Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayani renon yaran,idan yana gida kuwa a wajenshi suke yini,ni kuwa bana garajen zuwa inda yake saboda Yusuf Kiri Kiri yake sake son sanyani wata nakudan tun ganin da yayi ina sallah yake ta bibiyata Albarkacin kakata da takemun zaman arbain ne ya ceceni...ita ma abinka da babba ta gane ne sai ta sanya mana ido sosai,ranar da ta shigo bedroom ta iske yusuf tsam ya rungumeni yana rokona naje dakinshi .sai ko karaf kaka ta cafke da cewa yau me zangani da yaran zamani,wato ke baki gama warsakewa daga wannan nakudar ba kuke kokarin shiga hakkin yara kanana,toh bada ni ba maza ka tashi ka bar mana dakin,kai gaskiya tsofi basu da kunya.

Sumsum Yusuf ya mike ya koma dakinshi to tun daga ranar duk zuwan da zaiyi idon kaka a kanshi bayan fitanshi take sanarmun cewa sai sun kuma gyarani na tsawon sati hufu kafin na koma wajen Yusuf...muna cikin sati na biyar tafiyar gaggawa ta Kama Yusuf zuwa Brazil official visit ne da za su tafi da shugaban kasa amma shi zaiyi wata daya kafin ya dawo.daren ranar yaso ya kasance da ni amma sai ga jini ya kuma zuwa ba dama cikin dubara na dan sauke mashi kewata da yake damunshi.da safe kuwa tun karfe takwas ya yi mana sallama,ni kuwa har da dan kukana na ban kwana da masoyi.ya tafi badan ya so ba...

da nayi mashi rakiya wajen motarshi tsawon lokaci muka dauka muna sumbatar juna da kanshi ya gaji ya sakeni bayan ya sumbaci ummu ayman da na fito tare da ita.Safe journey my hubby may Allaah protect you and return you safely back to me.

Shima cikin murmushi ya yi mun sumba a bayan hannuna sannan ya ce I will my wify ki kularmun da kanki da yarana...kai kawai na gyada mishi saboda kukan da yakeson kamani...

Sai da na koma cikin gidan na iske su kaka da nanny's din suna ta hiransu cikin kwanciyar hankali.na wuce na shige bedroom..a daddafe muka gama wankan kwana arbain har da 'yan kwanaki daidai sati hudu da tafiyar yusuf kenan duk da wayan da muke yi da shi hakan bai hanani kyawarshi ba.wasa wasa har ya kai wata biyu bai dawo ba yana dai jaddadamun cewa aikin da yaje yi ne har yanzu basu kammala ba.cikin wannan lokacin kuwa komai na jikina ya canja nayi wani irin fara sai kyalli nake saboda gyara turaren tsugunno kuwa babu garin Allaah da zai waye banyishi ba.

A haka har Yusuf yakai wata shida bai samu dawowa ba cikin wannan lokaci kuwa na matukar shiga damuwa har nake ganin kamar bazai dawo ba sai korafi nake mashi yana bani hakuri da cewa ya ma fi mu shiga damuwa saboda yaranshi yanzu har sun shiga wata na shida.duk da mun koma gidanmu da humaira ta haihu muka je gida bamu koma ba.watan yaran bakwai daidai suka fara tafiya da kafafunsu sai kiciniya suke,saboda rashin zamansu awajena duk sai suka daina shan nono.yau laraba na shirya su tsab muka je gidan khalid,tarba na musamman sukayi mana da shi da matarshi gaskiya tana da kirki sosai.muna kan shirin komawa gida khalid ya rokeni da na bar musu yaran su kwana biyu da shi tunda basa shan nono.saboda da kawaici na barsu amma badan ina so ba haka na hada su da nanny's din,na koma gidana dagani sai khadiza dayar nanny din kenan saboda ta tayani zaman gidan.

Ina zaune bisa sallaya bayan na idarda sallah ina lazumi,tunanin mijina ya tsayamun yau wata bakwai da tafiyarshi bayan ya ce mun wata daya duk kiran da zai yi sai ya ce ya kusan zuwa hakuri ya bani akan ankuma kara masu kwana ishirin akan wasu dalilai da bazai yuwu ya fadesu a waya ba.to gashi yau lokacin yayi ko me zaicemun?


Yau alkamis da safe sai kaiwa da kawowa nake a cikin gidan kewace ta fi komai damuna 'ya'ya na watansu daya a gidan Khalid ga yusuf shiru ga karatuna kuma ya kare bani da abin yi sai zaman gida,wayar Lil Yusuf na kira akan ya je gidan Khalid ya debomun yarana shiru bai kuma cemun komai ba da na tambayeshi sai ya ce shi gaskiya bazai iya zuwa gidan Khalid karbar yaran ba tunda shi khalid din bai kawo su da kanshi ba...ni kuma na kasa zuwa gidan Khalid karbarsu.ina kwance kan gadona ni kadai na lulluba da bargo barci ya kasa daukata duk da ana muku mukun snow garin duk ya Kara sanyi.waya ta yi Kara ina dagawa kuwa muryar Yusuf ne ya shiga bani hakuri da cewa kiyi hakuri my wify mutanen nan sun kuma karamun sati shida kafin na dawo haba tun kafin ya karasa zancenshi na shiga yi mashi kuka ina cewa nikam zaratun na shiga uku da wannan lamarin,na ce ni na gaji watanin bakwai sun kare bayan ancemun wata daya na hakura sannan yanzu zaka kuma cewa sun Kara maka har sati shida,to ni ya isheni idan kai baka damuba.

Cikin sauri ya ce haba maman 'yan uku ke kina kuka yaran kuma fa?

Na ce oho suma sun san kewar ubansu ta dameni.

Sai ya ce kedai budemun kofa.
Na ce eeh!ya ce budemun kofa my wify kar snow ya daskarar da ni.

Na tabbata da gaske yake tunda Ana snow din sosai,cikin Sauri na sauko na bude mashi kofar,ya na tsaye da dan brief case dinshi a hannu,tsalle na yi na makalkaleshi shima ya kankameni ya shure ni da gudu sai dakinshi,dama kuwa kullum a tsaftace yake ga kamshin turare da ke tashi Wanda duk wayewar gari sai na gyara na sanya turaren wuta.ba tare da muncewa juna komai ba Yusuf ya shiga tubeni,nima na shiga tubeshi,saboda tsananin matsuwa da mukayi da juna sai na ji tamkar ba mu taba mu'amala mai dadi na ran nan ba ina kwance a jikinshi Yusuf ya na mayar da numfashi a hankali ya ce yarinya yarana fa ina son ganinsu.

Na Kara kankameshi sosai na gyara kwanciya ta na shiga bashi labarin komai har da sanya Lil Yusuf ya daukomun su yaki zuwa,ya ce shi yanajin kunya ya je ya debosu tunda Khalid din bai maido su ba.

Ya yi murmushi ya ce gaskiya Lil Yusuf ya yi tunani mai kyau ko ni ne bazan je wajen khalid amso yarana ba.idan ya kawosu to idan bai kawo ba sai mu hakura mu nemo wasu.

Na yi murmushi na shiga bashi labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarshi shima yashiga fadamun abubuwan da yayi da course din da ya yi da komai tsawon lokaci muna hira,sannan muka fito mukayi wanka,ya wuce part dinshi ni kuwa na wuce kitchen domin hada mashi girki,dama na yi kubza na sai na hada miyarshi da nikekken nama da green beans da potatoes da na yayyanka kanana sai kuma na shirya mashi York shire pudding da roast beef,ga abubuwan da na yi amfani da su,flour,Kara,madarar ruwa,man gyada,sai gishiri kadan.naman saniyar nawin kilo daya nayi amfani da shi,na huda shi da kusurwa biyu na daureshi da irin jijiyar nan da aka samu a kings way ta yin gashin nama na dauko blue band na da ya ji hadin Maggi gishiri spices na dinga murzawa ajikin naman sai da na tabbatar sun gama shiga jikin naman sannan na sanya shi cikin oven na rufe su.na shiga aikin flour da na kwabashi na shiga suyan Yorkshire pudding da man gyada yana fitowa bisa tsarin yankar da na yi tamkar kobo kobo .sai da na tabbatar komai ya kammalu na shiga wanka nayi na fito na tsara kwalliya ta musamman na tarbar mijina sai da na jera komai bisa danning sannan na wuce dakin Yusuf fuskata sai kyalli yake saboda make up ga wani kamshi da ke tashi a jikina kamar amarya....
Ina murza kofar kuwa shima cikin shirin fitowa mukayi kicibis da shi ido ya zubamun ya tsaya kallona tamkar yau ne ya fara kallona........







_wannan kenan_







*vote@Wattpad teemacool2020*


⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*

Wattpad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


*Today's Beautiful Hadith is about Dua*

It was narrated that Mu'adhbin Jabal (RA) said: "The Messenger of Allah (peace be upon him) took my hand and said: 'I love you, O Mu'adh!' I said: 'And I love you, O Messenger of Allah (peace be upon him).' Then the Messenger of Allah (peace be upon him) said: 'Never forget to say in every prayer: Rabbi a'inni 'ala dhikrika wa shukrika wa husni 'ibadatik (My Lord, help me to remember You, give thanks to You and worship You well.)"

(Sunan an-Nasa'i, Book 13, Hadith 125)

*_Every person in your life has been put there by Allah (SWT). Over 7.5 billion people in the world yet Allah has put a handful of people in your life, your community who make up the experience you will have. Take care of your family, your community and yourself, knowing that by remembering Allah, thanking Him, praising Him and loving one another for the sake of Allah not only gains you blessings and rewards, it cements your legacy too. We thank Allah for every single person He has put in our lives and we thank Allah for YOU!_*



*Xea saeed*
*Aceyer*
*Madeenah*
*Munayah*
*Mameey*
*Nerhnerh*
*Asiya Musa*
*Khadija m*
*Sa'adatu ishak*
*Fatima zarah*
*Maman fareed*
*Ummul ihsan*

*Sai fans na group din Hausa novel*
*Hausa online novel*.
*Gaskiya kuna da yawa da sauran fans na group ma bambamta ina samun sakonninku ina sonku sosai da sosai thanks for your care and courage*

*Musamman xea,Aceyer munayah da Madeenah Ku na dabanne comment dinku ma na dabanne loves you more❤*

*my endless love goes to Friend indeed shalele maman mamee thanks for your care's*

*Bazan manta da ke ba jagoran kainuwa Aunty fauza 'Yar amana much of love*

_And the entire members na kainuwa writers association_





*Dubun godiya ga Hassan Atk*





Ganina ya sanyashi yin cak ya tsaya,ya budemun hannayenshi na shige ya rungume ni tsam,ya shiga sunsuna gashin kaina da yasha gyara sai kamshin turaren gashi ke yi,ya maida hannayenshi kuguna cikin seduce voice dinshi,ya radamun
I cannot get by a single day without looking into your pretty eyes and feeling the warm touch of your hands. What can I say, I am addicted to your love.my wify kullum yarintarki karuwa take you look sweet sixteen!

Na kwantar da kaina bisa kafadarshi sosai,sannan nayi murmushi na ce wa ce ni? Maman 'yan uku duk sun tsufar da ni,na kanne ido na ce dubeni fa cikin wani irin salo na ja na tsayi. idanuwanshi duk akan boobs dina,da suke tsaye standard saboda gyaran da suke samu.

Tsawon lokaci bayyi magana ba amma da ganinshi yana cikin shukin so.
na ja hannayenshi ya fara bina kamar kamar rakumi da alakarshi zuwa kan dinning.
Ina bude kulolin abincin kamshinsu ya buge hancinshi cikin sauri ya waro ido ya ce uhmmm! Its delicious.

Sai da nagama saving duka varieties din abincin da na girka,aiko yana sanyawa bakinshi yashiga sanyamun albarka.

ya ce nayi missing wannan abinci a lot my wify, kin shagwabani da kalolin abincinki tsawon tafiyar nan bantaba koshi kamar na yau ba, kinbiyani sosai ina godiya....

Na dan saki murmushi, na ce haba dear meye na godiya? I am always at your service.nima ina jin dadin girkina ,na sanyaka nishadi...
Sai da na jira yakammala cin abincinshi, na kuma kama hannunshi muka koma parlor lokacin kusan karfe biyar da mintina.


Muna cikin hira mai nishadantarwa sai ga kiran jack hand free na sanya wayar tare muka sha hira da Yusuf yawancin hiran yaushe zamu kawo masu ziyara ne munyi mashi alkawarin zuwa idan mun shirya har zuwa wannan lokaci bamu samu labari akan mahaifinmu ba sai dai bazamu gaji wajen nemanshi ba.

daya bayan daya muka gaisa da matarshi da yaranshi.sai da muka gama wayar na kashe na juyar da hankalina ga Yusuf na ce my hobby am serious fa muyi fixing tafiyar nan kullum muna mashi alkawari...

Sai da yadau tsawon lokaci baice komai ba sannan ya juyo sosai ya ce insha Allaah zan fara processing din visa.

Ai bansan lokacin da na yi tsalle na fada kanshi ba cikin murna na shiga yimashi sumba ta ko'ina saboda farin ciki.

Yau wata daya kenan da zuwan Yusuf daga tafiya tun da sanyin safiya na kammala komai domin munyi shirin zuwa gidan khalid.kwalliya sosai na yi na yafa laffaya fari sol mai duwatsu sai walkiya yake.shi kuwa Yusuf shigan manyan kaya ya yi sabuwar motarshi kirar Bugatti kusan wannan shine tafiyarmu ta farko da ita.
cikin kasaita Yusuf ke tukinshi gwanin burgewa a haka har muka iso gidan Khalid tarbar da sukayi mana ba karama ba ce,a yau ne na kara gane kaunar dake tsakanin Yusuf da Khalid don kuwa tarbar girmamawa da ya yi mashi tana da yawa.hour biyu cif Yusuf da Khalid suka yi suna ganawa ni kuwa da matar khalid muka baza namu hiran sai da muka gabatar da sallar la'asar Khalid ya kira su dadday da triple da suke saudiya muka gaisa da su sunyi matukar yin farin cikin ganinmu yaran sun girma sosai bazaka ce yanzu ne suke wata goma sha biyar ba...
bayan katse wayar ne sannan muka koma gida da zamu fita Yusuf kyautar sarkar diamond irin shigen nawa ya baiwa matar Khalid.

Tsawon tafiyar na sanya mana wakar Celine Dion
Cikin wakarta am alive,Yusuf ya kalleni ya yi murmushi ya ce ke dai kina son matar nan.
Na tayashi murmushi na ce ai ni a wajena ita ce uwar mawaka.

Ya sake murmushi ai nima kin koyamun sonta a tafiyar da na yi duk lokacin da kewarki ta dameni man shafawarki love nature body almond nake tsiyaya a hannuna in ji kamshinshi sai in ji kamar jikinki nake sunsuna in kuma na sanya wakar Celine Dion din sai in ji kamar muna tare tunda bakya rabo da jin wakokinta.

Dadi ya kamani cikin zuciyata tana ayuanamun irin dacen miji da Allaah ya yi mini baiwar samu duk a dalilin rashin son abin duniya yanzu gashi na dace da mijin da ke so na tamkar ranshi....

Da daddare muna hira da Yusuf na sako maganar aunty maryam tun kafin na nagama maganata ya bata fuska ya ce daina kiramun sunan wannan abar a gabana Bana so.

Na danyi murmushin yadda ya yi na ce afuwan habibty tuba nake bazan kuma ba dama ba komai nakeson sanar maka ba face ta saduda da abubuwan da ta aikata ta neme yafiyarmu kuma mun yafe mata a hanlin yanzu ta samu sauki sai dai fatar jikinta bazai gyaruba kamar yanda likitoci suka tabbatar.

Ya jinjina kai bai kuma ce komai ba.muka shiga shirin Lafiya Amsterdam shiri sosai muka yi na musamman kayayykakin da muka dauka saboda tsaraba ba magana.da dare daga ni har shi bamu runtsaba har gari yawaye...sai da nagama shiri na tsab sannan na nufi dakin Yusuf shima yana cikin shirinshi,takalmi black moccasin ne a kafarshi bakin wando Chinese product din DKYN ya sanya rigar t shirt fari sol Nike,sai long sleeve beach wear milk color,a gogon hannunshi kuwa Rolex sai daukar ido yake ya kammala taje gashin kanshi ya yi murmushi ya ce ya dai my wify na cinye?


Na kalleshi nayi murmushi kafin in yi magana na jero atishawa har kusan shida.

Ya kalleni cikin tausayawa ya ce yarhamakillah

Na amsa mashi ta hanyar rama mashi addu'ar da ya yimun.

Ya ce anya zaratun wannan murar taki ba nine sanadinta ba?

Na kalleshi na ce kamar yaya?

Ya yi murmushi ya ce to naga taki karewa duk yawan magungunan da Kika sha ko ajikinta.

Na yi kamar bangane meye yake nufi ba na ci gaba da hada sauran kayan da zamu bukaci amfani da shi a tafiyar.......

Sai da muka biya gidanmu mukayi masu sallama daddy sai tsokana ta yake da cewa na kishi yanzu bana kula da shi murmushi shagwaba na dinga yimashi Shiko sai murmushi yake, sai da naga mikamun chocolate din da ya saba bani.gaskiya nayi missing gida haka muka musu sallama muka wuce gidansu Yusuf cikin sauri suma muka yi masu sallama saboda lokacin tadhinmu ya gabato gidan humaira mukafi dadewa saboda sunfi kusa da airport tare kuwa suka rakamu ita da mijinta Dr zayd....
Sai da suka jira jirginmu ya tashiga sannan suka koma gida.....

Mun sauka a birnin Amsterdam,babban birnin Netherland.muna landing ko sai ga jack da matarshi har da mummy shi suka zo tarbarmu dukkanninmu munyi farin cikin ganin juna sosai tsawon tafiya gidanshi duka cikin hiran yaushe gamo mukayishi.

Muna zuwa gidan kuwa nan ne muka ga tsantsar kaunar da jack da iyalanshi suka nuna mana. hakika jack babban mutum ne a wannan kasa ganin irin daular gidan da yake zaune kamar aljannar duniya.kayan ciye ciye kam kasa wanne zamu zaba mukayi.abokan arziki kuwa sai zuwa suke ganinmu sana nuna farin cikinsu akan samun juna da mukayi koda bamu samu mahaifin namu ba st least mun samu dan Uwa shakiki.

Sati guda muka dauka a cikin wannan sati kuwa munyi yawon bude ido sosai.daga wannan kasa zamu wuce Italy,north korea,Japan,daga shi zamu wuce kasa mai tsarki domin gabatar da umara.

Cikin wannan tafiye tafiye da muke duka nikam ina ta laulayina,Yusuf din ne ke tallafamun da komai duk magungunan kuwa ya hanani sha ko wane irine duk da faman zazzabin da ke addabata....

A daddafe muka dawo san Francisco lokacin cikina har ya shiga wata biyar laulayin ya danyi sauki.bayan zuwanmu da kwana biyar ina zaune a parlor local news nake kallo sai ko ga bayanin nada sabbin gomnoni da sugaban kasa ya bayar na state of emergency cikin jerin sunayen sai ga na general yusuf Abduljalil tun kafin na gama warsakewa daga kidima wayar latifa ina dagawa kuwa tana your excellency,muna gama wayar da ita sai wayoyi ne ke ta shiga har na rasa wanne zan daga gashi lokacin yusuf din baya ma garin yaje califonia.

Washe gari kuwa
gidan cike yake da baki masu yi mana murnar samun mukami da Yusuf ya yi. Humaira da zayd,Khalid da matarshi,sai ga latifa ma da angonta,yaran vaishali ma su Sophia.sai su mummy da family su yusuf ciki har da yarana da suka girma Masha Allaah gwanin ban sha'awa kowa yana nuna farin cikinshi kasancewar Yusuf shine mutum na farko da ya rike mukamin gomna yana musulumi

Ranar da aka mika musu karagar mulki kuwa Yusuf din ne mutum na farko da ya godewa Allaah bisa wannan baiwa da yayi mushi , sai da ya neme izini a wajen delegate din sannan ya dinga nanata Allaahu Akbar sauran daidaikun musulumai suna amsawa.

Da aka neme sanin ayyukan da zai gabatar.ya yi bayani cikin ilmi da hikima gamshashshiya sannan ka watse.



Da daddare muna zaune da Yusuf yana messaging jikina saboda gajiya da nake fama da ita na ce your excellent sai gashi nawi yahau kanku ina yi maka fatan ka saukeshi lafiya..

Cikin tausayawa kanshi Yusuf ya ce ayya my wify mulki abin tsorone ban taba sha'awar shi ba amma gashi Allaah ya dauramun taimakeni ki tayani adduar sauke wannan nawi...

Nima cikin tausaya mashi na ce insha Allah zaka saukeshi lafiya kana da ilmin addinni dadai gwargwado kana tsare dokokin Allaah kuma ka karanci duk wani abu da ya danganci hukunci a cikin littafinka alkur'ani mai girma wannan kadai zai taimaka maka wajen gudanar da mulkinka...


Tsawon lokaci Yusuf ya dauka yana kallona daga bisani ya nisa! Ya ce na gade Allaah da ya arzurtani da mace ta gari mai sanin ya kamata da sanyani hanyar tsira hakika da goyon bayanki zan samu na mulki kasata cikin adalci.....


Misalin karfe biyu na dare na tashi da mawuyacin ciwon Mara banyi niyar tayar da Yusuf ba amma saboda tsananin ciwon na tayar da shi a lokacin kuwa har faya ta fashe,cikin kidima Yusuf ya sanya hand glove ya yimun VE lokacin har kan yaro ya kawo kai cikin sauri ya daukeni zuwa clinic a gidan tare da nurses Biyu suka taimaka mashi na haifi yara 'yan biyu mace da na miji.farin ciki awajen Yusuf baya misaltuwa.sai da ya gama tofesu da addu'o'I ya mikamun dayan yaron na sanyashi nono,bayan ya tsosa ya kuma bani dayar ma na sanyata tafara tsosa.


Da safe kuwa gida ya cika da baki kan wannan karuwa da muka samu.bamuyi wani taro sosai ba kawai 'yar kwarya kwaryar walima muka gabatar ranar suna yara suka ci sunan khalid da Humaira...


A wannan mulki da Yusuf ya gabatar ya kawo canji sosai ta yanda masu adwanshi ma sun fara jinjina mashi bisa adalcinshi ni Kai na ina taimakawa marasa galiho da ke zuwa gudun hijira daga kasashen ketare irin su Afghanistan,Syria, busnia da sauransu.cikin kankanin lokaci sunan Yusuf ya karade duniya wajen adalci baya bambamta kabila ko addini.nima na zama wata acikin family su Yusuf da yarana biyar kyawawa da su.....haka rayuwa ta kasance mana cikin jin dadi da walwala bani da buri sai taimakon talaka a duk inda yake ina gwargwadon karfina ciki kuwa har da kasa ta Nigeria muna taimakawa wadanda suke sansanin gudun hijiri yusuf&zaratun foundation ta wannan dalili donor's agency da dama suna taimakawa

Yayin da soyayyar mu kullum kara bunkada yake yi .Muhammad Ameen da Yusuf suka hada gwiwa suka bude babban makarantar koyon addinin musulunci tun daga matakin nursery zuwa university.....

A rayuwa nasamu dukkan burika na duk da har yau Alllaa bai nufemu da samun mahaifin namu ba amma nida dan uwana hankalinmu kwance yake kanmu kuma a hade muna zumuncinmu sosai baya wata uku sai ya kawomun ziyara.auntie maryam ma Allaah ya taimaketa ta samu wani malamin islmiyar da ta shiga da yaji labarinta ya aureta to ba laifi suna zaman lafiya......


Bayan Yusuf ya dawo daga dan gajeran tafiya na nufi dakinshi da wani irin rikitaccen kwalliyata yau inason rikita man dina ne da yadau tsawon lokaci bamu farantawa junanmu rai ba kasancewar aikin da ya sanya tukuru a gaba kayan baccin dake jikina wani yalolo da shi yabi jikina duka na iskeshi kenan ya fito daga wanka dan karamin towel ne ajikinshi yana ganina ya matso ya shureni bai zame ko ina ba sai kan makeken gadonshi da yasha gyara.......a kunne na ya radamun da cewa yarinya yau zaki biya basussukana da ya dade akanki......
Na kanne mashi ido cikin salon kissa zanyi magana yarufemun bakin da nashi cikin wani irin solonshi Yusuf dina karshene a komai....kullum da irin solonshi daban daban.....



Anan na kawo karshen wannan labarin *WACECE NI* kamar yadda na fada muku tun farko labarin true life story ne duk da fafutukar neman mahaifinta zaratun da jack basu samu nasarar samun mahaifinsu ba.....








*ina mika godiyata ga Allaah mahaliccina da ya bani ikon kammala wannan labarin cikin koshin lafiya*

*sannan ina mika dinbin godiyata ga Aunty fauza 'yar amana shugaba jagoran kainuwa writer's association da daukokin members dake cikinta Allaah ya kuma kara kanmu* *bazan manta da Hassan ATK ba wajen nuna na mijin kokarinshi da jajircewashi*

*sai members na wacece ni fans 1&2 nagode ga kulawar Ku sai mun hadu a cikin book din NAJMAH*













*vote@Wattpad teemacool2020*




An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to

Please Login or Register in order to submit comment