu bai fi taku biyu ba, sai ya rera wannan baitin:
Tana da ɗauri kitso uku a bisa kanta,
Maimakon dare ɗaya yau ya zama huɗu
Ta kalli wata mai haske da goshinta,
Haskenta ya sa hasken wata ya daɗu
Ta sake matsawa kusa da shi za ta rungume shi sai ya ja da baya ya tsaya, ya ce mata, “matsa daga can nesa kada ki harbe ni da cuta.” Ta yaye kafaɗunta har k’irjinta ya bayyana. Farin k’irjinta kamar farar k’asa wadda ruwa ya bi ta kan ta.” Ta ce da shi “kai ya kamata ka yi nesa da ni domin kana ɗauke da cutar kuturta kada ka shafa mini.” Ya cika da mamaki sannan ya ce, “wa ya faɗa miki haka cewar ni kuturu ne?” Ta amsa masa da cewar tsohuwar kuyangar nan wadda ta shigo ɗazu.” Ya ce, “to ai ni ma ita ce ta gargaɗe ni a kan ki, ta ce min kina fama da albaras.” Sannan ya buɗe hannayensa ta gan su mik’ak’k’u babu karkata ballantana alamar cuta, suna santsi kamar jauhari ko azurfa. Da ta ga haka sai ta rungume shi a k’irjinta, shi ma ya rungume ta. Ta rik’e shi ta maraita da shi bisa bayanta sannan ta kwanta ta cire tufafinta sannan

2 Comments On HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI
avatar
saidou

1 year ago

Reply

Tyhfhhhjg

avatar
ummitah

1 year ago

Reply

Wow

Please Login or Register in order to submit comment