Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin nan da mahaifinsa ya bar masa ya soma aiki yana mai cewa, “ya shugaban jijiyoyi ga lokacinka.” Ya mik’a hannunsa ga kuturinta ya gyara saiwar daɗinsa zuwa ga k’ofar k’una, ya bayar da ita zuwa ga saduwa ga k’ofar rabo. Magangarar ta kasance zuwa ga k’ofar nasara. Har zuwa inda ya shiga babbar magangara a buɗaɗɗiyar k’ofa. Bayan haka ya shiga kasuwa ta biyu, ta uku, ta huɗu da ta biyar ya iske shimfiɗa ya zauna gwargwadon zamansa yadda zai iya jurewa har aka jefar da shi. Da gari ya waye sai ya ce mata, “ya farin cikina, abin nan da ya kasance mai kama da hankaka ya zo.” Ta ce masa, “menene ma’anar haka?” ya ce “ ki sani yanzu ne lokacin da za mu rabu.” Ta ce “saboda me?” Ya ce, “mahaifinki ya kafa min sharaɗi a gaban alk’ali cewar na biya dinari dubu goma a matsayin dukiyar aurenki muddin na zarta wannan lokaci ban sake ki ba. Idan kuma na k’i aikata ɗayan biyun to na uku shi ne zan kasance a kurkuku. Ni kuwa a halin yanzu ban mallaki ko da rabin dirhami ba.” Da ta ji haka sai ta ce, “ya shugabana, shin takardar auren nan tana hannunka ko tana hannunsu?” ya ce, “ni kam ban mallaki komai ba na daga takarda, wala dukiya.” Ta ce, “kwantar da hankalinka, wannan abu ne mai sauk’i, kada ka ji tsoro.” Ta mik’a masa jaka ta ce, “rik’e wannan dinari ɗari ne, shi kenan da ni, da akwai wasu wallahi da na k’ara maka. Mahaifina ne saboda na nuna ba na son ɗan baffana ya kwashe dukkan abin da na mallaka ya mayar wurinsa, yanzu ba ni da komai. Idan ya aiko maka da kira zuwa gidan shari’a. A nan asubahi ta riski Shaharzad ta katse zancenta mai dadin saurare.
DARE NA 257
A dare na dari biyu da hamsin da bakwai, Shaharzad ta ce na samu labari ya kai wannan hamshakin sarki, Yarinya ta ce da Aladdini, “Idan mahaifina ya aiko maka da kira zuwa kotu ka tafi ka tsaya gaba ga alk’ali. Idan mai shari’a ya buk’aci saki ka ce musu, “shin wajibi ne bisa doron shari’a mutum ya yi aure da dare kuma washegari a ce tilas ya saki matar? Sannan sai ka sunkuya ka sumbaci hannun alkali ka sunna masa dinari hamsin. Sauran mataimakansa ma ka bi su da irin wannan gaisuwar. Na san za su cigaba da bibiyarka suna cewa, ‘ka sake ta mana ka mallaki tufafi da alfadara da dinari dubu ka yi tafiyarka shagalinka a bisa sharaɗin da kuka yi?’ Sai ka amsa musu da cewar ai silin gashin matata ya kai darajar dinari dubu, ba zan yarda na rabu da ita ba, ba zan karɓi riga ko kuɗi ko wani abu a madadinta ba.” To daga nan za su ce, ‘kawo dukiyar aure.’ To sai ka nemi a ba ka kwana uku za ka kawo. Na san alk’ali da jama’arsa za su lamunce maka har kwana goma kafin ka kawo.” Suna cikin wannan tattaunawa sai suka ji sallama daga k’ofar gida. Aladdini ya fita sai ya ga yaron alk’ali ya ce masa, “mai shari’a yana nemanka tare da surukinka.” Aladdini ya ba shi dinari biyar sannan ya ce da shi, “ya kai Malam Na-kira, a wace shari’a ce aka ce mutum zai yi aure da isha’i sannan a matsa masa ya saki matar da asubahi?.” Mai kira ya ce, “ai babu wannan shari’ar a bayan k’asa, sai dai wadda aka iza ta bisa son zuciya. Idan kuma kai ka kasance wanda bai san hukunce – hukuncen shari’a ba, ni zam zama mai tsaya maka.”05 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

Da haka suka tafi dakin shari’a, alk’ali ya ce da Aladdini, “don me ba ka sallami matar ba ka amshi hak’k’inka kamar yadda kuka yi yarjejeniya?” Yana jin haka sai ya mik’e tsaye ya k’arasa wurin alk’ali ya sunkuya ya sumbaci hannunsa ya faki ido ya danna masa dinari hamsin sannan ya ce, “ya shugabanmu mai shari’a, wace shari’a ce ta ce mutum ya yi aure da isha’i sannan ya saki matar da asubahi ba tare da son ran a ba?” Alkali ya ce, “ ya yi saki bisa takurawa da matsawa ya zama miji haramtacce a mazhabobin musulmi. Sai dai idan akwai hujja mai k’arfi.” Dattijo mahaifin yarinya ya mik’e gaba ga alk’ali ya ce, “to idan ba za ka sake ta ba sai ka biya dukiyar aure dinari dubu goma kamar yadda muka yi sharaɗi.” Aladdini ya ce ina rok’on a jinkirta min zuwa kwana uku.” Amma alk’ali ya ce, “kwanaki uku sun yi kaɗan bisa wannan sharaɗi, mun ba ka kwana goma.” Duk aka amince bisa wannan jinkiri na kwana goma, idan ba haka ba kuma ya sake ta. Daga nan ya tafi zuwa kasuwa ya sayo shinkafa da nama da mai da sauran dangogin abincin da yake bukata ya kai gida ya faɗa wa yarinya yadda suka yi duka a kotu. Yarinya ta ce, “tsakanin dare da rana akwai abubuwa al’ajabi da suke faruwa. Allah ya shi albarka ga wanda ya faɗi cewa:
Ka zam mai hak’uri ga jarrabar fushi,
Da lokacin da masifa ta zaike maka
Ka dubi dararen da suka shusshude,
Su ke samar da al’ajabi a lamuranka
Ta tashi ta shirya musu abinci ta kawo gabansa, suka zauna suka ci tare suka sha, sannan suka yi walimar aurensu a tsakaninsu. Aladdini ya ce mata yana buk’atar jin kiɗa daga gare ta. Ta ɗauko molo ta gyara tsarkiyarsa, ta goga dutse sannan ta fara kada shi da sauti mai daɗi wanda ke iya sa dutse ya rausaya. Suna nan suna ta wasanni cikin farin ciki suna nishaɗi da wasa a shimfiɗa sai suka ji an k’wank’wasa k’ofa. Ya sauka ya buɗe sai ya ga sufaye huɗu a tsaye. Ya ce musu “me kuke nema?” suka ce “ya shugabanmu, mu bak’i ne mun zo domin wa’azi muna neman abinci mun ji sautin wak’a na tashi a nan muka zo domin mu ji wak’okin masu faranta ciki. Nufinmu mu kwanta a nan har zuwa asubahi sannan mu kama gabanmu. Ladarka na wurin Allah maɗaukakin sarki. Mu muna begen ji daga kiɗa, babu ɗaya daga cikinmu da bai san wak’a ba wadda ke ɗebe kewa.” Ya ce da su, “bari na shiga na yi shawara.” Ya je wajenta ya sanar da ita ta ce ya shigo da su. Ya kai musu abinci da abinsha suka ce masa, “mu abincinmu shi ne mu ambaci sunayen Allah sannan mu ji wak’ok’i da kunnuwanmu kamar yadda wani yake cewa:
Manufarmu shi ne mu ji daɗi,
Mu daina ci sai dai dabbobinmu
To yanzu muka ji wak’a na tashi daga nan sai muka zo, amma da muka shigo sai muka shigo sai muka ji shiru, muna tunanin shin wannan mai wak’ar bak’a ce ko fara, kuyanga ce ko matar gidan.” Ya ce musu, “matata ce.” Ya faɗa musu abin da yake buk’ata game da kuɗin da zai biya na dukiyar aure dinari dubu goma. Ɗaya daga cikin sufayen ya ce, “kada ka damu, ni tsoho ne mai arziki wanda a k’ark’ashina akwai mutum arba’in da nake hukunci tsakanin su
Zan je wajen su na tattara dinari dubu goma na kawo maka kai kuma ka biya surukinka. Amma yanzu dai muna buk’atar ka umarci matarka ta yi mana kida domin k’irazanmu su samu nutsuwa, domin kiɗan wasu jama’ar abinci ne, ga wasu magani ne ga wasu kuma nishaɗi ga wasu kuma hutawa ne ga mai gajiya.” Su fa waɗannan masu shigar sufayen ba wasu ba ne face Khalifa Haruna Rashid da Wazirinsa Jafaru Barmakiyu da Abu Nawwas Alhassan ɗan Haniyu da kuma hauni Masruru mai takobi. Yadda abin ya kasance shi ne, Khalifa ne ya kasance zuciyarsa ta ɓaci, hankalinsa ya tashi sai ya kirawo wazirinsa ya ce masa, “ya kai waziri ina so ka raka ni mu zaga cikin gari domin na samu k’irjina ya haskaka daga k’uncin da nake ciki.” Sai suka yi irin wannan shiga irin ta matafiya masu gudun duniya suka yi ta shiga lungu da sak’o cikin Bagadaza har suka zo wannan gida inda suka ji sautin molo na tashi wata zazzak’ar murya na rera wak’a, sai suka tsaya domin sanin bahasin haka. Suka kwana a nan suna masu nishaɗi da farin ciki har zuwa gabatowar asubahin. Khalifa ya ajiye dinare ɗari k’arkashin dardumar sallah, sannan ya umarci waziri suka tafi bayan sun yi sallama da mutan gida. Yayin nan Zubaidatu ta tashi domin gyara ɗakin, ta ɗage darduma sai ta ga dinari ɗari k’ark’ashi, sai ta ce wa mijinta, “ɗauki kuɗin nan da na tsinta k’ark’ashin dardumar sallah, ina ganin waɗannan matafiyan ne suka ajiye mana yayin da za su tafi ba tare da saninmu ba.” Aladdini ya ɗauki kuɗi ya tafi kasuwa ya sayo kayan abinci da na sha daidai buk’atarsu.
Da dare ya yi, ya kunna fitila da turare sannan ya zauna kusa da matarsa ya ce mata, “mutanen nan ba za su kawo min dinari dubu goman nan ba kamar yadda suka yi alk’awari, ki dube su fa, dukkansu matalauta ne.” suna cikin hira sai suka ji matafiya na k’wank’wasa k’ofa, ya tashi ya bu’de ya shigo da su. Sannan ya ce musu, “shin kun kawo dinaran?” suka ce, “ba mu kammala tattarawa ba tukunna, amma ka kwantar da hankalinka, kada ka ji tsoron komai, in sha Allahu gobe za mu kawo maka wata dahuwa ta kunya. Muna so ka umarci matarka da ta nishadantar da mu da kiɗanta. Zubaidatu ta ɗauko molonta ta gyara shi sannan ta soma kiɗa mai sa wa a rausaya ko babu niyya. Suka shafe daren nan suna nishaɗi da annashuwa suna hira suna dariya har zuwa asuba sannan Khalifa ya ajiye dinare ɗari kamar yadda ya yi jiya. Haka suka cigaba da ziyartar su har kwana tara, kuma kullum Khalifa na ajiye dinari ɗari su kuma suna kwashewa suna cefane da su. A cikon kwanan goma sai ba su zo ba. Amma dalilin rashin zuwansu shi ne Khalifa ne ya aika zuwa ga manyan fatake cewa, “ina so ku kawo laftu hamsin na tufafi waɗanda ke zuwa daga misira kuma wannan kayan ya zama na kimanin dinari dubu kowanne laftu sannan ku sanya bawa Bahabashe ya kawo mini dukkan abin da na ce muku.” Fatake suka aikata kamar yadda ya buk’ata. Khalifa ya rubuta takarda cikin harshen Shamsuddini zuwa ga Aladdini ya ce da bawan, “rik’i waɗannan laftu da dukkan abin da suka k’unsa ka tafi ga unguwa kaza waje kaza ka tambayi gidan Aladdini Abu Shammata ka kai masa cewa daga mahaifinsa ne.” Bawa ya rik’i kaya ya tafi inda aka umarce shi.
Wannan kenan game da al’amarinsu. Amma game da ɗan baffan Zubaida watau tsohon mijinta kuwa, ya tafi wajen mahaifinta ya ce da shi, “gara mu gaggauta zuwa wajen alk’ali mu sa ya saki matarsa tunda lokaci ya yi bai zo ya biya ba. Suka fito za su tafi sai suka ga laftun kaya hamsin da alfadarai da sauran dukiya, ga kuma bak’in bawa na kora su a kan alfadara. Suka ce da shi, waɗannan kayan fa?” Ya ce musu, “waɗannan dukiya ce daga shugaban fataken Misira, watau Shamsuddini mai alheri, mahaifi ne ga Aladdini Abu Shammata ya samu labarin cewar ‘yan fashi sun tare ɗansa sun k’wace dukkan dukiyar da ya taho da ita don haka ya aiko masa da wannan a madadin wadda ya yi asara.”
Da uban yarinyar ya ji wannan maganar sai ya ce, “wanda kake nema surukina ne, zo mu je na kai ka wurinsa.” Aladdini na zaune a gidansa yana tunanin abin yi sai ya ji ana k’wank’wasa k’ofar gida. Ya tashi ya buɗe a zatonsa alk’ali ne ya aiko masa sammaci. Yana buɗewa sai ya yi ido huɗu da surukinsa da madugun fatake da kuma bak’in bawa mai jan kyakkyawar shiga haye bisa alfadara. Bawan ya sauka ya sumbaci k’asa a gabansa sannan ya ba shi labarin cewar daga Misira yake ubansa ne ya aiko shi da waɗannan kayan, sannan ya ba shi takardar nan Alladdini ya buɗe ya karanta kamar haka:
Idan masoyi ya gane ka ya ɗauki k’asa,
Ga takalmi a kai masa domin nutsuwa
Yi jinkiri kada ka zamto mai gaggawa,
Domin sannu sannu ba ta hana zuwa
Bayan gaisuwa cikakkiya da aminci da girmamawa daga Shamsuddini zuwa ga ɗansa Aladdini Abu Shammata, ka sani ya ɗana, cewa labarinka ya ishe ni an kashe mutanenka, an k’wace dukiyar ka. Saboda haka na aiko maka waɗannan laftu hamsin na daga tufafi Misiriya da riga da takalmi da hula da shantali na zinariya. Kada ka ji tsoron komai, dukiyar nan fansa ce a gare ka. Ya ɗana kada ka yi bak’in ciki har abada. Kuma mahaifiyarka da duk jama’ar gida suna nan lafiya da alheri da aminci. Suna gaishe ka da kyau. Na samu labari ya ɗana cewa an yi maka gida da auren wata yarinya, Zubaidatul Udiyati an sa maka sadakinta dinari dubu goma. Saboda haka na aiko maka da dinari dubu hamsin tare da bawa mai suna Salimu.” Yayin da Aladdini ya gama karanta wasik’ar sai ya karɓi kaya ya sauke sannan ya juya ga surukinsa ya ce, “ya babana, ga kuɗin dukiyar auren ‘yarka dinari dubu goma sannan ka karɓi waɗannan kayan ka tafi ka sayar da su ka ɗebe tsawurwurinka ka bar min kan dukiyar.” Ya ce masa, “A’a wallahi, ba zan karɓi komai daga gare ka ba, sadaki da dukiyar aure kuwa ka shiga ku daidaita tsakaninka da matarka.” Sannan suka sa aka kwashe kayan aka shiga da su gida. Zubaida ta ga mahaifinta na nuna inda za a sauke kaya sai ta ce masa, “ya babana waɗannan kayan kuma fa?” Ya ce, “na mijinki ne babansa ya aiko masa a madadin waɗanda ‘yan fashi suka k’wace masa. Bayan wannan ma ya aiko masa da dinari dubu hamsin da tufafin sa wa da kayan ado da alfadara da shantalin ziniariya da kyankyandi da sauran kaya duka. Amma game da dukiyar aure da sadaki yanzu zance na wajenki.” Aladdini ya tashi ya buɗe akwati ya ba ta dukiyar aurenta da sadaki. Yaron nan tsohon mijinta ya ce, “ya baffana ka tilasta masa ya sake ta yanzu.” Dattijo ya waiwaya ya kalle shi ya ce, “hakan ba mai yiwuwa ba ne, domin igiyar aure na hannunsa.” Saurayi ya tashi ya fita cikin bak’in ciki da ɓacin zuciya ya tafi gidansa ya kwanta. Zuciyarsa ta harbu da mummunan ciwo ya k’are ya mutu. Shi kuwa Aladdiniya k’are ya mutu. Shi kuwa Aladdini bayan ya kammala karba’r kayan ya shirya ya tafi kasuwa ya sayo musu kayan abinci da nama da sauran buk’atun yau da kullum kamar yadda ya saba. Ya zauna kusa da matarsa ya ce mata, “waɗannan mak’artyatan matafiyan har yau ba su cika alk’awarin da suka ɗauka ba. Ta ce masa, “kai da kake ɗa ga shugaban fatake, ka zamana ba ka da ko da rabin dirhami, ina kuma ga su da suke matalauta?” Ya ce, “to dai ga shi nan Allah ya hore mana ya wadata mu, amma ba zan sake buɗe musu k’ofa ba idan sun zo.” Ta ce, “Saboda me? Alhali kuwa zuwansu ne ya haifar mana da nasara, kuma kullum fa sai sun ajiye mana dinari ɗari waɗanda muke samun na cefane a ciki. Ni dai ina ganin ka buɗe musu k’ofar da zarar sun zo, shi ne abu ma fi alheri.” Da rana ta yi k’asa da haskenta dare ya kawo jiki, suka kunna fitila sannan ya ce mata, “ya Zubaidatu zo ki yi mana kiɗa kamar yadda kika saba.” Ta jawo molo ta gyara tsirkiya sannan ta soma kaɗawa sai ga k’wank’wasa k’ofa na zuwa. Ta ce da shi, “je ka ka ga ko wanene.” Ya tashi ya buɗe sai ga matafiya su huɗu. Ya ce, “sannunku da zuwa mak’aryata! Marabanku lale ku shigo ciki!” Suka shiga suka zauna aka halarto musu da abinci kamar yadda aka saba, suka ci suka sha sannan suka yi nishaɗi. Bayan sun nutsu sai suka ce masa, “ya shugabanmu zuciyarmu na cike da damuwa saboda kai, kullum cikin tunaninka muke.” Ya ce, “kada ku damu, Allah ya musfaya min da abin da ya wuce wanda nake buk’ata.” Suka ce, “wallahi mu mun kasance muna jin tsoro saboda kai, domin alk’awarin da muka yi maka ba mu k’i cikawa ba sai domin rashin samun dukiyar a hannunmu.” Ya ce, “to ai taimakon gaggawa ya zo daga ubangiji maɗaukakin sarki, mahaifina ne ya aiko min da dinari dubu hamsin da laftu hamsin na kaya.” Ya zayyana musu dukkan abubuwan da aka kawo masa har da bawa mai yi masa hidima. Ya k’ara da cewa, “yanzu mun daidaita da surukina, na ba shi dukiyar auren ‘yarsa.” Daga nan Khalifa ya tashi domin gusar da lalura. Waziri Ja’afaru ya karkata ga Aladdini ya ce, “ka yi ladabi, ka yi biyayya, ka yi magana mai taushi domin a fadar Sarkin Musulmi kake.” Aladdini ya ce, “Me na yi na rashin ladabi a fadar Sarkin Musulmi? Wanene Sarkin Musulmin a cikinku?” Ja’afaru ya ce, “wannan da ya fita shi ne Sarkin Musulmi Khalifa Haruna Rashid, ni kuma ni ne wazirinsa Ja’afaru, wannan na dama shi ne Nawwas Alhassan Bin Haniyi, wannan kuma na hagun Masaruru kenan hauni. Yanzu kai Aladdini ka dubi nisan tafiyar da ke tsakanin Bagadaza da Masar. Kai kan ka kwana nawa ka yi kafin ka iso nan.” Ya amsa ya ce, “kwana arba’in da biyar.”
“To ka yi tunani, kwana goma ne yanzu kacal da yi maka fashin dukiyarka. Ta yaya har labari ya isa ga mahaifinka har ya shiryo maka wasu kayan ya aiko maka da su duka cikin k’asa da kwanaki goma alhali zuwa da dawowa kwana tis’in ne kenan?”

06 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

Aladdini ya ce, “ya shugabana, to daga ina kayan suka zo?”
“Daga wajen Sarkin Musulmi.” Waziri Ja’afaru ya ba shi amsa, “Saboda ya yaba da ɗabi’arka kuma yana k’aunarka.” Suna cikin hira sai ga Khalifa ya dawo, Aladdini ya mik’e ya sumbaci k’asa a gabansa sannan ya ce, “Allah ya ja zamaninka ya Sarkin musulmi. Allah ya taimake ka ya kiyaye ka sharrin zamani. Kada Allah ya sa mutane su daina samun alherinka da baiwarka.” Khalifa ya ce, “ya Aladdini umarci Zubaidatu ta yi mana kiɗa yadda ta saba mu samu wartsakewa.” Ta ɗauko molo ta soma kaɗawa da sauti mai sa kurman dutse ya amsa. Molo ya kaɗa taken wak’ar ‘ya masoyina!’ Suka kwana a wannan dare suna masu nishaɗi da farin ciki. Da gari ya waye Khalifa ya ce da Aladdini “ka same ni a majalisa an jima.” Aladdini ya amsa, “na ji, na bi, Allah ya ba ka nasara.” Sannan ya shirya, ya ɗauki ɗaba’a goma ya zuba kayan kyauta a ciki masu tsada ya lulluɓe da alharini sannan ya tafi fada ya tarar da Khalifa zaune bisa gadon sarauta. Ya rera waɗannan baitoci:
Alheri ya sauko maka kowace safiya,
Da girma da turmuza hancin mahassada
Fararen ranaku su tabbata a gare ka ya sarki,
Bak’ak’en kuwa su yi nesa da kai har abada
Khalifa ya ce, “Barka da zuwa ya Aladdini.” Aladdini ya ce, “ya Sarkin Musulmi, hak’ik’a Manzon Allah mai tsira da aminci su tabbata a gare shi yana karɓar kyauta. Don haka na taho maka da waɗannan faya-faye goma a matsayin kyauta gare ka daga talakanka.” Khalifa ya karɓi kyautar sannan ya ba shi tufafi masu kyau na alfarma sannan ya ba shi muk’amin shugaban fatake a majalisar.

Yana nan zaune sai ga surukinsa, uban matarsa ya shigo fada. Ya ce da sarki, “ya Sarkin Musulmi, yaya na ga wannan kuma a wajen da nake zama?” Khalifa ya ce, “na maishe shi shugaban fatake domin ya zama magajin mahaifinsa Shamsuddini Tajiri mai alheri na birnin Misira, kai kuwa na tuɓe ka.” Suruki ya ce, “ka kyauta ya sarki kuma ka yi daidai, domin ya kasance ɗaya daga cikinmu. Allah ya yi mana kyakkyawan jagoranci. Da yawa k’arami yakan taso ya zama babba!” Daga nan sarki ya rubuta takardar naɗin Aladdini ya bai wa wakili. Wakili ya rarrabawa sarakuna cewa Aladdini ya zama shugaban fatake na birnin Bagadaza. Mai shela ya zagaya gari yana cewa, “daga yau babu wani shugaban fatake da tajirai sai Aladdini Abu Shammata ɗan Shamsuddini Shugaban fataken Misira, kuma tilas a ji maganarsa, a yi aiki da umarninsa, a hanu da haninsa. A girmama shi da biyayya da iyakar iyawa!” Haka kuma bayan fada ta tashi, Aladdini ya kintsa zai tafi gida sai aka sa mai shela a gabansa yana tafe yana nanata matsayin da aka ba shi da irin kwarjininsa a fada. Washegari Aladdini ya tafi kasuwa ya buɗe rumfa ya dank’a ta a hanuun bawansa Salim domin ya soma saye da sayarwa, shi kuma ya kintsa ya wuce zuwa fada yayin da bawansa Salim ke kula da kasuwa. Haka ya cigaba da yi har lokaci mai tsawo. A nan wata rana ana zaune a fada sai ga wani mutum ya shigo ya ce, “ya Sarkin Musulmi, Allah ya ba ka yawan lada! Hakiminka yau ya amsa kiran ubangiji, Allah ya cika ni’ima a gare shi, ya tafi zuwa jin k’an Allah maɗaukakin sarki Allah ya ja zamaninka!” Khalifa ya ce, “ina Aladdini Abu Shammata?” Ya mik’e gaban Sarkin Musulmi, ya yi umarnin a sa masa rigar alfarma aka naɗa masa rawanin sarautar madadin wancan hakimin da ya rasu. Sannan aka rubuta masa albashinsa duk wata dinari dubu. Ya tabbata bisa ga haka lokaci mai tsawo. Wata rana suna zaune a fada sai wani mutum ya shigo ya ce, “ya Sarkin Musulmi, Allah ya ja zamaninka! Tutarka mai ɗauke da mutum sittin yau shugabanta ya rasu.” Khalifa ya sa aka ba wa Aladdini sutura ta alfarma aka naɗa masa rawanin shugabanci bisa zaɓaɓɓu sittin, ya zaman jagoransu, domin wanda ya rasu ba shi da mace ba shi da ɗa ballantana ‘ya.

Aladdini ya sa aka tattara dukkan dukiyar mamacin nan sannan ya mik’a wa Khalifa. Khalifa ya ce, “ku bunne shi sannan ka rik’e dukkan abin da ya mallaka na daga dukiya da bayi da kuyangi.” Sannan ya karkaɗa mayanin da ke hannunsa, fada ta tashi. Aladdini ya tafi tare da Muk’addam Ahmad Danafi a damansa, sai Muk’addam Hassan Shaumani a hagunsa, kowannensa na jagorantar mutane arba’in. Ya juya ga Hassan Shaumani da mutanensa ya ce, “ku sa baki ga Ahmad Danafi ya rik’e ni a matsayin ɗansa.” Ahmad Danafi da ya ji haka sai ya ce, “daga yanzu za mu kasance tare da kai dare da rana ni da jama’ata.” Daga wannan lokaci Aladdini ya cigaba da hidimtawa Khalifa lokaci mai tsawo, har wata rana ya dawo daga fada ya sami Ahmad Danafi da jama’arsa yana zauna tare da matarsa Zubaidatu na kaɗa masa molo yana rausayawa, ya kukkuna fitilu ko’ina cikin gidan. Ta tashi ta shiga ciki domin ta gabatar da wani abu. Kwatsam sai ya ji wata kururuwa mai tsanani da ban firgici daga ciki, ya tashi ya zabura zuwa ciki, nan ya ga matarsa ce ke wannan kururuwar ya tarar da ita kwance rigingine. Nan da nan ya ɗauke ta ya ji babu numfashi a tare da ita, ta rasu. To gidan mahaifinta na kusa da gidansu, shi ma ashe ya ji wannan kururuwar sai ya fito da hanzari ya shiga gidan domin ganin abin da ke faruwa. Ya tarar da Aladdini durkushe gaban gawar Zubaidatu yana kuka. Shi ma mahaifin ya rik’a kuka. Aladdini ya rarrashe shi yana mai cewa, “girmama mamaci shi ne a binne shi.” Da gari ya waye suka tara mutane aka kai ta kushewarta sannan suka zauna suna yi wa junansu ta’aziyyar rashin da suka yi. Aladdini ya sa kayan makoki ya zauna a gida ya k’i zuwa fada yana hawaye gami da alhinin rashin masoyiyarsa.
A fada kuwa Sarki ya duba bai ga Aladdini ba, sai ya ce da Waziri Ja’afaru, “lafiya yau ban ga Aladdini ba? Waziri ya ce masa, “mun samu labarin matarsa ta rasu jiya bayan isha’i, yana gida yana karɓar gaisuwar ta’aziyya.” Sarki ya ce “to kuwa mu ma sai mu yi harama mu je mu yi masa ta’aziyya.” Aka kawo dawaki, Khalifa ya hau tare da Waziri da wasu hakimai suka tafi gidan Aladdini. Yayin da ya gan su sai ya mik’e tsaye ya sumbaci hannayensu, sannan suka zauna.

2 Comments On HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI
avatar
saidou

1 year ago

Reply

Tyhfhhhjg

avatar
ummitah

1 year ago

Reply

Wow

Please Login or Register in order to submit comment