Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Khalifa ya ce, “yau lafiya ba ka zo fada ba?” Aladdini ya ce, “Allah ya kiyaye ka ya Sarkin Musulmi. Na yi rashin matata Zubaidatu.” Khalifa ya yi mata addu’a sannan ya ce, “ka daina bak’in ciki da rashinta domin ta tafi ne zuwa ga jin k’an Ubangiji mai girma da ɗaukaka. Kuma yawan kukan ba zai amfane ka ba. Aladdini ya ce yana matse – matsen hawaye, “ya sarkin musulmi, a yadda nake ji ba zan iya daina kuka saboda rashinta ba har abada har sai ni ma na mutu an binne ni a kusa da ita.” Khalifa ya ce, “komai na Allah yana da musaya amma ban da mutuwa, kuɗi ko mulki ko wayo ko dabara ba za su hana zuwanta ba, matuk’ar lokacinta ya zo. Haka nan wani masani yake cewa:
Kowanne rai ba shi gujewa mutuwa,
Babu shakka zai ɗanɗani kaifinta
Don me ake wasa da rai don jin daɗi,
Alhali an san rayuwar nan ba ta tabbata?
Yayin da Khalifa ya gama yi masa ta’aziyya sai ya umarce shi kada ya daina zuwa fada ya cigaba da aikinsa. Saboda haka bayan an kammala zaman makoki da sassafe Aladdini ya shirya ya nufi fada ya sunkuya gaban Sarkin Musulmi ya sumbaci k’asa, Sarki kuma ya mik’e domin yi masa marhaba gami da sake yi masa gaisuwar ta’aziyya, sannan ya umarce shi da ya zauna a mazauninsa. Ya ce da shi, “ya Aladdini, yau ina buk’atar ka zama bak’ona da isha’i. Ya shiga da shi turakarsa ya kira kuyangarsa wannan da ake kira Kutal – Kulubi ya ce da ita, “Aladdini yana da mata mai suna Zubaida, wadda take masa kiɗa tana rera masa wak’ok’i da ke nishaɗantar da shi kuma tana tarairayarsa, yanzu ta koma ga mahaliccinta. Ina so ki ɗauki matsayinta ki dinga yi masa k’ida da molo.”kina yi masa wak’a, domin ya samu yayewar bak’in ciki da ɓacin ran da ke tattare da shi.” Ta tashi ta ɗauko molo ta gyara tsirkiyarsa sannan ta soma kaɗawa tana rera wak’oki masu tsima zuciya da tattausar murya. Khalifa ya ce da shi, “me za ka ce game muryar kuyangar nan?” Aladdini ya ce, “ya Sarkin Musulmi, hak’ik’a muryar Zubaidatu a wajena ta fi wannan daɗi, domin ita kiɗan ma kaɗai na iya sa kurman dutse ya yi amo.”

Khalifa ya tambaye shi, “to ta k’ayatar da kai?” ya amsa, “k’warai kuwa ta k’ayatar da ni.” Khalifa ya ce, “na rantse da rayuwata da mutuwa da kabarin iyayena ta zama kyauta a gare ka tare da dukkan matan dake tare da ita.” Aladdini sai ya yi tsammanin Khalifa wasa yake masa, suka rabu a kan haka, amma washegari Sarki ya shiga wurin Kutal – Kulubi ya ce da ita, “na bayar da ke ga Aladdini.” Ta yi farin ciki da haka, domin tun da ta gan shi ta ji tana k’aunarsa, sannan ya koma ya umarci ‘yan dako su ɗauko laftun kaya biyu dominta, ya ce mata, “ku kai mata kayan can gidan Aladdini tare da dukkan kuyanginta.” Suka shiga jidar kaya suna kai wa ga Aladdini alhali shi yana majalisar Sarki ana fadanci har zuwa faɗuwar rana aka tashi kowa ya tafi muhallinsa. Wannan kenan. Ita kuwa Kutal-Kulub yayin da ta sauka gidan Aladdini tare da kuyanginta su arba’in ban da babanni da tsofaffi. Ta umarci tsohuwa ɗaya ta zauna a gefen gado, ɗayar kuma ta zauna a k’ofar ɗaki ta ce musu idan Aladdini ya shigo su mik’e gaba ɗaya su gaishe shi sannan su ce masa, ‘uwargidanmu Kutal-Kulubi tana buk’atar ganinka domin Khalifa ya bayar da ita kyauta a gare ka ita da dukkan kuyanginta.” Suka amsa da biyayya.
Da Aladdini ya dawo ya tarar da bayin gidan Khalifa a k’ofar gidansa, sannan ya shiga ciki ya ga tsoffin nan a k’ofar ɗaki, sai ya tambaya “lafiya, me ya faru?” Suka mik’e suna masu gaishe da shi sannan suka faɗa masa sak’on gimbiya Kutal –Kulubi. Ya ce, “to ku faɗa mata cewar ina gaishe ta da kyau, amma matuk’ar tana cikin ɗakin nan ba zan shiga ba, domin abin da yake daidai ga ubangida bai cancanci bawa ba.” Ya tambayi bayin nan, “nawa kuke kashewa na cefane a kullum?” Suka ce dinari ɗari kullum. Ya ce a ransa, ‘ni kam ba zan iya sarrafa Kutal – Kulubi bisa wannan adadin kuɗi tsububu, ga shi kuma ba sauran dabara game da haka.

..Zanci gaba gobe insha Allah'.07 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

Ya zauna da ita bisa ga haka, kullum yana aika mata dinari ɗari domin buk’atunta da na jama’arta amma bai taɓa shiga wurinta ba, a nan wata rana ya k’i zuwa fada, Khalifa ya ce da Waziri Ja’afaru, “ka sani cewa ni na bayar da Kutal – Kulubi ga Aladdini domin ta maye gurbin matarsa da ya rasa, menene kuma dalilin yankewar sa gare mu?” Ja’afaru ya ce, “ya Sarkin Musulmi wanda ya ce, “ya gamu da masoyinsa ya mance masoyansa” ya yi gaskiya.” Khalifa ya ce, “na san ba zai k’i fashin zuwa fada ba tare da dalili mai k’arfi ba, ku tashi mu ziyarce shi.” To kafin wannan rana kuwa Aladdini ya samu Waziri Ja’afaru ya ce masa, “na kai maganar rashin matar da na yi ga Khalifa ya ba ni Kutal – Kulubi.” Waziri ya ce masa, “domin yana k’aunar ka ne ya yi maka haka, ba domin haka ba, ba zai ba ka ita ba. Ka faɗa min shin ka taɓa kwanciya da ita?” Aladdini ya ce, “A’a, wallahi ban taɓa yi ba. Ban san tsawonta ba, balle faɗinta ba, ballantana zurfinta.” Waziri ya ce “saboda me?” Aladdini ya sunkuyar da kai sannan ya ce, “ya babban waziri, abin da shugaba ya taɓa bai halatta ga bawa ba.
Bayan wannan tataunawa ce sai Khalifa da Wazirinsa suka ɓatar da kamanni suka je gidan Aladdini bayan isha’i, suka k’wank’wasa ya buɗe musu k’ofa, nan da nan ya shaida su, ya sunkuya, ya yi gaisuwa yana mai yi musu maraba lale. Khalifa ya dubi fuskarsa ya gan ta da alamun bak’in ciki babu annuri a tattare da shi ya ce masa, “ya Aladdini, me ya faru kake bak’in ciki haka? Shin ba ka shiga wajen Kutal – Kulubi ba ne?” Ya amsa ya ce, “ya Sarkin Musulmi, abin da yake ga shugaba bai kamaci mabiyi ba. Ni har yanzu ban ziyarce ta ba, ban san tsawonta ba ko faɗinta ba, na yi kaɗan a gare ta, ni dai ina rok’on Sarki ya maida ita nan wajensa ta fi dacewa da shi.” Khalifa ya ce, “ni dama muradina ta zama a madadin matarka da ka rasa domin ta rik’a deɓe maka kewa, amma tunda haka ne sai ta koma gida kan bakin aikinta.” Aladdini ya ce, “na ji, na ɗauka, Allah ya taimaki Sarki, Allah ya k’ara maka lafiya da nisan kwana.”
Khalifa ya shiga inda Kutal – Kulubi take, ta mik’e tsaye domin girmama shi, sannan ya ce da ita, “shin Aladdini ya shigo wurinki?” ta amsa, “a’a, ya Sarkin Musulmi, na aika masa ya zo sau da yawa amma ya k’i lek’on inda nake.” Khalifa ya yi umarnin ta koma gidanta a fada, sannan ya ce da Aladdini. “ka daina ɗauke k’afarka daga gare mu.” Suka yi masa sallama. Da gari ya waye Aladdini ya hau zuwa fada ya zauna a mazauninsa na shugaban zaɓaɓɓu sittin. Khalifa ya umarci Ma’aji ya ba wa Waziri dinari dubu goma ya ce su tafi tare da Aladdini kasuwar kuyangi ya zaɓi wadda ta yi masa a wannan kuɗin. Sai aka dace a wanan ranar Sarki Halidu wanda babu jimawa Khalifa ya naɗa shi hakimin birnin Bagadza ya shiga kasuwar shi ma domin ya saya wa ɗansa kuyanga. Kuma babban dalilin zuwansa kasuwar shi ne, matarsa mai suna Hatunu ta haifar masa ɗa namiji mai suna Habzalam Bazaza, wani mummunan yaro ne, wawa, mai k’iriniya ya kai munzalin shekara ashirin bai koyi yadda ake hawa doki ba balle yak’i, ita uwar ce ke biye masa yana shagwaɓarsa yadda ya ga dama. To amma ubansa gwarzon yak’i ne, yana iya hawa ingarma ya ratsa kogunan dare ya keta abin da yake so ya dawo lafiya. Wata rana Habzalam Bazaza ya yi mafarkin yana tarawa da mace, da ya farka ya ga gabansa a jik’e, sai ya shaida wa mahaifiyarsa, ta yi murna cewa ɗanta ya kawo k’arfi, ta faɗa wa mijinta irin mafarkin da ɗansu ya yi. Sannan ta ce masa, ‘buk’atata ka samo mace domin yanzu ya isa aure.” Halidu ya ce, “wannan yaron da yake k’azami mai warin dauɗa babu matar da za ta k’aunace shi.” Sai ta ce, “to a samo masa baiwa.” To, sai ya kasance bisa hukuncin Allah a wannan rana kuma a daidai lokacin da ya shiga kasuwar Waziri Jafaru da Aladdini ma suna ciki, suka ga wata kuyanga kyakkyawa mai kyawon sura a hannun wani dillali. Waziri ya ce da shi, “a faɗa wa mai ita mun saye ta dinari dubu.” Dillali ya tafi da yarinyar domin sanar wa mai ita sai Sarki Halidu ya gan ta, ɗansa ma Habzalam Bazaza ya k’yalla ido ya ga yarinya irin kallon da yake matsayin dubu gare shi. Ta k’ayatar da shi k’warai. Ya ce da mahaifinsa, “a saya min wannan kuyangar.” Sarki ya sa baki ya kirayi dillali ya zo da yarinyar sannan ya tambaye ta sunanta. Ta ce, “sunana Yasmin.” Sannan Sarki ya ce wa ɗansa “tunda ta k’ayatar da kai sai ka taya farashinta.” Ya juya ga dillali ya ce, “nawa aka taya ta?”
“Dinari dubu ɗaya.” Dilalli ya bada amsa. Habzalam Bazaza ya ce, “na saye ta dinari dubu da ɗaya.” Dilalli ya faɗa wa Aladdini sabon tayin da aka yi, shi kuma ya ce ya saye ta dinari dubu biyu. Dillali ya koma ya shaida wa ɗan Sarki, ya fusata da wannan tayin, ya k’ara dinari ɗaya a kan dubu biyu, Aladdini ya k’ara dinari dubu ɗaya. Wawan yaron nan ya fusata, ya ce da dillali, “wai wanne shaiɗanin ne yake irin wannan mugun tayin?” Dilalli ya faɗa masa cewar Waziri Ja’afaru ne zai saya wa Aladdini Abu Shammata ita. Da ya ji haka sai ya kuma k’ara dinari ɗaya a kan tayin k’arshe. Aladdini kuwa ya yi ta k’ara farashin har ta kai darajar dinari dubu goma, mamallakinta ya amince ya sayar da ita a kan wannan farashin. Ya ɗauke ta ya tafi da ita gida sannan ya ce mata, “na ‘yanta ki saboda Allah.” Sannan ya nemi aurenta, aka rubuta takarda aure ya biya sadaki.” To, da dillalin nan ya koma da kuɗi sai Habzalam Bazaza ya ce masa. “ina yarinyar?” Dilalli ya ce, “an sallama ta kan kuɗi dinari dubu goma ga Aladdini kuma har ya ‘yanta ta, ya aure ta.” Wannan batu ya bak’anta ran Habzalam Bazaza ya tafi gida yana nishi yana huci saboda ɓacin rai ya kwanta a gida ba ya cin abinci ba ya shan ruwa saboda k’aunar yarinyar da ta shiga ransa. Da mahaifiyarsa ta gan shi a halin k’unci da ciwo sai ta ce masa, “Allah ya kawo maka sauk’i ya ɗana. Me ya same ka?” Ya ce, “ni a sayo min Yasmin.” Sai ta yi tsammani yana nufin furen k’anshi wanda yake da wannan sunan yake nufi, sai ta ce, “idan mai sayar da fure ya zo zan saya maka kwando guda na Yasmin. “ Ya ce, “ni ba wannan ba, wata kuyanga ce mai wannan sunan wadda babana ya k’i saya min.” Ta tafi wurin mahaifin ta ce masa, “don me ka k’i sayo masa wannan yarinyar?” Ya ba ta amsa da cewa, “abin da babba yake so ba ya halatta ga yaro ballantana kuma bawa, ni kuma ba ni da ikon karɓarta. Ba wani ne ya saye ta ba sai Aladdini shugaban zaɓaɓɓu sittin.” Daga nan ciwon yaron ya sake k’aruwa kullum ba ya iya cin abinci sai maganar Yasmin yake yi. Daga baya ya daina barci, mahaifiyarsa kuma ta shiga rigar bak’in ciki tana taya ɗanta takaici. Tana cikin wannan abu sai ga wata tsohuwa ta shigo gare ta ana kiranta Uwar Amadu ɓarawon gidaje, ya shahara wajen haura katanga mai tsawo ya yi sata. Wata rana ya haura wani gida ya shiga sashen matar gidan ya saci kurantandu. Haka yake wannan ɗabia ta sata tun yana yaro har abin ya zame masa jiki. Da ya daina sai aka ba shi sarautar masu gadin gari cikin dare, amma mai hali ba ya fasa halinsa, wata rana ya shiga wani gida ya sato kuɗi sai shugaban tsaro ya kama shi ya wuce da shi wurin Khalifa nan take ya yi umarnin a tafi a sare masa kai. Ya kama k’afa a wajen Waziri wanda ya tafi gaban Sarki ya yi gaisuwa ya nemi alfarmar maimakon kisa a ɗaure shi. Khalifa bai taɓa juya maganar Waziri ba. Amma a wannan rok’on sai Khalifa ya ce masa, “haba Waziri, yaya za ka nemi ceton wanda ya kasance yana cutar da rayuka?” Waziri ya ce, “duk da haka Allah ya ba ka nasara, ai kurkuku wajen horo ne kuma wajen tarbiyya ne, domin ya kasance kabarin masu rai ne.” Da haka Sarki ya yi umarnin a kai shi kurkuku a ɗaura masa dabaibayi a k’afa, ya sa aka rubuta a jikin dabaibayin, ba za a kwance wannan daurin ba sai a wajen wankan gawa. Suka jefa shi cikin kurkuku. Mahaifiyarsa ta kasance tana yawan ziyartar gidan Sarki Halidu wanda yake hakimi kuma shugaban masu gadin birnin Bagadaza, kuma ta k’ark’ashinsa take ziyartar ɗanta har takan ce masa, “ba na sha gargaɗinka ka daina wannan mugun aikin naka ba?” Shi kuma sai ya ce mata, “wannan hukuncin Allah ne ya faɗa kaina, amma ina rok’onki ya uwata, idan kika je wajen matar Sarki Halidu ki nemi alfarmar a sake ni a wajenta.” To yau wannan niyya ta zo wajen wannan matar kuma ta gan ta cikin halin bak’in ciki. Ta ce mata, “a kan me kike wannan bak’in ciki?” Ta ce, “saboda ɗana Habzalam Bazazah.” Tsohuwa ta ce, “Allah sarki, me ya same shi?” Ta kwashe zance kaf ta shaida mata. Ta ce mata, “shin za ki fito min da ɗana daga kurkuku ni kuma na warkar da matsalar ɗanki?” Hatunu ta ce, “me kike buk’ata.” Tsohuwa ta ce, “ina da ɗa sunansa Amadu yana da ɗabi’ar sata, yanzu haka an ɗaure shi a kurkuku kuma an sa masa dabaibayi a k’afafu, sannan a jikin k’arfen an rubuta cewar ba za a cire su ba sai bayan ya mutu. To ina so ki yi shiga mai kyau na tufafinka ki tafi wajen mijinki da murmushi kina mai dariya da fara’a, to idan ya buk’ace ki kamar yadda miji ke buk’atar mata sai ki ture shi ki ce, ‘wallahi wannan abu bai dace ba! Idan miji na buk’ata wajen matarsa tana k’ok’arin biya masa har sai ya gamsu, amma idan mace na da buk’ata a wajen miji ba zai ba ta ba.’ A lokacin kuwa ya matsu, zai ce da ke ‘me kike so?’ Sai ki ce masa ‘ba zan faɗa maka ba sai ka rantse min cewar za ka share min hawayena’ idan ya rantse miki da Allah ko da ransa sai ki ce masa, ‘ka rantse min da saki.’ Kada ki yarda da komai sai da haka. Idan ya rantse da saki sai ki ce masa, “kun je kun ajiye wani mutum mai suna Ahmad Kamakin kuma yana da uwa wadda take tsohuwa abar tausayi. Ta zo wajena tana neman alfarma domin ka shige mata gaba wajen neman alfarma ga Khalifa idan ya fito zai tuba ya gyara halayensa, kuma kai za ka rika kula shi.” Hatunu ta ji wannan shiri sai ta amince, ta ce da tsohuwa, “na ji na

Zanci gaba insha allah08 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

tsohuwa ta shirya wa Hatunu matar Sarki Halidu duk abin da za ta ce da shi idan ya shigo, lokacin da ya shigo sai ya nufe ta da buk’atarsa gare ta. Ta sa ya rantse da saki kamar yadda aka koya mata, sannan ta gabatar da buk’atarta gare shi ya amince. A wannan dare ya kwanta da ita, sannan da safe ya yi wankan janaba ya yi alwalla ya yi sallar asuba sannan ya shirya ya tafi kurkuku ya samu Amadu Kamakin, ya ce da shi, “shin za ka tuba daga mugun aikinka?” Ya amsa ya ce, “ni tuni na tuba ga Allah maɗaukaki Sarki zuci da baki, kuma ina ta yin istigfari da hailala kullum.” Ya sa aka fitar da shi daga kurkuku amma dabaibayin na jikinsa har suka ce wurin Khalifa ya sunkuya ya sumbaci k’asa a gabansa.Sarki ya ce, “me kake so ne kai Halidu?” Sarki Halidu ya matso da Amadu Kamakin gaba ga Sarki yana tsalle saboda dabaibayin k’afarsa, Khalifa ya ce, “kai Amadu dama har yanzu kana nan da ranka?”

Sarki Halidu ya ce, “ranka ya daɗe ya kasance yana da mahaifiya wadda ba ta da mai kula da ita kuma ta tsufa ba za ta iya komai ba sai an taimaka mata. Shi ne ta rarrafo ta kama k’afa gare ni domin na nemi alfarma a gare ka a cire shi daga sark’a, domin kuwa ya tuba daga aikata mugun aiki.” Khalifa ya ce da Amadu, “shin ka tuba daga munanan ayyukanka?” Ya ce, “na tuba Allah ya ba ka nasara, ba zan sake aikatawa ba.” Daga nan Sarki ya umarci mak’eri ya zo ya datse marin, sannan ya maida shi tsohon muk’aminsa na shugaban masu gadin dare. Ya zo gaban Khalifa ya sunkuya yana mai godiya da fatar alheri. Khalifa ya sa aka ba shi tufafin masu gadin dare, sannan aka sanar da naɗinsa ga jama’a. Ya cigaba da aikinsa lokaci mai tsawo har wata rana uwarsa ta tafi wajen Hatunu matar Sarki Halidu domin yi mata godiya bisa k’ok’arin da ta yi ɗanta ya fito da kurkuku. Hatunu ta ce, “ni na cika miki alk’awari na faranta miki, amma ke har yau ba ki taimake ni bisa nawa burin ba, ba ki kawo Yasmin ga ɗana Habzalam Bazaza ba.” Tsohuwa ta ce, “da ma abin da ya kawo ni kenan wannan maganar.” Daga nan ta tashi ta tafi wajen ɗanta, ta same shi ya yi mankas da giya, ta ce masa, “ya kai ɗana, ka sani cewar dalilin kuɓutar ka daga kurkuku shi ne matar sarki Halidu da na samu ta shiga maganar ta kama k’afa da mijinta har ga shi ka fito. To kuma mun yi da ita zan umarce ka da ka hallaka Aladdini domin matarsa Yasmin ta fito, ɗanta Habzalam Bazaza ya aure ta.” Ya yi dariya ya ce, “wannan shi ne abu mafi sauk’in aikatawa, a daren yau ɗin nan zan samu dabarar halaka shi ta cikin ruwan sanyi. To a lokacin kuwa farkon wata ne, kuma a bisa al’adar Sarkin Musulmi a wannan daren yake shiga wajen uwargida Zubaidatu. Yakan sallami duk bayinsa da babanni da kuyangi ya kadaice da ita, haka kuma yakan ajiye kayan sarauta a wani ɗaki daban da takobinsa da hatimin Sarki duka a bisa wata kujera sai bayi su zagaye ta suna gadi har gari ya waye ya zo ya ɗauka. Haka kuma yana da wata butar azurfa wadda aka yi wa ado da jauhari ɗamara uku, sannan aka yi mata wani marik’i na zinariya wanda yake da tsada ainun. Duk waɗannan kayan a nan yake barin su tare da bayi suna kula da su har ya fito daga wajen uwargida. To, Amadu Kamakin ya san da wannan tsarin, ya bari sai da dare ya raba hasken wata tuni ya bace an kunna fitilu kowa ya yi barci, gari ya yi tsit, sai ya ɗauki takobinsa ya rike a hannun dama da k’ugiya da igiya a hannun hagu, ya doshi ɓangaren Khalifa ya haura ta sama ta hanyar amfani da k’ugiyar nan sannan ya faɗa ciki yana mai sanɗa da takawa sannu a hankali har ya je inda tagar ɗakin take ya lek’a ya ga duk bayin suna barci. Ya shak’a musu abin shak’awa na daga banju ya kwashe tufafin Khalifa da wuk’a da takobinsa da hatimi da mayani da kuma butar zinariyar nan. Sannan ya tafi gidan Aladdini wanda ke shan shagalinsa da amaryarsa har ya tara da ita ta samu ciki. Amadu Kamakin ya haura katanga ya ɗaga ɗaya da murafun magudanar ruwa ya hak’a rami ya sa kayan a cikin wani mayani sannan ya turbuɗe su cikin ramin ya mayar da murfin ya rufe, amma bai haɗa da butar zinariyar nan ba sai ya sa aljihu ta zama tasa. Bayan ya gama komai ya kama katanga ya haura ya koma mazauninsa kamar babu abin da ya aikata. Ya zauna a gidansa yana cewa bari na mayar da wannan butar abar da zan rik’a sha daga gare ta. Da asuba ta yi Khalifa ya baro wajen uwargida ya shiga ɗakin shak’atawa sai ya ga dukkan bayin suna sharar barci, ya dudduba su, ya gane cewar an shak’a musu wani abu ne. Ya kai hannunsa ga kujerar da yake ajiye kayan sarauta ya ji babu komai; babu rawani, babu alkyabba, babu hatimi da takobi da kuma butar zinariya. Nan take ya cika da matsanancin fushi ya tafi majalisa ya zauna yana kumbure. Waziri Ja’afaru ya zo gaba gare shi ya sumbaci k’asa sannan ya ce, “Allah ya tsare ka daga dukkan aibu ya Sarkin Musulmi.” Khalifa ya ce, “watau Waziri aibu mummunan al’amari ne!” Waziri ya ce, “me ya faru?” Ya faɗa masa abin da ya faru, a lokacin kuwa shugaban tsaro kuma hakimin Bagadaza, Halidu na wajen tare da Amadu Kamakin duk suna cikin kayan aikinsu, suka shigo domin kwasar gaisuwa, suka iske Khalifa cikin tsananin fushi. Khalifa ya ce da hakimi, “yaya Birnin Bagadaza ke ciki?” Halidu ya amsa cikin girmamawa, “tana nan lafiya kuma cikin tsaro.” Khalifa ya yi kururuwa ya ce, “karya kake yi!” Jikin hakimi Halidu ya yi sanyi ya soma ɓari, ya ce, “ta yaya?” Khalifa ya ba shi labarin abin da ya wakana sannan ya ce da shi, “ina umartarka da ka nemo min kayana da aka sace min.” Halidu ya ce, “ya Sarkin Musulmi, ka sani cewar da ɗan gari ake cinye gari. Na tabbata babu wani bak’o da zai shigo gidan nan sata face ɗan cikin gidan ko wanda ya san sirrin komai.” Khalifa ya tunzura ya ce, “ko dai ka tashi ka lalubo ɓarawon ko wanene ko kuma a rataye ka.” Halidu ya ce, “ranka ya daɗe, ba ni ya dace a rataye ba, Amadu Kamakin za a rataye domin aikinsa ne bin sawun ɓarayi, kuma babu wanda ya san malafarsu kamarsa.” Amadu ya rusuna gaban Khalifa ya ce, “na tsayawa Hakimi Halidu zan fanshe shi, na yi alk’awarin zan bi sawun ɓarawon nan ma ci amana, zan zak’ulo shi ko wanene. Kuma zan tona masa asiri komai matsayin muk’aminsa. Ina so a ba ni alk’alai biyu da masu sa ido biyu da jarumai biyu domin wanda ya aikata wannan abin ba ya tsoron tumbinka, kuma ba ya shakkar cin amanarka.” Sarki ya ce an ba ka abin da ka buk’ata, kuma a soma binciken daga gidana sannan a tafi ga Waziri sai kuma a tafi gidan Shugaban ‘yan sittin sai a bi ragowar ‘yan majalisa gwargwadon muk’amin kowa.”
Amadu Kamakin ya ce, “wannan ya yi daidai Allah ya ba ka nasara, kuma ina jin cewar wanda ya aikata wannan abu ɗaya daga cikin waɗanda Sarki ya yi rainonsu tun suna k’anana har suka bunk’asa ko kuma ɗaya amintattun fadar Sarki.” Khalifa ya yi kururuwa sannan ya daka tsawa ya ce, “wallahi idan aka kama ɓarawon nan ko da ɗan da na haifa a cikina ne sai na yi umarnin a rataye shi!” Daga nan Sarki yayi umarnin a ba wa Amadu Kamakin takardar iznin shiga gidaje domin gudanar da bincike ya shirya ya fita a hannunsa akwai sandar k’arfe wadda aka cuɗanya farin k’arfe da tagulla da darma da kuma bak’in k’arfe. Ya shiga gidan Khalifa, Jakadiya na tare da shi. Ya soma tun daga ɗakin k’warori har zuwa ɗakin baibayi da babanni da hadimai. Sannan ya tafi gidan Waziri ya aikata haka. Bayan nan ya tafi gidan manyan hakimai da sarakuna ‘yan mori duka har dai ya iso

2 Comments On HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI
avatar
saidou

1 year ago

Reply

Tyhfhhhjg

avatar
ummitah

1 year ago

Reply

Wow

Please Login or Register in order to submit comment