Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dube dube amma har yanzu basu ga wata alama ko wani manuni ba da zai kusantar dasu izuwa wanda ya kashe dalibar.

Ba yan sandan kadai bane adaren basuyi barci ba harda malaman makarantar gamida hadimanta babu wanda yasami runtsawa wasu daga cikinsu kaduwar mutuwar budurwar ne ya hanasu barci domin basu taba jin abu irin wannan ba yayinda dayawa daga cikinsu kuma tambayoyin da yansandan suka sasu agaba sunayi musu ne ya hanasu barcin.
Tun magaribar daren jiyanne yan sandan suka sa shugabar makarantar hajiya falmata ta tattara musu duk malaman makarantar maza da mata gami da masu gadi da kuma sauran hadiman makarantar kamar masu gadi da kuma jami'an tsaron suka fara binsu daya bayan daya suna tayi musu tambayoyi kamar mala'ikun kabari. Basa ko barin mutum yayi kwakkwaran numfashi.
Dan haka awannan safiyar da motar yan sandan ta nufi farfajiyar makarantar zuwa ofishin firin sifal sai cikin dayawa daga cikin hadiman makarantar ya duri ruwa musamman ma masu gadi domin tun jiya ba'a tambaye su ba dan haka yau ta kansu zasu fara kuma tambayarsu saitafi ta kowa tsanani.

Acan bangare guda acikin makarantar wani busashshen dattijo dauke da butar ban ruwa ta karfe ya dubi abokin aikinsa wanda ke duke yanata faman sare ciyayin dake kasan fulawowin da suke baiwa ruwa yace.
Malam Buba ga bayin Allah nan sun karaso.
Buba ya dago ahankali yasa hannun rigarsa ya goge gumin dake zuba a fuskarsa sannan yace.
Suwa kenan?
Suwa kuwa in banda yan sanda kasan fa.... Ni wallahi duk na tsorata da tambayoyin nan nasu. Ni kasan mutumin da ne tsoron su nake. Buba ya dubeshi cikin dariya yace.
To in banda abinka malam na ta'ala menene abin fargaba? Yarinyar nan fa bakai ka kasheta ba ko kaine? Malam nata'ala yai sauri ya girgiza kai jiki na rawa yace.
A'a A'a Allah tsari gatari da saran shuka yanzu ni kana jin ko dan tsako zan iya bugewa? Buba yayi dariya.
Me zai hana tun da dai abin kwalama ne. Malam na ta'ala shima yayi dariya amma ta yake domin har yanzu cikinsa kugi yake. Daga inda suke tsaye suna iya hangen tike tikan yan sandan cikin bakake da fararen kaya sunata duruwa cikin katon dakin taro na makarantar inda anan ne jiya sukayi tambayoyinsu da daddare.
Malam buba yanzu idan sun fara tambayata me zance dasu?
Abinda ka sani shi zaka fada. Malam buba yace.
Kai ai ni asani agaba dinnan anata tambaya kamar cikin kabari shine ka.....
Maganarsa ta katse adaidai lokacin da suka hango malam S. Haruna mataimakin shugabar makarantar yana yi musu alama da su zo. Malam buba ya dauki malam na ta'ala yace. Shikenan ta faru ta kare.

***** ***** ****** ******* **** *****************

Mutane Ashirin da biyar ne cif acikin dakin goma sha biyu maza ne sha uku mata wasu masu gadi ne wasu kuwa hadimai ne kawai na makarantar. Duk dayake sun kai su ashirin da biyar idan zaka labe daga waje baka kallon ciki saika rantse babu koda bi'adama daya acikin tangamemen dakin taron saboda tsabar shirun da sukayi. Mutanen ashirin da biyar dakyar suke numfashi basa ko kwakkwaran motsi badan komai ba kuwa sai dan dirka dirkan jami'an tsaron guda takwas da suka sa su agaba da jajayen idanu sunata hadiyar yawu kowannensu sakale da bindiga kamar sa hadiyi mutum su sha ruwa.
Wani kato mai idon mashaya ya dubi jama'ar yace cikin wata fasasshiyar murya.
Kowa ya hadu? Kamar amsar tambayarsa sai kawai sukaji tafiya sadaf sadaf sannan ne to suka dubi mutumin daya shigo dakin. Atsaye agaban yan sandan idanunsa na zubar da hawaye bakinsa na rawa kamar maijin sanyin hunturu dan kesasshen maigadin nan ne mai lankwasashshiyar hula kamar makani. Idanunsa sun kukkumbura saboda uban kukan da yaci tun sa'ar da aka kawo gawar fa'iza.

Bari kuka baba tambayoyi kawai zamuyi muku ba wani abin tashin hankali bane. Wani dan sanda yace dashi sa'ar da yaga mutumin yana kuka ya tsaya agaban taron jama'ar.
Koma gurin yan uwanka ka jiramu yanzun nan zaka koma kan aikinka..CUTA TA DAU CUTA-19

Koma gurin yan uwanka ka jiramu yanzun nan zaka koma kan aikinka.
Dan sandan ya sake cewa dashi. Amma sai mutumin ya girgiza kai cikin kuka yace.
KU...... Sallami kowa ya tafi duk... Laifina ne.
Yan sandan suka dubi juna yayin da sauran jama'ar dake dakin suka yi ajiyar zuciya lokaci guda kamar mamu masu cewa ameen yayinda liman yakawo karshen suratul Fatiha.
Kana nufin kai ka kashe ta.
Wani Jami'in tsaro ya buga masa tsawa?? A'a bani bane Amma Naga wanda ya kashe ta laifi na ne ni... Ni na bari ya dauke ta jiya da yamma ina gadi ni na Kirata Wallahi ban.. San kashe ta zaiyi ba. Ya sake fashewa da kuka sannan saiya watsa musu damin naira ashirin ashirin din da labaran ya bashi.

BAKWAI 7
A Daidai lokacin dasu labaran da Aliyu ke ta hirar ikram basu san cewa ashe tun a safiyar ranar aka kawo ikram gida ba.
Wannan dawowar tata tanada alaka ne da mutuwar babbar kawar ta fa'iza ganin irin mawuyacin halin data shiga shiyasa aka yanke mayar da ikram gida wajen iyayen ta har saita dan mance da abinda ya faru.
Koda yake ga al'adar makarantar bashi yiwuwa in dai rashin lafiyar bai tsanani yayi ba ba'a dawo da dalibi gida to amma ganin cewa idan aka bar ikram a makaranta to zata Dade bata manta rasuwar kawarta ba shiyasa aka maida ita gida to hakan kuwa ya taimaka domin da safe aka kawo ta gida magashiyan amma da misalin karfe hudu na yamma sai gata zaune har tana dan cin abinci ana kuma hira da ita.

A can gidan su fa'iza kuma lokacin da jami'an tsaro suka sauka da mummunan labarin sai suka sami labarin ai duk kusan yan gidan ma suna asibiti sakamakon Maigidan da aka kwantar dan haka sai suka wuce kai tsaye zuwa asibitin. Tareda jami'an tsaron harda malamai biyu wato malamin da ya dauki Daliban nan zuwa cikin duwatsu da kuma shugaban makarantar.
A daidai lokacin da sharoro yafito daga cikin dakin sai ya wuce kai tsaye zuwa inda ya ajiye motar sa xuciyarsa cike da tunane tunane barkatai shi kam ya tabbatarwa kansa cewa gobe kan babu kuskure saiya karasa kwarangwal din tsohon nan.
In banda gingimenen jirgin mai rurin tsiya da yazo giftawa ba to da sharoro bazai taba ganin yan sandan ba.
Rugugin katon jirgin mai dauke da tambarin gunkin Okada ya girgiza ko ina a cikin asibitin musamman ma dab da inda sharoro yake domin a lokacin yazo daf da wata rumfar kwano ne don haka Rugugin jirgin yayi matukar girgiza rumfar wanda Hakan shiyasa sharoro daga kansa sama cikin gaggawa ya dubi sararin samaniya domin tun sa'ar dayaji labarin jiragen nan da suka tunkiya tagwayen benayen da suka fi kowane gini tsaho a duniya na amurka sharoro yafara Tsoron jirgin sama.
Bayan da sharoro ya tabbata dai jirgin ba kansa yayo ba sai ya sauke kansa da niyyar ya duba inda motarsa take sannan ne to sharoro yayi ido biyu da bakar motar yan sandan tana shigowa asibitin.
A cikin dakikun daya hangi motar yan sandan saida duk wani tunanin sa da wata nutsuwa suka bar jikin sa na dan lokaci yaji kamar ya ruga da gudu.
Kai shashashan banza daga ganin jami'an tsaro saika fara rawar jiki kamar mazari kasan abin da ya kawo su?
WATA ZUCIYA Ce take cewa da sharoro hakan. Tunanin shi yasa sharoro nutsuwa sannan cikin hanzari sai ya kutsa ta tsakanin motar nan hajiya ba duwawu dake daf da tasa ya bude motarsa batareda ya bari yan sandan sun kawo hankalin sa gare shi ba ya shige shi motarsa gamida ajiyar zuciya.
Meke damuna ne? Sharoro ya tambayi kansa lokaci guda kuma ya fara goge gumin dake diga daga fuskar sa da wani farin kyalle.
Daga inda sharoro yake zaune yana iya hangen jami'an tsaron ta cikin gilashin gaban motar sa dan haka sai yayi shiru abinsa yana kallon inda zasu nufa.
Yan sandan suka fito su shida duka kosassu in ka dauke daya mai wuya shigen na sharoro. Ba'a Dade ba sai jami'an tsaron suka nufi cikin asibitin sannan ne to zuciyar sharoro ta dulmiya domin ko shakka babu dakin daya fito suka yi wa tsinke.
Sharoro ya sake share gumi akaro na biyu.
Me yiwuwa zuwa suka yi suce dashi fa'iza ta mutu wata zuciyar tace dashi idan har akwai abu daya da sharoro yaki jini yanzu a duniya shine wani ya kaiwa kwarangwal din mutumin labarin mutuwar fa'iza kafin shi.
Domin akullum fatansa shine ya fadawa dattijon mutuwar fa'iza yaga yadda idanun munafuki zasu fito kamar yadda ya ke kiran shi.
Sakarcin ka yayi yawa sharoro wata zuciyar ta sake cewa dashi in banda abunka tayaya suka san fa'iza ta mutu bayan labaran yace dakai cikin kogon dutsen daya boye gawar ba wanda ya isa ya ganta.
Akaro na farko tun sa'ar da sharoro yayi ido biyu da yan sandan sai yaji dan sanyi sanyi sannan saiya yayiwa kansa murmushi yace a sanyaye.
Daina damun kanka a banza sharoro duniya gobe Warhaka ka aika da shege barzahu yana nan yana ta kulle kulle har yan sandan suka fice daga asibitin.
Sharoro yabi bakar motar da kallo kamar yadda kare ke kallon motar yan wasa da kura.
ABUNDA sharoro bai sani ba shine tuni labarin mutuwar fa'iza ya baza ko ina koda yake dai acikin asibitin an hana a fadawa dattijon dokin kowa yasan yadda yake kaunar yarinyar idan ya sami labarin ko shakka babu biyu babu za'a yi.
DUK kusan fuskar jaridar daka duba a ranar hoton fa'iza ce kwance acikin kogo to sai dai kuma in akwai abu daya da sharoro bai damu dashi ba yake ganin duk bata lokaci ne da rashin aikin yi to shine karatun jarida.

******* ******* ******** ******** ******************

NEXT...CUTA TA DAU CUTA-20

Idan akwai abu daya da sharoro bai damu da shi ba yake ganin duk bata lokaci ne da rashin aikin yi to shine karatun JARIDA.

********* ********* ********* *********************

Alhaji mukhtar gajere fari mai faffadan fuska kamar murfin Randa da manya manyan kumatu tsohon dan boko ne domin in har littafin na nan idan ka je kafara bincike zaka tarar sunansa Shine na uku a jerin sunayen wadanda aka fara baiwa kyautar mota LADA yayin da suka kammala digirin su na farko.
Wannan mutumin kamili ne dayawa daga cikin mutanen unguwa sun yi masa shaidar mutunci yayinda acan kuma Bangare guda yan samarin zamani na unguwa ke ta faman Allah wadai dashi.
Wannan ya biyo bayan wata halayya ce guda daya da Alhaji mukhtar yake da ita.
Al'adar kuwa itace aduk yammacin duniya in kazo wucewa anan zaka same shi zaune a kofar gidan yana karatun jarida sanye da katon farin gilashi a idanunsa yana muzurai kamar waziri AKU.
Dan haka yan kananan samari wadanda kan kawowa yan matan gidan hari ba kasafai sukan sami wata kwakkwaran nasara ba domin kafin ka sami ganin wata budurwa sai mahaifin nasu yayi maka dogayen tambayoyi kamar a dakin jarrabawa sannan daga karshe idan yaga ka dace sai ya shiga da kansa ya kirawo ta a bude muku babban falon gidan ku zauna amma kafin nan zaice dakai zuwa uku kawai ya baka kuma minti arba'in arba'in zakayi ka nemi amincewar ta in kun daidaita sai yace to ka turo iyayen ka a tsaida magana.
To wannan ita tasa samarin Unguwar suka tsani al'amarin sa.

Kamar kullum yauma Alhaji mukhtar zaune yake akan farar kujerar daya saba zama sanye da farin tabaransa yana karatun jaridar weekly trust yanitsa cikin jimamin mutuwar fa'iza domin yana gurin aiki da safiyar ranar aka dawo da yarsa Ikram daga makaranta Hakan nan da dawowar sa aka bashi labarin abunda ya faru to kuma sai gashi ma ya tsinci cikakken labarin cikin wannan jarida
Sautin tsayuwar motar shiyasa alhaji mukhtar dagowa cikin damuwa domin atunaninsa irin samarin da suka saba sintiri agidan ne suka karaso. Dan banda Ikram ma akwai yayyanta ne hassana da hussaina.
Yayi matukar girgiza lokacin daya dago kai suka yi ido biyu da bakar motar yan sanda.
Maigida barka da yamma wani daga cikin jami'an tsaron yace dashi lokacin da suka fito daga motar suka nufi inda yake.
Yawwa sannunku da zuwa ina Fatan dai lafiya.
Kwarai kuwa lafiya suka bashi amsa gamida dan saurarawa suna tunanin ta inda zasu fara sannan ne to daya daga cikin su ya hango hoton labarin fa'iza ajikin jaridar dake hannunsa.

Alhaji Daman bawani abin tashin hankali ne yakawo mu gidan ka ba sai dan wani taimako da muke son samu daga gurin yarka Ikram.
Alhaji mukhtar yadube su a rude.
Ban fahimce ku ku ba..... Wanne irin taimako kenan daga gurin yara? (repeat your self men) yace gami da cire tabaransa faffadan fuskar sa a yamutse?? Ajikin wannan Labarin da kake karantawa zakaga hoton wata Daliba da aka tsinci gawarta acikin wani kogon dutsen an kasheta to mun fahimci cewa yar ka ce babbar kawarta shine to muke son yi mata wasu yan tambayoyi wadanda muke tsammani su zasu taimaka mana mu kama azzalumi.

Hakane Alhaji mukhtar yace.
Amma haryanzu dai ban fahimci from which angle ne yarinyata zata taimake KU ba..
Alhaji tun jiya muke ta bin jama'a da tambayoyi acikin tambayoyin ne har muka zo kan wani mai gadi wanda yace shi yaga saurayin daya dauki fa'iza da yammacin ranar kuma shi ne ma ya kirawo masa ita.
To wannan saurayin shine zargin mu na farko a jerin wadanda Muke tunanin sun kashe wannan Daliba kaga kuwa in hakane to dole mu bukaci taimakon yarinyar ka domin babbar kawa tana iya sanin dukkan samarin kawarta ina Fatan yanzu ka fahimce mu?

INA FATAN KUMA MASU KARATU KUN FAHIMCE NI DA KYAU?

ASHA RUWA LAFIYACUTA TA DAU CUTA-21

Domin babbar kawa tana iya sanin dukkan samarin kawarta. Ina fatan yanzu ka fahimce mu?

Sure you have a point. Alhaji mukhtar yace gamida mikewa tsaye ga mamakin sai yaga tuni har mutane sun fara taruwa daga can nesa suna kallonsu.
Ko zamu shiga daga ciki? Alhaji mukhtar yace. Duk abinda akeyi ikram na tsaye akan bene tana hangensu ta cikin tagar gilashi.

****** ****** ******** ****** **********************

Ikram ta rabe acan gefe guda na falon jikinta na rawa tana duban yan sandan guda biyu.
Tun sa'ar da suka shigo gidan daya daga cikin jagaba na jami'an tsaron yayiwa sauran inkiya da hannu akansu jirasu awaje hakan ita tasa shima alhaji mukhtar ya dakata daga waje to amma baiyi bisa ba anan kofar falon ya ringa safa da marwa yana kokarin satar jin tambayoyin da ake yiwa yar tasa. To amma duk abanza dan baijiyo komai ba sai guna guninsu.

Malama ikram. Daya daga cikin jami'an tsaron biyu ya kirata.
Na.....am ta amsa a tsorace.
Ki kwantar da hankalinki ki daukemu amatsayin yayye kada ki ji fargabar komai domin wannan yan tambayoyin da zamuyi miki dan amfanuwar duk mai kaunar fa'iza ne. nasan dai ai kema zakiso kiji an kama azzalumin daya kasheta an hukunta shi ko? Ikram ta gyada kai cikin gaggawa.
Yawwa ikram to yanzu muna son ki saurareni da kyau tambayoyin masu saukin amsawa ne ya dan saurara lokaci guda kuma ya dubi abokin aikinsa wanda tuni ya zaro wani dan karamin littafi da alkalami yana shirin kwafar duk wani bayani da ikram zatayi sannan sai yafara.

Shin ikram acikin samarin kawarki fa'iza kin taba jin wani acikinsu mai suna LABARAN? Ikram ta girgiza kai lokaci guda.
Wallahi ban ko taba jin sunansa ba abakinta. Yan sandan biyu suka dubi juna gamida yiwa junansu sigina da gashin baki.
Kidai yi tunani ikram domin mun tabbatar da cewa wannan labaran saurayinta ne kuma shine wanda yazo har makaranta ya dauketa a mota ayammacin da aka kasta kinga kuwa in har akwai mutum daya a doron kasa da zai san wannan saurayi to kece domin ance bata da wata kawa sama dake. Ikram ta gyada kai tace.
Tabbas. Amma wannan ada ne ba yanzu ba jami'an tsaron ya dubeta cikin mamaki saidai bai bari alamun sun nuna karara a fuskarsa ba ya shafi tumbinsa yace.
Kina nufin kice min kun bata da ita kafin rasuwar tata?
A'a ina nufin dai bama jituwa da ita sosai ne kamar da.
To jituwa kamar yaya kenan?
Eh kasan kowa da irin rayuwarsa adacan lokacin da muka fara makaranta lokacin muna aji biyu zuwa uku hanyar rayuwar mu iri dayace da kawata fa'iza Allah jikanta.... Ikram ta fara sheshshekar kuka.
Kiyi hakuri malama ikram duk mai rai ai mamaci ne.
Jami'in tsaron yace duk dayake sautin muryarsa bai sauya ba to amma cikin zuciyarsa ya kagu taci gaba da bayaninta domin suna ta bata lokaci.
A..... Aranar da abin zai faru ma babu irin nasihar da banyi mata ba akan tabar irin wannan halayyar banza amma saitaki ta nuna min ita babu ruwana acikin harkar rayuwarta.
Kina nufin kice lokacin da zata fito daga makarantar ma kuna tare?
Eh lokacin kwalliya takeyi acikin hostel ni kima nasan fita yawan banza zatayi domin duk kusan karshen sati sai samarinta suna fita da ita.
To malama ikram koda adacan din da rayuwarku take daidai ba zaki iya tunawa ba da wani saurayinta mai suna Labaran. Ikram ta goge hawaye da gefen gyalenta.
Ai awancan lokacin da nake fada muku bama kula samari domin ko anan gida kullum in tazo gurina sai baba ya hadamu yayi mana fadan mu daina kula samari barkatai. Domin zasu iya hanamu karatu. To shiyasa bamu da samari alokacin. Kodayake ita ta taba yin kwaya daya sunansa ALHASSAN.
Watan su uku dashi yayi Accident ya mutu.
Yansandan biyu suka dada duban juna akaro na biyu domin sun san tabbas basu kara samun taimakon komai daga wannan yarinya ba.
Jami'an tsaron biyu suka mike tsaye lokaci guda.
Malama ikram mun gode me yiwuwa kuma ki ganmu mun dawo kafin nan kina kara tunowa dai ko acikin hirarku da ita in ta taba ambaton wani mai suna LABARAN.
Da haka suka fice daga dakin suka nufi kofar gida inda sauran jami'an tsaron da Alhaji mukhtar mahaifinta ke jiransu koda suka nufi inda suke sai daya daga jami'an tsaron ya dubi dan uwansu yace.
Me yiwuwa fa duk wahalar banza mukeyi. Dayan ya dube shi cikin mamaki yace.
Dan Me kace haka?
Yanzu kai a tunaninka in ba mahaukaci ba wanene zai zo da niyyar kashe mutum agurin da ba'a sanshi a ya fadi sunansa na gaskiya? Ni ina tunanin sunan nan LABARAN sunan BOGI ne.

TAKWAS 8
Ya kasance lokacin data fito daga wanka karfe da kwata ne daidai wanda kuma yazama mintina ashirin daidai da barin yan sandan daga gidan mintuna goma sha biyar cif da yan dakiku ta kwashe tana kwalliya in ka dauke dan kumburin da kumatunta suka dan yi na rashin sabo da yawan kuka saika rantse da Allah hankalin ikram akwance yake domin kwalliyar data caba ta taimaka wajan yi mata badda bami.
Ta shigo cikin falon tana kamshi sanye take da koren leshi mai dauke da fararen duwatsu masu daraja sunata walwalin dauke idanu acikin dan abinda ya rage na daga hasken ranar yammacin.
Kinyi kyau Wallahi. To ko kefa bakiga yadda kike ba lokacin da nazo duk duk kin jeme ba kyan gani... Duk mai rai ai mamaci ne wata kawarta ce ke fadin hakan wacce zuwanta gidan shi ya tashi wankan ikram domin neman kawartata tayi na ta rakata unguwa
Uhm dan dai ke baki santa bane kawai... Kokuma ince bakwa dasawa da ita amma Allah bakiji ba yadda mutuwar nan ta girgizani. Ikram tace.
To Allah ya jikanta kawarta tace gamida mikewa tsaye.
Ai sai mu tafi ko? Yan matan biyun suka fito tsakar gidan adaidai lokacin da mahaifiyar ikram itama ta fito daga...CUTA TA DAU CUTA-22

Mahaifiyar ikram itama tafito daga dakin girke girke ta dubesu tace.
RAKIYA sai kuyi kokarin dawowa da wuri kada ku dade babanta yayi fada... Kundai san halinsa.

Toh Ummi rakiya ta amsa cikin girmamawa yan matan biyu suka fice daga gidan hannayensu rike dana juna.
Har suka fice mahaifiyar ikram na binsu da kallo ba'ason ranta ta barsu suka fice da wannan yammacin ba domin itama kamar mijinta Alhaji mukhtar bata fiye son ya'yanta su rinka yin yawace yawace barkatai ba. To amma ganin irin halin da aka kawo yarta ikram aciki daga makaranta yayi matukar girgizata dan haka ganin cewa ikram ta dan fara warwarewa cikin yan sa'o'in da suka wuce saitaga barinta tafita unguwa tareda kawarta a laifi bane domin yin hakan na iya sawa ta dada mantawa da wannan mummunan mutuwa data gani.

Mijinta Alhaji mukhtar yashigo cikin sauri har yanzu jaridar na hannunsa.
Ina kuma ikram zata bayan kina ganin halin da aka kawota daga makaranta dazu?
Kawarta zata raka unguwa nima da banso na barta ba to ammaa sainaga hakan na iya taimakawa wajen tausasa zuciyarta.
Hakane fa. Alhaji mukhtar yace yana sosa 'keya sannan yaci gaba
Daman ni yawace yawacen banza ne bana so da ku janye janyen marasa kunyar samarin nan barkatai. Uwar gidan nasa ta dubeshi cikin murmushi.
Amma duk da haka Dai Alhaji ai yakamata yarinyar nan ace yanzu ta sami miji kaga tunda yan kwanakin suka rage su kammala tana gamawa ayi mata aure kowa ya huta.
Eh ai nima baki nayi ba kuma sanin kanki ne duk da yake ni dan boko ne banfiya barin yarana su wuce karatu mai tsayi ba saboda lalacewar zamani to amma yana da kyau ace an samu dan mutunci kafin a amince mata da yin hira da samari kamar dai yanda yayyanta sukayi.
Alhaji to ai kaine duk wanda yazo saika kore shi tayaya ne to za'a tantance dan mutunci? Alhaji mukhtar yayi murmushi yace
Ai ke da kinga dan mutunci zaki ga yafita daban yanzu misali yaran da nace dake na kora rannan kina ganinsu kinga yan iska bakiga wani dan banza ba gashin kansa kamar shekar ungulu da wani burgujejen wando kamar buhu ko mufa a zamanin da mukayi boko ba muyi irin wannan sakarcin ba.
Hakane Alhaji saidai kuma kaci gaba da lura dai sosai domin acikin masu kamannin mutuncin ma akwai bata gari cuta a lullube saikaga saurayi tsaf dashi cikin dogayen kaya ga hula ta kamala kamar yaja limanci amma idan ya kuntata maka wani abin tsiyar to ko kare bazaici ba.
To muyi addu'ar Allah zaba mata na gari tunda abin haka ya zama. Alhaji mukhtar yace yana dubanta.
Lallai kam sai addua'a ta dada da cewa.

****** ****** ******* ******* **********************

Me ke damunka ne? Ilyasu ya tambayi labaran lokaci guda kuma yai fakin da motar a kofar katon kantin sayar da kayan tande tande da lashe lashe.
Tun sa'ar da suka fito daga gida ilyasu ya lura da shirun labaran yayi yawa da farko ya dauka tunanin yar budurwar nan ikhram ne ya hana labaran magana to amma sa'ar da tafiya tayi tafiya sai ilyasu ya lura da cewa ko magana yayi wa labaran baifiya amsawa ba wani lokacin sai yaga kamar labaran shi yake sauraro to amma da zarar yayi magana sai yaga labaran ko motsi yakasa yi ya kurawa gilashin gaban motar idanu kamar mutum mutumi wani abu kuma daya fara damun ilyasu shine haka kawai saiyaga labaran yayi doguwar ajiyar zuciya sannan kuma saiyaga nan da nan gumi ya lillibe shi. Dan haka koda yayi fakin da motar yanzu akofar kantin yaga kuma labaran baisan ma anzo ba sa yadace ya tambaye shi abinda ke damunsa.
Labaran ya juyo kusan arazane ya share gumi.
Wallahi..... wallahi tunani kawai nake labaran ya dubeshi cikin mamaki lokaci guda kuma ya bude kofar motar.
Tunanin menene haka kakeyi har da gumi? Labaran yayi kokarin watso murmushin yake to amma fatar bakinsa duk ta bushe dan haka sai murmushin ya tsaya a iya fata bakin nasa.
Kada ka damu..... Daman lokaci lokaci nakan yi irin wannan tunanin. Labaran yace adaidaii lokacin da suka fito daga cikin motar.
Ilyasu ya sake duban labaran yaso ya yasake cewa dashi wani abu to amma ganin gumin dake ta faman kwarara akan goshinsa kamar ruwa saiyaga bai kyautu ya dada damunsa da tambyoyi ba domin a tunanin ilyasu labaran shirin sumewa ma yake yi saboda irin alamun firgitar dake fuskarsa.
Samarin biyu suka fito kafada na gugar kafada suka nufi katon kantin.
In banda fuskar fayan ta jike sharkaf kamar yayi ido biyu da ifiritu to da sai ace tafiyar tasu gwanin sha'awa ce alokacin.
To amma duk da haka idan aka dubesu daga baya tafiyar na burge wasu musamman ma wasu yan mata kyawawa guda biyu dake binsu abaya suma suna kokarin shiga kantin.

Kai!!! Rukiya kinga wasu....budurwar tayi sauri ta tsaida kalamanta cikin gaggawa domin ganin duk dayake kalaman da take fadi kawarta ne to amma bai kyautu ba a matsayinta na yace domin zubar da aji ne?
Su wa zan gani? Rakiya ta tambaya tana duban kawarta Ikram.
A'a daman wallahi....uhm... Sai tayi

Please Login or Register in order to submit comment