Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dara dara cikin firgici A'a iro don Allah kada Jauje ya halaka ka kamar yadda ya kashe buba da Salele.
Iro ya dunkule hannu daya ya naushi daya don yayi nasa akan buba da Salele ba lallai bane yayi nasara akaina ba in yayi wasa nine ajalinsa sai na karar da ruhin numfashinsa.
Don Allah iro ka hakura Jauje ba imani ne dashi ba bayan haka babu irin abunda baya rikida yazama kada kaje ka halaka.
Iro ya dube ta kina sona har cikin zuciyarki?
Ta gyada kai..
In kuwa har auren ki ne zai jefa ni cikin mawuyacin hali to na kuduri aniya babu gudu babu ja da baya.
Jaru ta takawa iro har zuwa waje mai dan nisa alokacin da zasu rabu sai ya fiddo wasu zobba guda biyu ta mikawa jaru daya ta karɓa cikin mamaki wannan fa iro?
Yayi murmushi ki dube shi da kyau jaru na zinariya ne.
Ta dubi zoben kamar yadda ya umarce ta babu shakka zoben na da kyau.

Iro ya fadada murmushinsa nayi farin ciki da kika Yaba da kyaun sa sannan ya nuna mata na hannunsa musamman na tanade su ne don rana irin ta yau jaru Nasha jin labarin cewa ta irin wannan hanya Larabawa ke nuna dimbin soyayyar su ga a baban begen su saboda haka yau nima zan nuna miki balarabiyar soyayya.
Tayi murmushi yayinda ta boye fuskarta a tafin hannunta.
Iro Yakama hannunta ya sanya mata zoben a dan yatsanta sannan yace kema sanya min na hannun ki adan ya tsana sannan ta mika mata dan yatsan.

Ta kasa cira kai ta dube shi don kunya can zuwa wani dan lokaci saita cira kai ta dube shi haryanzu cikin jin kunya ta dubi hannunsa daya mika mata sannan takama hannun ahankali ta sanya masa zoben.
Ai kamar jira ake ta sanya masa zoben sai sukaji wata kara mai dode kunne suka waiwaya a firgice wani irin hayaki ya turnuke. Daga cikin hayakin sai sukaji wata irin mahaukaciyar dariya.
Hankalin jaru ya tashi ta firgita ainun shi kuwa gogan iro bai ko yi gezau ba maimakon haka ma shi sai kallon al'amarin yake cikin sha'awa da al'ajabi.
Ta cikin hayakin saiga Jauje ya dan sarkin tsafi Dannau ya ratso yana ta keta dariya yana sanye da munanan kayansu na tsafi ya nufo inda suke yanata cigaba da dariyarsa abinsa.

NIMA GANGARIYA BARI NAJA BIRKI ANAN NA BARKU KU HUTASIHIRTACCE-05

Saiga Jauje nan dan sarkin tsafi Dannau ya ratso yana ta keta dariya yana sanye da munanan kayansu na tsafi ya nufo inda suke yanata cigaba da dariyarsa abinsa.
Jaru ta shiga gaban uri tayi banga banga cikin razana iro ya tambaye wanene wannan?

Ta amsa masa cikin murya kasa-kasa batareda ta dauke idonta daga kan matsafin ba. Shine Jauje da nake shaida maka
Awannan lokacin sai Jauje ya tsaya kyam yana mai zazzaro idanu dariyar dake fuskarsa ta bace babu abinda yayi saura a fuskar sa mai muzurai mai ban tsoron gaske.

Ba zato ba tsammani sai ya sheka ihu ya daga dan kulkin dake hannunsa sama yasake sheka ihu sai ni Jauje na Dannau mai danne mutum ya zam turbaya tsafi ba haye bane gado ne sai ni na Dannau mai danna bawa barzahu kududdufin barkano iyakacin mace gwiwa yayi ihu yayi karaji ya sake yin kirari sannan ya dubi iro cikin zazzare ido yaro ka shafawa kanka ruwa tun kafin na zaike maka da ajalin ka ka rabu da jaru tun muna shaida juna wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa in kuwa kaki na shayar da jinin ka ga GUNGUME sarkin aljanu dan damtsen uwan nan...

Jaru tana gaban iro ta babbake cikin tsoro iro yasa hannu ya janyeta suka yi gaba da gaba da Jauje..

Wusss karyar ka ta sha karya makaryacin banza ya tunkari Jauje gadan gadan koda kuwa kana tsafi ne da bakar jaɓa ni na sha gaban ka naci na sha ba domin ka ba.

Jauje ya kece da dariya yaro kada ka kinkimo wa kanka dala ba gammo babu wanda zaiyi tarayya dani akan jaru batareda naga bayan sa ba mutuwar ma a gareni wani dan kankanin aiki ne da bai wuce jan numfashi ba ina sauran Masoyan nata? Bayan duk naga bayan su ballantana kai karamin alhaki dan damtsan uwan nan..

IRO ya nufi Jauje a fusace kafin yaje garesa sai Jauje ya buga layar zana iro ya shiga waiwayen inda zai ga Jauje babu Jauje babu alamunsa.

Kai matsoracin banza matsoracin wofi irin taka jarumtar kenan ka fito fili in ba tsoro ba ka fito fili in ka isa ka gani in ban nuna maka iyakar ka ba.

Sai yaji an sake rusa dariya Jauje yasake bayyana saidai wannan karon ya bulla ne acan da nisa ya cigaba da dariya wadda ta sake razana jaru ya waiwayo ya dubi iro kana ya daure fuska ya Mike hannu ya turbune fuska ai kamar wasa sai ga wuta ta kama gadan gadan wutar ta mike ta nufo iro. Iro ya kurawa wutar ido.
A inda iro yake mahada ce wadda ta kunshi ta kowace hanya saiga wuta ta nufo shi gadan gadan yayi ta duban wutar yayinda take matsarsa cikin tsananin sauri tana ritsa shi sai yayi alkafira yafadi can gefe guda yayinda wuta ta kama daidai inda ya bari.

Jaru ta kwalla ihu cikin firgita ta zaci wuta ta kama iro.

Da Jauje yaga ya haye wannan tuggun sai yayi wani irin ihu Jauje ya sake bulbula dariya kana ya bace jin kadan ya sake bayyana yana keta dariya yaro wannan abinda nayi maka ba komai bane face Gargadi dan damtsen uwa kada ka Kuskura na sake ganin ka da jaru in na sake ganin ka to ka tabbata kwanan ka yakare. Ya sake rusa dariya sannan ya bata.

Jaru ta nufo inda yake tana haki iro ya waiwayo suka dubi juna.
IRO kaga abinda nake shaida maka ko? Kayi hakuri kada na zama sanadiyar mutuwar ka ta fashe da kuka.

IRO ya isa gareta ya dafata kiyi hakuri mana banason Naji kina karaya akan wannan sha'ani namu me akayi akayi Jauje? Ni nayi miki alkawari sai naga bayan sa saboda haka kada ki damu halaka Jauje ne kadai tukuicin da zan iya tabbatar miki da cewa babu bai iya baki bacin ni.

IRO wallahi tsorona daya kada ka mutu ta dalilina bana son duk wani Masoyina ya mutu ta dalilina.
Mutuwa dalilin soyayya gado ce ga masoya in har bazan iya sadaukar da raina ga masoyiyata ba menene amfanina balle akan wani azzalumin matsafi kinsan Allah ni mai iya yin yaki da Jauje ne kodon na kwatar miki yancin ki balle yin yaki don na mallaki masoyiyata.

Ki ajiye wannan a zuciyar ki kodon gaba ni iro nine ajalin Jauje.

Suka dubi juna na dan wani lokaci
Sannan tace IRO INA SONKA.

Nima inason ki jaru
Sukayi wa junan su murmushi kana suka juya suka tafi.

BABI NA HUDU 4

Jabiru na gida yana kintsa wasu kaya lokacin da yaji sallamar iro ya Amsa shigo mana iro ina ciki.

IRO ya shiga ya nufi inda Jabiru yake
Har ka dawo?
Ehh na nadawo ya janyo wata tabarma dake jingine ya warwareta ya zauna dawowata kenan
Sannu da hanya ya tsagaita da aikin yayin daya dube shi kaka dai? Inafatan dai an dace.

Ehh to naje na same ta ya gyara zama mun zanta da ita akan al'amura da dama.

Kace an dace kawai.

IRO yace don dacewa an dace saidai akwai wata matsala ta daban ashe dai ba banza ba zuzzukewar da jaru takeyi aduk lokacin dana tuntube ta da maganar aure ko kuma na nemi ta amince nakai mata ziyara ashe wani shedanin matsafi ne a kauyen nasu ya hanata auruwa har ya kashe manemanta biyu kai in takaice maka labari dai Ayau din nan munyi arba da juna har yayi min kurarin in ban rabu da ita ba saiya halakani har ya ma nuna min ire iren takadarcin daya gada daga mahaifinsa.

Ahalin yanzu Jabiru ya tsagaita da abunda yake yi yana sauraron iro.

Haba ni nasan ruwa baya tsami banza yadda yarinyar nan naga ta girma da mamaki ace batayi aure ba in ba da wani dalili ba.

Sukayi shiru zuwa wani dan lokaci sannan ya dubi iro yace...

GANGARIYA KAIMA KAYI SHIRU ANAN NA DAN WANI LOKACI..
SIHIRTACCE-06

Sukayi shiru zuwa wani dan lokaci sannan ya dubi iro yace.
To amma mecece shawarar ka gameda sha'anin?
Iro ya dube shi ai ni tuni ma har na shaida mata cewa babu gudu babu ja da baya duk da kisan manemanta biyu dayayi na gaya maka har musanyan yawu munyi dashi har ma ya soma yi min wasan wuta don ya razani amma duk abanza hasalima na kuduri aniyar yakarsa da duk karfina da dabarata.
Jabiru ya gyada kai dakyau Naji dadi da baka karaya ba wannan ne dalilin dayasa nake kaunarka iro inda duk ake neman jarumi ka kai a matsayina na amininka zanyi kokari na baka duk Gudunmawar da zan iya don ganin ka rinjaye shi.

Nagode Jabiru wannan shine yasa nake takama dakai akoda yaushe kaine amini abin dogaro wanda aduk lokacin dana shiga wani hali zan iya sa rai da Gudunmawar ka nasan zaka taimaka min daidai gwargwadon karfinka don ganin nayi nasara akan wannan matsafin dake shirin shiga tsakanina da jaru.

Jabiru ya taimakawa iro da abubuwa uku watau layar zana gurun karya makaru ko tsafi da kuma maganin karfe
Ka rufa layun da gurun koda yaushe ka kasance dasu hakanan zan gargade ka kada ka Kuskura ka shiga KOGON DUTSE yin haka zaisa ayi galaba akan ka.

Da haka yaci gaba da kaiwa jaru ziyara sau biyu a mako banda gamuwar da suke yi a kasuwa.
Tun jaru na fargaba har ta soma sakin jiki a kowane mako yakan je sau daya ko sau biyu suyi tadin soyayya in yaje takan fito masa da damammiyar fura mai zuma wadattaciya wasu ranakun in baza'a je kiwo da nisa ba jaru ke fita da shanun gidansu iro yakan rakata kiwon suyi tadinsu acan bayan gari.

Saida suka sha'afa tukunna bayan wata biyu rannan yazo sunyi hira ta raka shi zai koma gida sun baro rugar bello da yar tazara sai sukaji an barke da dariya ta gauraye gaba daya jejin iro da jaru suka tsaya suna waiwaye-waiwaye jaru cikin tsoro iro cikin mamaki.
Bayan an dauki wani dan lokaci ana dariya sai hayaki ya bulla a gabansu kafin kace menene wannan gogan yafito ta cikin hayakin nan take ya kaiwa iro sura suka kaure da kokawa ya daga iro ya raba da kasa zai kayar iro ya dire shima ya cira Jauje zai kayar shima ya dire suka sake cakune juna suka fadi kasa rikica.
Jaru ta bisu cikin razana yayinda suke mirgina mirgina Jauje ya fiddo wuka ya cira zai dabawa iro amma iro yayi dace ya cafke hannun mai wukar sukayi yar gwajin kwanji lokacin da iro ya mirgina ya turmushe Jauje ya danne hannu mai wukar sannan ya danne hannunsa ya kirba masa naushi a fuska.
Nan take Jauje ya bata.
Iro yayi zumbur ya Mike tsaye yana sanda yana waiwaye yana ja da baya sai Jauje ya bullo ta bayan sa zai soke shi da wuka jaru wadda ke kallon abinda yake faruwa tayi kara. Iro ya waiwayo cikin hanzari ya kaiwa Jauje sura ya sake bacewa can sai iro ma ya tuno da tasa layar da Jabiru ya bashi nan da nan ya lalube ta ya matsa shima ya bata habawa ai nan take fada yakoma na shaidanu ba'a ganin mutane sai naushi kawai akeji saidai in sun bangaji karamar bishiya kaga tana rangaji ita kadai suka dauki lokaci suna gwabzar fada jefi jefi sukan dan bayyana sai su sake bacewa. Daga karshe dai sai kawai suka fito duk sunyi wujiga wujiga dasu.

Jauje yayi girgiza sai ya zama bukka iro ya zaro gurunsa ya tafkawa bukkar nan take Jauje ya sake bayyana yau sake yin girgiza yazama ruwa iro ya tsulawa ruwan guru Jauje ya sake bayyana yazama kura abanza guru ya tashe shi yazama dutse iro ya sake dawo dashi hayyacinsa da guru.

Da dai yaga rikidar daya saba yi taki yin tasiri sai ya runtuma aguje iro ya bishi sukayi ta gudu ta cikin ciyayi da bishiyoyi da duwatsu hardai ya cimma Jauje yakai masa cafka ta baya.

Jauje ya rikide ya zama hayaki iro ya shiga cikin hayakin yayi ta tsula masa guru adaidai lokacin da jaru ta iso wajen tana leken abinda ke faruwa.
Can kuma sai sukaji dariya ta kaure jejin iro ya shiga kasa kunne yana so yaji inda dariyar ke fitowa can daya jiyo saiya nufi wajen.

Iro ka tsaya kada kaje... Kada kaje..
Ya daga mata hannu ma'ana kada ki damu ya nufi inda dariyar ke fitowa jaru ta fito aguje ta kwalla masa kira amma ina! Kafin ta isa garesa tuni ya isa inda dariyar ke fitowa wani Kogon dutse ne bai saurari kiran da takeyi masa ba sai kawai yasa kai ya shiga Kogon itama tabi shi abaya shigarsa keda wuya sai ya daina jin dariyar.

Kogon na da girma ainun a rataye ako ina ajikin bangon tarkace ne iri daban daban na tsafi wajen na da ban tsoro iro wanda haryanzu yana rike da guru ahannu ya soma takawa ahankali cikin sanɗa da lura yana rarraba ido inda zai ga ko yaji motsin Jauje.

Daga rufin Kogon saiyaga wani sirrin haske ya keto kamar hasken rana ya kura masa ido zuwa wani dan lokaci kana ya kawar da kai ahankali ya cira kafa zai ci gaba da sanda saiyaji hasken ya janye gamida wata irin kara ya yi firgigi ya sake waiwayowa ya dubi gurbin da tun asali hasken yake arazane.
Bayan wani dan lokaci saiya daga ƙafa zai ci gaba da tafiya yaji adaidai kansa wasu duwatsu gamida kura sun zubo yayi sauri yayi baya. bayan da yaga rubdugun duwatsun ya lafa saiya gewaye ya nufi cikin Kogon yana cikin tafiya da sanda saiya iso wajen da wani ruwa yake a gabansa.

Jaru ta iso ga Kogon ta leka ta hango iro can yana tafiya ta kwalla kara amma ina karar bata yi amfani ga iro ba.
Wani mulmulallen abu ya sulalo daga sama ya gwabji iro har saida yafadi adaf da ruwan nan kiris ya rage yafada ciki ya dogare hannayensa kana ya juyo a firgice ya dubi abinda ya doke shi mulmulallen abun nata reto abinsa ya yunkura ya Mike ya gewaye mulmulallen abun a rankwafe.
Wannan karon da iro yaji kuwwar jaru sai yayi ta maza ya goce cikin azama sannan ne yaga ashe lamarin ya fi karfin gocewa wani katon dutse ne ya nufo shi zai murkushe shi ya juya aguje ya fita daga Kogon.
Sannan yaji dariya ta sake cika jejin Jauje ya bayyana a gabansa yana dariya rike da wata yar butar duma iro yayi kukan kura yayi kan Jauje sadidan zai afka masa Shu'umin na rike da butar duma bai jira komai ba sai ya tsiyaya masa ruwan butar ajikinsa iro yayi cak. awaje daya kana ya rinka curewa ahankali kafin kace wuri tuni ya zama SHURI
JARU TA KWALLA KARA HAR JEJIN YA AMSA.

NA SADAUKAR DA WANNAN KASHI NA SHIDA 6 KACHOKAN DINSA GA MACE DAYA TILO DAKE SHIRIN AZABTAR DA ZUCIYATA TA HANYAR YAKICE NI DAGA RAYUWAR TA 😢 😭 😭 😭

KU TAYA NI LALLASHIN TA IDAN KUNA SON NA CIGABA 😭 😭 😭SIHIRTACCE-07

Shu'umin na rike da butar duma bai jira komai ba sai ya tsiyaya masa ruwan butar ajikinsa iro yayi cak. awaje daya kana ya rinka curewa ahankali kafin kace wuri tuni ya zama SHURI
JARU TA KWALLA KARA HAR JEJIN YA AMSA.

BABI NA BIYAR 5

An shiga rana ta biyu tun tafiyar iri kauyen su jaru bai dawo ba wanda hakan ya tayar da hankalin iyayen sa da abokin sa Jabiru aranar farko Jabiru bai damu sosai ba amma da aka shiga rana biyu tun dare ya kasa barci saboda zulumi da kai kawon zuci. Musamman saboda sanin acikin hatsarin da iro din yake gameda Jauje dan sarkin tsafi.

Ga dukkan alamu sunyi arangama da Jauje kodayake baya son tunanin da zuciyar tasa ke yi masa amma ko shakka babu yasan ba lafiya ba duk inda iro yake ahalin yanzu yana cikin wani hali.
Bayan an idar da sallar asuba sai ga TALLE kanin iro ya zo ya same shi a kofar daki a zaune yana lazimi yaron yayi sallama ya durkusa ya gayar da Jabiru.
Baba ne ya turo ni yace nagaya maka wai yana son ganin ka kafin Kafita kasuwa.
Lafiya dai Ince ko?
Talle yace Nima bansani ba yace dai kaje.
Jabiru yace masa to kace gani nan zuwa.

Baiko karya kumallo ba yana idar da lazimi sai ya shuri takalmansa yafita bai zame ko ina ba sai unguwar ya isa gidan yayi sallama ya shiga daga zaure.
MALAM MAMMAN mahaifinsu iro ya daga murya Jabiru ne? Muryar na fitowa ne daga dakin cikin zaure.
Eh nine baba.
To shigo mana ina ciki.
Jabiru ya cire takalmansa yayi sallama ya shiga baya ganin ko tafin hannunsa saboda duhu ya durkusa suka gaisa acikin duhu kafin su kammala gaisawa idonsa ya soma zama jiki da duhun dakin.
Malam Mamman na zaune ne akan wata faffadar tabarma yana sanye da wata farar babbar riga kansa da rawani ga wata katuwar casbaha ahannunsa.
Jabiru..
Na'am baba..
Kaka mahaifin naka? Kwana biyu bama gamuwa a kasuwa.
Yana nan lafiya lau sarkin dawaki ne ya aike shi Zamfara yau kwana uku da tafiyarsa.

Dama dalilin dayasa na kira ka saboda abokin ka tun shekaranjiya da hantsi daya bar gidan nan da sunan zashi unguwa har yau bai dawo ba hankalin mu yayi matukar tashi baran ma mahaifiyarsa don jiya ko abinci bata iya ci ba dalilin dayasa na kira ka Daman don naga yadda kuke ne mai yiwuwa bazaka rasa sanin inda ya je ba ko Allah yasa kafin ya tafi ya gaya maka inda ya tafi.

Jabiru ya gyara zama da gyara gyatta hularsa ba shakka yagaya min ni kaina jiya ina cikin tashin hankali da yawan zulumi saboda tunanin rashin dawowarsa wani kauye yaje dake yamma da kasuwar dausayi ana kiran kauyen TSAMIYAR KARA daman kuma yana zuwa saidai bai taba kwana ba.
Malam mamma ya cika da mamaki to amma me yake zuwa yi shi kuwa?

Gaban Jabiru yafadi don bai taba tunanin iro bai sanar da maganar jaru a gidansu ba.
Yanzu kaka za'ayi Jabiru? Dattijon ya tambaye shi.
Baba ai Daman ni tun jiya nayi niyyar yau zan bi sawun sa don naga ko lafiya.
To zan hada ka da TASI'U da HALADU su taimaka maka me kuma kake bukata?
Bana bukatar komai baba
To ko baka bukatar komai dai na hada ka da tasiu da haladu ku tafi tare mai yiwuwa ka bukaci taimakonsu.
A'a baba ka kyaleni ni kadai ma na isa..

****** ******* ****** ******* ******* **************

Da hantsi ya dauki hanya akan dokinsa tayi tafiya ta kimanin sa'o'in uku kafin ya isa kauyen tsamiyar kara ya isa rugar Bello da azahar yayi sallama ga wasu samarin Fulani su biyu dake zaune a gindin bishiyar dake farkon rugar suka amsa cikin mamaki suna duban mahayin.
Ya sauko daga kan dokin don Allah tambaya nakeyi.
Daya daga cikin su ya dube shi Allah yasa mun sani
Ko nan ce rugar Bello?
Kwarai kuwa Modibbo inji dayan harshensa akwai alamun fillanci.

Jabiru yace don Allah jaru nake nema aiko ni akayi wajenta daga birni.
Ya dubi Jabiru cikin sauyin murya yace BIRNIN DABO?
Eh inji Jabiru saurayin nan dake da bafillacen harshe ya Mike tsaye
Wa za'a ce mata?
Kace mata jabiru ne abokin Iro.

Ya ratsa yan maruƙa da suka saura agida ya shige jin kadan saigashi yafito tana zuwa..

Yawwa Alaraini nagode fa.

A'a babu komai ya dubi dan uwan nasa HAIDO taso muje dandali kaji ya mike ya bishi suka tafi.

Bacewar su keda wuya sai gata Tafito ta dubi Jabiru bata shaida shi ba da fari saida ta matso kusa sannan ta shaida shi.
LA.... Kaine dama?
Jabiru wanda ganin jaru akullum ke sanya zuciyarsa dakan uku uku yayi murmushi.
Nine Jabiru.

Ina zuwa takoma ciki lokacin data sake fitowa sai gata dauke da karauni ta shimfida masa a gindin bishiya takoma ta kawo masa fura damammiya da butar kasa yasha fura kana yayi sallah sannan suka gaisa.

Jabiru yace naga alamar kamar ma bakiyi mamakin ganina ba.
Eh banyi mamaki ba Daman ina jiran zuwan wani daga cikin ku.

Yaji gabansa yafadi kina nufin iro yazo kenan?

Yazo shiyasa ma banyi mamakin ganin ka ba ta dubi zoben da iro yabata tun kafin ta sake yin magana sai hawaye ya soma zubar mata daga ido.
Jabiru yayi zumbur ya mike tsaye me ya faru jaru?
Taci gaba da kuka
Ko Jauje ne.... ?
Kafin ya karasa tambayar jaru ta gyada kai..
Yaji wani irin kunan rai ya bijiro masa nan da nan yaji gashin jikinsa ya mimmike idonsa ya kada yayi ja.. Me ya faru? Ya kashe iro ne?

Ta share hawaye tace ya... ya...MAYAR DA IRO SHURI.

Jabiru ya soma tsima shu..me? Da gaske koda wasa?
Na rantse da Allah ko ta share hawaye..
Jabiru ya sad da kai kasa cikin tunani zuwa wani dan lokaci sannan ya cira kai ya dube ta yace jaru..
Itama ta dube shi na'am
Zo ki rakani naga shurin.

Ta gyada kai eh saina rakaka bari na mayar da kayan nafito ta nade tabarmar ta dauki gidauniyar da butar Kasar ta shigar dasu gida bayan dan lokaci ta fito.
Mu tafi..

Suka ratsa ta cikin jejin tafiyar dan lokaci ta kawo su ga shurin Jabiru ya kurawa shurin ido cikin tafarfasar zuciya daga karshe ya dubi jaru Jauje!!!.....
Karyarsa ta sha karya Ayau din nan sai ya karya wannan surkullen komai kin Allah dinsa.

Jaru ta dubi Jabiru cikin kyautata fata amma zuciyarta cike da fargaba amma ba tunkarar Jauje Zakayi ba dai kaima ko?
Ya zame min tilas na tunkare Shi.

Ta girgiza kai nidai na gaji da dauke dauken rayukan nan haka don Allah kada ka tunkari Jauje ya halaka ka.

Jabiru yayi huci daga yau ya kare daukan ran kowa babu wanda zai taba min aboki ya kwan lafiya.
Jabiru kada fa ya kashe ka kaima..
Bazai kashe ni ba bakuma zamu yi ragas ba yau karshen sa yazo komai tsafinsa.

Ta fuskanci Jabiru don Allah don Annabi kayi hakuri kaga iro ma haka ya dage babu yadda banyi dashi ba yace saiyaga bayan Jauje.

Jabiru yace ki kwantar da hankalin ki ni na san kaina nasan abunda zan iya da wanda bazan iya ba in har nasan bazan iya dashi ba bazan soma tunkararsa ba ki kaini inda yake kawai babu ruwan ki.

Dayaga ta dage saiyace to in bazaki kaini inda yake ba kiyi min kwatance.
Tayi shiru cikin tunani sannan daga karshe tace SHIKENAN ZAN RAKA KA.

****** ******* ****** ******** ********* ***********

Tana Gaba yana biye da ita abaya rike da ragamar dokinsa ta waiwaya ta dube shi nan ne jejin.
Jabiru ya dubi jejin inane gidansa?

Bansan gidansa ba Nima sau tari adaidai nan yakan bayyana adaidai nan ya bayyana alokacin da muke tareda Iro.

Jabiru ya sake duban jejin a tsanake sannan ya kwanto wata jaka dake daure ajikin sirdin dokinsa ya budeta ya fiddo da wasu guraye da layu harda kambu cunkusss ya zuba su akasa sannan ya fiddo da wani kunshi awani kyalle ya tsugunna ya dauki gurun ya daura a kugu ya rataya kayan ya sanya kambun sannan ya koma ga dokin ya kwanto takobinsa wanda rabon da ya yi amfani dashi tun gwabzawar su da jama'ar sarkin gaya lokacin basasa yakai dokin ya daure ajikin wata bishiya.

Duk wannan abinda akeyi jaru kallonsa kawai takeyi taga ya debo wasu duwatsun wuta guda biyu da yar guntuwar auduga ya tattara kana ya murza audugar ya buga duwatsun yatashi wuta ya debo garin maganin yasa acikin wutar hayaki ya tashi ya turnuke a gabansa.
Can jimawa sai dokin Jabiru yayi hayaniniya Jabiru ya cira kai ya dubi jejin cikin harzuka sannan ya soma jiyo ihu acikin jejin idanuwansa suka kada sukayi jazur kamar garwashi.
Jaru na dubansa saita ji cikinta ya kada Jabiru ya canza gaba daya kamar ifritu ta bishi da kallo yayinda ya soma yin takun jarumta cikin gwaninta

Hayaki ya tashi a gabansu Jauje ya bayyana ta cikin hayakin menene ake kirana kuma wane ne yake kirana? Yana sanye da warki da kayan tsafi rakwacam.

Ubangidanka ne yake kiran ka.
Ya dubi Jabiru wanene ubangidana?

Baka bukatar a baka amsar daka jima da sani.

Jauje yayi huci yace.......SIHIRTACCE-08

Ubangidanka ne yake kiran ka.

Ya dubi Jabiru wanene ubangidana?

Baka bukatar a baka amsar daka jima da sani.

Jauje yayi huci ni Jauje gadon tsafi ni kududdufin barkono iyakacin mace gwiwa ni marucin kan dutse dan Dantsen uwan nan.

Kai makaryaci Jabiru ya daka masa tsawa yau duk wani kurari bazai kai ka ba da maza kake magana ba mata ba ka amsa bukatata

Please Login or Register in order to submit comment