Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji hankali ta ya kwanta..

Hajiya wannan itace dije wannan kuma diyarta ce Allah yasa tayi miki ta fada tana washe baki..

Hajia tai murmushi tana kallona nida ummata tace ba komai jummai tayi nagode kwarai..
Ina fata kin sanar mata kamar yadda mukae kuma Allah sa zata iya.. Sae a lokacin Ummata tae magana in sha Allah hajiya zanyi iya kokarina..

Hajiya ta jinjina kanta tace ba komae dije.. In sha Allah gobe aikin zae fara sae maganar kudin aikinki.. zamuyi wata akalla zan biyaki dubu goma yayi miki.. Umma ta zaro ido dubu goma hajiya kai amma nagode.. Wani murmushi na saki A zuciata nace Alhamdulillah..

*Next day*
Kina ina ? Ko kinaso mu makara ne?? Ganinan umma ta fto rike da hijab dinta a hannu ta. Tayi wa umma murmushi tace muje umma.. Suka fito suna tafe suna dan taba hira har suka samu abun hawa kasancewar hajia ta basu kudi jiya dashi suka samu suka hau keke napep. Nassarawa Gra suka ce masa yace bismillah..

Suna zaune a falo gaba dayansu, momy, daddy,, khalil da twins mutum daya ne babu.. khalil sae zuba ma momy shagwaba yake " ni gaskia momy na sae na biki ni bazan zauna ba.. Iman ta kallesa c dis boy tau skul dinfa zakace sae ka bisu.. Islam ta karbe kyalesa sis kinsan dama shi karatun be dameshi ba.. yana jin haka ya kua kara turo baki kinji su ko momy??

Momy tayi daria tace rabu dasu little ina zua zan turo jet ya dauko min kai.. ya saki ihun murna are u crioux mom??( khalil yana son jet a rayuwarsa inde kace zaka sashi a jet zae daena abunda yke) Tace ofcourx kaide make sure u r obedient to ur sis sannan kuma banda rashin ji kaji my son. Yae nodin kansa ..


A hankali suka tura gate en gidan malam idi na zaune ya gane su jia hakan yasa be dakatar dasu ba suka gaisa a mutunce

Karasawa sukai cikin falon gami da yin sallama dukkansu suka juyo suna kallonsu.. momy tace a ah dije kun karaso yanzu nake tunaninku a raina.. ku karaso mana.. Muka karasa muka zube muka fara gaishe su daya bayan daya.. Momy ta kalla daddy tace Daddy wannan itace dije ita na dauko nakeso ta kula dasu little.. Daddy yae murmushi yace ba komi duk yadda kikae yayi.. Har ga Allah sae yaji matar ta kwanta masa..

Momy ta kalli su twins tace dis is ur new nanny.. Suka ce owk mom. Khalil ya mike ya karasa gurinsu umma ya tsaya yana kallon nurr.. Ya juya yace momy dis luks like barbie ta cikin cartoon din disney.. gaba dayansu suka sa dariya..

Momy tace amma fa dije na mnta ban sanar miki ba ko zaki bar nurr ta dunga kwana dasu iman kinga in kika zo kika wuni ita kuma sae ta kwana.. Sae ya zama albashinta daban

Dije ta jinjina kai tace hajiya matsalar shine Nurr tae sauri cewa ba komi hajiya zan kwana dasu..
Momy tae murmushi tace na gode nurr.. Dama naga alamun ma tasu zatazo daya da little kinga ya samu abokiyar hira..
Umma ba yadda ta iya dole taja bakinta tai shiru amma zuciarta bata so wannan hukuncin da nurr ta yanke va.. Nurr din da bata fi a kula da ita ba ita zata kula da wasu.. Amma kuma ya zatai tunda ta amsa zatayi ai shikenan.. Tasan dae dole kabir yaji haushi.


Umma ta dukufa aiki nurr na tayata kafin kace wannan sun kyara ko ina.. Momy ta kwala wa umma kira tace nurr taje ta shirya little cox 12 flight dinsu zae daga..

Duk sun fito suna tsaye a falo daddy yace wai ina *safwan* ne.. kinsan shifa da nauyi iman je kira bro enku tym yana wucewa.. Am so sorry dad gani na fto suka ji daga bayansu.. Saukowa yake yana daura agogo a hannunsa..

Momy ta kira umma tace ga dije nan zata zauna dasu little har mu dawo.. Batare da ya tsaya ba suka gaisa ya fice yana we are about to b late..

*12:30* jirginsu momy ya daga.. su iman suka juyo gida bayan sunga tashin su..
[9/13, 3:21 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
3⃣1⃣➡3⃣5⃣

By harphsart Rano✍


Daidai kofar gidansu yayi parking, ta fita da sauri, ta tura kyauren.. Ta shiga tana kwala wa umma kira, turus tayi ganin dakin nasu an jawo shi

Alamun babu kowa ya ciki, juyowa tayi da sauri tarar dashi a zaune cikin mota..

Ganin yanayin fuskar ta ya sashi saurin fitowa yana tambayar ta lfy? Tuni hawaye ya wanke mata fuska..

Banga umma ba, ba kowa a gidan.. Wani makocinsu Malam idris ne yaxo wucewa,. Tae saurin karasawa gurinshi, malam ina kwana?? Ta ambata..

Lafiya kalou yan nan.. Ya kuma me jiki?? Dazu na fto ina saurin zan tafi kasuwa, naga yayan naki sun fto da ita dijen zasu tafi asibiti da alamun bata jin dadi..

Allah yasa kaffara ne ya wuce bai jira amsarta ba alamun dai yana da wani uzurin..

Juyowa tayi tana kallonsa hankali tashe..

Wanne asibiti kike tunanin zasuje ya jefa mata tambayar..

Nima ban sani ba ta fada tana share hawaye.. Ta rasa mema zatayi?? Me sami ummanta?? Innalillahi.

Kinga ba kuka zaki tsaya yi ba, In sha Allah umma zata sami sauki.

Da kina da number yayan naki ne ma sae mu kirasa muji,..

Ni kuma kinga zanje aiki though ma dae na makara ya fada yana duba agogo..

Yanzu ki hau adaidaita sahu ki koma gida, anjima sae mu sake dawowa mugaa in sun dawo..

Ji tayi bazata iya masa musu ba, amma harga Allah bataso komawa ba..

Taso ta jira taga dawowarsu, amma ba yanda ta iya.. Ya juya ya shiga mota, daidai bakin titi ya tsaya, ta bude motar ta fito, ya zaro 5k ya mika mata..

Zaro ido tayi ta kasa karba, murmushin nan nasa ya sake sakar mata.. Karbi in wuce ina sauri ya ambata..

Tasa hannu ta karba, kafin tayi magana ya figi motar sa..

Adaidaita sahu ta samo ta shiga sae nassarawa GRA.

Shiko safwan yana tuki yana murmushi, shi kansa yana mamakin yanda yake jin farin ciki, Mesa yake jin wani abu game da ita?

Kodai sonta nake ne, Ya fada a zuciyarsa, a ah wannan ba so bane, ina tausayinta ne kawae.. ya bawa zuciyarsa amsa..
yarinyar tana da innocent face..

Haka dai yaeta tunane tunane har ya karaso
Kofar AKTH..(Aminu kano teaching hospital)

Masu gadin ne suka shga daga masa hannu alamun sun saba dashi..
Yayi saurin sauke glass yana dariya, Sannu da zuwa Dr, fari me farar aniya.. suka shiga yi masa kirari.. Ya saki murmushi ya wuce parkin space..

Fitowa yayi yana tafiya cikin takunsa, direct office ya wuce saboda yasan patient suna nan suna jiransa..

Sae daya zauna ya fara
Duba files din mutane.. Daya bayan daya suka dinga shigowa yana dubasu

Khadija kabir aka kira, yai saurin riko umma saboda jirin da take fama dashi, suka shga dakin likita..

Cikin fara'a ya kalli umma, ya ganeta suna gaisawa sumtyms..

Yae saurin mikewa.. Ya bawa kabir hannu, sannan ya kalli umma ya gaishe ta.. Ta ganeshi itama

Bayan ya dubata, yaga ya dace a dan sa mata drip.. ya kalli kabeer yace zamu dan kwantar da ita saboda jikinta yayi weak..

Kabeer ya dan zaro ido, wannan kudin ma dayaya aka sameshi balle kuma ace zaa kwantar da ita..

Safwan ya danyi nazarinsa, yace baka ce komi ba.. Dr wlh ba kudi yanzu a hannuna amma zanje na nemo in sha Allah..

Sae daya ga an bawa umma daki an jona mata drp sannan ya shaida mata zaeje ya samo kudi..


Safwan kua Bai samu ya gama ba sae wajen 5.. Nurr kuwa kwata kwata hankalinta baa jikinta yake

Su iman har sun dawo daga skul sun tafi islamiyya..

Tana zaune taji karar motar sa, da sauri ta fito har tana tuntube, sae de tana zuwa tsakiyar falo ta tsaya chak,..

Tunani take in taje me zata ce masa, kuma ma don ya taimaketa dazu bashi ne yake nufin ya chanja daka miskilin nan data sanshi ba

Kar taje ma ya wulakanta ta, tana tsaye tana tunani ya turo kofa ya shigo,

Dama yayi tunanin zae ganta tana jiransa, kuma da alamun ma shi taji ta fito..

Kallonta yayi kadan sae kuma ya basar ya haura sama..

Wani kululun bakin ciki taji, jiki ya sabule taja kafarta ta koma daki ta rafka tagumi..

Tuni taji wani zazzafan hawaye ya gangaro a fuskarta..

Lalle talauci baeyi ba, yanzu badan ita tana matsayin yar aiki ba, ai da ba abunda zae zaunar da ita..

Sae taje taji halin da ummanta take ciki..

Sae daya watsa ruwa ya dauro alwala sannan ya sauko..Lokacin an fara kiraye kirayen sallah, Direct masallaci ya wuce..

Sae daya idar da sallah yayi yan adduo insa sannan ya shigo..

Su islam ya samu suna zaune duk kansu ba walwala..

Yane twins en momy na ganku haka.. Khalil nae yae saurin zuwa gareshi yae huggin dinsa.. Big bro ga anty nurr chan tana ta kuka bamu san me akai mata ba..

Kazo muje kaji me yasa ta kuka kaji.. ya shiga jan hannunsa..

Binsa kawae ya shiga yi don ya riga yasan dalilin kukanta..

Sallama yayi ya tsaya a kofar dakin yana kare mata kallo..

Ta dago tana dubansa, sannan ta maida kanta tsakanin cinyoyinta ra cigaba da kuka..

Ki shirya yanzu muje muga umma ya ambata sannan ya juya ya fice..

Tae saurin mikewa har taso ta manta da daukar hijab dinta..

Suka fito gaba dayansu bayn sunyi ma mai gadi sallama

Iman, islam da ita suna baya.. khalil kuma nagaba.

Mamaki ne ya kamata ganin an dauke hanya ba hanyar unguwarsu ba..

Bata kara shiga mamaki ba sae da taga anzo kofar AKTH..

Bayan yayi pakin suka fto ya wuce gaba suka bishi a baya, kasancewarsa likiti baesa sun samu matsala da shga ba duk da ba lokacin ziyara bane..


Suka hau kan barender wanda zae sada ka da aminity..

A hankali ya bude kofar room 3 gami da sallama..

Umma ce kwance hannunta daure da drip, sae ya kabeer a gefenta.. A guje da karasa gaban gadon, saura kadan ta bangaje safwan..

Fashewa tayi da kuka ta riko hannun umma.. Sannu ta shiga yi mata ba kakkautawa..

Yaran suka gaishe da umma da ya kabeer sannan shima safwan ya gaisheta yana kara mata ya jiki.

Sannu dan nan mun gode fa wannan hidimar da kayi damu Allah ya saka da alkhairi umma ta fada taba dubanshi..

Murmushi kawae yayi yaja hannun kabeer suka fita..

Sae bayan sun fta ne take tambayr umma abinda yayi take masa wannan godiyar..

Nan take sanar mata, shine ya biya kudin komae har kudin daki.. kuma shine likitan daya dubata..

Baki bude take kallonsu iman.. Dama big B likita ne?? Wlh ni banma sani ba umma..

Nan itama take bata labarin zuwan da sukae gida nemanta..

Sae 10 suka fto daga asibitin wanda da kyar nurr ta yarda zata bisu don ma umma ta nuna mata rashin kyautwa da zatae idan taki binsu..



Harphsart khabeer
[9/13, 3:21 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
3⃣6⃣➡4⃣0⃣

By harphsart Rano✍


Lokacin da suka zo gida already dare yayi.. Duk yaran sunyi barci..

Zagayo wa yayi ya dauki khaleel ya wuce ciki, Iman , islam ta shiga kiran sunansu.. Amma ina basu san tana yi ba saboda nauyin barci.

Tana tsaye tana kokarin ganin ta tashe su don bazata iya daukar su ba..

Ya dawo bayan ya kai khaleel ya dauki islam..
Yace kije ciki zan daukosu..

Ta shiga daki ta ajiye hijab dinta ta shiga toilet dan watsa ruwa..
Bayan a fito ta saka doguwar riga me kauri dalilin ana dan sanyi a garin.. Ta saka hijab dinta ta tada sallah..

Tana sallah taji an murdo kofa an shigo..
Wuri ya samu ya zauna yana karewa dakin kallo..

Daki ne da ake ajiye masu aiki a gidan amma ta gyara shi fes fes sae kamshin turarenta mai araha da yake tashi..

Sae data yi shafa'i da wutri sannan tae sallama..

Ta juyo a nutse tana kallonsa, shi dinma ita yake kallo..

Wani abun kake bukata ta tambaya.. Eh ena bukatar ruwan lipton. Ki hada mun ki kawo mun falo amma karki sa sugar..

Tace masa to sannan ya mike ya fice.. Bayan ta hado masa ne ta sameshi a falo zaune yana duba wasu takardu..

Ya rage hasken falon sae hasken system dinsa daya haske msa fuska.

Ashe shisa kullum yake busy ashe likita ne, for d first time taji ya burgeta..

Yana sanyi da doguwar riga ash, fuskarsa zagaye take da shaje me kyau wanda ya kara fito da zahirin kyawunshi.. Ga wani medicated glass da yasa wanda ya kara fito dashi..

Sallama tayi masa gami da ajiye cup din akan center table.. Ya ajiye takardun ya maida hankalinsa kanta..

Ta juya zata wuce taji yace dawo ki zauna.. inaso muyi magana..

Komawa tayi ta zauna ta takure gefe daya.. Sae daya gama abinda yake sannan ya dauki cup din ya kai bakinsa..


Kadan kadan yake sippin, ya kalleta duk ta wani takure..

Nurr ya kirata sunanta cikin wani salo, sae da taji wani irii wanda yasa ta kasa amsawa illa dagowa da tayi tana dubansa..

Ba wani abu yasa na kiraki ba illa inason sanin wani abu game da rayuwarki..

Nasan yanzu lokaci yaja dare yayi bazae yiwu ki fadan komae ba, amma inason na dan miki wasu tamboyoyi..

Ina fata zaki amsa mun tambayoyi na yanda ya kamata.. Daga mishi kai kawai tayi alamun tana jinsa..

Ko zaki iya gaya min dalilin da yasa kike aiki a nan gidan wanda a tunani na ya kmata ace kina makaranta..

Ta dan kallesa kadan sannan ta ce,

ina zuwa makaranta har ma naje aji shida, dalilin daena zuwana makaranta kuwa shine rashi,

iyaye na basu da karfin biya min kudin jarabawa.. Duba da yanda abinci ma wataran nema yake ya gagare mu..

Ganin zaman da nake haka ba shida wani amfani shisa nake aiki saboda na samu kudi na biya jarabwata..

Ta danyi shiru sannan ta cigaba

A rayuwata inason karatu.. Ina son nayi karatu mai zurfi ko dan na taimaki ummata..

Wannan shine dalilina.. Da fatan ka gamsu da bayani na..


Naji duk abinda kikace kuma na gamsu, amma tambaya ta anan shine ko ina mahaifinku?? .

Jin ya ambaci mahaifinta yasa wata kwalla ta gangaro daga idonta.. Ya rasu ta fada murya na rawa..

Ya fama mata inda yake mata cio, duk wannan rayuwar da suka shiga ta faru ne sakamakon rasuwar mahaifinsu..

Abinda yafi tayar musu da hankali shine rashin ganin gawarsa da basuyi ba.. An dae ce musu kawae sunyi accident ya mutu amma an binne shi a chan..

Kuka ta shiga rerawa mara sauti, matuka ya tausaya mata.. Haka nan kuma yaji kukan da take yana taba masa zuciya..

Mikewa yayi yazo daf da ita ya tsugunna.. Ya zaro wani farin handkerchif me kyau ya mika mata.



kin karba tayi, ta cigaba da kukanta.. Sae kawae taji mutum yasa hannu yana share mata hawaye..

Kallonsa tayi ya shiga girgiza mata kai alamun ya isa haka..

A hanakali ya furta, kiyi hakuri banyi nufin bata miki rai ba..

Zuciyarta ta shiga bugawa da karfi da karfi sakamakon kafe ta da yayi da sexy eyes dinsa..

Shidin ma wani feelin yaji yana shigarsa..
Ji yayi yana neman losin control..

Kokari yayi ya tattaro nutsuwarsa ya mike ya koma kan kujera yace

kije ki kwanta, zamuje asibiti da safe.. Sannan kuma kinsan jibi su momy zasu dawo so akwae shirye shiryen da zaai musu..

Ta daga masa kai ta mike ta wuce tana tafiya a hankali..

Binta yayi da kallo har ta shige sannan shima ya kwashe ta kardunsa ya kashe wuta ya haura sama.

Harphsart khabeer✍
[9/13, 3:21 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
4⃣1⃣➡4⃣5⃣

By harphsart Rano✍


Raba dare yayi yana tunanin nurr.. Haka nan yaji yarinya tana burgeshi.. Yaji lalle yana so ya taimaka ta..
A haka har barci ya daukeshi..


Bangaren nurr kuwa tunda ta koma daki tunanin rayuwarsu ta shiga yi.. Yanda rayuwa ta juya musu.. Daki daki take tuno komae wanda take iya tunawa..


Alhaji Abubakar sumaila shine asalin sunan mahaifinmu.. Yan asalin karamar hukumar sumaila ne dake cikin jihar kano.

Kakanmu malam hamza sumaila yana da mata biyu.. Inna gaje ita ce uwar gida tana da yaya biyar.. Jaafaru shine babba, sae sulaimanu, tukur, lami sai autansu kamalu..

sae baba halima amarya wadda take da da daya Habu..

Baba gaje mace ce sam wacce bata san mutunci ba.. Kwarai ta tsani kishiyarta da tilon danta..

Ba irin makarkashiyar da batai ba don ganin bayansu amma Allah bai bata saa ba..

Su kansu yayanta ta koya musu wannan mummunan akidar..

Sam basa son habu da mahaifiyar sa..

Sam zaman gidan baya wa baba halima dadi da ita da habu.. tsana da kyara suke sha..

Shi kanshi malam hamza baya iyawa da masifar inna gaje.. Haka dae ake rayuwar da dadi ba dadi..


Kasancewar habu shine karaminsu don sa'an kamalu ne.. Sai suka maidashi wani bawa..

Duk wani aikin wahala shi yake musu shi..

Ana haka su jaafaru sukai aure suka tare a cikin gidan kasancewar shi babban gida..

Ba abunda ya chanza na daga tsangwamar da ake musu.. Har matan su jaafaru basa ganin girman baba halima saboda tsoron inna gaje..


Watarana malam hamza kwanta cio me tsanani.. Ya sa aka kira masa gaba daya yayansa da matan.. yae musu nasiha akan zumunci sannan ya rokesu da su kula da baba halima ko bayan ransa..

Suka amsa kamar gaske.. bayan kwana uku da faruwar haka malam hamza yace ga garinku nan..

Mutanen garin sunji mutuwar malam hamza kasancewar shi me son jamaa..

Bayan sati biyu da rasuwar malam inna gaje da yayanta suka fara fito da salo salon wulakanta baba halima..

Kwarai take shan wuya don abinci ma wataran sae an ga dama ake basu..

Ranan dae ta dubi jaafaru yana zaune kan dakalin kofar dakin baba gaje tace "Ya kamata jaafaru a saukewa malam hakki..


Nan danan ya hayayyako mata yana gaya mata bakakin maganganu

Dama ita bata damu da mutuwarsa maalam bq, dan abinda ya bari shi ta sawa ido..

Tou bari kiji in fada miki ba abinda zaa raba a baki nine nan zan cigaba da kula da kadarorin malam..


Baba halima tayi dana sanin dauko wannan maganar wanda akarshe sae data zubar da hawaye..

Cikin dare tana zaune a dakinta ta rafka uban tagumi tana tunanin rayuwa..

Habu yae sallama ya shigo.. guri ya samu yana kallonta yace, baba kiyi hakuri kome ake miki watarana sae labari.. Shikenan Ba komae Allah yayi mana jagora tace

Nan suka shiga hira
Inda yake sanar mata
Dazu yaji mai gari yasa a sanar ,wasu baki sunzo daga gwamnatin jiha suna bukatar yara za asasu a makarantae boko... Ta jinjina kai tana tunani..

Da sanyin safiya jaafaru yazo yana bubbuga wa baba halima daki..

Ta bude da azama a tunaninta ma wani ne ba lafiya.. Ganin jaafaru tsaye fuskar nan ba walwala yasa tasha jinin jikinta.

Ina habu yake ne tun dazo nazo ban sameshi a dakinsu ba..

Ki fito dashi dan yau zasu tafi birni na bada sunanshi..

Kuma ko kiinaso ko bakyaso dole yaje don na gama maganata..

Bae jira amsa ba ya juya fuuu ya wuce..

Kuka ba irin wanda baba halima batae ba ranar da aka tafi da habu...
habaici kuwa ta shashi a tsakar gida har sae data gwammace bata auri malam ba.. A kwana a tashi ba wuya



Assalamu alaikum, ina mutanen gidan ne?? Baba gaje ce ta fito tana gyara dan kwali..

Wanna dan iskanne ke ta mana sallama haka ne.. Turus ta tsaya ganin habu cikin kyakkawar shiga, janye yake da troly yar madaidaiciya..

Baki bude ta ke kallonsa mamaki karara a furkarta..

Shi kuwa murmushi yayi ya tsuguna har kasa yace baba ina wuni, mun sameku lfy..

Ganin bata da niyyar amsawa yasa shi mikewa yaja jakar shi ya wuce dakin babarsa..

Akan dadduma ya tarar da ita tana lazimi..
Tana ganinsa ta mike da sauri tana kallonsa..

Ta rasa wanne irin farin ciki zatae duk da tana samun labarinsa a gurin mai gari..

Ya samu wuri ya zauna yana murmushi, itama din murmushin take.. Bayan sun gaisa ne ta mike don ta kawo masa ruwa..

Baba gaje ta tarar tana zarya hankali tashe..

Baba halima ta kalleta ta watsar sannan ta wuce ciki..

Bayan ya huta ya fito don gaisawa da mutanen gida..kallonsa suke da abun mamaki.. Ganin sauyawar dayayi wanda duk su atunanin su ma yanzu ko bashi da rai..

Da laasar mazan gidan suka dawo daga gona.. Turus sukae suma ganin wanda basu taba tunanin gani ba..

Ya tashi da sauri ya karbi kayan hannu yaya jaafaru.. Baki galala duk suke binsa wanda ya lura da hakan..

Nan suka shiga kuskus tsakaninsu..

Da daddare suka hadu duka suka sa aka kira musu habu.. Ya fto a nutse kana ganinsa kaga dan boko ga kamshin turarensa sae tashe yake..

Wani zazzafan yawu baba jaafaru ya hadiya sannan ya kai dubansa ga yan uwansa..

Habu muna so kai mana bayanin yanda ka sauya gaba daya kuma ka dau wannan lokacin mai tsawo baka zo ka ganmu ba..

Nan yake labarta musu ai daya tafi kano aka kaishe makarantar kwana dake dawakin tofa,

nan yayi karatunsa daga karshe gwamnati ta kara daukar nauyinsu zuwa kasar cyprust inda ya karanci bussiness and finance..

Yanzu haka yana aiki da FIRS dake abuja..

Kuma duk abinda yake faruwa ana sanar wa mai gari.. Yanzu haka ma yazo musu da maganr aurensa ne..

Sanna zae tafi da baba halima..

Zo kaga tashin hankali wajen su kuma duk yana lura dasu sarai..

Ganin basu da alamun magana yasa ya zaro kudi yan dari biyar biyar na 20k a jiye musu yace gashi nan yaya ba yawa...

Ba irin haukan da baba gaje batayi musu ba, hr Allah ya isa sae data yi musu wai sun cuceta da kamalu suka kai ai ba haka ba..

Sae bayan ta nutse ne suke sanar mata da shawarar da suka yanke.. Murna ta shiga yi tana samusu albarka.. ( kome suka shirya ??))

Matuka habu yaga chanji a tattare da yanuwansa.. sae wani nan nan suke dashi..

Murna kuwa a gurinsa baa magana Allah ya shiryi yan uwansa sun gane gaskia


Haka dae akae shagalin bikin habu da budurwarsa dije(umma) wadda suka hadu a gombe yaje wani seminar..

Kasancewar itama iyayenta sun mutu sae ita da yayarta suka rage..

Bayan shekara daya da auren Cikin ikon Allah umma ta haifi yaya kabiru wanda yaci sunan babanta..

Tsakaninmu da yaya kabiru kuwa shekara goma ne cip cip..

Nan aka samini suna *MARYAM*, sunan da abba na yake so.. Amma ana kirana da nurr..

iyakar jin dadi da gata muna samu wajen mahaifinmu kasancewar ya zama hamshakin mai kudi...

Ya samu a makaranta mai kyau inda yaya kabiru yake jss 1 ni kuma ena primary 2..

Kwatsam muka sami sauyin rayuwa, wani babban alamari ya faru wanda shine sanadiyyar duk wani hali da muke ciki yanzu..

Jin da tayi kamar ana kiraye kirayen sallah asubah yasata mikewa da sauri..


Harphsart khabeer
[9/13, 3:21 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
4⃣6⃣➡5⃣0⃣

By harphsart Rano✍


Alwala ta dauro tazo ta tada sallah.. Ta dade tana addua asujadda Allah ya bawa ummanta lfy..

Sauri sauri take ta kammala komae kafin ya fto don tana son zuwa asibity..

Hatta kayanta ta gama hadawa don tana sa ran su momy na dawowa zata koma gida

Bayan ta gama shirya khaleel su kuwa su iman dama sun iya shirya kansu...

Sukae breakfast sannan suka fice zuwa skul..

Wanka ta fada bayan ta fto ta dan shafa mai ta kawo wata jar atamfar ta ta saka, duk da atamfar ta dan kode amma bae hana yi mata kyau ba..

Hijab ta zura ta fto zuwa falo don taga fitowarsa..

Tasan sarai zae iya tafiya batare da ta sani ba..

Turarensa ne ya fara yi mata maraba.. Kanta na kasa tana wasa da hannunta yazo ya wuce ta gaban ta..

Sae daya gama yangarsa yana lura da ita duk ta matsu ya gama..

Ya mike ganin bata da niyyar masa magana, ko gaishe shi ba tae ba..

Ya fice abunsa bai ce mata kala ba.. da sauri tabi bayansa..

Tsaye ta ganshi jikin mota yana magana da mai gadi..

Ganin ya zuya zae shiga ne yasa tae

Please Login or Register in order to submit comment