Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan. "Yanzu nan gidan mu ne?"

Sulaiman ya ce. "Kwarai kuwa. Ba zaka shaida gidan ba don an sake masa fasali, ai shekarun da yawa."

Ya yi shiru zuwa wani lokaci kan ya soma tambayar. "Ina Babana..." sannan ya yi shiru, jikinsa yabashi. "Ba dai ya rasu ba."

Sulaiman ya sunkuyar da kai dan lokaci kana ya cira ya dubi Iro. "Allah ya jikansa ya rahamshchi.

"Ya rasu..." bakinsa ya soma. "Na sani." Ya sake yin shiru zuwa wani lokaci

Alhaji Sunusi ya fito sanye da doguwar riga.

Iro ya ce "Talle fa, kanina."

Alhaji Sunusi da ke fitowa ya amsa masa, "shi
ma Allah ya yi masa rasuwa." sannan Alhaji Sunusi ya fadi kalmar da ta girgizashi.

"Ni ne dan autansa, ni kadai na rage a manyan dake gidan nan. Ka san zamani ya tafi shekara dari ba kwana dari ba ce.'

"Jaru fa.'

Alhaji Sunusi yace. "Ita ma ta rasu."

"Karya ne Jaru ba ta rasu ba, na ganta da...
"Ba ita ba ce wannan Jaru karama ka gani jikar 'yarta ce

Ya waiwaya ya dubi Sulaiman cikin shakka amma gami da amincewa da abin da zuciyar tasa bata son amincewa.

"Jaru? jikar 'yarta ba zata yiwu ba." Abin da kawai Iro ke fargaba shi ne duk sa'o'insa sun gabata.

Babu shakka a halin yanzu ya san babu wani sauran sa'ansa da ya yi saura, duniyar ma ta zame masa wata bakuwa...

KUCI ALBARKACIN GIMBIYATA

Maman Faruk Kifadawa Gimbiyata Na sadaukar da wannan domin farin cikintaSIHIRTACCE-18

Babu shakka a halin yanzu ya san babu wani sauran sa'ansa da ya yi saura, duniyar ma ta zame masa wata bakuwa.

Rana ta gota tsakiyar sama, zafinta gami da jimawa a tsaye ya sa Jaru tasare, littafan da ke rungume a kirjiinta suka yi mata nauyi. Ta samu kusan sa'a guda da rabi ba ta samu mota ba. Ita ba abin ta tafi gida a kasa ba saboda dan karen nisan unguwarsu.

Tana cikin wannan zulumin ne ta ji an yi mata ham, ta waiwaya ta dubi motar cikin shakka da mamaki. Wata dalleliyar mota ce shudiya mai sheki ta tsaya. Ta dubi mutumin dake cikin motar ta ga yana murmushi, nan da nan sai ita ma ba tare da ɓata lokaci ba ta yi masa murmushi. Tarkonta ya yi kamu don kuwa babu shakka kokarin ketarowa yake yi da motar. Ta yi ajiyar zuciya.

Lokacin da Jauje ya wuce sai ya taka birki ya dawo da baya a hankali. Ya kura mata ido cikin kaduwa da mamaki, ga dukkan alamu bata lura da tsayawarsa ba.

Yasauke gilas ya sake dubanta. Kai wannan kama da yawa take. Bata da wata maraba da Jaru ya yin mata ham ta waiwayo ta dubi motar, nan take ya lura ya ga motar ta tafi da hankalinta, ya jira har ta gama kallon motar ta dube shi sannan ya yi mata murmushi. Ga mamakinsa sai ya ga ta amsa masa da tattausan murmushi. Saboda haka bai bata lokaci ba sai ya yi sauri ya ketaro da motar ya nufo inda take. Godiya ga NAFISA yarinyar da ta horar da shi mota a tsawon mako biyu kacal.

Ya zo daidai inda take ya taka birki. "Sannu 'yan mata." Ta isa ga motar tana cikinshi, "yauwa sannu da hanya." rausaya ta leka

"Ina zaki je ne haka?"

"Gida zani, tun dazu ban samu mota ba."

"Shigo na kaiki."

Ta ji wani sanyi a ranta. "Na gode." Ta bude gidan gaba ta shiga ta zauna Jauje ya daga motar ya bi titi

"Sunana Jauje

ita dube shi. "Jeje" "A'a Jauje na ce."

Ta kyalkyale da dariya. "Sunanka da wuya. In baka damu ba zan kiraka da JEJE.

Ya dan yi nazari ya ga babu wani aibu ga yin hakan. "Zaki iya mana. Ke kuma kaka sunanki. "Ni sunana JARU.

Jauje bai san lokacin da ya taka burki a tsakiyar titi ba, Jaru ta firgita ta waiwaya ta dubi Jauje taga idanuwansa duk sun fito. "Me ya faru haka?"

Ya dubeta a hankali. "Kika ce sunanki Jaru."

Ta gyada kai cikin rashin fahimta. "I, suna na ke nan, mene ne ya razana ka?"

Ya girgiza kai gami da murmushi. "Babu komai." sannan ya ja motar ya cigaba da tafiya. Yana mai tunanin babu shakka duk inda yarinyar ta fito jinin Jaru ce

Ya dube ta, har yanzu kallonsa take yi. "Sai kim nuna min hanyar unguwar taku kada na wuce ban sani ba."

Sai da ya kai ta har kofar gida, ta bude kofa fita tana yi masa godiya,

Ya ce "Ni ma na gode da kika amince na dauke ki. Ko da yake ban sani ba ko kina da aure?"" Tambayar ta dan bata mamaki, amma ta amsa

masa. "Ba ni da aure."

Kana ya yi murmushi. "Ina da wata 'yar bukata

kuwa in da zaki amince.

Ta tambayeshi. "Wacce irin bukata?"

"idan kin yarda zan rinka zuwa muna tadi, haka kawai sai na ji ina kaunarki Jaru."

Jaru Ta dan lumshe ido gami da murmushi. "Ka iya zuwa Jeje, ina gida ko da yaushe da yamma."

"To shi ke nan na gode, sai kin ganni,"ya zaro kudi masu yawa ya bata "Ga wannan kya ci goro."

"Har da wahala haka Jeje" ta risina ta karɓa hannu bibiyu. "Na gode."

Suka yi sallama ya tafi, ta jira har sai da ya bасе sannan ta dubi kudin da ya bata ta yi murmushi ta shige gida.

********* ******** ********* ******* ************

Aka baiwa Iro daki a bene, da fari bai saba ba, amma cikin kwana biyu kacal ya saba dole. Tun ranar da aka kawo shi mutanen gidan suka yi ta shigowa suna gaishe shi manyan su da yaran su, maza har mata. Abin da ya fahimta shi ne duk a tsorace suke kamar masu gaida wanda ya je lahira ya dawo. Shi kansa Iro yana duban al'amarin da ke faruwa ne kamar almara, yana mai ji a jikinsa cewa mafarki yake yi, a kowane lokaci zai iya farkawa ya ganshi a garinsu na gaskiya tare da 'yan uwansa na gaskiya a al'ummarsa ta gaskiya cikin al'adunsa na gaskiya.

Yana cikin bacci, kwankwasa kofar da aka yi ya farkar da shi, ya waiwaya ya dubi kofa sai ya tarar ashe Sulaiman ne

"DATTIJO, har yanzu baka tashi ba ne?" Iro ya juya kalmar a ransa. Dattijo! wanene Dattijo?

Ya mike zaune gami da salati.

Sulaiman ya ce. "Ya kamata ka fito kaci abincinka kada ya bushe. Bayan haka Dakta ma yana son ganinka don tun daga ranar da muka samo ka 'yan jarida duk suka hana mu sakat. Haka nan Sadiya ma ta zo ta samu kana bacci."

Iro ya tambayi saurayin "Su wane ne kuma 'yan jarida?"

Sulaiman ya yi murmushi "Masu neman labarai ke nan. Bayan haka Sadiya ma ta zo ta samu kana bacci amma ta ce idan ta samu sarari zata dawo."
"Sadiya Kawar Jaru kake nufi?"

Lokacin da suka zo falo Dakta Labaran na tare da Alhaji Sunusi. Dakta ya mike tsaye. "Dattijo ka tashi?" Iro ya hasala. "Kaka zaku bata min suna ne, nine dattijo.?

Dakta ya yi murmushi, ya ce ba tare da ya nuna damuwa ba. "Allah ya huci zuciyarka, ga abincinka can a ajiye. Idan ka gama ci muna so mu je unguwa da kai.

Alhaji Sunusi ne ya amsa masa."Muna so mu kai ka wurare kamar su kasuwar kurmi ne da gidan sarki ko ka ga wasu abubuwa da zasu tuna maka da zamaninku."

Yaga gidan sarkin mai wata mahaukaciyar katanga mai yawan ado har tsohuwar kasuwar ta kurmi ba su yi komai ba face dada dagula masa tunani, duk sun kasance ne wasu abubuwa daban da tunaninsa hatta masallacin gidan sarki ba yadda ya san shi yake ba

A wannan fita tasu sun sada shi da mutane da yawa wanda har ya soma tunanin me mutanen wannan zamanin suka dauki hajji ne, kusan kowa ka gani Alhaji ne

Da la'sar sakaliya suka dawo da shi gida. Ba su jima da dawowa ba Sadiya ta sake zuwa Iro ya same ta tana jiransa. fito ya
"Iro." Ta kira sunansa cikin murmushi.
"Na'am Sadiya. An ee kin zo lokacin ina bacci.." Ya zauna a kujerar dake fuskantar ta.
"I, na zo. Na ce in ka tashi na dawo. tunda aka taho da kai nake ta son na zo ban samu damar zuwa ba sai yau."

Ya girgiza kai. "Sadiya mene ne ma bai faru ba Sun yi min bayani tun ramar wai ashe ni ban sami ba ma na zama tsohon ya yi. Wai shekara dari ce tsakanina da wannan zamanin. Jaru ma sun ce wai ba Jaruna ba ce jikar "yar ta ce da dai zantuka iri-iri na tabuwar hankali, har na rasa tsakanin ni da su wanene mahaukaci

"Daga kai har su babu mahaukaci." Inji Sadiya. Illa dai abin da suka gaya maka shi ne gaskiyar abin da ya faru

"Ke ma kin yarda da su kenan?"

"Ba maganar haka ba ne ka ga dai Jaru kawatace tun muna kanana, na kuma samu labarinku Iro, ko da yake dai kowa na jinsa ne a matsayin al'amara ni yanzu na yarda labarin gaskiya ne."

Ya dafe kai ya jingina da kujera cikin saduda. "To, ai shi ke nan, Jaru ta mutu, Jabiru ya mutu, iyayena sun mutu, Talle ya mutu, duk wani mahaluki da na sani ya mutu, bani da kowa a duniya shin mene ne amfanina a wannan bakuwar duniyar?"

Tausayinsa ya kama Sadiya. "Kada kace haka

Iro, har yanzu kana da 'yan uwa....... "Su wane ne 'yan uwan nawa kin ga yadda suka rika dubana kuwa kamar sun ga fatalwa, 'yan uwana duk sun mutu. Abin da zan yi yanzu shi ne, zan je na samu Jaru na bata hakuri a bisa abin da ya faru. Daga nan sai kawai na shiga duniya har ni ma ta Allah ta kasance a kaina.

******** ****** ******** ******* ****** **********

Kwanaki Bakwai Jauje ya jera yana kaiwa jaru ziyara....

ARADU ZAN DAKATA ANAN SAI NAGA COMMENTS DIN KU YAKAI GEJI.SIHIRTACCE-19

Kwanaki bakwai Jauje ya jera yana kaiwa Jaru ziyara a duk zuwan da ya yi sai ya yi mata hidima mai tarin yawa. Kafin wani lokaci sunansa ya kafu agidansu Jaru.

A cikin wannan 'yan kwanakin har irin hamshakan kantinan zamani din nan suka rinka ziyarta yana yi mata siyayya.

Wata ranar asabar da hantsi suna tare suna hira a kofar gidan su Jaru, sai Jauje yake yi mata maganar aure. Nan da nan ta cafa da cewa."Wannan shi ne babban burina, a gida ana ta jiran a ji lokacin da zaka yi magana.

Ya ce. "To ai ga shi yanzu na yi saboda haka ke nan ya dace ki kai min ziyara ki ga gidana ko sau daya ne kafin ki zama amaryata.

Ta yi shiru dan lokaci sannan ta ce. "Ina tunanin yadda zan yi ne na samu lokacin ziyartarka saboda zuwa makaranta.

Ya ce "In dai har zaki amince ko gobe sai na zo mu je tun da lahadi ce ba ku zuwa makaranta. Kada ki damu bajimawa zamu yi ba da mun je kin gani zamu dawo"

Ta dan yi nazarin maganar, sannnan ta dube shi ta ce "Shi ke nan sai goben idan ka zo.'

Ranar lahadi da safe Sadiya ta rako Iro gidansu Jaru, ya jira a waje yayin da ta shiga ta samu Jaru ta yi mata bayanin abin da ya faru ga Iro. "A halin yanzu ya gane gaskiyar abin da ya faru ya fahimci ba ke ce Jarunsa ba, jiya da na same shi a gida yake shaida min zai zo ya baki hakuri a bisa kuskuren da ya yi. Baki ganshi duk ya sauya hali yanzu ma tare muke da shi yana waje yana jira," Jaru ta rasa abin da zata ce

Sadiya ta ce, "kada ki damu ba zai yi miki komai ba, bayan haka ma shi kansa yanzu ya dawo cikin tunaninsa. Abin da nake so dake don Allah ki rufa min asiri ba don halinsa ba ki je ki saurare shi ko daida da minti biyar ne"

Da kyar Jaru ta amince ta fito cikin sanda da dan birbishin fargaba, ta hange shi sanye da hartun da wando kansa da hular gashi ga mamakinta kamar ba shi ba in ban da Sadiya ta yi mata bayani zai yi wuya ta shaida shi. Ta isa wajensa a hankali, tana dubansa daga nesa, yayin da ya hangeta sai ya soma murmushi. Ta iso gare shi ta tsaya dan nesa da inda yake.

Ya gaisheta ta amsa sama-sama.

"Ki kwantar da hankalinki, komai ya wuce tunda na fahimci duk abin da ya faru. Kin san wannan al'amari ne mai wuyar fahimta. Musamman kamanninki da nata, sunanki da nata ke hatta muryarki irin ta Jaru ce. Bayan haka ga zoben da na gani a yatsar ki shi ne wanda na baiwa Jaru. Saboda haka don Allah don annabi ki gafarce ni na yi kuskure mai girma."

Ta sunkuyar da kai cikin tunani sannan ta cira ta dube shi, ta ce "Shi ke nan babu komai na yafe maka."

Ya ce. "Yauwa Jaru na gode." A daidai wannan lokacin ne motar ta shigo

layin. Ya lura hankalinta ya tafi ga motar, saboda haka sai ya koma dubanta yana duban motar har motar ta samu waje ta tsaya.

"Shi ke nan jeka haka." Ya ji tana cewa "Ga saurayina nan kada ya zargi wani abu a ransa."kafin ya yi magana tuni ta bar shi nan a tsaye ta nufi inda motar ta tsaya.

Iro ya dan taka a hankali ya tsaya yana dubanta. Ya soma muurmushi a daidai lokacin da Jauje ya bude Rofa ya fito daga motar, nan take murmushin ya ɓace daga fuskar Iro. Gabansa ya fadi da ya ga abin da ke faruwa, Jauje tare da 'yar jikar Jaru. Duk da ya sake kayan jikinsa, amma ya shaida shi. Ya mai da tunanin sa ga wasikar Jabiru wadda ya bar masa, wanda hakan ya tabbatar masa da lallai wannan Jauje ne. Saboda haka nan da nan sai ya janye aniyarsa ta tafiya. Tun kafin ya zo sai da ya yiwa kansa alkawari wannan ne zai zama gani na karshe da zai yiwa Jaru, amma in har wannan mutum Jauje ne ai kuwa tafiya bata kama shi ba ke nan, a irin sanin da ya yi masa in har shi ne ya san ba zai taɓa zama alheri ga rayuwar Jaru ba. Babu shakka ya wajaba a gare shi ya tsaya ya taimaketa ta fita daga sharrin Jauje.

Iro ya nufi in da suke, daga Jauje har Jaru hankalin su ya tafi ga juna ba su ma san ya iso kusa dasu ba. Ya ji Jauje na fadin. "To, Jaru kaka maganarmu ta jiya, kin amince zaki bi ni ki ga gidan nawa?"

"Ni ba komai nake tsoro ba, kada na dade a yi min fada."

Iro na tsaye ba su lura da shi ba. Ya ce "Jauje." Jauje ya juya tamkar an tsira masa allura, ganin Iro ya razana shi, Ya gyara tsaiwa, zuciyarsa ta soma bugawa.

Iro ya matsa a hankali ba tare da ya dubi Tara wadda ke binsa da kallo ba. "Ashe ba ka rabu da zuriya gidan nan su sarara ba haka, ka nemi ka rasa rayuwar kakarta ba ka yi nasara ba bai dace ka hakura haka ba To, ba ka isa ba, na rantse da Allah sai dai bayan raina,"

Sannan ya juya ga Jaru. "Yanzu Jaru ina ke ina wannan tsohon mayaudarin matsafin, shi ne fa matsafin da ya maishe ni shuri shekaru dari da suka gabata: Shi ne wanda ya hana kakarki aure a wancan zamanin." Da ya Jura da irin kallon da take yi masa sai jikinsa ya yi sanyi. "Na san ba ki yarda da batuna ba, amma don Allah ki yi wa kanki fada, abin da kike shirin yi ba zai
haifar miki da da mai ido ba. Ta ce "Iro lafiya dai, ko abin ne ya dawo ne?

Ya ji wani irin kunci a ransa. "Kina nufin ni mahaukaci ne, na san abin da ki ke nufi ke nan." Ya dubi Jauje sannan ya sake dubanta. "Shi ke nan." Ya tafi ya bar su.
Suka bi shi da kallo, ta dubi Jauje. "Ka san shine?"

"Yau na fara ganinsa ma, wane ne?"

"Warkakken mahaukaci ne, kwanaki can haka ya biyo ni wai ni ce budurwarsa da zai aura. Dazu Sadiya ta kawo min shi wai ya warke yake ba ni hakuri, ina jin ko abin ne ya sake dawowa."

Suka yi dariya.

"To, kaka maganar tamu?" Ta dube shi. "Ka tabbata ba zamu dade ba?"

Ya gyada kai. "Yanzu zamu dawo."

"To bari, na je na shirya na fito." Ta juya ta nuti cikin gida. A kofar gidan kafin ta shiga suka sake
gamuwa da Iro. Ta isa in da yake tsaye a kofar gidan, ya kira sunanta, da fari ta yi kamar ta yi banza da shi, amma da ta tuna da Sadiya sai ta tsaya, ta waiwaya ta dube shi a hankali.

"Don Allah me kika sani game da Jauje? Ko ba ki taba yin bincike a kansa ba?" Ta amsa masa cikin ɓacin rai. "Me ya shafe ka da abin da na sani game da shi?" "Ba maganar ɓacin rai ba ce, ya dace dai mutum ya yi bincike kafin ya yi hulda da abokin huldarsa musamman a mu'amala ta soyayya. Jaru a matsayina na aminin kakanki ina so zan ba ki shawara.

"Aminin wanne kakan nawa? Kai Malam ba na son rainin wayo."

Ya dan yi tunani, hakika ya san ba zata amince da duk bayanin da zai yi mata ba. Sannan ya ce. "Jaru ni mai kaunarki ne tsakani da Allah, kin kuwa san ba zan so duk wani abu da zai lalata rayuwarki ba, amma Jauje bai dace da rayuwarki ba, na san shi ne ta dalilin kakarki. Haba Jaru, 'yar mutunci irin ki ina ke ina matsafi..."

"Kai Malam, ka fice min daga ido in ba so kake na saɓar maka ba, in kare nake so me ya shafe ka."Ka da ki ce haka Jaru, ya dace ki koma ki biyo tarihi sannan ne za ki gane abin da nake nufi."

Ta ja numfashi. "Shi ke nan, ba laifinka ba ne laifin Sadiya ne da ta kawoka wajena." Ta kada kai ta shiga cikin gidan. Ya bita da kallo ya na mai girgiza kai cikin takaici.

Wani saurayi ya zo zai shiga cikin gidan ya yi wa Iro sallama ya amsa, ya ce da saurayin. "Don Allah
Bawan Allah in ba za ka damu ba ka ce da Sadiya Iro na kiranta.

"Wacce Sadiya ce?" Saurayin ya tambaya.

"Kawar Jaru, tare muka zo da ita." Jim kadan bayan shigarsa sai ga Sadiya ta fito.

Ta zo ta tsaya a kusa da shi. 'Me kuma ya sake hada ka da Jaru? Ta shiga tana ta guna-guni tana zargina wai ni na kawoka."

Ya labarta mata abin da ya wakana. Ta yi shiru tana saurarensa har ya gama. Sannan ta tambaye shi. "To, kai yaya aka yi ka tabbatar shi ne, baka zaton ko shi ma jinin wancan mutumin da ka sani ne."

Ya girgiza kai. "Bana zaton haka, Jauje ne ba wani ba?"

Ya labarta mata wasikar da Jabiru ya bar masa wadda ke shaida masa cewa Jauje ma ya zama shuri. Kuma da kin ga yadda kamanninsa suka sauya lokacin da ya ganni da kin fahimci abin da nake nufi."

"To, yanzu yaya za ka yi ke nan? Ni dai da za ka dauki shawarata, da sai na ce ka rabu da ita, don ta yi nisa ba ta jin kira."

"Wallahi sadiya amincin da ke tsakanina da kakan yarinyar nan da irin soyayyar da ta wanzu a tsakanina da kakarta ba zasu bar ni na iya sa ido na ga yarinyar nan ta cutu ba."

Ta ja numfashi. "To, ai shi ke nan. Ya Yanzu za a yi ke nan ni dai unguwa zamu yanzu ni da Jaru, ko can gidanmu za ka je ka jira ni kafin mu dawo."
Ya dube ta, yayin da ya tuno da maganar Jauje
ta dazu. "Rakata gidan Jauje za ki yi?"

"Kada ka damu babu abin da zai faru, ka je can gida ka jira ni, sai mun dawo." Kafin ya sake yin magana tuni ta shige cikin gida ta bar shi.

Bai jira dawowarsu ba, sai kawai ya koma gida, Sulaiman kadai ya tarar a zaune a falo, ya yı masa sallama.

"Har ka dawo."

Iro ya gyada kai. "Na dawo, kai kadai ne?"

"I, ni kadai ne.

"Alhaji Sunusi ya fita ne?"

"A'a ina kyautata zato yana cikin gida."

"To don Allah ka kira min shi, ina son na yi wata magana da ku biyun."

RIGIMA SABUWA....SIHIRTACCE-20

Inason magana da ku biyun."
Ya zauna yayin da ya jira dawowarsa. Suka fito

tare, Alhaji Sunusi wanda ke sanye da babbar riga ba "yar ciki ba hula na biye da Sulaiman, suka zauna. "Yaya aka yi ne?" Yayin da ya saɓe rigarsa.

"Ina so zan yi muku wasu tambayoyi ne game da gidan aminina Jabiru."

Suka dubi juna sannan Sulaiman ya dube shi ya ce. "Wacce tambaya ce?"

"Wacce irin dangantakar zumunci ke tsakaninku yanzu?" Suka dubi juna sannan suka sake dubansa, amma ba su tanka ba, ya cigaba."Zumuncin da ke tsakanin gidan nan da gidan sarkin baka tsohon zumunci ne wanda ya yi kama da 'yan uwantaka. Duk abin da ya shafi gidan baka ya shafi gidan nan. Kusancina da Jabiru ya yi daidai da na Malam falalu kakan kakana da na Zubairu sarkin baka kakan kakan Jabiru. Ina fatan ba kuna so ku ce min dangatakar ta sukurkuce ba a cikin shekaru dari.

Har yanzu ba su sa bashi amsa ba
"Ban ji kun ce komai ba

Alhaji Sunusi ya gyara zama."Abin da ya faru dangane da sukurkucewar dangantakarmu da gidan sarkin baka ba laifin gidan nan ba ne, su suka yashemu Kamar Kaka suka yashemu? ko dai kuka ya da Juna. Yanzu babu wata sauran dangantaka a tsakanin ku? Alhaji Sunusi ya soma, "Akwai dangataka sauran da su ke nan?"
Sulaiman ya katse shi. "Kawu, zai fi dacewa ya san aininhin gaskiya. Wacce dangantaka ce ke tsakaninmu dasu, in kuwa har akwai dagantaka to mu yayanku ba mu santa ba."

Alhaji Sunusi ya ja numfashi, kana ya dubi Iro. "To wai me ya kawo wannan tambayar ne?"

Iro ya ce. "Matsafin da ya sihirce ni ya maishe ni shuri wanda shi ma ya zama shuri daga bisani da taimakon Jabiru, shi ma a halin yanzu ya bayyana. Abin da ya tayar min da hankali shi ne ya gamu da Jaru ya kuma ribaceta ta amince da shi wanda na yi imanin kasancewarsa tare da ita ba zai zame mata alheri ba. Yanzu in da akwai sauran dangantaka mai karfi a tsakanin gidan nan da na su ai da sai ayi amfani da damar a raba ta da shi

Alhaji Sunusi ya ce. "In dai wannan batun ne babu yadda zamu yi sai dai hakuri

Mene manufar sai dai hakuri? A zuba ido ana ganin irin wannan danyen hukuncin ya faru."Haka zamanin ya zama? Shi ke nan ku je abinku."

Bayan sun tashi Iro ma ya koma daki ya kwanta yana tunanin mafita.

******** ******** ******* **** ******** **********

Ana idar da sallar la'asar ba da jimawa ba sai aka yi sallama da Iro da ya fito falo sai ya tarar da Sadiya ce, ta sanya kaya wasu farare zane da riga da fatala.

lafiya?" "Sadiya, kaka na ganki haka da maraice,

Ta yi ajiyar zuciya. "Lafiya Iro amma ba lau

Ya matso kusa. "Me ya faru?" Sadiya Ta ce. "Zuwa na yi don na yi maka wani bayani."

"Game da Jaru?" Ta gyada kai. "I, game da Jaru." Ya samu waje ya zauna. "Kaka aka yi?

Ta gyara zama. "Mun je gidan Jauje saurayinta dazu. Ban taɓa zuwa bakuntar da aka karrama ni kamar wannan ba a rayuwata. Ya shirya liyafa ta fita kunya domin mu, sai dai gidan ya tsorata ni. Na farko dai duk inda ka samu gida irin wannan a biyu za'a yi daya, ko dai gidan wani hamshakin attajiri ko gidan saraki. Karancin shekarun Jauje da rashin sanin shi ko dan wane ne ne ya sa na firgita tun daga isarmu kofa lokacin da mai gadin gidan ya bude mana kofa muka shiga. Haka nan lokacin da muka zagaya gidan na ga zubinsa."

Babban abin da ya fi razana ni shi ne, da ya Janye mu da ga wani daki da muka nufa yace "Wai ba'a zuwa kusa da dakin. Wannan dabi'ar da ya yi ta kada min hanjin cikina har na ji ka fado min a rai. Da muka koma gida na yiwa Jaru maganar sai ta ce babu komai, na yi kokari na wayar mata da kai, amma sam ta Ki ta fahimta. Shi ne na ce bari na zo na yi maka bayani na kuma shaida maka cewa na amince da

Please Login or Register in order to submit comment