Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banyi zaton kaba amma dai ina farin ciki gashi kuma munyi sa'a ma baba yatafi aiki.
Labaran ya tausayawa kansa domin yasan duk irin kaunar da yakeyi mata dolene ya gujeta wannan shine ganin karshe.
Tafiya ce ta sameni ta gaggawa shine nazo muyi sallama dan sai jibi zan dawo kada kice na karya miki alkawari shiyasa nazo yanzu. murmushin da take fuskar ikram ta subuce.
Tafiya......!!! Labaran yayi murmushin karfin hali kada ki damu jibi dana dawo ta nan zan biyo. Ikram ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da zoven dake dan yatsanta.
Wallahi Lab.... Kwana daya kacal da saninka amma ji nakeyi babu wanda na saba dashi aduniya kamarka dan Allah darlin da ka dawo ka biyo ta nan jibin.
Hakan da tace shine abinda yafi komai farantawa agareshi. Labaran ya dan mao kusa da ita wata yar bakar jaka mai fadi ahannunsa yace.
Ikram bani aron zoben nan dake hannunki idan na dawo jibi saina baki kinga idan ina tare dashi kamar kece kusa dani cikin annashuwa dajin kunya jikinta na rawa ta zare zoben daga danyatsanta ta mika masa.
Gashi nan Darling nabaka shi har abada domin abin farin cikina ne da alfahari ace duk inda zaka kana tunawa dani. Labaran ya mika mata dan yatsansa yace. Samin da kanki. Ikram na murmushi ta kama hannunsa jikinta na rawa domin tunda take bata taba kama hannun wani namiji baligi ba. Tasa masa zoben.

Ikram ni zan tafi amma don Allah inason ki fadamin kalma daya wacce zata zamo itace jagorata awannan tafiya.
Me kake son nafada maka?
Kice inasonka labaran har abada bazan mabta dakai ba. Ikram ta rufe idanu cikin jin kunya sannan tace.
ina kaunarka darling kaine farin ciki na har abada tana fadin hakan saiya miko mata bakar jakar dakuma wasika yace.
Idan kinje gida saiki shige cikin dakinki ke kadai ki karanta wannan jakar kuma ki ajjemin idan nazo jibi zan karba ya bude motarsa ya shiga.
Ikram ta dubeshi jakar da wasikar ahannunta tace.
Allah ya dawomin dakai lafi.... Bata karasa ba.
Toh ikram dina. Koda ya tuka motar yafara fice daga layin saiyaji hawaye shar shar suna zubowa akan kumatunsa. Har yafice daga layin ikram na nan tsaye tana daga masa hannu bai iya juyowa ya kalleta ba to amma yana kallonta ta cikin madubi,

Ya hau babban titi yafara kwarara wuta ya kura manejin motar har karshe.
To akalla dai yasan yayiwa wacce yake so wani abin alkhairi duk kuwa da cewa shi ya kashe kawarta yace da kansa. Sannan sai yayiwa kansa murmushi sa'ar daya tuna da Ilyasu ko ya zaiyi idan yaga kwana daya sati zzuwa wata bai dawo ba domin tunda misalin karfe takwas yace da Ilyasu yabashi aron dan makullin motarsa zaije unguwa acewarsa karfe goma zai dawo. Ganin irin halinda labaran yake ciki shiyasa ilyasu yabashi aron dan mukullin batareda ya tambaye shi inda zashi ba.

Labaran ya dada take totur din motar ba kakkautawa zuciyarsa cike da tunanin ikram lokaci lokaci yakan dauke idanunsa daga kan titi ya koma ga kallon zoben dake hannunsa. To ai irin dauke idanun nasa ne yazo wata lankwashashshiyar kwana bai kuma kula da katuwar motar katakon da tayiCUTA TA DAU CUTA-28

KARSHE

To A irin dauke idanunsa ne yazo wata lankwashashshiyar kwana bai kuma kula da katuwar motar katakon datayi fakin akan titin ba acike take kuma da lodin itatuwan wuta yana zuwa saiya shuka kansa akarkashinta.
Saida kyar jami'an tsaro da sukazo gurin hadarin suka banbaro dan abinda ya rage na daga ragowar GAWAR LABARAN.

****** ****** ****** ****** ******** *************

IKHRAM ta shiga dakinta tana farin cikin da bata taba samun kanta acikinsa ba sannan saita ware wasikar tafara karantawa Kamar Haka.

Abar Kaunta Ikhram....
WANNAN SAKONE DAGA ZUCIYA ZUWA ZUCIYA. IKRAM TUN SA'AR DANA FARA DORA IDANUNA AKAN HOTONKI NAJI DUK DUNIYA BABU WACCE NAKE KAUNA KAMARKI LOKACIN DAKUMA NA HADU DAKE AZAHIRI SAINAGA ASHE KIN WUCE DUK YADDA NAKE TUNANI IKRAM DAIDAI LOKACIN DA KIKA NISA CIKIN KARATUN WASIKAR NAN NIKUWA SAI DADA NISA NAKEYI ACIKIN DUNIYA DOMIN KWANA DAYA KACAL DIN DANAYI DAKE YAFI MIN DUKKAN KWANAKINA ADUNIYA AMFANI.
IKRAM KI RIKE WANNAN ARANKI HAR IYA RAYUWARKI NI MASOYINKI NE TO AMMA ANYI RASHIN SA'A DOMIN KUWA KWATA KWATA BAN DACE DAKE BA DOMIN IN HAR ZAKIYI LA'AKARI DA ABINDA NA AIKATA TO BAZAKI IYA KIRANA MUTUM BA SAIDAI KO DABBA.

IKRAM NAYI KUKA AKANKI HAR HAWAYENA SUN KARE DANA SANI DA'ACE NASAN ZAN TABA HADUWA DAKE ADUNIYA TO DA IN ZA'A BANI DUK DUKIYAR DUNIYAR NAN BAZAN AIKATA ABINDA NA AIKATA BA.

GA KUDIN NAN SU SUKA YAUDARENI SON SU DA BEGEN MALLAKARSU TA KOWANE HALI SU SUKA JEFANI CIKIN WANNAN HALI.... NA BAKI SU IKRAM SU KADAI NAKE DASU.... NASAN IN ZAN BAKI DUK DUNIYAR NAN BAZAN SAKA MIKI DA FARIN CIKIN DA KIKA JIYYAR DANI BA NA SA'A DAYA.

NAGODE NAGODE IKRAM ALLAH YABAKI MIJI DAIDAI DAKE MAI KYAWUN HALI BA IRINA BA...

INASON KI INA KAUNARKI INA BEGENKI INA KUMA BAKI HAKURI DOMIN NINE LABARAN DIN DA YA KASHE FA'IZA.!!!

Ikhram ta kwalla kara cikin dakin sa'ar data kawo karshen wasikar sannan saita fadi kasa sumammiya.

****** ****** ****** ****** *********************

Adaidai lokacin da take karatun wasikar sharoro shima nacan cikin falonsa yana karatun tasa wasikar kamar haka....

SHARORO...
Nasan kagama kyamata da tsanata nasan kuma zaiyi wuya in har zaka taba yafemin amma duk da haka zan kokarin neman gafara agareka.
Sharoro nasan cewa ni nayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarka duk kuwa da cewa dai daman kwananta ya riga ya kare nasan na cuceka sharoro bakuma sanadiyyar mutuwar mahaifiyarka bane kawai cutar da nayi maka ba hakika akwai wani abu da bakowa ya sanshi ba daga ni sai Allah sai mahaifiyarka.

Sharoro mun taba zaman bariki ni da mahaifiyarka aboye ahaka aka sami cikinka lokacin danaga zanji kunya saina roketa data data rufamin asiri sharoro tun da nake ban ganin mace mai kaunata kamar mahaifiyarka ba domin saida ta nemi na aureta naki domin ina ganin mutuncina zai iya zubewa a idon mutane amma duk da haka mahaifiyarka ta rufamin asiri ta jure dukkan zagi akace da ita karuwa aka ce shegiya ce itama batada iyaye amma duk tayi shiru har aka haife ka.
Sharoro ba karamin farin ciki nayi ba lokacin da mahaifiyarka ta rasu domin kullum saina bata yan kudi na rufe bakinta duk kuwa da cewa wai tana kaunata saboda akullum sai tayimin barazanar kodai na aureta kokuma ta tona min asiri dan haka mutuwarta saina yi farin ciki. To amma duk abanza domin hakan bai kareni da komai ba sai bakin cikin rayuwa kowa ya tsaneni a unguwa saboda rashin imanina

Sharoro kadan kenan daga cikin abinda yafaru inasan ka sani cewa FA'IZA KANWARKA CE TA JINI. Ayanzu kuma tunda banida DA namiji dole na kaunaceka duk kuwa da cewa ahanyar banza muka sameka.
Dukkan wata dukiya sharoro tana hannun Alhaji Shu'aibu shine wanda kullum yake nan taredani. Ka sameshi yana da rikon amana akwai kudi dana bashi nace kada yabaka saina mutu suna nan agurinsa NAIRA MILLIYAN BIYAR NE kyauta nabaka su sharoro kayi hakuri ka yafeni ga yar uwarka nan fa'iza ka riketa kada ka bari ta bata kasonta na kayan gado don Allah ka kular min da ita duk ina kaunarku KAIMA DANA ne. Sharoro daga yau dai akalla kasan waye maihaifinka shikenan

Sharoro Allah hada fuskokinmu a durassalam. Sai watarana ka kula da FA'IZA. Yar uwarka ce.
MAHAIFIN KA.....

Sharoro yayi mutuwar zaune sa'ar daya gama karatun wasikar yafara safa da marwa.
Mahaifina.... Yace cikin kuka yanzu mahaifina da kantawa na kashe?? Na shiga uku!! Sharoro ya fadi akasa yanata gunjin kuka yana haka har safe har karfe hudu na yamma.
Sa'ar da sharoro yaga hawayen idanunsa sun kusan karaewa saiya tashi idanunsa duk a kumkumbure yafita ahankali jiki babu karfi sannan saiya nufi inda motarsa take sa'ar daya shiga motar saiya wuce ofishin yan sanda kai tsaye karfe hudu da minti ashirin ya isa.

Sajan dake dakin tarbar baki yadubeshi yana muzurai yace.
Malam lafiya? Sharoro ya dubeshi yace.
Zuwa nayi ku kamani jin haka shiyasa sauran jami'an tsaron tasowa suka zagaye shi cikin mamaki.

Ku kamani nace!! Sharoro ya buga musu tsawa.
Mahaifina na kashe dazu da safe shekaranjiya kuma nasa aka kashe kanwata aka jefata cikin kogon dutse itace wacce mutanenku suke bincike akai. Yansandan suka dubeshi cikin kaduwa wani sajan ya matso kusa dashi yace.
Kai kasan kuwa me kake cewa? Sharoro ya dubeshi a fusace yace.
Dakikin banza kai bakajin hausa ne?

Nace dakai mutum na kashe. haryanzu yansandan dubansa suke cikin shakka domin babu mamaki buguwa yayi yazo zaiyi musu shirme.

Kai nifa da hankalina yau Talata Gobe laraba ashirin da uku ga watan takwas ku takwas ne cikin dakin nan ku yarda yanzu da hankalina ?

Kwarai kuwa. Wani sajan yace dashi.
Ku kamani. Nan da nan aka buga masa ankwa hannu da kafa sannan aka wuce dashi zuwa dakin bincike koda suka fara tafiya sai sharoro yace

AKWAI MUTUM DAYA DA KUKE BUKATAR YA SHIGA HANNUN KU KUYI GAGGAWAR KAMA SHI SUNANSA LABARAN.

KARSHE....

NAZIR ADAM SALIH (Nas)

Alhamdulillahi
Alhamdulillahi
Alhamdulillahi

CIKIN TSOFAFFIN DAI WANDA NAYI ABAYA WANNE ZAN SAKE NANATAWA KAFIN ASAMU SABO ?

INA DAKON RA'AYOYIN KU TA INBOX KO TA WHATSAPP AWANNAN LAMBAR 08038831020

(Yarima A. Gangariya)
JIKAN SIDI MAI JAKA
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment