Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi a jikinshi yana shareman hawayena yana yi man alamun lailashi, kama hannuna yayi ya zaunar dani a kujera shima ya zauna yana kallon Aunty Asiya sannan yace “sannu Baiwar Allah, ina kika samu Auta." Murmushi tayi sannan tace “da zaka bani dama da ka taso munje gida wajen Mama sai na gaya maku yanda akeyi kai da Mama." tashi yayi dan murna ta hanashi magana ya dauko key din motarshi yace mu wuce mu shiga mu tafi da kanshi ya dauki kayanmu yasa a boot sannan muka dauki hanyar zuwa gida wajen Mama....



Tunda muka dauki hanya Yaya yake kiran su Yaya Fatima yana ce masu su hadu gidan Mama yanzun koda sun tambayeshi lafiya sai yace idan sunje sun gani haka ya kama kiransu yana gaya masu, kallonshi nayi sannan nace “Yaya wai ina su Dejja suka je ne."? Dariya yayi sannan yace “ai Dejja ta koma da zama gidan Mama, su kuma yau sukaje yini wajen Mama duk suna can." naji dadi sosai sai naji na ƙara mu isa gidan Mama dan naga Dejja duk da ba daɗewa nayi bani gida ba amman nayi missing din Dejja sosai, nasan itama tayi missing dina.

Haka muka ida isowa gidan Mama, abun Mamaki duk su Yaya Fatima sun rigamu isowa duk da daman basu da nisan da Yaya yayi ma gidan Mama fitowa mukayi Yaya ya kama hanuna yace ma Aunty “Baiwar Allah Bissimilla muje ko."? Tafiya muka fara yi sannan muka shiga....



Manage pls, ina aiki ne sosai, dan kar na barku babu na dan yi maku wannan, sannann na gode da ruwan comment dinku🥰

Share
Comment
And
Vote





*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 31⏩32


Muna shiga ciki suka tashi tare lokaci guda, kowa nunani yake da yatsa ya kasa cewa komai Yaya Amina ce tayi karfin halin zuwa wajen Yaya tace "Yaya da gaske Auta ce wannan ko kuwa dai webuwa take mana."? Murmushi Yaya yayi sannan yace "itace Amina, Auta ce da kanta Allah ya anshi adduar mu Allah ya maido mana da Auta cikinmu da kuma taimakon wannnan baiwar Allahr." ji nayi Mama ta rumgume ni tana kuka tana cewa "Allah nagode maka da mamaidoman wannan yarinya cikin koshin lafiya, Allah nagode maka tabbas babu abun bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad S. A. W bawansa ne kuma manzonsa ne." nima kukan nike dan na kasa cewa komai dan nasan na jefasu cikin kunci guduwar da nayi, amman bani da zabi dole tasa na gudu, kama hannun Aunty Asiya Yaya Fatima tayi ta zaunar da ita sannan nima ta zaunar dani ta kawo mana ruwa da abinci tace munci sai muyi magana, nan mukaci abinci na kai mana kayanmu room dina nan naga Dejja kwance tana bacci ban tadata ba na fito kallon su nike suma ni suke kallo zama nayi sannan Yaya Aisha tace "Auta sannu da dawowa cikin yan'uwanki, barka da dawowa hanya mafi inganci da kuma ƴanci." ɗukar da kaina kawai nayi ina share hawaye Yaya ne yayi gyaran murya sannan ya fara cewa.


"Alhmdulillahi godiya ta tabbata ga Allah ubangijin taliƙa, mabuwayi gagara misali, Allah STW cikin ikonsa da yarda sa yasa mararniyar Allah ta dawo cikin tushunta, musan wannan ba wayaunmu bane ba kuma dubararmu bace ya yarda Allah ce, dan haka sai kawo yayi salati goma ga Annabi sai muka a karanta fatiha." nan mukayi salati da karatu kowa ya shafa Yaya ya kara addu'a sannan yace



"Malama zamu so ki gaya mana inda kika Nana Khadija." numfasawa Aunty tayi sannan ta cigaba da basu labarin haduwarmu har labarina da na bata zuwa tuban da tayi daga harkar da take har yau da ta maidoni gida wajen su.


Sosai wajen sukayi mata godiya inda Mama tace "Asiya mungode kuma kin taimakemu da kika maidota kuma kema kin nema ma kanki hanyar tsira daga azabar ubangiji da kike tuba kika daina kazamar harka, dan haka mu bamu da abunda zamu iya biyanki dashi sai dai muci Allah ya biyaki da gidan Aljana Fiddausi sannan kuma Allah ya jikin Mamanki ya kuma ganar da Babanki dan haka zamu zauna nan dake tsakani ga Allah, amman bayan kinyi sati biyu kin huta sosai zamuje kano kiga dangin mamanki nasan har yanzun hankalinsu ba kwance yake ba, idan yaso daga baya kin dawo mudai muna maraba dake dan kin zama yar'gida ko ya kuka gani Jamilu."?


Yaya Jamilu yaji dadin hukuncin da Mama ta yanke dan baison ace bamu dauki Aunty ba, cewa yayi. "Ai hakan shine dai dai Mama, Allah yasa Babanta ya gane gaskiya ya gane hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yada Allah yasa mudace, ku kuma su Fatima ga yar'uwa kun samu tunda kune mata ku dauketa kamar yanda kuka dauki kanku kuyi shawara da ita akan matsalarku itama ta kawo matsalarta ku kashe ku rufe ba wanda yaji ba wanda ya gani ina fatan ta samu karbuwa a matsayin da nike bukata a gareku."?



Cikin jindadi Yaya Fatima tace "sosai ma Yaya, ai yanda na dauki su Amina haka na dauketa muna godiya sosai Asiya, Allah ya bar zuminci."

"Amin ya Allah, na gode da hallacin da kuka nuna man kuma insha Allah zaku samaini mai rikon amana insha Allah ba zakuyi da nasanin aminta dani ba da yarda Allah." cewar Aunty Asiya tana share hawaye muna cikin magana mukaji anfasa ihu an fado samana nima ihun nayi na makyalkakyaleta muna murna dan naji dadin ganin Dejja sosai, Aminiyata kuma ɗiyata kallona tayi sannna tace "Alhmdulillahi Aunty Auta kin dawo garemu, sannu Aunty Auta." shafa fuskarta nayi ina Murmushi sannna nace "yauwa Dejja ya hutu har yanzun ba'a koma season ba."!? Cikin jindadi tace "eh ba'a koma ba sai cikin satin nan insha Allah, fatan kindawo da shirin komawa ko." girgiza mata kai nayi sannan nace "wallahi Dejja ina tsoran jami'a dan Jami'a ta koya man darasi wanda ban iya mantashi na hakura nidai da zuwa jami'a a barni gida nayi zamana kusa dasu Mama." girgiza man kai itama tayi sannan tace "ban sanki da saurin karaya ba Aunty Auta, dan Allah ki koma karki bamu kunya mana, nasan zaki iya sosai ma." zanyi magana Aunty Asiya tace "tabbas ko Dejja zata koma ai karatu shine mutun dan haka ki fara shiri ma yarinya idan kuma kunje sai a karatu a kuma sama rai jin tsoron Allah a duk idan kuka tsinci kanku."


Sai a lokacin Dejja ta lura da Aunty nan ta gaidata suka kara ƙaraman kwarin giwar komawa makaranta sannan su Yaya suka tafi gida aka bar mana gidanmu daga ni sai Dejja da Aunty da kuma Mama.



Sosai Mama take nunaman kulawa sannan kuma take nuna ma Aunty, dan kuwa Dejja ji take kamar ta goyamu dan dadi, a daren ranar ta gaya ma registra nadawo ya maganar da sukayi na sake man course da kuma maidoni level one, nan yake cewa lafiya lau idan mun dawo ansan yanda za'ayi bama baya za'a maidoni ba dropping din level two zanyi na gyara co din na kwaso idan kuma na shigo level 3 shima sai nayi dropping haka har na gama, amman tace duk da haka a sake man course nan yace sai ya maidoni microbiology, sannan a daren ta kira Aminu ta gaya mashi dawowa ta yace mata gobe zai shigo sai murna yake ni abun har Mama ma ya dunga bani duk tsanar da nike nuna mashi hakan baisa ya tsane ni ba a lokacin da yadace sai ma sona da kara shiga a ranshi laile Aminu masoyin gaskiya ne, amman na kasa yarda da hakan har yanzun.



Washe muka tashi da shirin tarbar Aminu, Sosai Dejja da Aunty suke hada mashi kayan dadi, dan dafa wannan sauke wannan haka suka kamayi ita kuma Mama sai biye masu take dan da sunce babu kaza zata bada kudi a sawo ko kuma tasa hijab da kanta ta sawo idan ba nisa tun abun yana bani mamaki har ya bar bani suna gamawa sukace naje na shiga wanka ina fitowa Dejja ta fara yi man makeup da yake daman tanayi ma Amare har kid gareta, kallona Aunty tayi sanan tace "nasan har yanzun baki jin son Aminu a zuciyarki ko Auta."? Nidai ban ce mata komai ba sai ma kasa da nayi da kaina ina Murmushi, itama murmushin tayi sannan tace "zaki soshi kamar mai ni na gaya maki abunda zakiyi Yanzu ki ringa kulashi a hankali zakisha mamakin komai dan ga sonshi nan a idonki zuciyarki ce ta hanaki ganin haka."



Nidai dariya kawai nayi sannan aka cigaba da yi man kwaliya ana gamawa na shirya cikin laces dina mai kyau suma suka shirya sannan suka jira zuwan nashi, bamu fi ten minute sai gashi yazo nan Dejja taje tayi mai iso ya shigo Inaji yana gaida Mama sannan suka kawo mashi abinci cewa yayi "nidai Sis ban iya cin komai har sai ra fito na ganta fa." Murmushi Dejja tayi dan tasan za'a rina sannan tace "tom bari naje na taho maka da ita sai ka ganta, dan na lura ba ka yarda da ta dawo ba." Murmushi kawai yayi, itama ta taho dan tahowa dani...





Share
Comment
And
Vote






*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 33⏩34





Tunda Dejja ta taho naga tana dariya nasan da magana a bakinta, kallonta nayi sannan nace "fatan dai yaci abinci ko."? Dariya tayi sannan tace "kwantar da hankalinki Aunty Auta yace baya iya cin komai har sai ya saki a cikin kwayar idon shi." Murmushi nayi kawai sannan nace kice yau Aminu baya cin abinci, dan ba idan zani har sai yaci abinci kije ki gaya mashi haka injini." marairaice fuska Dejja tayi sannna tace "haba dan Allah Aunty Auta ya kamata ki tausaya mashi mana, yana bukatar ganinki hankalinshi ba zai kwanta ba har sai yayi tozali dake please kisa ma ranki soyayyar Aminu, dan shine masoyinki na gaskiya wallahi ko Aunty."


Naunauyen numfashi na sauke sannan nace "zanyi kokari insha Allah Dejja je kice mashi gani nan zuwa yanzun nan." Murmushi kawai tayi sannan ta wuce, tana zuwa tace mashi. " to Uncle Aminu sai hankali ya kwanta ga Aunty nan fitowa tace tana zuwa yanzun." Murmushi yayi sannan yace "Daughter anshi wannan gift ne na kawai kin gayaman dawowar Auntynki sannna gudar kyautar kuma sai kin jini." Murmushi tayi sannna tace "ina godiya sosai Uncle Allah ya barka da Aunty Auta." ɗaga hannu sama yayi sannan yace "Amin ya Allah." tun daga nesa naga ya kafeni da ido sai kallona yake kamar zai haɗiye, ban san na fara dabarbarcewa ba wajen tafiyar dan kallon yayi man yawa sosai, kallonshi Dejja tayi dan taga hankalinshi baya wajen ta gani tayi nice na taho shiyasa attention dinshi baya wajenta tashi tayi tana dariya ta bar mashi wajen tana zuwa dai dai setin kunnena tace "ki daure pls Aunty Auta nasan zaki iya ma, dan nasan Auntyta jaruma ce." Murmushi kawai nayi sannan na ida isa wajen shi, sallama nayi na shiga kasa amsa sallamar yayi kallona kawai yake samun waje nayi na zauna sannan nace "ina kwana." Nan ma shiru baice komai ba sai da aka dan jima sannan yace "Amin wa'alaikumus sallam, masha Allah Alhmdulh, Allah nagode maka da ka maido man da matata gida, lafiya Noor fatan kina cikin koshin lafiya."? Kasa nayi da kaina ina wasa da hannuna sannan nace "lafiya lau, fatan kaima kazo lafiya."? Murmushi yayi sannan yace "lafiya lau Alhmdulh, ina sonki ina kaunarki Khadija bansan ya zan misultamaki son da nike maki ba Khadija, ban son sonki a jinin jikina yake ba har sai da kikayi mana nisa, Khadija nasha wuya sosai wallahi baki san halin da nashiga ba,amman na wahala sosai dan Allah karki sake yi mana nisa ni Aminu inasonki duk yanda kike wallahi."



Kasa ce mashi komai nayi, danni alamarin Aminu mamaki yake bani na yarda yana sona, kuma so na gaskiya da amana, amman ni zuciya ta kasa yarda da hakan dan kuwa duk maganar da ya gama yi man jinshi kawai nayi amman banji komai a zuciya ta ba, amman nasa ma raina zan koya zan tusa ma zuciya ta sonshi dan shine masoyi, ya isa a kirashi da suna masoyi wanda ko wace ƴa mace take burin samu a duniya, tabbas inajin soyayyar Nurandeen a cikin zuciyata dan ta kasa mantawa da shi,amman wannan karan zanyi yaƙi da zuciya ta ba kori son da take ma mayaudari mahaƙinci na tusa mata son masoyin gaskiya wato Aminu, ji nayi yace "dan Allah Khadija karki juyaman baya a wannan karon karkiyi fatali da soyayya ta, ina sonki ina kaunarki ban cancanci kora a wajen ki, ki amince da aurena zan koya maki sona please Khadija." take naji ya bani tausayi daman ashe haka so yake? Tambayar da nayi ma kaina kenan, son maso wani koshin wahala, amman insha Allah zanyi iyakar kokari na Murmushi nayi wanda bansan nayi shi ba, kuma ba komai ya sani Murmushin ba sai maganar Dejja da ta fado man a rai da tace tabbas nasan zaki iya, saboda Auntyna Jaruma ce, take nasa ma kaina iyawa nace mashi. "Karka damu Malan Aminu, Allah ya tabbatar da abunda yafi zama alkhari a tsakaninmu, ya kamata kaci abinci idan baka ci ba niko ba zan ji dadi ba gaskiya." Murmushi yayi take naga kuzarinshi ya dawo kallona yayi sannan yace "duk banjin yunwa amman zanci abincin nan idan har hakan zai saki farin ciki da nishiɗi da kuma annashuwa." fari nayi mashi da ido sannan nace "hakane mudun kaci zanyi wannan abubuwan da ka lissafo, amman idan har baka ci ba zan rasa abubuwan da ka lissafo." zuba mashi nayi sannan na tashi na bashi waje yaci yanda yasan ba zance bai ciba, sannan ya kira Dejja yace tace man ya gama ina zuwa muka kara gaisawa sannan ya bani sabuwar Samsung galaxy S10 sabuwa yace gashi nan yasan yanzun banda waya harda sim duk ya saya man ya sanya man, ansa nayi nayi godiya sannan na raka shi har bakin mota ma dawo na nuna ma yan gida suka taya ni murna.


Tunda Aminu ya bani waya kullun sai munyi waya dashi idan bamu waya to muna online muna chatting sosai yake nuna man kulawa yana nuna man soyayya tsantsa wanda har mamaki take bani idan naga yana rawar ƙafa a kaina sai kace baisan abunda ya faru dani ba.



Nima a wajena ba laifi dan na fara koya kuma ina iyakar bakin kokarina wajen nuna mashi kulawa da kuma soyayya kuma ina addu'a Allah ya tabbatar da alkhari, su Mama sunje Kano da Aunty Asiya wajen family din Mamanta kuma sunyi murna da ganinta sosai, da sun so ta zauna wajen su amman tace aa ba yanzun ba su bata lokacin, basu yi mata gardama sannan sun amshi number wayarta da yake Yaya Jamilu ya siya mata waya haka sukayi kwana biyu sannan suka dawo suna dawowa da sati ɗaya muka shirya muka koma makaranta .




*yawan comment yawan typing ba zan sake yi maku complaining ba yanda kukayi nima haka zanyi insha Allah🥴*




Share
Comment
And
Vote



*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 35⏩36






Tunda muka koma makaranta muka sa karatu a gaba ba kama hannun yaro, dan nima na ture komai na jindadin duniya nasa karatuna gaba, dan yanzun an sake man course an maidoni microbiology 100 level, tabbas hakan ya sosa man zuciya amman na barma Allah kuma nasa a raina kaddara rata ce tazo man haka, kuma na manta da baya nasa gaba ina rokan Allah ya bani sa'a da nasara a gabana albarkacin Annabi Muhammad S. A. W, bani da ƙawa sannan kuma bani kula kowa duk da samarin suna yi man magana amman bani kulasu dan na barma Allah zaɓi kuma ina addu'a.


watarana ina zaune Dejja ta shigo tace "Aunty Auta yaushe zamuje kasuwa wai? Naga kayan miyarmu duk sun kare amman baki ce komai ba." kallonta nayi sannnan nace "wallahi Dejja ina sane, amman bansan shiga cikin gari dan ni tsoran mutanen kano nikeyi." Murmushi tayi sannan tace "Allah yana tare dake Aunty Auta dan Allah tunda yau bamu da komai tashi mu tafi mu je kasuwa pls." kallonta nayi sannan nace "amman Dejja baki gani... "Haba Aunty Auta dan Allah ki karkiyi gardama ki tashi mu tafi ko mundawo." ba dan naso ba na tashi mu duka ba wata kwaliya mukayi ba poder ce kawai muka shafa sai dan lipstick sannan muka saka dogayen ruguna muka mukayi rolling muka tafi kasuwa.



Tunda muka fito gabana yake faduwa, tun ina hakuri har yakai da na kasa nayi, sai da nayi ma Dejja magana nace "wallahi Dejja bakiji yanda gabana yake faduwa ba, ji nike kamar wani abu yana shirin faruwa dani fa." Murmushi tayi sannan tace "kiyi addu'a Aunty kuma insha Allah ba abunda zai faru dake sai alkhari.".... "Allah yasa." nace mata sannan muka cigaba da labari, ji nayi tace "wai kinsan Dr Umar yana sonki kuwa."? Sosai na tsorata kuma gabana ya kara faduwa sosai cikin tsoro nace mata "na shiga ukuna, wane Dr Umar din."!? Lura da yanayin da nike yasa tayi dariya sannan tace "haba Dan Allah Aunty Auta sai kace wanda aka gaya ma sakon mutuwa, Dr Umar na depertment dinku shi ya gayama registra yana sonki kuma aurenki yake so yayi shine ya gaya mashi abunda ya faru dake, amman yace yaji a haka yake sonki, shine jiya da yazo wajena yake gaya man wai Dr Umar ya matsa mashi shidai zai bashi number dinki, amman nace kina da wanda zaki aura sai yace ai matar mutum kabarinsa idan Allah yasa Dr ne ba yanda za'ayi kinji yanda mukayi." numfashi na sauke sannan nace "ya kike ganin za'ayi kenan Dejja."? Ceman tayi "ki bashi dama kawai, mu cigaba da addu'a Allah ya tabbatar da abunda yafi zama alkhari.".... "Amin ya Allah." daga nan bance komai ba, shiru mu duka mukayi kowa da abunda yake saƙawa a zuciyarshi har muka iso kasuwa.



Tunda muka iso kasuwa nike jin kaina wata iri, dan ba abunda yake man dadi amman kawai tafiya nike haka muka kama shiga shaguna muna sayaiya amman da an kalleni ansan ina cikin damuwa sosai, kuma ban san abunda yake damuna ba, addu'a kawai na cigaba da yi dan itace tafi dacewa dani a wannan lokacin da nike ganin shine daidai.


Har mun gama yin abunda ya kawo mu Dejja tace ita dole sai na raka ta wani shago ta saya turare naso nayi mata gardama amman kuma sai na hakura nace mata mu tafi, tafiya mukayi mai dan nisa kadan sannan muka iso shagon muka shiga muka fara tambayar turaren da ya kawo mu, ji nayi ance "Alhmdulillahi Khadija ashe zan kara ganinki a rayuwata? Allah nagode maka da ka maido man da Khadija a lokacin da nike bukatar a tare dani." a tare muka jiyo nida Dejja kayan hannun na saki ina kallonshi na kasa motsin komai, cikin fushi da zafin nama Dejja ta ture ta maidani bayanta sannna ta kalleshi tace....




*wata sabuwa kuma shin waye Auta ta gani a kasuwa, sannan ga kuma Dr Umar nan ya kutso kai a rayuwar Auta 🥴*




Share
Comment
And
Vote





*A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t


*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 37⏩38


Wani banzan kallo tayi mashi sannan tace. "Kai ɗin banza kai ɗin wofi, wallahi wallahi cikinka uwarka bata ɗauka ba balle har ta haifoka a cikin duniyarnan, idan da kayi nasara akan Aunty Auta to ka sani Nurandeen yanzun ba zaka taɓa yin nasara ba a kanta, abunda nike son kasani shine wata shara'a sai a lahira to kasani wani abun da kayi mata sai ranar Allah zai ansar mata da haƙinta." tana gama faɗin haka ta fisge hannu muka fito shagon turaren da bamu saya ba kenan, dan ko ni ba abunda nike sai kuka dan ganin da nayi ma Nurandeen ya tuno man da abubuwa da dama wanda bani fatan sake tunasu a rayuwata, tsaye muka barshi kamar gunki ba abunda yake sai hawaye, kallona Dejja tayi sannan tace “Aunty Auta idan na fahimta har yanzun son wannan tsananen dan'iska mazinaci kuma fasiki yana cikin zuciyarki ko? To wallahi tun wuri kiyi ma kanki fighting, dan ba wanda zaiyi maki wallahi ko kuma ki sani mudun kika ce zaki sake kulashi to wannan karan ba zan maku ido ba Baba kawai zan kira waya na gaya mashi kin sake komawa ruwa sai su san abun yi, dan na tabbata mudun Nurandeen ya dawo cikin rayuwarki ida lalata maki rayuwa zaiyi ya kama gabanshi ya barki da kuka, amman ki sani wannan karan kikayi kuka ba wanda zai saurareki sannan ba wanda zaiji tausayinki sai ma tsanarki da za'ayi, abunda zai baki mamaki shine cikin mutane masu tsanarki nice kan gaba wallahi wallahi wallahi Aunty Auta nayi rantsuwa mudun kika koma ma wannan bunshunrun bani ba dake har gaban da abada wallahi ko."




Da sauri na ɗago kai na ina kallonta dan furincinta ya bani mamaki da al'ajabi sosai gami da ban tsoro, wai ni Dejja take cewa bata bani har abada saboda wani soko banza wanda a faɗin duniya bani da maƙiyi kamarshi wanda ko fuskarshi bani son sake gani a rayuwata, da ace nasan zanga Nurandeen a cikin kasuwa da ba abunda zai kawoni cikinta dan babu amfanin zuwan nawa, amman ace kamar ni ina ƙanwar ubanta take gaya man magana haka san ranta nima cikin fushi nace. “ban san iskanci da shirme fa Dejja, wai shin na tambayeki mana? Kin fini tsanar Nurandeen a rayuwa? Ko kuma kin fini jin zafin rabani da budurcina da yayi? Ko kuma kin fini jin ciwon yaudarata da yayi? Sannan kin fini jin ciwon maidoni baya a akayi a makaranta duk A SANADIYAR SOYAYYAR SHAN MINTIN DA NAYI DA NURANDEEN? ko ɗaya baki fini ba Dejja, asali ma ni har na mutu na koma ga ubangijina Allah ba zan manta da wannan abubuwan ba a rayuwata kuma ba zan daina kuka ba koda kuwa kukan zuci ne Dejja." kuka na ƙara fashewa dashi sannan na cigaba da cewa. “wallahi wallahi Dejja da ace yau ni Khadija Bello ina yawo da wuƙa a cikin jikka to wallahi a yau ɗinan sai na lumama Nurandeen ita a ƙahon zuciya sai dai nima a kasheni idan na kashe shi, kinsan kukan mai nikeyi ne Dejja."? Itama hawaye take ta girgiza man kai kawai dan Dejja ta fini saurin daukar fushi da zuciya shiyasa ta kasa magana, Murmushi nayi mai ciwo sannan nace. “ina kukan baƙin ciki ne yau naga maƙiyina wanda nafi tsana a duniya wanda nike fatan Allah ya haɗani da shi na dauki fansar abunda yayi man, burina akan Nurandeen shine na zama a jalinshi Dejja kuma wallahi insha Allah ni Khadija Bello sai na zama a jalin Nurandeen, ina mashi fatan haduwata ta biyu dashi lokacin zai baƙunci lahira wannan kuɗirina ne, dan ni bani auren kowa tsakanin Aminu da Dr Umar, dan ban dace dasu ba banda abunda zanyi taƙama dashi a gidan miji Nurandeen ya ansheshi cikin dubara ba tare da na fargaba, Dejja tabbas A SANADIN SOYAYYAR MINTI NA ƁATA RAYUWATA😭, rayuwata bata da amfani dan bani iya auren wani ban kai mashi budurcina ba hakan na iya sa zuciyata ta bugu, kinga kenan banda amfani a duniya mutuwa ce tafi dacewa dani dan haka zan kashe Nurandeen sannann na kai ƙaina a hukuma nima daga ƙarshe a kasheni hakan shine dai dai kuma haka shi yafi dacewa dani Khadija Bello."


Kuka Dejja ta fashe dashi tana girgiza man kai dan tasan ni sarai

Please Login or Register in order to submit comment