Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan Aladdini Abu Shammata, lokacin yana tare da matarsa suna hirar soyayya. Da ya ji ana k’wank’wasa k’ofa ya sauko daga bene ya buɗe k’ofa sai ya ga shugaban tsaro tare da mai bin sawu tare da wasu gungun mutane, ya tambaya “lafiya?” Suka faɗa masa abin da ya kawo su, sannan suka nuna masa takardar izni daga Khalifa. Aladdini ya ce, “to ku shigo ku bincika.” Sarki Halidu ya ce masa, “ya shugabana, kai ne wanda aka amincewa fiye da kowa a fadar nan, Allah ya kiyaye ka daga cin amanar Sarki. Ni ina ganin ba sai mun duba gidan nan ba.” Aladdini ya ce, “ai babu makawa sai an duba shi kamar yadda aka bincika na kowa.” Suka ɗuru zuwa cikin gidan gaba ɗayansu tare da alk’alai da shaidu kamar yadda suka shiga gidajen baya. Amadu Kamakin ya wuce kai tsaye zuwa inda ya ɓoye kayan nan da ya sato na Khalifa, ya daki murfin da k’arfi da sandarsa har sai da ya rugurguje sai ga haske na tasowa daga k’asa. Ya sa dungun sandar nan yana mai cewa, ‘bismillahi da sunan Allah mai rahma mai jin k’ai. Abin da Allah ya so shi zai tabbata! Albarkacin zuwanmu wannan waje mun samu kayan Sarki da aka sace. Bari mu tona mu ga abubuwan da ke ciki.” Alk’ali da shaidu suka matso kusa ya nuna wajen da sandarsa, bayi suka tone sai ga kaya a ciki. Aka fito da su duka aka baje, sannan aka rubuce dukkan abin da ke ciki ɗaya bayan ɗaya, alk’alai da shaidu suka rattaba hannu. Dogarai suka cafe Aladdinu, suka hamɓare rawaninsa, sannan aka aiko da wasu suka tattara dukkan dukiyarsa da kadarorinsa aka k’wace. A gefe ɗaya kuma Amadu Kamakin ya kamo kuyangar Aladdinu Yasmin wadda ke ɗauke da k’aramin ciki, ya ce a kai ta wurin matar sarki Halidu. Habzalam Bazaza na ganin ta sai ya warke daga cutar da ke damunsa ba tare da ɓata lokaci ba ya yi farin ciki mai yawa, ya tashi ya tafi gare ta zai rik’e mata hannu. Ta fisge hannunta, ya sake bin ta, ta ɗauko wuk’a daga ɗamararta ta ce, “tafi daga gare ni, ko kuma na kashe kaina.” Uwarsa da ke kallonsu ta ce, “ke sakarya, ki k’yale ɗana ya ji daɗi da ke mana.” Yasmin ta kalle ta a fusace ta ce, “ke shaiɗaniya faɗa min wacce shari’a ce ta yarda mace ta auri maza biyu a lokaci guda? Bari wannan maganar ma, ina kika taɓa ganin kare ya ci abinci tare da zaki?” Da wannan mummunan yaron ya ji wannan maganar sai ciwonsa ya dawo ya ji matuk’ar ciwon rashin biyan buk’atarsa da abar k’aunarsa. Ya kwanta ya rungume matashin kai. Uwar ta zabura da kanta ta ce, “ke mazinaciya don me ba za ki yayewa ɗana bak’in cikinsa ba? Wallahi sai na ɗanɗana miki mugunyar azaba. Aladdini kuwa kamar an rataye shi an gama ne.” Yasmin ta harare ta ta ce, “wallahi ni da Aladdini mutu ka raba.” Hatunu ta tashi a fusace ta fisge jauhari da zubarjadi da dukkan kayan adon Yasmin, ta k’wace mayafinta da tufafinta na alharini. Ta bata wata k’aramar riga da da falmaran mara yalwa irin kayan Habasha da mayafin gashi, ta aika da ita wajen dahuwa tare da kuyangi masu aikin gida. Tana mai cewa, “wannan shi ne sakamakon taurin kan ki. Daga yau ke ce mai ɗauko itace, ke ce mai hura wuta, kuma ke ce mai yanka albasa.”
Ta ce, “na yarda da kowace azaba da wulak’anci amma ba zan yarda ɗanki ya raɓe ni ba.” To amma Allah da ikonsa sai kuyangin dahuwar nan suka ji suna k’aunarta, suka zama suna yi mata hidima. Wannan kenan game da Yasmin. Shi kuwa Aladdini dogarai suka cukuikuye shi tare da kayan satar zuwa fada, Khalifa na zaune bisa gadon sarauta ya hakince ga manyan fada nan a zazzaune hagu da dama, kana ga dogarai sun zare takobi ba sa ko motsawa. Ya dubi kayan satar sannan ya ce da su Amadu Kanmakin, “a ina kuka gan su?” Suka ce a tsakiyar gidan Aladdini Abu Shammata.” Sarki ya cika da fushi har ya batse, ya rik’a duba kayan ɗaya bayan ɗaya, ya ga babu butarsa a ciki, ya waiwaya ga Aladdini ya ce, “ina butata?”
Aladdini ya marairaice ya ce, “ni ban yi maka sata ba, kuma ban taɓa ganin waɗannan kayan ba, ban ma san komai dangane da su ba.” Sarki ya harare shi ya ce, “ka tabbata ma ci amana! Ta yaya zan jawo ka jikina kai kuma ka yi jifa da ni nesa, na amince maka, ka ci amanata?” Ya bada umarnin a rataye shi. Shugaban tsaro kuma hakimin Bagadaza ya zagaya da shi cikin birni mai kira yana shela yana cewa wannan shi ne ma fi k’arancin sakamakon wanda ya ci amanar Khalifa Sarkin Musulmi. Mutane suna da yawa a inda za a rataye shi.

Zanci gaba09 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

Aladdini ya marairaice ya ce, “ni ban yi maka sata ba, kuma ban taɓa ganin waɗannan kayan ba, ban ma san komai dangane da su ba.” Sarki ya harare shi ya ce, “ka tabbata ma ci amana! Ta yaya zan jawo ka jikina kai kuma ka yi jifa da ni nesa, na amince maka, ka ci amanata?” Ya bada umarnin a rataye shi. Shugaban tsaro kuma hakimin Bagadaza ya zagaya da shi cikin birni mai kira yana shela yana cewa wannan shi ne ma fi k’arancin sakamakon wanda ya ci amanar Khalifa Sarkin Musulmi. Mutane suna da yawa a inda za a rataye shi. Wannan kenan game da Aladdini. Ahmad Danafi kuwa, wanda ya rik’i Aladdini a matsayin ɗansa kuma yake kula da shi, a ranar ya kasance yana gonarsa yana nishadi tare da jama’arsa sai ga wani mai shela nan daga fada ya zo wajensa ya sunkuya ya gaishe shi sannan ya ce, “kai kana zaune a nan kana ta nishaɗi ba ka san abin da ke faruwa ba.”Ya zauna sosai daga kishingiɗar da ya yi ya ce masa, “me yake faruwa?” Mai labari ya ce, “sun tafi da ɗanka Aladdini zuwa marataya ga shi can za su rataye shi.” Ya kwashe zance kaf ya shaida masa. Ahmad Danafi ya waiwaya ga Hassan Shaumani ya ce, “me kake gani game da wannan al’amari?” Hassan ya ce, “na tabbata Aladdini ba zai aikata wannan ba, k’arshenta wani mak’iyinsa ne ya shirya masa kutuguilar nan domin ganin bayansa.” Ya ce, “to ina dabara?” “Insha Allahu za mu je yanzu mu cece shi Ya zabura ya tafi kurkuku ya ce da mai tsaron k’ofa, “ba mu wanda aka yanke masa hukuncin kisa.” Ya ba shi wani da yake kama da Aladdini, suka rufe masa ido suka tafi da shi wajen rataya yana tsakanin Ahmad Danafi da Aliyu Zaibaku mutumin Alk’ahira. Suka tarar har an ɗora Aladdini a bisa itace za a zarga masa igiya, Ahmad Danafi ya matsa ga mutumin mai rataya ya zungure shi da k’afa, ya waiwayo yana cewa “ku k’yale ni na cika aikina.” Ahmad ya ce masa, “kai sakarai ka manta alherin wannan mutumin? Ungo wannan da ya cancanci rataya a maimakonsa. Ina tabbatar maka bai aikata abin da ake zarginsa ba, za mu musanya shi da wannan kamar yadda aka fanshi Annabi Isma’ila da rago.” Mai rataya ya karɓi wannan mutumin ya rataye shi. Ahmad Danafi ya tafi da Aladdini gidansa. Aladdini ya ce da shi, “ya babana kuma shugabana, Allah ubangiji ya biya ka da mafificin sakamako.” Ahmad ya ce, “ba komai Aladdini.”
A nan asubahi ta riski Shaharzad ta katse zancenta mai dadin saurare.
DARE NA 265
A dare na ɗari biyu da sittin da biyar, Shaharzad ta ce na samu labari ya kai wannan hamshakin sarki, Ahmad Danafi ya ce da Aladdini “babu komai don wannan, amma ina so ka faɗa min ainihin abin da ka aikata. Allah ya jik’an wanda ya ce, ‘kada ka yi ha’inci ga wanda ya amince maka ko da ka kasance maha’inci. Khalifa Sarkin Musulmi ya amince maka, ya ambace ka cikin amintattu ya jawo ka jikinsa amma don me za ka ɗauki kayansa?” Aladdini ya ce, “wallahi ya baffana, na rantse da ubangijin halitta mamallakin sama da k’asa ban aikata wannan ba kuma ba ni da hannu a ciki sannan ban san wanda ya aikata ba.”
Ahmad ya ce, “babu shakka wannan sa hannun mak’iya ne amma da sannu aniyarsa za ta koma kansa. Sai dai ka sani ba ka da sauran zama a birnin Bagadaza, domin ba a gaba da sarakuna a ci nasara. Idan sarakuna suna nemanka da mugunta ba ka da sauran zama a wurin domin ba za ka kai labari ba.” Aladdini ya ce, “ya abbana ina kenan zan tafi?” Ya ce, “zan sadar da kai ga birnin Iskandariya domin gari ne mai albarka ga korayen bishiyu sannan abincinsu mai daɗi ne.” Aladdini ya ce, “na amince da hakan ya babana.” Ahamad ya ce da Hassan Shaumani, “idan Sarki ya tambaye ni ka ce na tafi yawon rangadi cikin yankin birane.” Ya dauki Aladdini suka tafi suka bar Bagadaza, suka isa wani gari mai tuddai da korayen bishiyu da gonaki, a nan ya ga wasu Yahudawa su biyu a kan alfadarai ya je gabansu ya tsaya ya ce, “ku kawo kudin hakk’i.” Suka ce “saboda me za mu baka kudin hak’k’i?” ya ce musu “saboda ni ne wakilin waziri Ja’afaru mai kula da wannan yanki.” Suka ɗauko kuɗi suka ba shi, kowannen su dinari ɗari. Ya sa takobi ya sare su suka mutu, ya ɗauke alfadarunsa ya hau ɗaya, Aladdini ya hau ɗaya. Suka ci gaba da tafiya har suka kai Birnin Ayas, suka shigar da dabbobinsu cikin wani daki suka yi barci. Da gari ya waye Aladdini ya sayar da alfadararsa ya bayar da ta Ahmadu Danafi ga mai tsaron k’ofar gidan bak’i. Sannan suka hau jirgi zuwa birnin Iskandariya.
Da suka isa sai suka wuce kasuwa suka ga wani dillali yana shelanta wata rumfa da kayan cikinta a kan dinari ɗari tara da hamsin. Aladdini ya k’ara dinari hamsin ya zama dubu. Dillali ya sallama masa domin rumfar ta baitulmali ce, ya biya kuɗin tare da la’ada aka ba shi mukullanta ya buɗe ya ga zannuwa ciki shimfiɗaɗɗu da zanannu masu kyau da dardumai. Kuma ya ga wani waje cike da kayan jirgin ruwa da tarkace masu yawa na daga jaka da alharini da masaukai da igiyoyi da turare da abinci da kayan faɗa su takobi da wuk’a da kibiya da masu, da sauran su da yawa. Aka shaida masa cewa ma’abocin rumfar baba ne, ya mutu ba shi da magaji, ya kasance yana sayar da kayan hannu masu rangwamen farashi. Aladdini ya zauna a rumfa ya gyara waje sannan Ahmad Danafi ya ce masa, “ya ɗana yanzu dai ga rumfa ka samu har da wurin kwananka ciki. Ka yi zamanka a nan kana saye kana sayarwa, ka nemi albarka daga ciniki domin Allah maɗaukakin Sarki ya sanya albarkarsa ga ciniki.” Bayan wannan ya zauna da shi kwana uku, a rana ta huɗu ya yi masa sallama yana mai ce masa, “ka zauna nan har na samu zarafin da zan nemar maka gafara wajen Khalifa.” Sannan ya hau jirgi ya koma birnin Ayas ya hau alfadararsa ya tafi Bagadaza. Ya tambayi su Hassan Shaumani cewa, “Khalifa kuwa ya tambaye ni?” Suka ce, “bai yi maganar ka ba.” Ya cigaba da aikinsa amma ya kasance kullum yana k’yank’yasar labarin Aladdini a fada.
A fada kuwa ranar da aka ce a rataye Aladdini ana cikin fadanci sai Khalifa ya yi ajiyar zuciya ya ce da Waziri, “kai Waziri, wai haka Aladdini ya yi min ko?” Waziri ya ce, “Bai kyauta ba ko kaɗan, amma dai ka yi masa abin da ya kamace shi ka sa a rataye shi.” Sarki ya ce, “tashi mu je mu gan shi.” Yayin da suka isa wajen tuni mutumin da aka rataye rai ya yi halinsa, an kwantar da shi za a tafi a turbuɗe shi. Khalifa ya dubi gawar ya ga wannan ba Aladdini ba ne. Ya juya ga Waziri ya ce masa, “wannan ba Aladdini ba ne! Kai ba ka san shi ba?” Ya k’ara da cewa, “Aladdini gajere ne, wannan kuwa dogo ne.” Waziri ya ce, “k’ila igiyar rataya ce ta ja shi ya yi tsawo haka.” Khalifa ya ce, “Aladdini yana da hasken fata, wannan kuwa fatarsa ta yi duhu.” Waziri ya ce, “jininsa ya yi k’asa saboda zafin rataya.”Sannan Sarki ya duba k’afafun wannan mutumin ya ga tafukansa ya rubuta sunan Abubakar da Umaru domin muzanci. Khalifa ya ce da Waziri, “kai Waziri, Aladdini Sunni ne na hak’ik’a wannan kuwa Shi'a ne.” Waziri ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allah da ya bayyanar da gaskiya, ashe Aladdini Tak’iyya yake mana ba mu sani ba.” Khalifa ya so ya buɗe fuskar mutumin suka hana shi domin ya saɓa shari’a.Daga nan Khalifa ya yi umarnin a turbuɗe gawar. Aka mance da zancen Aladdini kamar daɗai duniya ba a yi shi ba. Wannan kenan.10 HIKYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

Shi kuwa Habzalam Bazaza kullum sai ciwon son Yasmin ke k’aruwa cikin zuciyarsa har ciwon dai ya yi k’amari a k’arshe ya mutu. Aka binne shi. Matar Aladdini kuwa ta ida kwanakin cikinta, ta durk’usa nak’uda tare da taimakon kuyangin da suke aiki tare ta haifi ɗa namiji. Suka wanke shi suka sa masa riga sannan suka ce mata, “yaya sunansa.” Ta ce, “da a ce mahaifinsa na kusa shi ya dace ya ba shi suna, amma tunda ba ya duniyar na ambace shi da Aslanu.” Ta raine shi har shekara biyu sannan ta yaye shi, ya soma koyon zama daga nan sai rarrafe sai tafiya. Wata rana uwarsa na aiki a wajen dahuwa ba ta lura ba har ya fita waje ya hau bene ya wuce zuwa ɗakin bak’i har zuwa farfajiyar maigidan. Sarki Halidu ya ganshi ya ɗauke shi ya ɗora shi a kan cinyarsa yana masa wasa, yana tsarkake Allah game kyawon wannna yaron. Ya dube shi sosai ya ga alamun kamannin Aladdini tattare da shi. A waje kuma mahaifiyarsa na ta nemansa ba ta ganshi ba. Ta lek’a ko’ina ba ya nan sai ta hau kan bene tana k’wala masa kira sai ga Sarki Halidu ya fito yana rik’e da shi. Ta sunkuya cikin jin kunya, da yaron ya ga uwarsa sai ya yi nufin zuwa gare ta amma Sarki Halidu ya rik’e shi domin k’aunarsa ta afu cikin zuciyarsa. Ya ce da Yasmin, “matso kusa mana.” Ta matsa kusa. Ya ce, “wannan ɗan na wanene?” Ta ce “shi ne furen zuciyata.” Ya ce, “wanene mahaifinsa?” Ta ce, “mahaifinsa shi ne Aladdini Abu Shammata amma yanzu ya zama ɗanka.” Sarki Halidu ya ce, “to ai shi Aladdini ya zama ma ci amana, Sarki ya la’ance shi.” Ta yi farat ta ce, “Allah ya kiyashe shi da wannan mugun aiki, babu ta yadda mai gaskiya da rik’on amana zai juye ya zama maha’inci mai warware alk’awari kuma ma ci amana.” Da ya ji haka sai ya sake babin zancen ya ce mata, “ina son wannan yaron, kuma ina so na raine shi a matsayin wanda na haifa.” Ta ce, “Allah ya taya ka rik’o.” Ya ce, “ko da ya girma ba na so ya gane cewar ba ni ne na haife shi ba. Idan ya tambaye ki game da babansa ki jadadda masa cewar ni ne.” Ta amsa, “na ji, na bi.” Ya cigaba da rainon yaro har ya isa kaciya sannan ya mik’a shi ga masana ilmi da dabarun zaman duniya. Aka koya masa ilmin addini da balaga da hadisai da nahwu da Kur’ani mai girma. Ya sauke Kur’ani sau biyu kuma ya haddace shi da kansa. Ya girma tare da Sarki Halidu yana masa ladabi da biyayya a matsayin babansa. Haka nan kuma kowa yake masa wannan kallon. Sarki Halidu da kansa ya koya masa doki da sukuwa da jifa da mashi da sara da harbi da suka, da sauran dabarun faɗa da yak’i. A lokacin da ya kai shekaru sha huɗu ya zama sadauki tsakanin sa’o’insa har ya zama yana iya jan tawaga ko fita taya ubansa aikin tsaron gari.
Ana nan wata rana ya ziyarci Amadu Kamakin sai ya nemi ya raka shi mashaya domin ya shawo giya. Da suka je aka kawo masa giyar a kasko sai ya juye ta cikin butar nan da ya sata ta Sarkin Musulmi. Ya rik’a tuttulo giyar daga ciki yana sha har ya bugu. Aslanu ya ce da shi, “ya shugabana ba ni wannan butar ina so.” Ya ce, “ina, ai ba zan iya ba ka wannan butar ba.”
“Saboda me? Aslanu ya nemi bahasi.
“Saboda a dalilinta har rai aka yi asara.” Amadu Kamakin ya faɗa yana gyatsar giya. “Ran wa aka rasa?”
“Bari dai na faɗa maka labarin tun da ya riga ya wuce, ka sani wannan butar ta janyo a kashe wani mutum mai suna Aladdini Abu Shammata, wanda shi ne shugaban zaɓaɓɓu sittin.” Yaro ya sake gyara zama ya ce, “faɗa min labarin da yadda ya rasa ransa a kan buta.” Amadu Kamakin ya ce, “kai kana da wani ɗan uwa sunansa Habzalam Bazaza, lokacin da ya balaga ya isa aure sai mahaifinka ya nemi ya saya masa wata kuyanga mai suna Yasmin.” Ya shiga ba shi labari daga farko har k’arshe, har ma da cutar da ta kashe Habzalam Bazaza da yadda suka shirya makirci akan Aladdini. Duk fa bai san Aslanu ɗan Yasmin ba ne, domin a iyakacin saninsa ubansa Sarki Halidu kaɗai ya sani. Yayin da ya gama jin labarin sai Aslanu ya ce a ransa, “duk yadda aka yi kuyangar nan ita ce mahaifiyata, kuma ubana shi ne Aladdini domin na ji a mafi yawan lokuta tana ambatonsa. Daga nan yaro ya fita cike da bak’in ciki da ɓacin zuciya ya nufi gida, ya wuce ta gaban su Ahmadu Danafi, yana hango shi sai ya zabura ya ce, “tsarki ya tabbata ga wannan da ba shi da kishiya kuma babu kamarsa a halitta!” Hassan Shaumani ya ce masa, “me ka gani haka kake mamaki?” Ahmad ya ce, “wallahi yaron nan mai wucewa kamar an tsaga kara shi da Aladdini domin har tafiyar ma irin tasa ce.” Ya sa baki ya kira yaron, ya tambaye shi sunansa ya faɗa masa, sannan ya ce, “yaya sunan mahaifiyarka?” Nan ma ya faɗa masa. Yana jin haka ya ce, “yaron yi murna ka daina bak’in ciki, idanunka su yi sanyi domin babu wanda ya kasance mahaifinka sai Aladdini Abu Shammata.” Ya faɗa masa duk abin da ya sani. Daga k’arshe ya ce masa, “ka tafi wajen mahaifiyarka ka tambaye ta wanene mahaifinka na gaskiya za ta faɗa maka.” Ya tafi ya samu uwarsa ya ce mata, “wai shin wanene ubana na gaskiya?” Ta ce masa, “Sarki Halidu shi ne mahaifinka.” Ya ce, “ba shi ba ne, an ce min sunan ubana Aladdini Abu Shammata, wanda aka rataye bisa zargin cin amanar Khalifa.” Uwar ta yi kuka mai yawa sannan ta ce, “wa ya faɗa maka haka?” Ya ce “shugaban masu gadi Ahmadu Danafi.” Saboda haka ta habarta masa labarin daga farko har k’arshe. Ta k’ara da cewa, ya ɗana, hak’ik’a gaskiya ta bayyana, k’arya kuma ta gushe, domin babu shakka Aladdini Abu Shammata shi ne ubanka na gaskiya, amma Sarki Halidu shi ya raine ka ya yi maka tarbiya kamar yadda uba ke yi wa ɗansa. Kuma ina so idan ka sake gamuwa da Ahmadu Danafi ka haɗa shi da girman Allah domin ya taya ka ka ɗauko fansar kisan da aka yi wa mahaifinka bai ji ba, bai gani ba.” Da ya same shi kuwa ya fada masa irin yadda mahaifiyarsa ta umurta. Ahmad ya ce, “ba komai Aladdini.”
A nan asubahi ta riski Shaharzad ta katse zancenta mai dadin saurare.
DARE NA 266
A dare na ɗari biyu da sittin da shida, Shaharzad ta ce na samu labari ya kai wannan hamshakin sarki, Yaro ya tafi Ahamdu Danafi yana kuka, ya rok’e shi tamkar yaddda mahaifiyarsa ta umarce shi. Ahmadu Danafi ya ce, “to wanene ya hallakar da mahaifin naka?” Aslanu ya ce, “Amadu Kamakin ne.”
“Wa ya faɗa maka haka?”
Aslanu ya shaida masa yadda suka yi da shi lokacin da ya ziyarce shi har zuwa abin da ya faɗa masa a mashaya game da butar shayin Sarkin Musulmi wadda ya mayar ta abar shan giyarsa. Ahmadu Danafi ya yi shiru sannan ya nisa ya ce, “abin da nake so da kai shi ne, duk lokacin da ka ga Sarki Halidu ya yi shigar ɗamara zai tafi fada, sai ka ce ya tafi da kai domin ka kwashi gaisuwa wurin Khalifa. Idan ka tabbata a gaban Khalifa sai ka aikata wata bajinta ta jarumai yadda za ka k’ayatar da shi. Sarki zai ce ka faɗi buk’atar ka a biya maka. A nan sai ka ce burinka shi ne a ɗauko fansar kisan da aka yi wa mahaifinka. Idan Sarki ya ce ai mahaifinka yana nan a raye kuma ga shi nan ma tare da mu, sai ka ce hak’ika Sarki Halidu shi ne marik’ina wanda ya raine ka har na girma. Amma mahaifinka na gaskiya shi ne Aladdini Abu Shammata. Idan sarki ya ce maka to wanene ya yi sanadiyar mutuwarsa? Sai ka ce ba wani ba ne sai mai bin sawu watau Amadu Kamakin. Daga nan sai ka faɗa musu dukkan labarin da ka sani. Kuma ka k’ara da cewa a bincike shi yanzu haka butar na nan tare da shi.” Aslanu da ya ji haka sai ya ce, “na ji na amince.” Ya sumbaci hannun Ahmadu sannan ya tafi wajen Sarki Halidu, cikin sa’a ya same shi yana shirin tafiya zuwa fada, nan take ya nemi alfarmar a ba shi damar shi ma ya je. Suna zuwa suka tarar Sarki da jama’arsa gaba ɗaya an fito ana harama za a fita bayan gari domin gwajin yak’i tsakanin askarawa. Sarki ya raba askarawa kashi biyu; aka ajiye wata sanda ga kaso ɗaya na askarawan aka ce kaso gudan su yi k’ok’arin ɗauko wannan sandar su kuma sauran kason su hana su ɗauka.
A cikin jama’ar da suka halarci wannan gwajin ashe akwai wani da aka ɗauko hayarsa domin ya hallaka Khalifa. Ana cikin gumurzu ya ɗauki mashi ya girgiza ya saita Khalifa ya jefe shi a saitin kirjinsa. Aslan na lura da shi ya daka tsalle ya cafe mashin sannan ya mayar masa, da yake an shirya mashin yadda ba zai yi kisa ba sai ya shiga a tsakanin kafaɗarsa da wuyansa ya faɗi sumamme. Khalifa ya yi kururuwa yana mai cewa, “Allah ya saka wa Aslanu da alheri!” Gaba ɗaya suka sauka daga dawaki Sarki ya zauna bisa kujera aka zo da wanda ya yi wannan yunk’uri a ɗaɗɗaure. Ya ce masa, “faɗa min dalilinka na son halaka ni. Shin kai masoyinmu ne ko mak’iyi?” Mutumin ya ce, “ni mak’iyinka ne, kuma ina nufin na kashe ka ne.” Khalifa ya ce, “don me zaka kashe ni? Kai ba musulmi ba ne?” Ya ce, “A’a, ni Bajushe ne.” Khalifa ya sa a tafi a sare wuyansa. Sannan ya waiwaya ga Aslanu ya ce masa, “tambayi abin da kake buk’ata a gare ni.” Aslanu ya faɗi tamkar yadda aka koya masa, ya k’ara da cewa “mahaifina shi ne Aladdini Abu Shammata.” Khalifa ya ce, “to ai idan haka ne mahaifinka ya ci amanar k’asa ne, ya aikata aikin da ba za a yafe masa ba.” Aslanu ya ce, “Allah ya ja da ran sarki, ina neman tsari ga Allah mahaifina ya zama tamkar haka. Amma abin da ya faru shi ne mak’iyinsa ne ya shirya masa wannan musiba.” Ya kwashe zance gaba ɗaya kaf ya shaida wa sarki. Tun kafin ya kai k’arshe ya fashe da kuka ya marairaice wa sarki yana mai cewa, “ka ɗauko min fansar jinin mahaifina ya Sarkin Musulmi!” Khalifa ya daka tsawa ga dogarai ya ce, “ku kama Amadu Kamakin!” Nan da nan aka damk’e shi yana rantse – rantse. Khalifa ya umarci Ahmadu Danafi ya bincike shi sai ga buta a tare da shi. Khalifa ya ce masa, “kai maci amana zo nan gaba gare ni! Ina ka samo wannan?” Amadu Kamakin ya soma rawar jiki saboda firgita ya ce,

2 Comments On HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI
avatar
saidou

1 year ago

Reply

Tyhfhhhjg

avatar
ummitah

1 year ago

Reply

Wow

Please Login or Register in order to submit comment