Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawarta fa'iza ta fice ance haryanzu bata dawo ba. Abinda ya dami ikram kuwa da'ace saida sukayi nisa da fa'iza jiran domin hanata fita yawan banza da lalatattun samari to amma duk da haka dan abin ya dameta dan kuwa tunda fa'iza take bin samari yawace yawacen banzanta bata taba kwana awaje ba sai wannan karon. To gashi yanzu har lokacin fita darasin su mai matukar muhimmanci yayi amma shiru babu ita tasan kuwa da fa'iza na nan to da babu abinda zai hanata zuwa domin itama tana son darasin duk da cewa lokaci lokaci takance da Ikram. Nifa ban fiye son ganin wadannan duwarwatsun ba wallahi ni sam sam basa birgeni idan na kallesu sainaji gabana yana ta faduwa. Tunanin ikram ya karse adaidai lokacin da muryar malam habibu zago ta ratsa dodon kunnenta yana cewa
(Listing Student) afara shiga ahankali (Please one by one dont rush in you may hurt yourself).
Koda daliban suka fara shiga motar sai ikram taji gabanta na faduwa ras ras ras kamar ana kidan kwarya atsakiyar kirjinta.

***** ****** ******* ****** ****** ***************

Dajin tsit bakajin komai sai hayaniyar daliban gamida jefi jefin kukan tsuntsaye nan da can hakanan kuma lokaci lokaci sukan dirga akan doron doguwar motar safa data kawo daliban sunata gada abinsu domin dayawa daga cikin tsuntsayen sun dauka wata sabuwar bishiya ce kokuma bakuwar halitta mai dadin hawa da sauka adajin.
Acan kuma tsakiyar manya manyan duwarwatsun malam habibu zago ne ke zazzagayawa da daliban yana ta bayani.
Wancan dan dogon dutsen da kuke gani mai launin jaja-ja tsatsa-tsatsa din can to shine kashi na uku na rabe raben ajujuwan duwarwatsu dana sha yi muku bayani acikin aji. Wata daliba mai suna Rakiya Rabiu ta daga hannu.
Sir shine (Metamophic Rock) ta tambaya.
Kwarai kuwa shine kunsan shi wannan dutse yana samuwa ne ta hanyar sauya kamanni ne daga wadancan ire iren duwarwatsun guda biyu dana fara yi muku bayani abaya wato Igoneos) dakuma (Sedimentary) wannan sauyawa danace muku abaya sunayi ta samo asali ne sakamakon canjin yanayin dake faruwa ashekara Alal misali ruwa iska aradu da walkiya su suke sauya shi ya rikide kamanninsa su koma tsatsa tsatsa wasu lokutan kuma zasu je bakin kogi zakuga irin duwarwatsun wanda dayawa daga cikinsu suna samune ta ragowar matattun namun daji tsirrai dakuma kwanson baya halittun ruwa kamar irinsu kunkuru dakuma dodon kodi ina fatan kun gane?
Yes sir daliban suka amsa baki. Jin haka shiyasa malam habib cigaba da tafiya tsakanin duwarwatsun su kuma daliban na binsa abaya koda yafara tafiya sai sawun kafarsa yayi kuskuren taku sai kuwa ya fadi rica da katuwar jakarsa mai siffar kalangu ahannu daliban sun so su gintse da dariya amma ina sai suka bushe da dariya. Malam habibu zago yayi sauri ya tashi tsaye sannan saiyace cikin Kunya.
Ina ganin tunda mun fara gajita sai duk masu daukar hotuna suje su dauka don lokacin tashinmu ya karato.
Yawwa malam daliban suka dau shewa cikin dariya sannan sai suka fara kutsawa cikin duwarwatsun domin daukar hotunansu.

Ikram na zaune agefe guda tayi tagumi sai rukayya rabiu ta tabata akafada tace.
Haba Ikram kin zauna ke kadai kamar an yi miki mutuwa zo muje mu dauki hotuna mana gasu nana da salima haruna can bakin wani kogo suna jiran mu Wallahi bakiga cikin kogon ba zaiyi kyau da daukan hoto,
Cikin kogo fa kikace kina jin kuwa hoton zaiyi kyau Duhu fa? Ikram tace gamida mikewa tsaye lokaci guda
Haba ke hasken fa yana shiga kuma ai kyamarar ma tanada filasha muje mu lallabi malam sai ya daukemu mu duka batareda mun rarrabu ba. Wallahi gurin na da kyau.
Malam habibu na zaune kusa da wani dutse mai siffa irinta mutum ya daga kai sa'ar da sukazo kusa dashi yadubesu yace.
Yes me zan muku kuma kada fa ku dameni.
Sir dan Allah hoto zaka taimaka kayi mana acikin kogon can.
Ni zan dauke ku hoton? Ya tambayesu a yatsine.
A'a sir wallahi sauran student din duk sun shige can ciki shine to... Shine...
Kunga muje dan Allah kada ku dameni yace.
Lokacin da suka karasa bakin kogin sai suka fara jin wani wari wari gum yana busowa daga cikin kogon warin babu dadin ji ko kadan.
Kai warin me nakeji haka na fitowa daga kogon nan?
Malam habibu zago yace.
Meyiwuwa wata dabbar ce ta mutu aciki Salma Haruna tace dashi.
Kai amma wannan wari yayi yawa bari in shiga na gani ku jirani anan.
Sannan saiya kutsa kai can cikin kogon su kuma daliban sai suka ki tsayawa kamar yadda ya umarce su saboda tsegumi sai suka bishi abaya.
Sannan ne to gaba dayansu sukayi turus kamar sun fada cikin fasassun kwalabe akwance acikin kogon har ta fara kumbura gawar mace ce sanye da kyawawan kaya fuskarta a kumbure harshenta ya zazzago kamar zaifito daga bakinta sannan kuma jini yayi dan karamin tafki akusa da gawar.
Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un Malam habibu yace jiki na rawa.
Ai mu....tum ne daliban suka juya a guje cikin firgice suna kururwa koda malam habibu ya juyo a rude saiyaga har yanzu Ikram ita tana nan tsaye abayansa ta kurawa gawar idanu ko kiftawa batayi sannan ba zato ba tsammani saiyaji ta fasa kururuwa.
WAYYO ALLAH NA...... Na shiga uku na lalace.... Malam... Wallahi..... Fa'iza ce..... Fa'iza ce..... Ta mutu malam fa'iza ce... Wayyo!!! iska tayi jifa da amsa kuwwar kururuwar ta cikin duwarwatsun suka amsa baki daya.

ZANCI GABA A LITTAFI NA BIYU IN ALLAH YASO.

Nazir Adam Salih
(Nas) 2002

CUTA TA DAU CUTA
LITTAFI NA BIYU......CUTA TA DAU CUTA-15

LITTAFI NA BIYU 2

BIYAR 5
Tun sa'ar daya fara tuka motar da niyyar zuwa asibitin ya tabbata yau kam saidai Allah ya sauke shi lafiya domin murna da tunane tunanen kashe yar budurwar sun gama dabaibaye zuciyar sharoro.
Dan haka adaidai lokacin daya dauke kan motar kai tsaye batareda ya kunna signa ba ya shiga asibitin saiyaji zagi da ife ifen direbobi ya biyo baya.
Shashasha nan hanyar ubanka ce? Wani direban hayis yace dashi cikin karaji.
Sharoro baiko juyo ba ballantana ma yabada hakuri sai kawai yayi murmushi yana gyada kansa. Abanza dai wai talaka ya girmi sarki.
Sharoro yayi fakin da motar a farfajiyar asibitin kusa da wasu motoci guda uku toyota biyu da hajiya babu duwawu guda daya.
Yafito ahankali sannan ya rufe motar ya nufi wani dogon farin gini adaidai lokacin da wata farar motar asibiti ta shigo farfajiyar da gudu tana jiniya. Ba'a dade ba malaman asibitin ska fito su uku dogo daya da mace katuwa mai kamar giwa.
Kofar motar ta bude ta baya sannan daga cikin motar sai malaman asibitin suka janyo wani gado na karfe irin na asibiti. Akan gadon kwance wani mutum ne abushe duk ya kare kamar kwarangwal. Duk abubuwan da suke faruwa akan idanun sharoro ne domin daga inda yake tsaye saida yayi imani da cewa mutumin matacce ne. To amma duk da haka saiyaga malaman asibitin sun dauki gadon da mutumin ke kwance sunyi cikin dakin da sharoro yayiwa tsinke dashi.
Sharoro yayi ajiyar zuciya sa'ar da wata zuciya ta ayyana masa cewa yanzu idan da shine wannan yaya zaiyi? Wani zazzafan gumi ya karyo masa sannan lokaci guda ya kawar da tunanin cikin gaggawa daga zuciyarsa yana mai addua'ar indai har zai kamu da rashin lafiya irin wannan to Allah yayi masa jinkirin ramuwar gayya akan wanda yayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa.
Sharoro yaci gaba da tafiya zuciyarsa nata sake sake wannan rana tana da matukar muhimmanci agareshi ba dan komai ba kuwa sai don itace ranar dayake son ya lura sosai da irin zirga zirgar da malaman asibitin dakuma yan dubiya sukeyi agurin majinyacin wato Alhaji Sabitu. Hakan shi zai bashi damar gane kyakkyawan lokacin daya kamata yakai sumame asibitin dan tabbatar da burinsa na kashe mutumin. Domin ayadda ya shirya wannan shine karo na biyun karshe na zuwa asibitin daga nan kuwa sai ya aika dashi Barzahu yanzun ma abu daya ne zuwa biyu zasu hana shi karasa marar lafiyar na farko shine domin ya karasa sauraron jawaban marar lafiyar wadanda yafara yi masa awancan lokacin daya sa aka kirashi amma bai karasa ba sai malaman asibitin suka katse su domin yabar marar lafiyar ya dan huta.
Domin acewarsu bai kamata ba mai cutar hauhawan jini ya ringa yawan maganganun da zasu tayar masa da hankali ba.
Na biyu kuma shine sharoro yayiwa kansa alkawarin yadda alhaji sabitu yasa uwarsa tasha wuya yaja mata hankali yayi sanadiyyar mutuwarta cikin bakin ciki da takaicin rayuwa to shima saiya dandana masa bakin cikin mutuwar yarsa fa'iza sannan ya kashe shi cikin wannan tunanin. In kuwa hakane to dole ne ya dan jinkirta kashe shi ayau domin ya tabbata ayanzu gurin cike yake da yan dubiya.

Da wannan tunanin sharoro ya isa kofar dakin da Alhaji sabitu ke kwance cikin matsanancin hali.
Sharoro ya kwankwasa kofar dakin ahankali sannan saiya maida hannunsa cikin alhihun kwat dinsa yana sauraro. Ba'a dade ba saiyaji tafiya an nufo kofar dakin sannan ahankali sai aka bude kofar dakin.
Wata katuwar mace fara mai manya-manyan maganai ta dubeshi fuskarta babu alamar farin ciki ko bakin ciki tace.
Sannu da zuwa sharoro shigo da sauri dan Allah jikin nan nasa ya matsa tun dazu yake ta faman tambayarka.
Sharoro yayi dariyar zuciya sannan kuma lokaci guda yayi kokarin sa alamun tausayi a fuskarsa duk kuwa da cewa yin hakan har gumi ya sashi to amma dai akalla matar dake tsaye akofar ta dauka harga Allah sharoro ma shirin kuka yake.
Kai Allah sauwake Alhaji dai. Sharoro yace sannan saiya bita abaya suka shiga dakin. Sharooro ya dubi fankadeden dakin na musamman wanda ko a marasa lafiyar ma ba kowa ake sawa ciki ba sai mai hannu da shuni. Dakin yanada fadin gaske wanda hakan shi ya bashi damar daukan yan lokoki nasa yan komatsan majinyacin guda uku acan bangaren kudu kuma na dakin gadon da Alhaji sabitu ke kwance ne wanda fanka daya jal ke ta wanawa ahankali ahankali ta hanyar da zama ka iya lura da kyawawan launinta na ruwan zuma.
Sharoro ya dubi sauran matan guda hudu duk manya manya dasu kosassu kaida ka gansu kasan basu san abinda ake kira da talauci ba. Hakan nan acan gefe guda zaune akan wata kujerar karfe mai launin azurfa wani mutum ne dogo mai faskeken hanci kamar begila yanata huci kuma kaida ganin idanunsa kasan yaci uban kuka domin jajur suke kamar garwashin wuta. Shashashan banza huhun ma'ahu ko menene kuma na kukan dan wannan tsohon macucin bashida lafiya oho. Sharoro yace azuciyarsa sa'ar daya dubi kamannin mutumin kuma lokaci guda yana mai tambayar kansa ko wanene shi? Meyiwuwa dan uwansa ne sharoro yace cikin zuciyarsa barareda ya damu ba.
Sannu da zuwa sauran matan sukace da sharoro.
Da sauki suka amsa baki daya duk kusan suna harararsa amma shi bai ma ga hakan ba domin hankalinsa gaba daya da duk nutsuwarsa tana kan gadon yana duban marar lafiyar dake kwance kamar matacce yana numfashi da kyar.

Mutumin dake kwance akan gadon dattijo ne matuka domin ya tsufa zaikusan shekaru sittin da takwas aduniya idan kuwa har zaka yi la'akari ne da yamushewar da bushewar da yayi ya zama kamar gonar auduga to saika rantse da Allah ya ma kai shekaru dari aduniya.
Sharoro ya matsa kusa da marar lafiyar sannan yaCUTA TA DAU CUTA-16

Sharoro ya matsa kusa da marar lafiyar sannan saiya dafa bakin gadon ya rankwafa akansa lokaci guda kuma yana tunanin ai kashe wannan kwarangwal din ba wuya zaiyi ba domin ko kwakkwaran rankwashi kayiwa wannan ramammen kan mai kamar molo to mutuwa zaiyi.

Sannu Alhaji. Sharoro yace cikin muryar da in kaji saika dauka wani Babban wali ne mai yawan tsoron Allah. Mutumin dake kwance kamar kwarangwal ya dago kai ahankali yana haki yace cikin rarraunar murya.
Sannu da zuwa sharoro.... Kazo to Allah yayi maka albarka yayi shiru yana kokarin shakar numfashi. Sharoro baice Ameen ba.
Dattijon ya dago kansa ahankali ya dubi manya manyan matan dake zaune gamida dogon mutumin nan dake ta faman sharbar kuka yace.
Dan...... Allah..... Ku dan bamu guri zamu gana.
Nan da nan namijin ya mike cikin sauri ya fice daga dakin. Amma sauran matan dakyar suka fice sunata hararar sharoro akwai daya daga cikinsu ma datayi tsaki to amma sharoro baiji ba domin shi ba itace agabansa ba.
Bayan duk sun fice sun rufe kofar dakin sai motsatstsen dattijon ya sake dago kansa ahankali yace da sharoro.

Duk zaman nan da kaga sunayi ba zaman tausayi bane ko kuma jinyata.
Kamar yaya kenan kake nufi?
Sharoro ya tambaya dattijon yayi atishawa sannan yace cikin shakakkiyar murya.
Zaman jiran mutuwata sukeyi ba so suke na tashi ba.

***** ****** ******** ********* *****************

Maganar tayi matukar girgiza sharoro domin bai taba tsammanin hakan daga bakin matsiyacin dattijon ba kamar yadda ya kirashi.
Ashe bani kadai nake son ka mutu ba sharoro yace cikin zuciyarsa.

Saurareni da kyau sharoro dattijo alhaji sabitu yaci gaba da fadi sannan saiya mika hannunsa ga mamakin sharoro saiyaji busassun hannayen sun kama nasa hannun.
Haka nan dattijon yana zubar da hawaye.
Sharoro wannan CUTA bazata barni na rayu ba bata tashi bace. Shine dalilin dayasa na kira ka domin na damka wata amana ahannunka wacce ita zata fitar dakai daga cikin wani duhu mai tsananin gaske daka dade kana ciki tun sa'ar da aka haife ka.
Dattijon yayi shiru yana maida numfashi sannan yaci gaba da cewa.
Matan daka gani anan zaune duk matan dana taba aure ne abaya amma ayanzu duk bama tare dasu sai dai rabon ya'ya dake tsakanina dasu. Acikinsu akwai mai ya'ya uku sauran kuma duk ya'yansu biyar biyar. Basa kaunata koda daidai da kwayar zarra. Badon komai ba kuwa sai don irin wulakancin danayiwa kowacce daga cikinsu kafin na aureta. Abin kuma dayasa kaga duk sun tattaru akaina suna zaman jinyata. Baso suke na warke ba kowacce zuwa tayi dan kada nazo mutuwa nabar wata wasiyya basu ji ba gahi kuma duk akwai ya'ya tsakaninmu kowacce daka gani anan zaman jira take na mutu araba gado ta dauki na ya'yanta.
Ina mai tabbatar maka da cewa kuma kowacce yanzu daga cikinsu addua'a takeyi Allah sa na mutu. Dattijon yakarasa maganar cikin tari.
Gara ma su addua'a sukeyi ni da kaina zan kasheka matsiyaci Allah ya kusan karbar addu'arsu. Sharoro yace cikin zuciyarsa sa'ar da yaci gaba da sauraren kwarangwal din tsohon.

Sharoro arayuwata ban kyautawa kaina ba. Domin ban tsinana wani abin kirki da mutane zasu yabeni dashi ba kowa Allah wadai yake dani. Shiyasa na kira ka na nemi gafararka domiin hakika nasan na cuce ka iyakar cuta.
Bakin alkalami ai ya bushe saina kasheka matsiyaci ashe kana sane. Sharoro yasake cewa cikin zuciyarsa.
Sharoro ayanzu kam babu wanda nake kauna duk duniya KAMAR KAI.
Domin kai Nawa ne. Dattijon yaci gaba da bayani.
Kama nemi naka tun dare baiyi maka ba. Sharoro ya sake maimaitawa acikin zuciyarsa.
Gobe in Allah ya kaimu ban mutu ba saikazo akwai abinda nake son na baka domin ya yaye duhun dake zuciyarka.
N ina jin kunyar sanar dakai domin ban kyauta maka ba. Sharoro dama ace zan sake koda shekara daya ne aduniya da Wallahi na faranta maka fiyeda yadda na bakanta maka baya ka yafeni. Ka kuma daure kazo goben kaji? Zan damka amana ta ahannunka. Dattijon yace yana zubar da hawaye.

Kada ka damu Alhaji. Sharoro yace yana dariyar zuci shima Allah ya kamashi macucui. Sannan sai sharoro ya tuna sa'ar da yake karami yana zaune gaban mahaifiyarsa take ta aman jini ana aikawa Alhaji sabitu yana cewa saidai a sayar masa da gidansu.
Na roke ka don girman Allah sharoro ka kularmin 'YA' TA FA'IZA.
Domin duk cikin mutanen dake tare dani babu wacce nake kauna sai ita dakuma KAI ayanzu. Ka rike min fa'iza don Allah idan an raba gado ka kular mata data kasan macece tana da rauni kada ka bari dukiyarta ta lalace ta shiga halin matsi..... Sai goben idan kazo.
Dattijon yakoma lamo dashi akan gadon kamar ya mutu sharoro ya dube shi saiyaji kamar ya cakumo dan siririn wuyansa yace dashi NA KASHE FA'IZAR DA YAKE KAUNA. To amma bai fadi hakan ba sai goben dai dan samari rabu dashi gobe war hakan ai yana can barzahu inda mahaifiyarka take. Mummunan zuciyarsa ce ke bashi shawara. Adaidai lokacin ne to kofar dakin ta bude sannan wata yar siririyar malamar asibiti fara sol mai kamar zabiya tashigo dakin mararta a daure da shudin Belt kamar ta tsinke.
Lokacin ziyara ya wuce ka barshi haka ya huta kada kasa jininsa yasake hawa. Tace da sharoro.
Sharoro ya dubeta ido da ido sannan saiyace azuciyarsa jinin nasa yafi jirgin sama hawa baice da ita kala ba sai kawai ya juya da sauri ya fice daga dakin. Malamar asibitin ta bishi da kallo atsorace. Akwai wani abu a fuskarsa data gani taji kwata kwata ta tsani dan farin mutumin.

SHIDA 6
Karfe hudu saura kwata na yamma yayi fakin akofar sabon gidan da abokin nasa ya nemi ya tare aciki suke kwana.
Labaran yafito cikin sauri lokaci lokaci gabansa yakan idan........CUTA TA DAU CUTA-17

Labaran yafito cikin sauri lokaci lokaci gabansa yakan fadi idan ikram ta fado azuciyarsa haka nan yakan taba aljihunsa dan jin ko hoton yana nan. Labaran yana son ya dauko hoton badan komai ba sai dan kawai ya kalli kyakkyawar fuskar ikram wacce cikin awowi arba'in da takwas kawai da suka wuce ta mamaye zuciyarsa tamkar ambaliyar kogi cikin dare. To amma tsoron kada fa'iza ta sake yi masa gizo shi ya hanashi ya dauko hoton.
Tun kafin labaran ya karasa kofar dakin shakatawar yaji sautin kida na tashi kamar zai ruguzo rufin gidan baki daya akan doron kasa wannan shi ya tabbatar masa da cewa lallai ILYASU yana gida baifita ko ina ba.
Ilyasu tsohon abokin labaran ne tun suna yara. Hakanan shima ilyasu kamar labaran bazaka iya kiransa wali ba domin duk inda tsohon tsinanne yake Ilyasu ya dade da wuce nan abin saidai addua'a. To amma duk da haka kana iya kiransa Kamili in dai har zakayi la'akari da labaran domin shi ilyasu bai taba fashi ba saidai yakan taba yan kananan sace sace suma a taskar mahaifinsa yakeyi wanda babban attajiri ne akasuwar yan katako. Hakanan kuma ilyasu bai iya kashe koda zaka ballantana ma azo ga kashe mutum. Ilyasu da labaran an dade ba'a hadu ba dan haka awannan ranar misalin sha biyu bayan labaran yaje banki yagama tabbatar da zaman kudin da sharoro yabashi sai kwatsam suka hadu da ilyasu abankin.
Danja ta tsayar dasu suna jira ta sauya launi su wuce. Bayan sun tsallaka titin ne kowa yayi fakin da motarsa suka tafa tas. Kamar sa tashi Walkiya alokacin ne to labaran ya nunawa ilyasu cewa to fa shima ayanzu ya shigo gari amma abu daya yake damunsa shine gidan da zai kama mai kyau yana kwana ciki kafin ya sayi nasa.

Kada ka damu Ilyasu yace dashi da ranar.
Akwai gida da boss dinmu yabani sabo ne nima banfi wata uku da tarewa ciki ba ni kadai nake kwana kuma daman yayi min girma ni kadai. Don haka in kana ganin ba damuwa yauma kana iya tarewa da yamma sai muyi zaman mu ciki har sai sa'ar dakaga damar tashi.
Dan haka ayanzu da labaran ya nufi kofar falon gidan yaji kida na tashi sai yayi murna kwarai ba dan komai ba kuwa sai dan tunanin Ikram da wutar begenta sai dada kona zuciyarsa suke hakika yana bukatar wani da zai tattauna abin dashi.
Labaran yakarasa kofar falon tun kafin ya kwankwasa sai kofar ta bude ilyasu yayi murmushi.
Shigo mana ai inajin tsayuwar mota nasan cewa kaine Ilyasu yace.
Zo muje ka tayani dauko jakan kayana suna bayan mota labaran yace. Ilyasu yabishi abaya mintuna ashirin da faruwar hakan sai samarin suka dawo dakin shakatawar suka zauna tuni ilyasu ya nuna masa dakin kwanansa hakanan basu zauna ba saida labaran yashiga bandaki ya watsa ruwa sannan suka dawo falon suka zauna kowanne kofin gilashi cike yake da madara ahannunsa Ilyasu ya busa hayakin sigari sama yace.
Yaya akayi ne mutumina meye labari nifa naga bakinka kamar yana motsi kuma ka cika yawan jugum tunanin me kakeyi?
Labaran ya dube shi gamida wani fatalwan murmushi.
Wallahi Ilyasu na kamu da ciwon da ban taba tsammanin zan kamu dashi ba. Ilyasu ya daga girar sa sama sannan ya kurbi madararsa ya kuma zukar sigari yace.
Ina fatan dai ba cutar kanjamau ka kamu da ita ba dai ko?
Labaran ya bushe da dariya.
Eh to kusan tafiyarsu daya ai da kanjamau din domin cutar so wani lokacin har tafi kanjamau barna.
Haba labaran baka san cutar kanjamau bane ita ta kashe wata bebita.
Me yiwuwa inkaji labarin kayi min dariya labaran yace yana duban Ilyasu gamida murmushi domin ban ma taba ganinta azahiri ba.
Ilyasu ya bude baki cikin mamaki.
Baka taba ganinta ba ko aljana ce? Labaran ya girgiza kai
ba aljana bace mutum ce kamar kai nima hotonta na tsinta ina tafiya kallo daya kawai nayi mata naji kaunarta ta mamaye zuciyata abin kamar tsafi. Ilyasu ya fashe da dariya yace.
Kai labaran me yake damunka ne naga nema kake ka koma wani Laushi....
Kada kace haka labaran ya katse shi.. Dan baka taba kamuwa da so bane shiyasa kake fadin haka amma wallahi cikin awa arba'in da takwas din da suka shude duk motsin danayi tana zuciyata.
Awa arba'in da takwas kawai ma da tsintar hoton amma duk ka rikice haka? Ilyasu yace cikin kaduwa to ayanzu ina hoton yake bani in gani ko aljana ce.
Koda Ilyasu ya fadi hakan sai labaran yaji gabansa ya fadi nan da nan jikinsa ya fara rawa wani sassanyan gumi yafara ratsowa ta goshinsa domin tsoron hoton yake yi tun bayan abinda ya faru adaren jiya.
Bani mana Ilyasu yace sannan lokaci guda ya kurbe madararsa ya kuma mikawa labaran hannunsa domin karbar hoton.
Labaran baison dauko hoton to amma bashida zabi domin hana ilyasu hoton na iya kawo yawan tambayoyi daga gurin Ilyasu. Dan haka ahankali kamar mai zaro maciji daga cikin aljihinsa saiya zaro hoton batareda ya yarda ya kalli hoton ba ya mika masa.
Ilyasu ya karbi hoton sannan azuciyarsa yana mai mamakin abinda yasa labaran gumi to amma baice komai ba sai kawai ya kurawa hoton idanu,
yaya sunanta? Ilyasu ya tambaya. Gashinan abayan hoton. IKRAM labaran yace dashi muryarsa na rawa don tunani yake ko shima hoton fa'iza zaiyi masa gizo kamar yadda yai masa adaren jiya.
Kai lallai banga laifinka ba wallahi kyakkyawa ce.
Itace ta farko ko daga hannun dama? Ilyasu ya tambaya.
Labaran ya gyada kai baki abushe.. Ilyasu yaci gaba da kallon hoton kamar zai hadiye shi. Can sai yayi ajiyar zuciya yace.
Wacece ta farkon daga hannun hagun? Labaran ya dubeshi a tsorace yace..
Yadda ka ganta haka nima na ganta. Jin haka shi yasa ilyasu ya sake juya bayan hoton sannan sai ya sake ajiyar zuciya akaro na biyu.
FA'IZA.... Wai kasan wani abu kuwa labaran wallahCUTA TA DAU CUTA-18

Jin hakan shiyasa Ilyasu ya sake juya bayan hoton sannan saiya sake ajiyar zuciya akaro na biyu.
Fa'iza.... Wai kasan wani abu kuwa labaran? Wallahi da zaka sami Ikram dinnan taka dani kuwa ba wacce zance ta nemo min sai wannan FA'IZAR dan Wallahi ta kwanta min Ilyasu yace yana jujjuya hoton sannan saiya dada da cewa.
Yazama dole na taya ka nemo wannan Ikram din taka aduk inda take domin samunta shi zaisa na sami fa'iza abar kaunata. Labaran yayi shiru bai amsa ba.

***** ****** ****** ****** ***** *****************

Lokacin da labarin samun gawar fa'iza ya isa makarantar saida kowa ya girgiza tun daga kan dalibai da malaman da suka santa har zuwa kan wadanda basu ma santa ba. Ba wani abune yasa su kaduwa ba sai irin muguwar mutuwar da aka kawo labarin tayi hakanan kuma ga karin zance irin na mutane domin wasu sunyi ta yada jita jitar cewa wai har saida aka kwakwule mata idanun fa'iza sannan aka kasheta wasu kuma suce a'a harshe aka yanke mata yayinda wasu kuma daga cikin manya manyan shehunnai makaryata sukace wai saida akayi gunduwa gunduwa da ita to duk da yake dai kusan rabin labarin da aketa yadawa duk karya ne amma abinda ikram ta gani ya isa ya gigitar da ita gaba daya. Tun sa'ar da suka gano gawar fa'iza cikin kogon dutsen ikram bata kara moruwa ba. Domin asume aka dawo da ita cikin makaranta ganin jikin nata ya ttsananta shiyasa suka maida ita gida.
Karfe goma na safiyar ranar daidai sai wata bakar fito ta jami'an tsaro tayiwa kofar makarantar tsinke tun jiya daman suke ta faman sintiri tsakanin makarantar da inda abin yafaru har garin Allah ya waye basu daina sunturi ba. Sun dade acikin duwatsun sunata aune aune da

Please Login or Register in order to submit comment