Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murmushi bata karasa ba Rakiya ta fashe da dariya cikin murya kasa kasa.
Kai amma dai yau Wallahi ikram kin bani mamaki abinda ban taba zato ba bankuma taba ganin kinyi ba yanzu kece wacce ko sanarin bakya kulawa sosai shine kuma yau harda yimin nunensu? Ikram tayi murmushi adaidai lokacin da suka kaw daf da inda ake fakin din motoci akofar kantin sannan abin kaddara sai ta dan jingina ajikin motar ilyasu tana duban kawarta cikin murmushin da rabon rakiya taga irinsa a fuskarsa ikram tun soyayyarta da saurayinta na farko wato Marigayi ALHASSAN.
Lah! Ikram meye kuma na tsayawa anan muda muke sauri agabanki fa mama tace mu koma gida da wuri gashi yanzu har wajen shida saura Rakiya tace.

Mu bari su fito rakiya. Ikram tace har yanzu bakin ta na zubar da murmushi.

ME YAKE SHIRIN FARUWA NE AWANNAN BABIN?

IKO SAI LILLAHI......CUTA TA DAU CUTA-23

Mu bari su fito Rakiya.
Ikram tace haryanzu bakinta na zubar da tattausan murmushin. Rakiya tadubeta cikin kaduwa domin ganin da safiyar ranar nan fa aka kawota daga makaranta saboda kaduwar mutuwar kawarta fa'iza sai gashi kuma yanzu yan sa'o'i kadan ganin saurayi yadawo da ita cikin walwalar da aka dade ba'a ganta aciki ba.

Wanne ne daga cikin nasu? Rakiya ta tambaya baki bude.
Na daga nan hakan dan dogon.
Ilram ta amsa mata gamida nuna su labaran da bakinta adaidai lokacin dasu kuma suka shige cikin kantin basu ma san abinda ke faruwa ba.
Ikram amma kinga dai magariba ta karato fa yakamata mu shiga mu sayi abinda zamu saya mu wuce gida kada mominki tayi fada. Ikram ta gyara jakarta dake makale a kafadarta ta dubi motocin dake ta zirga zirga abakin titin dake gaban kantin sannan ta rike kugu cikin annashuwa tace.
Rakiya bari su fito wallahi inna kalle shi kirjina har bugawa yakeyi....
Kina nufin kice min wai ke da gaske son sa kikeyi?
A'a tsokanarki nakeyi ikram tace cikin dariya.
Kinga dan Allah ikram muyi magana seriouse sonsa kikeyi? Rakiya ta sake maimaitawa.
Uhm to kina iya kiran abin haka Rakiya ikram tace akwai wani yanayi a fuskarta irin na mutumin da zuciyarsa ta koma ga tunanin wani abu daya faru acan wani shudadden zamani daya wuce.

Rakiya nasan zakiyi mamaki dan jin haka amma wallahi idan nace dake saurayin daya shiga kantin nan yanzu ba sonsa nakeyi ba to na yaudareki nakuma zalunci kaina dan Wallahi da ganinsa naji yafada min zuciya kamar sartse. Ta danyi shiru tana duban rakiya ido da ido.
Kyakkyawa ne rakiya kuma ba wai abanza nake son sa ba kinsan dai tunda nake bantaba kaunar wani dan adam ba adoron kasa kamar Alhassan... Allah yajikansa kinsan kuma mutuwarsa tana daya daga cikin abubuwan da suka tauyeni bana yawan iya kula samari.... To amma da kinga wannan saurayi sosai da bazakiyi mamakin wannan kauna tawa ta lokaci guda agareshi ba domin kamarsu daya da Alhassan tafiyarsu kallonsa dariyarsa murmushin sa ke hatta numfashinsa ina tsammanin irin na Alhassan ne.
Rakiya tayi ajiyar zuciya.
Tab yau naga ta kaina ni rakiya yanzu kina nufin kice min duk wannan abubuwan da kika lissafo duka awannan dan lokacin kika lura dasu?
Kwarai kuwa kuma ni fa daman tun kafin mu tsallako titi na hango su suna fitowa daga cikin motarsu.
Wacce motar rakiya ta tambaya.
Wannan motar mana da muke jiki.
Ah! To zo mu bar gurin Ikram ta girgiza kai.
To kina nufin kice magana zakiyi masa ki tallata kanki kokuwa? Rakiya tace cikin daga murya. Hakika ranta yafara baci da irin wannan canjin halayya na bazato babu tsammani daga kawarta. Ga mamakinta saitaga ikram tayi murmushi.
Ba tallata kaina zanyi ba rakiya kisa ranki a inuwa amma inason ki sani ban barin gurin nan sai nagaida shi......
Talla kenan fa......
Yan matan biyu sukayi shiru lokaci guda sa'ar da suka hangi su labaran suna fitowa daga cikin kantin.
Ikram taji wani abu kamar katon dutse yana safa da marwa tsakankanin kirjinta sa'ar da ta dubi kyakkyawar fuskar Labaran.
Ilyasu ya rike jakar leda biyu cike da kayan tande tande da lashe lashe haka shima labaran dauke yake da farar jakar leda amma guda daya. Ahaka suka fito daga kantin fitowarsu keda wuya sai ilyasu yaga labaran yayi turus ya tsaya kamar wanda ya fada cikin fasassun bulullukan kasa. Ilyasu ya juyo cikin mamaki ya dubi labaran.
Lafiya ka tsaya cak kamar an taka maka birki.
duba jikin motar ka... Gani ilyasu gaskiya ne ko kuwa idanuna ne suke fadamin karya. Ilyasu ya bushe da dariya yace.
Wallahi labaran kafara zama soko to yanzu me ye abin wani tsayawa dan yan mata sun tsaya ajikin motarmu kasani ma ko neman adauke su suke mu ai ta fadi abanza rabo na Minallahi tsuntsu daga sama gasashshe ai kawai mu karasa mu tsarasu mu rudasu mu yaudaresu mu kuma wuce dasu gida kai tsaye. Bakin mu alaikum dan samari.....
Amma sa'ar da ilyasu ya gama wannan surutu yaga kamannin labaran ko sauyawa basuyi ba saiyaji gabansa ya fadi sannana akaro na farko sai yayiwa labaran tambayar da tun dazu yake son yayi masa ita amma gudun zuciya ya hanashi fada.
Labaran ko kayi shaye shaye ne mai yawa dazun?
Labaran ya dube shi bakinsa na rawa yace.
Nima abinda nake tambayar kaina kenan....
To amma duba min yan matan can dake jikin motarmu da kyau kagani in har doguwar can ba ikram bace to ina kyautata tsammanin haukace... Take neman ta sameni. Jakar dake hannun ilyasi na rungume ta subuce.
Ikram!!! Ya kira sunan cikin daga murya da har yasa mutanen dake shiga suna fita daga cikin kantin suka juyo suna kallonsa. Ya kurawa inda yan matan suke tsaye idanu. Lokaci guda kuma yana tunanin hoton daya gani agurin labaran ko shakka babu ikram ce jikin motarsu atsaye kai wannan abu da ban mamaki yake.
Wall....Wallahi itace labaran tabbas Ikram ce.
To nagodewa Allah da ba hauka ce ta sameni ba nakuma gode Allah daya hadani da abar begena cikin sauki ni kam ko yanzu na mutu to burina ya cika.
Labaran yace fuskarsa tafara washewa nan da nan saji duk tunane tunanen kashe fa'iza dake ta dagula hankalinsa ya manta dasu zuciyarsa tayi fari Tasss.
Zo mu karasa gurinsu labaran yace da ilyasu baiyi nusu ba sai suka tattaro jakar data subuce yabi labaran suka nufi inda yan matan suke abinda ya fara bashi mamaki sa'ar da suka nufi yan matan shine yan matan sai kallonsu sukeyi kai kace daman su suke jira su fito.
Koda suka fara tafiya sai Ilyasu yace da labaran waccan ta kusa da ita din itace Fa'iza? Cikin labaran yayi kugi gabansa yafadi yaji kamar ilyasu ya watsa masa wuta a fuska.
Kai makaho ne kokuwa baka taba ganin hoton fa'izar bane?

********* ********** ****** ***********************

NEXT 24 LOADINGCUTA TA DAU CUTA-24

KAI MAKAHO NE KO BAKA TABA GANIN HOTON FA'IZAR BANE?

******* ******* ******* ***** ****** ***************

Yan matan biyu suka dauke kai gefe guda na bogi sa'ar da sukaga samarin sun taho ta inda suke kai in ka dube su saika rantse da Allah ba zancen samarin suke ba.

Sannunku yan mata. Labaran yace sannan lokaci guda yasaki kwararren murmushin nan nasa da baya amfani dashi ako ina sai airin wannan ranar. Da irin murmushin ne ya yaudari fa'iza afarkon haduwarsu da ita.

Oh!! Mun kare Muku mota ko. Ke rakiya zo muyi gaba zasu dauki motarsu. Ikram tace sannan saita dubi labaran ta jefe shi da murmushin farar madara tace dashi cikin murya mai amon sarewa.
Don Allah kuyi hakuri fa mun jinginan muku ajikin motarku.
Ah babu komai Wallahi ai mutum ma yasamu kyakkyawa kamar ki ta jingina ajikin motarsa ba karamar sa'a bace agareshi. Ikram ta fashe da tattausan dariya.
Wallahi ka burgeni da kalamanka.
Ni kuwa kin burgeni da fara'a da walwalarki.
Ilyasu ya dubesu cikin gaggawar ganin soyayya na kulluwa cikin gaggawa kaikace cikin wasan kwaikwayon yan koyon da basa yarda da gyararraki ba.
Ni kuwa hirar kuce ta burgeni. Labaran da ikram suka bushe da dariya sannan ne to Rakiya ta dubesu sannan tace akaro na farko.
Nikuwa kaine kawai ka burgeni idanunta akan ilyasu hakanan abinda ta fada bawai kawai a fatar bakinta ya tsaya ba har cikin zuciyarta. Suka fashe da dariya su duka hudun jin abinda rakiya tace.
To tunda dai kowa ya burge kowa bai kamata ba mu barka anan saiku shigo mu kaiku gida. Ikram ce tafara shiga gidan baya. Rakiya tayi kokarin itama tashiga gidan baya na motar su zauna tare da kawarta amma sai labaran yayi sauri ya shige gidan baya sannan yace da rakiya.
Shige gidan gaba ki zauna da wanda ke burgeki suka sake fashewa da dariya cikin farin ciki da annashuwa sannan sai ilyasu ya tuka motar suka tafi kowa na hira da wanda ke burge shi.
Abayan motar sa'ar da suka hau kan kwalta suna tafiya sai labaran ya dubi ikram yace cikin murmushi.
Ko sunanki bansani ba.
Ikram ta lumshe idanu tana murmushi sannan ta kalle shi da fararen idanunta ta harare shi tace. To ai kaima bakafada min sunan ka ba.
LABARAN SUNANA. Ke kuma yaya sunanki?
Da'ace idanun labaran basu rufe da masifar soyayya ba to da yaga subucewar tattausan murmushin daga fuskar ikram sa'ar dayace sunansa Labaran to amma bai kula da hakan ba.
Sunana Ikram tace dashi labaran yayi mata murmushi yana mai nuna farin cikinsa karara saboda jin sunanta dayayi kai kace daman can baisan
Sunan kenan ba.

Ikram ta fara tunanin zuci sa'ar data tuna da tambayoyin da jami'an tsaron sukayi tayi mata akan kashe kawarta fa'iza da akayi. Jin sunan labaran shi yadawo mata da tunanin marigayiya fa'iza.
LABARAN tasake maimaita sunan cikin zuciyarta ko shakka babu wannan shine irin sunan wanda yan sandan suke nema ruwa ajallo shine kuma wanda akace ya kashe kawarta fa'iza to amma wannan ai abin begenta ne ikram tace cikin zuciyarta sannan saita sami kanta tana mai nadamar inama ace ba sunan abin begenta labaran ba. Haba gashi dai kyakkyawa mai kamannin mutunci da kamala amma da sunan mugaye inna aure shi gaskiya darling kawai zanke cewa dashi.

Ikram! tayi firgigit tana dubansa tunanin da take shi ya mantarda ita cewa ashe ma akusa da ita yake ta mance dashi.
tunanin me kkeyi? Labaran ya tambaya adaidai lokacin da suka shigo layin gidansu Ikram.
Ku ajjemu anan idann kun karasa damu kofar gida babanmu fada zaiyi. Rakiya tace da ilyasu adaidai lokacin da taga anza kofar gidan. Ilyasu ya taka burki sannan yajuyo yace dasu labaran.
Romiyo da Juliyat saiku farka ko.
Ina zuwa dan Allah kuci gaba da hirarku mana minti daya bari mu gama wata magana ni da ikram sai mu sallame su tunda magariba tayi inyaso gobe sai mu dawo labaran yace da ilyasu baijira amsarsa ba saiyake komawa kan Ikram.
Umhum ina saurarenki tunanin me kikeyi ikram ta kanne idanu cikin murmushi tace.
Kai ba fa wani abu bane Wallahi tunanin wata kawarmu data mutu nakeyi. Gaban Labaran yafadi.
Ayya wacece wannan rashib lafiya tayi? Labaran yace gamida dasa alamun taysayi a boyayyiyar fuskarsa.
Wallahi abin dai ba'a magana abu saikace a fim wani tsinannen saurayinta ne da baya son cikawa da imani yazo har makaranta ya dauketa kawai sai gawarta muka tsinta awani kogon dutse da muke ziyarta duk karshen wata.
An kasheta......kwalla ta fara sartu akan kumatun ikram.
Allah ya jikanta... Labaran yace shi kansa saida yaji kamar wani katon takunkumi aka sawa bakinsa. Ikram ta dubeshi tace.
Ameen in Allah ya yarda ai sai an kama shege azzalumi allah ya tona asirin tsinanne. Labaran yaji kamar an kwara masa ruwan zafi tunda yake arayuwarsa bai taba jin maganar data kona zuciyarsa kamar wannan ba. Akaro na farko duk saiyaji ya tsani kansa. Yafara nadamar inama tun fayake ba'a halicce shi ba. Wacce yake kauna fiyeda kowa aduniya ita take zaginsa da tsinewa wannan abu ya tafasa zuciyarsa.
Gaskiya ba zan sake fadar sunan ka ba. Saidai ko ince maka... Darling. Ikram tace cikin jin kunya. Jikinsa na rawa yace.
Dan me kikace haka fadin sunana laifine? Idan kika kirani da labaran kin faranta min.
Babu sunan dana tsana arayuwata ayanzu kamar LABARAN.
Kamannin labaran suka sauya gabansa ya fadi.
Kada kayi zaton muzantawa ce darling tunda nake bantaba ganin wanda kaunarsa da begen kasancewa tare dashi har abada ba ya mamaye zuciyata kamarka amma kasan abinda yasa na tsani sunanka? Labaran ya girgiza kai bakinsa abushe.
SUNANKU DAYA DA WANDA YA KASHE FA'IZA.

Shin kai baka karanta jarida ne??
Ai labaran yana nan akan kowace jarida ba'a fi awa biyu ba jami'an tsaro suka sani agaba da tambayoyi tunda wai nice babbar kawar fa'iza wai me yiwuwa zan iya sanin sunan wani saurayin ta wanda suka ce tabbas shi YA KASHETA SUNAN SA LABARAN. Irin naka shiyasa nace na tsani sunan ka!!
Maganar data fada tamkar ruwan batir ne aka digawa zuciyar LABARAN.CUTA TA DAU CUTA-25

MAGANAR DATA FADA TAMKAR RUWAN BATIR NE AKE DIGAWA AZUCIYAR LABARAN.

TARA 9
Karfe uku na daren ranar. asaman kan rufin dakin da su labaran ke kwance wasu mutanen boye su biyu suka fara jayayya. Wadannan aljanu basuda kyan gani domin dayan dogo ne tankwararre kamar baka kawunansa shida kowanne kai kuma yanada baki biyu ajikinsa. Kafafunsa siri siri ne kamar tsinken sakatar hakori hakanan kunnuwansa faka faka ne abin mamaki kuma dasu yake amfani wajen tashi sama kamar fukafiki shekarar wannan aljani dubu uku da dari biyar.
Abokin jayayyar tasa saurayi ne dan shekara dari biyar. Hakanan shima kamanninsa kusan irin na wancan gayyar tsiyar ne to saidai shi wannan me yiwuwa yadan fi wancan kyawun sura domin shi Allah yasa yanada dogayen kahonni zaga zaga atsakiyyar kansa kamar tabare kuma duk lokacin daya buda bakinsa saiya dinga aman kudaje.

Ka hakura ka rabu dashi DAN TSAMAGE kai kacika naci da taurin kai haka ma fa rannan nayi nayi dakai ka kyale shi amma saida kai ta tsorata shi. Tsohon aljanin nan dan shekara dubu uku da dari biyar dinne yake cewa dan shekara dari biyar din.
Gaskiya DAN DAMISHERE dama ka daina bata bakinka kayi domin tunda ya kashe abar kaunata saina tagayyara shi haba ka tuna fa saida na auri kakar kakarta na auri kakarta na auri uwarta hallau kuma nazo na aureta kuma kai kasan babu wacce nake so kamar fa'iza domin da ace bata mutu ba da bazan bari ta auri kowa ba amma saan shegen ya kasheta to kabar ni dashi Dan Damishere ya kada manyan kunnuwansa wanda atake agurin suka tashi wata bakar guguwa mai karfi tayi yamma. Sannan yace kaidai ka kyale shi mana nace dakai nima na taba auren uwarsa kuma rabi aka haife shi domin ubansa yanada rauni bayason yin addu'a yayin da suke gawa da mahaifiyarsa shiyasa nima na samu dama har aka sami cikinsa dani. Don haka kaga ya kangare yazama cikakken marar imani don rabinsa na mutum ne rabinsa kuma MU.
Bashijin wata magana in ba tamu ba to shiyasa nace ka rabu dashi don inka kyale shi ma to ba albarka zaiyi ba tunda na gama dashi tun da yana gudan jininsa dan tsamage ya girgiza katon kansa mai kahonni yace.
Na face dakai saina karasa tagayyara shi to kabar ni mana kufa tsofaffin nan yan nema masu tsage tsagen kafafu kun cika takurawwa samari.
Bahaka bane Dan Tsamage ni ganyi bata lokacin ka kawai kakeyi akansa da haka me zaihanaka kaje ka auri kawarta Ikram ai itama kyakkyawace.
Kai rufamin asiri ko kake na kone kenan Kurmus.? Dan tsamage yace.
Ai da ka taba wannan gara ma ka taba garwashin wuta domin yarinyar nan kullum cikin karatun alkur'ani take da yan addu'o'i domin duk lokacin da zan wuce zuwa kasar rasha ta saman gidansu nake wucewa da suba sainaji tana karatun alkur'ani gashi kuma shegiyar ita ko dan gashinta ma waje bata bari ballanata ma mu sami abin dafewa. Ai wannan kam ni tafi karfina dan ko kai kaje gurin wannan ikram din sai wannan kahon naka ya kone kurmus uban mita ni dan Allah kyaleni inyi abinda yakawoni gashi har asuba ta kawo kai. Dan Damishere yayi sama Fuuuu yana cewa.
Ai saikaje kayi tayi shekararka dari biyar kawai aduniya amma harka koyi girman kai da raina shawarar na gaba dakai? Dan Tsamage yafashe da dariya sannan saiya girgiza nan da nan sa rikide yakoma Fa'iza sannan sai yayi tsalle ya fada cikin dakinsu Labaran ta cikin rufin dakin.

****** ********* ******* ****************** ********

INAFATAN ZAMU SHA RUWA LAFIYA YAN UWA MASU ALBARKA

NIMA BARI NA BARKU KU SARARA INYASO MA CIGABA DAGA INDA ALJANI DAN TSAMAGE YA DIRGA DAKIN.CUTA TA DAU CUTA-26

NAN DA NAN YA RIKIDE YA KOMA FA'IZA SANNAN SAI YAYI TSALLE YA FADA CIKIN DAKIN SU LABARAN TA CIKIN RUFIN DAKIN.

******* ***** ***** ***** *** ************* ******

Lokacin da suka bari gidansu Ikram basu iya barci da wuri ba aranar badon komai ba kuwa sai dan irin tunane tunanen dake addabar kowa daga cikinsu.
Har karfe dayan dare basuyi barci ba Ilyasu na kwance yayi fakare yana tunanin mutuwar da akace fa'iza tayi to amma duk ba wannan bace tafi damunsa domin haduwarsa da rakiya ta shafe wancan yar kwayar son fa'iza data dan darsu acikin zuciyarsa abinda yafi damunsa shine irin halin dayaga labaran aciki atun sa'ar da suka baro gidan duk kuwa da cewa abinda yakamata yaga labaran aciki shine walwala tunda dai yau yayi ido biyu da abar begensa Ikram.
To amma maimakon haka har suka zo gida labaran na tsumma hakanan ya nemi labaran dasu fita yawon dare su dan zagaya bariki amma labaran yace yatafi shi kadai kawai.
Ilyasu yayi mamaki sa'ar daya dawo yaga karfe goma sha biyu ya tarar da labaran kwance yana ta sharbar kuka.

Meke damunka ne?
Kada ka dameni! Kai baka iya ganin abune kayi shiru tun daga wannan mummunar amsar daya samu ilyasu bai kuma buda bakinsa ba har barci ya dauke shi yanata tunanin sabuwar masoyiyarsa rakiya. To amma abin mamaki shine sa'ar da barcin ya dauke ilyasu baiyi mafarki da rakiya ba sai fa'iza. Wai tana ta kiransa cikin fara'a a mafarkin tana cewa ZO GARENI ILYASU.
Amma sa'ar daya nufeta saiyaga gaban rigarta ajike sharkaf da JINI.

Labaran kuwa sa'ar da barci ya daukeshi zuciyarsa da kwakwalwarsa arikice suke.
Jin cewa yan sanda na nemansa ruwa a jallo shiya narkar da dukkan wani mafarki na mallakar ikram agareshi.
Yayi mamakin yadda yan sanda suka gano shi haka kuma da wurwuri ya zargi kansa da wauta wajen boye gawar fa'iza cikin kogon da har mutum zai iya shiga. Hakika kam shi yasan tafiyarsa tazo karshe domin yasan ko badade ko bajima yan sanda zasu cimmasa dan haka kafin barcin ya dauke shi saiya yanke shawarar barin garin gobe tun kafin jami'an tsaro su cafke shi. Da a cikin yan sa'o'in da suka shude kafin yayi ido biyu da ikram to da ba zai damu da wai yansanda na nemansa ba domin shi daman tuntuni yaji ajikinsa cewa yana daya daga cikin mutanen da basu da sa'ar duniya dan haka mutuwa ma bazatayi masa wata barazana ba domin yasan ko da jami'an tsaro sun kamashi ma karkarinta ayanke masa hukuncin kisa to saime tunda babu abinda ya bari.
Amma ayanzu hakika abubuwa da dama sun faru cikin awowi ashirin da hudu kawai. Tabbas yanzu bai iya yarda akamashi akuma harbe shi ko rataye shi ikram tasami labari ba. Idan yabari haka ta faru to hakika yaci amanar masoyiyarsa.
Wannan shi yasa shi yanke shawarar guduwa amma yayi alkawarin kafin yatafi dole ne saiya biya ta gidan su ikram yayi mata ganin karshe koda tunanin hakan yazo masa saiya tashi zaune alokacin tuni har barci ya dauke ilyasu.
labaran ya nemi takarda da biro ya rubuta wata yar gajeriyar wasika zuwaga abar begensa Ikram sannan saiya linketa ya tura acikin aljihunsa.
Akaro na farko tun sa'ar daya sami labarin yan sandan na nemansa saiyaji dan dadi dadi aransa domin akalla dai zaiyiwa masoyiyarwa wani abu wanda dai kota tsine masa to kuwa bazata manta dashi ba kuma akalla.......
Akallai dai tace wannan tsinannan ne yai min wannan kyautar.

Da wannan tunanin barcin ya dauke shi.
Sa'o'insa biyu da fara barcin saiyaji an tika masa kulli tim!! Labaran ya farka a gigice.
Lafiya.... Wayyo Allah atsaye akansa tanayi masa murmushi har yanzu sanye da kayan nan daya kasheta dasu ajikinta FA'IZA CE.

Idanuwan labaran suka zazzaro kamar idanun kwado cikin kaskon tafashashshen mai.
FA'IZA... FA'IZA KECE?
Uhm nice labaran me kuma ya hakada da kawata ikram itama din kasheta kake son yi?
Uhm... Uhm... Uhm... Wall... Wayyo Allah fa'iza dan Allah kiyi min rai...
Nayi maka rai dani na halicce ka? Ta dada tika masa dundu tim tim abaya labaran ya kwalla ihu lokacin dayaji bayansa ya sage kamar an doke shi da tabarya. Ihun dayayi shiya farkar da ilyasu daga nasa mafarkin.
Nayi ta wahalar dakai kenan bazan kashe ka ba labaran amma tunda ka kasheni to kai da kwanciyar hankali aduniya har abada saika gwammace mutuwarka da rayuwarka. Tana fadin haka saita dada Tika masa dundu tim abaya ta bace... Labaran ya sake kwalla ihu.
La..... Lafiya me ye hakane labaran baka san dare bane? Labaran cikin kuka ya dubi ilyasu Wallahi mafarki nake anata dukana.
Duka? Ilyasu ya tambaya.
Kwarai kuwa duka baka ji ba bayana wallahi kamar zai tsage gida biyu Ilyasu ya girgiza kai yana dube dubensa.
Lallai kam inajin labaran shaye shaye yake masu karfi yace cikin zuciyarsa.
Nima fa kusan mafarin nake yi yanzu ihun kane ya tashe ni Ilyasu yace.
Mafarkin me Labaran ya tambaya.
MAFARKIN FA'IZA.

******* ****** ******* ****** **********************

Karfe tara na safe sharoro ya isa asibitin tuni masinjoji sun gama share share sannan yan dubiya da marasa lafiya dake da dan dama dama sun fara zazzagawa cikin farfajiyar asibitin.
Sharoro yai fakin da motarsa sannan ya nufi inda dakin yake lokacin dayaje dakin baiyi mamakin ganin mutanen gidansa sun cika dakin ba.
Sharoro yace azuciyarsa lallai kam meyiwuwa maganar kwarangwal din mutumin nan gaskiyace mutanen jira suke ya mutu suci gadonsa. Ya'yansu banda matan kuma akwai katon mutumin nan da sharoro ya tarar jira wanda baison ko wanene ba.
Sannu da zuwa sharoro matan sukace gaba daya.
Yawwa sannunku dai sharoro yace lokaci guda kuma yana cewa cikin zuciyarsa saiku shirya kowacce shegiya ta kwashi rabonta domin yau Allah zai karbi addua'ar kuCUTA TA DAU CUTA-27

Domin yau Allah zai karbi addu'arku dan kuwa yau zan karasa muku shi izuwa Kiyama.

Yi sauri ka shiga tun wajen asuba daman yake tambayarka. jikin nasa ya tsananta katon mutumin yace da sharoro.
Zai samu sauki ai. Sharoro yace kusan a fusace sannan saiya shige dakin ya turo kofar ahankali ya rufe sannan saiya murda dan makullin ya kulle ta ciki.
Busasshen dattijon ya bude idanunsa da kyar sa'ar da sharoro yashigo dakin.
Yawwa... Yawwa sharoro kazo.
Uhm nazo.
To zauna mana dattijon yace yana duban sharoro ba zama yakawo ni ba fadi abinda kace zaka bani.
Sharoro yace sannan lokaci guda kuma ya durkusa agaban gadon mutumin.
Sharoro daga kaina zakaga wasika akarkashin filo na ka dauka kaje ka karanta ina rokonka don Allah duk abinda ka gani acikin wasikar nan ka aikata in na yine in kuma na yarda ne to ka yarda dashi. Dattijon yayi shiru sannan saiya kama hannun sharoro yace.
Allah ya maka albarka sai watarana in Allah ya hadamu dan banajin zan wuce yau shikenan sharoro kana iya tafiya daman sakon kenan da nake son baka komai yana cikin wasikar nan. Sharoro ya fusata sa'ar daya dauko wasikar daga karkashin filon yanzu daman busashshen tsohon nan dan nema da wuya kamar marikin garaya wasika kawai zai bari to kuwa yanzu zai gani.

Shin ka sami labari kuwa.? Sharoro yace da tsohon.
Labarin me ? Dattijon ya tambaya sharoro yayi kasa kasa da muryarsa yace.
FA'IZA TA MUTU NINE KUMA NA KASHETA KAMAR YADDA KAYI SANADIYYAR MUTUWAR MAHAIFIYATA.
Kaga nida kai babu bashi kenan. Idanun dattijon suka zazzaro jikinsa yafara rawa kamar zai mace.
Kada ka damu da saika mutu da kanka nima da kaina yanzun nan zan karasa ka. Yana fadin haka sai sharoro ya kama kan tsohon ya murde. Wuyan tsohon yayi wani irin sauti irin wanda idan ka balla kara zakaji yayi.
Sharoro ya dago kansa ahankali sannan yace.
Shege azzalumi sai kuma kaje kiyama ku hadu da fa'iza.
Dattijon ya haura kafa sau biyu sannan yace ga garin ku nan koda sharoro yaga ya karasa saiya juya ahankali ya bude kofar dakin sannan saiya fita tun kafin ya karasa kofar yafara zubar da hawaye. Matan suka taso cikin sauri tareda katon mutumin lokacin da sukaga sharoro yafito yana zubar da hawaye.
Lafiya yaya!! Suka tambaya baki daya.
Alhaji ya rigamu gidan gaskiya sharoro yace dasu yana goggoge idanu kamar bididdigi.

****** ******* ******* ****** ********************

Ikram ta dubi labaran cikin farin ciki da girmamawa sa'ar data biyo yaron daya tura ta same shi tsaye ajikin motar da suka kawo su gida jiya itada Rakiya.
Darling haka da sassafe

Please Login or Register in order to submit comment