Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naga ya kamo hannuna ina,da sauri na dubeshi ya dake baidamu da kama hannunnawa da yayi ba,sai ga dan karamin box zobe yaciro na what gold mai matukar kyau sai da ya sanya a yatsana na tsakiya das yayimun kyau kuwa sosai,sai da ya tsumbaci hannun nawa ya ce I love you, ki adanamun kanki,take care ki koma gida lafiya.

Wani irin kallo nayi mishi mai rikuta duk Wanda akayi mashi sannan na ce thanks so much my man,Allaah yakara budi ya tsaremun kai.thanks once again.har wurin motarshi na rakoshi sannan na bi haryar hall naga har amfara shiga....






***************



Haka rayuwa tayi ta tafiya,yayinda nake zuwa makaranta na cikin kwanciyar hankali da walwala ,duk da kowane banagre na masoyan nawa suna ta damuna da neman iznin gabatar da su wa daddy hakuri nake ta basu har ta kai ga cewa shi daddy da kansa ya ce mun my princes yanzu lokaci yayi da ki zabi daya daga cikin wadannan yara saboda gaskiya nima na gaji da yadda suka rige rigen kamun kafa a wajena,yanzu ni kaina kasa ganin waye ya dace acikinsu nayi saboda dukkansu ba kanwar lasa bane mudai addu'armu Allaah ya zabar maki magi alkahairi acikinsu,na ce Aameen daddy,a dan bani lokaci saboda yanzu ina dab da fuskantar council exams dina,ya ce toh amma kiyi tunani ki cire daya daga cikinsu musan abinda ya dace.

Muna zaune ni da Latifa
Yau tsawon daren na kasa bacci sai kawai na tashe ta daga baccinda take gaskiya ni kaina abubuwa sun fara rikicemun yanzu,kasa yanda zanyi da rayuwata nayi maganganu sun fara isata,na ce, sounty na please ina tsaka mai wuya fa yau ina son ki bani shawara ne I mean goyon bayanki nake nema,kawai mafita zaki nemomin,kuma duk abin da na ce shi da shi zaki nemomun mafitan na kura mata idanuna ina jiran abin da zata ce.

Sai da ta dan harareni da gangan,sannan ta ce badai Neman shawara kike nema ba kawai ki ce commanding dina kike.

Ya ce koma meye zaki ce,let me talk my issues first. Kinga akansu Khalid ya Fara matsamun da na cire daya daga cikinsu ina ganin suna zuwa wurin daddy suna damunshi kinga ni kuma bazan so hakan ba,at long last kuma ni suke jawowa ruwa.saboda ni gaskiya zuciyata,yusuf take so take so ta karasa rayuwarta tare da shi....yanzu muka gama waya da yusuf,cewa kudaden da suke cikin account dina zan bayar ayi mushi final operation da za'ayi amma wannan zamu canja country.toh shi ne na ce ki zana witness dina saboda yaki yarda da karban kudin ba sai da sa hannun dan uwana ,kuma kinsan bazan sanar da su mummy ba sai bayan yusuf ya warke.sai da nagama maganata itako Latifa ta kuramun idanu daga ni mamakin maganganuna take.

Sai da ta dan nisa sannan kamar tayi kuka ta fara magana da cewa,
Lallai *zaratun* Sai yau nagane cewa you are insane,how could you let such a thought enter your mind?at the first place ma toh ni Wai waye ne Yusuf? Menene asalinshi da hakikanin inda ya dosa akan sonki?
Let me predict, ace ma inda da gaske sonki yake toh ko da bashi da lafiya dole ya nuna kanshi agaban kowa idan har soyayyar gaskiya yake maki kenan amma ki duba fa a koda yaushe yana cikin boye maki kanshi da zuriyarshi.duk jinyar da kikayi ya kasa turo ko da kaninshi ko kanwarshi,su dubaki idan shi bazai iya zuwa ba amma baiyi ko daya ba.
Ke kuma da yake giyar sonshi ke dibarki yasanya kika sanya kafa Kika shure.toh nikam gaskiya bazan sanya hannu cikin wannan gangancin da rashin sanin tudun madafa ba.
Kuma gaskiya idan baki janye wannan shawarar bashi kudaden nan ba zan sanar da su daddy hakikanin gaskiyar lamarin...

Aikuwa bansan lokacin da kuka ya kubcemun ba da jin kalamenta masu zafi ne akan yusuf dina,wallahi da tasan yanda nake ji da shi,baza tayi garajen furta wadannan maganganun ba.
Sai da nadan samu relief daga zafafan kalamunta sannan na dubeta ido cikin ido na ce,sosai nagade da kalamenki amma don Allaah ina rokonki da cewa keep it to yourself wannan maganar banason kifitar munshi,hakan da zakiyi shi zai kawo zaman lafiya a tsakaninmu kamar yadda kishiyar hakan zai kawo gagarumin matsala sakaninmu,ina fatan kin fahimce abin da nake nufi? Yusuf kuma zuciyata ce ta yardada shi,so babu abin da zai sa nadaina sonshi duk halin da yake ciki.so be careful with your word against yusuf duk wannan maganganun ina yinsu cikin bacin rai wanda ita kanta Latifa sai da ta tsorata da ni.daga haka bankuma cewa Kala ba na juya nayi kwanciyata.

Itama ta kwanta duk jikinta yayi sanyi da maganganuna,bata taba kawo a ka cewa har haka nakeson yusuf lallai wannan abu azimun ne....


Da safe misalin karfe goma na safe,kasancewar yau lahadi ne duk muna gida full house kenan kowa kuma harkar gabanshi yake,sai na dauko wayata na kira Humaira akan maganar liyafar da ake kan shirin shiryamun na musamman daga gidan gomnati Nobel price,akan taimako da na bayar wajen kama wannan gagarumin dan ta'adda da ya gagaresu shekara da shekaru.shiri sosai da zai samu halartar manya manyan jigagen gomnati.

Muma kuma muna kan shirin ne duk wani nawa sai da muka gayyata kama daga dangi,har da kawayena.Yau ya kama saura kwana uku kenan.
duk wani shiri da nake bukata kuma Khalid shine akan gaba.ga zayd da yadinga zirga zirgan bin government official don raba musu nvitation card. Bayan tayimun bayanin abubuwan da suke gudanarwa a gida na gamsu sosai da bayananta sannan na katse wayar,na juyo na fuskanci Latifa na bayyana mata abubuwan da ke Lafiya ta jinjina kai sannan ta ce Allaah yasa muyi wannan taro mu gamashi lafiya.

Na ce Aameen Allaah dai yakaimu lokacin.


Bayan mun idarda sallar isha'imuna shirin fara cin abinci, sai ga kiran Khalid
Bayan mun gaisa ina yimashi bangaji ,yashiga yimun bayanin abubuwan da ya gabatar sannan ya ce ki duba WhatsApp na turo maki da PDF na bayanan abubuwa da ya dace kiyi maganarsu a wajen taron,kuma kin tun yanzu ki bi ta kansu saboda tsayuwa agaban dinbin jama'a akwai wahala sai kin hada da kokari da juriyar kallon idon mutane....

Na gamsu da duk bayananka kuma zanbisu nagode da kulawarka gareni inajin dadin kasancewarka cikin rayuwata.

Stop it abin da ya ce kenan,bana son kina godemun a duk lokacin da nayi maki wani abu.
bayan mun gama cin abincinmu banida niyar yin kallo saboda haka bedroom na wace nayi shirin kwanciyata,sai ga kiran zayd shima yayi ta yimun bayanan abubuwan da ya gabatar da duk gunda yakai katin yafadamun shima nayi ta yi mashi gidiya,da yake shi dan love ne sai da yayi ta kasheni da kalmomin soyayyarshi sannan yabarni na kwanta.

Kamar kullum karfe biyu da rabi sai ga kiran Yusuf don sabawa har na saba da kiran da yakemun tskiyar dare,munsha hirarmu na love sannan na kuma tuna mashi cewa liyafar da za'agabatarmun saura kwana uku,ko da bazai samu damar zuwa ba ya turo wani nashi da zan gani kuma na nunawa su daddy,saboda sun fara kunnomun kai da maganar aure cikin damuwa ya ce toh my wify tunda haka kike so toh zan sanya kanwata ta halarci taron in sha Allaah..

Naji dan sanyi a raina ko ba komai dole a wannan rana su Mummy su san da maganar yusuf.




Yau Alkamis yayi dai dai da ranar zagayowar Haihuwa da kuma gagarumin taron da aka gabatar musamman saboda ni wajen ya tsaru matuka ta yadda tsayawa ina bayyana maku shi kauyencine .manya manyan jigagen gomnati da masoya da abokan arziki duk sun hallara a wannan taro. Ko ina ana haskawa da camera kala daban daban na tashoshin TV na kasan da ma ba na kasan ba.sai da aka dinga gabatar da zuwan manya baki da gabatar da su ga taron,bayan wadanda ya dace suyi magana sun ciki kuwa har da ni da na gabatar da dan ta kaitaccen bayani,tun da na mike cikin taku dai dai na amshi mic din,sai da nayi nazarin cikin dakin taron da mutanen daya bayan daya duk zaratan samarin nawa sunsha kamshi da shigan da sukayi kamar Wanda zasu je gasar African idol.daga zayd har Khalid din sun zauna a waje ma banbanta.amma dukkaninsu sun kuramun idanuwashi cikin sha'awa,bangama kare musu kallo ba sai kawai idona ya hangomun Yusuf zaune akan wheelchair,kamar gizo idona kemun na kuma murza su sosai na kuma kallon wajen babu tantama shidin ne zuciyata ta ba dam ganin da yayina kura mashi idanu babu kakkautawa,ya sanya yimun nuni da hannu cewa bai samu wanda zai zo taron ba,sai kawai ya zo da kanshi saboda ya farantamun jinjina kaina nayi,na kuma bayar da hankali na ga dimbin jama'ar dake gabana suna jiran jin bayanai na.
Cikin bayani mai kayatarwa da gamsar da mai saurarona nake bayani a tsanake cikin nutsuwa, Sannan na koma ma zaunina na zauna.sai da kowa ya gama bayaninshi,sannan aka bude kofar bayar da kyaututtuka....
Sai ga sanarwa cewa prince Khalid zai gabatar da kyautar soyayya ga masoyiyarshi da suka shafe kusan shekaru biyu suna soyayya wato uwar buki *Zaratun Hameed* da dam dam zuciyata tabada lallai ko yau Khalid ya gama da ni dama dan abin da yakeson shiryamun ne yadinga zumudin zuwan ranan nan tab,yau za'ayita kenan ta kurum kus.bangama dawowa daga tunani na ba sai ganin Khalid nayi ya fito da wani irin gift duk an nannadeshi da wani abu mai walkiya kamar diamond, sai aka kuma kiran mai girma gomna shi ne Wanda zai gabatar da kyautar Khalid a hannunshi.ganin bani da niyar fitowa aka kuma Kira na da cewa masoyiyar prince dinmu mai girma ki fito maraba da isowarki ya mai girma.babu yanda na iya sai kawai na mike na fito kan step kafin na karaso kuwa sai ga zayd shima shima yafito dauke da gift dinshi,kaka tsara kaka sai ga uban gaiya yusuf ya ja wheelchair dinshi yadinga kokarin hawa kan step din da ya kasa wani dake kusa da shi ya taimaka mashi shima yahau kan step din.shima kuma da dan karamin kwalinshi na gift suka ja suka tsaya kallon kallo aka tsaya yi da juna kowa kuma yanason sanin wannan cakwakiyar MC da tun faruwar lamarin ya kare musu kallo don shi baisan abin da su zayd ke nufi,ya kuma cewa to princess zaratun ke prince dinmu ke jira don mika maki zoben alkawarin aurenshi taka da hankali ki amshi wannan gagarumin kyauta.daya bayan daya na tsaya kallonsu dukkan ukun kuma yana mikamun abin da ke hannunshi nuna alamun na karbi nashi.
Sai da nagama yin nazari akansu hankalina gaba daya ya koma kan yusuf da ya zama abin tausayi..da na juya shima Khalid din yau yabani tausayi,ga Dr zayd uban love shikam tun ba'aje ko ina ba ya fara raurau da idanuwanshi.dukkan dakin taron kuma sai yanzu suka farga da cewa wadannan masoya na ne kuma ko wannensu kuma yana Neman na zabeshi ne a matsayin gonina...su mummy da suka ganin abin kamar a film sai pointing da hannu suke na zabi Khalid.

na yi kamar bangane abin da suke nufi ba na rufe idanuna nayi nazari sosai da zuciyata abinda ta zabarmun shi zan dauka,sai ko ta zabamun Khalid ne ya cancanci na zaba tunda bani da tabbas akan warkewar Yusuf,da sauri na nufi wajensu Khalid dake tsaye da gomnna,kamar zan sanya hannu na karbi kyautar sai na kuma juyowa na kalli gunda yusuf da ke zaune rike da dan Karamin gift dinshi take wani irin tausayinshi da sonshi ya ziyarci zuciyata habawa da sauri na koma wajen yusuf na karbi kyautar da ya kawomun,jikina sai bari yake kaina kuma sai juyowa take saboda fargabar abin da na aikata sai kawaici na tsinci Kai na da fadin wallhai kai ne kai ne yusuf ta amince ta zauna da kai ina sonka ina kaunarka don Allaah kuyimun uziri bisa abin da na yanke a yanzu sai ga hawaye daga idanuwan yusuf shar shar ,take kuma wani irin sautin wakar Celine Dion,cikin wakarta na

For all stand you stood for me
For all joy you brought to my life
you are the one who help my life,never let me go,your the show me truth,truth enough

.sai kuma tafi raf raf raf duk dakin ya dauka,sai wadansu abubuwa masu kyalli da suke ta zuba akanmu.sai da na dawo da kallona sai naga har da su Khalid ake wannan tafi suna murna aiko bangama mamakin su ba sai da naga Yusuf ya mike tsaya yana taku dai dai yana zuwa gunda nake furkarshi cike da annuri da murmushi,ai bansan lokacin da ya tafi kasa lu ba sai gani sumammiya...





_kuyi hakuri da typing errors da zakuyi encountering,saboda banyi editing ba_












*comment*
*share*
*vote*
_Wattpad teemacool2020_


⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*

Wattpadteemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 4⃣8⃣4⃣9⃣


*Dedicated this pages to my real fans I thanks u all*


_"It's really an opportunity and privilege been in 500 level, after cruising helter skelter to every nook and cranny of this University and other course related Ministries, finally we are here for our Final Year Project, we all need to thank God for his blessings, by then we have to work harder, let's keep pillows with the zeal of sleeping aside, and start the Final Battle, 500 level deserves only As and hardly Bs for better Class of Degree, and as a Project where everyone belongs to a group of 10 or 20 or 30 fellow course mates, Team work is of great significance and most importantly prayers at all times."_



Ina farfadowa daga suman naganni kwance akan lallausan darduma da aka shimfida akan step din,da hankali na bude idanuwana,duk sunyi cirko cirko a kaina,yusuf nagani da first Aid box,ya gama dubani sannan ya ce bawani abu bane kawai shocked ne tasamu na sadden surprise,amma yanzu komai ya zama normal.

Tunda yake maganganunshi jira nake acemun ki tashi daga mafarkin da kike saboda kwata kwata ban gaskata wannan al'amarin ba gani nake mafarki nake,sai na juya ga Humaira da take kusa da ni dagani tasha kuka.
Na ce sister don Allaah ina mafarkine ko kuma na zauce please fadamun gaskiya saboda ke ba za kiyimun wasa ba?

Humaira cikin girgiza kai ta ce sister duk da ni ban fahimci komai ba,amma kina cikin haiyacinki ba mafarki kike ba.sai a sannan ne na juyo da kaina na Fara duba mutanen da suke kaina.Khalid,Dr zayd,mummy,dad,da gefe daya kuma Auntie Maryam ce, sai daidaikun mutane da bangane ko su waye ba,na kuma juyowa da mummy na ce,da gaskene mummy ba mafarki nake ba?

Cikin takaici ta ce haba my angel ki nutsu ki dawo haiyacinki,taso ki dawo kusa dani,ta nunamun gefenta na taso da sauri na zauna.sai da aka nutsu kowa ya koma mazauninsa,sannan MC ,yafara bayani da cewa hakika yau mun riski gagarumin al'amari kamar almara,lallai wannn al'amari zan iya cewaToday, tomorrow and forever there will be one heart that would always beat for you.

a wannan rana,a wannan lokaci zamu so musan wannan cakwakiya da yasanya wadannan dimbin jama'a da suka taru musamman,saboda princess zaratun Hameed tauraruwa acikin tauraru.wannan taro anshirya shine musamman saboda wannan ranar,hakika gimbiyarmu kin cancanci numbar yabo,saboda dimbin 'yan mata sun fadi a wannan jarrabawar, tun kafin aje ko' ina amma ke sai da kika tsallake wannan keshi,muna tayaki murna,kuma muna maki fatan alkhairi,ke ta dabance kowa kuma ya tabbatar da hakan,mungode.Without much wasting of time zanso na gabatar maku da kanin yusuf,prince Khalid don ya warware mana wannan cakwakiya ,daganin idanunku nasan cewa kun kagu da son jin wannan al'amarin.

Duk wannan bayanai da MC ke yi ni kuwa tunanin abubuwan da suka faru da yanda naga yusuf tsaye da kafafuwanshi what a surprised,dama Ashe haka yusuf dina yake,duk da dimbin mazan dake wajen,duk tauraronshi sai da ya haska wajen,jarumine, a mike yake dogone.gashi da irin lallausar farar fata da ko mace take dashi zatayiwa maza yanga.duk hankalina ma baya cikin hall din sai da naji muryar Khalid cikin lafiyayyen turancinshi.sai da yayiwa taron gaisuwa sannan yafara bada tarihin Yusuf kamar haka

An haifi yusuf Abduljalil a Canada shine da na uku a cikin jerin yara goma da mahaifinmu sarki Abdujalil ya haifa,mahaifinmu Sarki ne na anarbour Muslim community,kasancewarshi shine founder na wannan community da ya tara dimbin musulumai dake fadin Canada.asalinmu larabawane daga Syria.ya yi karatunshi daga primary har zuwa jami'a a nan Canada,ya karanci aikin likitanci fannin mata wato gynecologist.
da yafara bautar kasarshi na shekara daya akan aikin soja sai yaci gaba da karatun koyon aikin soja shidin yanzu sojane mai mukamin Major,ya samu mukamai masu dimbin yawa daga gida har waje ,yanzu haka shine security intelligent to the president of united states of America.Allaah yayi mashi baiwa sosai.kasancewarshi ba asalin dan kasar ba.
Sai da yadan tsaya yaja numbashi sannan ya ci gaba.

amma kuma yasamu mukamai masu dimbin yawa da yayiwa 'yan asalin kasar fintinkau hakan yasanya ya dinga haduwa da makiya masu yawa.
yashiga neman wata yarinya Sophia 'yar prime minister ta ce,sai daga baya yagane asalin munafurci aka hada don kasheshi ta hanyar hadin bakinta.

saboda sunyi iyakan kokarin ganin sun kasheshi amma Allaah baibasu dama,toh tun daga wancan lokaci ya watsar da maganar neman aurenta.sai ya kuma neman wata acikin unguwarmu,itama daga baya yagane, yaudararshi take saboda haka ya hakura da ita.haka yayita Neman aure amma daga baya sai yaga akwai munafurci da ake hada mashi. ahaka dai ya tattara maganar Neman aurenma ya hakura.


Tun daga wannan lokaci na shiga nema mashi mafita sai wani tunani ya fadomun akan cewa ya nemi friend mata a social media yayi testing dinsu idan ya dace zai samu mace ta gari idan kuma ba'a daceba za'a iya samun kishiyar haka.

Sai da ya ce mun yasamu wata da yake so amma yayi basaja bai nuna mata ko shi waye ba,saboda ya tsorata da halin mata.duk da ance ,cewa never lose hope.hope is rope that swings you through life.
To a hakane na taimaka mashi,
Bana manta wata rana
da yayana Yusuf ya kirani a waya,yabasu kabarin yadda muka hadu da duk hidima da yayi akaina da motar da yabani duk daga yusuf kaf ya kwasha labari yafada musu,sannan yadan ja numfashi yayi murmushi ya ce kutayane jinjinawa wannan jarumin aboki kuma aminina wato zayd ,ya ce lokacin da wancan killer yayi attempting din kashe zaratun da akayi na buya a gidansu coincidence ne,lokacin da naji labari naje asibiti ne muka hadu da shi yake sanarmun cewa a gidansu na buya .

Ni kuma na bashi labarin komai sannan na ce ya tayani campaign har lokacin da zamu kai ga gaci.ahaka har muka kawo matakin da Yusuf yakasa jurewa yayi insisting zai bayyanawa zaratun hakikanin wayeshi. saboda taci,
wannan jarrabawar dari bisa dari.saboda tun lokacin faruwar kisancan yaso ya bayyana kanshi.

amma na ce yabani dan lokaci kadan nayi hakane saboda yasamu fully support akan zaratun din.
lamarin ni kaina yana bani mamaki ace,a wannan zamani kasamu Wanda zai soka saboda Allaah gaskiya sai an bincika.Kada Ku manta duk irin soyayya da kulawa da nake yiwa zaratun bantaba jin ta furtamun kalmar ina sonka ba,haka yake agun zayd saboda dukkanmu muna amfani da CCTV camera duk lokacin da zamuje wurinta hira,Wannan halin natane yake ingiza Yusuf son baiyana kanshi tun ba'ayi nisa a gwajinba,sai da yadanyi murmushi,kafin yaci gaba dakin kuma duk sun maida hankalinsu sunajin wannan labari mai ban mamaki da ban sha'awa.
Ya kuma yin murmushi ya ce Dan Allaah Ku tafawa wannan dadaddiyar soyayya da tashirinshi ya taramu anan,na tabbatar muku cewa yusuf irin mutane ne da ake cewa born with a silver spoon in their mouth.ya so aikin likitanci, shidin likitane,sannan kuma hamshakin soja ne mai mukamin major.

yanason zaratun kamar kamar son ranshi gashi yau zaratun ta tabbatar maku cewa soyayya su acikin jini take.sai ko aka dau tafi raf,raf,raf.tunda Khalid ke bayani tsananin mamaki ne fal acikin zuciyata,sai kallon yusuf din nake da ya dake zaune kusa da gomna,shima kuma kallon nawa yake cikin tsananin so ko kunyar mutanen wajen ba yayi.
Sai da Khalid yaje kusa da zayd suka jeru dukkansu uku naga suna maganganunsu cikin walwala.yayinda ni kuma hankalina yayi mugun kwanciya ganin yanzu bani da sauran fargaban cewa na yaudaresu.ina cikin wannan tunanin,MC ya kuma Neman yusuf da yadan bayar da takaitaccen bayani, sannan a rufe taro.

Cikin kasaita da taku daidai na irin jinin sarauta ya mike sai gashi dakin taron ya dauki kananan maganganu kasa kasa,sai yanzu kuma nagama karewa yusuf din kallo gaskiya ina cikin matan da sukayi sa'ar samun mijin nunawa sa'a.
Sai da yayi hamdala ya godewa ubangiji,sannan yafara bayani cikin dense voice dinshi,duk tsayuwar da yayi ni yake facing,ya zubamun lumsassun idanuwanshi,duk maganganun da yayi abin da yashafeni ne da abubuwa alkhairi da na nuna mashi daga karshe ya ce to the extend abin da yarinya ta munyi Wanda bazan iya mantawa da shiba,ya ce we all know what is money is all about but my wify ta sadaukarmun duk abin da ta mallaka saboda kawai ta ganni ina takawa da kafafuna.gaskiya wannan wane irin so ne? meye nayi maki har hakada yasanya kika soni haka?sai ga hawaye shar daga idanuwanshi.
Abubuwa da nake tambayar zuciyata kenan
Sai daga baya nagane Allaah baya zaluntar bawanshi matukar bawan yana bin dokokinsa.

Nima kuma sai hawayen ke zubomun shar,ji nake kamar naje na rungumi yusuf saboda tsananin sonshi ne ya rufeni a take. Ko ban fada ba
shima ya nuna kamar yazo ya dauke ni ya hadiye yake ji.duk wani masoyanmu awajen sai da ya jinjina mana,sai sanya albarka suke mana.

Sai yadan ja numfashi sannan ya ce,there are no enough word to describe what I went through in my mind,when I set my eyes on you.how very precious this is?
Thank you Allaah,for making this possible.....
I love you and I will always love you to the rest of my life.

Sannan ya godewa mahalarta taro da su koma gidajansu lafiya.kyautukka sosai aka raba awurin wanda naga su Humaira da sauran kawaye nane suke rabarwa.sai yanzu na tuno da Auntie Maryam juyawan da zanyi sai banganta a wurin da take zaune ba nayi mamaki da alama nayi nuni da Humaira take wucewa kusa da ni tazo.
A hankali ta dawo kusa da ni ta sunkuya kusa daidai kunnena
.na tambayeta ina Auntie Maryam?

May be ta tafi gidane naga tana kuka da na
tambayeta, take sanarmun ciwon ciki ke damunta.
Na tabe baki na ce, ayyah Allaah yabata lafiya.cikin zuciyata kuma fadi nake rigiji rigab,yau ga Auntie maryam da yusuf ido cikin ido wannan yaya kenan?

Sai da aka watse sannan nagane ashe dai yusuf da yawancin danginshi ne suka zo wajen taron.farin ciki awajensu mummy ba'a magana 'yan jarida kuwa sun samu hanya sai jefa musu tambayoyi suke.
A hankali yusuf yazo kusa da ni ya radamun akunnena yarinya wallahi kintaka babbar sa'a ba aure aka daura mana ba.da yau sai na sauke dimbin kasalan da Kika dauramun yau.

Na zungura bakina cikin shagwava na ce ni ka kyaleni babu abin da nayi maka,bacin kaine ma ka kacuceni ka tsoratani da salonka why all this game? Wallahi am serious kun sanya kwakwalwata ta daina aiki for some minutes. Muna cikin haka sai ga Khalid da zayd sunzo wurin dariya sosai suke,niko na sadda kaina don nafara jin kunyarsu ,sai dai da na tuna duk kalmomin soyayya da suke furtamun na bogine?
Oh oh oo garin dadi na nesa!
Masu photo kuwa sunyi ta haskamu da camera.sai ga daddy acikinsu suna ta murna shima yayi ta yiwa Yusuf godiya da tayashi murnar cikan burinshi.

Da 'yan wan yusuf da nawa kuwa anhadu Ana ta raha ahaka muka fito wajen parking lot........
Juyawar da zanyi sai ganin Auntie Maryam nayi cikin korkosa da girgiza jikinta ta nufomu dama gashi tana da duka biyu daga sama har babu kunya balle tsoron Allaah tayi fari da ido ko gunda nake bata kallaba balle na sanya ran zatamun murna,cikin salon jan hankali ta fara gaishe da yusuf............





_kudinga hakuri da typing errors coz bana iyayin editing cikin kwanakin nan_








*comment*
*share*
*vote*
_teemacool2020_
Wattpad

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*

Wattpad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United

Please Login or Register in order to submit comment