Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register





✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*

Wattpad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 6⃣0⃣&6⃣1⃣




*Today's Beautiful Hadith is About Knowledge*

_Abu Hurairah (RA) said: "I heard the Messenger of Allah (peace be upon him) saying: ‘This world is cursed and what is in it is cursed, except the remembrance of Allah (dhikr) and what is conducive to that, or one who has knowledge or who acquires knowledge.'_"

(Sunan Ibn Majah, Vol. 5, Book 37, Hadith 4112)


*Dedicated to Hassan ATK*





*kada a manta yau juma'a a karanta suratul kahf*







Tsawon tafiya daga airport zuwa gida cikin farin ciki muka yishi,sai gamu a gida daddy ne ya Fara shiga gida hannunshi rike da na jack sai Lil Yusuf da Yusuf suka bi bayansu.daga nan muma muka bisu daya bayan daya.bayan mun nutsu mun zazzauna,muka kuma shiga sabon farin ciki daddy ne ya ce my son feel free and be at home we are happy to meet you.

Jack ma cikin nuna farin cikinshi ya ce thank you daddy my pleasure to meet you,I don't know how to explain how i feel.
Hundred percent na gamsu da wannan 'yar uwata ce na jini just DNA test da zamuyi to make ourself clear ne amma kook at my sister dad we look alike,kamar wasu twins gaskiya naji dadi kuma nasan mummy na ma zata ji dadi..sai ta ciro wayarshi yashiga kiranta, sai da ta daga ya sanya a hand free ya labarta mata komai da yanda ya same mu duk muka gaggaisa ta nuna farin cikinta sosai, duk muncika gabanshi da kayan marmari da abinci kala kala.kadan ya danci,sannan muka shiga labarta yanda muka fuskanci rayuwa lokacin kuruciya...

Na gabatar mashi Yusuf da cewa shi ne fiance dina nan da sati shida aurenmu.

Ya kuma mika hannunshi sukayi musabaha da Yusuf a Karo na biyu,shi ma ya ce,ya yi aure da yarinyarshi daya.Tunda muka dawo gida ina kusa jack tsantsan sonshi ne ke cikin zuciyata ina ganinshi kamar mahaifina saboda kamannin da mukayi da shi....

Mummy ce ta juyo ta dubeni cikin murmushi ta ce my angel da zaki bar my son ya huta haka duk kin takura mashi kamar Wanda aka ce wani zai dauke maki shi?

Kowa yashiga murmushin maganar mummy,niko na zungura baki na ce,yau ina cikin shukin ganin brother toh ko dole ku hakura da yanayin da zaku riskeni today I am totally different....
Shi ma jack ya ce nima haka abar so na,such a emotional experience I cried and so happy beyond words,for this beautiful sister god has definitely blessed me I love you so much....

Nima na kamo hannayenshi duka biyu na ce,thank you brother you are precious to my eyes,you such a wonderful brother to me,I love you too!there are no words to describe what i when through on my mind,when I saw you for the first time.I just feel like you are father to me, nasha gwagwarmaya sosai akan wannan figure 489....


Shi ma ya girgiza kai ya ce my Lil,I knew what exactly you when through,saboda amma nasan cewa kin fini gata nisa ba kusa ba tunda ke kin taso da Wanda yakasance tamkar mahaifi,idan na tuna tun ina nursery school na Fara fuskantar kalubale da kirana bastard kasancewar sunana jack 489 kawai babu wani suna sai wannan figures.ina mallakan hankalin kaina na dukufa da neman mahaifina...
Wallahi babu abu mafi girma kamar mahaifi,saboda haka 'yan mata mara sa kamun kai da zuwa daukan ciki kalubale gare Ku, idan da zaku san yanda yaranku da kuka haifa ba tare da mahaifi ba za su ji cewa a titi aka haifesu,domin ko a turai babu abu mafi kaskanci irin a haifeka babu uba. bama addini ba al'ada kenan.....

Daddy ne ya gyara murya ya ce,gaskiya kun bani tausayi sai yanzu kuma nagane yanda kuke ji ina rokon Allaah da ya baiyana maku mahaifinku,duba da wannan shaidu da ka tafo da shi ya nuna mahaifiyar ta yi amfani da tube 489 shekaru takwas kafin mahaifiyar zaratun.kenan tsakaninku akwai ta zarar shekaru takwas da ita......Ku gode Allaah da ya baku damar hafuwa da hakikanin kanwarka ta jini wannan abin alfaharine......

Yusuf yayi mana sallama ya tafi,sannan muma muka bashi dama ya dan huta,muka shiga part dinmu......


Kwanan jack uku ya ce zai koma Amsterdam,zasu shirya kafin zuwan bikina muma muna kan yin shirin zuwa Nigeria,saboda shiri sosai zamu gabatar don bikin.tafiyar daga ni sai Humaira da auntie Maryam,su mummy zasu gabatar da sauran shirin kafin mudawo.tare muka shirya da jack zuwa airport.sai zumudi nake na zuwa Nigeria,saboda mun kwana biyu bamu je ba.Yusuf kam Sam bayason wannan tafiyar,Wai yafison bayan aure toh wadannansu abubuwa idan banzo Nigeria bazai yuwu ba na gyaran amarya...to ita Humaira ma da dangin Dr zayd sun kawo sadaki don daddy ya ce zai hadamu da ita a yi auren.uban love sai nan nan yake da Humaira tunda muka zo airport ban kuma sanyata a ido ba sun koma can baya suna hirarsu kafin zuwan jirgi.jack kam muna isowa sai ga jirginsu,yayi mana sallama suka daga....
Bayan kamar minti talatin sai jirginmu,cikin murna na mike ,sai ga zayd da Humaira ma suna zuwa Yusuf yayi kicin kicin ya zubamun lumsassun idanuwanshi masu daukar rai,muna kusa sosai har ina jiyo hucin numfashinshin ya rankafo daidai kunnena cikin muryarshi kamar rada,ya ce you leave me wanting nothing more than wanting more of you,I am going to missed you,I love you.safe trip my wify.

Nima na markwada muryata cikin seduce voice na ce nima haka my hubby,promise to love you more and more and more, going to miss you badly..... Sai naji kamar karmu rabu,sai gashi ana bamu umarnin shiga muna daga musu hannu har muka gama shiga cikin jirgin.....


Tafiyar hour goma sha biyu muka yi a sararin samaniya mun sauka a france,muka kwana da safe muka kuma kama hanyar Nigeria....karfe hudu na yamma muka yi landing a Maiduguri international airport.uncle mustapha da uncle Anas,sai Nur kanin barrister mukhtar ne suka zo tarbarmu.

Cikin farin ciki muka kama hanyar unguwar kakaninmu wato shehuri North.muna zuwa gidan cike yake da danginmu,kakarmu Hajja bintu tayi matukar farin ciki da zuwanmu saboda farin cikin ganinmu batasan inda zata sanyamu ba duk da jikin manyanta amma tana da karfinta,saboda yanayin da take akwai hutu sosai...tun kafin mu gama wassakewa,auntie maryam ta mike ta ce za ta wuce gidansu,muna rokonta ta bari mu kwana sai mutafi tare amma fafur taki amincewa.....ita duk ta damu tabarmu ne saboda gobe da sanyin safiya zata je wurin bokanta da takalmana....tun da dare Ammi ta Fara yimun halawa a jiki, ta ce kuma tsawon sati uku zamu dauka wajen gyaran da zasuyimun sauran Kayan ma mussamman daga ndjemaina tazo da shi.

Da muku mukun sanyin safiya auntie maryam suka dinga kulla yanda zasuyi su
rabani da yusuf,daga ita har mahaifiyarta bakinsu daya saboda ta shirga mata cewa ni na munafurceta na rabata da Yusuf.ta ce mama ki barni da su sai na kwato 'yancina,bakiga irin kayan arziki da suka kawo ba ma tukun,maman ta ce kaiya nagani dai da kakar tasu duk ta nuna mana video silalan gold....mama ki bari kawai ai irin su Yusuf sune mazan da mata kan macewa akansu ga kudi ga mulki,yanzu dai bara naje wajen mallam..
Maman ta ce toh da waye zaku je ko zamu tafi tare ne?

Auntie maryam ta girgiza kai ta ce Aa mama zamu tafi da Halima kawata,kedai ki zauna duk yanda mukayi zan sanar maki.....

Duk da hanyar gwoza bashi da kyau sosai, amma saboda son cika kudirinta suka kama hanya...hawa kan dutsen kanshi aikine,da kyar suka hau kai...ta cire ta kalman ta mika mashi.

Boka cikin dariyar mugunta da wadansu zaro zaron jajayen hakoranshi ya zaro manyan idanu ya ce toh ki kuma fadan abin da zamuyi mata shakiskis yaji saboda mu bama yin abu da karan kanmu!

Auntie Maryam duk wani imani da take da shi ta sanyashi a gefe guda sai tsantsar mugunta da rashin jin tsoron Allaah duk ta manta abin da Manzon tsira Muhammad sallallahu alaihi wassalam ya ce duk wanda yaje wajen boka kuma ya gaskata abin da ya ce toh hakika ya karyata abin da aka saukarmun,wato qur'ani....a wani hadisi kuma ya ce,duk Wanda yaje wajen boka kuma ya gaskata abin da ya ce baza'a karbi sallolinshi na kwana arbain'.

Ta karkace baki ta ce mallam ina son rabata da Yusuf na har abadah,sannan tabar garinma gaba daya,sai kuma ka mantar da kowa tunaninta ciki kuwa har da mahaifiyarta.

Boka ya ce toh angama,sai da ya gama duk abin da zaiyi da takalmin sannan ya mika mata,ya ce gashi ki mayar mata da shi matukar ta sanyashi cikin kafarta shikenan aikin gama ya gama....

Cikin farin ciki auntie maryam ta karbi takalman,saboda ta mayar gidan kaka kafin mu farka daga bacci saboda ta kalman da nazo da shine ta dauka wancen da kawarta ta karba a san Francisco bata bi takansu ba tunda tasamu wannan...hakan ko a kayi da suka tashi a wajen boka direct gidan kaka ta wuce,lokacin kuwa ko bacci bamu tashi ba taci sa'a ba kowa ta ajiyesu kamar yadda ta dauke su, da sallama ta shigo, muntashi kenan daga bacci da mamaki a fuskata na shiga tambayar yaushe ta zo?

Fuskarta dauke da murmushi ta ce yanzu zuwa na don tafiya da Ku wajen mama tun zuwa take ta damun mai yasa bantaho da Ku ba...

Nima ina murmushi na ce ayya big mama nima ina missing dinta bara mu shirya,Humaira do quick zamu fita yanzu,daga cikin dakin ta ce toh.na ratsa parlor na fito kofar daki ina kuma cewa kaka da tafito daga bedroom dinta granny zamu fita fa me kikeson zamu taho maki da shi?

Cikin sakin fuska ta ce,'Yar yawo ina kuma zaku je keda ammi take jira zata fara aikinta.

Cikin shagoba na ce nidai kubarni na huta daga zuwa sai kace dama ni kuke jira sai kushiga sanyani wahala,na jiyanma ya isa sai after two days zan yarda ta kuma yimun.ta dan harareni ta ce ai sai kiyi to ina amfanin zuwan naki idan ba zamu gyaraki ba da kinyi zamanki gasar gasar akaiki gidan mijin.

Ina murmushi na fito wurin da takalmanmu suke, zan sanya kenan sai kiran kaka yatsayar da ni na amsa da na'am....











_please show love for me, and vote teemacool2020@ Wattpad_


⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*

Wattpad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 6⃣2⃣&6⃣3⃣




*Today's Beautiful Hadith is about Sincerity*

It was narrated that ‘Abdullah bin ‘Amr (RA) said: “It was said to the Messenger of Allah (peace be upon him): ‘Which of the people is best?’ He said: ‘Everyone who is pure of heart and sincere in speech.’ They said: ‘Sincere in speech, we know what this is, but what is pure of heart?’ He said: ‘It is (the heart) that is pious and pure, with no sin, injustice, rancor or envy in it.'"

(Sunan Ibn Majah, Vol. 5, Book 37, Hadith 4216)

*_May Allah help us be the best of people and make us pure of heart - Ameen!_*





_Masoyan zaratun jinjina gareku,tanajin dadin addu'o'inku, kuci gaba da taya ta addu'a,auntie maryam dai lamarinta azimunne....._



Na'am ganny gani nan tahowa,daga ciki kaka ta ce ida abin da kike carbina nakeson zaki daukomun a daki.

Na ce toh,sannan nayi bismillah na sanya takalmana,saboda tun ina yarinya abin da daddy ya koyar da mu kenan duk abinda zamuyi mu fara da bismillah,sanya riga da cireshi,ko sanya takalmi da duk abin da zamu fara gabatarwa. *fa inna kulla shai'in la yabda'u bismillahi fahuwa akdha*.wannan ya sanya bana manta yi koda ina cikin Sauri ne.
Ta cikin corridor nabi naje dakin kaka na dauko mata carbin daidai auntie maryam da humaira kuma sunfito kenan,sai da na dubesu sannan na ce shall we?

Hankalin auntie maryam duk akan tafin kafana tana nazarin takalman da na sanya,sai washa baki take daganin takalman da ta kawo ne na sanya

Ta ce yes dear muna jiranki a parking lot,tun dazu driver ke jiranmu.

Na ce bara na kaiwa kaka wannan,Humaira ce ta ce OK ki same mu a can.suka fita ni kuma na kaiwa kaka carbinta sannan na fito har sunshiga motar,nima nashigo driver ya ja motar mukabar gidan....

Lafiya lafiya muka iso gidansu auntie maryam,kamar da gaskiya mahaifiyarta ta tarbemu cikin sakin fuska da murnarta har rasa gunda zata ajiyemu tayi saboda farin ciki,sai nan nan take da mu.

Tun zuwanmu naga mood din auntie maryam ya canja,har humaira tashiga tambayar lafiya auntie mu kinyi shiru fa?

Firgigit ta dawo daga dogon tunaninta da danyi murmushin gefen baki ta ce ki bari kawai my Lil ina tuna abubuwan duniya ne kawai.

Har muna hada baki da Humaira muka ce ki daina dogon tunani babu kyau komai na duniya mai wucewa ne.ta dan sako murmushi ta ce hakane my sister kuci gaba da kallonku ina zuwa nan bada dadewa ba.

Muka toh auntie mu hope ba nisa zakiyi ba?

Ta ce no nan shop zansoyo mana shawarma,ta mike ta fita mu kuwa muka cigaba da kallonmu dake gidan nasu ba kowa duk suna boarding school.

Auntie maryam tana fita waje sai da ta faki layin unguwar tasu ba kowa sannan ta kira number bokanta,ringing na farko ya daga.cikin Sauri ta shiga cewa mallam na kirawo ne ta sanya takalman fa amma maganar da nake maka yanzu haka muna tare da ita.

Daga wancen bangare boka ya ce kina nufin ta sanya takalman kenan amma kuma babu abin da ya same ta?

Auntie maryam ta ce eh mallam lafiya kalau ka ka zo gidanmu kuma ko alama bata nuna ba na wani abu zai same ta.

Boka ya anya ko takalmin da na baki shi ta sanya?

Auntie maryam ta ce kwarai kuwa mallam daga fita ta a wajenka direct gidan da suke na wuce kuma takalmin shi kenan babu irinshi awajensu balle na ce maka ko ansamu akasi ne ta canjoshi da wani..

Shima bokan yashiga mamaki sosai yashiga kiran aljanin da suka tura wato shakikis,shiru bai baiyana ba kusan minti goma yana abu daya amma shiru.sai ya ce toh wannan al'amari akwai abin al'ajabi,yanzu dai zamu jira zuwan shakiskis tunda yanzu yaki ya baiyana tokou akwai wani abu tsawon shekara ashirin muke aiki da shi baitaba kin baiyana kanshi ba duk lokacin da na bukaceshi.yanzu abinda nake bukata kijira nan da anjima zan nemeki.

Ran auntie maryam yayi bala'in baci tashiga yiwa boka magiyar ya taimaka wannan aiki yayi kyau.
Ya amsa da karkisamu damuwa komai zai daidaita...

Allaah sarki ni da Humaira da bamusan wainar da ake toyawa ba,munbar ranmu muna ta cin abubuwan da auntie maryam ta baza agabanmu,sai gashi shimi shimi tashigo da Fara'arta hannunta dauke da ledar shawarmar.

Da murna muka ce well come back auntie.

Ta ce thanks dear na.jefi jefi muna ta hirarmu har yamma tayi sosai sannan muka je wajen mama muka mata sallama,sai da suka rakomu wajen motor auntie maryam taja ta tsaya,na ce auntie bazaki bimu bane naga kintsaya?

Ta ce no akwai abubuwa da zangabatar zuwa jibi zanzo muku.muka ce toh auntie don't fall us,muje muna ta jira kiki zuwa.

Ta ce zanzo karku damu.

Muka ce toh sannan driver yaja mukabar gidan....tun acikin mota sai ga kiran yusuf hira sosai muke na soyayya bansanma lokacin da muka iso gidan ba,jin tsayuwar motarne ya fargar dani ko jiran Humaira banyi nashige ciki,Ammi na samu a parlor tun kafin nayi magana tashiga yimun fada ban tanka ba saboda muna waya da Yusuf.jin kamar muryar mutum sanyashi tambayata menene naji kamar ana maki fadi my wify kinje yawo ba tare da umarninsu ba ko?

Cikin muryar shagwaba na ce A'a so take tabani wahala ne. halawa zatayimun ,duk tabi ta cire gashin jikina wai gyaran jiki,ni abin nasu ma duk ba sauki!....

Ya ce ayyah my wify ki ce anayimun gata ne bansani,ki daure a gyaramun ke.amma nima banbayar da goyon bayan baki wahala Ba,ki cewa Ammi ta biki da hankali jikinki bai saba da wahala ba..

Nashiga tambayarshi da cewa toh kaifa yaushe zasu gyaraka ne,ina magana har da zunguro bakina?

Dariya mai isarsa yayi sannan ya ce A'a my wify ai ni sungama gyarani tsaf, ina ganin tun ina yaro,amma kuma yanzu ma ina kan gyara maki kaina coz you are so special.kinsan akwai bambamci tsakanin gyaranki da nawa.
Mace tamkar kwai take kullum kuma tana bukatar mai lailayata da bata lura ta musamman,shi ya sanya kowane miji Wanda yasan darajarta bazai taba bari wani abu ya same ta ba,a zahurinrta da badininta duka......

Na ce hubby ka kyaleni Ammi tafara hararata kar abin yayi yawa ta hadamun da duka....

Cikin Sauri ya ce OK my wify kije kar naja maki laifi,I miss you and love you a lot.
Nima na mayar mashi martani.mukayi sallama na fito wajen Ammi da ke zaune gabanta duk kayan gayara ne.......


Auntie maryam sai kaiwa da kawowa take a tsakiyar parlor su ta kulla wannan ta kulla wancen tana jiran boka shiru kamar an shuka dusa,mama ce ta fita ta isketa cikin wannan hali.tana kokarin gyara daurin zaninta taja ta tsaya sai da ta gama nazarin 'yarta ta sannan ta ce lafiya kuwa na ganki haka cikin damuwa tayi mata tambayar.?

Sai da tadago kanta sosai ta dubeta,ta ce mamaki kiga kamar aikin da muka fara bazai dau hanya ba..

Maman cikin damuwa ta ce kamar yaya?

Auntie maryam ta ce takalman da na kaiwa Malam, yayi abin da zaiyi da zumar in har ta sanya a kafarta zatabar garin,amma ki gani, shi ta sanya muka zo nan gidan ko gizau batayi ba.nakirashi shima yayi ta mamaki yanzu haka ina jiran kiranshi.

Mama cikin karkace kai,ta gyata zamanta, ta ce,kai ni dama ban so kije wajen irin 'yan danfarar malaman nan ba.don kawai kindage ne.da wajen Malam mai kunfa yakun mukaje yanzu anwuce wajen.

Auntie maryam cikin ware ido ta ce Allaah mama idan bai kira anyi wannan aikin ba zaki kaini wajen wancen din. dandai su basason hada musu aikine, amma zanjirashi naga gudumuwarshi...

Maman ta gyada kai ta ce a toh kyayiwa kanki karatun ta nutsu kema kisamu Wanda zai aureki dubadai kigani duk sa'o'in naki da yar
zanda zanda da yaran su...

Ta zungura baki ta ce mama toh yanzu nima meye nake ba mijin nakeyiwa wannan abubuwan ba....

Haka suka dunga kulla makirce makircensu.


Akwana a tashi babu wuya a wajen Allaah yau har satinmu biyar zuwa Nigeria,cikin wadannan kwanakin kuwa,Ammi ta gyaramu sosai, jikinmu yayi matukar yin kyau,duk gunda muka gifta kuwa kamshi ke tashi,tun fitarmu zuwa gidansu auntie maryam basu kuma barinmu mun leka koda bakin get ne ba, Wai haskenmu zai dushashe.Yusuf da Dr zayd sun turo mana kudaden sayen kayan kawayenmu,kayeyyakin al'adunmu,muka saya adadin yawan kawayenmu.

mun shirya komai na komawarmu USA.cikin satin da ya saura mana da dare muka dunga zagaye danginmu muna musu bankwana....yayin da auntie maryam kuma take ta bin malamai don kuwa duk yanda tayi burinta baicika ba....
Nidai bansan shirin da take a kaina ba....tare muka gabatar da komai har kayan da zamu saka ranar daurin aure ita takai wajen tellan ta ya dinka mana k,wato kayan al'ada gambara kajiye.kafin takai wajen tellan sai da takai wajen malam kunfa yakun ya gamayin siddabarunshi akai sannan yabata wani dan karamin laya ta kaiwa tellan ya dinga ajikin kayan yadda baza'a gane ba.



Yau da misalin karfe takwas mun shirya tsaf komai ya kimsu daga turarokan wuta,humra da duk kayan kamshi da dukkan abubuwan da mukasan zamu bukata mun shiryashi. Kusan mutane ishirin masu zuwa bikin,duk muncika airport din da jama'a masu yi mana rakiya.
Duk mutanen wajen babu mai farin ciki irin auntie maryam saboda Malam kunfa yakun ya tabbatar mata cewa ina sanya tufafin auren zai wargaje Yusuf tuburan zaice sai ita yakeso kuma a take za'a maida auren kanta.....













_wannan kenan muje zuwa_



*show me love vote @ wattpad,teemacool2020*


⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*

Wattpad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 6⃣4⃣&6⃣5⃣




*Today's Hadith is about Funerals*

It was narrated that ‘Imran bin Husain (RA) and Abu Barzah (RA) said: “We went out with the Messenger of Allah (peace be upon him) to attend a funeral, and he saw some people who had cast aside their upper sheets and were walking in their shirts only. The Messenger of Allah (peace be upon him) said: ‘Are you adopting the practice of the days of ignorance?’ or; ‘Are you imitating the behaviour of the days of ignorance? I was about to supplicate against you that you would return in a different form.’ So they put their sheets back on and never did that again.”

(Sunnan Ibn Majah, Vol. 1, Book 6, Hadith 1552)






Karfe biyu daidai jirginmu yayi landing,bamu wani jira sosai ba sai ga daddy da Lil Yusuf da motocin wajen aikin dad sunzo daukarmu.munyi murna sosai da ganinsu daddy, ni da humaira ne muka shiga motar da daddy yake,sai sauran baki, kuma suka shiga sauran motar.daddy sai zaulayenmu yake,ya ce my princess ya duk kun girma kunyi kiba, lallai kaka ta iya reno mai kyau.duk mukayi murmushi,na ce daddy dama nasan dole zamuyi kiba,Ammi kullum sai tabamu kwai da milk munsha a dole.

Yayi murmushi ya ce gaskiya nagodewa Ammi tayi maganinku ace mutum bayacin abinci sai ruwan tea da coffee,ko mu a likitance muna supporting balance diet,amma Ku kunbijire wai sliming to fashion.haka muke ta hira,naso kiran Yusuf amma kunyar daddy yahanani.

Tafiyar minti ishirin yakawomu gida,sosai su mummy sun shirya gidan sai kyalli yake,ga kayan ciye ciye Kala Kala sun shirya muna shiga, da gudu muka fada kan cinyar mummy cikin farin ciki.

Itama cikin farin ciki ta rungumemu sai sumbatarmu take.....sannan ta ce Ku dagani karku karyani,tun kafin na tari manyan bakina tashiga yiwa family da mukazo tare da sunnu da zuwa cikin farin ciki da sakin fuska.

Muka mike muka shiga bedroom,daga ni,har hunairan mun shiga kiran mazajen namu domin sanar da su zuwanmu.

Yusuf dan zumudi bai barni namashi ko gaisuwa ba yashiga fadin cewa my wify well come to my world saukan yaushe?

Cikin taushin murya na ce yanzu zuwanmu gida ko zama bansamu ba na kira ka my hubby.

Ya ce okey hope kowa lafiya?

Na ce, lau suke,ya gida ya shirye shirye?

Sosai akwai but Khalid yana taimako da yin komai sai su dad kinsan ni dan gatan mummy ce,like you with your Daddy.

Na danyi murmushi,na ce kai! Ka ce ina da aiki cikin mu biyu waye zai rarrashi wani tunda yanzu zamubar karkashinsu?

Ya danyi dariya har ina jiyo muryarshi ya ce,nine my soulmate koda yaushe miji shine mai taltalin matarshi,haka itama matar takasance mai lura da duk wani abu da tasan mijinta na so,ta tabbatar da hakan ta zama jaruma wajen mallaka mashi kanta aduk lokacin da yake bukatarta,sannan uwa uba tsabta,iya girki,kwalliya da shagwaba,kissa da hila na halal.idan Kika lizamci wannan toh ba makawa kin mallaki duk wani namiji mai ji da kansa..

Sai da na ji ya yi shiru,sannan nima na nisa! na ce wadannan abubuwa da ka lissafo kam abu ne mai sauki idan har na yisu zasu mallakamun a man like you,in sha Allaah I will be a person doing more than you expect...Ina missing naka fa when are you coming?

Ya ce nima haka my wify zanzo na kwashe gara expect us within an hour, muna tare da Khalid da ango zayd right now,duk da shima tun dazu yake waya da iyalin nashi...

Na ce muna jiranku sai kunzo,sai da ya katse wayar na mike zan fito na ce wa Humairah da take waya har yanzu,idan kingama wayar ki sameni a part din Lil Yusuf...Banjira amsarta ba nafito parlor.

Auntie maryam tana ganina ta mike tare da fadin amaryar karni barkanki da fitowa nadanyi murmushi na ce muje dakin Lil Yusuf zan dan huta.tare muka gama yin arranging komai da su Ladifa itace kuma duk ta kai kayan da kawaye zasu saka ranar events,Wanda zai fara rana alkamis,har agama bikin.sai ga jack da matarshi Cynthia,sai yaranta mace da na miji.princess,prince.
Har mummy shi sunzo musamman saboda auren.






**************




Yau alkamis shine yakama ranar sakun lalle a wannan rana shigan kayan culture da mukayi yayi bala'in burge duk wanda ya halarci wajen,dangin angoye sun nuna bajinta sosai kido yake kusan

Please Login or Register in order to submit comment