Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ilminta da karatun da tayi batayi amfani da su ba saboda son zuciya,Allaah dai yasa mufi karfin zukatanmu.

Jama'ar wajen su ka ce Aameen.

Yinin ranar babu wanda ta rintsa aka shiga yin shawarar maida ta Nigeria domin nema mata maganin sunnah tunda ciwon ba na asibiti bane....

Kamar karfe shida duk kawaye suka watse cikin farin ciki kamar kar sutafi nake ji suka barni daga ni sai Adde da aka ajiye zaman bakwai da ake yiwa amare a al'adarmu.amarya babu abin da za ta yi sai dai tayi wanka ta shafa mai ta harde akan kujera kamar sarauniya daga girki gyaran gida wanda aka ajiye zaman bakwai dince za ta dinga yi.hakan ya sanya bayan na fito daga wanka Adde ta kawo kaskon turaren wuta da ta zuba turaroka masu matukar kamshi na tsuguna akai dama jikina da danshin ruwan da nayi wanka,sai da yagama turarani sannan na sanya kayan baccin da ta gama turarrashi akan kaffasa sai kamshi ke tashi,da yake komai sai da ta turarashi undies bra duk.kasancewar kayan elastic ne sai yabi jikina ya fitomun dukkan halittar jikina sambal.


tun fitan yusuf bai kuma shigowa ba saboda abokaninshi da suka cika part dinshi suna 'yar kwariya kwariyar walima a tsakaninsu.wayar Humaira na daga da ta kira muka shiga hirarmu amma bata cemun komai ba game da sirrin dake tsakanin ta da mijinta sai abubuwan da suka faru game da auntie maryam ta ce my angel auntie maryam ta zama abin tausayi aljanun sun canja mata halittar ta daddy ya bada umarnin maido ta Nigeria dan nema mata magani.

Na tabe baki na ce Allaah yasa adace ya kuma kara tsaremu daga sharrin mutane da aljanu.

Humaira ta ce Aameen ya gajiyan buki?

Na ce Alhamdulillah yanzu su latifa suka bar gidan.ya naki da angonki?

Ta danyi murmushi ta ce gashi nan ya ce na gaishaki.

Na ce toh ina amsawa ki gaida Ammi ki ce ina son musuk dahara yusuf zaije ya karbomun.

Ta ce toh zan sanar da ita sannan muka tsinke kiran lokacin har Yusuf ya shigo,baiyimun magana ba yashiga bedroom yana daddana system nashi...

Jin shirun da nayi ya sanyashi fitowa parlon yana kokarin zama ya ce wasa wasa yarinya kin murmura fa naga sai wani kara killi kike naga zazzabin ya tafi da wani irin sihirtaccen kallonshi yake magana.

Na danyi murmushi na langabe kai,cikin sanyin murya na ce na danji sauki dai..ya ce kinyi sallah isha'i ne?

Na gyada kai na ce eh! Yanzu na idar.

Ya ce gud ki tashi mu shiga ciki ki bani labari...

Na sadda Kai na kasa ban runsa ba saboda har ga Allaah kasana har yanzu yana yimun zogi,bansan yanda ya yi ba kawai sai ya surata kawai naga ya yi ya nufi dakinshi da ni,bai zame ko ina ba sai kan makeken gadonshi da yasha gyara.

Shima ya dare kan gadon ya hada bakinmu tsawon lokaci yana ta sumbata ta,ganin wasan nashi yana so ya wuce gona da irin nayi saurin kwace bakina daga nashi cikin tsaro na ce Yusuf bani da lafiya wajen har yanzu ciwo ke mun.

A kasalance ya ce na sani my wify,zanbi da ke ahankali ba zaki ji ciwo ba, yashiga rarrashina.duk da kokarin da na yi na in zama jaruma in bar Yusuf yayi yanda yaso, kasa hakuri nayi,nikam banga banbanci da jiya da ya kawar da budurcina ba.duk da ban hana biyan bukatarshi ba,amma ya sha mita da korafi da kuma roko,ina makale jikinshi bayan ya gama biyan bukatarshi,sumbatu yake yi ta ko ina yana fadin maganganun da bai kamata in fadesu wani ya ji ba,a haka barci ya daukeni,wani irin nannauyar barci na yi mai nutsuwa ban farka ba sai da Yusuf ya tasheni sallar asubah...

Da Kai na na shiga bathroom nashi ruwan da ya hadamun mai dumi duk yabi ya zuba kayan kanshi ke tashi na dade a cikin ruwan saboda na ji dadin zama a ciki.sai da na yi wanka na dauro alwala na fito har lokacin ni yake jira,sai da na yi sallar raka'atanil fijr,sannan muka gabatar da sallar asuba.sai da muka gama azkar na mike na hau kan gadon don rama sauran barcin da ke damuna.Shi ma ya dawo kusa da ni ya kwanta ba mu muka tashi ba sai kusan karfe goma sha biyu,sai da na shirya na kimsa sannan na dawo part dina na sanya English wear lemon da fatsi fatsi ja da duwatsu masu daukan ido...cikin wannan yinin daidaikun baki ne daga danginshi suke zuwa duba amarya duk Wanda ya zo kuwa idan ya tashi tafiya da kyautar kaya masu yawa nake sallamarsu,a haka har dare yayi Yusuf bai samu shigowa ba saboda jama'ar da suke zuwa mashi taya murna.banjirashi bayan na gama komai na shirya cikin kayan barcina nabi lafiyar gado na kwanta..

Wajen karfe goma sha daya Yusuf yashigo dakin cikin shirin kwanciya yana dora kafadarshi ya jawoni jikinshi ya dora bakinshi a nawa sannan ya rungume tsam gaba daya ya kidimani,na kasa tsayawa wuri daya sai zillo nake ina bashi hakuri da kyar na samu ya sakeni yana kallona cikin murmushi na ce gaskiya Yusuf yau kam A'a.
Ya yi murmushin shagwaba ya ce yi hakuri my wify.
Nikam eh zanyi magana ya Kara kankameni a jikinshi come on zaratun kar ki zama raguwa mana bazai wuce ki ce jiya kaza da kaza ba.

Na ce to kullum ne?

Ya ce eeh mana idan naga zan iya,zo ki ji,ya na kokarin juyo da ni na fuskanceshi.kin dai san juyawa miji babu kyau?

Na ce uhm!

To juyo nan ki gani da haka ya shawo kaina na hakura na bashi hadin kai.watannin bakwai da aurenmu ina zaune gaban madubi ina shafa mai tare da kallon katon cikin dake gabana,Yusuf kuma ya fito daga bathroom kananan kayan da na jika ya yanke mun,yana goge hannayenshi da towel ya ce yarinya anya wannan cikin bai wuce lissafin da kike mashi ba?

Na kalleshi na ce toh kai yakai nawa kenan a ganinka?

Yadan karkata kai ya kuma kallon cikin ya ce zai kai wata tara.

Na yi murmushi na ce to kuma auren wata nawa?

Ya ce wata takwas, na ce ah toh!

Ya mikamun riga ina sanyawa ya karbi towel din ya je ya shanya ya dawo rike da jakata ya ce ga jakarki ko na rike maki banyi magana har muka fito wurin motarshi sai da ya budemun na shi sannan shima ya zagayo ya zo yabude ya ja mu muka tafi asibiti ante natal....

Dr Zainab ne ke yimun scanning tsawon lokaci tana ta duba na 'urar abin da ta gani ne bata gane sosai ba sai ta nemi sauron Doctors dake zaune da cewa please Dr Fatima can u help me sort this duk sun mayar da hankalinsu kan na 'urar dayan ta ce 'yan biyu ne duka maza sai dayarta ce eh haka ne but take a good look dayan yaron hannu uku ke dashi,Dr fatima kuma ta ce A'a Ku duba da kyau yara biyu ne da hannu daya daban.

Kafin na wartsake daga faduwar gaban da na samu sai kawai na ga Yusuf ya fizge socket din ya kashe computer.

Dakata yallabai inji daya likitar.

Yusuf ya ce a'a a barshi kawai.

Dr Zainab ta ce to kuwa duk abin da ya faru mu babu ruwanmu.

Yusuf ya wulwulo wani irin ashar ya kundumawa likitan na razana har bansan lokacin da na tashi zaune ba.saboda banta jin yayi ashar ba.

Ya kamani ya sauko da ni a kan gadon,Dr fatima ta ce ka yi hakuri a sake yin scanning din don mu gani.

Ya ce a'a a barshi kawai,zo mu je zaratun ya rike hannuna da hannununshi na dama hannnunshi na hagu kuwa jakata ya rike da shi.har muka iso wajen motarshi ban daina kukan ba.ya bude mun motor na shiga shima ya shiga ya ja muka bar asibitin.

Yana ta dura musu ashar da cewa basu iya komai ba,kin taba ganin mutum mai hannu uku?

Na ce toh yusuf mu koma su kuma dubawa mana.

Ya ce a'a bana so,na barwa Allaah al'amarin,kuma kema gareshi ya kamata ki dogara ki daina wannan kukan kike yi my wify kina ta da mun da hankali!.


















*vote@Wattpad teemacool2020*


⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*

Wattpad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 7⃣2⃣&7⃣3⃣



*Today's Beautiful Hadith is about Dhikr of Allah*

Narrated Abu Musa (RA): The Prophet (peace be upon him) said, "The example of the one who celebrates the Praises of his Lord (Allah) in comparison to the one who does not celebrate the Praises of his Lord, is that of a living creature compared to a dead one."  

(Sahih al-Bukhari 6, Book 80, Hadith 102)

*_Revive your soul, your heart and your being! Always be in a state of remembrance of Allah. Dhikr is light on the tongue but heavy on the heart, so fill your heart and praise your Lord for everything is a blessing and every moment an opportunity to thank Him, praise Him and worship Him._*





Ciki na ya shiga wata tara girman cikin yakai matuka har ba'a magana,gaba daya hankalin Yusuf ya koma kaina,a wannan lokacin ya shiga shirye shirye maternity,kayayyakin da ya saya duka biyu biyu ne ,daki daya ya gyara ya zuba kayan yara komai biyu biyu ne daga gado da komai.hatta abinci da zamu ci shi yake dafa mana,yauma baije office ba ina zaune a kasa gaban Yusuf latsa kumbirin kafafuna yake yi,ya ce me suka ce game da kumbirin nan?

Na ce sunce babu damuwa amma na kuma yin scanning,Yusuf ya zuba mun ido zaratun ba na ce a'a ba?
Na ce eeh.

Ya ce toh na sake ce a'a kuma kar ki sake min maganar kina tsammanin akwai mai canja lamarin ubangiji ne?
Na ce a 'a

Ya ce toh shikenan kina zuwa awo ne don tabbatar da lafiyarki,kuma a tsarinmu bai kamata na dubaki ba tare da wani likita dan uwana bai dubaki ba,amma da tuni na hanaki zuwa yin awon ma duka.yana magana yana matsamun kafafun nawa sannan ya ce idan Allaah ya yarda zaki haihu lafiya.

Muna cikin haka sai ga Khalid yayi mana sallama,Yusuf ya bashi umarnin yashigo,cikin murmushi idonshi a kaina ya ce madam barkanki da zaman gida.

Nima cikin murmushin na ce ango yau kaine a gidan namu duk ka boye har na sanya ran cigiyarka.

Ya kuma yin murmushi ya ce wallahi abubuwan ne sai a hankali duk bana samun zamu wannan lokaci amma ai kina kwasan gaisuwa ta awajen yallabai.

Na yunkura zantashi da niyar kawowa Khalid ruwa Yusuf ya hanani tare da cewa Khalid kai serving kanka kaga dai yanayinta kar ta wahala.

Khalid ya dan sosa keya ya ce no bana bukatar komai,na zo naganka ne.

Yusuf ya ce OK ina sauraronka sunyi maganganunsu duka abin da ya shafi family sannan suka tattauna akan auren Khalid da za'a gabatar.Yusuf ya tashi ya shiga ciki na juyo na fuskanci Khalid na wasa wasa har auren gashi ya gabato Allaah dai yasa muna ciki.

Khalid ya jinjina kai ya ce Aameen na so ke ce zaki hadamu kayan auren saboda yarinyar har zuwa lokacin bukin tana busy ne.na ce Khalid babu damuwa zan duba maka in sha Allaah..

Yusuf ne ya katse mana hiranmu cikin mika mashi wani takarda bansan na me ba.sannan ya yi mana sallama ya tafi.

na juyo na kwantar da Kai na akan cinyar Yusuf sannan cikin sanyin murya na nuna mashi bukatar khakid na shopping din aurenshi.

Tsawon lokaci Yusuf ke kallona sannan ya danyi murmushi ya ce da wannan katon cikin me ye zaki iya yi?

Na dan zunguro baki cikin shagwaba na ce wannan cikin kai ne kake ganin girmanshi amma ni zan iya yin komai har wajen bukin zanje idan na haihu ma gida ne ya yi murmushin jin dadi ya toh shikenan gobe ki kira latifa tayo maki rakiya tun da ita ma Humairan da ke abu daya ne.

Na dan rausayar da ido na ce amma zan rigata haihuwa dai.

Sai da yayi dariyarshi mai kayatarwa ya ce na Sani yarinya,ai ni babu wasa ko sanya a lamarina farat daya na dasa maki irina.

Ban maido mashi da martani ba saboda nagama karantarshi Neman magana yake ni kuwa banshirya karbanshi yanzu ba.
Washe gari kamar karfe goma sai ga kanwarsu Yusuf Arifa don ta tayani zaban kayan auren bamufi minti goma da shirin Lafiya ba sai ga latifa ma ta danno kai.a motar Arifa ne ta kaimu kantunan sayen gwalagwakai da sarkan diamond irin tawa sak na dauka mata kayan da muka jibge mata babu magana kowa idan ya kalla sai sanya albarka duk kuwa wannan kudin hidimar daga Yusuf ne.

Washe gari da safe muka tarkace komai muka koma gidansu Yusuf gunda ake bukin kenan ba karamin dadi dangin Yusuf suka yi ba da gani na tsohon ciki sai nan nan suke da ni hidima sosai suka shirya kamar babu gobe.bayan munje mun dawo daga gidansu amarya a gajiye na hau kan gadon umma wato mahaifiya m Yusuf da ta ce yauwa 'ya ta taho nan ki kwanta kedai Allaah ya saukeki lafiya kinyi ma kokari.cikin jin kunyarta nahau gadon na kwanta,sai ga Yusuf ya shigo dakin sai da ta gaishe da umma sannan ya matso kusa da gadon ya zauna cikin tambayata ko ina bukatan wani ne?

Kai na girgiza mashi sannan na ce ni da nake kusa da umma meye zan bukata.

A hankali ya sunkuyo daidai kunne na ya radamun yarinya zaki shigo hannune har kina cewa baki bukatar komai ba idan kina wajen umma to ni ina nawa hakkin kin sauke ne?
Cikin wani irin Shu'umin murmushi yake magana.

Nikam bance komai ba gudun kar umma taji abin da muke magana akai.

Sai da ya jira umma ta idarda sallah ya yi mata sallama ya koma shashinsu.washe gari ranar liyafar kuwa komai ya tsaru ango da amarya kuwa sai kyalli suke kana shiga wurin zakasan ba karamin ta'adi akayiwa turare kafin a zo.ina zaune kusa da Yusuf muma mun sha kwalliya,Zainab matar abokin Yusuf Dr suhaib ne ke gefenshi.ta ce lallai wannan amarya tana da kyau duba duk cikin kawayenta ta fito tauraruwa.

Na gyada Kaina na ce gaskiya Khalid yayi sa'ar samun mata.kawar amarya ta mike ta karanto tarihin amarya cikin tsari da nutsuwa,naji wani irin masokiya ta soke ni ai bansan lokacin da na ce wayyo Allaah na ba.
Dadin abin Yusuf din ne yaji cikin sauri ya juwo ya ce menene zaratun?

Na ce bana jin dadin kujeran nan ta matseni dubi duk matan wajen nan ni kadaice mai katon ciki Yusuf dukkansu kwalliyarsu gwanin ban sha'awa.

Da sauri ya ce wa ya ce maki kwalliyarsu tafi taki kyau?katon cikinki abin takamarki ne,don kema ya ganki yasan mijinki yana sonki.ni in Kika kyaleni zan ce dukkansu sha'awarki suke.

Nidai na yi murmushi kawai na hakura,sai da aka gama ciye ciye da tande tande,aka raba kyaututtuka.sannan Yusuf ya dauko ni gida saboda har lokacin cikina a dunkule yake,muna isa gida kawai kayan haihuwa yusuf ya dauka muka wuce asibiti.

,munyi sa'a kuwa Dr Fateema ne on duty,nan da nan takarbeni muka shiga labor room ta yimun VE ina 4cm ne.ta juyo ta ce wa Yusuf zaka iya Lafiya tunda har yanzu da saura ya ce no babu inda zani a haka Yusuf jifi jifi yana lekoni har kusan awa hudu ban haihu ba,matukar gakaibata nasha wuya har nake ganin bazan iya haihuwar da kaina ba,azaba ta gallebeni na shiga wani hali na gajiya na rasa inda zansa tsoma rayuwata in ji dadi tun bayan sallar isha'I muna tare da Yusuf a dakin haihuwar har wajen hudun asubah,na kalleshi lokacin da yake aikin gogemun gumin da ke ta ketomun,na ce Yusuf ka rakiramun mummy ina ganin mutuwa zanyi.

Ya yi Sauri ya ce stop it zaratun ya kankameni ya shiga radamun a kunne na,yana Kara karfafamun gwiwa karkiji tsoro Karki karaya haka iyayenmu suka sha wahala suka haifemu,shi yasa ya zama tilas muyi musu biyayya.

Muryata na rawa na ce Yusuf zan mutu.ya kuma kankameni sosai yashiga fadin ba za ki mutu ki barni ba my wify na roki Allaah akan idan har zan rayu ya rayani tare da ke kullum kuma ina cikin rokonshi haka.kiyi hakuri kiyi hakuri abin da yake nanata fadi kenan ,kiyi nishi umarnin Dr Fateema kenan,Yusuf yana rike da ni don karamun karfi yanamun magana daure ki yi nishi zaratun ko ma samu Allaah ya taimaka mana ki huta da wannan wahalar,da iya karfina nake nishi na ji tahowar wani abu na ji tamkar zai rabani biyu jikina sai bari yake na kidime saboda azabar da nake ciki na saki komai na koma kiran ubangiji.ina cewa hasbunallahu waniimal wakil a haka na haifi daya Yusuf sai gogemun gumi yake a gefen rigarshi yana fadin alhamdulillah kin haifi daya sauran daya,cikin Sauri na ce Yusuf duba ka gani ko shine mai hannu ukun?
Da sauri ya dauko ya zo kusa dani ya ce kinganshi lafiyarshi kalau duba da kyau dogo ne kyakkyawa ki kalla da wa ya yi Kama?

Duk da bangama warsakewa ba sai da nayi murmushin maganarshi.ya gama tofeshi da addu'o'i sannan ya mikawa was Dr shi.a gajiye na kuma haihuwar dayan yaron don kuwa shima na wahala sosai,kafin na haifeshi.cikin matsananciyar murna ya shiga fadin zaratun duba ki gani shima hannu biyu gareshi Alhamdulillah shima kamar na farkone santalele kamaninsu daya da dan uwanshi sanya mana shaida don mu gane su a kokarin da likita take yi na ganin ta wankemun mahaifa ta ci karo da wani yaron cikin sauri ta shiga shaidawa Yusuf akwai wani yaron,hasbunallahu waniimal wakil abin da Yusuf ke nanatawa kenan.
Nikam na shiga cikin fargaba da dimuwar jin maganar saboda duk karfina ya kare jikinta babu kwari ya shiga Kara karfafamun kalmomin karfafa gwiwa ciwo ya taso mun sabo har ina ganin yafi na farkon saboda jikina yayi tsami duk gunda aka taba ciwo ke mun,na rasa inda zansa kaina .cikin rarrashi Yusuf yake cewa kiyi nishi zaratun ya fadi hakan kusan sau ishirin,ya yi iyakan taimakonshi na kasa,zaratun zaki kashe yaron fa gashi ya sauko ki yi nishi ya fito mana Dr Fateema ke fadamun a firgice ,hankalina Yusuf ya kai matuka wajen tashi ya yi duk abin da zai yi na kasa nishi ji ya yi tamkar ya yimun nishin babu hali,yana rike da ni jikinshi sai bari yake ya yi kokari zaratun.

A hankali na dago kaina na kalleshi da kyar na bude baki na ce mashi kayi hakuri Yusuf karfina ya kare ji nake tamkar numfashi na zai tsaya ka yafemun laifunfukan da nayi maka na sake lumshe idona saboda jirin dake dibata.

da gwiwowinshi biyu ya durkusa kasa ya kife fudkarshi akan tawa yana shishshika tamkar mai yin kuka yana fadin ya Allaah.

Abin da na sani shine kawai ganin Dr Fateema tana sanyamun wani karfe a cikina ta ja ban kuma sanin komai ba sai da na dawo haiyacina ganin su mummy da daddy har da Humaira da ke kaina sai sannu suke yi mun innalillahi abin da ya zo kaina kenan na ce sun cira yaron ne ko har yanzu yana cikina?

Cikin sauri Yusuf da ke tsaye cirko cirko kamar tare mukayi nakudar da shi ya ce sun ciro baby girl ce kyakkyawa da ita kamar 'yan uwanta.Nagode Allaah bisa wannan ni'ima da ya yi mun sai da suka tabbatar da lafiyar mu sannan kusan motoci uku suka zo daukarmu domin maida mu gida.farin cikin awajen Yusuf kuwa baya misaltuwa...





_wannan kenan_






*vote@Wattpad teemacool2020*


⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐


*WACECE NI*




✍🏼by

*Fateema Muhammad Suleiman*

Wattpad teemacool2020



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is ton entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*page* 7⃣4⃣&7⃣5⃣



*Today's Message is about Spending in the name of Allah*

In the Quran, Allah guarantees to increase the wealth of a person who gives to good causes. Don't you want to be this type of person?

The example of those who spend their wealth in the way of Allah is like a seed [of grain] which grows seven spikes; in each spike is a hundred grains. And Allah multiplies [His reward] for whom He wills. And Allah is all-Encompassing and Knowing. *(Quran 2:261)*



_masoya zaratun da Yusuf gaskiya ina jin dadin yadda son book din ya sanya zumunci mai karfi a tsakaninmu ina ganin korafinku kan cewa bana updating cikin lokaci da masu bina private basu ga amsa ba to ina mai baku hakuri,saboda ina jarrabawa ne kuma mai daukan dogon zango.due to that from now upward gaskiya sai na samu sarari zan na maku typing,ina sonku kuma ina yinku sosai da sosai Ana mugun tare💋_






Tunda muka dawo gida Yusuf bai bar mu mun huta ba sai zirya yake tsakanin part dinshi zuwa nawa ko kunyar su mummy baya ji yaran kuwa daukan daya bayan daya yake musu saboda da so da kula da yake basu har na farajin kishinsu coz baya bin ta kaina sai ta yaranshi yake.duk wanda ya zo gaisuwa kuwa awajenshi za'a karba a baiwa masu zuwa.yau ma muna zaune da shi a bedroom ina bawa dayan jaririn nono,ina gama bashi Yusuf ya mikomun dayar da take ta tsala kuka na karbeta ina sanya mata nonon kuwa tayi shiru,cikin zungura baki na dan bata fuska na ce ni gaskiya duk ciwo suke sanyani idan suna tsotsan nonon nan nidai ka sayo madara mu dinga basu ko nima nasamu hutu kadan.


Yusuf ya bata fuska ya ce haba my maman 'yan uku ki zama jaruma mana wannan zafin zai daina ne,kuma in banda abinki bayar da nono ma jariranki kara maki daraja da ban sha'awa ke yi,sannan babu abin da yafi nonon uwa kyau da kara lafiya wa jariri ni a ra'ayina exclusive breast feeding zaki masu wannan shi zai sanya jariri lafiya da kuma kara masu immunity da zai kare su daga kamuwa da kananun cututtuka da ka kama yara kanana.sannan duk lokacin da zaki bada nono ki tabbatar kin tallafi kan jaririnki sosai sannan kada ki cire nonon daga bakinshi sai kin tabbatar ya saki da kanshi...

kamar yanda kika fara basu nono a labor room wannan yellowish ruwan nan shi ne abu mafi tsada da uwa za ta baiwa jariri domin duk wani magani da Kika sa ni yana cikin wannan ruwa da kakanninmu suke sanya shi a matse a zubar kafin sanya yaro nono to su sunyi a rashin sa ni ne amma yanzu saboda buncikenmu na likitoci sun gane amfaninshi.

Ranar suna kuwa yara sunci sunan mahaifina da mahaifin Yusuf da mahaifiyarshi wato Abduljalil,Abdulhameed da ummu ayman.hidima sosai Yusuf ya shirya kyaututtuka kuwa an rabar,waliman sunan yayi sosai yayin da sheikh Yusuf green ne ya yi bayani akan muhummancin tarbiyar yara da hakkinsu akan iyaye.anci ansha suna yayi suna masha Allaah duk Wanda ya halarci sunan zai tabbatar da cewa lallai wadannan triple babies din 'yan gatan mahaifinsu ne.ni kaina na yi wani shar da ni....hakika dangina sun nunamun gata domin sun zo sunan ammu Vaishali da yaranta ma sun halarci sunan....

Idan muka koma bangaren auntie maryam kuwa duk yanda aka yi wajen nema mata magani abin yaci tura tun suna zuwa wajen malaman zaure Ana ci masu kudi daga baya kuwa suka fauwala wa ubangiji lamarin suna koma wajen malaman sunnah toh yanzu dai zamu iya cewa ta dan samu sauki amma fatan jikinta yana nan kamar ba dadin gani...yanzu ma video sunan zaratun din take kallo sai ga hawayen bakin ciki suna kwarara daga idanuwanta,umman ta ce ke bata baki da tayi hakuri ta dauki kaddara.wannan kukan bazai amfane ki da komai ba sai ma kara maki wani ciyon ne,sai ga auntie maryam tana nadaman ayyukan da ta shuka da hannayenta yanzu ta girba da kanta...cikin fushi ta mayar wa umman na ta cewa ki barni na yi kuka ai tun farko ke ce kika ingiza ni na fada wannan halaka,da nakawo zancen zuwa wajen bokan baki nutsar da ni hanya madaidaciya ba gashi yanzu ni da ke duka muna nadama...haka suke ta jujjuya lamarinsu da neman Mafita...


Haka na kasance da jariraina cikin koshin lafiya ina basu nono akai akai saboda babu abin da nake basu face nonon ko ruwa Yusuf ya ce kar na basu sai sun kai wata shida wato exclusive breast feeding.baby friendly...yaran sunyi bulbul da su yau satinmu hudu kenan da haihuwar nanny's har uku Yusuf ya dauka domin

Please Login or Register in order to submit comment