Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saurin karasawa..

Jifan ta yayi ta wani kallo, sannan yace lafiya?? Cikin inda inda tace dama asibiti nakeson zuwa..

Ohh sae yanzu kika ganni kenan, ko gaishe ni kin gagara yi kina kallo na fto..

Kinga malama ba inda zanje dake ya fada yana sake shiga mota..

Rau rau tayi da ido ganin da gaske tafiya zaeyi ya barya..

Da azama ta zagaya bangarensa ta tsuguna har kasa sannan tace "Ya safwan dan Allah kayi hakuri wlh bansan ban gaishe ka ba.. inason zuwa naga umma dan allah ka taimaka min.

Kiris ya rage daria ta kufce masa, ganin yadda ta hade hannu ta wani runtse ido..

Hakan ya bashi damar kare mata kallo.. Zara zarar gashin idonta wanda suka kwanta kan kyakkyawar doguwar fuskar ta..

Ya kai dubansa kan kancinta wanda ya karawa fuskar tata kyau..

Dan bakinta ya kalla wanda in ka gani zakae tunanin tsokali bazae iya shiga ciki ba.. saboda kankanta.. Lumshi ido yayi ya bude yasake dora su akan face enta..

Lalle Allah yayi halitta.. Jin shirun yayi yawa yasata bude idonta..

Yanda ya kafe ta da ido ya sata jin kunya.. Tae maza ta rufe fuskarta ta tafin hannunta..

Mikewa tayi da sauri zata shige gida, yai saurin riko hannunta.. Wani irin shock sukaji dukkansu.. Tae saurin zame hannunta tana dubansa..

Ina zaki kuma?? Ban gama kallon kyakkyawar fuskarki ba..

Mamaki ne ya kamata, anya kuwa safwan ne yayi wannan furucin?..

Dariya yayi yace na baki mamaki ko?? Hmm ya gyara tsayuwa sannan ya dora..

Nurr an taba gaya miki ke kyakkyawa ce.. Kina da wani kyau me daukar hankali.. Lalle Allah yayi miki baiwa wanda ya dace ki gode masa..

Tsananin mamaki yasa ta kasa magana.. Kallonsa ma ta kasa yi amma tana tsaye kamar wadda aka dasa..

Ganin bata da niyyar tanka masa yasa shi kyara tsaiwar shi sannan yace in dae baki kalle ni ba ba inda zakije..

Shiru ya kara biyo baya.. Ganin haka yasa shi fadawa mota yace shikenan ni na wuce..

Da azama tae saurin kallonsa.. Murmushi yayi ya bude mata kofa dayan site en ta shiga suka kama hanyar AKTH...




Kawu tsaye yana Jijjiga kofa,
Kamar wani mahaukaci haka yake bubbuga wa yana kwala wa dije kira..

Kwafa yayi sannan ya juya yana bambamin masifa..

Dawowarsa uku yana dubawa ko sun dawo amma shiru..


Nurr kuwa bayan taje ta duba umma ta koma don kar yaran su dawo bata nan..

Gashi kuma tanason ta kara gyara gidan don dawowarsu momi.

Tun safe aka sallami umma amma safwan ya hanasu tafiya..

Sai bayan ya gama ganin patient sannan suka tafi yaje ya ajiyesu sannan ya wuce jifatu store don yin shopping..

Wata doguwar riga ya gani pink colour mai masifar kyau.. Hakanan ya shiga hango nurr acikin rigar..

Da sauri yakae hannu daedae lokacin wani guy dake dayan side en shima yakae hannu..

A tare suka dago suna duban juna.. Murmushi sukayi wa juna sannan kowa ya cire hannunsa alamun ya barwa san uwansa..

Dayan guy en ne ya zagayo ya mika ma safwan hannu sannan yace ni sunana *barrister Sadeeq auwal kibiya*..

Safwan yayi murmushi ya mika masa hannu sannan yace *Dr safwan naseer mai sana'a*..

A take suka kulla abota sukae exchangin complementry cards en juna..

Gurin biyan kudi ne kowa ya dage shi zae biya wa daya.. A karshe barr.sadeeq shi ya biya saboda yafi safwan baki..

Wata leda sadeeq ya wullu masa yana kokarin tada motarsa..

Seda ya hau titi sosae sannan ya mika hannu ya jawo leda..

Wannan rigar ya gani.. Lalle wannan da gaske so yake muyi abota ya fada yana jinjina kai..

Seda yayi sallar magariba sannan ya shiga ciki.. Dukkansu ya samesu a falo, ganinsa ya sasu tasowa da sauri sukae huggin nasa.

Khaleel ne yace big B wae gobe su momy zasu dawo inji anty nurr..

Daga masa kai yayi alamun Eh haka ne, yaron ya shiga tsalle yana murna..

Sai data bari sun gama masa sannu da zuwa zae wuce sannan tace masa ina wuni..

Lafiya klou ya amsa sannan ya wuce sama..

Tara daidai ya sauko ya iske su suna kallon wani indian film a zee world..

Guri ya samu ya zauna.. sae a sannan ya tuno da kayan da ya siyo..

Mikewa yayi yace musu kuzo muje mota ku tayani debo kaya..

Bayan sun gama shigowa da kayan ita kuma tana zaune tana kallo da alama film din ya tafi hankalinta..

Ki tashi ki dauki kayan nan asasu inda ya dace..

Ta mike a hankali tana waywayen tv.. Sae data gama kintsa komi sannan da dauko ledar rigar nan ta fito da ita..

Zuwa tayi gabansa ta mika masa.. Wannan fa ya ambata.. Tace bansan inda zansa wannan ba shisa na kawo ma..

Kin karba yayi ya dan dubi bangaren su iman.. kallonsu suke hankali kwance basu masa meke faruwa ba..

Ki dauka naki ne yace da ita batare da ya dube ta ba.. Nawa? ta tambaya yae mata banza kamr bae jiba..

Ganin zata sake masa tambaya yasa shi cewa oya kowa ya tashi aje a kwanta.. Kar wani ya makara na tafi airport na barsa..

Yaran najin haka yasa su mikewa da sauri suka nufi daki don basaso ya tafi ya barsu..

Juyawa tayi zata bisu batare da ta dauki ledar ba... yae saurin katseta ta hanyar cewa kawo min ruwan zafi..

Bayan ta kawo ya hana ta tafiya sae daya gama yangarsa yana sha yana satar kallonta..

Ganin shirun yayi yawa yasata cewa, um dama dama inason nai maka godiya kan kokarin da kayi da umma Allah ya saka da alkhairi..

Nan ma shiru taji yayi batare da ya bata amsa ba.. Duk ya wani tsare ta da idonunsa masu bata tsoro.. (Wannan ya fiya shegen kallo ta fada a ranta.. lol)

Kada kai yayi bayan ya sauke cup en daga bakinsa sannan yace ba komai fatanmu Allah ya kara mta lafiya..

Amin ta ambata sannan tace, zan iya zuwa na kwanta ina jin barci..

Lumshe idonsa yayi sannan ya bude, yana jin dadin maganarta shiyasa inta fara baya so ta tsaya..

Ban sallameki ba tukunna ya fada sannan ya maida kallonsa ga tv..

Tun tana duba lokaci tana satar kallonsa har ta fara hamma..

Yana lura da ita amma ya share.. chan ya juyo da niyya mata magana taje ta kwanta..

Mamaki ne ya kamashi ganin har tayi barci..

Tsakaninta da Allah take barcinta ba tare da wata matsala ba..

Hannunta daya ta dafe fuskarta dashi.. Saukowa yayi yazo daedar inda take ya zauna..

Ya jawo hannunta ya damke cikin nasa..

"U av change me alaot nurr, in ina tare dake sae na kasa controllin kaina, I jst lurv everytin about u.. Ur eyes, urs smile, ur innocent face en above all ur charmin voice..

Promise u Zan taimaka miki, zan kawo sauyi a rayuwarki..

Haka yayi ta sumbatu shi kadae kamar tana jinsa.. ( woo su likita bokan turai an fada tarko).

Gyara mata kwanciya yayi sannan ya lulluba mata bargo ya koma kan kujera yana jiran farkawarta.. (niko nace wayaga sabun shiga..

Barci barawo ne yayi awon gaba dashi anan wurin batare da ya shirya ba..



Harphsart khabeer
[9/13, 3:21 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
5⃣1⃣➡5⃣5⃣

By harphsart Rano✍


Mika yayi da niyyar juyi, ganin haske kamar na rana ya sashi bude ido da sauri..

Innalillah ya ambata yana jawo wayarsa. Karfe shida hadda minti goba..

Zumbur ya mike ya maida kallonsa inda ya bar nurr.. Wayam ba kowa..

Yai saurin fadawa toilet ya dauro alwala.. Bayan ya idar da sallah yana zaune islam ta shigo..

anty nurr ce tace nazo na tambaye ka wai da karfe nawa su daddy zasu sauka..

12 noon jirginsu zae sauka ya fada yana ninke dadduma.

Make sure kun shirya b4 d tym if nt zan tafi na barku..

Tom yaya ta fada sannan ta fice..

Duk wani shirye shirye sun gma shi by 10 duk sun matsu a tafi.. kwata kwata sun kasa breakfst saboda murna.


Fitowa yayi sanye da shadda blue colour tasha aiki.. Hular daya sa da dace da yanayi aikin shaddar..

kamshin nan nasa mai dadi shine yake fara yin sallama..

Ya dan zauna kadan a falon, jin motsin ta a kitchen ya sashi mika musu key din motar.

Kuje mota ku jirani yanzu zan fto.. Dama chan sun matso shisa yana fada suka mike da sauri suka fice.

Foldin hannunsa yayi yana kallonta, ita kuma duk sae taji da kasa nutsuwa..

Wuka ce a hannunta tana yanka nama amma hannun sae rawa yake..

Ji take kaman ta tsaga kasa ta shige.. Wata muguwar kunyarsa takeji musamman da ta farka ta gansu a parlour suna brci..

Shigowa yayi kitchen din ya mika hannu ya rike wukar, kallonsa tayi ya kashe mata ido..

Nan ta tuno maganar gaisuwa, ina kwana ta furta a hankali..

Bazan amsa ba, kinyi min laifi, shine kina gani na na makara maimakon ki tashe ni ko..

Kayi hakuri ta fada.. Umm ni bazan hakura bafa..

Akwae ma maganr da nakeso muyi amma sae da yamma..

Ai yau zan koma gida ta bashi amsa. Nan danan yaji hankalinsa ya tashi har ya kasa boyewa..

Gida kuma ya tambaya?? Daga mishi kai tayi..

Shikenan tam, amma ki jirani ni zan mayar dake. Inason naje na kara duba umma..

Nan ma sake daga masa kai tayi.. Sae mun dawo ya fada sannan ya fice..

jin bude gate yasa ta saurin lekawa, motoci ne guda biyu suka shigo sannan suka nemi wuri sukai parkin..

Safwan shi kadae ya dawo a motarsa saboda yaran duk motar su daday suka shiga..

Momy ta fara hangowa tayi fari, alamun hutu da jin dadi ya bayyana a tare da ita..

Hannunta rike da khaleel..

Tana jin shigowarsu falo ta fto da sauri..

Har kasa ta tsugunna tana gaishe su..

Sun ji dadin ganin yaransu cikin koshin lfy.. Sun kuma jinjina wa yarinyar..

Bayan sun natsa suka hau cin abinci, farar shinkafa ce da miyar koda, sae coslow..

Kunun gyada ta dama musu yayi fari kal dashi.. ga zobo me sonyi..

Suka dinga sha suna karawa, kwarai zobon yayi wa daddy dadi..

Bayan sun huta ne tazo ta iske momy a falo, nurr naji ance yau zaki koma ko?? Bazaki zauna ki cigaba da aiki damu ba??

Kinga yanda little ya shaku dake.. Kasa tayi da kanta don har ga Allah tfi son tafiya..

Amma tana jin nauyin hajiya..

Kinga bakomae bazan takura miki ba, in kin gama shiryawa kizo in sallameki..

Shiru shiru safwan tunda ya fta ba alamunsa.. Gashi ta matsu ta tafi..

Ganin yamma zatae mata yasa ta fto kawae.. Bayan sunyi sallama da momy ta hada mata sha tara na arziki.. Sai kuma ta kasa tafiya..

Duk yaran sun rike ta musamman mutuminta.. Kuka yake sosae yana cewa karta tafi..

Da kyar aka lallashe shi bayan an masa wayon zata dawo anjima..

Haka ta fito bakin titi tana share kwalla.. Sabo turken wawa..



Umma tana kwance a tsakar gida tana shan iska, Ta sami sauki sae rashin karfin jiki..

Kabeer ya fita tun sassafe.. Alhajin da yake aiki karkashinsa ne ya kirashi yana nemansa..



Kawu tukur ne ya banko kofa ya shigo, wannan karon bashi kadae bane.. tare suke da baba ja'afaru..

Fuskokinsu a murtuke babu alamun dariya.. Umma na ganinsu sai da gabanta ya fadi..

Jiki na rawa ta mike, dan tasan zuwansu ba alkhairi bane, musamman data ga har da baba jaafaru da kansa..

Girma ya riga ya kamashi shi yasa ba kasafai ya fiya fita ba.

Lalle zuwan nasu ba alkhairi bane.. Sannunku da zuwa ta fada..

Ba wanda ya tanka mata, sae da suka gama kalle kallensu sannan kawu tukur ya kalleta shakeke.. Keee Ina yaran nan suke??

Kafin ya rufe baki kabeer ya shigo hankali tashe...

Yasan sunxo yiwa umma diban albarka ne, Gashi bata gama warwarewa ba.

Suka juyo gaba daya suna kallonsa, ko arzikin gaisuwa basu samu daga wurinsa ba..

Ya shige ya ajiye kayan hannunsa sannan ya kalle su.. Me ya kawo ku gidan mu?? Ya fada yana zare ido..

Duban juna sukae sannan suka hada baki suka ce *kabiru* mu kake gayawa haka??


Umma ce ta daga masa hannu tace banason rashin kunya abba, ba sa anninka bane..

Kwafa kawu yayi sannan ya kalli umma, dama ba wani abune ya kawo mu ba illa ina son sanar dake zamu dauke maryama zata koma gurinmu da zama..

Bazamu zuba miki ido ki bata maata rayuwa ba.. Kuma nan da dan lokaci kadan zamuyi mata aure..

Zanxo gobe na dauke ta kuma Allah sa na tarae bata nan..

Kaikuma mara kunya ka kiyaye ranar haduwarmu don bazatae ma kyau ba.


Suka juya fuuu kamar kububuwa suka fice...



Harphsart khabeer
[9/13, 3:21 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
6⃣1⃣➡6⃣5⃣

By harphsart Rano✍


Da safe ta tashi cikin farin ciki.. Ita kanta bata san me yasa ta wannan farin cikin ba..

Bayan tayi share share ta samu wuri ta zauna tana jin shirin rai dangin goro..

Tana son taji ya zata kasance tsakanin masoyan cikin littifi.. Kwarai suna burgeta yanda suke tafiyar da soyayyarsu..

Ya kabeer ne ya fto da alamun aiki zae fta, gaishe shi tayi sannan ta cigaba da jin radion ta....

Dakin umma ya leka yayi mata sallama sannan ya fice..

Har yamma umma nata zuba idon ganin su kawu amma shiru.. Addu'a take tayi Allah yasa bazasu zo ba..

Sallama yayi a daedae kofar gidan, umma ce tace taje ta gano waye ke sallama..

Tana fita taci karo dashi har ya shigo zauren, sanye yake ta riga da wando jeans.. Gashin kansa ya kwanta luff alamun yasha gyara..

Murmushi ya sakar mata me kayatarwa.. Itama din dae murmushin tayi masa sannan ta juya don sanar da umma.

Tare suka shigo tana gaba yana bayanta.. Duka wa yayi yace umma ina wuni?? Lafiya lou sannu da zuwa ta fada.. Ya manyan naka??

Lafiya kalou umma.. Ya kuma karfin jiki,,? Da sauki ta amsa..

Ruwa tazo ta ajiye mishi sannan ta samu gefe ta zauna..

Shiru ya dan biyo baya, chan kuma yace" umma dama nazo ne akan maganar nurr, munyi magana da ita akan karatun ta..

Ya dan numfasa, sannan ya cigaba.. Shine nakeso naji raayinki don inason nayi mata register a makarantar su khaleel..

Jin ya ambaci zae biya mata taje tayi examz yasa ta dagowa da sauri tana kallonsa.. Kashe mata ido daya yayi..

Muryar umma ce ta dawo dashi, Dr baka gajiya, an ta dawainiya damu a asibity ga kuma wannan.. Allah ya saka maka da alkhairi mungode mungode..

Ba komai umma ai duk daya na daukesu dasu iman.. Sun ce ma na gaisheku da zasu biyoni naki..

Muna amsawa.. Zanje nima in sha Allah nayi wa hajiya barka da dawowa.. So nake na dan kara samun sauki..
Allah ya kaimu ya fada..

Ita kuwa nurr murna ce ta hana ta sakat; Hangowa take kamar burinsu ya gama cika ita da yayanta..

Kallonsa ta dunga yi suna mgana da umma.. matukar burgeta yake..


Karaf ya dago suka hada ido, da sauri ta sauke idonta shi kuma yayi murmushi..

Ya mike zae tafi, bayan sunyi sallama da umma..
Ba rakiya kanwata ya fada yana kallonta..

Kefa sokuwa ce Jeki rakashi mana cewar umma..

A zauren gidan yaja ya tsaya.. ita dinta sae ta tsaya, Sunkuyar da kai tayi tana wasa da hannunta..

Nan ya samu abunda yake so, ya kura mata kallo.. Lalle ya fada tarkon so..

Ada ba abunda ya tsana irin maganar soyayya musammam ma in yaga abokansa na kula yan kananan yara..

Shi a tunaninsa raini zae jawo.. Shi kuma mutum ne mai son girma.

Amma sae gashi tun baa je ko ina ba ya kamu da son yar karamar yarinya.. Ya rasa yanda zaeyi ya sanar mata..

Lalle in abokansa suka ji zasuyi masa dariya.. Amma ya zaeyi Haka Allah yake al' amarinsa.. (Dama hausawa sunce dan hakin daka raina shike tsone maka ido)

Muryarta ce ta dawo dashi daga duniyar daya lula.. Zan shiga ciki tace..

Ya hakuri wlh wani tunani ne ya dauke kaina.. Ba komae tace..

Kinyi kyau ya furta yana mata kallon kasa kasa.. Kasa magana tayi.. Dama yasan bazatai magana ba..

Ji tayi ya ruko hannunta, ya tsuguna akan guiwowinsa.. yace _Nurr_ *kina sona*?? *Zaki aure ni??* *Bae jira tayi magana ba ya cigaba*

*Allah ya dora min tsananin sonki* *tun ranar dana dora ido na akanki na kasa samun nutsuwa*

*Tun daga ranar na zama wani iri, Tun ina karyata zuciya ta akan cewa ina sonki, har nazo na fara gaskata hakan*

*Kece farin cikin rayuwata, I lurv u so much, i lurv u beyond imagination.. Dan Allah ki taimaki rayuwata*


Kafin ya kara magana suka ji an banko kofa da karfiii, gaba dayansu suka juyo a da saurin ganin waye haka......




Harphsart khabeer
[9/13, 3:21 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
5⃣6⃣➡6⃣0⃣

By harphsart Rano✍


Adaidaita sahu ta samu ta hau sae unguwarsu..

Daidai kofar gida ya ajiyeta, ta ciro kudinsa ta bashi, ta wuce ciki..

Da murnar ta ta shiga gidan, Cak ta tsaya ganin umma da ya kabeer cikin wani yanayi..

Karasawa tayi ta zauna tana duban umma.. Umma lafiya na ganku haka??

Ko dai jikin ne?? Girgiza mata kai umma tayi sannan ta shafo kanta, kin dawo?? Sannu da dawowa..

Bayan sun gaisa, tana lura dukkansu akwae damuwa tattare dasu..

Amma basu san su nuna mata.. ganin haka yasa ta share ta shga yin abubuwan da zasu faranta ran umma..

Da daddare suna zaune, Suna tattauna batun zuwan su kawu, amma basu bari tasan gudurinsu a kanta ba..

Kabeer ne yace umma nazo miki da albishir amma ganin mutanen nan yasa duk naso na manta..

Albishir din me kuma abba?? Kodai aikin ya samu ne?? Eh tou kusan hakan ne sae de wannan ya dan banbanta..

Wato kiran da alhaji yayi mun dazu ba komae bane illa ya sanar dani na zama cikin shiri rana ita yau zanje interview abuja..

Gwamnati tayi niyyar tura dalibai kasar waje.. Shine ya bada suna na wajen abokinsa kwamishi nan ilima..

Yanzu haka har na cike form din, sae dae addu'ar Allah ya bada sa'a.

Wani wawan ihu nurr ta saki ta dane shi kamar zata yarda shi..

Umma kuwa, bakinta yaki rufawa sae faman hamdala take wa Allah.. Tana fatan Allah ya bashi saa..

Dariya yake yana kallonsu, wannan farin ciki haka kamar ance yaci interview din..

Yayanah Allah ubangiji ya baka sa'a ta fada tana dan tsallen murna.. Amin kanwata

Abdoul yaron makocinsu ne yayi sallama, ya gaida umma sannan yace wai ana sallama da kabeeru a waje..

Wane ne ya tambaya?? Wani ne a cikin mota nima dae bansan shi ba yaron ya fada sannan ya juya..

Tashi yayi ya fita don ganin waye ke nemansa..

Safwan ne tsaye ya harde hannunsa jikin mota, da sauri kabeer ya karasa ya mika masa hannu..

Bayan sun gaisa ne yake sanar masa yazo ya sake duba jikin umma..

Ai dama baka aika an kirawo ni ba, ai yanzu an zama daya da shigowa kawae kayi ya fada sannan ya juya yace bismillah.

Ta dora kanta akan cinyar umma tana ta dariya, murna take kamar me..

Kabeer ne ya shigo, sannan ya biyo bayansa..

Umma tare fa muke da Dr ya fada yana jawo tabarma..

Sannu da zuwa likita kaine a gidan namu, ya gaishe ta nan take tambayarsa yasu hajiya suka dawo..

Sun dan taba hira a karshe ya mike zae tafi, dama tun shigowarsa nurr ta shige daki bayan ta gaisheshi..

Kabeer ne ya sake shigowa bayan ya raka shi yana kwala mata kira..

Kije dr yana san ganinki ya fada sannan ya wuce dakinsa.

A jikin mota ta tarar dashi ya kurawa hanya ido.. Karasowa tayi ta dan duka kadan ta gaishe shi..

Tsare ta yayi da manyan idanunsa..
Umm kinsan kinyi mun laifi ai shisa kikai saurin gaishe ni..

Laa laifin me nayi ma?? Ta fada tana turo baki.

Kinfi kowa sani ai.. Amma yanzu ba wannan ba..

Na same ki lafiya??
Lafiya klou ta amsa

Ya dan mata tambayoyi tana bashi amsa.. Sannan yace
Ya maganar danace zamuyi??

Umm zamu iya yinta yanzu ai ko?? Ta tambaya..

Ya dan kalli agogon hannunsa sannan yace. Owk lemme make it fast..


So nake naji Yaushe kike son komawa makaranta? Wat i mean shine kinason komawa skul dinku ne kiyi examz en achan.

Ko kinfi son wata skul din kije as external student?.

Kinga nan da two weeks zaa fara registration..

Nafiso nayi a skul dinmu, Kasan da tsada in dae wata skul dince.. Wannan ma da yaya zamu biya balle wata skul din..

Amma kinsan baa fiya cin examz a public skuls ba??

Eh na sani tou amma yaya zanyi,, banida zabi tunda ita ma public skul din sae mutum ya biya inde beci qualifyn ba..

Kuma kudin bae kai rabin na privt skul din ba..

Tom shikenan zan dawo in na samu lokaci.. Zanzo naga umma..

Akwae maganar da zamuyi da ita..

Duk maganar da suke kanta na kasa, bata san mesa ba batason hada ido dashi..

Kiran sunan ta yayi chan cikin makoshi, ta dan kalle shi kadan..

Mesa kike jin kunyata?? Ko har yanzu tsawar dana taba miki ce kika kasa amsawa??

Ni ba komae, kawae dae ina jin nauyinka ne..

Toh dago ki kalle ni.. Da dago da kanta a slow kamar wadda zata kalli dodo..

Da sauri ta sauke, dariya ma abun ya bashi..

Sae ji tayi mutum ya riko mata hannu, tayi kokarin ta kwace ya kuwa rike kam kam..

Zan tafi *nurr* ki shiga gida.. Toh ka sake ni, ta fada..

Kwaikwayon muryarta yayi yace um um ni bazan sake ki ba sae kin kalle ni..

Ganin bata da niyya yasa shi sakin hannunta aikuwa ta ruga da gudu ta shige gida..

Bubbuga kansa yayi yana murmushi..Sannan ya shiga mota yaja..

Ita kuwa tana shiga ta tarar da umma da ya kabeer a zaune..

Ka tsaye daki ta wuce suka bita da kallo kowa yana raya wani abu a ransa..

Cikin dare duk kansu sun kasa barci, juyi kawae suke kowa yana tuna dan uwansa..

Dukkansu ba wanda yasan soyayya cox basu taba..

Lalle koma mene wannan nakeji game da yarinyar nan me girma me safwan ya raya a zuciyarsa.(Ka fada lurv Malam jst admit it)lol..

Haka umma ma ta kwana da tunanin zuwansu kawu.. Tana jin tausayin yarta ta..






Harphsart khabeer
[9/13, 3:22 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
6⃣6⃣➡7⃣0⃣

By harphsart Rano✍



Tsaya wa tayi sororo tana dubansu.. Sake sake ta shiga yi a zuciar ta.. Wannan ai kamar dan gidan hajiya..

Gefen su ta bi da wuce tana kwala wa umma kira..

Dukkansu ba wanda ya tanka mata.. Mikewa yayi yana kallonta.. Baki bani amsa taba..

Ummm.. Ahhmm, duk ta duburburce. Jikinta sae rawa yake. Mtsw ya dan ja tsaki a hankali..
Wannan ta fiya kunya ya fada a ransa..

Juyawa tayi zata shige ciki, aikuwa ya tsare hanya..

Ya kafe ta da ido, ta dan kalle shi kadan, ya wani langabar da kai kamar karamin yaro..

Duk sae taji ma ya bata dariya.. Aikuwa ta shiga yi ba tsayawa..

Bai taba ganinta tana dariya irin haka ba.. Duk sae yaji ta burgesa..

Bayan ta dan tsaya da dariyar ne tace, ni ka matsa na shiga gida..

Aikuwa baki isa ba, sai dai mu kwana anan in dai baki amsa ni ba..

Wayar sa ce ta shiga kara, ya matso da bakinsa daedae kunnenta, daddy yana kirana, ki jira ni zan dawo anjima. And make sure kin tanadar min amsa na.



Ni kuwa dije in tambayeki mana, yaron nan dana tarar a zaure sae naga kamar dan gidan hajiya..

Eh shine a cewar umma, yaron yana da kirki sosae..

Emmm gaskiya jummai ta fada.. Toh ko akwae wata alaka tsakaninsu da yarinyar nan ne??

Gaskiya banajin akwai wata alaka, kawae mutunci.. Amma mesa kika ce haka??..

Hmmm, Ina tunanin yaran nan soyayya suke, dalili shine..

Lokacin da nazo kofar gidan nan, na dan buga kyauren naji shi kamar a rufe..
Tunani na ma ba kowa..
Har na juya sae naji magana sama sama, wannan dalilin yasa na bugo kofar da karfi..

Aikuwa naga yaron tsugunne gaban yarinyar wajenki kamar me neman gafara..

Umma ta danyi jummm sannan tace nidai jummai bana ce komai ba tunda bansan dalilin yin hakan ba.. Amma zan tuntube ta naji..


Ita kuwa nurr yana tafiya sae ta kasa shiga gidan.. Ta dade a tsaye, ganin tsaiwar vazatai mata ba, yasa taja wani dan dutse a kusa da ita ta zauna akai.

Tunani ta shiga yi, tana tuno yanda safwan ya tsaya yana fallasa mata asirin zuciyarshi..

Wani irin feeling taji yana shigarta.. hade da wata zazzafar soyayyarshi..

Ta lumshe ido ta bude, a hankali ta furta.. Ina sonka nima.

Umma ta fto raka jummai kawae taga nurr a zaune, Me kike yi anan

Please Login or Register in order to submit comment