Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a makaranta kuma.... Fa'iza ta kasa karasa abinda take son fada koda ta dubi fuskar sa saita sami kanta tana mai kokonto anya kuwa wannan shine labaran din daya dauko ta daga makaranta ne? Wannan mutumin dake zaune yanzu akusa da ita kamanninsa sun jirkice sun sauya tamkar yadda ruwa ke sauya wa yayinda aka watsa masa garin zabibi ko kusa ko.. Alama wannan baiyi kama da labaran din data sai ba ma'abocin fara'a da kirki da lallashi cikin tattausar murya.
Labaran ya ja birki ahankali tsakanin dogayen tsaunukan.bakajin komai agurin sai motsin busassun gayayyakin bishiyoyi dake gurin da iskar yammacin ke busawa gamida jefi jefin kukan tsuntsayen dake ta wucewa ta kan tsaunukan suna kokarin kaiwa ga gida kafin almuru ya shigo.
Labaran ya kashe motar sannan ya juya akaro na farko suka hada ido da Fa'iza nan da nan taji hanjin cikinta ya yamutse.
Wayyo nashiga uku. Ta kwalla ihu abinda gani a fuskar sa yaso yayi kama da irin munanan fuskokin ban tsoro dakan hana mata rintsawa cikin mafarke mafarken data yi lokacin sanyi to amma a wannan karan ba mafarki bane gaske abin ke faruwa.
Hannunsa daya akan sitiyarin motar dayan kuma rike yake da zundumemiyar wukar.
Yadubi Fa'iza wacce tuni tayi mutuwar zaune.
Wayyo...... Wayyo... Dan Allah....... Nashiga uku labaran me zakayi min? Fa'iza tace cikin kuka a firgice.
Kada ki damu darling... Labaran yace cikin wata irin busasshiyar murya dashi kansa ya kasa ganewa a matsayin tasa. Me.... Me zakayi min Fa'iza tasake cewa lokaci guda kuma tana matsawa can jikin kofar motar idanun ta akan wukar.
NACE DA KE KADA KI DAMU FA'IZA.
KASHE KI ZANYI AHANKALI CIKIN TAUSAYI BATAREDA KIN SHA WUYA BA.
Labaran yace...

******* ******** ********* **********************

KASH DATA YAYI TSIYAR KU YI HAKURI DAI HALLAU SAI MUN HADE A WANI LOTONCUTA TA DAU CUTA-10

Nace dake kada ki damu fa'iza. Kasheki zanyi ahankali cikin tausayi batareda kinsha wuya ba. Labaran yace.

****** ****** ******* ******* *******************

Kasheni zakayi? Fa'iza ta tambaya cikin kuka. Haba labaran me nayi maka? Labaran baice uffan ba saiya fara matsota da wukar fuskarsa tayi sharkaf da gumi sai diga takeyi kamar ledar kankara.
Bai ankara ba sai fa'iza tayi wuf ta bude kofar motar ta ruga aguje cikin tsaunukan labaran ya dubeta cikin kaduwa domin yasan idan ya barta ta tsere kokuma tayi ihu wani yaji to shi kam kashinsa ya bushe kenan hakan kuma mafarkinsa na dora hannunsa akan masu kyau yasha ruwa kenan.
Duk yadda za'ayi ka kasheta kada ka sake ka dawomin nan baka kasheta ba ka sani cewa kasheta din yanada matukar muhimmanci acikin shirinmu kana kasheta to shikenan mun tsallake kadangar farko kenan saikuma ta biyu wacce itace ta karshe. Jawabin dan farin mutumin yadawo garai garai afaifain zuciyarsa.
Labaran ya zabura yafice daga motar sannan ya rufa mata baya aguje hannunsa rike da wukar tsirara tuni ta bashi rata mai yawan gaske daga inda yake yana iya hangen fa'iza ta nufi can cikin tsakanin wasu tsaunuka wadanda tunaninta zata sami hanyar da zata mayar da ita bakin kwalta. Koda labaran yaga tabi wannan hanyar sai yayi turus ya tsaya yana haki sannan yayiwa kansa murmushi yace da kansa.
Bi ahankali dan samari daman ka gaji gashi rabonka da wani wasa na motsa jiki ka dade rabu da ita ta kai karshen dutsen nan babu hanya dole ne ta dawo da baya kaga sai ka labe ka cafketa cikin ruwan sanyi. Wannan tunani da zuciyarsa tabashi shiyasa labaran tsayawa sannan ya dane bisa wani dan madaidaicin dutse mai fadin gaske da siffa irin ta mutum ya boye kansa sanan kuma lokaci guda yana hangen fa'iza waace ke ta sheka gudu kamar zata tashi sama. Labaran ya laluba aljihunsa ya dauko karan sigari sannan ya cinna mata wuta ya busa hayakin sama abinsa yana tunani.
Ba'a banza ya bata kusan sati guda yana sintiri atsakanin tsaunukan ba. Tun sa'ar da farin mutumin yabashi izini ya dauke yarinyar daga makaranta yatafi da ita ya kashe.
Sai labaran ya fara tunanin to fa dole ne ya sami wani kebantaccen guri inda ba kowa ne ke zuwa ba. Hakan ita tasa yayi ta sintiri atsakanin gurin har yagano inda tsaunukan suke lokacin daya gano tsaunukan saida ya shafe sama da kwana biyar yana zazzagawa tsakanin gurin wanda hakan shi yabashi damar sanin cewa hanya daya da zata mayar da mutum kan hanya daga cikin tsaunukan itace hanyar da suka biyo a mota wannan shine dalilin dayasa lokacin daya ga fa'iza ta nufi cikin tsaunukan saiya tsaya abinsa yana bulbula hayaki sama domin yasan batada mafita....
Tunaninsa ya katse sa'ar daya hangi fa'iza acan kololuwar wani dutse ta fadi ruf da ciki.
Labaran ya dubi agogonsa sannan yayi tsaki yace wannan yarinyar fa bata min lokaci zatayi bari dai tun data fadi na lallaba na karasata. Tunanin hakan keda wuya sai yafara bin tsakanin duwatsun cikin sanda ya nufi inda take kwance wukarsa tsirara rike ahannunsa sai kyalli take acikin abin daya rage na daga hasken yammacin.

*** **** **** **** **** **** *********************

Fa'iza ta juya ahankali akan dusen jini na zuba daga hancinta sakamakon faduwar datayi sannan ga mamakinta saijin shawarar da kawarta Ikram tayi mata yafado mata.
Adaidai lokacin ne to taga kamar inuwa ta rufe ta. Fa'iza ta dago ahankali nan da nan numfashinta ya dauke jikinta ya sandare takuma kankame yar karamar jaka irin tasu ta mata akirjinta.
Don Allah kayi min rai labaran... Tace cikin kuka kada ka kasheni don Allah Darling haba labaran ka tausayamin mana kaunarka fa nake... Son ka... Bata karasa ba sakamakon wani abu dataji ya soki zuciyarta. Sannan wasu bakaken taurari suka rufe idanunta tabbbas kam tasan duhun mutuwa ne ke daukarta.

Labaran ya zare wukar daya soka daga kirjinta ya dube jikinsa na rawa toh!! Yau fa na fara kisan kai yace da kansa sannan sai ya lalubi aljihunsa ya zaro karan sigari akaro na biyu ga mamakinsa saiyaga tabar ta kwace daga hannunsa ta fadi akan dutsen sannan ta fara gangarawa ahankali.
Bi ahankali dan samari akwai fa sauran aiki fa agaban ka dole ne ka sami wani dogon dutse ka boye gawarta to in banda abin ka ma menene na rawan jiki tun da ka yi mai wuyar. Zuciyarsa ce ke bashi shawara.
Labaran ya sunkuya da niyyar ya dago gawar fa'iza adaidai lokacin ne to jakar dake kankame akirjinta ta bude iskar yammacin dake busawa ita ta taimaka wajen fadowar hoton zuwa kan dutsen labaran ya sunkuya ahankali ya dauki hoton sannan saiyaji tsigar jikinsa tayi yarr....
Hoton yan mata ne su uku atsakiyarsu Fa'iza ce to amma ta farko daga hannun hagun hoton ita tasa zuciyarsa bugawa.
Tunanin farko daya fara zuwa zuciyarsa shine da wannan ce akace ya kashe da bazai taba iya kasheta ba. Koda labaran ya daga hoton sama yasake kallonsa saiya tabbatarwa da kansa cewa tabbas yakamu da ciwon son wacce bai sani ba.
Yasake duban yarinyar da kyau saiyaga akusa da ita an rubuta sunanta IKRAM.CUTA TA DAU CUTA-11

Yasake duban yarinyar da kyau saiyaga akusa da ita an rubuta sunanta IKRAM.

UKU 3
Adab da inda kayatacce gidan nasa yake akwai wani katon lambu ma'abocin kayan marmari kamarsu gwanda fasadabur lemon zaki gwaiba kashu da dai sauran ire iren danginsu ma'abota zaki.
Banda kayan marmarin kuma lambun cike yake da tsuntsaye fal ma'abota daddadar murya da munana domin daya daga cikin tsuntsayen dake ziyartar lambun hardasu mujiya to amma sabanin sauran lokutan baya wanda mujiya ta saba bata barci da mummunar kukanta to awannan karon wata irin mummunar murya ce marar dadin ji sannan kuma mai wuyar siffantawa domin har sa'ar da labaran yayi firgigit ya farka a tsorace bai iya tantancewa ba cewa shin kukan tsuntsu yaji ko kuma kukan mutum?
Labaran ya yunkura ahankali daga kan gadon yatashi zaune jikinsa na rawa hakanan zuciyarsa sai harbawa takeyi kamar ta fasa kirjinsa tafito sararin Subhanahu wata'ala banda wannan kuma kansa sai sara masa yakeyi da matsanancin ciwon kai mai kama da dukan guduma acikin kwakwalwarsa.
Mafarki nakeyi ne. Labaran yace da kansa zuciyarsa nata wasi-wasi ya dada yunkurawa ahankali ya leka farfajiyar gidan ta cikin tagar dakin dake dab da inda gadon alfarmarsa yake. Labaran yaga ashe haryanzu ma da sauran duhun dare domin shi a tunaninsa ya dauka ma garine ya waye.
Labaran ya sake muskutawa kamar mace mai tsohon ciki sannan saiya tura hannunsa ahankali ga makunnar lantarkin wuta dake dakin. Labaran naso ya kunna wutar lantarkin koya sami damar ganin lokaci ajikin agogon bangon dake makale to amma tsananin tsoro da fargabar mummunan mafarkin ya hanashi.

Kai shashashan namiji meye na tsoro bayan aikin gama ya gama tunda dai ka kasheta yaya zatayi dakai? Wata zuciya ce ke cewa da labaran haka kuma hakan datace dashi ita tasa yayi ta yan maza ya kunna wutar dakin ya gauraye da haske.
Labaran yayi ajiyar zuciya gamida share zazzafan gumin da haryanzu ke zuba ko ina ajikinsa kamar ruwa. Ya daga kai ahankali ya dubi agogon dake jikin bangon dakin karfe uku da yan mintuna shin yaushe gari zai waye ne? Labaran ya tambayi kansa ko kusa ko alama labaran bai son ya sake komawa barci domin kuwa yasan in ya sake ya koma barcin to babu abinda zai hanashi sake mafarki da...... Tunaninsa ya tsaya guri guda domin labaran baison yayi imani da abinda yagani acikin mummunan mafarkin to amma ya zame masa dole ya yarda da cewa tabbas bada kowa yayi mafarki ba sai da yar budurwar nan daya kashe cikin duwatsu wato Fa'iza.
Labaran ya dada kankame tattausan mayakin dake jikinsa sa'ar da zuciyarsa taci gaba da dawo masa da yanayin mummunan mafarkin garai garai acikin faifan zuciyar tasa.

Acikin mafarkin babu zato babu tsammani sai labaran ya tsinci kansa yana ta sheka uban gudu cikin wata tafkekiyar gona wacce ke cike da dogayen ciyayi amma duk busassu labaran baisan dalilin gudun nasa ba to amma abin da zuciyarsa ke fada masa acikin mafarkin shine wata mata ce ke biye dashi abaya dauke da zungureriyar wuka tana kokarin cimmasa ga dukkan alamu kuma idan ta sameshi rabashi gida biyu zatayi. Labaran yaci gaba da gudu afirgice yanata keta ciyayin gamida haki kamar ransa zaifita to amma wani abin tashin hankali shine duk gudun dayakeyi saiyaji kamar ma aguri guda yake tsaye hakanan kafafunsa kamar akan iska yake tafiya yana cikin gudun ne bai aune ba sai kawai yaga wani katon dutse gingirin agabansa bakikirin dashi kama anyi masa wanka da bakin mai hakanan tsayinsa bashi misaltuwa da komai domin ya tokare sararin samaniya labaran yayi turus cikin firgice domin yasan gudu ya kare kenan yajuya da baya saiyaga doguwar budurwar tsaye akansa tana kyalkyala dariya hannunta rike da wukar sai kyalle takeyi kamar mudubi.
Munafiki ka gama gudun... Tace dashi cikin karaji sannan saita sake fashewa da dariya.
Dan......Allah kayi min rai labaran yace a tsorace yana kuka idanunsa kamar su fado.
Kashe ka zanyi kamar yadda ka kasheni nima bazan tausaya maka ba. Tana gama fadin hakan saita daga wukar sama tayi kan labaran da gudu zata daba masa a kirji.
Ah!! Labaran ya kwalla ihu a firgice sannan saiya farka.

Dan haka ayanzu da labaran ke zaune akan gadon yana tunanin mafarkin sai jikinsa ya sake daukar rawa sa'ar daya sake tunawa da inda ta daba masa wukar.
Idan har akwai abu daya da labaran bayaso arayuwarsa to mutuwace shidai yasan yayi sanadiyyar rasa rayukan wasu to amma idan akazo kansa to yafi koa tsoro wannan ita tasa ayanzu dayake zaune kan gadon ko labulen tagar dakin ya motsa saiya firgita domin a tunaninsa ko matar ce zata sake biyo shi.
Labaran yasake kallon fuskar agogon bangon haryanzu uku da rabi batayi ba yayi tsaki sannan kuma sai tunanin kyakkyawar budurwar daya gani ajikin hoto yasake mamaye zuciyarsa nan da nan yaji gumi ya sake rufe shi amma awannan karon sassanyan gumi ne mai tada tsigar jiki. Kai wannan abu ya zame min bala'i labaran yace cikin zuciyarsa.
Hakika zuciyarsa tayi masifar kamuwa da kaunar budurwar jikin hoton. Wanda hakan shiyasa zuciyarsa dulmiya cikin wani zuzzurfan tunani bai aune ba yana cikin tunani sai barci barawo ya sace shi
baifi mintuna talatin ba da fara barcin saiyaji an kwalla masa kira cikin wata irin kakkausar murya.
Labaran... Tashi gani nazo gareka!!! Labaran ya farka a firgice yace.
Wayyo Allah na... Nan da nan gumi ya rufe shi yayi fakare akan gadon ya kasa motsi yana zazzare idanu kamar barawon tagiya baiji motsin komai ba sai na numfashinsa dakuma tik tik tik din agogon dake jikin bangon dakin. Adaidai lokacinne to babban limamin masallacin unguwarsu labaran.....CUTA TA DAU CUTA-12

Wayyo Allah na... Nan da nan gumi ya rufe shi yayi fakare akan gadon ya kasa motsi yana zazzare idanu kamar barawon tagiya. baiji motsin komai ba sai na numfashinsa dakuma tik tik din agogon dake jikin bangon dakin.
Adaidai lokacin ne to babban ladanin masallacin unguwarsu labaran ya fara kiran sallar asuba na farko.
Akaro na farko kuma cikin shakeru goma sha biyu sai labaran yaji yana sha'awar zuwa masallaci. To amma ba sallah ce zata kaishi ba atunaninsa zuwa masallacin shi zaisa ya daina wannan mugun mafarkin.

Labaran yatashi zaune ahankali sannan ya sauko daga kan gadon ga mamakinsa saiyaji duk gwiwarsa tayi rauni babu wani karfi atareda ita kamar ma bazata iya daukarsa ba. Koda labaran ya mike tsaye sai hoton yan matan yafado atsakiyar dakin. Labaran yadubi hoton a tsorace saiyaga ashe hoton yan matan daya tsinta ne ajakar fa'iza to amma abinda ya dada firgitashi shine sa'ar daya dubi hoton saiyaga hoton fa'iza ya bace daga jikin kwalin hoton saina sauran yan matan biyu. Daya baisanta ba dayar kuwa wacce zuciyarsa ta mace akanta ne wato IKRAM.
Labaran na tsaye jiki na rawa yana duban hoton saiyaji an tabashi abaya ya juya a firgice a tsorace to amma baiga kowa ba sai inuwarsa.

**** **** ***** ***** ****** ***********************

Misalin karfe tara da rabi na safe. Dan farin mutumin da mutane sukafi sani da SHARORO yayi fakare akan lallausar katifar gadon alfarmarsa yana shafar dogon wuyansa mai kamar na fakara hakanan kuma yana duban katon akwatin gilashin wanda ke dauke da ruwa gamida ya'yan kifayen nasara sunata ninkaya acikin nishadi kaikace da gaske ne. Ba bingidar kwali bace harsashin ruwa.
Tun kusan asuba sharoro ke zaune agurin ko cikakken motsi bayayi kamar gunki abune mai wahala kaga wani na motsi ajikinsa idan ba girar sa kokuma bakinsa wanda lokaci lokaci yake motsawa muts-muts yana zancen zuci. Ga mai hankali da nutsuwa idan ya kalli sharoro alokacin zaisan cewa ba akwatin gilashin yake kallo ba domin zuciyarsa ta tafi gaba daya ga tunanin halinda labaran yake ciki awannan lokaci. Tun jiya sukayi da labaran zaizo cikin dare domin ya bashi labarin ko ya kashe fa'iza ko kuma bai kasheta ba domin ayadda suka rabu da labaran yayi masa alkawarin ko shakka kada yayi yau zai kashe masa ita.
Sharoro ya mike tsaye ahankali kamar wanda ke tafiya cikin mafarki adaidai lokacin da hannuna agogon dake dakin ya dunguri tara da mintuna biyar daidai. Lallai kam me yiwuwa ba lafiya ba sharoro yace cikin zuciyarsa. Sannan saiyaji wani bakin ciki ya soki zuciyarsa kamar zata fashe.
Bashi da wani buri aduniya daya wuce na ya rama abinda makwabcin nan nasu yayiwa mahaifiyarsa kullum idan ya rufe idanunsa saiya ringa ganin mahaifiyarsa sa'ar da take ta famar masifa akan kada atabashi alokacin dauake karami suna wasa da yan abokansa wasu lokuta kuma idan yana tunanin ko kuma idan ya rufe idanun nasa yakan hango hoton sa'ar daya shiga cikin kunci yaje gaban attajirin Alhaji Sabitu ya rokeshi taimako amma ya watso masa kasa aidanu kodayake alokacin ba'a riga an bashi labarin cewa shine yayi sanadiyar mutuwar mahaifiyarsa ba domin daya san da labarin da mutumin baije ga neman taimakon gare shi ba to amma kuma sai gashi kwatsam yau wai alhaji sabitu ya kirashi yace dashi wai dashi kawai ya amince fiyeda kowa wannan abu na da ban mamaki.
Sharoro ya katse tunaninsa sannan ya dubi agogo shin me ya tsaida labaran ne? Ya tambayi kansa. Gashi kuma lokacin zuwa gurin wancan matsiyacin attijirin yayi. Domin yaune sukayi dashi zai koma asibitin misalin goma na safe. Sharoro yayi murmushi sa'ar daya tuna da irin shakar da yake son yiwa busashshen mutumin dake kwance ba lafiyar. Bazan kashe shi ba saina fada masa cewa yarsa fa'iza na kasheta saiya dandani bakin cikin rashinta sannan na kashe shi shima ya dandani ciwon mutuwar bakin ciki kamar yadda mahaifiyata tayi.
Sharoro ne yake yiwa kansa mummunar alkawarin cikin zuciyarsa wanda kuma adaidai sa'ar ne aka kwankwasa kofar dakin.
Wanene? Sharoro ya tambaya zuciyarsa na harbawa zal'zal...
Wa kake tsammani? Akace dashi a fusace sannan sai kofar ta bude labaran ya fado dakin duk jiki na rawa fuskarsa sharkaf da gumi kamar yaga fatalwa.

******* ******* ******* ****** *********************

Sharoro ya dubi labaran a tsorace domin da ganin fuskarsa yasan cewa lallai wani mummunan al'amari ne yafaru.
Me yafaru? Sharoro ya tambayi labaran bai amsa masa ba sai ya nemi guri ya zauna sannan kuma ya hada hannayensa biyu yana duban kan tattausan kilishin da ya mamaye dakin.
Yi magana mana in kasa kasheta kayi ai sai kayi bayani ko amma kayi zugum kamar an gina ka da tabo. Labaran ya muskuta sannan ya dubi sharoro.
Na kasheta amma ta dawomin jiya da daddare.
Shaoro yayi masa kallon karen kulawa, yace.
Sakarci ka taba ganin mutum ya mutu ya dawo?
Uhm to imma ba'a tabayi ba to jiya anfara sharoro yayi sororo yana yiwa labaran kallon masu roro.
Labaran me ke damunka ne in ka kasa kasheta ne kayi menene na wasa da hankalina kuma? Labaran ya dago kai ya kalleshi ido da ido yace. Kada kayi shakkar komai na kasheta amma dai jiya bata barni nayi barci ba kadan ya rage ta sani na zautu.
Ban fahimce ka ba sharoro yace amma fuskarsa da alamun murmushin nasara domin ko shakka bayayi yasan labaran ya kasheta.
Tun kafin shigowar al'umuru na kashe ta tsakanin duwarwatsun dake kan hanyar makarantar. Wadanda na baka labarin na gano din nan.
Inajinka sharoro yace.
Yawwa. To ban dawo gida ba sai kusan goma na dare lokacin dana dawo na gaji dan haka sai kawai na kwanta nace bari saida safe nazo nayi maka bayani to inaCUTA TA DAU CUTA-13

To ina kwanciya kuwa saita fara bina wai zata kasheni kuma dana fara gudu......
Labaran yayi shiru lokaci guda domin shi kansa yaji kamar labarin nasa duk sakarci ne babu wanda zai yarda dashi. Sharoro ya fashe da dariya.
Shashashan jarumi kayi abinda ake so amma ka bari tunanin rashin sabo yana so ya tsoratar dakai haba. Aika gama min komai Wallahi labaran ya girgiza kai cikin shakka.
Dan baka ga abinda nagani bane shiyasa kake fadan hakan.. Me yiwuwa ba zaka yarda ba idan nace dakai har ta bata a hoton dana tsinta cikin jakarta lokacin dana kasheta. Alokacin hoton tane ita da wasu yan mata guda biyu amma sa'ar da hoton yafado atsakar daki jiya da daddare saina nemi hotonta sama da kasa na rasa.
Sharoro ya sake yasake fashewa da dariya.
Kai jinan dan samari bi ahankali kada ka zautu abanza babu gaira babu dalili. Ba wani abune ya saka duk ganin wayannan abubuwa ba sai rashin sabo saboda tunda kake baka taba kashe mutum ba in kuma baka yarda ba to daukomin hoton da ka tsinta.
Labaran ya dubi sharoro cikin rashin fahimta to amma ba musu saiya lalubi aljihunsa ya dauko hoton hannunsa na rawa kowa ya ajjiye hoton sai sharoro ya dauka.
Kace babu hoton ta aciki ya bace? Wannan ba ita bace? Labaran ya mike tsaye jiki na rawa ya leka hoton dake hannun sharoro ko shakka babu hoton fa'iza ne.
To... Toni na rasa abinda ya sameni... Labaran yace baki na rawa.
Kada ka damu nan da kwana biyu zaka warware na fada maka rashin sabo ne sannan saiya lalubi aljihunsa ya dauko wata takarda ya mikawa labaran.
Ga wannan cek din naira dubi dari biyar din data rage ne na kudinka daman nace dakai da zarar ka kasheta zan cika maka kudinka motar kuma ka rike na baka.
Labaran yaji kamar an zuba masa ruwan sanyi koda ya karbi cek din kudin saiyaji duk ya manta ma da abubuwan daya gani a daren jiya. To amma duk da haka lokacin da ya mike tsaye saiya lalubi aljihunsa ya dauko wasu yan makullaye ya jefawa ssharoro su yace.
Ga makullan gidan ka nan bazan sake kwana ciki ba me yiwuwa ma gidan ne da kwankwamai suke son zautani. Sharoro ya dauki dan makullin gamida dariya.
Ka cika camfe camfe kaidai kawai ka tsorata ne ya danyi shiru kamar yana tunani sannan saiya dada da cewa.
Nan da sati biyu saika dawo kafin nan nagama da wannan tsohon shegen. Abinda na danne zan ajje maka rabonka koda yake dai nasan dole ne abin ya dauki lokuta to amma dai ban kasheshi sai ya damka amanar ahannuna sannan zan kashe tsohon macuci ya karasa maganar cikin karaji. Labaran ya mike tsaye.
To ni zan tafi saina dawo kenan?
To labaran nagode sosai inkuma ka sauya shawara duk sa'ar daka bukaci gidan kana iya dawowa ka amshi dan makullin daman su biyu na saya wannan danake ciki dashi. Labaran ya girgiza kai.
A'a bana bukata sannan saiya juya da gudu gudu yabar dakin da niyyar tafiya banki domin ya maida takardar da aka bashi ta cek zuwa TSABA.
Koda labaran ya fice sai sharoro ya nufi karkashin filon alfarmar dake kan gadonsa ya zaro hoton da akullum saiya kalleshi sau shida arana. Hotonsa ne shida mahaifiyarsa tun yana karami koda ya duba hoton saiya fara kuka
kada ki damu umma da sannu zan rama miki abinda yayi miki wayyo Allah ummi dama kina da rai ki nuna min mahaifina zanso na sanshi. yace cikin kuka.

HUDU 4
Wata doguwar mota fara kirar mutanen nahiyar shiya ta salalo tsakiyar makarantar kamar macijiya saboda kyan tafiya.
Tun kafin tagama tsayawa agindin bishiyar da ta yiwa tsinke daliban mata suka dauki sosa suna tafi da murna domin kusan awa biyu kenan suna jira sai yanzu tazo.
Wani dogon malami mai dogon gemu mai karangiya kamar burushin wanke kwalbar kunun zaki. Ya leko daga ofishin firinsifal dauke da wata katuwar jaka mai siffar kalangu sannan lokaci guda kuma ya bugawa daliban tsawa.
Kai kai meye haka baku taba ganin mota bane? Wata daliba tayi kasa kasa da murya tace.
Yau muka fara ganin irin wannan shiyasa.
Wacce marar kunya ce ke magana? Malamin ya tambaya a fusace daliban sukayi tsit babu wanda ya amsa malamin ya tsura musu idanu yana kokarin gane mai maganar to amma in ya hango kamar wata tana dariya saiyaga ta kusa da ita ma dariya take hakanan idan ya hangi wata tabata rai saiyaga ta kusa da ita ma ranta abace yake. Bai sami mai maganar ba.
Wannan bashine karo na farko ba da daliban suka saba wasa da dogon malamin ba badon komai ba kuwa sai dan idan yaga dama yakanyi wasa da daliban har dariya ma yana koya musu darussa.
Wannan shiyasa daliban suke son darasin malam habibu zago wanda shine malami na biyu dayake koya musu jogirafi ilmin sanin yanayin sama. Dan haka wannan rana da daliban mata suka taru suna ta doki tana da matukar muhimmanci agaresu domin rana ce da malam habibu zago yake kirkira lokaci lokaci domin daukar daliban zuwa cikin dan karamin daji ma'abocin duwarwatsu domin nuna musu irin yanayin halittun Subhanahu Wata'ala dake doron kasa wannan kuwa sun hada ne harda koguna koramu da duwarwatsu da ajujuwansu siffarsu da kamanninsu wanda duk mafi yawanci saidai ayi ta basu labarin a rubuce ayayin da ake darasi batareda wasusn su sunma taba ganinsu ba. Kai wasu ma idan an fadi yadda kamannin duwarwatsun suke har karyatawa sukeyi to wannan ita tasa malam habibu zago yake kirkirar irin wannan rana dan kara wayar da kan daliban.

Idan kun gama hayaniyar saikubi layi ku fara shiga motar malam habibu zago yace danan da nan daliban suka fara shewa lokaci guda kuma suka kafa layi wasun su kuwa sai kokarin sakawa kyamarorin daukar hotonsu batir da fim sukeyi domin al'adar dalibance duk ranar da akaje wajen duwarwatsun sai sun......CUTA TA DAU CUTA-14

Domin al'adar dalibance duk ranar da akaje wajen duwarwatsun sai sun dauki hotuna domin tunawa da tarihi.
Duk da wannan hayaniyar da liban keyi acan gefe guda kuma Ikram ce tsaye cikin tagumi babu alamar walwala afuskarta balle ace ma tana murna da tafiya. Abinda yake tayar mata da hankali shine tun jjiya da

Please Login or Register in order to submit comment