Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masoyiyata kizo mu koma duniyar mu ta gaskiya..

Ta isa gida kamar ranta zai fita don haki da fargaba ta zarce dakin mahaifiyar ta tana ta haki ta hada gumi kashirban.

Mahaifiyarta na zaune tana kallon talabijin.
Hajiya! Hajiya!
Hajiya ta mike a firgice menene?
Ta rungume mahaifiyarta cikin Faduwar gaba.
Mahaukaci ne ya biyo ni mahaukaci....
WANNE irin mahaukaci?
Mahaukaci ne ya biyo ni Lillibe ni hajiya.
Ke don Allah rufe min baki bana son sakarci...
Wayyo Allah... Hajiya......

BABI NA TAKWAS 8SIHIRTACCE-11

BABI NA TAKWAS 8

Jaru ta farka can dare misalin karfe biyu amma bata mike daga kwance ba. Tun lokacin da ta tserewa mahaukacin nan tazo gida a firgice har magariba bata samu nutsuwa ba hasalima abincin dare bai ciyu ba agareta sai wajen tara da rabi tayi sallolin da ake binta bashi kana taje tayi wanka bata kuma yiwa mahaifiyar ta maganar ba don ta fahimci ba yarda zatayi ba tayi godiya ga Allah daya tserar da ita daga mahaukacin nan.
Tun lokacin data soma bacci sai yanzu ta farka saidai taji kamar tashinta akayi daga barcin ita kadai ce ke kwana a dakin Daman gata da tsoro kamar farar kura wanda hakan yasa batayi bacci ba saida ta garkame kofar aranar.

Ahalin yanzu tun farkawarta jikinta yabata cewa akwai wani a dakin to amma tayaya mutum zai shigo dakin yayinda yake a kulle ta dubi kofar ta ganta a kulle.

Jaru taji muryar mahaukacin na fadin Jaru karo na biyu.
Hantar ta ta kada yayinda ta mike zaune ta soma waiwaye cikin firgita.
Kada ki firgita nine iro masoyin ki iro.
Muryar na magana ne acikin rada. Ki tuna da irin soyayyar dake tsakanin mu jaru kin rigaya kinsani bazan cutar dake ba nazo ne na dauke ki mu koma.
Jaru ta kwalla ihu a firgice mahaifiyar ta da yayan ta MAMUDA suka kawo dauki.

Jaru menene inji mahaifiyarta.
Mahaukacin nan ya shigo cikin nan.
Mamuda ya doki kofar da kafada da karfi sau uku ta bude suka shiga.
Menene? Mahaifiyarta ta tambayeta.
Mahaukacin nan ne na dazu ya shigo nan dakin ta takure awaje daya kamar mai jin sanyi.
Mamuda ya tambaya ke bama son iskancin banza.
To ta ina yabi ya shigo? Uwar ta tambaya a kufule.
Wallahi ya shigo cikin dakin nan hajiya bansan yadda yayi ya shigo ba.
Ya kunna fitila babu kowa acikin dakin.
Kikace yana cikin dakin inji hajiya ina yake?
Mamuda yace hajiya karya takeyi babu kowa aciki.
Wallahi saidai in fita yayi hajiya.

Rufamin baki yar banzar yarinya ki koma ki kwanta banason shashancin banza don iskancin banza saikin tayar da makwabta daga bacci tukunna?
Ta kyakkyabe baki ni wallahi bazan kuma kwanciya ba ni kadai ba mahaukaci yazo ya kashe ni.
Mamuda yace hajiya ina ji gamo tayi saidai ayi mata rukiyya gobe.

******** ******** ******** ********* ***************

Kashegari da hantsi taje makaranta suna tare da sadiya take bata labari.
Jiya bayan kin ajiye ni wani mahaukaci ya bini wai nice masoyiyarsa harda nuna min zoben sa na gwal irin nawa yana cewa wai shi yabani wannan zoben ta nunawa sadiya.

Sadiya ta tuntsire da dariya kice kin caba.
Duk yarinyar data tsinci saurayi Awannan zamanin ai tafi kowa cabawa.
Ta harari sadiya mahaukaci ne fa.
To menene don mahaukaci ne mahaukaci ba mutum bane?
Baki gani ba fa har daki ya bini da tsakar dare.
Sadiya ta cika da mamaki cewa yayi ya sanki?

Jaru tace eh har sunana ya kama.
Ke kar dai SIHIRTACCEN SHURI nan ne ya tashi kinsan dama dakta labaran yace zai ga wata yace ya santa gashi dama shurin a garin ku yake.
Ke don Allah bana son iskanci wannan tatsuniyar zaki saurara kuma koda gaskiya ne ma ai shurin ba'a garin mu yake ba a gunduwawa yake.

Kikace yace shine yabaki zoben gwal din nan dake dan yatsan ki?

Haka yace mana mahaukacin banza.

To in bashi yabaki ba ke tayaya akayi kika same shi.?
Jaru ta harari sadiya hajiya ce fa ta bani itama gadarsa tayi daga wajen KAKARTA.

Ke zo muje wajen dakta labaran muyi masa bayani duk yadda akayi shurin nan ne ya biyo ki.

Ke bana son iskanci kinji ko sadiya.

Wallahi da gaske nakeyi cewa yayi fa shi ya baki zoben da babarki ta baki ke kuma kikace asalin zoben na kakarta ne.

Allah ya kiyaye ba zanje ba ta juya tayi tafiyar ta.

Sadiya tace ina zakije jaru?

Batareda waiwayo ba ta amsa dakin karatu zani in zakije kizo muje in bazaki ba Kisha zaman ki.

Sadiya tayi kamar bazata ba amma saboda tunanin rashin abin yi Saitace tsaya ni mu tafi ta daga ƙafa ta bi Jaru.

JAUJE.....
JAUJE kuwa ya rikide ne daga shuri ya zuwa mutum kwana biyu bayan tashin iro.

Adaidai lokacin daya bayyana saida yayi mummunar razana musamman saboda ganin irin yanayin.

Ya Mike ya soma yan dube dube cikin rarraba ido bai dauki wani tsawon lokaci ba yaji ajikinsa cewa lallai a sabon zamani yake lallai Jabiru ya kwarara masa ruwan butar nan ta duma kenan.

Babu shakka ahalin yanzu yana shekaru dari shudaddu daga zamanin sa wanda hakan ke nufin sauyin mulki sauyin al'adu da sauyin mutane shin koma harda sauyin harshe ne?

Shekaru dari ba kwana dari bane..

Ya nausa yayi yamma saida yayi doguwar tafiya sannan ya soma hango abubuwan MAMAKI.SIHIRTACCE-12

Ya nausa yayi yamma saida yayi doguwar tafiya sannan ya soma hango abubuwan mamaki gine-ginen gidajen sama ne suka fara yi wa idanunsa barka da zuwa sannan wasu irin halitta dake kan wata irin bakar hanya sai tsere sukeyi ya rinka matsawa ahankali har ya isa kusa dasu ai kuwa daya lura saiya ga mutane acikin abubuwan nan na mamaki.

Jauje ya kece da dariya ya kyakyata ya sake kyakyatawa dan Dantsen uwa shekaru dari kenan?

Haka kanon ta zama kai yau naga abun mamaki.
Ya Mike yayita tafiya har ya zo wata dangar karfe mai kama da tubkar ragaya anyi mata wata kofa mai girma ita ma ta karfe sai kawai ya danna kai ciki. Baiyi nisa ba yaji ana daka masa tsawa ya waiwayo kana ya tsaya kai mahaukacin banza ina kake zato zaka daka biyo nan? Mutumin kato ne yana sanye da wata doguwar riga fara da rawani sai duban Jauje yake yi sama da kasa.

Jauje yace cikin gari zani..
Mutumin ya Harare shi nan ce hanyar zuwa cikin garin? Kai wanne irin bagidaje ne da bai iya ko karatu ba ya nunawa Jauje wani dan allo mai dauke da zanen gunkin kwarangwal da kafafu baka ga an rubuta HATSARI KAUCE bane sai kaje ka mutu abanza a wofi ka janyo min Salalan tsiya ace na kasa aiwatar da aikina.

Jauje yace toh kayi hakuri...
Ni kada ka bani hak'uri kaji fita kasan inda ka nufa in har ka bar nan kaje koma inane ka haka rijiya gaba dubu kafada ka mutu ba abunda ya dameni bane.

Bayan Barinsa wajen mafadacin mutumin nan saiya biyo gefen bakar hanyar nan Abu na farko daya fara fahimta shine haryanzu hausa din dai da akeyi a Kano bayan shekaru dari yana tafe yana Kalle Kalle yana rayawa aransa lallai da bai zo wannan zamanin ba da yayi hasarar zuwa duniya.

Ahankali yana tafiya har ya soma shigowa mutane. Mutane sai kallonsa sukeyi kamar sunga mahaukaci yasan shigarsa ce tasa suke bin sa da kallo in kuwa baiyi hattara ba bada jimawa ba zai tara yan kallo saboda haka yana yin gaba kadan saiya yi layar zana ya bace.

Ahaka yayi ta tafiya mai tsaho har ya isa cincirindon mutane gasu birjik ga dukkan alamu kasuwa ce ga irin karafan nan da mutane ke shiga tuli awajen sai yanzu ne ya fahimci ashe wadannan karafan ababan hawa ne dangin su rakumi da jaki da doki da makamantansu bambanci su daya ne wadannan basu da rai kuma suna diban kaya da mutane masu yawa alokaci daya kana ga kafirin gudu kamar damisa.
Awajen akwai wata makekiyar katanga mai katuwar kofar dake da maka-makan tagwayen ƙyamare wasu mutane sun gindaya igiya a kofar suna tare Zunduma Zunduman karafen nan da dukkan alamu suna karbar haraji ne.

Jauje ya shiga ya tarar ciki a cunkushe take da irin wadannan karafan haka nan akwai dakuna aciki masu Kunshe da kaya iri iri na sayarwa mutane mazan su da mata suna ta kai kawo sun yi shiga iri iri tufafi masu yawan launi dake da wuyar fasaltuwa duk da haka akwai wasu wadanda ke sanye da manyan riguna da hula wasu jamfa da wando kai harda masu yar shara.

Da ya matsa gaba kadan saiya hangi wasu acikin wani budadden masallaci suna sallah.
Washhhh kai ashhha! Ashe haryanzu mutanen nan basu bar irin wannan al'adar ba.?

******** ******** ******** ******** ********** *****

Iro ya hango su daga inda yake zaune a gindin bishiyar dake daf da gidan ya hango su nufo gida ya shaida jaru itace mai sanye da korayen kaya ya Mike tsaye ahankali jaru ta yi sauri ta rike hannun sadiya ta dube shi daga inda suke sannan ta waiwaya ta dubi jaru zo muje gunsa.
Jaru tayi ajiyar zuciya Allah ya tsare in ina son ganinsa inason mutuwata kedai kikace kinji kin gani to bismillah.

Sadiya tayi karfin hali tace jirani ina zuwa ta nufi inda yake tsaye yana dubanta kawai acikin mamaki.

Ta isa gareshi tayi karfin hali tace bawan Allah sannu da warhaka.

Yawwa baiwar Allah Sannun ki ya amsa mata don Allah in bazaka damu ba na tambaye ka mana.

Ya gyada kai bazan damu ba mecece tambayar taki?
Ta waiwaya ta dubi jaru kana ta dawo da kanta ta sake dubansa shin ko zaka iya shaida min sunan ka da kuma garin daka fito?

Yayi kokarin boye mamakinsa sunana Ibrahim amma an fi sanina da iro kuma daga birnin Kano nake.

Menene hadin ka da waccan da kake binta?

Iro yayi ajiyar zuciya jaru kike nufi? babu shakka kinyi tambaya budurwar tace wadda nake da burin aure akwai wani matsafi mai suna Jauje shine ya shiga tsakanin mu ya sihirce ta yayi mata surkullen da ta kasa shaida ni don kawai ya rabani da ita sadiya ta kura masa ido cikin mamaki.

Sannan iro ya tambaye ta don Allah ke kuma wacece kuma menene gaminki da jaru?

Tace ni sunana sadiya jaru kawata ce tun muna yan kanana.

Ya tsuke ido cikin mamaki kaka akayi bansan ki ba in har ke kawarta ce.

Eh ba lallai ka sanni ba amma tare aka samu a makaranta da ita.

Iro yayi dan tunani zuwa wani lokaci to don Allah ko zaki taimaka min ki shawo min kanta afff ashe fa sha'anin ya fice haka.

Sadiya tace bai wuce ba zan iya taimaka maka amma fa akwai sharadi.
Wanne irin sharadi ne fadi Naji.
Sharadin shine saika daina tsorata tukunna.

Tsorata ta? Yace cikin mamaki.
Eh zaman da kake yi ahanya in ta ganka tsorata takeyi.

Yayi ajiyar zuciya kaka zanyi kenan?

Abu mai sauki ka daina tsare mata hanya don kaga ahalin yanzu ta dauke ka mahaukaci.

Mahaukaci... Idanunsa suka fito ruku ruku nine mahaukaci? Lallai Jauje ya cuce ni yanzu har ya juyawa jaru tunani ta dauke ni mahaukaci ya share kwalla daga idonsa Jim kadan saiya dubi sadiya kema Kin dauke ni mahaukaci ko?

Shi ne na shaida maka ka daina zama ahanya kana tsare ta yayinda ta taso daga makaranta ni kuma zanyi iya kokarina na fahimtar da ita ko kai wanene. Tayi shiru zuwa wani dan lokaci sannan ta tambaye shi bakada yan uwa ne agarin nan?

Banida kowa sai Allah sai ko jaru.

Toh Allah ya sauwake kana da kudi ne? kiris iro yace eh amma saiya tuna da kudinsa ya sha bamban da nasu saiyace A'a banida su.
Ga mamakinsa saiya ga sadiya ta bude Jakarta ta fiddo wasu takardun kudi ta mika masa ya mika hannu ya karbi kudin ya kura musu ido kana yabi sadiya da kallo yayinda takoma wajen jaru sannan yabar wajen ya koma can gefe daya ya tsaya yana kallonsu suka taho suka shiga gida.

Suna shiga cikin gida sai sadiya taja Burki ta waiwayo ta dubi jaru kinsan Allah jaru wannan ga mahaukaci bane.

Menene shi? Ta tambaya cikin gatse.

Sadiya ta kwantar da murya inama kinji lafazin sa da baki kira shi mahaukaci ba abin kawai da na fahimta wata irin hausa yake yi.

Ba wani mahaukaci ne yaya bansan mutun ba bantaba ganinsa ba zaice wai ni Budurwarsa ce wani dan kauye kucaki Irinsa.

Sadiya ta danyi tunani jaru nifa har yanzu ina fargaba musamman ma da yace kece budurwar da zai aura Naji ya ambato wani matsafi ne ya sihirce ki kika juya masa baya anya kuwa ba maganar dakta lab........

Zaki fara ko zaki fara ko?

To ai ni abin ne biri yaso yayi kama da mutum.

Kinsan Allah sadiya in kika kaini bango da wannan maganar komai nayi miki ke kika ja.
Shikenan Allah ya baki Hakuri

************ *********** ********* ********** ******

Jauje Ya Shiga shagon wanda ke cike da tufafi iri iri kyawawa da munana wasu mutum biyu suna ciniki da mai kayan Jauje wanda ke cikin baduhun layar zana ya ratsa ya shiga daga ciki ya zabi taguwa da wando da babbar riga masu kyau ya sace yafita bayan ya samu waje kebantacce ya cire tsummokaran jikinsa ya zubar ya sa sababbin ya saba jakar sa ya dauki hanya....SIHIRTACCE-13

Ya cire tsumokaran jikinsa ya zubar ya sa sababbin ya saba jakarsa ya dauki hanya.

Ahalin yanzu yana tafiya ne a bayyane dayake ya cire tsumokaran babu wanda ya damu dashi saboda yadawo mutum kamar kowa.

Yana cikin tafiya yunwa ta soma damunsa ya soma tunani me zai samu yaci Agefen titi a gindin wata bishiya saiya hangi wata mai sayar da abinci wasu suna zaune su uku suna ci akan wani irin abun zama mai kama da dakali daya iso wajen yayi musu sannu matar ta amsa.
Abinci kike sayarwa?
Tace eh abinci ne
Me da me? akwai tuwon shinkafa akwai shinkafa akwai tuwon masara.

Yayi murmushi akalla dai sunayen abincin duk basu sauya ba. Zubo min shinkafa ya zauna akan dakalin af... Ashe ma na itace ne.

Ta mike ta soma zubawa dame za'a hada salak ko makorani? ya dubeta su kuma kaka suke? tayi saroro tana kallonsa mutanen nan dake zaune sai yanzu suka soma dubansa cikin rudewa.
Daya lura da abunda ke shirin faruwa sai yayi sauri yace hada da abunda ya kamata duk daya ne ni awurina.

Har ta soma magana sai dai tayi shiru ta juya ta cigaba da hadin abinci ta hada ta mika masa yana karɓa saiyaga wani irin Ganye akai da tumaturi asama ya diba ya rike a hannu yana juya shi me ke nan wannan mai abinci Lansur ne.?

Mutanen nan suka dube shi a lokaci daya kana suka maida hankali ga abincin su amma suna saurare.

MAI abincin ta tuntsure da dariya yayinda tace malam kai kuwa wane irin mutum ne da baka san SALAK ba?

Haka fa sannan ya yaɓa hannu ya cakuda kamar kwado ya soma ci ya rasa kan irin dandanon da gindinsa amma dayake yunwa yakeji sai yaci gaba da ci haka.

Mutanen nan dake cikin abinci sun soma kallonsa cikin damuwa amma gogan ko ajikinsa bai ko damu dasu ba biyu acikinsu suka gama suka sha ruwa suka zaro kudi zasu biya to anan ne fa Jauje ya rama kallonsa yan takardun dayaga sun fito suna kidayawa suna mikawa mai abincin wadanda ya tabbata ana nufin kudi ne sunyi hannun riga da tarin WURIN dake cikin jakarsa.
Yaji daya daga cikinsu na cewa BANI CHANJI. Yayinda ya mika mata takardar.
Ya saurara yaga menene chanji saiyaga ashe wai RARA ce chanji mai abinci ta kidayo wasu iri da keda bambancin launi da irin tasa takardar kudin daya bayar ta mika masa jikin Jauje yayi sanyi watau a tsawon shekaru dari har an sauya kudi daga wuri ya zuwa takarda yaci gaba da cin abincin hankalinsa baya tareda shi.

Wasu mutane su biyu suka zo aka zuba musu abinci suka zauna adaidai inda mutanen dazu suka tashi suka soma tadin da Jauje ya fahimci sun dora ne akan wani tsohon hira da suka taho suna yi.

Naira.. Naira! Haba malam Ai itace mutum..
Ai fada ma bata baki kaji na gaya maka LEGAS kawai zamu tafi neman Naira koma samu muma mu dawo mu rama wulakancin da akeyi mana wulakancin mutanen garin nan ya ishe ni haka.
Ace in bakada kudi kare wannan ya fika.
Ni nasan baba Yamai dani saniyar ware ne don duk sauran yan uwana sunada kudi agidanmu fa dan autan mu saiya fadi magana abi in ni nafada ba za'a Kalle ni ba.

Abokina in fa mukaje Ikko din nan mukayi dace muka samo yan chanji da mun dawo in aka ga mun shigo gari saikaga ana tarihin rayuwar mu ko?
Kana shakka ne? Ai gani Zakayi kamar za'a bauta mana.

Jauje ya kurbi ruwa yana mai gyada kai watau wannan takardar sunanta NAIRA kuma itace abar nema Awannan zamani ba wuri ba ya soma yan waige waige yana tunanin ta yadda zaiyi ya gudu.

Ahalin yanzu mutane sun soma lullube mai abincin can siaya dauki numfashi ya Mike yayi gaba yana bayar da yar tazara saiya surfafa aguje.

Bayan ya baiwa wajen rata mai yawa sai ya tsaya yana haki yaci gaba da tafiyarsa yana kalle Kallen abun al'ajabi iri iri saida ya iso wani wajen cincirindon mutane sun baibaye wajen anata kida ya kutsa ya shiga saiya tarar ashe mai wasa da maciji ne ya cika da mamaki dayaga ashe haryanzu akwai masu irin wannan harkar.

Ya tuna da maganar mutanen nan masu cin abinci gameda takardar kudi da suka fara sanar dashi sunanta Naira ga dukkan alamu wannan zamanin zamani ne na kura tsira dana bakin ki zamanin da kudi ke mulkar kowa da komai Jauje ya gano sana'ar dazai yi nan take indai har wasan maciji zai ci Awannan karni to kuwa babu abinda zai hana sana'ar sa ci ya raya a ransa kai lallai da banzo wannan zamani ba dana zo duniya a baibai na koma a baibai.

************************************************

Sadiya tazo daidai inda iro yake kishingide idonsa a lumshe ya tada kai da Hannayensa tace iro.
Ya bude ido ahankali ya dubi inda muryar ta fito dayaga sadiya ce saiya Mike zaune yana murmushi sadiya ce..
Ta durkusa akusa dashi eh nice kana nan?
Eh ina nan
Suka gaisa..
Yaya mutumiyar dai? Ya tambaya
Jaru? Tana nan da taurin kanta yadda ka santa.
Don Allah kiyi kokari ki tuna mata ni.
Nima ina iya kokarina kullum ni kenan acikin addu'a ina rokon Allah.
Ta nazarci wajen a tsanaki kana ta dube shi iro wai ni kuwa na tambaye ka mana.
Allah yasa nasani.
A ina kake kwana naga duk lokacin dana zo nan saina same ka.
A ina kuwa zan in ba anan ba..
Duban da sadiya keyi masa ahalin yanzu na razana ne.
Anan fa kace kake kwana.
Kwarai kuwa ko kina jin zan iya nisa da jaru ne?

Sadiya tace gaskiya kana son jarun nan Ibrahim inama kowacce mace haka masoyin ta ke sonta amma in ba zaka damu ba zan so Naji labarin wannan soyayya taku asalin ta dakuma yadda gundarinta ya kasance.

Iro ya tambayeta jaru bata taba baki labari ba?
Ta girgiza kai bata taba ba ita da bata son ma nayi mata zancen ka.
Amma kikace ke kawarta ce tun kuna yara?
Ta gyada kai eh anyi haka amma nidai don Allah ka daure ka bani labari ko a gaggauce ne.

Iro ya gyara zama ya soma bata labari irin soyayyar su da jaru tun daga farkon haduwar su a kasuwa lokacin tana kai nono tareda yan uwanta.

Kai nono kasuwa fa kace ta tambaye shi.
Eh aduk lokacin da mukaje kasuwa acan muke haduwa.
Wacce kasuwa kenan?
Kasuwar DAUSAYI.
Ta nutsu sosai ita kuma daga wani gari take zuwa cin kasuwar?
Yace daga rugar su mana rugar malam Bello wai bata taba shaida miki duk wannan labarin bane?
Ko ta taba dai inajin na manta shin bayan kai ko akwai wani wanda ya taba sonta?

Eh kafin ni akwai mutum biyu buba da salele ai kinsan san su ko? Duk da sun mutu shaidanin nan ne Jauje ya kashe su matsafin banza.

Ta dubi zoben dake dan yatsan sa wannan zoben fa Ibrahim naga mai tsada ne.

Ya dubi dan yatsan sa na zinare ne guda biyu na saya akayi min nasa daya na baiwa jaru daya.

Sadiya ta saki baki taci gaba da sauraronsa alokaci guda kuma tunanin ta ya koma ga takardar da dakta labaran ya gabatar.
GASKIYA MAI KAMAR ALMARA SIHIRTACCEN SHURI.

Ibrahim ne mutumin da aka sihirce jaru ce tsatson kuma wadda tayi kama da asalin yarinyar da aka sihirce Ibrahim akanta to amma yaya zatayi ta wayar wa da jaru kai ta fahimci gaskiyar lamarin?

Ta dubi iro ina zuwa don Allah kafin ya amsa tayi zumbur ta mike da sassarfa ta nufi gidansu jaru iro ya bita da kallo bai ko iya bude baki ba balle yayi magana.
Tashiga gidan ta zarce dakin jaru ta same ta tana kwalliya agaban mudubi sadiya ta isa gareta ta zauna akusa da ita suna duban mudubi jaru inason don Allah nayi miki wata tambaya in har bazaki damu ba?
Jaru ta dube ta wacce tambaya ce?
Ta dubi zoben dake yatsan jaru wannan zoben dake hannun ki daga wajen wa kika taba ce min kin gaje shi ma?

Jaru ta cika da mamaki daga kakar mahaifiyata me ya kawo wannan tambayar?

Yaya sunanta.?

Jaru tayi kamar bazata amsa ba saidai ta jure tace sunanta JARU. Sadiya wai don Allah ina kika dosa ne da wadannan tambayoyin..?

Sadiya ta mike ta matsa nesa kadan da jaru sannan ta waiwayo ta dubeta yayinda ta dogara hannunta da garun dakin. KO KI ƘI KO KI SO ABUNDA ZAN GAYA MIKI GASKIYA CE TSAGWARONTA. Takardar da dakta labaran ya gabatar akanki ya TABBATA.

Jaru ta harari sadiya don tasan inda ta dosa da maganar me kike nufi..?

Ina nufin kece jinin matar da aka sihirce mutum aka mayar dashi shuri domin ta kece wadda aka mayarwa da sunanta aka kuma mallaka wa zoben daya bata saboda dimbin soyayyar sa gareta. Haka nan kuma ko ki so ko ki ki iro ne wanda aka sihirce aka mayar shuri saboda Tsantsar son mai sunan ki.
Idanun su suka hadu na tsawon lokaci jaru na huci tace ashe ban gaya miki cewa in kina son mu zauna lafiya ki daina hadani da wannan mahaukacin ba?

Sadiya ta sauke hannunta gaskiya in tazo dole ne a fade ta ni nasan a sannu saki gane shin iro mahaukaci ne ko kuwa ke da kika kasa fahimtar sa ce mahaukaciya.
ta fice daga dakin tabar jaru na binta da kallo.

BABI NA TARA 9

Sauran Jama'ar dake wajen sukayi shiru kamar ruwa ya cinye su kowa ya kuro ido cikin damuwa tuni wasu suka gudu daga wajen suna ganin Jauje ya mayar da yaron daya kira don yin gwaji ƊAN BIRI.
Tun farko ya shaida musu zai mayar da mutum biri ya kuma sake mayar dashi mutum.SIHIRTACCE-14

BABI NA TARA 9

Sauran jama'ar da ke wajen suka yi shiru kamar ruwa ya cinyesu kowa ya kuro ido cikin damuwa, tuni wasu suka gudu daga wajen suna ganin Jauje ya mayar da yaron da ya kira don yin gwaji dan biri. Tun farko ya shaida musu zai mayar da mutum biri ya kuma sake mai da shi mutum.

"Ku bani hankalinku mutane wannan saurayin dana maishe shi biri in kuka tsahirta min zan mai da shi mutum yanzun nan ba da jimawa ba." Jauje ya gewaya ya sake gewaya wa, yana wasu irin maganganu na surkulle, sai kallonsa kawai suke yi. Ya zo ya nuna birin nan da dan alinsa ya yi kuwwa kana ya ce "Koma mutum dan dantsen uwa."

A hankali sai biri ya soma rikidewa daga suffar biri ya dawo mutum kamar yadda yake tun asali. Jama'a suka ɓarke da tafi, fuskokinsu suna masu nuna alamar samun kwanciyar hankali, wasu kuma har da feduwa (fito) daga nan sai Jauje ya shiga tallan maganin samun kudi da yake idon mutane duka ya rufe sai suka yi ta bashi kudi suna karbar gaibu. Kafin wani lokaci mai tsawo sai ga shi ya tara kudi tuli.

Bayan mutane sun watse ya tsuguna a wajen yana ta kidayar kudin da ya tara yana keta dariya. Bai lura ba har mutanen su biyu, dogo da gajere suka iso kansa suka tsaya suna kallonsa. Can sai jikinsa ya bashi cewa wasu na kansa a tsaye ya daina dariya ya cira kai cikin firgici ya dube su.

Dogon ya yi masa murmushi, "Barka da warhaka. Jauje dubansu kawai yake yi bai tanka ba. "Kasuwa ta yi kyau, ko?" Da ya ji Jauje bai amsa ba sai ya cigaba. "Muna tsaye tun dazu muna kallon irin bajintarka, babu shakka kai din nan ba dama ne Jauje ya dubi dan gajeren wanda har yanzu bai ce uffan ba. Kana ya mayar da hankalinsa ga dogon.

"Su wane ne ku? me kuma kuke bida daga gareni?" Dogon ya dan rusuna ya ce "Aiko mu aka yi wajenka.

Ya cika da mamaki. "Wane ne

Please Login or Register in order to submit comment