Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanda zaeyi ya sanar mata..

Lalle in abokansa suka ji zasuyi masa dariya.. Amma ya zaeyi Haka Allah yake al' amarinsa.. (Dama hausawa sunce dan hakin daka raina shike tsone maka ido)

Muryarta ce ta dawo dashi daga duniyar daya lula.. Zan shiga ciki tace..

Ya hakuri wlh wani tunani ne ya dauke kaina.. Ba komae tace..

Kinyi kyau ya furta yana mata kallon kasa kasa.. Kasa magana tayi.. Dama yasan bazatai magana ba..

Ji tayi ya ruko hannunta, ya tsuguna akan guiwowinsa.. yace _Nurr_ *kina sona*?? *Zaki aure ni??* *Bae jira tayi magana ba ya cigaba*

*Allah ya dora min tsananin sonki* *tun ranar dana dora ido na akanki na kasa samun nutsuwa*

*Tun daga ranar na zama wani iri, Tun ina karyata zuciya ta akan cewa ina sonki, har nazo na fara gaskata hakan*

*Kece farin cikin rayuwata, I lurv u so much, i lurv u beyond imagination.. Dan Allah ki taimaki rayuwata*


Kafin ya kara magana suka ji an banko kofa da karfiii, gaba dayansu suka juyo a da saurin ganin waye haka......




Harphsart khabeer
[9/13, 3:23 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
5⃣6⃣➡6⃣0⃣

By harphsart Rano✍


Adaidaita sahu ta samu ta hau sae unguwarsu..

Daidai kofar gida ya ajiyeta, ta ciro kudinsa ta bashi, ta wuce ciki..

Da murnar ta ta shiga gidan, Cak ta tsaya ganin umma da ya kabeer cikin wani yanayi..

Karasawa tayi ta zauna tana duban umma.. Umma lafiya na ganku haka??

Ko dai jikin ne?? Girgiza mata kai umma tayi sannan ta shafo kanta, kin dawo?? Sannu da dawowa..

Bayan sun gaisa, tana lura dukkansu akwae damuwa tattare dasu..

Amma basu san su nuna mata.. ganin haka yasa ta share ta shga yin abubuwan da zasu faranta ran umma..

Da daddare suna zaune, Suna tattauna batun zuwan su kawu, amma basu bari tasan gudurinsu a kanta ba..

Kabeer ne yace umma nazo miki da albishir amma ganin mutanen nan yasa duk naso na manta..

Albishir din me kuma abba?? Kodai aikin ya samu ne?? Eh tou kusan hakan ne sae de wannan ya dan banbanta..

Wato kiran da alhaji yayi mun dazu ba komae bane illa ya sanar dani na zama cikin shiri rana ita yau zanje interview abuja..

Gwamnati tayi niyyar tura dalibai kasar waje.. Shine ya bada suna na wajen abokinsa kwamishi nan ilima..

Yanzu haka har na cike form din, sae dae addu'ar Allah ya bada sa'a.

Wani wawan ihu nurr ta saki ta dane shi kamar zata yarda shi..

Umma kuwa, bakinta yaki rufawa sae faman hamdala take wa Allah.. Tana fatan Allah ya bashi saa..

Dariya yake yana kallonsu, wannan farin ciki haka kamar ance yaci interview din..

Yayanah Allah ubangiji ya baka sa'a ta fada tana dan tsallen murna.. Amin kanwata

Abdoul yaron makocinsu ne yayi sallama, ya gaida umma sannan yace wai ana sallama da kabeeru a waje..

Wane ne ya tambaya?? Wani ne a cikin mota nima dae bansan shi ba yaron ya fada sannan ya juya..

Tashi yayi ya fita don ganin waye ke nemansa..

Safwan ne tsaye ya harde hannunsa jikin mota, da sauri kabeer ya karasa ya mika masa hannu..

Bayan sun gaisa ne yake sanar masa yazo ya sake duba jikin umma..

Ai dama baka aika an kirawo ni ba, ai yanzu an zama daya da shigowa kawae kayi ya fada sannan ya juya yace bismillah.

Ta dora kanta akan cinyar umma tana ta dariya, murna take kamar me..

Kabeer ne ya shigo, sannan ya biyo bayansa..

Umma tare fa muke da Dr ya fada yana jawo tabarma..

Sannu da zuwa likita kaine a gidan namu, ya gaishe ta nan take tambayarsa yasu hajiya suka dawo..

Sun dan taba hira a karshe ya mike zae tafi, dama tun shigowarsa nurr ta shige daki bayan ta gaisheshi..

Kabeer ne ya sake shigowa bayan ya raka shi yana kwala mata kira..

Kije dr yana san ganinki ya fada sannan ya wuce dakinsa.

A jikin mota ta tarar dashi ya kurawa hanya ido.. Karasowa tayi ta dan duka kadan ta gaishe shi..

Tsare ta yayi da manyan idanunsa..
Umm kinsan kinyi mun laifi ai shisa kikai saurin gaishe ni..

Laa laifin me nayi ma?? Ta fada tana turo baki.

Kinfi kowa sani ai.. Amma yanzu ba wannan ba..

Na same ki lafiya??
Lafiya klou ta amsa

Ya dan mata tambayoyi tana bashi amsa.. Sannan yace
Ya maganar danace zamuyi??

Umm zamu iya yinta yanzu ai ko?? Ta tambaya..

Ya dan kalli agogon hannunsa sannan yace. Owk lemme make it fast..


So nake naji Yaushe kike son komawa makaranta? Wat i mean shine kinason komawa skul dinku ne kiyi examz en achan.

Ko kinfi son wata skul din kije as external student?.

Kinga nan da two weeks zaa fara registration..

Nafiso nayi a skul dinmu, Kasan da tsada in dae wata skul dince.. Wannan ma da yaya zamu biya balle wata skul din..

Amma kinsan baa fiya cin examz a public skuls ba??

Eh na sani tou amma yaya zanyi,, banida zabi tunda ita ma public skul din sae mutum ya biya inde beci qualifyn ba..

Kuma kudin bae kai rabin na privt skul din ba..

Tom shikenan zan dawo in na samu lokaci.. Zanzo naga umma..

Akwae maganar da zamuyi da ita..

Duk maganar da suke kanta na kasa, bata san mesa ba batason hada ido dashi..

Kiran sunan ta yayi chan cikin makoshi, ta dan kalle shi kadan..

Mesa kike jin kunyata?? Ko har yanzu tsawar dana taba miki ce kika kasa amsawa??

Ni ba komae, kawae dae ina jin nauyinka ne..

Toh dago ki kalle ni.. Da dago da kanta a slow kamar wadda zata kalli dodo..

Da sauri ta sauke, dariya ma abun ya bashi..

Sae ji tayi mutum ya riko mata hannu, tayi kokarin ta kwace ya kuwa rike kam kam..

Zan tafi *nurr* ki shiga gida.. Toh ka sake ni, ta fada..

Kwaikwayon muryarta yayi yace um um ni bazan sake ki ba sae kin kalle ni..

Ganin bata da niyya yasa shi sakin hannunta aikuwa ta ruga da gudu ta shige gida..

Bubbuga kansa yayi yana murmushi..Sannan ya shiga mota yaja..

Ita kuwa tana shiga ta tarar da umma da ya kabeer a zaune..

Ka tsaye daki ta wuce suka bita da kallo kowa yana raya wani abu a ransa..

Cikin dare duk kansu sun kasa barci, juyi kawae suke kowa yana tuna dan uwansa..

Dukkansu ba wanda yasan soyayya cox basu taba..

Lalle koma mene wannan nakeji game da yarinyar nan me girma me safwan ya raya a zuciyarsa.(Ka fada lurv Malam jst admit it)lol..

Haka umma ma ta kwana da tunanin zuwansu kawu.. Tana jin tausayin yarta ta..






Harphsart khabeer
[9/13, 3:23 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
6⃣6⃣➡7⃣0⃣

By harphsart Rano✍



Tsaya wa tayi sororo tana dubansu.. Sake sake ta shiga yi a zuciar ta.. Wannan ai kamar dan gidan hajiya..

Gefen su ta bi da wuce tana kwala wa umma kira..

Dukkansu ba wanda ya tanka mata.. Mikewa yayi yana kallonta.. Baki bani amsa taba..

Ummm.. Ahhmm, duk ta duburburce. Jikinta sae rawa yake. Mtsw ya dan ja tsaki a hankali..
Wannan ta fiya kunya ya fada a ransa..

Juyawa tayi zata shige ciki, aikuwa ya tsare hanya..

Ya kafe ta da ido, ta dan kalle shi kadan, ya wani langabar da kai kamar karamin yaro..

Duk sae taji ma ya bata dariya.. Aikuwa ta shiga yi ba tsayawa..

Bai taba ganinta tana dariya irin haka ba.. Duk sae yaji ta burgesa..

Bayan ta dan tsaya da dariyar ne tace, ni ka matsa na shiga gida..

Aikuwa baki isa ba, sai dai mu kwana anan in dai baki amsa ni ba..

Wayar sa ce ta shiga kara, ya matso da bakinsa daedae kunnenta, daddy yana kirana, ki jira ni zan dawo anjima. And make sure kin tanadar min amsa na.



Ni kuwa dije in tambayeki mana, yaron nan dana tarar a zaure sae naga kamar dan gidan hajiya..

Eh shine a cewar umma, yaron yana da kirki sosae..

Emmm gaskiya jummai ta fada.. Toh ko akwae wata alaka tsakaninsu da yarinyar nan ne??

Gaskiya banajin akwai wata alaka, kawae mutunci.. Amma mesa kika ce haka??..

Hmmm, Ina tunanin yaran nan soyayya suke, dalili shine..

Lokacin da nazo kofar gidan nan, na dan buga kyauren naji shi kamar a rufe..
Tunani na ma ba kowa..
Har na juya sae naji magana sama sama, wannan dalilin yasa na bugo kofar da karfi..

Aikuwa naga yaron tsugunne gaban yarinyar wajenki kamar me neman gafara..

Umma ta danyi jummm sannan tace nidai jummai bana ce komai ba tunda bansan dalilin yin hakan ba.. Amma zan tuntube ta naji..


Ita kuwa nurr yana tafiya sae ta kasa shiga gidan.. Ta dade a tsaye, ganin tsaiwar vazatai mata ba, yasa taja wani dan dutse a kusa da ita ta zauna akai.

Tunani ta shiga yi, tana tuno yanda safwan ya tsaya yana fallasa mata asirin zuciyarshi..

Wani irin feeling taji yana shigarta.. hade da wata zazzafar soyayyarshi..

Ta lumshe ido ta bude, a hankali ta furta.. Ina sonka nima.

Umma ta fto raka jummai kawae taga nurr a zaune, Me kike yi anan kuma?? Umm ba komai. Ta tashi ta wuce ciki.

Umma tana lura da ita, duk ta zama wata silent..

Wai meke damunki ne?? Ehh?? Ba komai umma.

Tai ta zuba ido taga dawowar safwan amma har suka kwanta bashi ba alamar sa..

Umma kuwa murna take da su kawo basu dawo ba gashi har dare yayi...

Shi kanshi ba asan ranshi yaki dawowa ba.. Bayan yaga daddy kuma sae aka kirashi a asibity..

Ba yanda ya iya dole ya bar zuwan sae kuma gobe..

Bayan ya dawo daga aiki ne, ya shirya. Allah Allah yake yaje ya ganta..

Tsaye ya tarar da daddy a compound din gidan yana amsa call..

Jiransa yayi har ya gama.. Ya juyo da kallonsa, muje ka rakani wata unguwa..

Innalillahi ya furta, shikenan daddy ya kashe masa ranar sa..

Haka suka fita, suje nan suje chan basu suka dawo ba sae wajen tara na dare..

Aikuwa washe gari daga wurin aiki ya wuce..

Zaune take tana wanke wanke, suna hira da umma jefi jefi..

Kinga bari na shiga gidan malam bala nayi musu barkan nan..

Tom sae kin dawo.. Bayan fitar umma ya iso kofar gidan..

Kai tsaye yayi sallama, gabanta ne ya fadi.. Da gudu ta mike tayi daki, hijab ta saka sannan ta fto..

tsaye ta tarar dashi a zauren gidan.. Kwana biyun nan da bai ganta ba duk sae yaga ta kara kyau..

Bayan ta gaisheshi taja bakinta tayi shiru..
Nan ya shiga zayyano mata dalilin da ya hanashi dawowa..

Ba komai ta furta.. Ina muka kwana a zancen mu?? Kin samo min amsa ta kuwa??

Daga masa kai tayi.. Ok ina jinki.. Jin tayi shiru yasa gabanshi ya fadi.. Karfa tace bata sonshi.. In kuwa tace bata sonshi, bai san ya zaeyi da ransa ba.

Muryarta ya tsinkaya tana cewa _Na amince_.. Alhamdulillahi ya furta, farin ciki fal zuciyarsa..

Sae kuma ya dan hada rai, da son ya kureta.. kin amince kamar ya?? Ban fuskance ki ba..

Kina nufin kice kina sona?? Daga mishi kai tayi.. Amsa nakeso da bakinki..

Eh inasonka ta fada, ta gudo ta shige gida.. Dariya yayi sannan ya girgiza kai..

Anyi mai wuyar, saura wannan kunyar kuma. Yasan bazata sake fitowa ba, shisa ma bai takura mata ba ya wuce..

Ana i sauran kwana daya tafiyar ya kabir abuja, suna zaune suna tattauna wa akan jarabawar..

Ita kuwa nurr duk hankalinta baya kansu, tunanin safwan dinta take, a kwana biyun nan ya koya mata wata zazzafar soyayyar shi..

Umma ce ta dan zungureta, ta juyo da sauri.. Tunanin me kike ne?? Ba komai umma.

Da sassafe ya kabir ya shirya..Bayan sunyi sallama da umna, nurr Har bakin titi ta raka shi sannan ta juyo gida..

Da azahar umma na zaune tana saka, Nurr kuwa ta aike ta makota.. ba zato ba tsammani, sae ganin su kawu tayi sun shigo..

Hantar cikin umma ce ta kada, fuskar nan tasu a murtuke..

Kaĺlon kallon suka shiga yiwa juna da umma.. Tashin hankali ya hana umma ta gaishesu..

Wato dije kin rika ko?? Kina ganinmu amma baza ki gaishe mu ba ko?? Lalle wuyanki ya isa yanka.. cewar baba ja'afaru

Rabu da ita yaya.. Ba wannan ne ya kawo mu ba.. Ina maryama?? Kar kiyi tunanin rashin dawowar mu akan lokaci ko mun fasa kudirinmu. Ko daya, kawai tafiyar gwaggawa ce ta same mu zuwa kauye..
Dan haka tana ina?? Ta fito mu wuce..

Sai a sannan tayi magana.. Na aika ta nan makwafta bari na kira muku ita..

Da sauri ta fice.. Sai gasu sun shigo tare.. ganin su kawu tsaye yasa tasha jinin jikinta..

Gaishe su tayi suka amsa a dakile.. Ke ba bata mana lokaci zakiyi ba, ki dauko kayanki kizo ki wuce mu tafi..

Cikin rashin fahimta tace mu tafi ena umma??

Hawaye ta gani a fuskar umma, kafin tayi magana kawu takur ya fisgota ya hankada ta waje..

Tana ihu tana turjewa haka ya turata mota suka jaaa..

Durkushewa umma tayi a wurin tana hawaye..
Ba abinda take tunawa sae halin da nurr zata shiga a wurinsu kawu..

Da kyar ta mike jiri na daukarta ta shige daki.. Haka ta wuni.




Ya dade yana sallama kafin nan umma ta fito, shimfida mishi tabarma tayi sannan taja kujera ta zauna..

Bayan sun gaisa yake tambayar umma kabir fa?? Na kwana biyu ban ganshi ba.. Kabir baya nan yaje abuja interview..

Har ya gama zamansa bai ga fitowarta ba.. Umma ni kuwa ina nurr banji duriyarta ba..

Nan umma ta shiga matsar kwalla, nan yaji hankalin sa ya tashi, kar dae wani abun ne ya sameta..

Umma me ya faru?? Wani abun ne ya sameta??

Yan uwan mahaifinta sunxo sun tafi da ita.. Sun tafi min da ita bansan inda zasu kai min ita..

Ina tsoron kar su cutar da ita don nasan basu da imani. Nan kuka yaci karfinta..

Kansa ne ya kulle. Kwata kwata ya rasa inda zancen umma ya dosa..

Sai daya tattaro nutsuwarsa sannan ya shiga baawa umma baki..

Ba abunda zasuyi mata umma.. Ba yan uwan mahaifinta bane.. Ai inaga kamar bazasu cutar da ita bako??

Bakasan su waye yan uwan mahaifinsu bane shisa.. Mutanen nan sunyi nisa a zalunci..
Ni nasan halinsu..

Nan umma ta shiga bashi labarin rayuwarsu. Tun daga sumaila har zuwa lokacin da suka yi aure da babansu nurr, zaman su a abuja..

Nan ta dan numfasa sannan tace..

Ranar da bazan taba mantawa da ita ba, ina zaune a falo muna waya da alhaji,(Babansu nurr kenan)..

Nan yake sanar dani ya samu kwangilar nan fa yanzu haka ma gobe zai wuce lagos..

Murna na shiga yi saboda nasan indai akai kwangilar nan mun gama warkewa..

Sallama naji, na katse wayar sannan na amsa sallamar..

Su uku suka shigo, jaafaru ne a gaba, sae tukur da sulaimanu suna bayansa..


Da sauri na mike ina gaishesu.. Ba wanda ya amsa mini sae sulaimanu.. Sae ma wani banzan kallo da suka bini dashi..

Na riga nasan halin yan uwan mijina, sam basa son shi amma basu taba nuna wa a agaban sa.
Shi kuwa da zuciya daya yake zaune dasu.

Ina wannan sakaran mijin naki? Yaje aiki na basu amsa, na wuce kitchen don kawo musu ruwa..

Bayan na ajiye ruwan na juya na wuce daki..
Suna zaune naji shigowar Alhaji..

Aikuwa yana ganinsu ya shiga washe baki, nan danan ya hau dawainiya dasu..

Da daddare ina jinsu suna hira, nan yake shaida musu ai gobe ma zaeje lagos akan wata kwangila..

Sunka shiga washe baki, amma a mota zakaje ko?? Tukur ya tambaya..

A ah a jirgi nakeson zuwa, suka dan dubi juna, Kai amma munso a mota zaka ai da mun bika...
Don wallahi ina matukar son zuwa lagos a cewar ja'afaru..

Jim ya danyi sannan yace va komai sai muje a motar..

Yawwa kaga sai mu tafi muna hirar mu har muje..

Ranar saboda murna tare suka kwana.. Raba dare sukau suna hira..

Ni kuwa duk sai naji hankali na bai kwanta ba. Da asubah bayan ya shigo daga masallaci..

Na kira sunansa, umm ni kuwa abban yara bana son tafiyar nan taka a mota..
Hankali na sam bai kwanta ba..

Karki damu, ba abunda zai faru. Kinga sun nuna min zasuje bai kamata na watsa musu kasa a ido ba...

Ba yanda na iya dole naja bakina nai shiru..






Harphsart khabeer
[9/13, 3:23 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
7⃣1⃣➡7⃣5⃣

By harphsart Rano✍


Ta dan numfasa sannan ta cigaba..

Haka suka shirya ina jinsu suka fito, a falo na shirya musu a bin kari.. Sai da sukaci sukayi katt.. Shikuwa alhaji ko abincin ya kasa zama yaci..

Sun fito zasu tafi ne sulaimanu yace ai shi bazai bisu ba..

Galla masa harara ja'afaru yayi sannan yace kadda Allah yasa kaje.

Na lura dakai kwata kwata bakason zumunci wlh.. Shidai shiru yayi yana sauraronsa..

Bayan da Alhaji bai yi dashi akan ya bisu ba amma sam yaki..

Haka suka ja suka tafi ko driver basu bari yaa bisu ba..

Haka kawai naji zuciyata ta cinke, kwata kwata hankali na bai kwanta ba..

Na dawo daki na zuba tagumi, chan naji dawowar yara daga makaranta..

Dole na mike na fita kafin su shigo su tarar dani a haka.. Kasancewar su yara masu wayo..

Chan dare sai ga kiran Alhaji, jikina na rawa na daga..

Jin muryarsa yasa nayi ajiyar zuciya.. Nan yake sanar dani sun isa lafiya sai gajiya..

Haka mukayi hirarmu sannan ya nema na bashi yaransa yaji muryoyinsu..

Sun dade suna zuba masa surutu daga karshe yayi mana sallama..

Tou kwanansu biyu a lagos, abinda yaje nema anyi nasaraa..

Da haka ya kirana yana sanar dani, Murna yake sosae nima na shiga tayashi..

Washegari suka shirya don juyowa...

Ina zaune a parlour, Ina jiran isowarsu. A lissafin da nayi dga fitowarsu nasan suna gab da shigowa..

Tun Ina zuba ido ina duba lokaci har tara na dare babu su ba alamarsu..

Waya kuwa na kira sau ba adadi, amsar dae daya ce akashe take.. Nan fa hankali na ya tashi..
Ganin zaman bazae mun ba yasa na dauro alwala..


Ina nan akan sallaya naji shigowar mota, zumbur na mike nayi waje..

Sororo na tsaya ina kallonsu. Dukkaninsu sun sunkuyar dakai kasa.. Wani bakin mutum na gani gefensu yasha riga da wando. Babu alamun fara'a a fuskarsa..

Gabana ne ya yanke ya fadi, Muryata na rawa na shiga tambayarsu, Lafiya yaya na ganku haka?? Ina mijina?? Me ya faru ku sanar dani?? Ba wanda ya tanka min..

Na shiga rusa kuka, ganin zan tara musu jama'a yasa tukur daka min tsawa. Mijinki Allah yayi masa rasuwa..

Kuma maganar gawarsa mun riga mun binne ta achan saboda mun isa

Jiri naji yana dibana bansan sanda na yanke jiki na fadi ba..

Toh bayan sati daya da mutuwar alhaji, sun tsaya sosae wajen karbar gaisuwa...

Ina zaune a daki, tukur ya shigo min ko sallama babu..

Gobe ki shirya zamu je wani guri.. acewar tukur, Kuma tare da yaran, sannan bana bukatar ki dau wani abu..

Da sanyin safiya muka kama hanya.. Muna ta tafiya, sai gamu a kano.. Wannan gidan da muke ciki shi ya kawo mu ya dire, wannan shine abunda kula mallaka keda yayanki na daga dukiyar dan uwanmu..

Kuma anan nakeso ku cigaba da zama dan nima kwanannan zan dawo garin

Karki tunanin guduwa da yayan dan'uwanmu, duk wani motsinki ido na na kai, yana kaiwa nan yajuya ya tafi..




Safwan ya zaro handkerchp ya goge kwallar data zubo masa..

Lallai umma kunga rayuwa, In sha Allah nayi miki alkawarin sai na kwato muku yancinku..

A ah Dr karka sa kanka cikin hatsari.. Mutanen nan basu da imani..

Ba komai umma, Allah yana tare da mai gaskiya..

Yanzu ki bani adress din shi wanda ya tfi da nurr..

Iya zamana ban taba zuwa gidansa ba amma nasan a unguwar dorayi yake..

Toh shikenan umma ni zan koma amma kiyi hakuri.. Zan shigo da safe kafin na tafi aiki..




☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Bangaren nurr kuwa, tunda suka tafi hanya take kuka.. Ba wanda ya tanka mata a cikinsu..


Suna isa gidan duk suka fito daga motar, ganin bata da niyyar fitowa yasa kawu zuro hannusa ya rankwasheta sannan yace toh fito ja'ira mai halin uwarta..


Zabin rankwashin taji har kwakwalwarta.. Ba shiri ta fito..

Gida ne mai kyau, Suna shiga gidan ashariya ce ta fara yi musu maraba.. Suwaiba ce matar kawu tukur take ruwan balaee..

Toh jahila dabba, kefa kwta kwata kwakwalwar kifi gareki.. Sai ihu kike kamar wata jaka.. A cewar kawu..

Aikuwa ba shiru ta juyo kansa ta fara surfa masa ruwan masifa..


Kada kansa yayi ya shige ciki baba ja'afaru ya mara masa baya..

Sai a sannan suwaiba ta lura da nurr... Sarai tasan tare suke da mijinta don tasan komai.. Amma kuma sai ta nuna kamar bata masan wace ba..

Kallonta tayi a wulakance sannan tace ke kuma fa?? Kin wani tsare ni da ido kamar mayya.
Dallah zo ki wuce kafin raina ya baci.. (Har na hango idon maryama, dama ga shegen tsoro kamar farar kura🙊)

Sim sim sim nurr ta wuce ta dau hanyar dakin data ga su kawo sun shiga..

Ai kuwa sae ji tayi an fisgota, na yarda baki da hankali, ina kuma zaki.. Ga inda nake nuna miki chan..

Kallon hannun ta tayi taga inda take nuna matan, wani dan kurkutacchen daki ne irin na karkashin bene..

Da sauri ta mayarda kallonta zuwa ga suwaiba,

Auw wai kin zata zan kaiki daki na ne?? Lalle yarinya wuyanki ya isa yanka.. Dallah janye tsumman kafafuwanki daga nan..(wayyo Allah nurr dita😭😭)

Kuka ta shiga yi ta nufi dan kurkutacchen dakin..

Suwaiba ce ta shiga tafa hannu tana salati, kuka kike yi yarinya?? Lalle kuwa hawayenki zasu kare..


♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Bayan ya isa gida kai tsaye daki ya wuce, khaleel na ya shigo yace yazo mummy tana kiransa..

A falo ya tarar dasu dukka, gefen islam ya samu ya zauna..

Muje dakina inason mafana dakai.. Mikewa yayi yabi bayan mommy..

A gefen gado ya zauna ya tallafo fuskarsa yana kallon mommy..

Kasan dalilin dayasa na kiraka?? A ah mommy.

Toh ba wani abu bane illa jiya munyi magana da daddyn ku yace na fada maka, lallai lallai ka fada masa yarinyar da kake so, don ya lura kwana biyu kana yawan fita, kuma ana gaya masa ana yawan ganinka a hanyar hotoro.

Toh yasan duk yanda akai budurwa ka samu a unguwa..

Kasan daddyn ku baya son ai prolongin abu shi yasa yace ka sanar dani sai suje su tambayar maka aurenta..

Dankari ya fada cikin zuciyarsa.. Ana wata ga wata.. Shidai yasan yana son nurr amma a halin da ake ciki bazai iya kai daddy gurin yan uwan babanta ba saboda yasan halin daddynsa.. Baya son mutane irinsu kawu.. kuma madai ya fiso ta gama karatunta

Yadai? Naji kayi shiru.. Ummm dama mommy akwai yarinyar danake so amma kuma yarinya ce karama, She's jst 16

What?? 16?? Kaina kake son Yar 16yra?? I dont believ it, Anya ba raenan wayo zakai ba kuwa safwan?? Nasha jin hirarka dasu *jabeer* akan irin matar da kakeso..


Wallahi mommy da gaske nake miki yarinya ce karama.. Jinjina kanta tayi tana kallonsa.. Shikenan zan fada wa daddyn naku haka.. Tashi kaje.
Sai daya bude fridge ya dau fresh milk mai sanyi sannan ya wuce..






♡♡Thanks all for ur well wishes, Am getting much better






Harphsart khabeer
[9/13, 3:23 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
7⃣6⃣➡7⃣8⃣

By Harphsart Rano✍


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆


Yana komawa daki ya fada kan gado, Dafe kansa yayi.. Tunani ya shiga yi..

Labarin da umma ta bashi ya tsaya masa rae.. And gaskiya yana suspecting wani abu..

Allah sarki Nurr dinshi ko wanne hali take ciki?? Ba shida amsar tambayar nan..

Ji yayi yana bala'een son ganinta, Amma yasan ba hali.. Zuciyarsa tae masa nauyi..

Wayarsa ce ta shiga kara, dubawa yayi yaga bakuwar number..

Bin wayar yayi da kallo harta katse, after sum minutes sae ga kiran ya kara shigowa.

Tsaki yaja sannan ya daga wayar ya kara a kunnensa..

Daga dayan bangaren yaji ance haba Aboki ina ta kirankw tun last week amma baka piking..

Dan Allah kayi hakuri kila bangani bane ya bashi amsa..

Ba komai ya gida ya aiki, cire wayar yayi a kunne ya dan kalli numbar sannan ya mayar..

Sun dan gaisa sama sama, alamun da sadeeq yaji ya gane sam safwan bai gane waye ba..

Na lura sam baka ma gane waye bako?? Kafin yace komae ya cigaba,, Abokinka ne da kuka hadu a mall..

Lalalala kace naso nayi laifi,

Please Login or Register in order to submit comment