Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin ka ke zargin Jauje da shi.

Suka yi shiru zuwa wani dan lokaci. Iro ya tsinka shirun da ce wa. "Na gode Allah da kika hango abin da na hango. Sadiya ke kadai ce wacce ta rage da dan burbushin tunani a tare da ke, ki daukar min alkawari cewa zaki taimaka min a wannan kokari na yanto Jaru."

"A shirye na ke Iro da na taimakeka ta ko wanne hali. to amma me kake gani zamu iya yi? Ka san dai duk wani kokari da zamu yi sai da amincewar Jaru zai yi nasara, matsalar da muke fuskanta ita ce, Jaru na masifar son Jauje?"

Iro ya ce. "Akwai dubara, da farko ina so na
gana da mahaifinta tukuna. Sadiya ta ce mahaifinta ya rasu a hatsarin mota, sai dai mahaifiyarta ko yayanta MAMUDA.

Ya ce. "to mu je na ga ko da daya ne daga
cikinsu."

Ba dai nufinka ka yi musu bayani ba, tun wuri zan gaya maka ba zasu saurare ka ba, wannan zamanin namu na na wani lura mai kwakwalwa kake zato zai yarda ka taho daga zamani mai tsawon shekaru dari. Ni dai inda zaka dauki shawarata kada ka soma wannan danyen hukuncin."
"Ke dai mu je kada ki damu, na san yadda zan bullo musu da ita

Mamuda yayan Jaru ya kasance saurayin nan da Iro ya roka ya turo masa Sadiya lokacin da Jauje ya zo wajen Jaru. Ya fito suka gaisa. "Sadiya ce ta ce ka ce kana son ganina ko lafiya?"

Iro ya ce. "Lafiya lau sai alheri, dama na zo da wata yar gudunmawa ne akan kanwarka Jaru. Akwai wani saurayinta da yake zuwa wai shi Jauje, ban sani ba ko kun yi bincike a kansa. Ka san yana da kyau yin bincike kafin a hada zuriya da mutum."

Mamuda ya ce. "Wanne irin bincike kuma? A wannan zamanin ake bincike? Ai in ka ce bincike zaka yi kusan duk wani mahaluki da ke numfashi a doron kasa sai ka tarar da shi da guntun kashi. A wannan zamanın abin da kawai ake la'akari da shi shi ne, ko mutum yana da yadda zai yi. In dai kana da dan abin hannu shi ke nan ai bukata ta biya."

Iro ya girgiza kai. "Amma wannan batu naka ba yana nufin ko da mutum matsafi ba ne?"

"Ko mene ne shi, muddin yarinya ta ce shi take so bamu da zabi dole mu bata. Ya fi mana akan ta gudu ta zama KARUWA.

Iro ya tambaya a rude, "Mene ne karuwa?" "Kana nufin baka san karuwa ba? To KILAKI

Iro ya sake shiga duhu, amma bai sake tambayar ma'anar ba. "Wato yanzu baku da zabi ke nan sai kusa ido Jaru ta shiga mummuman hannu, wannan wanne in zamani ne, da sakaci ya yi yawa." Mamuda ya ce. "Idan shike man maganar zantafi." "Maganar ke nan, amma in mahaifiyarku na kusa ka yi min magana da ita ina son ganawa da ita. "

Mamuda ya ce. "Ina fata dai ba akan wannan maganar kake son ganinta ba, don kuwa ina tabbatar maka zaka ɓata lokacinka ne ba zaka samu goyon bayanta ba, tafi kowa ma son Jauje a gidan nan saboda alherin da yake yi mata."Mamuda ya shige cikin gida abinsa, jim kadan sai ga Sadiya ta fito.

Ya yi ajiyar zuciya."Ban yi nasara ba. "Dama na gaya maka bata lokacinka kawai zaka

Shin me ake nufi da karuwa? Ya tambayeta. Ta dube shi. "Karuwa? macen da ta gudu daga gida ta samu gida ta tare maza ke zuwa suna nemanta suna biyanta. Me ya kawo wannan tambayar" Iro ya dubeta a firgice. "A'uzubillahi, fasikanci ke nan!"

******** ******** ******** ******** *************

A ranar wata lahadi da rana ana zabga rana kamar kai zai tsage saboda zafi, amma cikin gidan, musamman dakin da take sanyi kalau kamar lokacin hunturu.Tana zaune ita kadai tana kallon tashar tauraron dan Adam Jauje ya shiga wanka, jimawar da ya yi yana bandaki har ta sa Jaru ta kosa da kallo kai hatta zaman duk ya isheta. Ta mike ta nufi tagar gilas ta dubi waje dan tawon lokaci. Sannan ta nufi wani daki ta tura Kofarsa ta leka duhu ya gaida idaniyarta, ta rufe ta isa Kofar gaba ta tura ta jita a kulle ko motsi bata yi. Ta bar wajen ta koma tagar dakin tana kallon allon talabijin din.

Tana jin kishirwa sai dai rashin sanin inda sabis din gidan yake, wanda duk zuwan da ta yi shi ke kawo mata kayan shaye-shaye hakan ya sa ta daure, to amma sai dai dauriyar ta gagara ta nufi kofar da ta kan ga shi sabis din ya kan fito a duk lokacin da zai kawo mata abinci ko abin sha, ta bude ta shiga, falo ne na musamman da ya bata mamaki, don kuwa Jauje bai taba nuna mata shi ba tun da suke zuwa gidan, falon ya hadu iyakar haduwa kujerun alfarma sun baibaye bangon ɗakin, kilishin dake shimfide a tsakar dakin ya gama bango da bango, daga can kuryar dakin a jingine da labule firji ne kato, ta ketare kilishin kai tsaye ta nufi firjin ta bude da zummar ta samu wani abu don zubawa makogwaronta.

A NAN AKA YI TA
Abin da ta gani a cikin firjin ya sa ta kidime nan take, idanunta suka fito a razane, gumi ya keto mata duk da sanyin dakin. Ta yi wata 'yar munafukar karar fargabar abin da ta gani a ciki firjin.

Nan da nan tunanin farkon zuwanta ya fado mata a rai, lokacin da Jauje ya zagaya da su gidan ya hana su zuwa kusa da wani daki, ta tuno gargadain da da sadiya tayi mata akan tayi taka Tsantsan da Jauje alokacin har haushin sadiya taji.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment