Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

motar ya haske mutune biyun dake zaune adaidai lokacin da saurayin yakai idanunsa ga kallon fuskar mutumin ga mamakinsa saiyaga hawaye na zuba shar shar daga idanun farin mutumin. Saurayin ya dauke kansa gefe guda domin in har akwai abu daya da bai sani ba a rayuwarsa to tausayine.
Mutumin danake baka labarin bana kauna makwabcin mune gidansa ajikin gidanmu yake to saidai shi nasa gidan gari guda ne domin har yanzun nan danake baka labarin nan arzikinsa bashi misaltuwa.
Akofar gidanmu akwai wani mutum sunansa HALLIRU ya dade yana sayar da taba da goro kusan sama da shekara ashirin da wani abu shi ya bani mummunan labarin dayasa na tsani makwabcin namu matukar tsana ayadda yake bani labarin lokacin dana shiga cikin tsanani cewa yayi dani makwabcin namu ne yayi sanadiyar mutuwar mahaifiyata domin ta kwanta wata matsannanciyar rashin lafiya sata aika akirawo mata shi domin ya taimaka mata da kudin da likitoci suka rubuta za'a kashe wajen yi mata aiki domin an tabbata da cewa amininta ne duk kuwa da cewa anayi mata kallon karuwa mai lasisi. Makwabcin namu yayi burus mahaifiyata tayi ta aike ga gida ga gida amma yaki zuwa har jinya..CUTA TA DAU CUTA-06

Har jinya taci karfin mahaifiyata shine da taga zata mutu in ta biye ta jiran taimakonsa saita aika tashi to yazo ya sayi gidanmu zatayi amfani da kudin ayi mata magani fadin haka keda wuya saiga maketacin yazo da gaggawa aranar akayi cinikin gidanmu alokacin ina karami ya saye gidan araha banza aranar da yabiya kudin mahaifiyata ta rasu ta barni cikin garari da wahalar duniya ahaka na tashi cikin tsanani kowa yana kina saboda wai banida uba daga karshe dai danaga Inna bari nima abanza zan mutu saina nafara yan dabaru nan da nan kuwa kudi suka fara taruwa cikin gaggawa har zuwa yanzun nan danake baka labari. To amma duk da haka haryanzu so nake naga nafi makocinmu arziki ninkin baninkin.
Saurayin ya dago kai sa'ar dayaji mutumin yayi shiru yace.
Toh ai ni haryanzu bangane ma'anar maganganunka ba kuma har yanzu baka fadamin dalilin kisan budurwar da kake fadi ba... Menene hadinta da labarin da kake bayarwa yanzu? Mutumin ya kyalkyale da wata irin kakkausar dariya wanda har tasa saurayin ja da baya cikin kaduwa domin daman tuni yana zargin mahaukaci ne. Bayan wasu yan dakiku mutumin ya daina dariyar sannan ya goge idanunsa da hannun kwat dinsa yace.
Budurwar danake so ka kashe min ai yarsa ce. Ba zan taba jin dadin rayuwata ba sainaga an kashe min yar nan tasa dan ita kadai ya mallaka kaga shima sai ya dandana yaji irin yadda akeji kamar yadda shima ya rabani da mahaifiyata.
Fogon mutumin ya danyi shiru yana duban saurayin sannan saiya dada da cewa.
Wani abin mamaki shine tunda na tashi mutumin bai taba nunamin cewa yasan mahaifiyata ba ada. Sai rannan kwatsam ya aiko har gidana wai ayi kirana abin yabani mamaki amma banki zuwa ba saina tafi gidan ina zuwa akace min ai wai yana asoibiti to shine na wuce kai tsaye zuwa asibitin acan na sameshi kwance likitoci burjik akansa amma duk da abanza domin taruwar tasu bata hana rabin jikinsa shanyewa ba hakanan dukiyarsa ba karamar kaduwa nayi ba sa'ar danaji yace dani wai ya kirawoni ne saboda ni yafi amincewa dani saboda wai mahaifiyata aminiyarsa ce to shine yake son ganawa dani yace yana da 'yarsa daya jar sunanta FA'IZA. Ko ban fada maka ba kai kasan bayan abinda yayiwa mahaifiyata ban taba jin tausayinsa domin ni lokacin daya tura akirawoni naje naji abinda yake fada sai naga kamar ma Allah ne ya kamashi yakawo min shi a hannuna dan na rama abinda yayi min duk da yake dai da nayi zaton rashin lafiyar ce tasa kansa ya tabu har ya aika akirani amatsayin wanda wao yafi amincewa dani. Ina fatan kana fahimtata ayanzu? Mutumin yace yana kifkiftawa saurayin idanu.
Tabbas ina fahimta. Saurayin yace yana girgiza kai to tunda ka fahimce ni yanzu bari in tafi kai tsaye ga abinda nake son kayi min. So nake ka kashe min yar nan tasa kwaya daya jal mai suna Fa'iza idan ka aikatamin hakan to nikuma zanje da kaina har gurisa na shaida masa cewa na kashe yarsa kamar yadda yayi sanadiyar mutuwar mahaifiyata sannan kuma Wallahi kaji na rantse maka saina mallake duk dukiyar daya mallaka.
Tayaya zaka mallake dukiyarsa bayan yanada yan uwa? Saurayin ya tambaya.
Da sannu ahankali zamuzo ga wannan kada fa ka manta nafada maka ni da yan dabaru nake ci to tunda Allah ya kama munafuki yazo hannu to kuwa zan jefi tsuntsu biyu da dutse daya.
Shin baka tsoron in kace dashi ka kashe yarsa agabansa zai iya hadaka da jami'an tsaro? Mutumin ya fashe da dariya.
Ai daga lokacin dayaji wannan kalamin daga bakina to shima kwanakinsa sunzo karshe kenan aduniya saurayin ya dubeshi cikin kaduwa.
Me zakayi masa? Ya tambaya.
Abinda ba zai taba mantawa dani ba in da har ace zai sake wasu kwanakin aduniya kaga kaidai bani amsa shin zaka iya kashe min ita? Saurayin ya sunkuyar da kai kasa yana tunani can saiya daga kai yace.
Bantaba kashe mutum ba kuma ni bana son nafara koda ace zan baka naira miliyan dayar ka ahannu ne ? Koda ace zan baka sabuwar marsani ? Koda ace zan baka sabon gidan da zaka zauna ne? Saurayin ya dubi mutumin shekeke yace.
A ina duk ka sami wadannan kudade da kakeyi min alkawari?
Banace dakai da yan dabaru nakeci ba? Ai in dan arzikine to ni kam na gama to amma tunda dai gashi yanzu yakawo kansa to tafadi gasassa sai nayi ramuwar gayya hakanan kuma na kara cikin akawun din bankina domin kayan nama baya kashe kura.
Saurayin ya mike tsaye jikinsa na rawa ya dubi dogon mutumin cikin shakka yace.
Indai zaka cika min alkawarina to zan gwada kashe maka ita.
Dakyau dan samari.. Haka nake son jarumi ai da ganinka daman ni jikina yabani cewa tabbas na sami gwanina. Mutumin ya sake fashewa da dariya sannan saiya fara magana amma bada kowa yake maganar ba sai da kansa kada.
Tab!! Wai ni tsohon macucui nan ya amincewa...
Tab amininsa lallai yau
CUTA TA DAU CUTA
kowa baisani ko wanene ba.

DAYA 1
Kada dai kice dani yauma fita zakiyi? Ikram tace Daga tsaye tana duban dakin kwanan daliban sama da kasa kamar wacce take tsammanin zai rubzo mata.
Kwarai kuwa saime idan na fita ko kina da aikin da zanyi miki?
Budurwar dake zaune akan kujera tana kwalliya agaban madubi ta fada gamidaCUTA TA DAU CUTA-07

Budurwar dake zaune akan kujera tana kwalliya agaban mudubi ta fada gamida hararar Ikram.

A'a ni babu aikin da zakiyi min kawai dai gani nayi kamar ya dace nabaki shawara akan irin yadda kika sauya takun rayuwarki ayan kwanakin nan agaskiya kina bukatar wankan tsarki.
Wankan tsarki yaya? Fadawa kwata nayi kikeji ina doyi ko kuwa kashi nayi acikin hostel? Budurwar ta tambayi ikram cikin fushi.
Bahaka nake nufi ba FA'IZA ikhram tace a sanyaye.
Abinda nake nufi kin fini sani fa'iza ki tuna fa karatu iyayenmu suka kawomu makarantar na ba yawon dandi ba.
Ikram ta danyi shiru tana duban fa'iza domin taga ko maganar ta fara ratsata.
Oho! Kin daukeni karuwa kenan ko?
Fa'iza tace tana duban ikram sannan lokaci guda kma saita dauke kanta ta fuskanci tagar dakin dake fuskantar farfajiyar makarantar. Daga inda take zaune tana iya hangen yan mata kungiya kungiya sunata sha'anin gabansu wasu na tafiya filin wasannin motsa jiki wasu kuma dakin karatu acan bangare guda kuma wasunsu zaune suke suna ta hira agindin bishiyoyin dake farfajiyar makarantar suna jiran yunifom din da suka wanke su bushe kafin suzo ga guga domin yau lahadi gobe kuwa ranar karatu ce ba wasa ba.
Shekaru kusan goma sha kenan da fara wata irin sabuwar dabi'a awannan makaranta ta yan mata. Ga samari bata gari dake son shagali da sharholiyar duniya wannan dabi'a abar marhabun ce.
To amma ga wasu daliban shiryayu da kuma iyayen yara wannan dabi'a ta munana agaresu tuni samari yan shagali suka dade da sanon cewa duk ranar lahadin duniya akan sami tsuntsu daga sama gasashshe akofar makarantar wadannan tsuntsaye dake fadowa daga sama gasassu ba wasu bane da suka wuce yan matan karantar wayayyu wadanda atunaninsu idanunsu ne suka bude budewa ta yahudu dan haka sai suke ganin ba laifi bane dan sun sheke ayarsu tunda dai na farko samari kan rabo a munafurce na biyu kuma masu gadi suka bada dama tun da suma ba'a banza ake barinsu ba samarin kan jikasu jagaf da naira wasu daga cikin malaman makarantar sun san da irin wannan mummunar dabi'a dake faruwa to amma basu da ikon magana domin ance wai mai bunu a gindi baya gudunmawar gobara. Jita jita na cewa sune ma kan gaba wajen sheke ayar da daliban.

Daga inda Fa'iza take zaune tana iya hangen malam AYYUBA DIKKO. Wanda ayan kwanakin baya da suka wuce batada wani gwani na sheke aya kamarsa to amma ayau kam da take ta faman sheka kwalliya gamida kokarin ta maida kanta baturiya domin jiran sabon saurayin da tayi ayayinda taje gida hutu saitaga tabbas tayiwa malam ayuba dikko nisa domin ai bama ajinsu daya dashi ba.
Ta saki wani tattausan murmushi sa'ar data dubi biyu biyu din gemun ayuba dikko. Tab in banda dai ina karuwa kuma wasu lokutan yakan taimakamun a jarrabawa me zai hadani da wannan kazamin! Tace cikin zuciyarta.
Fa'iza tayi ajiyar zuciya sannan ta dauke kanta daga kallon tagar dakin ta dawo da hankalinta ga ikram wacce ke tsaye haryanzu rike da kugunta tana kallon fa'iza cikin kaduwar ganin tama manta da ita ta shiga wasu tunane tunane.
Fa'iza dake nake magana fa ko bakya jina ne? Fa'iza.
Malama ina jinki! Fa'iza tace a fusace. Ba cewa kikayi dani karuwa ba ko bahaka... Ikram ta katseta.
Kinga ni bance dake karuwa ba.
To me kikace dani mumina?
Fa'iza ta tambayeta gamida mata wani busashshen murmu na izgili.
Fa'iza! Ikram ta kira sunanta cikin wata irin tattausar murya dake nuni da cewa wannan fa itace shawararta ta karshe ga kawarta.
Ina baki shawara ne badan ni nafiki ba sai dan dai ke kawata ce kuma yar uwata musulma ina ganin yakamata ke inma bakya tsoron Allah kibari mana ko dan gudun kada ki kamu da irin mugayen cututtukan nan na zamani mana ke bakya tsoron KANJAMAU?... Ga mamakin ikram da kuma kaduwa saitaga fa'iza ta saki wani tattausan murmushi sannan saita ajje janbakin dake hannunta akan teburin kayan kwalliya dake gabanta ta mike tsaye hannunta na hagun rike da zanin dake kugunta ta dubi ikram tace.
Duk naji abinda kikace kin cimin mutunci kince dani karuwa to kije ki Allah ya isa ni nasan ba karuwa bace nasan bakin ciki kawai kikeyi da samari na dan kinga ke bakida kowa ke ko yar soyayyar ma da akeyi da malamai bakya yi sai yawo kike sokai-sopkai ke kadai jallin jal kamar mayya. Ke sai anjima kinji malama kada ki batan lokaci kinji ko.
Kusan tsahon dakiku ashirin ikram na tsaye cikin kaduwa tana duban fa'iza sannan can saita nisa tace.
To shikenan fa'iza Allah ya kiyaye dahaka tafice daga dakin.

***** ***** ****** ****** *********** ************

Ficewarta keda wuya sai fa'iza ta nufi gindin akwatin da kayanta suke ta bude akwatin. Acike take da kayan zamani masu tsadar gaske wanda kaso mafi yawa daga cikinsu duk samarinta ne suka dinka mata su. Fa'iza ta fara jujjuya kayan tana tunanin shin wacce kala ya dace tasa domin ta burge wannan babban bako nata.
Kwatsam. Saitaji gabanta yafadi wata zuciya tace da ita shashashar banza yanzu idan yaki zuwa yaya zakiyi?
Tunanin hakan shiyasa wani zazzafan gumi yafara zuba akan goshinta gamida barazanar wanke kyakkyawar kwalliyar tsanakin data kwasheCUTA TA DAU CUTA-08

Wani zazzafan gumi yafara zuba kan goshinta gamida barazanar wanke kyakkyawar kwalliyar tsakanin data washe kusan sama da awa guda tanayi.
Sannan ne to tunanin farkon haduwar ta dashi ya Fado mata.

A hutun daya gabata ne suka fara haduwa dashi a garinsu a kofar shiga babbar kasuwar birnin. Koda yake farkon haduwar su kenan
Ganinsa kawai tayi a gabanta kamar an jefo shi yanayi mata lallausan murmushi bai kuma bata lokaci ba wajen yada manufar sa a gareta tun da take bata taba ganin mutumin da take kauna ba kamar sa kallo daya tayi masa ta tabbata zuciyarta ta makalu da kaunarsa abin kamar sihiri.

Gobe zan koma makaranta. Fa'iza tace dashi yayinda suka hadu itama ta jefe shida tattausan murmushi daga nan kuma duk sauran abubuwan da suka biyo baya masu saukine domin yashiga da ita kasuwar ya kashe mata kudi fiye da hankalin ta sannan yayi mata alkawarin zaizo makarantar ya dauke ta sannan ne to ta nuna masa cewa ita fa tsohon hannu ce a harkar takuma fada masa irin dabarar da akeyi idan za'a fita dasu yawon sharholiya daga makarantar.
Mutane da yawa sun sha cewa da ita kyakkyawa hakanan itama Fa'iza tasan cewa ita kyakkyawa ce to amma abu daya ne tafi yarda dashi abin kuwa shi ne dayawa daga mazajen da suke kallonta sunfi sha'awar ta fiyeda kaunar ta.
To amma sa'ar data kyalla ido ta hango kyakkyawan saurayin sai ta mace akan kaunarsa hakika kuma awannan Karon kauna ta Gaskiya take masa ga mamakin ta saitaji ko kusa bata sha'awar wata HARKAR banza ta hada su ita a yadda take mutuwar sonsa ayanzu zaifi kyau idan zai aure ta.
Sai naja ra'ayin sa yazama nawa ni kadai mijina......
Tace cikin zuciyar ta gamida yiwa kanta alkawarin yin hakan.
Koda taci gaba da birkita kayayyakin dake cikin akwatin domin zabo mafi kayatarwa a gareta sai wata zuciya tace da ita.
Kibishi a hankali yar budurwa zai kauna ce ki kamar yadda kike kaunarsa... Kuma zai aure ki nan D nan sai ta dauko wata doguwar rigar shadda shudiya wacce aka yiwa ado da duwatsu farare masu kyalkyalin daukar idanu ta rungume kayan a kirjinta ta rufe idanuwan ta tana shakar kamshin turaren dake jikin kayan.
Allah.... Allah sa dai ya zo tace a sanyaye ga mamakin ta saitaji wata sassanyar kwalla ta fara zuba shar Shar akan tattausan kundukukinta.
.
******** ********* **************
.
Karfe hudu saura kwata daidai wata dankareriyar marsandi baka mai doguwar eriya asama kamar husumiyar masallaci taja ta tsaya a kofar farko na makarantar yan matan.
Tun kafin kofar motar tagama budewa wani dan tsatstsaman mai gadi sanye da lankwashshshiyar hula mai kamar makani ya sheko da gudu zuwa gindin motar.kofar motar ta bude a hankali sannan wani dogon saurayi wankan tarwada yafito daga cikin motar yana murmushi kai saika rantse da Allah Daman can ya Dade da sanin mai gadin.
Saurayin sanye yake da doguwar ta zarce shudiya kusan rabin rigar tana shafar kasa. Saurayin yanada wani irin yanayi a fuskarsa wanda ke bashi karfin iko da isa dakuma tambari na mutunci da kirki idan ka kalle shi dakyau da wurwuri zaka raja'a da cewa baiyi kama da irin samarin birni ba daka saba gani suna sintiri loko loko lungu lungu acikin birane ba kallon farko idan kayi masa saikayi kuskurensa a matsayin lauya Kokuma wani kwararren Ma'aikacin banki ma'abocin karamci da nutsuwa dakuma yini yana Aiki a gaban na'ura mai kwakwalwa to amma a Gaskiyar al'amari duk wani abu da zuciyar ka zata fassara maka shi to bai bai ne.
Idan har kana tsammanin sa gabas to shi a yamma zaka same shi hakika duk inda tambadadde marar imani yake wannan saurayi yayiwa nan fintinkau nesa ba kusa ba.

Alhaji barka da zuwa... Maigadin yace bakinsa na rawa.
Yawwa dan Dattijo. Saurayin yace cikin fara'a da murmushi sannan ya dada dacewa nine LABARAN. Tun ranar da suka fara haduwa da Fa'iza tace dashi idan an tambaye shi ga abinda zaice da Maigadin kenan.
Oh..... Yallabai ka karaso kenan ai tun da safe Fa'izar tace dani zakazo tun daga nesa da man nace Kaine a zuciyata Maigadin yace.
Kwarai kuwa ai hanyar ce babu kyau in ba'a hankali mutum yabi ba sai ta bata masa mota. Labaran yace lokaci guda kuma ya cire bakin tabarau din dake fuskar sa ya goge sannan ya sake mayarwa ya rufe fuskar sa dashi.. Maigadin yafara waige waige yana mutsu mutsu. Bayan ya tabbatar babu kowa akusa kusa da wurin sai yayi kasa kasa da muryar sa yace.
Yallabai ba'a nan fa zaka dauke ta ba can bayan makarantar cikin dajin can zaka tuka motar ka nufi kudi amma fa kada ka saki hannun ka indai kaci gaba da haka zaka ga inda katangar wayar data zagaye makarantar ta fashe to anan zaka jirata saikayi sauri ka tafi kasan fa wani malamin ko kuma lebura na iya hango mu yafara tunanin wani abu Maigadin yayi shiru yana yake hakora.
Ina Fatan ka fahimce ni zata zo ta same ka agurin kada kuma ka wuce karfe goma na dare da ita ka tabbata ka dawo da ita kafin goman dare.

Na fahimta Dattijo. Labaran yace sannan lokaci guda kuma ya lalubi aljihun sa ya zaro damin naira ashirin sababbi kar ya turawa Maigadin a fuska yace.
Rike wannan ka sake sayawa kanka sabuwar riga dan Allah kuma kana yin wanka duk wari kake. Maigadin ya yi sauri ya warce kudin daga hannun labaran cikin gaggawa kamar yada a hawainiya kan warci kuda. Tunda yake ba'a taba bashi kyautar dubi biyu ba lokaci guda ba.
Nagode Alhaji bari in yi masa na turo Maka ita sai kayi sauri ka tafi kada kuma ka damu da kayan jikina kyale kyale ai saiku dan samari. Kafin labaran ya sake cewa wani abu Maigadin ya sheka da gudu ya nufi cikin makarantar.
Labaran ya gintse da dariya sannan ya shafi zungureriyar wukar dake aljihunsa ya girgiza kai sannan sai ya nufi motar yashiga ya tuka zuwa inda Maigadin ya kwatanta masa.....CUTA TA DAU CUTA-09

Labaran ya gintse da dariya sannan ya shafi zungureriyar wukar dake aljihunsa ya girgiza kai sannan saiya nufi motar yashiga ya tuka zuwa inda maigadin ya kwatanta masa.

Baifi mintuna biyar yana jira ba saiya hango Fa'iza ta ratso ta cikin jerin dogayen ciyayin da suka yi sahu sahu ta nufo inda yake tana rangwada gamida wani boyayyen murmushin sirri dake makale a Fatan bakin ta nan da nan sai labaran yaji gumi ya fara karyo masa zuciyar sa ta fara bugawa ba abin ayi imani dashi bane akace nan da sa'a guda ya kashe kyakkyawar yarinyar nan. Tun da yake bai taba kashe mutum ba yasha yin ayyukan ta'adanci da dama to amma har yau baizo ga kan kisan kai ba sai wannan karon da aka shawo kansa.

Indai har ka kashe ta ka kuma bi tsarin dana shirya ma to babu abunda zai hana duniya ta dawo hannun mu haba labaran ka tuna fa ka Dade kana fadi Can tashi can amma har yanzu Baka wuce yan mashahurin attajiri yasa kafa ya banke ka ba koma ya batar dakai..... Kaga idan hakane kuwa to haryanzu da sauran ka zaman duniyar nan saida nazari da yan dabaru na boye... Saika dauki duniya ka bajeta a faifai sannan ne to zaka Gane cewa ashe fa duniya cike take da taskokin arziki babu mai ganinsu kuwa sai irin mu masu kwakwalwa... Ina da kwakwalwa labaran kaikuma kanada karfi to me zai gana mu hada kanmu mu taimaki juna kaga kai zaka azurce nikuwa zan huce ranuwar gayyar dake zuciyata haka nan kuma akawun din bankina zai kara ƙiba.
Maganganun da farin mutumin ne ke ta faman kai kawo A Zuciyarsa sa'ar da daya hangi Fa'iza.

Fa'iza ta nufo gindin wayar sannan ta rankwafa ahankali ta fita waje ta nufi gindin motar inda yake.
Labaran ya sake shafar inda wukarsa take sannan ya dubi Fa'iza.
ANYA kuwa zan iya kashe budurwar nan?
Bawai kaunarta bace Kokuma tausayin ta ya sashi tunanin ba saidai kawai shi agurinsa ba karamar asara zai yi wa samari ba idan ya kashe wannan kyakkyawar budurwa mai rausaya
Fa'iza ta nufo motar da gudu tana zuwa saita fada cikin motar wacce dama tun kafin ta karaso ya bude mata kofar.
OH!! My darling Wallahi... Na dauka bazaka zo ba... I love you! Ta dafa hannunsa
Haba Fa'iza ni na isa nace bazan zo ba. Labaran yace sannan lokaci guda yasawa motar giya yafara tafiya.
Kada kabi ta kofar makaranta wani na iya hangen mu tabaya yadace ka zagaya Fa'iza tace dashi cikin murmushi labaran ga godewa shawarar data bayar cikin zuciyar sa dama in har akwai abinda ya tsana ayanzu to wani ya sake ganin fuskar sa bayan maigadin

Ina muka nufa ne? Fa'iza ta tambaye shi sa'ar da suka fara tafiya CITY HOTEL.
Labaran yace da ita batareda dube ta ba.

Dole ne in yi sauri na kashe ta kafin magariba yace cikin zuciyar sa sannan ya juyo cikin murmushi yace
Fa'iza kaunarki ya mamaye zuciyata.
Haba labaran ai ni nafika ta danyi shiru sannan ta dada dacewa labaran fadamin dan Allah ko naji sanyi araina ZAKA AURENI?
Me zai hana ki yace kai tsaye shi kansa saida yaji kunyar karyar daya dankara mata labaran ya shafi zungureriyar wukar dake gefen aljihun doguwar rigar sa sannan saiya dubi Fa'iza yace cikin murmushi.
Banida abar kauna kamar ki....

BIYU 2
KA manta dace dashi bafa nan bace hanyar...
Dogon saurayi labaran ya dan ragewa motar gudu sannan ya juya a hankali yace ai na sani sannan ga mamakin ta sai taga ya dada karawa motar gudu kuma lokaci guda yana duban agogon dake makale agaban motar kusan mintuna talatin kenan da barin su makarantar amma cikin shiru. Da farkon fara tafiyar su Fa'iza taso taci gaba da surutu musamman ma Dan kokarin da take na ta karkato zuciyar sa akan ya aure ta to amma sai yace da ita tayi shiru tabar duk wata magana sai idan sunje City Hotel din sa tattauna baki daya.
Kada ki damu Fa'iza labaran yace da ita sa'ar da suka baro makarantar. Tun sa'ar dana fara dora idanuwana a kanki zuciyata da dukkan wasu sassan jikina suka amince min dake a matsayin matata dan haka Inason Ki kwantar da hankalin ki kiyi Shiru har mu kai ga hotel din tuni na kama mana daki acan inda zamu zauna zamuci mai kyau Musha mai kyau sannan kinga zaifi dadin tattaunawa amma yanzu ke kinga yadace ina tuki muna hira ganganci kenan fa domin kyawun fuskar ki kawai na iya sawa na saki hanya.
Fa'iza tayi masa murmushi sa'ar dataji yakawo aya. Sannan saita dan dora kanta akan kafadar sa tace.
TOH Darling nayi shiru kada kuma ka manta I LOVE YOU.

Tun daga lokacin bata sake cewa dashi uffan ba sai dai lokaci lokaci idan yazo kaucewa rami akan kwalta Kokuma dabbobin makiyaya yakan dan waigo ya dubeta ta a zuciya sa yana tunanin inda yakamata ya soka da wukar a jikinta ita kuma saita jefe shi da murmushin tsantsar kauna.
To sai yanzu kuma Kwatsam taga ya dauke kan motar daga kan kwalta ya nufi wata yar Siririyar hanyar kasa wacce a iya sanin Fa'iza hanyar bazata kai mutum ko ina ba sai cikin wasu dogayen tsaunuka da ada can duk karshen sati sukan zo gurin suda malamin su Mr. Ade wanda ke koya musu ILMIN kimiyar sammai da kassai.
Lallai Kam ina Ganin kayi batan kai darling wannan hanyar ba ita zata kaimu city hotel ba nan fa hanyar tsaunuka ce Fa'iza tace tana duban fuskar sa cikin mamaki.
Nace dake nasani ko! Labaran yace da ita cikin wata irin murya data jefa zuciyar Fa'iza cikin rudani shin tsawa taji yayi mata ne kokuwa cikin kakkausar murya yafada? Kwakwalwarta ta rikice batada tabbacin abinda taji ita dai taso taji kamar tsawa ya buga mata to amma zuciyar ta ta kasa imani da hakan.
To amma Darling me zamuyi agurin duwatsu.? Fa'iza ta sake tambaya wannan karon a tsorace hakance to ta tabbatar mata cewa ko shakka babu dazu tsawa taji yayi mata.
Menene aibun duwatsu ke baki son ganin dogayen tsaunuka? Ai gurare ne masu dadin shakatawa. Labaran yace batareda ya dubeta ba domin yasan tana ganin fuskar sa zata fassara a abinda ke yawo cikin mummunan zuciyarsa.
Oh darling kai da kace city hotel zamuje mu tattauna yaushe to zamuje wajen wasu duwatsu bakaga gurin ba fa duk busassun bishiyoyi ne da kwazazzabai mun sha zuwa gurin da malamin jogirafin mu babu wani abin jin dadi agurin.
Meyasa ki tsammanin bazakiji dadi agurin ba? Labaran ya sake tambayar ta batareda ya dubeta ba. Tuni har sun fara shigowa cikin manya manyan duwatsun masu tsayin gaske dake barazanar rikitowa akan doron kasa a kowane lokaci.
Dar....ling gaskiya gara mu tafi inda mukayi niyya kasan fa idan muka wuce karfe goman dare waje sai asirina ya tonu

Please Login or Register in order to submit comment