Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sae kallon sadeeq yake yana mamaki, lalle dama ashe zuwan da yake wurin maryam don ya samu wasu informations ne.

Jin muryar sadeeq yayi yana tambayarsu ko zasu iya yiwa kotu bayanin kwangilar da za suyi da alhaji wada??

Da sauri zubair ya mike, ya mai grm mai shari'a barrister sadeeq bae kamata shima ya shiga personal affairs ba..

Barrister sadeeq a kiyaye cewar alkali..

Kada kai yayi sannan ya cigaba, inason kotu ta gayyato detective salim..

Ina detective salim kotu nasan ganinka.

Tsaf ya fito a alhaji wadan sa, shigowa yayi cikin kotu, baki galala su kawu suka bishi da kallo..

Bayan ya tsaya barrister sadeeq ya bukaci ya bawa kotu labarin abunda ya hada su da su kawu..


Nan ya kwashe komae ya sanar da kotu, karya kake inji baba ja'afaru.
Mu zaka ci amana? Daka masa tsawa alkali yayi sanna yayi shiru..

Sadeeq ne yayi wani mugun smillin sanna yace ko detectv salim zae iya bamu shaida akan abunda ya fada??

Ba tare da bata lokaci ba ya jawo recordersa ya mikawa sadeeq.. Nan shikuma ya mikata zuwa ga alkali.

Aka jona gaba daya muryarsu kawu ya karade kotu.. Kusan zawo su kawu suka kusa yi a wandoπŸ˜‚πŸ˜‚..

Barrister sadeeq ya kalli su bayan an gama ji yace ko zaku iya cewa wannan ba muryarku bace??.

Objection my lord, bae kamata barrister ya dunga neman dole sae sun amsa laifinsu ba.

In akae la'akari da zamanin da muke ciki yanzu, komae zaa iya yi da computer don a samu cinma wani burin..

Jin muryarsu bashi zae nuna sune sukae maganar ba..

Koarafi bai karbu ba, barrister sadeeq go ahead, nagode ya mai grma ma shari'a..

Bayan yan tambayoyi da yayi wa su kawu barrister zubair ya nemi kotu ta daga shari'ar zuwa wani lokacin.. Kwarai sadeeq yaji dadin wannan maganar. Nan take alkali ya amince aka daga shari'ar zuwa mako mae zuwa..


β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†

Bayan sati daya, kabeer ya daga zuwa kasar cyprust✈, kuka ne sun shashi, kamar bazasu rabu ba.

Bakin cikinsa daya baya nan zaa gama shari'ar amma ba komae duk yanda ake ciki yasan safwan zae tsaya musu..


Toh kasancewar mutane suna so suga yanda shari'ar zata kasance yasa kotun cika makil..

Bayan alkali ya zauna ya nemi fara shari'ar..

Shari'ar ta dau zafi duk wani hujja da sadeeq ya kawo sae zubair ya warwareta..

Kwata kwta sadeeq jikinsa yayi sanyi ganin kamar baza suyi nasara ba..

Bayan yan rubuce rubucen alkali, zare glass din sa yayi sannan ya numfasa.

A bisa rashi wasu gamsassun hujjoji daga bangarorin biyu, kotu ta....

A dakata dakata wani dan sanda ya shigo yana fada. Gaba daya hankalin kowa ya koma kansa..

Wani bakin mutum ne ke biye dashi,..

Kallon kallon suka shiga yi dasu kawu.. Bayan ya sami guri ya tsaya, sadeeq ya shiga watso masa tambayoyi, labari ya shiga bawa kotu tun tafiyar su kawu lagos har zuwa neman da sukayi masa,

Sun shirya akan ya tare su akan hanyarsu ta dawowa kamar yan fashi.. Suna so ya halaka musu dan uwa amma kafin nan sae dan uwan nasu yayi signin a duk wani kadarorinsa..

Haka kuwa akayi, bayan mun tare su nida yara na.. muka bukaci kudi masu yawa.. Ganin bae fito da kudi ba yasa muka yi masa barazanar halaka yan uwansa...

Nan take ya rikice, ya shiga bamu hakuri, dariya nayi sannan na kalle shi.. lalle kana son yan uwan nan naka da yawa while su kuma masu sonka..

Nan suka fada masa komae da irin tsanar da sukayi masa, a take suka umarce shi daya mallaka musu komae nasa ko kuma suzo su halaka iyalinsa.

Bae wani yi jayayye ba ya mallaka musu komae nasa..

haka tukur ya dauki wani katon dutse agefe ya kwala masa akae. Wata gigitacciyar kara ya saki, bae hakura ba sae daya kara kwala masa dutsen nan a cinyarsa

Ni kaina sae dana tausaya masa, take ya fadi kasa ba numfashi..

Haka muka shigo motar su muka taho gida..

Kasa nutsuwa nayi bayan abun ya faru, da safe na kama hanya na koma wajen, ina zuwa na tarar da bawan Allah nan ya kwance,..
Wani farin abu na fta daga bakinsa..


A nan zan tsaya ya mai shari'a amma inaso na gabatar wa kotu da wanda zae cigaba da yiwa kotu daga inda na tsaya..

Wani mutum naga an gurguro akan wheel chair,


Aikuwa kawu bae san lokacin daya sulale ya saki fitsari baπŸ™ŠπŸ™Š



waye wannan ya shigo?? Mene alakarsu da kawu?? Ku biyoni don jin yadda zata kaya.



Harphsart khabeer
[9/13, 3:23 PM] Fati Novel: πŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“Ώ

πŸŽ€Guguwar SoπŸŽ€
9⃣6βƒ£βž‘9⃣8⃣

By harphsart Rano✍


β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†

Wata irin zabura umma tayi, bakinta kwata kwata ya kasa furta komae, sae mika hannu da take tana kokarin yin magana..

Kirjinta ne ya buga da karfi, Tasa hannu ta dafe wajen. *ALHAJi* ta furta da karfin gaske wanda ya kara jawo hankulan mutane.
kuka ta saki mai ban tausayi ta karaso wajen kujerar ta tsuguna tana kallonsa tana kuka..😭😭

Shi kansa kuka yake yi, da yana da yanda zaeyi daya mike..

Sadeeq na hango yana ta murmushi, da alama yasan wani abu..

Shiko safwan kallonsa ya shiga yi alamar yana neman karin bayani.

Kotun gaba daya ta hargitse kowa na tofa albarkacin bakinsa..,

Alkali ne ya bugu table sannan akayi shiru..

Da kyar umma ta mike ta koma gun zamanta aka tura alhaji zuwa gaban alkali..

Gaba daya jikin barrister zubair ya gama sanyi..

Gefe ya samu ya zauna yana kallon yadda wannan shari'a zata kaya..

Alkali da kansa ya kalli alhaji yace bawan Allah ko zaka iya yiwa kotu bayanin kai waye??

Mene alakar ka da wannan mutumin da yake tsaye ya nuna audu lauje, da kuma wadannan mutanen ya nuna su kawu..

Sae a sannan na hango kawu yayi zaman dirshan, zufa duk ta wanke masa jikiπŸ˜‚..

Shiko baba ja'afaru bakinsa sae zikiri yake..

Kallonsu yayi a nutse sannan ya maida kallonsa zuwa ga alkali..

Murya chan kasa kasa ya fara magana.

Ya mai girma mai shari'a wa dannan bayin Allah yan uwana ne. Ubanmu daya dasu.

Dukkan abunda bawan Allah nan ya fada gaskiya ne.

Don kuwa bayan sun jima da tafiya sae na farfado..

Kasancewar dukan da yaya yayi mun aka yasa naji komae na manta dashi..

Bude ido nayi da kyar ina kallon wajen da nake, kwata kwata na kasa tunowa da abunda ya faru..

Haka na karasa kwana a gurin kasancewar dare ne.. Gashi ina jin wani zugi a kafata..

Inanan ina tunanin kaina, na kasa tuna komae na rayuwata..

Ji nayi kamar tafia, bana iya bude ido na sam.. bayan sun karadi naji daya yace taimaka ka kama min shi..

daga ni naji anyi an dora ni akan wani abu kamar jaki, sae da mukayi tafiya mae nisa sannan muka isa wani kauye.

Sati na daya a kauyen nan na far warwarewa sae dae bana tuna komae, gashi kafata ta sami matsala bana iya tafiya..

Kullum na tambayi mutanen nan waye ni sae suce suma basu sanni ba..

Wani mutum ne ya roke su dasu dinga kula dani shi kuma zae dunga zuwa yana dubani yana biyansu.

Sosae mutanen nan suka nuna min karamci tsawon shekarun nan..

Shi ko wannan bawan Allah yana zuwa lokaci zuwa lokaci ya duba ni.. Shi nake gani a matsayin dan uwana.

Katsam ranar nan sae gashi yazo, bayan mun dan taba hira yawanci hirar akan abubuwan da zaesa in tuno da kaina yake mun amma kwata kwata na kasa dawowa.

Sunan su yaya ya shiga fada min da karfin gaske, nan take naji kaina yana juyawa.. Ban sake sanin inda kaina yake ba sae dana farfado,..

Bin dakin nayi da kallo ina mamakin abinda ya kawo ni.. Wannan bawan Allah shi idona ya fara sauka akansa.

Zabura nayi saboda bazan taba mantawa da wannnan fuskar ba..

Umartar su yayi da su bamu wuri.. Daki daki ya shiga bani labarin abinda ya faru..

Nayi kuka sosae ganin cewa duk wannan tsawon lokacin bana tare da iyalina..

Daga karshe ya nemi tafiya dani, sosae mutanen nan suka ji ba dadi..

An riga an saba kwarai, Sati na daya a gidan wannn bawan Allahn..

Sae daya tabbaatar na dawo hankali na fully sannan muka taho nan.

Kuka yaci karfin sa, gaba daya kotun ba wanda bae zubar da hawaye ba..😭😭

Shi kansan alkali ina kallonsa yasa hanky ya goge kwallar data zubo masa..

Nurr kuwa kuka take kamar ranta zae fita wanda bata dade da zuwa wajen ba..

Shima ganin dole ya kamata tazo, alhaji na fara labarinsa safwan ya fita yaje ya daukota..

Alkali ne ya tattaro nutsuwarsa sannan yace..

Ko wa'anda ake kara suna da ja akan abinda wadannan bayin Allahn suka gabatar wa kotu??

Ba wanda ya iya daga kansa balle ya amsa..

(Ni ina ganin kawu saboda tsabar rikicewa sumansa gomaπŸ˜‚πŸ˜‚)


Toh abisa wadannan kwarararn hujjojin da mukaji, Kotu ta yankewa tukur hamza zaman gidan yari na Wata biyar, tare da tarar naira dubu dari biyar..

Inda ta yankewa ja'afaru zaman gidan yari na wata biyu.. Tare da tarar naira dubu dari biyu..

Bayan haka kotu na umartar su dasu damkawa alhaji abubakar da iyalinsa duk kadarorinsu..

Bugu table yayi sannan ya mike..

Aka tusa keyar su kawu..

Da gudu umma da nurr suka karaso wajen abba..

Kuka suke gwanin ban tausayi safwan yana tsaye yana kallonsu..

Sadeeq ne ya taho da fara'arsa, kafin ya karaso yaga wata kamar maryam dinsa.. Kara sauri yayi, yana zuwa dae dae kusa dasu yaji abban nurr yana shafa kanta..

Ya isa nurr dita kukan ya isa, ki bar kuka haka kinji maryama ta..


Innalillahi wa inna ilaihi rajiun...Jiri jiri ya faara ji yana daukarsa...

maryam dinsa ita ce nurr din safwan...

Ko gabansa baya gani, haka ya fito yana daddafa bango har ya ta fto wajen motarsa.

Sae daya shiga ya zauna kawae yaji bazae iya tuka motar ba..

Yafi minti talatin ya kifa kansa akan sitiyarin motarsa.

Wani kurtu ne ya lura da halin da yake ciki. Da sauri ya karaso ya shiga kwankwasa masa glass..

Da kyar ya dago kansa idonsa yayi jaa, Kallon kurtun ya shiga yi..

Sae kuma ya sauke glass din yana kallonsa. Yallabai naga ka dade anan shine nazo naga ko lafiya??..

Daga masa hannu yayi alamun ba komi sannan yaja motar..

Da kyar ya isa gida..
Fadawa yayi kan sofa, ya saki ajiyar zuciya, tunani ya shiga yi.

Wani irin son nurr ke dawainiya dashi.

Ya riga ya kamu da sonta dumu dumu,.. Ashe budurwar abokinsa yake so..

Bai ankara ba yaji wani zazzafan hawaye. Hannu yasa ya share..

A rayuwarsa mutum ne shi mai barkwanci.

Bae fiya daukar abu serious ba at all. Komi nasa a wasa yake yinsa.

Ya taba soyayya da wata yarinya a kibiya,

Sosae ya shaku da ita, amma bae taba furta mata so ba. Kwatsam yaji an sa mata rana..

Tun daga ranar bae sake soyayya da wata ba sae maryam... shikenan kuma shi bashi da sa'a..


Safwan ne ya fto yana duba sadeeq, mamaki ya kamasa ganin ba motar sadeeq..

Sae da su umma suka shiga motar da su abba sukazo sannan shima ya shiga tasa..


Ya lula duniyar tunani bae san ana ta buga masa kofa ba.. Firgigit ya dawo yaji alamun buga kofa..

Da kyar ya iya tashi ya bude kofar. Safwan ya gani tsaye

Kallon tuhuma ya shiga aika masa.. Malam ya na ganka haka kamar wani mara lafiya ya fada yana shiga ciki..

Mene ne ma dalilinka da zaka taho baka fada min ba..


Yake sadeeq yayi sannan ya amsa masa.
Kaina kedan cio.

Lalle ma barrister ban taba sanin irin zaman da muke kenan ba.. Ai ni a tunani na yanzu mun zama daya..

Banga alamun ciwon kai atare da kai ba.. Naga alamun kunchi da tashin hankali a idonunka..

Ka taimaka ka fada min dan allah..

Zuciyarsa yaji ta tsinke ganin yanda safwan ya damu..

Take yace masa kaga safwan kirana akae hajiyata bata da lafia amma dae ance da sauki shisa ka ganni haka..

Da sauri safwan ya mike, a ah zama bae same mu ba tashi tashi mu tafi..

Calm down aboki nayi waya dasu ma.. Da sauki.

Tom shikenan Allah ya kara mata lafiya..

Yanzu tashi zakayi mu tafi gidansu nurr don Alhajinsu yana son ganinka..

Nasan ma yanzu sun karasa mu kawae suke jira..

Allah sarki sadeeq😭😭



Harphsart khabeer
[9/13, 3:23 PM] Fati Novel: πŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“Ώ

πŸŽ€Guguwar SoπŸŽ€
1⃣0⃣0⃣ ➑ 1⃣0⃣5⃣

By _Harphsart Rano_


Tun daka dawo kake kwance a daki, haba abubakar sadeeq ya kamata ka sanar dani damuwarka..

Gyara kwancia yayi sannan ya kalli tsohuwa, hawaye ta gani a gefen idonsa..

Salati ta shiga rafkawa kamar anyi mutuwa.. Me zan gani?? Kuka abubakar??

Lalle koma mene wannan abu ne me girma. Ganin tsohuwa zata tara masa jama'a yasa shi mikewa da kyar..

Riko hannunta yayi suka zauna gefen katifa, cikin dauriya ya shiga yi mata bayani..

Dalla dalla ya warware mata komae, cike da tausayawa take kallonsa..

Ta sani sarai soyayya ba abune mae sauki ba, musamman idan mutum yana *son maso wani*..

Lallashinsa ta shiga yi tana bashi baki, daga mata kai kawae yake amma harga Allah ba sauraranta yake ba..

Bayan ta gama zuba waazinta ta tashi ta fta, maimakon ya mike kamar yadda ta umarce shi sae ya kara kwancia..

Shigowa ta sake yi rike da kwano a hannunta.. Sae jug din ruwa..

Tashi maza kaci abinci, kaga ko iyayen naka baka je ka gaishesu ba..

Dan dole ya ci abincin nan amma na dadinsa yake ji ba..

Wanka yayi ya fto ya shrya, so empty yake jinsa.. Wayoyinsa ya jawo wanda rabonsa da kunnasu har ya manta..

Yana kunnawa messeges suka fara rige rigen shigowa, wasu na abokan aikinsa ne, detective salim, Sae na kamfanin airtel..

Dayan wayar ya kunna wadda mtn dinsa ke kai, ai kuwa messeges din safwan suka dunga shigowa a jere..

Sae daya bari suka gama shigowa sannan ya fara dubawa daya bayan daya..

Duk yawanci akan dalilin kashe wayar sa ne kuma yaje gida bae sameshi ba..

Na karshen ne ya dan bashi daria wanda ya turo shi dazu dazun nan..

Malam in ka kunna wayar sae ka dawo ga maryaman ka nan na samo maka ita.. Zancen da nake ma yanzu haka ma ta amince ta soyayyarka..


Allah sarki safwan, nagode da kulawarka gareni, amma dole nayi nisa dakae..

Na riga na sani nurr itace farin cikinka...
Dukda nima itace farin ciki na amma tafi dacewa dakae..
Hakika kai masoyinta ne na gaskiya..

Shi kadae yake maganganunsa cikin kunar rae..

Kaka na gefe tana matsar hawaye.. Nima kaina sadeeq ya bani tausayi.. (Karka damu sadeeq zan baka yata *hanan*😜)..

Sake kashe wayoyin yayi sannan ya fice daga gidan, a tsakar gida ya taarar da hajiyansa tana alwala..

Maraba da abubukar sadeeq, yanzu kake tafe?? Yake yayi sannan ya gaida ta..

Daki ya wuce ya samu kan kujera ya kwanta..

a zaune ya tarar da sumayya tana danne dannen waya..


Tun shigowarsa hajia ta fuskanci yana tare da damuwa..

Sae data idar da sallah sannan kalle shi.. Abubakar me yake damunka?? Kana tare da damuwa, kar kayi kokarin boye min.. Ni mahaifiyarka ce..

Mikewa sumayya tayi ta shiga daki don basu guri..

Baeyi yinkurin boye mata ba, a nutse ya warware mata komae kamar yanda ya sanar da tsohuwa..


Sallama aka shiga yi, wani saurayin yaro ne ya shigo, hajiya ina wuni? Dama wasu ne suka ce nayi musu sallama da sadeeq..

Mamaki ne ya cika sa, shiko waxae yi sallama dashi.. Mikewa yayi yabi bayan saurayin don ganin me sallama..

Kunya ce ta rufeshi ganin safwan tare da detective salim..

Safwan ya harde hannu kawae yana masa kallon tuhuma..

Komawa ciki yayi ya sanar da hajiya sannan ya shigo dasu..

Sun gaisa da hajiya cikin mutunci, ruwa tasa sumayya kanwar sadeeq ta kawo musu..

Detective salim sae kallonta yake, sae da sadeeq ya kai masa duka sannan ya wayence..

Dakinsa ya kaisu, bayan sun zauna safwan ya hayyayako wa sadeeq..

Shiru bae tanka masa ba sae daya gama balbalin sa.. Hakuri ya shiga bashi..

Dalilin tahowarka ba sanar wa sannan kuma ka kashe dukka wayoyinka nake son sani inji safwan..

Dadina dakae rigima cewar sadeeq, nifa ba don wani abu na taho ba.. Kiran gaggawa ne ya sameni..

Kafin nazo kuma chargy ne ya kare..

Tun da nazo ina gidan tsohuwa, ban samu nayi chargy ba kuma..

Haka yaeta kare kansa har ya tabbatar da safwan ya gamsu..

Hira suka shiga yi ta yaushe gamo.. A cikin hirar ne safwan yake shaidawa sadeeq ai an riga an kai kudin aure gidansu nurr..

Ras ras kirjinsa ya buga, hannu yasa ya danne wajen.. jiri jiri yaji ya fara daukarsa..

Idonsa sam ya rufe baya ganin gabansa.. kansa suka yo gaba dya suna tambayarsa..

Bashida bakin amsa musu, cigaba da ganin baki yayi daka karshe ya sulale kasa ya fadi..

Da gudu salim ya fita yana kwalawa hajiya kira..

A hanzarce ta fito tana tambayar ki lafia.. Dakin sadeeq din suka shiga lokacin safwan ya dukufa ganin ya bashi first aid..

Kuka hajiya take wiwi sumayya na taya ta...
Sumayya ce ta ruga sae gidan tsohuwa..

Tare suka juyo da tsohuwar tana tafe tana sumbatu..

Tana zuwa ta fada dakin, lokacin sadeeq ya farfado amma har yanzu bugun zuciyarsa bae tsaya ba...

Rike masa hannu tayi tana kuka, yanzu dan nan so kake ka kashe kanka?? Akan yarinyar dabatasan kanayi ba ehee..

Ganin kaka zata tona masa asiri ya sashi saurin rufe mata baki yana girgiza mata kai..

Safwan ne ya kalli hajiya sannan yace, hajiya inaganin dole zamu tafi sa shi asibiti dan aduba lafiarsa sosae..

Ban taho da kayan aiki na ba, kuma akwae abunda nke son na tabbatar game da rashin lafiyar tasa..

Haka suka fto gaba daya, nan tsohuwa tace ai sam bata san zance ba da ita zaa.. dole hajiya ta hakura..

β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†

Nurr kwance sae faman kuka take tun da aka ce an karbi kudin aurenta ta ke jin wani yanayi..

Ba wanda take son gani sae sadeeq, mesa zae mata haka?? Tana son tayi magana dashi..

Umma kwata kwata ta kasa gane kanta.. Tun tana lallashinta har ta hakura da zuba mata ido.. Abba ne ma mae kokarin lallashin nata..

Tambayar duniya yayi mata akan in safwan din ne bata so ta sanar masa, shiko zae mayar msu da kudinsu ya basu hakuri..

In tace bata son safwan tayi karya, kawae dae ita ta tasa dalilin da yasa take jin sadeeq sosae a cikin zuciyarta..

β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘

Lokacin da suka isa asibiti safwan yayi makinv duk wani arrangement, gado aka bawa sadeeq bayan gano yanda jininsa yayi mugun hawa..

Yana kwance an jona masa drip sumayya da tsohuwa na gefensa..

Safwan ne a shigo,ganin har barci ya daukeshi yasa yayi musu sallama akan zae je ya dawo.. Godiya kaka ta shiga yi masa sannan ya wuce gida..

Sannin cewa mommy tasan dalilin tafiyarsa kibiya yasa da taji batun rashin lafiar yasa ta tausayawa sadeeq..

Kitchen suka shiga tare da mai aiki don hada abincin da zaa kai asibitin..

Bayan yayi wanka ya shirya, abincin ya dauka ya fice, yana hanya ya kira nurr kasancewar yau tru out bae ji taba..

A sanyaye ta amsa, shi ya rasa abunda yake damun yarinyar nan..

Yayi yayi ta sanar masa da damuwarta taki.. Gaisawa kawae sukae ganin taki sakin jikinta yasa yae mata sallama..

Lokacin daya isa asibitin sadeeq bae farka ba, Allurar da yayi masa mae karfi ce.. yana bukatar hutu..

Da sallama ya shiga dakin, bayan sun gaisa da tsohuwa ya ajiye musu basket din abincin..

Matsawa gefen gadon yayi yana kallon abokinsa cike da tausaya wa..

Dole na nemo maka farin cikinka kamar yanda nima kayi kokari wajen dawowa abar sona da nata farin ckin..

A zuciyarsa yake maganar, a fili kuma ya furta, ga abinci nan inji mommy sanann in anjima zan kaiku gida wajenta ni zan kwana da sadeeq..

Mun gode sosae yaron kirki Allah saka maka da alkhairi.. ba komae tsohuwa..

Lokacin da suka zo tafiya already sadeeq ya farka... Bayan kaka ta sashi a gaba ya dan sha tea sannan suka wuce..

Sae daya kaisu wajen mommy sannan ya dauki abunda zae bukata ya koma asibiti..

A kishingide ya tarar da sadeeq, idonsa ya lumshe daga gani ba barci yake ba..

Dafa shi yayi, da sauri ya bude idonsa wanda suka yi jaa..

Pls barrister ka rage wannan tunanin, yanzu a stage din da kake u need to zero ur mind from duk wani tunani..

Pls abokina kayi mun wanan taimakon.. Murya chan kasa ya amsa yana murmushi.. Shikenan aboki na daena..

Sae daya gama duba patients dinsa sannan ya dawo dakin.. Dama yasan bazae sami sadeeq ido biyu ba..

Computer ya zawo ya shiga dube dube, Shi dama ba mae yawan barci bane..

Nan yake ganin zaai private waec nxt month.. Har ma an fara registration..

Kwata kwata bae samu wani barcin kirki ba,..

β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘

Bayan yayi sallah ya tashi sadeeq yayi sallah shima.. Sabuwar jallabiya fara ya bashi yasa bayan ya watsa ruwa..

Duk magungunan da ya kamata yasha yasha sannan safwan ya fice zuwa office..

Wajen 12 su mommy suka iso asibitin tare da tsohuwa, sumayya, iman, islam da khaleel.

Direct dakin suka wuce, bayan sun masa ya jiki, an dan taba hira wanda duk hirar da ake sadeeq jinsu yake..

Safwan zaune cikin office, tunanin kiran nurr ya zo masa.. Wayar sa ya jawo ya kirata..

Tana zaune a dakinta tana faman tunani, tana jin ringing din wayar, sae data kusa tsinkewa sannan ta daga..

Bata hakuri ya shiga yi karta ga ya share ta sadeeq ne bashi da lafia..

Wata irin zabura tayi da karfi ta furta me sameshi, mamaki ne ya kama safwan ganin yadda hankalinta ya tashi..

Ji yayi kamar tana kuka?? Lafiya nurr?? Daga cewa sadeeq ba lafia duk kin rikice..

Tunowar da tayi safwan bae san alakarta da sadeeq ba yasa tae maza ta ta hadiye kukanta..


Umm ba komae zan fada wa umma anjima zamuxo mu dubashi...

Alright tom Allah ya kawo ku ya fada sannan yayi mata sallama ya kashe wayar..

Mesa nurr ta chanja masa haka?? Akwae abunda take boye masa.. Koma dae mene zae bincika..

A falo ta tarar da umma da abba suna maganar fta da abba waje akan kafarsa..

Gefe ta samu ta zauna, Umma dama safwan ne ya kirani wae an kwantar da sadeeq a asibiti..

Ya salam.. Allah ya bashi lafia, cewar abba da umma..

Anjima ki shirya sae kije ki duba shi nima zanje daga baya saboda bakin sumaila da zasu inji umma.

β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†

Bayan ta shirya ta fito, kudin keke nepep umma ta bata sannan ta wuce..

Tana zuwa harabar asibitin ta kira safwan, kasancewar zae shga tiyata a time din yasa ya bata room number din..

Lokacin data karasa kofar room din sae ta sami kanta da kasa shiga..

Tana tsaye bata da niyyar shiga wata nurse tazo wucewa ta ganta a tsaye..

Malama yana ganki a tsaye ko kin bata room din ne??

A ah nan ne dakin ta fada tae saurin murda handle din kofar, chan ciki tayi sallama..

Idonsa a lumshe kasancewar su tsohuwa sun koma gida..

Sam baeji karar bude kofar ba saboda Hankali ta murde..

ji yayi ajikinsa kamar ana kallonsa, bude idonsa yayi a nutse..

Nurr ya gani a tsaye tana zubar da hawaye.. Hannu yasa alamun tazo, kallonsa take bata da alamun motsawa..

Tashi yayi da kyar ya jingina da pillow, a hankali ya furta sunanta..

Bata amsa ba sae dae ta tsaya da kukan da take,

Takowa tayi zuwa gaban gadon, durkusawa tayi kamar me kneel down.

Mesa zaka kaurace min?? Mesa ka gujeni a lokacin dana fi bukatarka? Mesa sae daka bari na shaku dakae sannan zaka barni??
Mene alakarku da safwan?? Ina son ka amsa min dukka tambayoyin nan..


Haba maryam, duk wannan tambayoyin ni kadae?? Ko tambayar ya jiki na baki ba??

Kunya ta rufe ta, ganin wautar da tayi..

Ya jiki ta furta, jiki da sauki nagode..

Daki daki ya shiga amsa mata tambayoyinta, kafin ya gama ta tsananta kukanta..

Kiyi hakuri maryam, safwan ya fini dacewa dake, nasan kuma kinfi sonsa akaena..
Dan Allah karki yarda ya fuskanci wata alaka a tsakaninmu kinji kanwata?? Kiyi min wannan alkawarin..

Bazata iya jure kalamansa ba, da gudu ta fice daga dakin tana jin yana kwala mata kiran.

Safwan ya fto daga theatre room yaga nurr tana kokarin fta daga asibitin...




M sorry fanz, naso na gama book en nan a page 100 buh due to sum risinx bazae yiwu ba.. I hope zaku yi mun hakuri for late post.. Banjin dadin jikina sosae..



Harphsart khabeer
[9/13, 3:23 PM] Fati Novel: πŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“Ώ
πŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“Ώ

πŸŽ€Guguwar SoπŸŽ€
9⃣9⃣

By harphsart Rano✍

Baya so safwan ya zargi wani abu, dole ya mike ya fada toilet.

Sae daya sauya kaya sannan suka fito. A hanya suna tafiya suna hira wanda duk safwan ke kawo hirar..

Yawanci hirar akan yanda shari'ar ta kasance..
Anan sadeeq yayi masa bayanin yadda suka hadu da audu lauje.

Shine wannan da yazo Gida ya sameshi.. Yaji labarin shiga

Please Login or Register in order to submit comment