Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sha suka yi nishaɗi da farin ciki. Wannan kenan game da Aladdini da matarsa Zubaidatu da Gimbiya Husnu Maryam.
Game da mahaifin Husnu Maryam kuwa, babban ɗansa ya shiga gare shi ya same shi matacce da takardar nan rataye a goshinsa, ya ɗauka ya karanta ya fahimci abin da ta k’unsa. Ya fita ya shiga neman ‘yar uwarsa amma bai gan ta ba. Ya tafi wurin tsohuwa a ɗakin bauta ya tambaye ta Aladdini ta ce tun jiya da ya fita bai dawo ba. Nan da nan ya juya ya yi kururuwa ga dakaru mahaya dawaki suka zo ya faɗa musu abin da ya faru. Nan da nan suka hau suna masu gaggawa suna sukuwa har suka isa wajen rumfar nan. Husnu Maryam ta ɗaga kai ta hangi k’ura a murtuke tana murɗawa sararin samaniya. Ta mik’e tsaye da hanzari, yayin nan k’urar ta yaye ta ga yayanta tare da askarawa tunjim cikin kayan yak’i. Ya daka musu tsawa ya ce, “ko sama za ku tashi sai mun bi ku.!” Ta dubi Aladdini ta ce masa “ka iya yak’i sosai?” Ya girgiza kai ya ce, “ba abin da na sani game da yak’i ballantana gumurzu, ina rik’e da takobi balle jifa da mashi.”
Da ta ji haka sai ta ɗauko hirji ta juya fuska ta biyar mai ɗauke da zanen sadauki ta faɗi wasu kalamai sai ga wani mayak’i ya bayyana daga tsakiyar sahara yana gudu yana sukuwa tunjim da shi cikin kayan yak’i. Yana zuwa ya hau kan su da sara da suka har ya karkashe su baki ɗaya sannan ya ɓace. Daga nan ta ce da shi, “ina za mu daga nan, Alk’ahira ko Askandariya?” Ya ce, “mu tafi Askandariya.” Ta sa suka hau bisa gadon nan sannan ta yi addu’a, cikin k’ank’anin lokaci sai ga su a k’ofar shiga birnin Askandariya. Suka shiga cikin birnin, Aladdini ya ɓoye matar a wani sak’o, sannan ya samo manyan mayafai ya ba su suka rufe jikinsu suka tafi zuwa ga rumfarsa. Ya buɗe rumfar suka shiga suka zauna shi kuma ya tafi domin nemo abin karin kumallo. A hanya ya gamu da Ahmad Danafi wanda zuwansa kenan daga birnin Bagadaza.
Yana ganin sa ya ruga zuwa gare shi yana mai masa sannu da zuwa, suka rungume juna. Sannan Ahmad Danafi ya ba shi labarin cewa ya samu k’aruwar arzikin ɗa namiji mai suna Aslanu wanda yanzu ya yi kusan shekaru ashirin, suka juya zuwa rumfa, a hanya Aladdini ya ba shi labarin abin da ya faru gare shi daga farko har k’arshe, ya yi mamaki mai yawa, ya shigar da shi cikin rumfar ya zaunar da shi a nan suka kwana. Da gari ya waye ya sayar da rumfar tare da ragowar kayan ciki, ya haɗa da kuɗaɗen wajensa gaba ɗaya. Sai a lokacin ne Ahmad Danafi ya faɗa masa cewar Khalifa na son ganin sa, ya shaida masa dukkan abin da ya faru. Aladdini ya ce, ina nufin na je Alk’ahira wajen mahaifana domin na gaishe su na duba lafiyarsu. Suka hau bisa gado zuwa Alk’ahira cikin kiyayewar Ubangiji. Suka sauka a wani lungu wanda ake kira rawayan waje inda gidan Shamsuddini yake. Aladdini ya k’wank’wasa k’ofa, sai ya ji muryar mahaifiyarsa na cewa, “wanene wannan kuma, mun yi rashin abin son mu kenan har abada?” Ya amsa da cewar, “ni ne Aladdini.” Nan da nan ya buɗe k’ofa ya rungume shi yana murna da ganin sa. Matan suka shiga ciki aka ba su masauki suka zauna kwana uku. Bayan wannan ya yi nufin zai wuce zuwa Bagadaza, mahaifinsa ya ce, “ya ɗana ka zauna nan mana tare da mu.” Aladdini ya ce, “ina kewar ganin Aslanu.” Su ma suka ji suna son ganin jikansu. Suka hau bisa gado su duka su shida sai Bagadaza. Ahmad Danafi ya sauka zuwa wajen Khalifa ya ba shi albishir, Sarki da kan sa ya tashi tare da Aslanu zuwa yi musu marhabin lale.
Suka rungume juna suna ma su murna da farin ciki. Bayan an natsa kwana biyu Khalifa ya sa aka fito da Amadu Kamakin daga kurkuku. Ya mik’a wa Aladdini takobi ya ce, “kashe mak’iyinka!” Nan take ya sa takobi ya fille kan sa. Daga nan ya ji wani k’urji da ke zuciyarsa ya warke. Khalifa ya shirya gagarumar walima, kuma ya kirawo alk’alai da shaidu aka rubuta takardar aure tsakanin Aladdini da Husnu Maryam, a daren ya shiga gare ta, ya same ta tamkar ɗanyen lu’ulu’u rufaffe. Haka kuma Khalifa ya ɗora Aslanu ya zama shugaban zaɓaɓɓu sittin, ya k’arawa Aladdini da mahaifansa martaba da daraja. Suka zauna a haka cikin daɗi da annashuwa da nishaɗi har mai rabawa ta zaike musu, wadda ke rusa jin da daɗi da farin ciki mai wargaza dukkan birane.

Masha Allah wannan itac karshen hikayarmu insha Allah zamu huta na tsawon sati sannn mu duba wacce hikayace zamu saka
NOGODE DA GOYON BAYANKU

WhatsApp only
08032767547

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


2 Comments On HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI
avatar
saidou

1 year ago

Reply

Tyhfhhhjg

avatar
ummitah

1 year ago

Reply

Wow

Please Login or Register in order to submit comment