Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya aiko ku? Shin ma wane ne ya sanni da har zai aiko ku wajena?"

"Mutane masu basira da hikima irinku basa ɓuya a duniya, sai dai abu daya dake ɓata min rai da irinku, kuna da kadara, watau hikima amma ba ku san hanyar da zaku bi ku yi amfani da ita ba, yanzu dai ji don wahala ka zauna kana tara mutane kana basu magani kana karbar naira goma-goma yayin daya a ce dubbai kake karɓa."

Idanum Jauje suka fito fuku-ruku cikin zalama. "Kana nufin DUBU ALIF?

"Babu shakka abin da nake hufi ke nan. Yan wadannan canjin da kake karba ai basu wuce na sayen abinci ba."

Jauje ya yi zumbur ya mike. "Dakata min, kana nufin ni zan iya mallakar kudi makudai haka?" Dogon ya ce a Rufule. "Da hausa fa nake magana.

Jauje ya ce "Na jika ai to amma kaka zan yi nasamu kudi masu yawa haka?"

Gajeren ya yi magana karo na farko. "Hanyar itace, ka bi mu mu sadaka da shugabanmu." Muryarsa kamar gogen tsumma. Jauje ya dan yi tunani na dan lokaci sannan ya ce da su. "To, mu je ku kai ni gun shugaban naku.

Suka shiga gaba Jauje ya rungumi kayansa ya bisu a baya har zuwa gindin wata bishiya in da wata dalleliyar mota ke tsaye suka bude masa gidan baya. Jauje Ya tsaya saroro yana duban ta. "Wannan fa.?

dogon ya yi murmushi. "Tamu ce." Jauje ya dube shi. "Kaka kuke kiran wannan sundumemen karfen?"
Murmushin da ke fuskar dogon ya subuce ya kurawa matsafin ido kawai cikin shakka.

Gajeren ne ya amsa masa "MOTA kenan. Hala baka santa ba ne?"
Jauje ya isa gareta ya shafa ta a hankali. Yace Damtsen uwa. Ya shiga suka mayar da Kofa suka rufe sannan su ma suka shiga suka daga suka bi lafiyar kwalta.

Jauje sai duban cikinta kawai yake yi. Kafin su isa gidan Jauje ya rinka leke ta gilas yana kallon gine- gine da abubuwan mamaki.

Gidan wani hadadden katafaren gida ne wanda ya sa Jauje ya soma tunanin ko a mafarki yake ganin duk abin da yake gani ne suka yi fakin, suka bude masa kofa ya fito sai kallon gidan yake yi daga dabe zuwa gidan sama. Suka yi masa jagora ya zuwa dakin shakatawa wanda ya sake jefashi a wani bahagon tunanin. Nan take ya zama dan kauye tsantsa, ya zage da kallo sadidan. Akwatin talabijin na kunne wani bature na labarai a tashar CNN.

Dogon ya nuna wa Jauje doguwar kujera. "Zauna ka huta kafin Alhaji ya fito." Suka shiga ciki suka bude wata kyakkyawar kofa, bayan sun ɓace sai gogan ya soma kalle kalle daga kusurwa zuwa kusurwa, ya matsa a hankali zuwa ga talabijin din nan ya kurawa gilashin ido, yana mamakin ta inda mutumin dake cikin akwati ya shiga. Ya isa gareta ya shafa allon ya ji bai taɓa mutumin ba, sai ya leka bayan akwatin, nan ma ya tarar a toshe yake. Abin ya bashi mamaki har ya tuntsure da dariya.

"Shekaru darin dama ke nan? kai ka ce mutum ya zo a daidai dan dantsen uwa nan" Ya sake kecewa da dariya.

A daidai wannan lokaci wata tsaleliyar yarinya ta fito sanye da wasu irin tufafin alfarma masu yawan launi, tana dauke da wani dan tire dauke da kayan shaye-shaye da wasu kofuna kyawawa. Ya kafa mata ido ko kiftawa baya yi. Ya matso gareta yana kallonta sama da kasa sai ya sake ɓarkewa da dariya.

Ta dan razana har ta soma yi masa kallon mahaukaci, amma sai ta jure bata nuna a fuska ba, ta ajiye tiren akan dan tebur da ke tsakar dakin ta tsiyaya masa abin sha a kofi kana ta yi sauri ta bar dakin, bayan ya rakata da kallo sai ya waiwaya ya dubi abin nan da ta tsiyaya. Ya mika hannu ya dauka ya kura masa ido sannan ya kai bakinsa ya dan kurɓa. ai kuwa da zaki, nan take ya kwankwade yana lasar baki. Ya Kurawa gilashiin ido yana dariya,
A daidai wannan lokacin ya ji an sake bude kofa ya waiwaya ya dubi mai fitowa sai ya tarar wani mutum ne fari sanye da kayan alfarma. Nan take ya tsayar da dariyar da yake, ya kura masa ido har ya iso.

"Ni ne ALHAJI BABA, yarana sun min bayani game da kai, na kuma ji dadi, barkanka da zuwa gidana."
Bai amsa BA.
kallon mutumin kawai yake yì. "Yaya sunanka ne?" mutumin ya tambayeshi.

Sunana JAUJE DAN GUNGUME SARKIN TSAFI.SIHIRTACCE-15

Sunana Jauje dan gungume sarkin tsafi." Ya ajiye kofin dake hannunsa.

"An ce dani in na zo gidanka zan samu kudi kamar zubar ruwan sama, in har maganar da yaran ka suka gaya min gaskiya ce.'
Alhaji Baba ya yi murmushi. "Wannnan zai iya zama gaskiya in har abin da na ji game da kai gaskiya ne."
"Me kaji game dani?" Alhaji Baba ya ce "An ce kana iya rikida baki ya koma fari, kana iya mai da dutse ruwa, kana iya maida mutum dan biri

Jauje ya ce. "Kankanin aikina ne." ya fiddo wani dan sanda ya nuna dan sundukin roba da aka ajiye
akan tebur wanda ke dauke da abin shan da aka kawo masa, nan take ya rikida ya zama Zomo sannan ya nuna Zomon cikin dan kankanin lokaci sai shi ma ya bace sai filin. Jauje Ya tuntsure da dariya.

Alhaji Baba ya ja Jauje ya zuwa wani dan daki ya kai shi ga wani dan akwatin katako dake tsaye a jikin bango, ya bude masa, daga samansa har kasa babu komai a ciki sai takardun kudi.
Jauje ya zazzaro ido, ya mika hannu ya shafa su, don ya tabbatar ba dabo aka yi masa ba. "Damtsen uwa."

Sannan Alhaji Baba ya sake jansa izuwa wani daki na daban da ya fi na farko duhu, ya kunna ashana kana ya isa ga wani guntun kyandir yasa masa wuta, sannan ya isa ga wani tebur da aka lulluɓe wani abu da bakin kyalle, ya sa hannu ya yaye kyallen, kan mutum ne a ajiye. Jauje ya matso kusa ya sake kura ido. Alhaji Baba ya waiwaya ya dube shi dan lokaci sannan ya ce. "Miko wannan ruwan na kusa da kai."

Ruwan wanda ke cikin wata kwalba, Jauje ya mika hannu ya dauka ya mika masa. Ya karba sannan ya waiwaya ya dubi kan. ya bude "Ruwa!" Kan ya soma fadi "RUWA!

Jauje ya kura ido gami da kunne, ya lura sosai ya ga kan nan ne ke magana.

Alhaji Baba ya kuza wa kan ruwa, sai kudi suka rinka zuba dami-dami yana sake kuza ruwa kudi na sake zuba. Daga karshe sai ya mayar da kyallen ya lulluɓe kan, ya mayar da kwalbar in da take sannan y dubi Jauje wanda bakinsa ke bude cikin mamaki.

"A yau kudi su ne abin bauta ga jama'a in kan da kudi kai ne Sarki. Zaka taka kowa ka kwana lafiya
ba za'a zartar ba sai da yawunka. A yau in ka ji ana bin kwakkwafi da neman asalin mutum to bashi da masu gidan rana. Kudi su ne mabudin abin da duk ya kasance a rufe.

Jauje ya gyada kai cikin amincewa. Sannan ya matsa ga Alhaji Baba. "Wannan batu gaskiya ne, to amma har yanzu ban fahimci dalilin zuwa da ni wajenka ba. Wanne taimako zan iya yi muku bayan kuna da duk abin da kuke bukata."
Alhaji Baba ya sake jan Jauje ya zuwa dakin shakatawa. "Abin da nake so da kai shine, ina so ka zama daya daga cikinmu, ka koyar da yarana yadda zasu su mayar da mutum wani sassaukan abu da zai yi saukin sacewa, kamar yadda ka mayar da yaro biri."

Alhaji Baba ya sa aka kawo wa Jauje tufafi na alfarma, kana aka hada shi da wata zankaɗediyar yarinya don ta koya masa mota.

A dan kankanin lokaci ya tara kudin da bai san adadinsu ba. Alhaji Baba ya bashi wani gida mai girma a wajen gari, yana da makekiyar katanga, gidan yana da kyau matuka. haka nan ya na da kyawawan motoci guda biyu na shiga taro

************ ********** ********* ***************

Iro ya mike zaune ya jingina da bishiyar da yake zaune a inuwarta a daidai lokacin da ya hango Sadiya ta nufo inda yake. Ya kura mata ido har ta iso ta zo gaba gare shi ta tsaya.
"Har kin dawo?" Ya tambaye ta.

Ta gyada kai. "Na dawo Iro, na tambaye ka wani abu mana."
Iro Ya dubeta. "Bisimillah.

Ta rage tsayi ta hanyar tsugunawa. "Idan na samo maka wajen kwana zaka hakura ka bar nan wajen?" Ya cika da mamaki, amma bai ce komai ba

"Akwai 'yan iska da barayi kada su cutar da kai Ina ganin tun da ka gans gidansu Jarun taka ai ka yi mai wuyar.

Ta dubi fuskarsa ta ga alamun bai son barin wajen. Sai ta ce "In da nake nufi na kai ka din babu nisa fa daga nan.

Haka nan ta yi ta rarrashinsa har ya amince ta yi masa sallama ta tafi gida akan in an jima zata dawo. Da ta koma gida, sai ta jira har sai da yayanta ya
dawo wanda a hannunsa take zaune ta je dakinsa ta same shi ta yi masa bayanin Iron Ya kishingide a kujerar da yake zaune. "Sadiya wannan wanne irin rashin hankali ne baki san mutum ba ki bashi masauki."?

"Yaya wannan bakon bakon malamina ne, bana bukatar sai na je ga yin dogon bayani don na san mai yiyuwa ba zaka fahimta ba. Amma ina rokon ka taimaka ka bar Iro ya zauna a shagon kofar gida tun ba babu kowa a ciki." Ta samu dan tsawon lokaci tana rarrashin yayan nata kafin ta shawo kansa ya amince, ta fita cikin farin ciki ta koma wajen Iro, A ranar Iro a dakin ya kwana

Kashegari tana zuwa makaranta, sai ta wuce kai tsaye zuwa ofishin Dakta Labaran ta tarar ya yi wasu baki yana ganawa da su, saboda haka sai ta jira har suka kammala, lokacin da suka fito ya raka bakin suka yi sallama ya dawo sai yake tambayarta. "Yaya? Me ya faru 'yan mata kina son ganina ne?"

Ta mike tsaye. "Eh Dakta."

Ya duba agogo. "Wannan wane irin lokaci kika zaɓa da zai shiga aiyukana." Ya dubeta, "mene ne muhimmacin ganawa da ni din?"

Ta ja numfashi kaɗan. "Ba wani abu ba ne wata magana ce game da shurin nan da ka taba gabatar da takarda a kai."

Nan da nan Dakta Labaran ya saki fuska. "Me kike so ki sani game da shi 'yammata?"

"Babu abin da nake so na sani. Sai dai wani abu da ya faru ne a unguwarmu, wanda ya tunatar da ni ya kuma yi min kama da sihirtaccen shurin nan da ka taɓa yi mana bayani."

Dakta Labaran ya kura mata ido cikin tunani gami da mamaki. "Shigo mana daga ciki, ina ganin maganar bata tsaye ba ce." Ya shiga gaba Sadiya ta yi murmushi yayin da ta bishi a baya.

Bayan sun shiga sai Dakta ya mayar da kofa ya rufe don kada wasu su dame su. Ya yi mata nuni da kujerar da ke fuskantar tasa, Sadiya ta zauna yayin da Dakta ya zagaya ya kame a tasa. "Kina nufin kin zo min da labarin da ya danganci SIHIRTACCEN SHURI ?

Tace. "Ba shakka, Dakta. "Ina zuwa." Ya' mike ya isa ga tarin littafansa ya zaro wani kato kana ya dawo ya zauna ya dauki biro

"Da farko fara min da sunanki da adireshinki, kafin ki fara bani labarinki,"

Sadiya ta yi kamar yadda ya umarta, tana fada yana rubatawa. Ta soma labarta masa abin da ya faru yana rubuta muhimman bayanan, a wasu lokuta ya kan dan tsagaita ya dubeta cikin sha'awar abin da take fada masa gami da mamaki, bayan ta kammala bayanin da ta zo da shi sai Dakta ya dubeta. mutumin na nan a gidanku Yanzu haka?

"Ba shakka yana gidanmu, Dakta." Ya ja dogon numfashi "Nesa ta zo kusa. Ai a nan makarantar kike ko?"

Ta gyada kai "A nan nake."

"To yanzu ki je ki cigaba da harkokin karatunki, zan jiraki da yamma bayan azahar ki kai ni gidan naku na ganshi. Bayan tafiyarta sai ya yiwa Sulaiman waya cewa yana son ganinsa da Azahar.

*********** ******** ********* ****** ***********

Lokacin da Sadiya ta dawo sai ta tarar da Dakta tare da wani saurayi dogo, siriri baki suka gaisa Dakta ya gabatar da Sulaiman da Sadiya ga jumansu, sannan ya shaida mata Sulaiman ne mai taimaka masa akan harkokin bincikensa na sihirtaccen shuri! Kuma ainihi dan uwan Iro ne na jini.

A motar Dakta suka dunguma suka tafi. Lokacin da suka isa gidan su Sadiya ta shiga cikin gidan, ta fito sannan ta shiga dakin ta isheshi yana tilawa. Tayi masa sallama

JINJINA GA

Bukar Mada

Ibrahim Sani K-sauri

Jikan Makoyo

Nura Usman

Saudat.

Maman FarukSIHIRTACCE-16

Ya waiwaya ya dubeta. "Sadiya har kin dawo?"
na dawo, ka yi baki iro Ya dubeta cikin mamaki. "Wadanne irin baki?

Zo mu je ka gansu suna waje suha jiranka.
Sadiya ta fito Iro na biyewa bayanta, Dakta Labaran da Sulaiman suka kura masa ido cikin kaduwa da shakka.
Har suka iso, Iro ya 'yi musu sallama suka amsa. "Su wane ne, ban shaidaku ba."
Dakta labaran ya tambaya. "Iro ne?"

Iro ya amsa. "Ni ne."

Dakta da Sulaiman suka yi musayen kallo,

sannan Sulaiman ya ce "Ko da yake ba zaka san ko
daya daga cikinmu ba, amma mun zo ne mu kai ka gida." "Gida? wane gida?" ya tambaya cikin zargi. Ya
dubi Sadiya sannan ya dubi mutanen.

Saurayin ya ce. "Asalin gidanku, sakon da abokinka Jabiru ya bar maka yana nan an adana maka, haka nan sakon da kaninka Talle ya bar maka shima ma yana nan.

Ya matsa gare su cikin mamaki. "Kaka aka yi kuka san Jabiru da kanina Talle? Suna ina?"

Dakta yace. "Ka kwantar da hankalinka, waɗannan tambayoyin suna bukatar dogayen amsoshi, zai fi kyau ka tsahirta mu kai ka gida ka natsu sannan mu bayyana maka komai."

Iro ya dubi Sadiya wadda a halin yanzu ke yi masa murmushi. "Kada ka damu Iro ka bisu ku je zasu dawo da kai babu abin da zai sameka."

Da rarrashi aka shigar da shi mota yayin da saurayin ya dube shi yana murmushi, yace "BARKA DA DAWOWA.

Barka da dawowa ina? Ya tambayi kansa. Sadiya ta leka ta tagar motar ta dubeshi, duk hankalinsa a tashe.
Ya ce da ita. "Ki lurar min da Jaru." Ta ce. "Kada ka ji komai, sai ka dawo."

Aka daga motar suka tafi yana ta waiwayen Sadiya, har suka ɓace ya yi ta kallon titi da gine-gine masu ban al'ajabi da wasu abubuwa da ko a mafarki Iro bai taba zaton zai gansu ba, lokacin da suka iso gidan suka yi fakin suka fito, suka bude masa baya ya fito. "Mun zo gida."

Ya dube su. "Kun ce zaku kaini gida, ina gidan yake?"

Suka nuna masa wani gidan sama. Yana duban gidan sai kokwanto ya sake darsuwa a zuciyarsa.

Dakta ya ce cikin zakuwa "Ka ga Iro, dole ne sai mun yi maka bayani kafin ka gane abin da ya faru, amma ta yaya zamu iya yi maka bayanin haka a tsaye. Mu shiga daga ciki tukunna ka samu nutsuwa.

A daidai wannan lokacin wani yaro ya fito daga gidan kamarsu daya da Talle kanin Iro, Iro ya dube shi cikin mamaki. "A' aha! Talle ne wannan?"

Sulaiman ya girgiza kai "Ba talle ba ne, wannan MANSUR ne kanina. Shi ya sa muka ce mu shiga daga ciki a yi maka bayanin yadda sha'anin ya ke

Jikin Iro a halin yanzu ya yi sanyi suka kalallameshi har dai ya yarda ya shiga cikin gidan, suka kai shi dakin shakatawa suka zaunar, sai duban dakin
kawai yake yi daga dama zuwa hagu, daga gaba zuwa baya.

Sulaiman ya bude firji ya fiddo lemo ya zo ya zube musu kwalaben akan teburin tsakar daki. Dakta ya yiwa Sulaiman inkiya da ido ma'ana ya kawowa Iro ruwa. mai yiyuwa don ganin irin kallon rashin amincewar da Iro ke yiwa kwalaben. Sulaiman ya dauko ruwa a kwano ya ajiyewa Iro a gaba.

Sannan Dakta ya ce ba zato ba tsammani. "Malam Iro shin ko zaka iya tuna me ya faru gareka lokacin da kuka yi karon battar karfe da Jauje a bakin kogo?"

Iro ya dube shi."SIHIRCE NI ya yi ya rabani da garinmu.

"Wanne ne garin naku."

"Kano." Ya amsa.

"Babu shakka Jauje ya sihirce ka, amma bai rabaka da garinku ba. Nan ce Kanon da aka haifeka, Kanon da aka binne mahaifarka." Dakta ya mike tsaye. "Na san ba zaka fahimta in ba bayani aka yi maka ba." Ya dubi Sulaiman ya ce. "Ina ganin zai fi dacewa ka fara baje masa gundarin TARIHI daga sama har kasa kafin mu je ga bayanin da zamu yi masa."

Sulaiman ma ya mike tsaye daga bayan kujera yana rike da kwalbar lemo, ya fara da cewa. "Maguzawa masu bautar tsunburbura da Shugabansu BARBUSHE wanda ya kasance sarkin fada kuma wakilin Jama'ar maguzawa ga TSUNBURBURA, ya karbo sakon shekara ga jama'ar maguzawa. Ina kyautata zaton zaka iya tunawa da wannan.

Iro yace "Wannan ai tsohon tarihi ne."

"Na sani" Inji Sulaiman. "Ina so na dawo da kai cikin tunaninka ne ta hanyar tarihi. Zaka iya tunawa da zuwan BAGAUDA dan BAWO jikan BAYAJIDDA, zamanin da Kararraki suka yi yawa akan irin zaluncin da ake yi a Kano. Bawo ya turo dansa don ya yaki zalunci in da tsawon shekaru sittin da shida da ya yi yana mulki har ya mutu bai kai ga nasara ba, DAWACACA ya gaje shi tsawon shekaru talatin da uku bai kai ga nasara ba, har sai da GAJIMASU ya karbi mulki."

Iro ya katsi numfashinsa. "Wannan duk kana maimaita min abin da na jima da sani ne. Gajimasu ne na san ya ribaci maguzawa suka gina masa ganuwa saboda kare mahara. In dai tarihi ne daga nan har mulkin 'yan tagwaye Nuta da Magwata, da Tsaraki da Naguji har Guguwa da Sarki Shakarau gami da Sarki Tsamiya wanda ya kafa tarihin korar Tsunburbura daga Kano da Sarki Zamnagawa, da sarki Yaji wanda a zamaninsa musulunci ya shigo kai na takaice maka har zuwa kan sarki Yakubu sarki na sha tara kuma sarki na karshe a gidan Bagauda a tsawon shekaru dari hudu da saba'in da bakwai baka bukatar tuna min komai."

Dakta da Sulaiman suka yi musayen kallo cikin murmushi sannan Sulaiman ya nemi da ya cigaba. "sai ko gidan Rumfa......

Iro ya yi dariya. "Yanzu mutumin da ya sanar da kai gidan Bagauda kana tunanin zaka layance masa gidan Sarki MUHAMMADU RUMFA Allah shi. Daga kansa har zuwa kan sarki Muhammadu ya rahamshe Nazaki, sarki na tara kuma na karshe a gidan sarautar Rumfa wadanda suka yi shekara dari da sittin da uku suna mulki, kai na katse maka hanzari har ma da GIDAN...SIHIRTACCE-17

Daga kansa har zuwa kan sarki Muhammadu Nazaki, sarki na tara kuma na karshe a gidan sarautar Rumfa wadanda suka yi shekara dari da sittin da uku suna mulki, kai na katse maka hanzari har ma da gidan
sarki Kutumbi da duk ahalin gidansa su goma sha hudu watau zuwa kan sarki Alwali wanda ya riski lokacin da shaihun Malami Sulaiman ya karbo tuta daga Shehu Dan Fodiyo ya zama sarkin fulani na farko, tafi tafi har kan sarki Alu Mai duniya."

Dakta ya Kurawa Iro ido dan tsawon lokaci sannan ya dubi Sulaiman. "Gwanin tarihi ne a takaice." Sulaiman ya gyada kai. "Ba shakka tarihi.

A daidai wannan lokacin aka yi sallama Alhaji Sunusi ya shigo, suka yi masa barka da zuwa. Alhaji? Sunusi Dattijo ne dogo mai dan jiki ya cire babbar rigarsa ya jefar kan kujera da babu kowa. "Na ga kuna ganawa ko. Bari na shiga da ga ciki kafin ku gama."

Sulaiman ya ce. "Baba ai ya dace ka zauna maganar duk tamu ce ya nuna Iro "Mun samo Iro yau.

Alhaji Sunusi ya dubi bakon matashin mutumin. "Iro?" Cikin mamaki da kaduwa ya samu waje ya zauna shi ma. Sannan Sulaiman ya dubi Iro ya cigaba da.

"Haryanzu dai a cikin tarihi. Shin ko a zamanin sarki Alu zaka iya tunawa wane ne Wambai?" Iro ya yi tunani sannan ya dubi Sulaiman.
"Abbas ke nan kake nufi?" ne ya zama sarki bayan turawa sun kama sarki Alu, shi Shi." Sulaiman ya amince. "Wambai Abbas shi ya zama sarki na farko a zamanin mulkin mallakar turawa."
Ya kurawa Iro ido yayin da ya yi shiru yana jira ya gama hadiyar mamakin a halin yanzu da ya riske shi.

Hakika wannan labari na ba-zato ya tsorata, ya kidima Iro. Ya zauna shiru a inda yake baya ko motsawa. Sulaiman ya cigaba. "Bayan ya samu shekaru
goma sha shida akan mulki ya rasu sarki Usmanu ya gaje shi, amma shi bai jima ba, shekaru bakwai ya yi ya rasu, daga nan sai sarki Abdullahi Bayero ya gaji sarauta ya shekara ishirin da bakwai yana mulki kafin Allah ya karbi ransa, sai sarki Sunusi ya hau gadon sarauta ya shekara tara kafin ya yi murabus a bisa dalilin wani bincike da hukumar jihar Arewa ta yi. Sarki Muhammadu Inuwa shi ya gaje shi, sai sarkin Kano Alhaji Ado Bayero wanda a yau yana da shekaru talatin da biyu da hawa gadon sarauta. Wannan shi ne ragowar tarihin da baka sani ba."

Iro ya mike tsaye cikin shakka da zaton ko dai a garin mahaukata yake. Ya rinka dubansu dai-dai cikinam rudewa.

Dakta ya dubi Sunusi. "Baba taimaka ka ba mu sakon nan da Jabiru ya bari cewa duk ranar da Iro ya dawo a bashi.'

Alhaji Sunusi ya tashi ya je ya bude wani dan akwatin jikin tebur ya fiddo takarda ya warwareta ya mayar da sauran ya kulle, kana ya kawo takarda wadda launinta ya fita daban ya kawo ya mikawa Dakta. Shi kuma ya mikawa Iro. "Wannan sakonka ne.

Ya mika hannu, duk jikinsa a sanyaye, ya karɓa ya juya takardar a hannunsa kana ya budeta a hankalit ya duba. Rubutu ne a ciki ajami yana gani ya shaida hannun amininsa ne Jabiru ya bude wasikar ne da sunan Allah.

*Sako na musamman ga masoyina, aminina Iro. Na san lokacin da wannan sakon zai iskeka na zama turbaya. Ya zamar min wajibi na bar maka wannan sakon. Ban san yadda zan yi wajen bayyana maka wannan al'amari ba, ba na yi ne don na ci amanarka ba. In har baka manta ba na taba shaida maka cewa ina son wata yarinya amma na kasa gaya mata maganar har ka yi min alkawari in muka je kasuwa na nuna maka ita. To, a gaskiya ba wata ba ce illa Jaru, lokacin da na lakanci ita ce kake so sai na saduda. Har sai lokacin da Jauje matsafi ya sihirceka ya maisheka shuri muka yi iya kokarinmu domin mu karya surkullen daga karshe muka fahimci ashe duk wanda aka yi wa irin wannan sihiri ba zai taɓa karyewa ba sai bayan shekaru dari.. A dalilin haka sai na kwaci butar ruwan da Jauje ya kwara maka shi ma na kwara masa ya zama shuri kamar kai, saboda haka shi ma ba zai dawo mutum ba sai bayan shekara dari. A bisa wannan dalili ne na auri Jaru. A daidai lokacin da nake rubuta maka wannan wasikar na haihu tare da Jaru, ta haifa min 'ya mace . Da fatan zaka yafe min abin da ya faru nake cewa Allah ya sadamu a darussalam*
Ni ne amininka JABIRU.

Iro ya samu kansa a halin firgita babu zato babu tsammani. Ya ji jikinsa ya dauki ɓari. Nan da nan Sulaiman da Dakta suka daddafe shi suna tausarsa da kalamai masu dadi. Suka dauki ruwan nan da tun farko aka kawo masa bai sha' ba suka kara masa a baki sai ya kama kwankwada kamar kunu.

Sai da ya farka sannan ya san bacci ne ya kwashe shi, Sulaiman na tsaye a bakin taga yana kallon waje yayin da Dakta Labaran ke zaune ya cire hula yana karatun jarida, Alhaji Sunusi baya dakin.

Ya mike gami da hamma da salati ya zauna. Sulaiman ya dawo, yayin da Dakta ya ajiye jaridar.

"Ya farka," inji Sulaiman. Dakta ya ce." Yaya jikin dai?"

"Lafiya." Ya amsa duk kamanninsa da muryarsa sun sauya.

Suka yi shiru zuwa wani lokaci, sannan ya dube su, "Bayin Allah me ya sa kuke so ku ruda min tunani ne?"

Dakta ya girgiza kai, "ba nufinmu ke nan ba. Muna kokari ne mu taimake ka mu dawo da kai ga ainihin tunaninka na asali. Hakika mun san ba karamin aiki ba ne wannan shi ne dalilin da ya sa muka dawo da kai ainihin gidanku, don su taimake ka da duk abin da kake bukata.

Iro ya dubi

Please Login or Register in order to submit comment