Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaura mashi sonki kin san maiyasa nace haka."?



Matsowa nayi kusa da Aunty Asiya sanann nace "A'a." murmushi tayi sannan tace "saboda ya soki lokacin da kike tare da budurcinki, ke kuma a lokacin kika nuna mashi tsana mai girma gami da karfi a fili kike cemai kin tsaneshi amman hakan baisa ya hakura dake ba, a lokacin saboda shi da rai yake sonki ba da zuciya ba, sannan kuma sonki a jinin jikinshi yake baya iya rayuwa idan ba tare dake ba, saboda da soyayarki yake rayuwa da sonki yake yawo a jinin jikinshi, akazo kika rasa abunda zaisa yace ya fasa sonki dan yanaso yanda yake saurayi shima ya fasa budurwa, dan ko wani saurayi gurinshi kenan a duniya fasa sabuwar budurwa gal a cikin leda, amman shi bai damu da wannan ba ke kawai ɗin dai yake so ba budurcinki ba Khady, wallahi Khady Aminu shine masoyinki na gaskiya karki yarda dadin bakin Dr Umar ya kwasheki kizo kiyi da nasani daga baya."



Numfasawa tayi sannan tasha ruwa ta cigaba cewa." shima Dr Umar din mutumin kirki ne, kuma masoyinki ne na gaskiya, amman baikai Aminu sonki ba Khady, naji Dejja tace yana da mata kinga ko shi ya ɗanɗana zaƙin budurci kuma yana ƙasa zuciyarshi ba zai taɓa mantawa da ranar da ya fara kusantar matarshi ta farko ba, sannan kuma tsarin da take tafiyar da gidanta haka zakibi idan kinje sannan kuma watan watarana dole sai yayi maki gori a yanda ya samaiki, ke bari kiji yana da mata fa kuma dole tayi kishi dake balle ma taji abunda ya faru dake itama sai tayi maki gori ko kuma ta zugashi cikin dubara irin tamu ta mata har tayi nasara watarana a gabanta yayi maki gorin rashin kawo mashi budurci da bakiyi ba, shiyasa ake son a rike mutunci saboda da haka Khady, kiyi tunani sannan kuma ki cigaba da addu'a."



Shiru nayi kawai na kasa magana ina tunanin maganar Aunty Asiya, tabbas gaskiya ta faɗaman kuma take maganar Nurandeen ta faɗo man inda yake cewa babu wanda ya dace ya aureni sai shi, shinee kawai wanda zan aure mu rufama kanmu asiri tunda shine sillar rabani da budurcina da yayi, hawaye kawai na share na kwanta bance masu komai ba suma basu matsa da nace masu komai ba, sake kirana akayi ina dubawa naga number din Nurandeen ce dauka nayi, cewa yayi. "Haba Mylife mai yasa kike man haka? Ina sonki ina kaunarki amman ke baki gani, tabbas nasan ni mai laifine a gareki amman ki sani idan da laifi glove to harda na battery, saboda kece kika nunaman hanyar duk abunda nayi maki Khadija, karki manta ranar da na fara ganinki naji ina sonki kuma inason ki zamo mata a gareni kuma uwa ga ƴa'ƴana, tsakani ga Allah nayi murnar ganinki sosai amman ina zuwa da dare wajen ki kika zoman da wata irin shiga Khadija sannan kuma kinsa wani irin turare wanda ba zan iya control din kaina ba akanki ba Khadija, asilima kamshin turaren kawai naji na shiga cikin wani yanayi a lokacin idan banyi maki abunda nayi maki ba a ranar ina tunanin bani iya kwana duniya Khadija lokacin da na taɓaki abun mamaki bakiyiman shamaki ba sannan kuma baki nunaman ɓacin raiki ba, uwa uba kuma take kika biye ma bukata ta akanki Khadija, kenan duk abunda ya faru a tsakaninmu harda laifinki da kuma laifina wallahi ba halina bane kuma ban taɓa sex da wata yarinya ba duniya sai ke, ko Aziza da tazo man da bukatarta a kaina da na fara biye mata Khadija bayan rabuwata dake sosai muke soyayya da ita, amman ban taɓa kusantarta ba dan ban yarda da ita ba, ina tunanin bata rasa cuta dan na lura yar'hannu ce, kuma take na gane komai kikayi itace sila, itace tasaki a harkar duba da yanda Dejja ta nuna damuwarta akan ki, kuma ta gaya man yanda kuke da Dejja."



Yanda naji muryarshi nasan kuka yake shirin yi man da Nurandeen kuka baya yi mashi wahala, zaiyi magana na katseshi nace "dan Allah Nurandeen kayi hakuri ka rabu dani sannan ka barni naji da abunda ke gabana, dan ni yanzun na manta da baya ina gyara gaba ne, san... "No Khadija sai kin barni na ida gaya maki iyakar gaskiya ta, da ki yarda da karki yarda dole na gaya maki sannan na nemi yafiyarki akan abunda nayi maki Khadija, amman ki sani wallahi ni ba mazinaci bane kece kikasa na fara zina a rayuwata kuma akanki ban sake zina ba Khadija, haka na cigaba da soyayar shan minti da Aziza, amman ban yarda nayi sex da ita ba gudun matsala, ba yanda Aziza batayi ba akan na kusanceta amman naƙiya, ita kuma ta nace akan kudirinta akaina, wallahi Khadija watarana bayan mun gama waya da ita tace man gidana zata kwana tana wani hotel wajen saurayinta zai biya mata bukatarta dan tasan ko tazo wajena ba abunda zaiyi mata dan ta lura bani sonta kece kawai nike so shiyasa na baki kaina, amman ita na kasa dariya kawai nayi mata sannan nace sai tazo bayan na gama wayar da ita na cigaba da hidimata dan wallahi ko lokacin na kira wayarki sai naji ta a kashe duk ina cikin damuwar rashinki dan ni ba wanda nike so sai ke Khadija, dare yayi Aziza bata dawo ba dan har ɗaya tayi nikuma ina ganin haka na kwanciya ta nace ma gate man idan tazo ace mata karta tasheni."




Kuka Nurandeen ya fashe dashi sannan yace. "Wallahi Khadija da safe aka kirani waya wai nazo hotel din da Aziza ta kwana da wayarta aka kirani akace nazo, da nace bani zuwa akace dole nazo ko, haka na shirya naje wannan hotel din Khadija nayi baƙin gani *INALILLAHI WA'INNA'ALAIHIRAJUN* Khadija ina zuwa hotel din nace gani ance nazo akace na shiga wani room ina shiga na tadda gawar Aziza akan wani mutume suna cikin *ZINA* Allah ya aiko da mala'ikan mutuwa ya zare rain Aziza ita da wannan mutumin suna cikin aikata masha'arsu, wallahi Khadija a ranar naji na tsani kaina na tsani rayuwar da nayi dake, bansan lokacin da na fashe da kuka ba, nace ni maiye haɗina da ita da har za'a kirani? Kallona akafara yi ana mamakin maganar da nayi ina kuka, wani ne ya dafaman kafaɗa yace man Alhaji hakuri kawai zakayi amman ko matarka ta cuceka kuma ta cuci kanta da kanta gashi ta biye ma son zuciya ta mutu ta hanya bamai kyau ba, mu yanzun zamu kaisu Aminu kano mu samu a raba gawar sai mu baka taka suma mu basu nasu dan ba musulmi bane shi."



"Kallon mutumin nayi sannan nace a'a wallahi ni ba matata bace kawai dai muna soyayya kuma bansan tana wannan halin ba da ko soyayyar ma bani da ita."


"Nan take kallo ya dawo kaina mutumin yace kana nufin ba matarka bace wannan? Ɗaga mashi kai kawai nayi ina kuka Khadija kuma a lokacin ba wanda nike tunawa sai ke dan tabbas nasan nacuceki nida Aziza gashi ita Aziza ta tazo karshe tayi mutuwar asara Allah ma ya soni ba a gidana ta mutu ba, da bansan mai zance ma mutane ba sunaman kallon mutumin kirki, sannan bansan mai zance ma Dad dina ba da Mom, ji nayi mutumin yace yanzun kai bakasan gidansu ba? ɗaga masu kai nayi sannan nace wallahi bansan koda gidansu ba, asalima ban taɓajin tayi waya da yan gidansu ba, amman ta taɓa ceman majoji take anan kano daga nan bansan komai ba wallahi akan taba, shiru wajen kowa yayi yana mamakin abunda na fadi wayarta aka dauka aka nunaman yanda tayi saving din number ta tasa man *MIJINA* da abunda tayi saving kenan banyi mamaki ba dan nasan Aziza tace man tana sona kuma idan na yarda aurena zatayi nine na nuna mata rashin yarda da hakan da nasa tabar maganar ashe abun yana rainata."


"Jinayi mutumin yace man muje majoji mu nuna pictures dinta may be ayi dace, da wanda ya santa haka muka tafi cikin motata su kuma sauran suka dauki gawarsu aka wuce hospital da ita.


*~inason ki tsaya ki karanta please 👇~*

*INALILLAHI WA'INNA'ALAIHIRAJUN, nasan page din yau ya sosa ma wasunku zuciya wasunku kuma ba abunda sukaji duba da abunda Aziza tasa Auta akai ko🤔😭*



*bari kuji abunda nikeson ku sani shine, ba laifin Aziza bane kawai harda ita Khadija fa, dan ita taba Aziza fuska harta tasa bisa hanya, da ita Dejja bata bada fuska ba Aziza ta tasata?*


*sannan kuma ya kamata ku duba kuma kuyi tunanin maganar da Nurandeen yayi ma Dejja, tabbas harda laifin Khadija sosai, saboda idan zaku tuna randa zata fara zuwa wajen Nurandeen sai dai Aziza taba Auta turare mai karfi ta shafa, shin abun lura da abun shine shin shi Nurandeen ba mutum bane? Kuma babu jini a jikinshi ne? Dole yaji felling ya taso mashi idan har shi yana da lafiya.*



*Note:-zuwa gareku yan'matan ya kamata ku daina shafa turare mai karfi kuna fita ko kuna zuwa wajen samarinku yin hakan yana bada tasiri wajen zina da dai abuwa nagode*




*inason naga ruwan comment a wannan page din 🙏*


Share
Comment
And
Vote







*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 47⏩48



*Sannunku da kokari myreal fan's, kuna nuna man kauna wajen karanta wannan buk din gami da yi man comment, sannan kuma shi comment dinku maganar gaskiya yana sani farinciki sosai da Sosai, fatana dai Allah ya bar kauna ta fissabilillah, dan kuwa ina maku son fissabilillah 💜*


*Tom page din yau sai dai ayi hakuri, dan dole a samu winner da kuma loser tsakanin TEAM UKU, da Team din AMINU sai Team din Nurandeen sannan kuma Team din Dr Umar🌚, Allah yaba mai rabo sa'a kawai nidai zani ce😊*



Numfasawa Nurandeen yayi sannan yaci gaba da cewa. "Haka muka tafi unguwar su Aziza dan samun wanda Allah zai sa yace ya santa dan, dan kuwa addu'a tun ina wanda na sani har sai da yakai da ina yin addu'a kawai amman bansan abunda nike cewa ba tsabar shiga tashin hankali da nayi a ranar, cikin ikon Allah muka isa unguwar majoji nan muka raba ƙafa kowa da hoto a hannunshi muka fara nuna ma mutane ko sun san wannan baiwar Allahr, amman ansa ɗaya a'a bansan sanda kuka ya ida ƙwaceman ba saboda shiga ruɗu da nayi nidai bani ansa gawar Aziza saboda gidanmu ba'a santa , idan n kaita mai zance masu game da ita? Ita ba accident tayi ba balle na kaita gidanmu nace ba'a san danginta ba su taimakaman ayi mata sutura akaita gidanta na gaskiya, amman a hotel ta mutu suna zina, kinga dole mutuwarta tayi suna a faɗin nigeria Khadija, nidai bansan ina nike takawa ba kawai jefa ƙafa nike, sannna duk wanda na gani sai na nuna mashi picture dinta koda kuwa ƙaramin yaro ne wanda baisan kowa ba a unguwar, cikin ikon Allah naga wani matashin saurayi kamar ni koda ya girmeni ba zai wuce ya girmeni da shekara ɗaya ba, amman bada shekara biyu ba, zaune yake bakin wani shago a unguwar ga dukan alamu shagon nashi ne ma, ida zuwa nayi wajen shi na nuna mashi picture din nace ko ya santa, kallona ya tsaya yi sannan yace man ina na samu wannan picture din? Ce mashi nayi gidansu yarinyar ake nema a unguwar nan, dan Allah idan ya sani ya taimaka ya gayaman dan ana son gani iyayenta ne, girgiza kai mutumin yayi sannan yace ai na santa karka damu bari na kulle shagon na kai ka har gidansu, ai bansan sanda na rungume shi ba,na kuma fashewa da sabon kuka, kallona yake yana mamaki sannan yace kukan mai kakeyi ne bawan Allah, girgiza mashi kai nayi sannan nace nidai dan Allah abokina ka kulle shagon ka kaini gidansu kaji komai maiye idan muje, muna cikin magana muka hadu da mutumin da mukazo dashi , kallona yayi sannan yace fatan kai ka dace ka samu wanda ya santa ko? Bansan sanda Murmushi ya kauceman ba, na ɗaga mashi kai ina nuna mashi mai shagon nan, shima zuwa yayi yace mu tafi."




"Nan muka tafi mu dukanmu ba wanda yake magana, kowa da abunda yake saƙawa a cikin zuciyarshi Khadija, wani babban gida muka iso, dan gida yana da kyau ba laifi tsayawa mukayi bakin gate wannan mutumin ya shiga ciki bai jimaba sai gashi yace mu shigo, tare muka shigo dan harda police muke ni ban ma lura da wasu police ba sai lokacin da zamu shiga cikin gidansu, muna shiga aka kaimu part din baƙi nan muka zauna munyi jiran kusa ten minutes sai ga wannan mai shago ya shigo mana da ruwa da lemu yace kuyi hakuri mun barku zaune, ga Baban nan zuwa yanzun ya dawo baya gida, amman na kira shi waya yama shigo ya shiga part din shi dan ya rage kayan jikinshi, da sauri na ɗago kaina aiko muka haɗa ido biyu da wannan mutumin nan naga yana yar'kama Aziza, sauke kaina nayi kasa ban sake ɗagowa ba, can sai ga Babanta ya shigo da sallama a bakinshi, ansawa mukayi sannan muka bashi hannu aka gaisa, bayan an gama angaisawa aka fiddo picture din Aziza aka nuna mashi aka wannan yarinyar ƴarka ce."?



"Allah sarki ɗaga kai yayi kawai amman baiyi mana magana ba, kuma na lura tunda aka nuna mashi picture din Aziza fuskarshi ta chanza ta tashi daga walwala ta koma rashin walwala, tunda muka lura da yanda yanayin shi ya koma sai muka kasa yi mashi bayanin abunda ya kawo mu, daurewa wannan mutumin yayi sannan yace Alhaji hannunka ba zai ruɓeba ka yanke ka yada, duk abunda Aziza tayi maka ya wuce dan Allah ka yafe mata, dan yanzun ba abunda Aziza take bukata a wajen ku idan ba wannna yafiya ba, sannan kuma addu'a idan har kuka yi mata haka to kun gama mata komai kuma kunyi mata abunda ita ta kasa yi maku, dan Allah Alhaji karkace ba zaka yafema ƴarka ba ƴarka ce ta cikinka komai tayi maka ayi hakuri kar a tuna baya a yafe mata."



"Tunda ya fara maganar Baban Aziza yake kallonshi har ya gama, sannan shima yace Bawam Allah ai Aziza da bakintaa tace ni ba ubanta bane, sannan kuma tace man na manta da na taɓa haihuwar wata mai suna Aziza kuka ya fashe dashi ya cigaba da cewa yarinyar nan ta zaɓi wata gurba marar kyau nida yan'uwa ba yanda bamuyi da ita ba akan tabar wannan ƙazamar rayuwa amman tayi kunnan uwar shegu damu, kaga wannna har aure sai da na daura mashi da ita, ranar da aka daura masu aure a ranar ta gudu daga nan bamu sake ganinta ba, koda kuwa labarinta ban sake ji ba sai yau ku da kuka zo mana da labarinta, daman ai haka bariki take angama yayinta shine aka dawoman da ita ko? To wallahi bani ansarta taje ta cigaba da rayuwar da ta ga itace ta dace da ita."


"Dafashi wani police yayi sannan yace hakuri zakayi Alhaji dan yanzun haka Aziza bata bisa doron duniya, Allah S. T.W ya anshi rain Aziza dan kuwa yana hannunshi sai dai mai Aziza ta mutu ta hanyar da mai kyau ba dan kuwa a hotel ta mutu suna aikata *Zina* da wani wanda ba ma addininsu ɗaya ba, a haka rai yayi halinsa da akazo gyara room aka tadda gawarsu sai muka kira wannan bawan Allah ya nunani sanna ya cigaba da cewa munsa matarshi ce dan tayi saving din sunanshi da *Mijina* koda yazo yaga gawarta ya tsorata sosai kuma har yanzun bai daina kuka ba, yace mana baisan tana wannan harkar ba shi dai yana soyayya da ita suna shirin auren juna, sai yace mana ta taɓa ce mashi ita yar majoji ce, amman bai taba zuwa gidansu ba shine muka shigo majoji dan nemo gidansu yanzun haka gawarta ta hanya dan anraba gawar anba ancan nasu kuma mun bada address za'a kawo maku taku."



"Tashi tsaye Babansu yayi sannan yace inalillahi wa'inna'alaihirajiun, Allah sarki Aziza tabbas kinyi mutuwar asara sai dai muna rokan Allah ya yafe maki nidai ko na yafe maki ƴata na yafe maki har abada inalillahi wa'inna'alaihirajiun, Allah sarki Asiya Allah ya baiyanaman ke cikin aminci tabbas alhaƙin Asiya shine yake biyayarmu a gidan nan, alhakin marainiyar Allah shine yake biyayarmu Allah na tuba, tabbas na kasance uba marar kyautatama iyalansa, kallonshi muka fara yi sannam akace wacece Asiya? Ce mana yayi Asiya ɗiyarshi ce ta cikinshi mahaifiyarta ta rasu ta barta cikin matanshi suka matsa mata bata da gata sai su Aziza da suke da uwa a cikin gida ba soyayyar da bai nuna ma su Aziza ba da iyayensu amman banda Asiya da tazama baiwa a gidansu Aziza dan duk wani aikin bauta Asiya ce take yinshi lokacin da suna zaune a kunya chemist ɓarayi suka shigo gidansu nan sukayi ma Asiya fyaɗe yace mana yayi kuka a lokacin daga baya matanshi suka zugashi akan Asiya ta samu hanya tana bin maza tunda taga ɓarayi sunyi mata hanya, da bani yarda sai daga baya na fara yarda sai kuma ga ciki ya baiyana a jikin Asiya ni kuma ido ya rufe sai nace wajen iskanci ta samaishi dan daga yi mata fyaɗe rana ɗaya ciki ba zai shiga ba, da bakina da kaina na kori Asiya a gidana haka ta tafi tana kuka, ni kuma a lokacin ko a jikina dan gani nike ba zan yarda ba a haifa man shege a gidana ba, haka ta tafi muka cigaba da rayuwar mu cikin gidanmu muka manta da Asiya, bamu damu da wani hali take ciki ba sai ga Aziza ta bullo da halin bin maza na girgiza sosai tana level one a university ba faɗan da banyi mata ba, karshe na aure mata aure da Kamalu gashi nan ɗan ƙanenane amman sai ta gudu, bayan ta gudu kuma ƙanwarta ita kuma take neman mata😭, yanzun haka sana'arta kenan bin mata take dan itama ta tashi ta barman gidan tana zaman kanta, in kaiku karshe yanzun haka baki ɗaya yarana bana maijin magana daga mai shaye shaye sai mai yi ma ciki, yaran Amarya tane kawai masu ji su biyu ne suma ba wani girma sukayi ba sosai balle nasan ya nasu girma zai zo masu, inalillahi wa'inna'alaihirajiun 😭, wallahi Khadija sosai labarin Baban Aziza ya samu kuka muna cikin kukan akazo da gawar Aziza nan kuka ya zama sabo, haka aka gaya ma matan gida kamar anbusa isul haka unguwar ta kaure da rasuwarta haka muka hadu muka sallaci gawar Aziza muka rakata gidanta na gaskiya, bayan mutuwar da kwana uku nabar zuwa gidan su Aziza, kinji yanda karshen Aziza yazo Khadija dan Allah Khadija ki yafema Aziza na rokeki ki yafe mata dan al'farma Annabi Muhammad S. A. W."


Shiru nayi kawai ina hawaye dan har ga Allah naji mutuwar Aziza sosai, duk da ta bada gudumuwa wajen lalacewar rayuwata amman nasan harda laifina ba laifinta bane dan nice na bata fuska har ta sani a hanya, nayi mamaki da naji Aziza ƙanwar Aunty Asiya ce ji yayi shirun yayi yawa naji yace.



"Khadija ya naji kinyi shiru say something please Khadija." Nima ajiyar zuciya nayi sannan nace "tabbas naji mutuwar Aziza sosai Noor, na yafe mata balle ma batayi man komai ba, tunda komai ya faru dani bata sani nayi dole ba, asalima iyakacinta dai kawai ta bani shawara nice nan mai laifi da na biyema son zuciyata na aikata aikin da nasani, kuma da nasani ance ƙeyace kuma kuskure na riga na aikata sai dai mu roki Allah ya yafemana baki ɗayan mu, ita kuma Allah ya kyauta makwancinta Amin."


Ajiyar zuciya naji yayi sannan yace "Alhmdullh Allah abun godiya tabbas Khadija keɗin ta daban ce kina da kyawkywan hali, wallahi halinki mai kyau ne wallahi Khadija ina sonki ba zan iya rayuwa babu ke ba dan Allah Khadija ki yafeman mu auri juna mu rufama junanmu asiri Khadija, ki tuna son da kika nunaman a baya ki maidoshi wallahi zan kula dake sannan kuma zan baki kulawa ta mussaman wanda ba zakiyi tunani ba Khadija, kin... "Ya isa haka enough please Noor, har da sauran soyayya a tsakanin mu daman? Har kana da bakin da zaka dawoman da soyayyarka a cikin zuciya ta? Kayi hakuri Noor tabbas ka faɗi gaskiya da na soka so wanda na sani har na mutu ba wanda zan ƙara yi ma irinshi sai dai yanzun kayi hakuri ba zan iya aurenka ba, ina maka fatan Allah ya baka wanda ta fini." ina gama faɗa mashi haka ban barshi yayi magana ba na kashe wayar baki ɗaya na kalli su Aunty Asiya da suka zuban ido tunda na fara wayar cewa nayi.



"Daman bakuyi bacci ba."? Ɗaga man kai kawai Dejja tayi sannan tace. "Taya zamuyi bacci, bayan munji kinata salati harda kuka, mai kuma shi Nurandeen ɗin ya gaya maki."? Murmushi na ƙalilo mai ciwo sannan nace. "Aunty Asiya ina tambayeki mana."? Nayi mata maganar ina murmushi na samu na kauda damuwar da ke raina dan bansan na tada mata hankali duk da inajin ɗaci da ciwo na mutuwar Aziza, itama murmushin tayi sannan tace "tambayarni ina jinki Khady." kallonta nayi sannan nace. "Daman da kukaje kano kai da su Mama bakuje kuka gaida su Baba ba da matanshi."



Chanza fuska ta ɗan yi alamun tambayar bata yi mata dadi ba, kallon juna mu kayi da Dejja tayi man alamun mai yasa nayi mata tambayar sai na nuna mata ba komai, maida kalona nayi gareta nace. "Yi hakuri Auntyna bansan tambayar zata ɓata maki rai ba da banyi maki ita ba." kamo hannuna tayi tana murmushi sannan tace. "Ko ɗaya Khady, kawai dai nayi mamakin tambayar ne, ai ni bani zuwa gidanmu har abada, Baba da bakinsa yace na bar mashi gida, kinga kenan da hannunshi ya yankan man ticket din shiga duniya, Kinga kenan banga amfanin komawa wajen shi ba tunda ni yar'iska ce ina neman maza har sunyi man ciki, Khady ba amfanin komawa karda na koyama yaranshi bin maza."


Girgiza mata kai nayi sannan nace. "Dan Allah kiyi hakuri ki sasanta da Baba, nasan yayi nadamar abunda yayi maki Aunty kin manta kece kika maidoni gida? Maiyasa ke ba zaki sasanta da Baba ba ki maida komai ba komai ba please Auntyna." murmushi tayi sannan tace. "Zan koma gida saboda ke Khady, amman ba yanzun zan koma ba sai nayi aure may be har haihuwa sai nayi sannan zan koma masu da mutuncina, su san na cigaba ba baya ba."murmushi nayi sannan nace. "To fatan ankusa auren ko."? Dariya tayi sannan tace. "Ai naso gaya maku tunda kuka dawo sai naga kina cikin damuwa shiyasa ban gaya maku ba."



Dariya Dejja tayi sannan tace. "Wallahi Aunty ni nasan zakiyi aure kuma nasan Baba zaki aure." kallon Dejja nayi cikin surprise nace. "Ke wai wane Baban? Ba dai Yaya Jamilu ba."? Cewa tayi."ehmana shi, kiji Aunty Auta daman ina da wani Baban bayan shi."? Girgiza mata kai nayi ina dariya dan naji dadin yanda Yaya zai auri Auntyna, kallanmu tayi taga yanda muke ta farinciki tace. "Ku yanzun bakuji haushi ba? Bama kamar ke Dejja da za'ayi ma Mamanki abokiyar zama."? Girgiza kai Dejja tayi sannan tace. "Wallahi ba abunda mukeji harda Momy dan Momy ta gayaman yanda akayi har ƙin yarda da kikayi sai da aka sha wuya ai mun zama ɗaya Aunty kuma da zuciya ɗaya muke zaune dake, da yaje ya auro wata wanda bamu sani ba fa? Ai kinga gwara ke mudai fatanmu Allah ya bamu zaman lafiya."


"Amin ya Allah."nace dan kuwa Aunty kasa magana tayi, kallon su na sake yi sannan nace. "Dejja kinsan kuwa Aziza ta mutu."? Kallona tayi sannan tace. "Taya zan sani Aunty Auta? Allah ya jikanta da rahama muma Allah yasa mu cika da imani."
Banji dadin yanda Dejja ta nuna rashin damuwarta ba, akan mutuwar Aziza sai dai kawai nayi murmushi nace. "Amin, ni zan kwanta sai da safenku."
Haka

Please Login or Register in order to submit comment