Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan Allah kayi hakuri amma..

Noo ba komi i understand, nan aka sake sabon gaisuwa..

Kafin su gama wayar sae da sukae exchangin address din juna..

Cikin dare haka yayi ta juyi sam babu alamun barci a tare dashi.. Bayason sama kansa yawan tunani kasancewarsa likita..
Amma bazae iya resisting ba.. Abun da ya sami nurr kamar ya sameshi ne.. Yana sonta sosae and kuma yana jin zae iya komai akanta (Toh fa)..




♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Nurr kuwa Allah sarki, Ni kaina sae dana tausaya mata, kafin dare tasha masifar suwaiba harta godewa Allah..

Kuka kuwa tayishi kamar ba gobe.. Fuskar nan tayi jaaa..

Dadinta daya, kawu ya lallabi suwaiba bayan ya bata kudi akanta barta ta dunga kwana
A falo.

Cikin dare tana kwance a kasan carpet wanda in banda doyi ba abinda yake.. Zurr taji wani abu ya bi mata kafa.. Ta dan saurara taji ko zaa kara yi. Aikuwa taji kamar ala lasar mata kafa.. Innalillahi, wani narkeken bera ne kamar girman skul bag din ayadh🙊..

Ihu ta saki ta mike tana zazzare ido, a tunaninta suwaiba zata fito.. Ina ita bata san ma wainar da ake toyawa ba.. Tana chan ta hangame baki😧

Komawa tayi kan kujera ta dukunkune, suwaiba ta mata warning karta kuskura ta hau mata kujera amma ya ta iya,.. Kasa barcin tayi tana ta tunanin ummanta. sae chan wajen asubah barci mai nauyi ya dauketa..


Wani wawan duka suwaiba ta sakar mata a kafarta.. zambur ta mike tana raba idanu😳..

Uban waya baki izinin hawar min kujera iyeee??? Yau sae kin gane kurenki..

Hakuri ta shiga bata amma kamar kara ingizata take, sae data gaji don kanta sannan tayi shiru..

Mikewa tayi tayo alwala, tana idar da sallah taga suwaiba a tsaye akanta.. Bata jira ma tayi addu' a ba ta fara zayyana mata irin aikin da zatayi mata..

Aikuwa tunda ta fara aikin nan sae data wuni tana yi.. tana gama wannan zata jido mata wannan...

Sae gap da magriba ta samu ta kyaleta.. Wanka kuwa dama baa maganarsa...


♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Bayan ya shirya, ya fito.. Kai tsaye dankoli store ya wuce, Kayan abinci ya jidarwa umma da duk wani abu dayasan zata bukata..

A tsakar gida ya tarar da ita tana kokarin shimfida tabarma..

Basuyi wata doguwar magana ba ya mike saboda yana da patients da yawa.. Yara ya samu suka shigo masa da kayan.. Umma kawae gani tayi ana shigo da kaya.. Mamaki ne ya kamata, lallai yaron nan da kokari yake.. Bata kara shiga mamaki ba sae data ga dubu goma a cikin kayan.. Sae data zubar da kwallah..

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Bangaren kabeer kuwa anyi interview sae jiran sakamako.. Ganin yamma tayi yasa alhaji yace ya kara kwana sae ya taho da safe.. haka kuwa akayi.. Safiya nayi ya kamo hanya sae *kano*..

Da farin cikinsa ya shigo, Umma na ganinshi ta shiga murna, Lale da mutan abuja, sannu da dawowa..

Shiru baiji mutuniyar tashi ta fito ba,
umma kanwata fa??
Naji ta shiru ko kin aiketa ne??..

Nan umma ta shiga bashi labarin abunda ya faru.. mikewa yayi ya shiga balaee.. Sae daya gama dan kansa sannan umma ta zaunar dashi..
Ta dan lallabasa sannan ya hakura.. Amma ya kudurce a ransa sae yaje har gida ya dauko kanwarsa.. Gidan baba ja'afaru kawae ya sani shine da suke da zuwa in wani abu ya taso shima tunda nurr taje akae mata wannan wulakncin basu sake komawa ba.. Amma dukda haka sae ya nemo gidan..


♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Yau satin nurr biyu gidan kawu..har ta fara sabawa da wahala.. Ba laifi kawu yana dan raga mata.. Amma suwaiba kuwa inaa..

Suwaiba ce ta kwalo mata kira, zokije nan gidan da yake kallon layin nan ki kaimin markaden nna. Kuma saura ki tsaya wasa wlh sae na lahira ya fiki jin dadi..
Fitowa tayi tana tafiya a hankali, kwata kwata ta zama wata lazy..
Mika markadan tayi ta tsaya daka zauren gidan..

Parking yayi daidai kofar gidan, wani matashine hadadde ya fito, kana ganinsa kaga bafulatani..dogo ne sosae.. Kallon unguwar yayi sannan ya shiga danna wayarsa..
Ji nayi yace nafa karaso ina kofar gida.. Owk pls kayi sauri.. Ya katse wayar..

Yananan tsaye yana karewa unguwar kallo, gaskiya unguwar taci sunanta china😂 saboda yawan mutanen unguwar..

Fitowa tayi dauke da markaden a hannunta, hasbunallahu ya furta, Binta yayi da kallo har tazo ta wuce ta gabansa.. Ganin zatayi masa nisa yasa shi saurin binta yana yanmata yanmata.. Kamar daga sama taji ana mata magana..
Karasowa yayi suka jera, baby sannu ko.. Bata tanka masa ba.. Dan Allah ki tsaya ki saurareni.. Kinga bai ma kamata na tsaida ki a hanya ba.. Ni sunana barrister sadeeq kibiya.. Ko zaki fadi min sunanki?? Ganin bazae kyaleta ba gashi tazo kofar gida yasa tace mishi sunanta maryam sannan ta shige gida..

Dariya yayi ya daki kansa.. Komawa yayi ya tarar abokin nasa har ya fto.. A ah kai kuma dga ina?? Hmm mutumina wlh yau zuwana unguwarku na kama babban kifi.. Naga wata beautiful baby.. I jst fall for her.. Wlh lurv at first sight ..




♡♡Harphsart khabeer
[9/13, 3:23 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿 📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
8⃣4⃣➡8⃣6⃣

By harphsart Rano✍


Tana tsaye tana jiran shigowar kawu.. Tabbas tasan zae iya bugunta.
Addu'a duk wadda tazo bakinta fada take. Jin yana kwala mata kira yasa hantar cikinta ta kada..

Rarrabewa ta fara yi a bango, hasko torchlight din da yayi ne yasa ya ganta..

A ah kaga maryama yan mata, yarinyar arziki.. Wannan yarinya Allah dae ya zunduma ki a aljanna.. Maza koma wurin saurayin nake yar albarka.. (Kuji tsohon banza)


Mamaki ne ya kamaata amma tunowar da tayi cewa babu abinda zae kawo chanjin kawu ta farat daya haka sae kudi.. Lalle kudi sadeeq ya bashi..

Rabewa tayi ta wuce dan har lokacin a tsorace take. Yana tsaye ta fito..

Dariya taso ta bashi yanda take sanda kamar barauniya.

Ajiyar zuciya yayi sannan ya kalle ta.. Shine baki taba fada min a gidan kawunki kike da zama ba ko maryam?? Lalle dia is alaot da ban sani ba akanki.

Bae jira amsarta ba ya cigaba.. Tun Farkon haduwata dake Allah ya saka min sonki a raina..
Naso na bayyana miki tun a lokacin amma sae nayi wani tunani.
Gwanda na fara shiga jikinki mu saba. Daga baya sae na gabatar da kaina.

Banso na fara sanar wa da kawu ba, amma kuma dukda haka nasan bazaki kini ba.

Tunda ya fara magana take kallonsa da mamaki.. Ta san zaa rina. Alamunsa duk sun nuna mata sonta yake yi.
Amma ya zatayi da safwan.. Sonsa mai girma ne a ranta.

Shine mutum na farko daya fara haskaka musu rayuwarsu.

Lalle idan ta manta da alkhairinsa garesu ta zama butulu.

Toh amma shima sadeeq ya zama wani bangare na rayuwarta.. Ya taimaka mata alokacin da take neman taimako.

Kuka ta shiga, ganin tana kuka yasashi rudewa, me ya same ki?? Kardae kice mun maganar da nayi miki ce ta bata miki rai..

Kiyi hakuri, banyi dan na bata miki ba. Girgiza kanta ta shiga yi tana jaa da baya. Tana zuwa karshe kawae ta shige gida.

Tana ji yana kwala mata kira amma ina bazata iya zuyowa ba.
Bazata iya hada ido dashi tace masa bata sonsa ba.

Kai inma tace bata sonsa tayi karya. Amma hakan ba yana nufin tafi sonshi a akn safwan ba.

Dafe kansa yayi yana karanto innalillahi wa inna ilaihi rajiun.. Me maryam take nufi da haka??
Kardae ace bata sonsa, ya salam ya furta. Toh kenan akwae wanda zuciyarta yake so. Ganin tunanin bazae masa ba yasa ya shiga motarsa ya bata wuta.

Allah Allah yake ya gansa a gida. Kasancewar iyayensa duk suna kibiya yasa shi kadae yake zaune anan.

Yana shiga gida ya fada kan kujera. Bae taba tunanin zae sami matsala da maryam ba..

A yanda ya fuskanta akwae wani al'amari me girma game da yarinyar. Akwae abunda bae sani ba akanta. Zae yi bincike amma..


Jawo waya yayi ya kira safwan. Nan yake shaida masa yanda sukayi da maryam.. Kokari yayi ya kwantar masa da hankali. Ya muna masa lalle ya bata lokaci..

Shikenan aboki zanyi yanda kace.

Gobe in Allah ya yarda zanje gidan baba ja'afaru. Dga nan nakeson fara aiki na..

Fatan nasara sukayi wa juna daga nan suka ajiye wayar.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

A gurguje ya shirya, tea kawae yasa a cikinsa ya fice.

Sae daya biya ya dauki *Detective salim* sannan suka wuce..


Daga gefen gidan ya samu wuri yayi parking motarshi.

Sun jima suna karewa gidan kallo.. suna nan zaune cikin mota sae ga baba ja'afaru ya fito

Da sauri salim ya fito ya gyara zaman hularsa. Tsaf ya fto a babban mutum. Kana kallonsa zakayi masa kallon kudi.
Sae ka zata irin hamshakan alhazawan nan ne kasancewarsa me jiki.

Sallama yayi wa baba ja'afaru.. Mika masa hannu yayi sannan yace ni sunana alhaji wada, in bazaka damu ba inaso mu danyi magana..

Fara'a fal fuskar baba ja'afaru yace sannu da zuwa alhaji. Muje daga ciki sae muyi maganar ko.. Ba damuwa suka juya suka shige gidan.

Kwata kwata baba ja'afaru ya kasa zama., sae daya tabbatar ya cika masa gabansa da ruwa da juices sannan ya samu guri ya zauna.

Gaisawa suka kara yi sannan salim ya dora.

Dama naji labarinku ne kai da dan uwanka, ance kunayi aikin kwangila, kuma a gaskiya yanda aka bani labari naji kamar zamu daedae ta. Wata Kwangila ta taso, zamu sa miliyan biyu biyu, kuma indae anyi gwangilar nan a kalla dukkanmu zamu sumu ribar miliyan daya daya..

Wata iri zabura da baba ja'afaru yayi sae ta ya bawa salim tsoro..

Me me me kace?? Miliyan daya?? Baba ja'afaru basa wani aikin kwangila amma dan karya bari damar ta wuce su yasa ya amsa da zasuyi..

Zan kira tukur yau yau din nan muuyi magana..
Ai wannan damar bazata wuce muma alhaji..

Murmushi salim yayi ganin ya fara samo kan baba ja'afaru.

Shikenan alhaji ni zan koma, ga number wayata. Zan dawo dadaddare sae mu hadu da kanin naka gaba daya muyi magana..

Yana shiga mota ya shiga kyalkyala dariya, sadeeq ne ya tsaya yana kallonsa.

Sae bayan ya gama dariyar ya jawo yar recorder sa ya kunna.. Aikuwa sadeeq ya shiga dariyar shima saura kadan ya saki sitiyarin motar..

Salim ne yace lalle mutanen nan sunyi nisa wajen son kudi..

Kaga kenan bazamu sha wata wahala dasu ba, a cewar Sadeeq


Sae daya kaishi har gida sannan ya wuce asibiti wurin safwan.

Nan ya kwashe labarin abunda ya faru kaf ya fada masa.

Shima dariya ya shiiga yi. Suka dan kara tattuna wa akan batun sannan suka gangaro kan maganar nurr.

Safwan ne ya kalli sadeeq sannan yace, abokina akwae abunda ban fada maka ba..

Nan ya shiga bashi labarin soyayyarsu da nurr har zuwa koma warta gidan kawunta..

Shisa nakeso ayi gaggawar gurfanar dasu kawu a gaban koto don nurr dita ta dawo..

Inason ta koma makaranta, inason tayi zurfi a karatunta.

Dafa shi sadeeq yayi sannan ya kalle shi. Karka damu abokina.
Nayi ma alkawarin sai na dawo ma da nurr dinka..

Zaka aure ta, ni sadeeq nama wannan alkawarin.

Nima ka taya ni da addu'a kar maryam taki ni.. Dan Wallahi zan iya shiga mummunan halin akanta..

Sonta ya riga yayi mun mugun kamu...
Nan shima safwan ya shiga bashi baki. Basu rabu ba sae da sukayi convincin junansu..


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Dare nayi suka kara shiryawa sae gidan baba ja'afaru..

A mota ya kara zama yana jiranshi. Kasancewar motar tinted glass ne yasa ba wanda zae san da mutum a ciki.

Yana karasawa kofar gidan ya gansu a tsaye alamun shi kawae suke jira..

Bayan dogon sharhi da tsare tsare, sun gama amincewa zasuyi harkar.

Salim ne ya rage murya ya kalli baba ja'afaru. Nifa da kuka ganni nan ko ya nuna kansa. Zan iya yin komai akan kudi..

Na wuce duk tunanin mutum, in takae ce muku bayani ni din nan da kuka ganni, yayana na kashe na kuma kwace dukiyarsa.

Yaransa kuwa tuni na kada su suka bi duniya, bani da wata matsala daga ni sae yayana da matata.

A lokaci daya suka kalli juna, yana lura dasu, aikuwa ya cigaba da karanto musu abunuwanda zae iya yi akan kudi..

Kawu ne ya katse shi yace, ashe alhaji tamu tazo daya, mu din nan daka ganmu muma kaninmu muka batar, muka kuma ce ya mutu.

A karshe muka gaji dukiyarsa. Shine dalilin da kaganmu mun kawo wannan matsayin ko yaya ya fada yana kallon baba ja'afaru.

Kwarai kuwa anyi haka, sae dae mu matsalar mu daya yaran nasa, naga alamun zasu iya kawo mana matsala musamman babban.


Salim ya bata fuska. Kai amma alhaji kun bani mamaki, me kuka tsaya yi baku kawar dasu ba??..


Lallai kunyi sake, amma yanzu ma tunda har mun riga mun zama daya, zan muku taimako akae.


Godiya suka shiga yi masa sannan sukayi alkawarin gobe gobe zasu bada kudinsu..


Ran kowa fari kal suka watse. Yana zuwa ya rungume sadeeq.. We did it bro.. Saura shigar dasu kotu.
A kotu zasuyi mana bayanin yanda suka hallaka mahaifin yaran.


Sosae sadeeq yaji dadi, ganin zae cika wa abokinsa burinsa.


Yana zuwa gida ya kwashe komai ya fada wa safwan.. Shima murnar ya shiga yi yana hango nurr dinsa ta kusa dawowa. Kuma farin cikin umma ya kusa dawowa.


Shiko sadeeq hankalinsa duk yana wurin maryam, kwana biyu ya bata lokaci bai sake komawa ba. Amma yau kam hakurinsa ya kare. Dole yaje ta sanar dashi abunda yake ranta.


Shikuwa safwan suna rabuwa ya shirya sae gidan umma..








Harphsart khabeer
[9/13, 3:23 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
8⃣1⃣➡8⃣3⃣

By harphsart Rano✍


Washe gari kabeer ya shirya, a daedae kan layin ya tsaya yana jiran hamza.. Sha da daya sukae zasu hadu amma shiru ba hamza ba dalilinsa..

Ganin tsaiwar bazatae masa ba yasa ya yanke shawarar karasa wa gidan..

A daedae kofar gida ya tsaya yana tunanin shiga. Baya so ya shiga neman hamza baba ja'afaru ya ramfo su.

Tun yana sa rai har ya fara fitar da rae.. Haka kawae yaji ransa ya baci.. Juyawa yayi ya bar unguwar..



Nurr zaune ita da sadeeq suna hira.. A yan kwanakin nan sunyi bala'een shakuwa. Kwata kwata bae taba mata zancen soyayya ba.

Ganinsa take kamar yaya kabeer, yana debe mata kewar zaman gidan kawu..

Wayarsa ya jawo da take ringing.
Dr. safwan naga an rubuta akan screen din wayar..

Dagawa yayi. Hello safwan ya ambata.
Da sauri ta kalle shi jin ya ambaci sunan safwan. Safwan dinta ne ya fado mata. Yana chan Allah sarki. Wani hawaye taji ya zubo mata. A wayence ta goge

Kullum ta zauna ita kadae bata da aiki sae tunanin safwan da ummanta.

Ba abinda tafi bakin ciki irin burin da safwan yaci akan makarantar ta..

Gashi yanzu har an fara waec dinma..

Bata ji mae yace ba sae kawae taji yana sallama alamun ya gama wayar.

Kallonta yayi yace yadae kanwata?? Naga mood dinki gaba daya ya sauya?? Wani abun ya faru..

yake tayi da yunkurin boye damuwarta.. Ba komae.

Bae yarda da ita ba amma sae kawae ya share ganin bata son sanar masa.

Mikewa yayi sannan yace mata zae wuce saboda akwae wata yar unguwa da zashi.


♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

A shab'an restaurant su kayi zasu hadu.. Wajen lokaci daya suka karaso.

Bayan sun zauna ya musu orderin drinks.

Basu wata duguwar magana ba safwan ya shiga masa bayanin abunda ya kawo su.

Tsaf ya kwashe duk labarin da umma ta bashi ya sanar ma sadeeq.

Sadeeq yau shiru yana tunani.. Lallai wannan aikin zae danyi wuya. Amma kuma kasancewarsa kwararre akan aikinsa yasa ya tabbbatrwa safwan in sha Allah zae yi bakin kokarinsa.

Zae fara aiki daga gobe in sha Allah. Amma dole umma sae ta basu hadin kai.

Zan shigo gobe sae muje ka kaini naga umman..

Godiya safwan ya shiga yi masa sannan suka fito kowa ya shiga motar sa..

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Umma zaune ta zabga tagumi, tunanin nurr take. Lalle tasan zata sha wahala a gidan kawu.

Kabeer ne a gefenta yana kallon yadda ta damu..
dazu ya sake komawa ko Allah zae sa ya hadu da hamza, wani dan unguwar ya gani ya tambaya sa ko ya ga hamza..

Nan yake sanar masa ai hamza yana gida ba lafiya.. Zawo yake fama dashi wajen kwana uku da ya wuce..😜

Dole yanzu sae ya jira ya sami sauki.

Da yamma yayi wanka ya shirya sae gidan alhaji. Dama ya kirashi tun rana yazo gida yana son ganinsa..

Yana zuwa ya miko masa doguwar envelope..

Alhaji wannan fa ya tambaya..

Mika masa hannu yayi yace masa congratulation kaci interview da akae harma an tura ka *cyprust* Inda zakayi karatun _civil engineering_..

Ya salam, zo kaga murna wajen kabeee. Rasa inda zae sa kansa yayi.. durkusawa yayi har kasa yana ma alhaji godiya..

Dago shi yayi yana murmushi.. karka damu kabeer ni a matsayin da na dauke ka.. Kayi mun abunda bazan manta ba. Ka rike mun dukiyaa da amana. Wannan shine sakamakon hali na gari..

A sukwane ya shigo gidan, umma sae data dan tsorota. Daga ta sama yayi yana zagaywa da ita..

Kaji mun ja'irin yaro. Maza sauke ni ta shiga fada.. Sauketa yayi yana kyalkyala dariya.

Tsananin farin ciki yake ciki. Nan ya bayyaa nawa umma abunda ya sashi farin ciki.. Aikuwa umma sae data dan taka💃🏻.. Lol

Bayan sun natsa sae kuma nurr ta fado musu, da tuni da ita zaai wannan farin ciki.

Amma ba komae dole kafin ya tafi dole yaje ya dawoo da ita..

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Sallama akae wanda yasa kabeer fita don ganin me sallama.

Safwan ya gani tare da wani a tsaye. A ah dr dama kaina bari toh na sanar da umma.

Bayan ya sanar da umma ya dawo yae musu jagora zuwa ciki..

Zama sukayi suka gaida umma.

Nan safwan ya gabatar da sadeeq a wurin umma.

Sannu dan nan kaji, mun gode kwarai.
Ba komai umma.

Sadeeq ne ya numfasa sannan ya kalli umma, haka nan yaga umma tayi masa kama da wadda ya sani. Amma kuma sae ya kasa tuno ko wace.

Share wa yayi ya shiga aikin daya kawo shi. Ya samu gamsassun bayanai agun umma.

Nan take yae figuring yanda zae bullowa su kawu..

Shikenan umma na gode. In sha Allah in wani abu ya taso zan sake dawowa.

Sallama sukayi wa umma sannan suka wuce.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Kabeer ya shiga busy kwata kwata baya ko samun zuwa wajen nurr.

Duk wasu information ya gama hadawa. Aiki kawae zae fara aiwatarwa.

Da daddare yadan samu yayi squeezn tym dinsa ya nufi wurin nurr.

Taayi murna sosae ganinsa. Koba komae tayi missin dinsa kwana biyu.. Kuma har suwaiba ta fara takura mata kwana biyo taji shiru harka bata shigowa😂..

Duk abin nan da ake kawu sam bae sani ba.
Allah bae taba sawa sun hadu ba.

Aikuwa ranar suna zaune saega kawu faram faram da malun malun🙄..

Yana zuwa ya dalle su da torch light..
Kai kai kai kai wa nake gani kamar maryama. Lalle yau zakici kwal ubaki.

Ai tuni cikinta ya duri ruwa, shikuwa sadeeq ba shiri ya mike.
Ganin ya nufosu yasa ta arcewa tayi gida.

Matsowa yayi gaban sadeeq yana kallonsa. Sae kuma yaji yaron yayi masa kwarjini.

Masifar da yayi niyyar yi dole ya fasa. Gaisheshi yayi sannan ya gabatar da kansa a matsayin yaga maryam ne yana sonta..

Kafin kawu yayi magana ya zaro kudi ya mika masa yana murmushi..

Ai tuni kawu ya rikice, hannu na rawa ya warche kudin daga hannun sadeeq. Saura kadan dariya ta kwache masa..

Toh toh toh yaro, kayi kyan kai daka zo kana sonta.. Lalle ka cancanci na baka aurenta..

Maryama yarinyar kani nace amma kuma Allah yayi masa rasuwa.

Kaga nike da alhakin aurar da ita.. Toh karka ji komae inda wadannan suna magana ya nuna kudin hannunsa.. Toh baka da matsala. Bari na shiga ciki na turo maka ita. Ya juya yana yan wake wakensa...




Harphsart khabeer
[9/13, 3:23 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
7⃣9⃣➡8⃣0⃣

By harphsart Rano✍


Dafa shi kamal yayi yace haba abokina calm down.. Kasan yadda ka hadunnan ba yarinyar da zaka nema bata soka ba..

Ka fada min inane gidansu nikuma nayi ma alkawarin sae tasoka..

Hannu yasa ya nuna masa gidan da ta shiga, a rasane kamal ya maida dubansa gareshi.. Ganin sadeeq yana masa kallon tuhuma yasa ya dan wayance..

Lalle mutumina, toh karka damu zan bincika naji ko wacece duk da dae nasan yaran gidan yara ne.. Manyan duk an aurar dasu. Kila bakuwa ce tazo amma kabar komi hannuna..

Haka sukae sallama ya kama hanya yanata tunanin maryama😘.

Har ya dau hanyar gida sae kuma ya fasa, waya ya ciro ya shiga kiran safwan.. Shi dae haka nan yaji safwan yayi masa kuma. Yana son suyi abota..

Jin an daga wayar yasa ya katse tunanin.. Likita bokan turai, ya gida ya aiki.. Daga dayan bangaren safwan yayi dariya yace babban barister ka fiya tsokana wlh gida lfy wlh..
Sun dan taba hira sannan yace masa ya jira sa a gida yau zae shigo bayan magriba..


Haka kuwa akayi bayan sallar magriba sadeeq ya shirya sae nassarawa g.r.a

A daedae gate en gidan ya tsaya ya kirawo safwan.. Nan ya shaida masa ya karaso..

Fitowa yayi, yae masa iso zuwa falon baki.. Nan suka shiga hira kamar sun dade da sanin hira.. Tun safwan na baya baya har shima ya ware..

Yau fa nayi babban kamu aboki.. Dan Allah?? Wallahi kuwa. Nn ya bashi labari.

Tafawa sukayi safwan yace gaskiya ne yallabai.. Ba sanya wato har binta kayi..
Ai abokina wanann harkar ba'a sanya.. Gobe goben nan zan koma. Babe din ta hadu over.

Nurr ce ta fadowa safwan.. Allah sarki ko tana wanne hali.. Ganin yayi shiru yasa sadeeq kiran sunan sa.. Yadai aboki?? Ko dae ka tuno babe dinka ne😂..


Dariya yayi sannan ya dan harare sa.. Sae kace wani kai.. Suka tafa.

Sadeeq bai bar gidan nan ba sae wajen tara na dare, sae daya shiga ya gaida mommy. Ai tuni su khaleel suka manne masa.. Ya dinga jansu da magana suna dane masa jiki..


♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Kabeer ne ya kalli umma, sannan yace
Umma gobe zanje gidan baba ja'afaru. Inaso naji wani abu game da kanwata.. Dole su bani ita na taho da ita don wlh hakuri na ya kare..
Jin umma tayi shiru yasa yace umma baki ce komai ba.

Me zance abba? Ni abun nan ya ishe ni.. Kaje kaji yanda ake ciki.. Yawwa umma dama amincewarki nake nema..

Washegari ya shirya sae gidan baba ja'afaru .. A kofar gida ya tarar da hamza dan gidan baba ja'afaru.. Suka gaisa sannan ya shiga ciki.. Baba ja'afaru na ganinsa ya damke fuska.. Mara kunya me ya kawo ka gidana?? Ko yau ma kazo kamin rashin kunya ne?? Har zae tanka sae ya tuno umma tace karya kuskura ya tanka masa. Batason rashin kunya.

Dukar da kansa yayi ya shiga gaisheshi.. A dakile ya amsa sannan ya dora.. Kayi gaggawar sanar dani abunda ya kawo ka.

Dama zuwa nayi naga nurr.. Ka bani ajiyarta?? Toh bansan inda take ba. Tashi ka bani wuri..

Haka ya dawo gida batare da wani kwakkwaran bayani ba



☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Nurr durkuce tana wanke wanke, suwaiba kuwa tana zaune a kofar falo tana yan wake wakenta.. Duniya tayi mata dadi.. Ita fa yanzu bata wani aiki tun zuwan nurr.. Yaranta ne suka jeho mata ball daedae goshinta..

Kyalkyalewa sukayi da dariya, ganin ta taso zata kamasu yasa suka fice da gudu suna mata ihu..

Yana tsaye kofar gidan yaga yara sun fito, daya daga ciki ya kira yace ya shiga ya kira masa maryam..Kasancewar kawu tukur maryam yake cewa nurr yasa yaron ya gane wayake nufi.. makale kafada yayi yace masa bazan kirata ba sae ka bani kudi.. dariya yayi ya zaro sabuwar dari biyu ya mika masa.
Aikuwa da gudu ya shiga gida yana kwala mata kira.. Suwaiba ce ta ganshi ya shigo rike da kudi yana kiran nurr..

Tasowa tayi da sauri ta rike shi, kallon kudin hannunsa take tana masa dariya.. Yawwa yaron kirki aina ka samo wannan kudin haka?? Wani ne a waje yace na kiramai maryam shine ya bani..


Washe baki suwaiba tayi..
Maza maza wanke hannunki kizo kije ana kiranki a waje, ta juyo ta sauri tana mamaki.

Wani lafiyayyem murmushi ta kara sakar mata.. Taso mana karya gaji da jira kinji yar nan..

Zuwa tayi ta dauko hijab dinta, sae data zo zata fita sannan suwaiba tace karki yarda ki dawo min cikin gidan nan bako kwandala kingane ai..

Yake tayi ta wuce tana mamakin irin halin suwaiba..

Tana ftowa taga wannan na jiyan daya biyota.. gefe ta samu ta tsaya..

bae jira komae ba ya shiga zuba mata surutu.. Tambayoyi kuwa ta shasu.. Tana amsa masa wasu wasu kuma tayi masa banza..

Amma ba laifi yana da abun dariya ga saurin sabo.. yanda ya sake da

Please Login or Register in order to submit comment