Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka tsira daga azabar danayi nufin gana maka ka karya wannan surkullen da kayiwa sahabina ko na lahira yafi ka jin dadi.
Jauje yayi dariya har da kyakyacewa kai yaro karyar ka ta sha karya wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa ka rufawa kanka asiri ka koma gida dan Dantsen uwan nan sahabin ka yayi gaba saidai tashin zance in kuma kayi taurin kai saidai uwarka kaima ta haifi wani dan Dantsen uwan nan.

Wannan lafazi da yayi ai kamar ya yarfawa Jabiru wuta don kunan rai yayi ruri ya zare takobinsa ya kada a sararin samaniya ihun da yayi ya amsa kuwwa a jejin kamar wani gwauron zaki Jauje ma ya runtuma ihu mai tsoratarwa ragowar ihun ya makale a sararin sama.

Jaru ta kura musu ido a firgice yayinda suka soma kusantar juna suka zo kusa da juna da akalla tazarar murabba'in yadi biyar suka shata daga Jauje ya fiddo da nasa takobin suka auna tsini sannan suka shata da'ira.

Jabiru ne yafara shiga sukayi gamuwar battar uwar barai takubbansu sukayi wata irin kara kamar an buga guduma akan karfen da aka fitar daga karkashin zuga zugin wuta tayi tartsatsi suka ja da baya kana suka sake gamuwa wannan karon saboda tsananin gwabzuwa sai Jabiru yayi taga taga yafadi jaru ta kwalla kara yayinda taga Jauje yayi kansa da suka.

Jabiru ya mirgina cikin azama ta yadda sukan ya kare akasa kafin Jauje yayi aune Jabiru yasa kafa ya harbe shi a makogoro yayi wata irin kara yayinda ya tafi da baya yayi zaman yan bori Jabiru ya mike tsaye zumbur yayi kan Jauje yayinda shima ya Mike cikin hanzari suka sake karawa suka buga har sai da takubban su suka dakushe suka zubar suka koma kokowa kura ta turnuke kamar guguwa Jabiru ya cira Jauje yafyada da kasa yabi zai danne amma kafin ya danne Jauje Shu'umin tuni ya bace.
Adaidai gunda ya bace sai Jabiru ya kwance gurunsa yakai duka sai ga Jauje ya bayyana Jabiru ya cira gurun ya fyada masa aka Jauje ya rusa ihu Jabiru bai sassauta masa ba yayi ta dukansa babu kakkautawa da Jauje yaji al'amarin bana wasa bane sai ya runtuma aguje Jabiru ya bishi jaru ma ta bisu.

Kodayake jaru tayi farin ciki da ganin Jauje na ihun wahala don shine halinda bata taba ganinsa aciki ba amma tana mai fargabar sharrin sa tasan Kogon daya halaka iro zai ja Jabiru.

Suka rinka gudu Jabiru na lafta masa guru har zuwa ga Kogon nan Jauje ya shiga aguje.
Hankalin jaru ya tashi ta zaci shiga Kogon Jabiru zaiyi hankalinta ya dan kwanta da taga yaja ya tsaya abakin kofar Kogon ta daga murya da karfi ta kwallawa Jabiru kira.
Ya waiwaya yayi mata alama da hannu ma'ana tayi shiru ya labe a bakin kofar Kogon ya mayar da gurunsa ya daura kana ya cire layunsa na wuya ya rike su ahannunsa yana jira.

Jaru dake can daga bangare guda ta kura ido cikin rudewa ta kasa gane abinda ke shirin faruwa.
Can sai ga Jauje yazama kare yafito da gudu Jabiru yayi wuff ya rarumi karen ya shafa masa layu saiga karen ya dawo mutum yayi wuf ya kwace zai gudu Jabiru ya rike masa kafa jauje ya rinka yunkurin bude jakar sa yayinda yake kokarin kwacewa can sai ya fito da BUTAR DUMAR.

Jaru ta kwalla kara cikin firgici yayinda kafin Jauje ya karkata bakinta ya zubawa Jabiru ruwan butar ajiki yayi wuf ya rike masa wuyan hannu sukayi yar gwajin karfi. Da Jauje yaji ya matsu ya saki wani wawan ihu Jabiru ya fizge butar ya Mike tsaye.

Jaru ta nufo wajen aguje cikin farin ciki.
Jauje ya soma Jan gindi akasa idanunsa suka fito zuru zuru cikin firgici yayinda Jabiru ke bin sa ahankali.

Na tuba na bika kayi min rai..
Jauje yafita daga hankalinsa saboda fargabar abinda ke shirin faruwa a gare shi.

Jabiru ya karkata bakin butar zai tsiyaya masa ruwan
Ka cece ni ya shugabana ya daga murya cikin firgici.
Jaru ta iso wajen ta tsaya abayan Jabiru tana kallon Jauje cikin kafewar zuciya da tsana. Kayi ahankali dashi Jabiru.

Kana so na ceceka nayi maka rai? Jabiru ya tambayi Jauje.

Eh ranka ya dade inaso raina yana hannun ka.
Ina iro yake?

Tsoro ya shige shi daya tuna da abunda yayiwa iro idanunsa suka firfito ruƙu-ruƙu yace a tsorace ya zama shuri ranka ya dade.

Zaka karya surkullen ya Mike in kana so na barka da rai.

Yace cikin razana ina mai fargabar bazan iya karya sihirin ba duk wanda aka mayar shuri sihirin bazai karye ba sai bayan SHEKARU ƊARI

Lafazin ya firgita Jabiru me kake nufi sai bayan shekaru dari.?

Ina nufin bazai cigaba da rayuwa ba sai bayan shekaru dari.

Karya kake yi ya karkata bakin butar zai tsiyaya masa ruwan ajiki.
Ya kwalla kara kayi min rai ranka ya dade bazan sake ba.

To ka karya surkullen in kana son tsira da ranka.

Nagaya maka bazan iya ba

Jaru tayi ajiyar zuciya.

Jabiru yace Kanada zabi biyu ko ka karya surkullen da kayiwa abokina ya tashi ko na tsiyaya maka wannan ruwan ka bishi ya zuwa dogon Zangon shekaru dari kaima.

Can sai Jauje ya shammaci Jabiru yakai wa layar zanar sa shafa. Saidai kash ya makara don kafin ya shafi layar tuni ya tsiyaya masa ruwan butar bakinsa ya bude cikin kokarin yin kara amma ina ruwan butar dumar ya riga budewar bakin nasa nan take launinsa ya sauya cikin dan kankanin lokaci sannan shima ahankali sai ya soma rikidewa ya zuwa shuri Jabiru ya kura masa ido cikin firgita da ganin abinda idon nasa ya gane masa sannan kafin kiftawa da bismillah sai kawai shurin ya bace.

Jabiru ya daga butar dumar kana ya dubi jaru yanzu abinda yadace shine mu koma mu nemo wanda zaizo ya karya mana wannan surkullen Ayau din nan.

Ga mamakin sa saiyaga kuka takeyi yayi sauri ya isa gareta.
Jaru kukan me kikeyi?
Ta share hawayen batareda ta daina kukan ba tun aranar da ya mayar da shi shuri na shiga cigiyar wanda zai karya sihirin nasa an kira masana sama da goma don akarya sihirin amma an rasa.
Ta sake fashewa da kuka Jauje ya cuce ni.

Bata dubi Jabiru ba taci gaba da cewa yanzu ni da iro Shikenan har abada? Ni yau menene amfanin rayuwata aduniya
Meyasa Jauje bai hadani da iro ya halaka ba yau aduniya yaya zanyi na sake samun wanda zai so ni da zuciya daya kamar iro.

Jaru nine nake sonki kamar iro...

Ta cira kai ahankali ta dubi Jabiru bakinta ya bude cikin kaduwa.

Na jima ina sonki jaru ya sake matsawa gareta na hakura ne na danne shaukin begena agareki saboda ke budurwar aminina IRO ce na daure na cije saboda kusancin dake tsakanina dashi amma jaru na dade da sonki azuciyata.

Ta sunkuyar dakai kasa na dan lokaci sannan ta cira kai ta dube shi amma fa ka tuna kai abokinsa ne.

Kwarai nasan ni abokinsa ne saboda hakane nake so ki amince min na aure ki don na cikasa miki soyayyar da iro bai samu damar cikasawa ba in har sihirin da akayi masa bai karyu ba ki kuma taimaka min don Allah don Annabinsa na cike gibin dake zuciyata na Tsantsar sonki dana jima ina fama dashi ni kuma nayi miki alkawarin zaki same ni mai faranta miki rai aduk tsawon zaman mu tare.

Haryanzu bata tanka ba kanta a sunkuye sai numfarfashi takeyi.

Ki daure jaru kin riga kin sani indai iro na nan haka nan zan zauna na cigaba da jurewa da kunan sonki duk tsawon rayuwata yanzu ma na furta ne don kawai naga babu iro. In har ban same ki ba wani ne zai same ki ni kuwa ina ganin nine nafi miki kusa da iro fiyeda kowa.

Ta cira kai ta dube shi kana ganin haka ba CIN AMANA BANE GA IRO?

Ya sake zagewa da rarrashi ko kusa wannan ba cin amana bane jaru ni nasan iro inda yasan cewa sonki nakeyi nayi imani zai zanje yabar mini ke.

Jaru ta sake sunkuyar dakai ta afka a tunani shin kuwa haka zata yiwu Jabiru abokin iro ne fa to amma ai Jauje ne ya kashe iro ko ba komai dai Jabiru ne ya raba ta da karfen kafa wanda ya cuzguna rayuwar ta ya hanata auruwa ya dauki rayukan samarin ta in kuwa hakane ashe bai dace ta auri kowa ba sai shi a matsayin sa na wanda ya kubutar da ita daga babban makiyinta.

Ta sake cira kai ta dube shi ko ba komai dai kyakkyawa ne sannan ga jarumta kamar ANTARU.

Sannan jaru tayi masa murmushi murmushin da baya Kunshe da komai sai kauna da amincewa.

BABI NA SHIDA 6

3 GA WATAN MAYU 1995.SIHIRTACCE-09

BABI NA SHIDA 6

3 GA WATAN MAYU 1995

DOKTA LABARAN nata tayar da jijiyoyin wuya agaban allo yayinda masana da dalibai dake cikin ajikin suka kafa masa ido ko wannen su fuskarsa Kunshe da alamun kokonto ga abinda Dokta ke yin jawabi akai abisa takardar da yake gabatarwa mai taken
SIHIRTACCEN SHURI GASKIYA KO ALMARA?

Wata katuwar taswira na rataye ajikin allo dakta labaran na nuna daidai inda kauyen da abunda yafaru yake akusa da taswirar ga wani babban hoton shuri da aka dauka.
A tsawon bincikena na shekara goma Dokta yaci gaba da bayani.

An sihirce mutumin ne shekaru takwas kafin turawa su ci Kano wanda yazo daidai da shekarar 1985 kokuma shekarar Hijira ta 1316 tara ga watan Rajab wanda yayi daidai da ishirin da biyu ga watan Mayu. Yau shekara dari kenan cif wannan sihiri da masirhicin yayi amfani dashi sihiri ne da bashida makari saidai zai karye da kansa bayan shekaru dari cif.

Don haka muna masu hakikancewa dangane da binciken mu cewa ranar Talata 13 ga watan Mayu sihirin zai karye mutumin da aka mayar shuri zai sake dawowa mutum kamar kowa.
Gunaguni ya kaure tsakanin jama'ar dake dakin wanda hakan yasa dakta labaran ya saurara har sa'ar da aka dan lafa sannan yaci gaba.
Saboda haka acikin dangin matar da mutumin yaso yayin da aka sihirce shi in har akwai wata wadda sukayi KAMA kada tayi mamaki ganin wani yazo yace ya santa yayi dariya..

Sauran jama'ar dake dakin suka kyakkyale da dariya.
Dakta labaran yagama gabatar da takardarsa ahalin yanzu ya gabatar da godiya ga jama'a.
Dakta labaran masani ne a fannin ilmin kufai a sashen ilmin tarihi da kufai na jami'ar bayero
Bayan ya kammala ya koma ya zauna shugaban taro ya mike yayi sharhi sannan ya bude filin tambayoyi da sharhi.

JARU tace SADIYA tashi mu tafi kinji ni duk abin ma ya gundure ni.
Ki Saurara mana agama ba'a fara damu ba bai kamata ace mu riga kowa fita ba.
Nidai ki taso kawai mu tafi wallahi ji nake yi Kamara akan ƙaya nake kizo mu tafi dakin karatu jarabawa ta matso amma bamuyi wani karatun azo agani ba mun zo nan mun zauna muna ta jin shaci fadi da sakarci.

Suka tashi suka fita daga dakin yayinda suka baiwa dakin baya sai sadiya ta dubi jaru tana dariya ke daman kauyen naku matsafa ne? Ji don Allah har tsafe mutun sukeyi ya zama SHURI.

Jaru tace ke rabu dashi irin almaran nan ce ta mutanen da.
Bakuma kauyen mu shurin yake ba a GUNDUWAWA yake mu kuma kauyen mu DAN SARAI ne.
Yanzu ke kin yarda ana sihirce mutun a mayar dashi shuri?
Sadiya tace Gaskiya fa abun da mamaki.

******* ********* ********* ******** ***************

Aranar Babban labarin ban mamaki kenan da gidan rediyon Kaduna ya gabatar a filin jakar magori akayi hira da dakta labaran kowa ya cika da mamakin wannan bincike kokuma ace almara.
Jaridun gaskiya Ayau duk sun fito dauke da wannan abin al'ajabi wanda ya girgiza al'umma sihirittacen shuri Labarinsa har filin taba kidi taba karatu na rediyon BBC.

27 MAY 1995

Sihirin bai karye ba aranar sha uku ga Mayu ba sai ishirin da bakwai ga Mayu babu kowa awajen da hantsi shuri ya rikide yadawo mutum garau dashi kamar ba'a taba maishe shi shuri ba.

Yanayin ne ya rudar da IRO yayinda yatafi a sukwane don ya suri Jauje daya nemi Jauje ya rasa saiya tirje da fari ya zaci ko Jauje yayi layar zana ne kafin ya isa garesa amma acikin dan lokaci saiya janye zaton hakan.

Na farko dai sararin sama tayi hazo hazo kamar hayaki ba kamar a farkon inda suka fara fadan ba inda yanayin yake mai hasken gaske sannan bugu da kari acikin jeji suke fadan amma ahalin yanzu ya ganshi ne acikin wata makekiyar gona.
Abu na farko daya zo ran iro shine Jauje yayi masa sihiri ne ya zare takobi tsirara ya soma tafiya acikin gonar yana waiwaye waiwaye bayan yayi tafiya ta kimanin farsahi biyu sannan ya hango wani irin dogon gini wanda ga dukkan alamu bashida durkoki ya nufi ginin gadan gadan cikin mamaki kafin ya isa saiya soma jin hayaniya da bushe bushe da buge buge.

Babu shakka wannan ba komai bane face aikin sihiri bai sake rudewa ba saida ya isa kusa kusa yaga ashe kararrakin dayake ji gamida bushe bushe wasu irin SUNDUKAI ne suke ta gilmawa suna kugi suna busa.

Ga su nan birjik wata irin bakar hanya wuluk sai tsere sukeyi sunfi doki gudu babu ko musu.
Abinda ya kara bashi sha'awa da wulgegeniyar tasu itace wasu nayin gabas wasu na yin yamma amma tunda yafara dubansu ko sau daya basu yi karo ba daya matsa kusa sai yaga mutane kamar kura ya runtse ido ya bude ta sake rintsewa ya bude haryanzu cunkoson mutanen yana nan mutane ne ko kuwa iblisai?

Daya lura saiya ga ginin daya fara hangowa ashe daya ne daga cikin ire iren su bila adadin ya matsa garesu ganinsa da takobi tsirara duk inda yayi sai a watse sun dauka mahaukaci ne musamman dayake irin shigar da yayi basu taba ganin irinta ba.

Ya rasa dalilin gudun saida ya lura yaga takobinsa tsirara sannan ya fahimta yayi sauri ya mayar dashi gidansa sannan yayi ta ratsa su yana wucewa sai dubansu kawai yake ya gansu da wata irin shiga musamman ma dai mata har masu wando ya gani wasu kuma masu kananan kanadadden gashi shigen na buzaye.
Shi kansa ya lura suma kallonsa sukeyi abinda ya bashi al'ajabi shine sundukan nan masu gudu ashe mutane ne aciki.
Mutane ne kuwa ko aljanu wadannan?

Dan shi dai yana ganin irin wannan kafirin gudu na sundukan nan shigarsu ba dai mutum ba saidai iblisai wusss. ashe ma sundukan kala kala ne.
Iro ya hango wasu marasa lillibi yan sirara manya da kanana masu kafafu bibbiyu maimakon hudu ba wanda yafi mai hawan wadannan Lange Langen wauta da rashin hankali don da ganinsu saurin faduwa zasuyi amma don karfin hali saikaga har iblisai biyu ne suke hawan mahayi daya.

Kai wannan abin mamaki dayawa ya ke ashe suma mutanen boye irin halittar mu daya damu yan adam? Gaskiya in na koma gida akwai labari su Jabiru da jaru da mutanen gidanmu zasu sha labari.

IRO AI BA IYA SU JABIRU DA JARU BA

MASU KARATU MA YANZU SUNA ZAMAN JIRAN KA DON SU SHA LABARISIHIRTACCE-10

Gaskiya in na koma gida akwai labari su Jabiru da jaru da mutanen gidanmu zasu sha labari.

Yaji wani rugugi a sama ya cira kai ya dubi saman saiyaga wani kalar sundukin har da fuka-fuki Yana tafiya kamar tsuntsu ya cika da al'ajabi kai wayannan iblisai iblacinsu da yawa yake kaga harda na sama wannan shine mutuwa kusa.

Ya Mike bakar hanyar nan da sundikai ke ta bi yana bin gefen ta yana kallon su yayinda suke ta gilmawa babu kakkautawa.

Wasu su biyu dake tafiya a gabansa suna tadi da ya saurara saiyaji kamar suna maganar ne da harshen Hausa ya matsa kusa dasu ya kasa kunne don yaji ko me suke cewa saiyaji babu shakka suna hira ne da harshen Hausa suna magana ne akan wata kasuwar da zasu je.

Iro ya saki baki cikin mamaki lallai lamarin hausa yayi nisa kaji iblisai ma da harshen Hausa suke magana kai daya lura saiyaji ashe kowa ma hausa yakeyi acikin mutanen da suke wucewa ya rinka shakkar shin in yayi musu hausa kuwa zasu ji.?

Bayan yayi tafiya mai tarin yawa saiyaji shi ya gaji likis gashi yana tafiya ne shi kansa baisan inda zashi ba ya hangi wani dattijo a gindin wata bishiya a zaune yana hutawa ya isa gare shi yayi masa sallama dattijon ya amsa masa yaje ya durkusa akusa dashi sannu da hutawa baba.
Yawwa ɗana barka da hanya tsohon sai duban iro yake a razane saboda ganinsa dayayi cikin wata irin shiga.
Suka gaisa iro yayi mamaki dayaji tsohon Najin hausarsa in banda wasu bakin kalmomi dayake amfani dasu wadanda shi iro bai taba jin su ba.

Ya share waje ya zauna baba don Allah wasu tambayoyi nake son zanyi maka.

To Allah yasa nasani ɗana
Baba don Allah wannan wane gari ne haka?
Tsohon yayi murmushi wannan KANO kenan ɗana.

Gaban iro yafadi watau aljanu ma suna da gari Kano?
Kai Kodai ana neman a haukatashi ne da gangan.?
Kano fa kace baba.
Babu shakka ɗana yaci gaba da murmushi amma inajin akwai wata kanon bayan wannan ko baba?
Dattijon ya girgiza kai nidai a iya sanina babu wata Kano bayan wannan.

Iro ya dan yi tunani sai ya yanke shawarar ya burma tsohon baba shi kuma sarkin garin fa kaka sunansa?
MAI martaba sarki Ado Bayero.
Iro ya dan samu yar sa'ida babu shakka wannan Kano wata ce daban ya raya a ransa hakika kuwa sannan ya waiwaya ya dubi sundukan nan da suke ta gilmawa akan bakar hanyar nan wadannan sundukan su kuma baba kaka sunan su?

Al'amarin ya soma ruda dattijon gami da firgita shi yaro hala kai bako ne?

Ya gyada kai lallai kam baba ni bako ne ya dubi hanyar sannan ya maido da hankalinsa ga iro wadannan MOTA kenan Jimlar su kuwa ana cewa MOTOCI.

Ikon Allah iro ya dubi dattijon shikuma gwadaben da suke bi fa Baba?

Yaro kai kuwa daga wanne kauye kake haka da baka san mota ba baka san TITI KWALTA ba ni ai na dauka babu sauran wani kauye a doron kasa da baisan mota ba.

Baba ni ba dan kauye bane.

Kai bana son sakarcin banza ni sa'anka ne da zaka zo kana tsokana ta kasan dai na haife ka yaran zamani da ba kunya ce daku ba shine zaka zo kasani agaba kana tsokana ta kamar wani tsaranka.

Don Allah don Annabi kayi hakuri baba wallahi ba tsokanarka nakeyi ba da gaske nakeyi.

Sannan dattijon ya kurawa iro ido ga dukkan alamu yaron yafadi gaskiya saboda haka saiya sauko daga fushin da yayi amma wannan wane irin bagidaje ne? Ya raya hakan a ransa.

Iro ya tambayi dattijon shin ko kasan SARKI ALU baba?

Dattijon yayi murmushi kwarai kuwa sarki alu mai sango? Iro yaji dadi a ransa ashe ko a biranen aljanu ma an san Alu mai duniya yayi murmushi.
Baba da kace wannan Kano kadai ka sani?
Eh ɗana kodayake kasan ilmi yawa garesa.
Amma ni in ka dauke wannan kanon bansan wata ba.
Haba baba kasan sarki alu mai duniya amma baka san kanon sa ba? Ni nan nine shaida sarki alu mai duniya shine sarkin daya kanon ni nan da kake gani daga kanon sa na fito.

Dattijon nan ya kurawa iro ido cikin karkarwa biri ya so yayi kama da mutum ashe ni duk tadin danake yi da mahaukaci nakeyi yayi zumbur ya Mike tsaye ya janye yar dardumar dayake zaune.

Baba ina zaka? Ko baka yarda da batuna bane?dattijon bai tanka ba.
Baka yarda daga kanon sarki alu mai duniya nake ba baba?

Babu ko shakka na yarda ɗana.

Iro wanda ya lura dattijon bai yarda da batun sa ba saiyace bari ma na nuna maka shaida ka gani in ma shakka kake yi ya bude jakarsa ya soma yan dube dube aciki da dai tsohon nan yaga hankalin iro ya koma ga jaka sai ya arce daga gindin bishiyar.

Iro ya Mike yabi dattijon yana kwalla masa kira firgitaccen tsohon nan ko waiwayo baiyi ba.

******* ******** ******** ******* ***** ************

Lokacin Da iro yakara yin gaba saiya ga ashe jama'ar kamar dada turo su akeyi gasu nan kamar farin ɗango ga irin gidajen nan masu gida kan gida babu adadi sundukan nan nan da tsohon nan yace masa sunan su mota kuwa kamar anan aka halicce su saboda yawan cinkoso da har iro na shirin ketarewa amma ganin wata mota ta make wata akuya ko shurawa batayi ba sai jikinsa ya dauki ɓari ai kuwa da ganin kura zata ci akuya shi daman tunda ya ganta yasan kisa zatayi yana nan yana ta raragefe saiyaga wata yarinya da kaya niki niki akai ya kirawo ta ke yammata menene wanna kike sayarwa?
Tace shinkafa ce da makaroni da salak.

Abinci ne?

Ta gyada kai eh abinci ne.

Ya yafito to kawo na saya ya nufi gindin inuwar wata bishiya tazo gabansa ta tsaya kama min in sauke.

Ya Mike ya kama mata ta sauke.
Yarinyar ta bude masa kwanukan ya soma dubawa don ya zaba yafara duba mai ganyen.
Wannan zogale ne ko rama yan mata.?
Yarinyar tace A'a Salak ne.

Menene kuma salak.?
Ya ajiye ya dauki dayar mai wasu dogayen fararen abu kamar tana nawa nawa ne?
Sha biyar. Ta mika masa Cokali
Ya jahilci Cokali nata ya yaɓa hannu ya cakuda kamar kwado ya kai baki ya tauna ahankali yana son ya gane dandanon abincin babu laifi ya hadiye yarinyar sai kallonsa kawai take yi.
Bayan ya gama ya sude yatsunsa kana ya zura hannunsa a aljihun wando ya zaro WURI ya kidaya goma sha biyar ya mika mata.

Yarinyar ta dubi wurin dake hannunsa malam ni bazan karbi wannan ba ka bani kudina.

Ba kince sha biyar ba ki karɓa mana ai sha biyar din ne.

Nan yarinyar ta tubure masa kafin wani dan lokaci sai gashi an taru awajen kowa ya tambayi abinda yafaru in iro yayi masa jawabi saiyace malam bakada gaskiya nemi kudinta ka biya ta iro yana ji wani na cewa hala wannan mutumin mahaukaci ne?
Ya zakaci abincin yarinya ka debo wuri ka bata kaida Allah ka biya yarinya kudinta.

Daga karshe wani ne ya zo ya tausaya ya biya kudin a madadin iro. Iro ya kurawa takardun da mutumin nan ya bayar ido cikin mamaki.
Wannan wanne irin kudi ne haka na takarda kai Allah wadaran naka ya lalace ba zasuyi karko ba.

******* ******* ******* ******** ****** ************

Yamma tayi likis rana tayi ja ta tafi faduwa iro ya tsaya karo na biyu don ya huta a kofar wani gida saiga wani sundu..... Af ashe wai sunanta Mota..

Wata kyakkyawa mai launin toka toka ta taho ahankali daga inda yake zaune a gindin wata bishiya yana duban motar kofa ta bude yarinyar ta fito ya kura mata ido cikin Faduwar gaba ya Mike tsaye ahankali kirjinsa na dakan uku uku yarinyar ta leka tana magana da yarinyar dake ciki.
Yarinyar na sanye ne da wasu riga fatala da zane kore masu kyawun gaske ga gashin kanta mai tsayin gaske ya sha kitso sirara suka yi sallama motar ta tafi ita ma ta juya zata tafi..

JARUNSA ce babu ko shakka Jaru ce kaya ya tsinke a gindin kaba ya kwala mata kira.

Jaruuuuuuu....

Jin an kira sunanta saita waiwayo da sauri ta dubi inda ake kiran.

Babu shakka itace ya runtuma aguje ya nufi inda take.

Jaru Allah ya taimakeni ya isa gareta
Ta kura masa ido a tsorace ta dube shi daga sama har kasa shigarsa ta sake razanata.

Jaru nine iro kaka kike dubana kamar baki sanni ba?

Ta soma ja da baya a tsorace
Jaru me ya same ki ne nine masoyin ki iro nine wanda nayi miki alkawarin sadaukar da rayuwata fa domin ki nine fa naki ko kin manta halinda Jauje ya jefa ki ne? Na rantse miki da Allah har yanzu a shirye nake na cece ki daga garesa.

Malam ka tafi ka bani waje ni bansan ka ba.

Ya girgiza da jin wannan lafazi matuka jaru ya kwantar da murya nine baki sani ba? Banyi mamaki ba mai yiwuwa Jauje ne yayi miki surkulle don kada ki shaida ni ya dubi yatsun ta yaga zoben nan daya bata.

Lebbansa suka rikida ya zuwa murmushi jaru dubi yatsar ki kin manta lokacin dana baki wannan zoben don tsananin kaunar ki ya masoyiya ta? Sannan ya nuna mata nasa zoben wanda babu wani bambanci da irin wanda ke hannunta dubi nawa nasan zaki tuna ya masoyiyata.

Jaru wadda keta dubansa cikin firgita tana ta neman dan sararin da zata gudu daga wajen wannan mahaukacin. Acan cikin zuciyar ta kuwa sai addu'a take yi Allah ya kubutar da ita daga gare shi.

Ta kuwa samu dan fili ta sharce aguje kamar zata fadi tana ihu MAHAUKACI YA BIYO NI....

Iro ya bita cikin kaduwa yana daga murya jaru ki tsaya ya

Please Login or Register in order to submit comment