Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsa ba,
sannan tabi matan da kallon raini tace sann--- muryarta ta sarke saboda ganin Gaje da tayi,
cikin mamaki tace gaje,
gaje ta dago tace na'am,
oyizah tace long time ina kika shiga haka tsawon shekaru uku babu ko zuwa duba mu,
Gaje tace walhy kuwa aure nayi shiyasa, oyizah ta tabe baki tace na miki murna,
bari a kawo muku abinci,
Baffa ya kalli alhj basheer yace labarin zeenatu har yanzu shuru ko?
Alhj basheer yace wallhy kuwa baffa, amma mun baza addu'a ana nan anayi kuma muna sa ran in shaa Allahu zata bayyana,
oyizah tayi murmushi a zuciyarta sannan a fili tace alhj in ta mutu fa,
shekara uku mutum ya bace har yanzu babu labari ay ni ina ganin ta mutu,
Baffa ya galla mata harara yace bashiru ina ganin Allah ya amsa addu'armu dan kuwa na samu labarin inda zeenatu take,
saboda firgici oyizah saida ta kusa karya kujerar da take kai, zaro ido tayi tace kana da labarinta,
Baffa ya kalli cikin idonta yace kwarai kuwa inada labarinta mai karfi ko kuma ince ina tare da ita ma,
alhj basheer ya dafa kafar Baffa cikin rawar murya yace tana ina Baffa,
kafin baffa yayi magana an murďa kofar palourn an shigo, da sauri alhj basheer da oyizah suka daga idonsu ya sauka kan zeenatu da tayi wata irin muguwar rama,
da sauri ya mike yana fadin z-e-e-natu, Abida da yadikko dake rike da ita suka nemi guri suka zauna, gabanta ya karaso ya kamo hannunta saboda ya gasgata ita din ce,
murmushi Abida tayi tace ita ce alhj zeenatun ka ce matarka kuma uwar danka,
Allah yayi zaku kuma ganawa,
alhj basheer ya tsuguna a gabanta idonshi ya ciko da kwalla yace ina kika shiga zeenatu,
idonta ya ciko da kwalla ta kalli gurin da oyizah ta sankare a tsaye tace na shiga cikin ukubar da bawa baya iya fitar da danuwansa bawa saidai Allah ya fitar dashi,
an so kasheni amma da yake shan ruwana bai kare ba sai gashi Allah ya dawo dani bayan mutuwar danayi ta dan lokaci,

mikewa tayi a hankali kamar zata fadi saboda rama, ta karasa kusa da oyizah tace ribar me kikaci a wannan izayar da kikayi mana,
me kika samu mai amfani bayan tafiyarmu,
meyasa zuciyarki ta zabi ta dinga kisan kai akan abun duniya da zaki tafi ki barshi a duniyar,
meye ribarki dan na mutu ni da ďana ke kuma kina rayuwa keda yayanki,
ki sani safiya Allah na kare wanda yaso a lokacin da yaso, kin---- oyizah tayi saurin katseta cikin tsawa tace duk wadannan maganganun na menene,
ina ruwana dake da zan kasheki, me kikayi min,
ta fara kukan munafurci ta matso kusa da alhj basheer tace sharri zatayi min dan kawai ta shiga duniya ta kwaso cutar kanjamau shine zata ce ni nayi niyyar kasheta,
alhj inda zan kasheta da Affan shekararshi nawa ina kula dashi ban kasheshi ba,
ba'ayi min godiyar kula dashi ba sai dai a bini da sakayyar sharri,
kan alhj basheer ya ďaure sosai yace wai meke faruwa ne, zeenatu zata fara magana
"Affan ya fito yace ni zan faďa maka duk abinda ke faruwa daddy"
cikin mamaki suka mai da kallonsu kan Affan,
karasowa yayi ya rungume zeenatu yana faďin baki mutu ba umma,
ta dago fuskarshi tana shafawa tace kaima baka mutu ba, ashe kana nan da ranka Affan,
kuka sosai suka dinga yi na tsawon mintuna,
alhj basheer ya janyo Affan cikin mamaki yana shafa kanshi yace kaji sauki ne Affan,
Affan ya gyaďa kanshi yace na dawo cikin hayyacina daddy,
Allah ya kwatoni daga hannun wannan azzalumar da take kiran kanta matarka,
farida da shigowarta parlon kenan ta karaso da sauri ta buge hannun Affan tace karka kara zagar min mahaifiya,
Affan yayi mata wani irin kallo yace kice kar in kara zagar miki matsafiyya ba mahaifiyya ba,
oyizah ta sa kuka tace alhj kanajin sharrin da danka yake min, ko da yake bazan ga laifinshi ba dan nasan mahaukaci ne shi baya cikin hayyacinshi,

alhj basheer dai kanshi ya ďaure yace dan Allah karku rikirkitani, ku fada min abinda ke faruwa,
Baffa ya kalli Affan yace zauna Affan bari mu fara jin komai daga bakin mahaifiyarka
sai muji naka..

Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah

A hankali zeenatu ta fara jawabinta kamar haka...

Ranar asabar bayan sallar isha'i ina zaune a daki sai naji kamar ana ihu acan sama gurin shan iska,
da sauri na mike na isa gurin dan duk tunanina Affan ne a gurin shi da jabeer dan mun rabu dashi zaije gurin jabeer,
ina isa gurin naga wasu kartin maza zaune kan wani jan kyalle da wani jan kaya a jikinsu,
juyawa nayi da sauri zan koma daki saboda sun matukar bani tsoro,
ina juyowa naga safiya cikin jajayen kayan itama tana dariya,
da sauri naja baya ina ambaton sunanta sai naji saukar sanda a tsakiyar kaina,
dishi2 na fara gani ina salati ina neman dauki gurin Allah,
cikin karaji naji muryar safiya tana fadin kunji ko addu'a takeyi na faďa muku wannan sai kunyi da gaske saboda nasha yin aiki akanta yana lalacewa,
jin haka yasani sake bude wani shafin na addu'a, sai naji sun ďaga ni, daya ya bankareni yana faďin zo ka shake mata wuya muga ta inda addu'ar zata fito,
da sauri ya matso ya matsemin wuya inata kakari na hango wata katuwar wuka a hannun safiya tana faďin wannan gara kawai mu kasheta sai mu kaita asha jininta, tana kokarin daura wukar a wuyana muka ji ihun Affan,
da sauri ta yar da wukar su kuma suka sakeni na faďa kan wani farin kyalle,
daga nan ban kara sanin inda kaina yake ba saida na ganni gaban wata mata wacce halittarta kaďai ta isa ta tsoratar da mai rai,
ajiyeni tayi a wani daki tana faďin yau dake zamuyi dinner,
tana fita naga wasu yara su biyu sun shigo dasauri suka tanbayeni wa ya kawo ni nan,
cikin rawar murya na ce musu kishiyata ce,
daya daga cikinsu tace nasan oyee ce dan bata da mutunci tunda ta kawo uwarta kowa ma zata kawo,
dayar tace har wani karamin yaro ma ta kawo lokacin da take neman cikin ďa namiji,
cikin sauri suka ce in tashi zasu fitar dani, da sauri na mike ina tambayarsu su bazasu tafi ba,
amsar da suka bani tasani zubar musu da hawaye sukace sunfi shekara ashirin a haka, yanzu gangar jikinsu ya riga ya zama kasa,
wani hanya suka nuna min nayi saurin bi na dawo jikina,
dakyar na iya mikewa ina kallon sanda suka dauki Affan zasu jefoshi daga sama su karasa shi dan kar ya tona musu asiri,
da sauri na fito dan kar su ganni na sakko kasa ina bin bango ina neman wanda zaizo ya taimaki ďana dan karsu kasheshi,
a kofar kitchen na hadu da Gaje ta dawo daukar sakon da safiya ta aiketa dashi,
da sauri ta rikeni tana tambayata,
dakyar na iya takaita mata, na kuma ce dan Allah ta dauko min Aff--- ban karasa faďi ba naji karar saukar mutum kasa da karfi, tun daga lokacin ban kara sanin inda kaina yake ba sai kwana biyar da suka wuce,,
ta karasa tana kuka mai tsuma zuciya,,

Ajiyar zuciya Gaje tayi tace kwarai abun da ya faru kenan dan tana faďuwa nayi saurin janta store saboda jin muryar madam da nayi ta sakko nemanta,
munfi minti talatin a store sannan na daukota na fito da ita da sauri dan kar wani ya ganni,
ina fitowa naga wani me keke napep a kofar gidan alhj bara'u, dasauri na karasa nasata nace ya kaini dorayi gidan kawu na,
bai tsaya musun kudi ba saboda ganin halin da muke ciki,
tafiya sosai mukayi har muka iso nace ya jirani,
ďakin matar kawuna na kaita nace dan Allah su kular min da ita kafin gobe da safe,
ba musu tace ba komai saboda sunsan irin alherin da hajiya ke musu,
sai kusan goma na koma gidan,
ranar a tsorace na kwana,, washe gari ina tashi na tattara kaya na nayi ma madam karya nace mata mahaifina bashi da lafiya acan nijar,
kudi ta bani tace Allah ya bashi lafiya tare da jaddada min in dawo da zarar ya samu sauki,
amsata kawai nayi na fita daga gidan na wuce ďorayi,
a ranar muka wuce nijar ni da hajiya dan nasan acan ne zata fi samun kulawa saboda kawuna malamine,
babu irin addu'ar da ba'ayi ba amma sam babu sauki dan ko motsi batayi,
A can na barta na dawo jigawa ina wani aikin, har Allah ya hadani da wani mukayi aure,
yau kwanana biyar da zuwa gida na tarar ta farfado,
shekaran jiya ne ta matsa ita akaita can gidansu a cameroon,
bamu so mu kaita ba har saita kara samun sauki amma malam yace lallai mu kaita saboda ta samu nutsuwa,
a can cameroon da muka je ta labarta ma mahaifinta komai shine yace a shirya a taho nan kano domin a fayyace komai dan kar aja lokaci a kuma kullo wani mugun abun da zai fi na da..

Cikin tashin hankali oyizah tayi kukan kurah ta shako wuyan zeenatu tana fadin ni zakuyi ma sharri wallahy yau sai na kasheki,
da sauri Affan ya taso ya banbare mahaifiyarshi a jikin oyizah ya shiga dukanta yana haki yana fadin duk abubuwan da tayi mishi da kuma wanda tayi ma Afeeyah da kuma kisan da tayi ma jabeer,
shaketa yayi idonshi yayi jawur cikin ďaga murya yace me jabeer yayi miki kika kasheshi,
kakarin wuya oyizah keyi idonta sun firfito waje tana girgiza kanta,
babu wanda yayi yunkurin hana Affan har farida da kuka yaci karfinta saboda jin mugun alkaba'in da mahaifiyarta tayi,
zeenatu ce ta taso da sauri ta fara banbareshi a jikinta saboda kar yayi kisan kai,
dakyar ya rabu da ita yana haki idonshi cike da kwalla,
mikewa oyizah tayi ta ruga dakinta da gudu tana haki kamar zata mutu,
tana shiga ta bankade katifarta da katakon, tana dagawa taga babu komai cikin ramin sai kasa,
da sauri tasa hannu tana tone kasar ciki kamar mahaukaciya tana fadin ina kuke, waye ya kwashe ku,
wayyo Allah na shiga uku na lalace,
buga kofar ďakin taji anayi da karfi kamar za'a ballata,
a hankali ta leka ta windon don ganin ko waye,
yansanda ta gani tsaye su kusan shida da mace daya,
dariya ta saki wacce da gani kasan ta takaici ce ta jawo jakar kayan tsafinta nan da nan ta bace daga ďakin....

Mrs tijjani shattima...
[15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣2⃣ By Aysha Ya'u kurah

Yan sandan sunfi minti goma a tsaye suna bugawa ba'a buďe ba,
cikin sanyin jiki alhj basheer ya taso ya dauko wani key yasa ya bude,
wayam suka gani ba oyizah ba sawunta sai katon ramin karkashin gadonta ne yayi musu sallama a idanuwansu,
alhj basheer idonshi ya kara ja yace jikina ya bani zata gudu dan shaidancinta bazai kare anan gurin ba,
da kun bar Affan ya kasheta mun huta dan yanzu wallahi bazata kyalemu ba,
malam maina ya taso yace ka kwantar da hankalinka in shaa Allahu babu abinda zai faru,
zamu toshe duk wata kafar da zata samu shigowa rayuwarku da addu'a,
alhj basheer ya sharce gumin goshinshi yace to Allah yasa, Ameen duk mutanen gurin suka ce,
Alhj basheer ya kalli Affan ya dawo kusa dashi yace Affan dama duk abinda kakeyi kana sane,
Affan ya girgiza kanshi yace ranar da mummy tayi niyyar kashe Afeeyah ranar na dawo hayyacina da taimakon Allah da taimakon Afeeyah,
nan ya kwashe duk labarin da kaka liman ya bashi na irin kokarin da Afeeyah tayi akansu ya fada musu sannan ya kuma faďa musu dalilin da yasa mummy ta kashe jabeer,,
ya share hawayen fuskarshi yace daddy dalilin da yasa kaga naki tafiya in bar Afeeyah a asibiti kenan saboda nasan muna barin gurin zata karasa ta,
doctr musah ma yasan na samu sauki saboda washe gari da mummy ta matsa sai mun tafi naje na sameshi na fada mishi komai nace ya taimakeni ya dauketa yace su zasu dinga jinyarta,
da kyar ya yarda dan a tunaninshi ban samu sauki ba shirme nake mishi,
muna tafiya yace min yaje dakin dan ya gasgata maganata sai ya tarar ta cire pillow tana kokarin kashe ta,
hankalinshi ya tashi a lokacin sai ya tabbatar naji sauki shine ya shirya plan din za'a kaita dakin hutu,
alhj basheer ya jinjina kanshi hawaye na fita a idonshi yana faďin ku yafe min, duk ni na jawo muku da na shigo da safiyya cikin iyalina,
gashi bata tsaya kai na ba har saida ta taba ya'yan makota na, dan Allah kuyi min afuwa ku dau duk wani hukuncin da ya dace a kaina,
zeenatu tace ka daina kuka alhj ba laifinka bane RABO ne ya shigo da ita rayuwarka, Rabon salma da Farida zai iya AJALIN duk wanda ya hana wannan auren a lokacin,
cikin kuka alhj basheer yace tabbas ya ko yi ajalin mahaifiyarta dan taki amincewa da zancen,
ashe safiyar ce ma ta kasheta da hannunta,
Affan yace har Anty salma itace silar mutuwarta dan jiya da mukayi waya da kaka duk ya faďa min hatsaririkan da Afeeyah ta tsallake a gidan nan,
mamakin alamarin kowa ya dinga yi haďe da ganin jarumta da jajurcewar Afeeyah,
Abida dai banda kuka babu abinda takeyi dan mutuwar jabeer ta dawo mata sabuwa fill a yau,
tabbas da an barta ita da hannunta zata kasheta ta huce takaicin rabata da nagartaccen ďanta mai cike da Haiba da tayi..,

Cikin kuka fareeda ta matso kusa da Affan tace dan Allah Affan ka yafe min abin da nayi maka wallahy sharrin shaidan ne da kuma ganin mummy nayi,
Affan ya janye kafarshi ya galla mata harara,
cikin tsawa alhj basheer yace tashi ki bamu guri yau dinnan zaki bi uwarki dan ban sani ba ko ke din ma ta tsafin ce,
fareeda ta rushe da kuka tana bashi hakuri, a hankali zeenatu tace alhj laifin wani baya shafar wani,
duk wanda yaga farida yaga jininka dan haka hannunka bazai rube ba ka yanke ka yar ba,
alhj basheer yayi saurin cewa saidai kuwa in bai isheni da wari ba,
yanzu ke kina so in zauna da jinsin matsafa a gida,
Baffa yace bashiru hakuri zakayi ya' dai taka ce dan haka dole ka riketa ku koya mata tarbiyar da addini ya koyar kuma ku aurar da ita,
nan suka cigaba tattauna maganar cikin tsananin al'ajabi....

Cikin tashin hankali oyizah ta bayyana a gurin tsafinsu,
kuka sosai takeyi a gaban chummy tana faďa mata duk yadda akayi har dawowar zeenatu da samun saukin Affan,
chummy ta kalli oyizah cikin mamaki tace ya akayi haka ta faru,
oyizah tace nima ban sani ba, komai na kayan aikina an kwasheshi a karkashin gado babu komai a gurin sai kasa,
sai kuma kwalbar nan da yan iskan yarannan suka fasa nasan shiyasa zeenatu ta farfaďo,
chummy tace na sakeyin wacce tafi tada karfi kin ganta can,
oyizah cikin mamaki tace to ya akayi haka,
chummy tace ni nafi mamakin na dakinki da wanda kika birne a bakin damo,
oyizah tayi saurin ďago kanta tace nasan wanda zaiyi min wannan aikin,
wannan yar iskar yarinyar ce zatayi min, wallahi I will not spare her,
yanzun nan zanje asibitin da take in kasheta,
chummy tayi murmushi tace daďina dake garaje,
bakya tunani kafin kiyi abu,
waye ya faďa miki suma yanzu zasu zauna,
, ai sun riga sun san sirrinmu so sai munyi da gaske ta karkashin kasa musa ki koma gidanki sai ki aiwatar da ayyukanki cikin kwanciyar hankali,
oyizah ta gyada kanta tace wallhi wannan karan mai zafin zanyi duk saina kashesu in mallake alhj da dukiyarshi muyi zaman mu tare har karshen rayuwarmu,,,
chummy tace yauwa ashe kin gane,
yau da daddare zamu fara aikin, kinsan akwai ďan tsoho da kika kawo to dashi za'ayi miki aikin, yanzu tashi muje gurin Dodo BELAH mu dawo kafin lokacin meeting yayi,
oyizah ta mike zuciyarta wasai dan a tunaninta komai nata zai koma normal tunda CHUMMY tayi assuring dinta,,,
oyizah sarkin sa'a........

Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣3⃣ By Aysha Ya'u Kurah

Kwance take kan kirjinshi ta cukwikwiyeshi tana kuka mai ban tausayi tana faďin
"meyasa ka tafi ka barni na tsawon lokaci, meyasa baka daukeni mun tafi tare ba ka barni cikin wannan wahalalliyar duniyar mai cike da azzalumai marasa tsoron Allah,
ta tsunguna a kasa kukanta ya tsananta tace dan Allah yaya jabeer karka sake tafiya ka barni,
ba karamin wahala nake sha ba saboda rashinka,
I grew up in your arms plss led me die in it, plsssss,
ďagota yayi suna kallon cikin idon juna taga wani haske mai matukar kyau a cikin kwayar idonshi,
a hankali taji yana faďin tafiyata bazata taba zama wahala agareki ba,
naso kasancewa tare dake amma Allahn da ya hallicemu bai halicceki dan ni ba shiyasa ya ďaukeni domin ki kusanta da wanda yake makusanci na hakika a gareki,
dama ni ba mazauni bane zuwa nayi in nuna kamannina in koma ga ubangijin talikai,
tabbas nasan lokacin da nake da rai baki da wata matsalar rayuwa, yanzu kuwa nasan ko baki gama sanin meye rayuwa ba kinsan kadan daga ciki,
mu'imuni ako da yaushe Allah na jarabtarshi ta kowane bangare, duk wanda ya kansance cikin farin ciki a kullum to tabbas ya binciki kanshi domin duniya kurkukun mu'imuni ce sannan aljannar kafiri,
kafiri marar tsoron Allah, ko wanda ke sabawa Allah shi kaďai ne ke samun farin ciki marar yankewa a duniya,
akwai lokacin da zamu shiga farin ciki amma cikin lokaci kalilan sai bakin ciki ya maye gurbin wannan farin cikin,
to ki sani duk musulmin dake yawan shiga cikin jarabawar Allah lallai ba karamar soyayya bace tsakanin wannan bawan da Allahn shi, domin shiga kunci ga musulmi kankarar zunubi ne,
wasu kuma zaki ga basu da wata damuwa komin zunuban da sukeyi ba shi zai hana Allah ya barsu cikin farin ciki ba, sannan kome suka nema suna samunshi kamar su suka tsara rayuwarsu, to wadannan Allah ya barsu da kansu ne har sai sun tuba,
kullum mu'imunin kwarai yana cikin jarabawar ubangiji masu tsananin rabo su ke cinye jarabawar dari bisa ďari,
ya share mata hawayen idonta yace zanso Afeeyata ta zama daga cikin masu cinye jarabawar ubangiji a koda yaushe,
zanso ki daina yawan zubar min da hawaye domin hawayen basu kara komai sai wahalarwa ga kyakyawan idanuwanki,
zanso ki manta batun soyayyata a matsayin wanda zai aureki ki sanya soyayyar yaya a zuciyarki domin samun tsaftattaciyar addu'a daga gareki,
ki kular min da Affan kamar yadda zaki kula dani domin ni da shi bamu da wata maraba kuma nasan zai kula dake kuma ya kaunace fiye da yadda ni nayi, ki yawaita istigfari domin istigfari yana kusanta bawa da ubangijinshi kuma mai yawan yinshi zai kasance kullum cikin nutsuwa da walwala,

cikin sheshshekar kuka Afeeyah ta buďe baki zatayi magana jabeer ya sa hannu ya rufe bakin yace karki ce min komai ga Affan can yana jiranki zaku tafi gida, nagode sosai da ziyara,
cikin kuka ta cire hannunshi a bakinta tace dan Allah yaya jabeer ka tsaya kaji abinda zan faďa maka,
girgiza kanshi yayi yana mata murmushi hasken hakoranshi suka rufe idonta ta durkushe a gurin tana kallonshi cikin hasken tana kuka sosai tana kiran sunanshi,
wata sassanyar iska ta shiga kaďawa a gurin har hasken jabeer ya bace ma ganinta,
runtse idonta tayi tana kuka sosai tana faďin dan Allah karka tafi ka barni,

Hannu taji cikin nata ana murzawa a hankali sannan taji saukar ruwa a kan hannun,
a hankali ta fara buďe idonta da yayi mata nauyi sosai ta saukesu kan Affan dake zaune kusa da ita kanshi a kan hannunta yana zubar da hawaye,
lumshe idonta tayi hawaye na zuba ta gefensu ta fara tuno mafarkin da tayi akan jabeer,
meyasa ya tafi bai tsaya yaji abinda zance mishi ba, meyasa be bari nasan abinda zan faďa mishi ba,
shikenan bazan kara ganinshi ba har in koma ga Allah,
to ni yaushe zan mutu, wayyo Ya Allah ka dauk---- Affan yayi saurin toshe mata baki da hannunshi yasa hannu yana share mata hawayen dake gangarowa daga cikin idonta,
buďe idonta tayi ta kalleshi tasa hannu ta ďan ture hannunshi cikin muryar kuka tace kukan me kakeyi,
da mamakinta sai taji ya kwanto jikinta yace kukan abin da kikeyi,
a hankali tace ai bakasan kukan da nakeyi ba,
ya ďago jajayen idanuwanshi yace nasan har duniya ta naďe bazaki taba yin kukan komai ba in ba na rashin jabeer ba,
cikin mamaki ta kureshi da ido hawaye ya kara zirarowa a cikinsu cikin rawar murya tace kasa--- ya fashe da kuka yace nasani Afeeyah, nasani,
nasan jabeer ya tafi ya barni,
nasan bazan sake ganin fuskarshi mai dauke da murmushi a kullum ba,,
nasan bazamu sake haďuwa mu rungume juna mu faďa ma juna damuwarmu ba,
bansan me yasa mutuwa ta zabi jabeer ta barni, bansani ba Afeeyah,
ya karasa fadi yana kuka kamar karamin yaro,,
kuka suka dinga yi babu mai rarrashin wani a cikinsu,
saida sukayi mai isarsu sannan Affan ya ďago ya kalleta murya a dashe yace nagode, nagode da abin da kikayi min,
kau da kanta tayi tace ka gode ma Allah da kaka liman,
ya juyo da fuskarta yana kallon rinannun idanuwanta yace kullum cikin gode musu nake,
godiyarki ta daban ce Afeeyah, babu wanda zai dauki kasadar da kika ďauka a duniyar mu ta yanzu,
kinyi mana abin da ko dan uwa na jini bazai iya yi mana shi ba, bamu da wata kalmar da zamuyi amfani da ita gurin gode miki, Afeeyah tace karka gode min na cika kudirin jabeer ne, wannan shine burinshi na karshe, saboda wannan kudirin aka kashe min shi,,,
Affan yace nasan komai Afeeyah kuma in shaa Allahu wacce ta kasheshi ba anan duniya ba ma har a lahirah bazata taba samun kwanciyar hankali ba,
Afeeyah tace tun a duniya nakeson Allah ya wulakanta min ita, wallhi da nasan ita ce silar mutuwarshi na rantse da bazan kyaleta ba da nayi mata abun da zata gwammaci mutuwa da rayuwa,

Affan ya share mata hawaye yace ki kwantar da hankalinki nasan yanzu duk inda take a cikin bala'i take,
Afeeyah ta girgiza kanta tace da hannuna nakeson in kasheta kuma yau dinnan,
Affan yace hmm nima naso hakan tun ranar da na dawo cikin hayyacina,
nan ya bata labarin komai harda dawowar umma da bacewar oyizah,,,,,
cikin mamaki Afeeyah tace zatayi abinda yafi haka muguwa azzaluma, Allah ya isa tsakanina da ita,
in shaa Allahu sai tayi mutuwar kask---Affan ya katseta da sauri yace wannan adduar bata kamace ki ba, Allah yasan yadda zai tafiyar da irinsu ki zuba ido ki jira lokaci,
Afeeyah tayi shuru tana kallonshi kamar ba shi bane tababben bawan da baya taba maganar da zaka iya fahimta a da,
Allah mai iko......

Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:38] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 6⃣4⃣ By Aysha Ya'u Kurah

Daren ranar suna zaune gurin meeting bayan sun dawo daga gurin dodon tsafinsu,
gaba dayansu suna sanye da jajayen kayansu da suke amfani dashi,
bayan sun gama tsaface tsafacensu sai chummy ta mike taje ta shigo da ďan tsoho,
a tsakiya suka sashi kamar yadda suka saba,
kewayeshi ta farayi tana yan sirkullenta a kanshi sannan ta zauna,
ďaya bayan ďaya tsohon yake bin mutanen gurin da kallo,
yana zuwa kan oyizah ya tsayar da idonshi kyarr a kanta baya ko kiftawa,
kureshi itama tayi da ido cikin rashin tsoro ta daka mishi tsawa tace daina kallona, idon wannan tsohon ko rawa baya yi ya fara motsa bakinshi da babu hakori ko ďaya a ciki,
oyizah ta kalli chummy tace my lord plss mu gama da tsohon nan mu cigaba da abinda ke gaban mu,
chummy bata kalli oyizah ba ta cigaba

Please Login or Register in order to submit comment