Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

“wallahi sayan ta na yi.”
“A ina ka saye ta?” Khalifa ya tsare shi da ido. Ya yi shiru yana inda – inda.
Dogarai suka shiga laftarsa da dorina har ya yi fitsari sannan wahala ta sa ya yarda shi ya aikata satar, kuma ya faɗi duk yadda aka yi. Khalifa ya harzuk’a ya cika da fushi ya sa aka kama Sarki Halidu.11 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

da fushi ya sa aka kama Sarki Halidu saboda faɗin Amadu Kamakin na cewa da matarsa aka shirya komai. Sarki Halidu ya ce, “Allah ya ba ka nasara, kodayake an riga an rataye Aladdinu bisa rashin da wannan makircin da aka k’ulla, amma ni kam wallahi ba ni da hannu a ciki domin ban san lokacin da duk suka shirya hakan ba tsakanin matata da uwar Amadu da shi kansa Amadun.” Aslanu ya faɗi gaban Khalifa ya ce, “ya Sarkin Musulmi, ina rok’on alfarma domin uban rik’ona Halidu.” Khalifa ya amince da haka, sannan ya ce da shi, “me ka aikata da uwar shi wannan yaron?” Ya ce, “tana nan tare da ni.” Khalifa ya ce “na hori matarka da yanzu – yanzu ta mayar da dukkan suturanta da ta kwace mata da kayan adonta duka, sannan a mayar da ita gidanta da matsayinta na matar aure ba kuyanga ba. Ya ce na ji, na amince, ya tafi zuwa ga matarsa ya umurce ta kamar yadda Khalifa ke buk’ata. Ta aikata hakan sannan da kan sa ya tafi ya cire takardar k’wace gidan ya mik’a wa Aslanu mukullan.
Khalifa ya waiwaya ga Aslanu ya ce, “faɗa min buk’atarka kuma.” Aslanu ya ce, “buk’atata ya Sarki ka sada ni da mahaifina.” Khalifa ya yi kuka mai yawa sannan ya ce, “kai kam haka kake tamkar mahaifinka. Amma wallahi na yi burin a ce yana nan a duniyar nan da na yi masa alheri fiye da na baya.” Ahamadu Danafi ya matso gaba ga sarki ya ce, “ni zan yi maka bayani, amma ina neman amanarka.” Sarki ya ce na ba ka amanata da kiyayewata.” Sannan Ahamadu Danafi ya ce, “hak’ik’a Aladdini bai mutu ba, yanzu haka yana can birnin Iskandariya yana sayar da kwancen kaya.” A nan asubahi ta riski Shaharzad ta katse zancenta mai dadin saurare.
DARE NA 267
A dare na ɗari biyu da sittin da bakwai, Shaharzad ta ce na samu labari ya kai wannan hamshakin Sarki, da ya ji haka sai Khalifa ya umarci Ahmadu Danafi da ya tafi ya taho da Aladdini, ya ba shi dinari dubu goma domin tsaraba ya tafi birni Iskandariya. Shi kuwa Aladdini yana nan yana cinikinsa, ya sayar da duk abubuwan da ya tarar a rumfar nan illa wasu ‘yan tarkace marasa yawa.

Daga cikin su akwai wata jaka a ɗaure da kaya ciki. Wata rana ya yi nufin ya gyara kayan sai ya karkaɗe wannan jakar ya girgiza ta sai ga wani dunk’ulen jauhari ya faɗo daga ciki, girmansa zai iya cika tafin hannu. Daga jikinsa kuma an ɗaura wata igiya ta zinariya. Dunk’ulen jauharin yana fuskoki biyar, watau siffar gizago an yi rubutu iri – iri ga sunaye nan birjik da ɗalamisai. Ya shafa kowacce fuska ya ga babu abin da ya faru, sai ya ce a ransa, wannan irin kayan ‘yan damfara ne. sai ya rataye abin a gaban rumfarsa yana reto. Ana nan rannan sai ga wani babban mutum ya zo wucewa sai ya ga dunk’ulen jauharin yana reto a rumfar, ya shigo cikin rumfar ya ce da Aladdini, “shin wannan jauharin na sayarwa ne?” Ya ce, “duk abin da ka gani a nan na sayarwa ne.” Ya ce masa za ka sayar min da wannan akan dinari dubu tamanin?” Ya ce, “albarka.”
“Ka sayar dinari dubu ɗari?” Ya ce, “na sayar maka, amma kuɗi hannu babu bashi.” Dan Sarki ya sa bawansa ya biya kuɗin. Bawan ya ce da Aladdini, “ba zan iya kwaso wannan adadin kuɗi ina yawo da su ba, saboda a Askandariya akwai ɓarayi da yawa. Amma ka bi ni jirgina na ba ka rigiza ta ulu ɗan Arjul da rigiza ta ta haɗalashi da ta ashafar da rigizar juha.” Aladdini ya rufe rumfarsa ya ba wa mak’wabcinsa mukullan ya ce, “ga ajiya har na je na dawo. Za ni na karɓo kuɗin hirjina, idan na jima ban dawo ba har Ahmadu Danafi, wanda ya kawo ni nan ya zo, sai ka faɗa masa inda na tafi.”
Sannan ya tafi tare da bawan zuwa jirgin ruwan. Da suka je ya fito da kuɗi ya ba shi, sannan ya ba shi rigiza huɗu kamar yadda ya yi alk’awari. Aladdini ya duba ya ga komai ya yi daidai. Sai bawan ya ce masa, “ya shugabana ba za ka girmama ziyarar nan ko da ruwan sha ba?” Ya ce a kawo masa ruwa ya sha. Aka kawo masa ruwa, ashe akwai sammu a cikin ruwan. Yana sha sai ya bingire a nan ya yi ta sharar barci. Suna ganin haka sai suka ɗaɗɗaure shi suka sa a ɗaki sannan suka kwance igiyar jirginsu suka nausa cikin bahar maliya. Sai da suka yi nisa a ciki sannan suka ɗauko wani magani kishiyar wanda suka soma ba shi. Ya shak’a, ya farfaɗo. Ya duba ya gan shi ya ɗaure, ya ce, “nan a ina nake?” bawan ya ce masa, “yanzu ka zama k’ark’ashin ikona ba ka da ikon zuwa ko’ina sai da iznina.” Ya ga wannan babban mutumin zaune a cikin jirgin yana dariya da wannan hirjin a hannunsa. Ya kalle shi ya ce, “wanene kai?” Ya ce masa, “ni ɗan fashin teku ne, kuma ina da burin na tafi da kai inda zuciyata ta raya min.” Suna cikin wannan halin sai ga jiragen ruwa na Musulmi sun dawo daga fatauci su arba’in. Nan da nan mafashin nan wanda yake nasara ne, ya zabura kan su, cikin k’ank’anin lokaci ya gama da su ya mallake dukiyar gaba ɗaya. Su kuma ya ɗaɗɗaure su ya haɗa su da Aladdini waje ɗaya. Suka cigaba da tafiya har suka isa birnin Jimwatu. Mafashin nan wanda ya kama Aladdini ya sauka tare da shi ya gabata zuwa ga wajen ɗaure jirage. Yayin da suka firfito sai ga wata yarinya nan sanye da mayafi ta rufe furskarta ta ce, “yalla kun zo da hirji da mamallakinsa?” Ya ce, “na zo da su duka.” Sai ta ce, “to ba ni hirjin.” Ya dank’a mata sannan ya koma cikin jirgin ya buga bindiga shaidar sun dawo, Sarkin garin ya taho gare shi ya ce masa, “yaya labarin tafiya?” Ya ce, “tafiya ta yi sa’a, kuma mun kamo mutane arba’in da ɗaya duk musulmi da kayan fataucinsu.” Sarki ya ce a tafi da su zuwa fada. Aka tafi da ɗaurarrun nan har da Aladdini zuwa fada, Sarki ya zauna aka rik’a shiga da su wajensa. Na farko Sarki ya ce masa “daga wanne gari kake?” Ya ce “daga Iskandariya.” Sarki ya c, “dogarai ku buge wuyan wannan.” Nan take aka fille masa kai. Aka shigo da na biyu, na uku na huɗu na biyar duk wanda ya tamabaya garinsu ya faɗa masa sai ya ce a fille masa kai. Haka aka yi ta kashe su har aka zo kan Aladdini wanda yake cewa a ransa, “Allah ya ji k’an ka Aladdini, yau kam ba ka zama wannan duniyar, kwananka ya k’are.” Sarki ya ce masa, “daga wanne gari kake?” ya ce “daga Iskandariya.” Sarki ya ce, “dogarai ku raba wuyansa da jikinsa!” Wani dogari mai girman jiki da k’arfi ya ɗaga takobi zai fille masa kai sai ga wata tsohuwa mai mummunar kama ta shigo. Sarki ya mik’e domin girmama ta. Ashe ita ce k’anwar mahaifiyar sarkin. Ta ce da shi, “ya sarki, ba na sha faɗa maka cewar idan jiragenka sun dawo da ɗaurarru, bayan ka tambaye su garuruwansu kada ka kashe su duka ka rage biyu ko uku domin hidima a ɗakin bauta ba?” Sarki ya ce, “ya uwata kin so ki makara, amma ɗauki wannan ɗayan da ya yi ragowa.” Ta juya ga Aladdini ta ce da shi, “shin za ka yi hidima a ɗakin bauta ko kuwa na bari sarki ya kashe ka?” Aladdini jikinsa na ɓari ya ce, “zan yi hidima a ɗakin bautar.” Ta ɗauke shi suka yi tafiya zuwa wani gida inda suke taruwa su yi bauta. Sai ya ce mata, “wanne irin aiki zan rik’a yi kullum?” Ta ce, “’yan ayyukan ba su da yawa, ya zama wajibi ka tashi da duku – duku ka ɗauki alfadaraina guda biyar ka tai daji ka Dauko itacen dahuwa sannan ka ɗauko ka kawo, kada ka yarda itacen dahuwa ya k’are mana. Sannan ka fita zuwa ɗakin bauta ka goge ko’ina, ka cire dardumar ka karkaɗe ta, sannan ka tafi ga madafa ka kai musu tukwanen girki, ka kai musu albasa, idan sun ce ka yanka sai ka zauna ka yanka, sai ka tafi ɗebo ruwa ka cika kwatarniya huɗu. Daga nan sai ka kora dabbobina ba su da yawa, duka duka su ɗari uku da sittin da shida ne, amma suna da fitina ka lura kada su shiga gonar mutane. Wurin da za ka je kiwon akwai gonata da na shuka albasa, ka ba ta ruwa kowanne fangali ka tabbata ya koshi. Idan ka dawo sai ka wanke kwanukan cin abinci sannan ka dauka ka ajiye wa kowanne mabiyi a gaban teburinsa.” Da Aladdini ya ji wannan yawan aiki sai ya ce, “mayar da ni wajen sarki ya kashe ni, ba zan iya wannan ɗawainiya ba.” Tsohuwa ta ce, “idan ka natsu ka yi aiki mai kyau, ya fiye maka alheri daga mutuwa, ko kuwa na bar Sarki ya kashe ka.” Da wannan kalamai Aladdini ya zauna da nannauyar zuciya, daga bisani ya amince ya yi hidimar gwargwadon k’arfinsa.
To a cikin ɗakin bautar nan akwai makafi, kuma guragu su goma, sai ɗaya daga cikinsu ya ce masa, “kawo min tukunya.” Ya kawo masa, ya yi fitsari a ciki sannan ya gundura kashi, ya ce masa. “je ka zubar ka dawo.” Ya je ya zubar ya dawo. Makahon ya ce, “Allah ya yi maka albarka albarkacin Masihu.” Daga can sai ga tsohuwar nan ta zo tana faɗa ta ce masa, “don me ba ka gama aikinka a ɗakin bauta ba har yanzu?” Ya dube ta a fusace ya ce, “hannu nawa gare ni da zan iya yin komai a lokaci guda?” Ta ce, “amma kai wawa ne, mahaukaci mara tunani, na kawo ka nan ba domin komai ba sai domin ka yi min hidimar aiki tuk’uru, ungo wannan sandar.” Ta mik’a masa sandar tagulla mai ɗauke da alamar gicciya ta ce, “ka tafi wajen wakilin garin nan ka ce da shi, ‘ina kiran ka bauta domin albarkacin Masihu shugaba.’ Zai maka ladabi da biyayya bisa ga haka. Sannan ka ɗauko alkama ka bushe ta sannan ka nik’a ka juya ka zuba ruwa ka yi mana gurasa sai ka zuzzuba mana a kwanukanmu. Idan wani zai yi maka fitsara ka dake shi kada ka ji tsoron kowa.” Ya ce “na ji na yi biyayya.” Ya rik’a aikata wannan aikin saɓanin na farko, ya rika tattara k’arami zuwa babba ga aikinsa, duk wanda ya taɓa shi sai ya rama. Haka har shekara goma sha bakwai. Ana nan wata rana sai tsohuwa ta ce masa, “tashi ka fita daga wannan gidan.” Ya ce, “ina za ni?” Ta ce, “ka tafi wajen ɗaya can waje ka kwana koko gidan ɗaya daga abokanenka.” Ya ce, “me ya sa kike kora ta daga ɗakin bauta inda na saba da shi?” Ta ce, yau Gimbiya Husnu Maryam ‘yar babban sarki Yuhana, mai mulkin birnin nan za ta kawo ziyara ɗakin bautar nan, bai kamata ga kowa ya gan ta ba.” Da ya ji haka sai ya yi kamar ya amince da umarnin, amma a k’ark’ashin zuciyarsa cewa yake yi, ‘ai kuwa sai na ga wannan matar, shin kyakkyawa ce kamar irin matanmu ko kuwa ba ta kai su kyau ba ko ta ɗara su? Babu inda za ni sai na kalle ta sosai domin na sakankance da kamar ta.” Ya samu wata malafa ya ɓoye yana lek’e. Babu jimawa sai ga ‘yar sarki ta shigo, ya yi duba zuwa gare ta, duban da ke haifar da dubun hasara, ya gan ta ma fi kyawu daga matan da ya gani, tana haske kamar wata ɗan dare sha huɗu yayin da yake tserereniya da gajimare. Ya ga a tare da ita wata yarinya a tare da ita.
A nan asubahi ta riski Shaharzad ta katse zancenta mai dadin saurare.
DARE NA 268
A dare na ɗari biyu da sittin da takwas, Shaharzad ta ce na samu labari ya kai wannan hamshakin sarki, Aladdini ya duba zuwa gare ta ya ga a tare da ita akwai wata yarinya, sai ya ji matar ta ce, “ya Zubaidatu na kasance mai farin ciki kasancewa tare da ke, na kuma nishaɗantu.” Ya zuba wa yarinyar nan ido sosai ya lura ba wata ba ce face matarsa Zubaidatul Udiya wadda ta kasance ta mutu. Sai ya ji ‘yar sarki na cewa, “a yi mana kiɗa ya Zubaidatu.” Sai ya ji ta ce, “ni ba zan yi kiɗa ba har sai kin amince da buk’atata kin kuma cika alk’awarin da kika yi min.” Daga jin muryarta ya hak’ik’ance matarsa ce dai da ta riga mu gidan gaskiya.
“Wanne alk’awari na yi miki?” ‘Yar sarki ta tambaye ta.
“Kin yi min alk’awarin za ki sadar da ni da mijina Aladdini Abu Shammata, mai gaskiya mai rik’on amana.” ‘Yar sarki ta ce, “Ya Zubaidatu ki yi farin ciki, idanunki su yi sanyi, ki yi mana kiɗan murna da farin cikin sake saduwarki da mijinki Aladdini.”
Zubaidatu ta zabura tana mai cewa, “yana ina?” Husnu Marya ta ce, “Yana waccan k’ofar yana sauraren mu.” Nan da nan Zubaidatu ta fara kaɗa molo da wani irin sauti mai sa zuciyar mai bege ta narke, mai sa kurman dutse ya yi amo, mai sa ganga ta fashe. Yayin da Aladdini ya ji wannan kiɗa sai ya tuna lokacin da suke tare, ya ji ya karkata gare ta, nan take ya fito daga inda yake ɓoye, Zubaidatu na ganinsa ta jefar da kayan kiɗa ta ruga gare shi ta rungume shi a k’irjinta. Shi ma ya rungume ta suka faɗi k’asa sumammu. Husnu Maryam ta taso bisa gare su ta yayyafa musu ruwan wardi suka farfaɗo.12 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

wardi suka farfaɗo. Ta ce musu, “ku yi farin ciki Allah ya sake gama fuskokinku.” Aladdini ya ce, “mun gode miki ya sarauniya.” Ya juya ga Zubaidatu ya ce mata, “ni dai na tabbata kin mutu har mun binne ki ni da mahaifinki, amma yaya haka ta faru kuma?” Ta ce, “bisa gaskiya dama can ban mutu ba, wani k’aton aljani ne ya ɗauke ni ya kawo ni nan. Wannan da kuka binne aljana ce ta kwaikwayi irin kamannina ta yi kururuwa kamar yadda ni zan yi ta faɗi a zaman na mutu. Bayan kun binne ta, sai ta fasa kabarin ta ci gaba da hidimtawa uwargijiyarta gimbiya Husnu Maryama. Ni kuwa ban san inda kaina yake ba, yayin da na buɗe idanuna sai na gan ni tare da wannan gimbiyar na ce da ita, ‘me ya sa kika kawo ni nan wurin?’ Ta ce, ‘zan kawo miki mijinki nan Aladdini Abu Shammata ki saki jikinki ki zama abokiyata.’ Hankalina ya kwanta, na zauna sosai na ce da ita, ‘to yaya za a yi?’ Ta ce, ‘amma ni ma zan aure shi sai mu zama tare yau darenki gobe nawa.’ Da na ji haka sai na ce, ‘na ji na amince, amma dai yanzu ta yaya zan gamu da mijina?’ Ta ce, ‘an rubuta a goshinsa cewa k’addara za ta kawo shi garin nan. Da zarar ya kammala abin da Allah ya nufe shi babu makawa sai ya zo nan gare mu. Amma kafin lokacin da haka za ta faru ki cigaba da nishaɗantar da mu da launukan kiɗa da wak’ok’inki masu nishaɗantar da mu.

Na zauna cikin waɗannan shekaru ina ma begen ganinka a kullum har zuwa yau ɗin nan da muka sadu a wannan waje.” Daga nan Husnu Maryam ta juya gare shi ta ce, “ya shugabana Aladdinin, shin ka amince na zama daga cikin iyalinka a matsayin matarka? Yana jin haka sai ya ce, “ta yaya haka za ta kasance alhali ni Musulmi ke kuma Banasariya? Ni kam ina gudun haka.” Ta ce, “ Allah ya kiyaye na zama daga cikin kafirai! Ni Musulma ce shekaru sha takwas kenan ina mai mik’a wuya ga ubangijin sammai da k’assai. Ni kuɓutacciya ce ga duk wani abu da ya saɓawa addinin Islama.” Ya ce mata, “ya gimbiyata, ni dai burina na koma zuwa ga garina.” Ta amsa masa ta ce, “babu makawa cewa na ga an rubuta a goshinka cewa za ka aiwatar da wani abu tukunna. Na hane ka da gaggawa. Kuma ina mai sanar maka cewa ka samu magaji daga Yasmin sunansa Aslanu, wanda yanzu haka yana zaune bisa matsayinka a fadar Khalifa. Kuma ina mai faɗa maka cewa yanzu gaskiya ta bayyana, k’arya ta gushe, Allah ya bayyana asirin da yake ɓoye daga satar da aka yi wa Khalifa shekara sha bakwai da suka wuce, yanzu an tabbatar da cewa Amadu Kamakin shi ne babban munafuki ma ci amana, maha’inci, yanzu haka yana nan tsare a kurkuku.
Kuma ka sani cewa ni ce na aika da wannan hirjin na jauhari na sanya masa fuskokin nan biyar kuma na rataya masa sark’ar zinariya na aika aka sa maka a jaka yadda za ka gan shi, sannan da ka rataye shi sai na aika da wannan mutumin cikin siffar attaijiri, domin shi ya kasance yana burin ya aure ni, sai na faɗa masa cewar ba zan amince da haka ba sai ya kawo ka tare da wannan hirjin. Na ba shi jaka ɗari, na aike shi gare ka. Da ma ya kasance shi mafashi ne kuma mayak’i. Yayin da ya kamo waɗannan mutane arba’in aka soma kashe su, sai na yi sauri na aiki wannan tsohuwar domin ta ceto ka.” Da ya ji haka sai ya ce, “Allah ya saka miki da alheri, kin kyautata min k’warai.” Sa’annan Husnu Maryam ta jaddada kalmar shahada a hannunsa, yayin da ya gasgata maganarta da karbar musuluncinta sai ya yi hamdala sannan ya ce, “ya gimbiyata, faɗa min alfanun wannan hirjin da kika aiko min daga ina ya fito?” Ta ce wannan hirjin ya kasance daga tsohuwar taska na mutanen farko, yana da daraja biyar game da buk’ace – buk’ace tare da su. Kakata wadda ta haifi ubana boka ce wadda ta k’ware wajen ayyukan sihiri ta kasance kuma tana bankaɗe – bankaɗen sirrin tsohuwar taska gami da bayanansu, to a haka ta samu wannan hirjin. Ni kuma na samu daga wajenta. Yayin da na isa shekaru goma sha huɗu na balaga sai na soma karanta Linjila da wasu littattafai, a inda na ga ana ambatar sunan annabi Muhammadu, mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Na ga cewa an ambace shi a littattafai huɗu su ne, Attaura da Zabura da Linjila da K’ur’ani, to sai na sakankance cewa addinin Musulunci na fiyayyen halitta shi ne gaskiya, don haka na rungumi Musulunci tun daga wannan lokacin. Na mik’a wuya da bauta ga Allah maɗaukakin Sarki wanda ba ya karɓar kowanne addini sai Musulunci. Yayin da kakata ta kamu da rashin lafiya ta ba ni wannan hirjin ta koya min yadda ake aiki da waɗannan fuskoku guda biyar. Haka kuma kafin ta riga mu gidan gaskiya mahaifina ya taɓa ce mata ‘ina so ki buga k’asa ki faɗa min abin da yake na daga al’amarina.’ Ta zana k’asa ta ce masa cewa zai halaka ta hannun wani da yake kamamme daga Askandariya. Daga wannan ranar ya rantse duk wanda aka kawo daga Askandariya zai kashe shi nan take, kuma ya faɗa wa mafashin nan cewar duk jirgin da ya haɗu da shi na Musulmi ya kamo su, kuma idan ya samu ɗan yankin Askandariya ya kashe shi ko ya kai shi wurin sa. Haka mafashin nan ya yi ta yi har ya kashe mutane da dama. Lokacin da kakata ta mutu sai na ɗauki faifai na zana k’asa domin gano wani abu daga al’amarina na wanda zai aure ni. Na duba sosai sai na ga babu shakka mijina shi ne wani mutum da ake kira Aladdini Abu Shammata, mai gaskiya da rik’on amana. Da haka na zauna ina jiran lokacin da za ka zo wurina inda lokacin haka ya yi.” Aladdini ya rik’e hannun matarsa ya ce, “ya gimbiya ni dai burina na koma garinmu.” Ta ce, “idan abin ya zama haka, ni ma ina so. Tashi ka biyo ni.” Ta kai shi wani wuri ta ɓoye sannan ta shiga fada wurin mahaifinta wanda ya ce da ita, “ya ke ɗiyata, yau zuciyata na cike da ɓaci a wannan rana, ina so ki zauna nan tare da ni mu nishaɗantu da giya ni da ke.” Ta zauna kusa da shi ta sa aka girka tebur sannan aka shirya kasaken giya. Ta rik’a cikawa tana ba shi yana kwankwaɗewa yana surutai har ya yi maye sannan ta faki idanunsa ta zuba masa guba a ciki. Da ya sha ya tuntsure da bayansa. Da ta ga haka sai ta zabura ta fito da Aladdini inda ta ɓoye shi ta ce, “zo nan yanzu ne lokacin da za ka yi maganin mak’iyinka na sa ya yi maye na ba shi sammu yana ta sharar barci ka aikata masa abin da ka yi nufi.” Ya fito ya isa wurin ya same shi rigingine, ya juya shi bai iya yin komai ba, ya ɗaure hannuwansa, ya dabaibaye shi, sannan ya ba shi.

insha Allah gobe zamu gaba hikayar duka13 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

Aladdini ya ɗaɗɗaure Sarki Yuhana sannan ya shak’a masa kishiyar maganin sammu, ya farfaɗo ya ga ‘yarsa Husnu Maryam da Aladdini na zaune kan k’irjinsa. Ya ce, “haba ‘yata don me za ki aikata min haka?” Ta ce, “hak’ik’a ni ‘yar ka ce, amma na musulunta na mik’a wuyana ga Ubangijin talikkai, yanzu gaskiya ta bayyana k’arya ta gushe, ni tuni na guje wa k’arya na rungumi gaskiya. Na mik’a fuskata zuwa ga addinin Islama, duniya da lahira. Ni nufina shi ne ka musulunta, idan ka musulunta shi kenan ka tsira da ranka da dukiyarka da mulkinka. Amma idan ka k’i haka to mutuwarka ta fi da rayuwarka.” Aladdini ya rik’a lallaɓarsa domin ya karɓi kalmar shahada shi kuma yana faɗin miyagun kalamai. Da suka hak’ik’ance ba zai saduda ba sai Aladdini ya fitar da takobi ya soke shi daga hak’ark’arin dama zuwa na hagu. Sannan ya fitar da takarda ya rubuta abin da ya wakana gaba ɗaya ya mak’ala a goshin gawar Sarkin, sannan ya ɗauki dukkan abin da yake maras nauyi a fadar nan na daga dukiya ya koma wajen bauta. Gimbiya Husnu Maryam ta ɗauko wannan hirjin ta rik’e a hannunta sannan ta shafa shi sai ga gado ya bayyana a gabansu, suka hau ita da Aladdini da matarsa sannan ta ce, “alfarmar sunayen da ɗalamisai da ilman addinin da jikin wannan hirji, ina so kai gado ka tashi da mu!” Gado ya tashi sama kamar tsuntsu ya kai su wani bigire mai yawan tsirrai da korayen bishiyu, sai gimbiya ta karkata hirjin ya kalli k’asa, sai gado ya yi k’asa da su. Ta juyo da wata fuskar hirjin ta ce, “ina son rumfuna a wajen.” Nan take sai ga rumfa kafaffiya, ta bayyana tare da kujeru, suka shiga suka zauna. To wajen duk da yake akwai ciyayi amma babu ruwa, sai ta juyar da wata fuskar ta ce, “albarkacin sunayen Allah tsarkaka da ke wannan hirji, ima so bishiyu su kafu a wurin nan tare da k’orama mai gudana.” Nan take kuwa sai ga bishiyu sun mik’e, ruwa na gudana tsakaninsu. Suka yi alwalla, suka yi salla sannan suka sha suka yi wanka. Sannan ta juya zuwa ga fuska ta hudu ta ce, “ina neman mazauni da kwanukan abinci.” Nan da nan sai ga shi ya bayyana da dukkan nau’ukan abinci da abinsha da kayan marmari da nama dangi iri daban – daban. Suka ci suka

2 Comments On HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI
avatar
saidou

1 year ago

Reply

Tyhfhhhjg

avatar
ummitah

1 year ago

Reply

Wow

Please Login or Register in order to submit comment