Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

da sakon mutuwa ta fada a fili zaratun ganin nan tahowa gareni!

New York city

Mun fito daga last paper mu na council exams saura mana papers uku mu gama makarantar kowananmu yana cikin farin ciki munyi matukar kyau cikin shigan lab coat gwanin ban sha'awa .sai haska junanmu da pictures muke.sai ga Yusuf cikin shigan suit baki da bakin glass tsayuwar shi da motor duk mutane hankakisu ya koma wajen motor da yazo da shi sauron 'yan matan da basu wayeshi ba,sanya fadin wow!what's a handsome guy with beautiful car!.

Kicin kicin nayi da jin wadannan 'yan mata gaskiya I am a jealous type balle kuma akan abin da nake kauna kamar raina.ko sallama ban tsaya yi musu ba cikin takuna mai burge Yusuf naje daf da motor fuskana kuma duk na daureshi ba wannan murmushi da nake mashi a duk lokacin da yazo guna.

Da sauri ya fito ya budemun motor na shiga ,su kuwa 'yan matan har bude baki sukeyi suna kallo love yanda na wani shagwabi abin sai ya burgesu.

Sai da yaja motor yake tambaya ta lafiya my wify keda kike cikin farin cikin gama council exams dinki cikin lafiya menene kuma na fushi?
Cikin rarrashi yake tambayata.

Na zangura bakina na ce ba kai bane.

Ya ce ni kuma wane laifi zanyiwa my wify tuba nake koma menene na amsa laifin to fadamun naji?

Na ce kashigo cikin 'yan mata duk sun kallemun kalan wata acikinsu sacemun kai.

Dariya sosai yayi sannan ya ce lallai my wify kin bani dariya to kene kike ganinsu mata a wajena dukkan ganin maza nake masu ke ce dayan da na kalla naga kuma kin dusashe haskensu da haskenki,kisha kuruminki idanuwan Yusuf sun riga da sun rufe da kallon ko wacce irin mace, in ba matarshi fatimatuzzahra'u ba.

Naji dadin kalamunshi a haka har muka iso supermarket din,tare muka dinga zaban kayayyakin,kusan awa daya bamu gama zaban kayan ba sai ya ce, gaskiya wify na gaji zan dan huta kici gaba zaba,na to na nuna mashi gun zama,inners wears da na zaba kawai abin kallo ne sai wani sarkar diamonds.sauran kaya kuma duk suna gidansu.

Sai da aka gama jido da kayan bayan motor shi ma yafito muka Kama hanyar gidanmu zanyi kwana biyu kafin mu Fara sauran papers.tsowon tafiyar da muke yana tukinshi a tsanake kalamen soyayya yake ta kasheni da su gaskiya Yusuf karshene wajen nuna kauna da soyayya.

har cikin gida muka shiga motor sai da yashi suka gaisa da su mummy.cikin Fara'a ta amsa mashi,sannan yayi musu sallama mummy tana ko ruwa kasha mana ya ce A'a. Yusuf kanina ne ya mike ya kamo hannushi suka fita waje suna hirarsu bansan me suke fada ba.

_wannan kenan_

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

*WACECE NI*

✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*

Wattpad teemacool2020

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*page* 5⃣4⃣&5⃣5⃣

💞 *Dedicated this page to my Shalele,anti habibty Nurul ainayya yama habbeta*
*You are so special to me,you guy really made my world,lots of love💋*
*May Allaah united us and bless our family*
*page din naki ne kiyi yadda kike so da shi*💕

*TAMBAYA*
mace ce bayan anyi mata aure da wata biyu,bayan tayi al'ada tayi tsarki sai kuma ta fara ganin wani digon jini kadan,shin wannan mata za ta sha azumine idan lokacin azumi ne ko kuma me zata aikata?

*AMSA*
Matsalolin mata a cikin al'ada da aure kogi ne Wanda ba shi da iyaka sai dai ka'ida ta gaba daya cikekkekiya shi ne idan mace ta tsarkaka taga tsarki tabbatacce daga al'adarta,wato farin ruwa bayan daukewar jinin al'ada,to idan wani bakin jini yazo bayan taga wannan farin ruwan ko fatsi fatsi ko wani dan digon jini ko wani danshi,to duk wannan abubuwan ba haida bane,kuma baya hana azumi da sallah.da jima'I ,domin shi ba Haida bane.
_akwai sauran bayani dangane da wannan tambaya a next page_

Bayan na koma makaranta da kwana biyu ina zaune a daidai student center su Latifa sun je karban online dinsu.ni ko ina kan duba PDF da aka turomun sai ga wata kyakkawar budurwa da gani ta girmeni sai dai yanayinta kamar sabuwar student ce.kusa da ni ta zauna,sai da tayimun sannu,sannan ta ciro wayarta suka fara magana sai ko jin tana kanuri tsab inajin maganganunta domin a gida ma shi muke.sai da ta gama wayar nayi murmushi na ce,sannunki 'Yar uwa.
Da mamaki ta juyota dubeni,sannan ta ce ashe na zauna kusa da 'Yar u wata ce, bansani.haka muka yi ta musayar magana da ita cikin jin dadi,muka kuma yi exchanging number waya. sai da ta mike,sai ta ce, 'Yar uwa naga takalminki flat ne duk na gaji da wannan high heel taimakeni da shi naje exams and record na dawo tunda kina zaune.

Na mika mata takalmana sannan na ce ba komai sai kindawo.haka ta barmun ta kalmanta ta sanya nawa ta tafi exams and record.niko naci gaba da harkokin gabana..

Itako tana barin wajen da saurinta ta iske aunty Maryam da take jiranta cikin farin ciki suka bar makarantar saboda abin da suke bukata sun sameshi cikin sauki.

Kusan awa daya ina jiran wannan baiwar Allaah da ta kira kanta da suna Nasreen,bata zo ba har na gaji na nufi exams and record din ko zan ganta amma babu ita babu dalilinta.da na tuna number wayar da ta bani nayi trying bata shiga,ina cikin nemanta sai ga su Latifa sun dawo har sun gama abin da suka je yi.
Ina gaya mata abin da yafaru sai ta ce kawai mu tafi gida,ai bazaki dauwama da nemanta ba ,idan ta tashi Neman takalminta ta sameki a gida.haka na hakura na sanya takalman da ba nawa ba muka koma gida.

Yusuf zaune a gaban mahaifinshi sarki Abduljalil mai martaba da haiba,cikekken malamin sunnah ne da yake gudanar da dukkan ayyukanshi bisa tafarkin manzo, tsira da aminci Allaah su tabbata a gareshi.Yusuf ya sadda kanshi kasa,yana sauraron maganganun mahaifinshi cikin girmamawa.abin da nake so da kai yanzu duk wani shiri da kake ka gamashi cikin sati biyun nan saboda zamu hada mugabatar da bukin sarautar waziri,nima kaina na yaba da halin yarinyar ga kuma mahaifinta ma kuma mutumin kirkine...Yusuf sai gyada kai yake cikin gamsuwa da maganar mahaifinshi sannan ya ce toh Baba in sha Allaah zamuyi duk yanda kuka ce.dama ina jiran ta kammala jarrabawarta ne amma yanzu sun kusa kammala wa,cikin kwanakin nan.

A kwana a tashi babu wuya awajen Allaah,sai gashi yau mungama last paper mu lafiya.farin cikin da muke ciki baiyuwuwa na tsaya misalta makushi...kowa yayi shiga irin na al'adunshi nima na sanya dau ngashau da manjil wuriya da ndoska.'Yar kwarya kwaryar walima muka shirya Wanda sheikh Khalid ya gabatar gudumawar zamu bayar akan al'umma musamman musulumai da ke basu da 'yanci sosai a nahiyar Europe din.'Yan uwa da abokan arziki duk sun halarci walimar........Humaira ma cikin shigan kayan gargajiyan take kuma gaskiya munbada Kala na daya muzo akan cultural and heritage da aka gudanar.kyaututtuka sosai aka dinga raba mana.....

Da daddare misalin karfe takwas duk muna parlor niko ina zaune kusa daddy,dagani yana cikin farin ciki marar misaltuwa burinshi akanmu na ganin mun samu ingataccen ilmi mun sameshi a yau na zama cikekkiyar medical lab scientist,yayin da ita kuma Humaura ta kasance cikekkiyar Barrister......duk da gama university kuna da sauran shekara.ke zaratun zaki yi internship,ita kuma Humaira school of law.
Amma wannan zakuyi shine daga cikin gidan mazajenku.abin da daddy ya ce,kenan tun da yafara maganar aure duk kunya takamamu,ke Humaira kiyi Sauri ki fito da Wanda kike so idan muka bincika halinshi sai ahada auren naku.sai danyi murmushi sannan na ce daddy ita fa Dr zayd ya ce yana sonta amma taki bashi hadin kai kuma wallahi yana son kullum yana damuna akanta sosai...

Daga daddy har mummy suka shiga murna da jin maganata sai ya ce toh shikenan nasan abin da zanyi Ku tashi kushiga ciki.da sauri muka mike muka shiga daki Humaira sai zunguramun baki take Wai me yasa na sanar sa su daddy maganar zayd....

Auntie Maryam dauke da waya malaminta ta kira akan sunyi nasarar samun takalmina suna nan zuwa cikin satin nan,
Daga wancen bangare Hatsabibin malamin ya ce to yinkin rigar fa kun samu ne?
Auntie Maryam ta ce A'a so nake mu gama da wannan idan ka watsata duniya tabar garin to sauran ni zanji da shi da Kai na zan kawo maka yinkin kayanshi shima ka gamamun aiki akanshi ta yanda zai soni ya manta dukkan danginshi idan na ce taka kara zai taka...bokan Nata ya ce angama aiki idan har baki kuskure kin saba umaranin shakikis ba.naga dalloli sun shigomun.auntie Maryam ta ce eeh mallam saura ma suna kan hanya abin da nake dai aiki yayi kyau boka ya ce angama.sai da ta katse wayar sannan tayi murmushi ta ce Yusuf ka kusan shiga hannuna.,..

******************

Sai da nagama yin komai na shirin bacci,na shiga cikin bargo saboda yau Ana muku mukun sanyi Snow ake ta yi.har karkawa nake saboda sanyi duk da room warmer dake kunne hakan bai hanani jin sanyin ba.da kyar na daga kiran da Yusuf ke yimun,cikin sanyin muryar mai jin sanyi nake mashi magana.

Ya ce Allah sarki baby na haka sanyin ke azabtarmun ke!yi hakuri na kusa yin maganinshi,ai wannan zalunci ne ina nan na bar wify na tana shan azabar sanyi bayan ni nasan ina da jarumtar da zan yi kutunkutun hanashi addabarki.

Cikin shagwaba na ce ni wallahi duk jiki waje biyu ne sanyin ke addaba tafikan hannaye da kafa....

Ya ce yes this are the most sensitive part da sanyi yafi shiga jiki,amma kada ki damu idan har muka kasance karkashin inuwa daya zaki daina jinshi ,ni zan maki maganin abin,cikin murmushin kasaita yake maganarshi with full confidence....

Nidai nayi shiru ina sauraronshi saboda,wata maganar, idan Yusuf yayita kasa bashi amsa nake saboda nawinshi.maza gaskiya basu da kunya ko kadan....

Ya katse shirun da mukayi na dakiku da cewa kin tabbatar komai na kayan sun isheki jibi za su kawo kudin sadaki kuma,sa ranar bazai wuce sati uku ba ina fatan hakan yayi maki ba za ki takuru ba wajen yin shirye shiryen ki?

Na ce eeh toh ta wajena babu wata matsala bandai san su mummy ba.

Ya ce ina jiran feedback zuwa da safe.

Na ce toh.

Sai da muka dauki kusan minti daya babu wanda yayi magana sai ya kira sunana da wata irin siga mai dadin ji..

Nima ta na amsa mashi da wata irin muryar da baisan ina da ita ba Yusuf kamar yanda yakira sunana,saboda na ganeshi duk sanda zaiyimun wata muhimmiyar magana ko soyayyar idan ta motsa sosai zaratun zai ce...

Ya ce wow nifa, bakiji yanda kike sanyani kunya ba idan Kika rangadamun sunana agaban wadanda nake jin kunyarsu.

Niyi shiru saboda nasan magana yake nema.

Sai ya ce ina sonki zaratun na matsu Inga anyi auren nan na nuna maki irin yanda nake sonki.
I wish I could say I Love You to you in 365 different ways every day of the year. But since I don't have 365 unique ideas, a simple kiss with a loud and romantic I Love You would suffice, wouldn't it?

Na gyada Kai na kamar ina gabanshi nima na ce ina sonka so mai tsanani Wanda ina ganin cewa dukkan motsin da raina ke yi tana yi ne tare da sonka.....burina kawai na ganni a gidanka ina mai yi maka hidimomi....

Sai da yadan nisa cikin farin ciki ya ce nagode my wify da wannan dadadan kalamenki bazan mantada su ba.

Bayan munyi sallama na kashe wayar gaba daya na lumshe idanuna na dinga tunano maganganun Yusuf ina ta murmushi har bacci yayi awon gaba da ni......

Da safe bayan munyi karin kumollo mun baje muna ta hira sai ga auntie Maryam da dan karamin akwatinta tana ja fuskarta cike da murmushi ta shigo.
Mummy ce ta amsa mata sallamar da tayi ni kuwa cikin mamaki nake kallonta.sai da ta zauna ta gaishe mummy sannan ta ce mummy na dawone na baki hakuri bisa abubuwan da na aikata na gane kuskure na yanzu na yarda zan bayar da goyon bayana akan lamarinsu zaratun.

Mummy cikin farin ciki ta ce Maryam ba komai,kuma naji dadi, da kika gane gaskiya.mu dama bamu rikeki da komai ba ai zumunci yafi komai.Allaah ya hada kawunanku.

Auntie maryam ta ce Aameen.

Ta mike tazo kusa da ni ta kama hannayena duka biyu,ta ce Lil sis ki gafarceni ki yafemun abubuwan da na maki nasan kuskure ne gaskiya ke ce Kika dace da Yusuf na maki farin ciki....

Nima ina ganinta ido cikin ido,da murmushi dauke akan fuskata na ce na yafe maki sis nagode da kulawarki.... Sai gashi duk mun shiga yin hirar yanda auren zai kasance da irin occasion da zamu gabatar ma bambamta......

Nidai har ga Allaah bankawo komai aka ba yanda auntie maryam ta warware a cikinmu tana gudanar da harkokinta.da na fadawa Yusuf zuwan maryam da komai,sai ya ce,toh yayi kyau amma kuma ki sanya hankali akanta gaskiya naji tsoron wannan irin saddened changed....

Na ce toh cikin zuciyata kuwa tana cemun Yusuf me yake nufi?bai yarda da auntie maryam ba kenan.?

Kuyi hakuri da wannan.

_wannan kenan_

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

*WACECE NI*

✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*

Wattpad teemacool2020

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*page* 5⃣6⃣&5⃣7⃣

*Today's Beautiful Hadith is about Believers*

Abu Musa al-Ash'ari (RA) reported Allah's Messenger (peace be upon him) as saying: A believer who recites the Qur'an is like an orange whose fragrance is sweet and whose taste is sweet; a believer who does not recite the Qur'an is like a date which has no fragrance but has a sweet taste; and the hypocrite who recites the Qur'an is like a basil whose fragrance is sweet, but whose taste is bitter; and a hypocrite who does not recite the Qur'an is like the colocynth which has no fragrance and has a bitter taste.

(Sahih Muslim, Book 6, Hadith 288)

*_Have you read the Qur'an today? Taking time out to read the book of Allah is not only a blessed way to start and end your day, it is also a break from the busy nature of life to reflect, focus your breath on reciting the beautiful words of the Qur'an and worshipping Allah. Take some time out today for the Qur'an and may Allah reward you immensely for every word your eyes read over and voice recites - Ameen!_*

Yau asabar tunda muka tashi da safe ayyuka muke da shirye shiryen tarban dangin Yusuf da zasu kawo kudin sadaki da kayan sanya Rana.babu wani taro da akayi na azo agani.daga ammu wato *vaishali*,sai Sophia da Najmi,sai daidaikun kawayen mummy.cikin kawayena kuwa Latifa ce kawai na gaiyata.

daga doughnuts,cake,biskiwit,garabiya,graver,kowanne 30 pcs aka nade cikin roll paper.duk kayayyekin nan su mummy ne suka shirya shi,kayan al'ada babu abin da aka bari gonin ban sha'awa kamar dai irin Maiduguri nan.har shigan kayan irin na al'ada mukayi.

sai kusan karfe uku daidai sai ga danginsu Yusuf nikiniki da kayan sa rana,sisin gold guda ishirin da hudu suka kawo an sanya rana wata biyu.komai ya tafi cikin tsari ta kowane bangare sun nuna farin cikinsu.

Auntie maryam ce ta faki idon mutane ta kira bokanta,malam duk kokarin ganin an kawo wadannan ta kalma bansamu dama ba sai sati mai zuwa zan dawo maganar da nake maka a halin yanzu sun kawo sadaki kuma an sanya rana wata biyu.

dan Allaah duk yanda za'ayi kayi kokari ka wargaza wannan aure ni ce,na dace da yusuf ba wannan banzar ba.ta wancen bangare boka ya ce yanzu dai kiyi kokari ki taho da takalmar musan abin yi kar lokaci ya kure.

Ta ce toh malam zanyi iyakan kokarina na kawo maka cikin lokaci.
Sai da ta juyo ta tabbatar babu Wanda ya jita sannan ta shigo falo kamar wanda sai yanzu ta fito a bedroom.

Ta bangaren yusuf kuwa sai washa baki yake saboda farin ciki,yaciro wayarshi yashiga Kira na da kyar na samu na dauka saboda hayaniyar da su Humaira da kawayenta ke yi.

Da tattausar mutyata na amsa mashi sallamar da yayimun,daga jin muryarshi zakasan yana cikin farin ciki Mara misaltuwa.

Ya ce my wify sai gashi nan da wata biyu za ki zama mallakina,amma Kai! Gaskiya ni da a son samu ne sati uku za su sanya,tun da abu ya zo da maganar manya buba yanda na iya.

Na ce,wannan kwanaki da kake ganin yawansu yanzu zakaga sun dawo har sun wuce mudai mu roki Allaah nisan kwana.

Ya ce hakane yarinya Allaah dai ya nuna mana lokacin.

Na ce Amen.

Ya shiga tambayata duk abubuwan da muka gabatar Ina bashi amsa,sannan muka shiga hirar soyayyarmu ni banma San lokacin da 'yan cikin dakin suka watse.sai da muka gama wayar na fito falo na 'iskesu sun bazu suna cin kupsa da sinasir,sai kamoniye da Humairah ta sanya gaba dagani ita kadai ke ci.

Sai da na zauna sannan na ce Humaira matso da kamoniyar,nagani ko zan iya ci. Na dan ci kadan, saboda yayimun dadi sosai.

Da misalin karfe goma na dare bayan mun gama waya da yusuf,sai na kunna system dina sakonni da suka dade da banbude ba nashi dubasu,sai kawai naci karo da wani sako da ke Neman tube number489 cikin turanci ya rubuta kamar haka.

I am jack from Amsterdam,am searching for bear of tube489,I came across to your post which happen to be,like your are also searching for the tube that I am also searching for......please meet me with my phone number,so that we can discuss......

Haba ai bansan lokacin da na dauki number wayar da yabari ba,na shiga danna number,sai da tashiga tayi ta kara amma ba'a daga ba.naci gaba dailing kusan sau uku a na hudu sai gashi an daga,sai da mukayi musayar gaisuwa sannan na shiga yi mashi bayanin cewa nice wanda yabarwa sako through e-mail da yake Neman tube 489.ya ce eh ya shiga bani cikekken bayani akan tube 489 din akan cewa mahaifiyarshi ce tayi artificial insemination da tube din to yanzu da ya girma,yakeson sanin hakikanin mahaifinshi shine ta gaya mashi yanda akayi aka sameshi ,kusan shekara uku yake neman mai wannan tube to shine yaci karo da sakon da na tura a net.......

Tunda yake magana nayi shiru Ina sauraronshi sai da yanzu ya takaita bayananshi,sannan nima nayi mashi bayanin nawa tarihin,kuma nima a wannan tube ne aka sameni..

Duk da bamu gama tabbatar da hakikanin gaskiyar lamarin ba amma mun shiga yin murna sosai,sai ya ce zai zo San Francisco da kanshi mu gabatar da DNA test saboda mu tabbatar da dangartakarmu.

Nayi farin cikin jin haka sati daya,ya bayar zaibar abin Yake yi yazo saboda haka na sanar da mahaifiyata zuwanshi.

Na ce toh........

*yawan comment yawan typing*

Please Login or Register in order to submit comment